GIMBIYA SA’ADIYA
CHAPTER 18
Tun da gariya waye kuyangun Salbiyya ke kai kawo a bangarenta. Masu gyare-gyare suna yi, masu girke-girke ma suna yi. Zuwan Zabbau wurin bai sa hankalinsu ya karkata gare ta ba, wanda dama hakan take so. Cikin alama ta yafito daya daga cikin kunyangun signal da ida sannan ta bar farfajalar. Ta tafi da kusan mintuna ashirin sannan waccen kuyangar mai suna Tabawa tabi bayan Zabbau zuwa bangaren Kursiyya.
Bayan ta isa ta zubekasa, Kursiyya ta saki murmushin mugunta, sannan tace,
“Shiya sa nake masifarkaunarki Tabawa. Kanki yanaja. Zabbau tace dani alama kawai tayi miki’ kika gane. Haka ne?”
Cikinjin dadin Kumyya ta yabe ta ta daga kai, ”Haka ne ranki shi dade.” “Dakyau to. Kuna ta aikin tarbar Uwargijiyarku k0?“ Nan ma daga kai tayi. “Yayikyau. Akwai sauran wannan garin k0 ya kare?” Sai da Tabawa ta danyi shiru jim, tana nazari sannan ta ce, “Nake ga akwai sauran kadan dai babu yawa.”
“Toki tabbalar kinyi duk abin da ya dace. So nake da zarar sun iso yau, gobe suyi ra,ayin tafiya. Idan harhakan ta kasance, ni kadai na san kyautarki. Zan ninka miki ta wancan karon.’
Washe baki Tabawa tayi cike da farin ciki.
”Ahh ai ranki shi dade ki riya a ranki gobe-goben nan zasu koma daga inda suka fito. Ni kam wai nace, ranki shi dade, mezai hana ayi aikin da za a dauwamar dasu can inda suke?”
Shiru ta yi sanadiyyar tsawar da Kursiyya ta daka mata.
“Ke har kin isa ki fada mini yadda zan yi?” Cike da tsore dagirmamawa Tabawa ta haujinjina hannu, kanta sunkuye tana fadin,
“Ayi hakuri ranki shi dade. Ayi mini gafara ba zan kuma yi miki shisshigi ba.”
“Tashiki tafi Ki tabbatar da kinyi abin da na sakaki. Idan abin nan ya tabbata kuma zan cika alkawarin dana daukar miki.”
Da sauri Tabawa ta mke,
“Godiya nake yi Fulani. ”
Ta bardakin. Sadda jirgin su Adnan ya sauka sun samu dreba da jeep yana jiran su. Shi ya taimaka musu suka kwasa kayayyakinsu, aka saka a motar sannan suka bar airport din, motoci biyu gaba
biyu bayansu. Bakidaya gidan ya dau haramar tarbarsu Adnan, wanda duk sun samu labarin’ cewa har jirginsu ya sauka, suna dafda zu wa gida.
Sa’adiyya tayi wanka, ta shirya cikin farar shadda mara starch, wacce aka ma surfani kalar baki. Ta matsa jikin madubi ta fara kokarin daurin dankwali, daya daga cikin abubuwan da bata iya be kenan. Dan dama ko kwalllyar fuska ba damun ta tayi ba, hakan tasa ma ba ta iya ba. Saukinta daya tana da kyau, haskenta natural ne, komai na fuskarzaune yake das. Ta daula dankwalin ya kai sau biyar duk babu kyau. A karshe ta cire tajefar, tajawo hular turban kawai ta saka.
”Ina ma ace su Yaya Adnan za su soni? Sai in ga kamar donni’ suke tafiya. Allah na rokeka kasa Inga canji a wannan karan. Allah kasa sun dawo ke nan ba zasu koma ba.”
Sai kuma taji saukar hawaye a kumcinta. “Ke!
Taji an fada cikin murya mai cike da izgilanci da lsa na rainin wayo. Tajuyo ta kalli mai kiran ta taje din. Zabbau ce ta ganidauke da kaya a hannunta tana tabe baki.
“Ungo wannan kayan inji Fulani. Tace ki saka su kuyi anko da Gimbiya Hafsa.”
Kallo Sa’adiyya tabi Zabbau da shi. Tana ganin yadda Zabbaun ke watsa mata harara cike
da tsana’. “Na riga na saka wasu.” Tayi karfin halin fada a takaice. Mamaki sosai taba Zabbau.
“To yanzu me kike nufi?” “Ba zan saka ba. ” Haba Zabbau ta tallabe idanuwanta waje tana jin tsantsar mamakin Sa’adiyya. “A mayar mata kike nufi?” ”ehh.”
Zabbau ta gyada kai hade da yin kwafa. A ranta tana mamakin yadda idon Sa’adiyya ya
bude a Iokaci guda har take iya mayar da magana. Amma tana ganin Iaifin Kursiyya ne, sakar mata fuskar nan da tayi ne yasa ta fara raina ta. Wato don dan sarkin Kubaisu ya zabeta a matsayin wacce zai aura ne yasa har idanuwanta sunyi budewar da zata fara
mayar da magana? Ta kara yinkwafa, a fusace ta yayi kayan ta bardakin. Sa’adiyya ta dage kafada alamun ko’inkula. A ranta tace hakan ne daidai dake. “Sannan kuma…” Zabbau tajuyo tana sauraren abin da Sa’adiyya za ta fada. “Ba sunana keba. Za ki iya ce min Sa’adiyya sunan da Abbana yake kirana da shi. Ko kuma Halimatu, kamar yadda Talle da Audi ke kira na. ”
Ta saki murmushin gefen baki. A wannan karab Zabbau ta gama karewa da al’ajabin Sa’adiyya. Diyar ta iya furta, Kalamai
“Kina nufin su Fulani Kursiyya ne Talle da Audi?”
K0 qala Sa’adiyya ba takara furtawa ba ta cigaba da harkargabanta. Turarurruka kawai take fesawa kala kala masu daddadan kamshi.
Cikin takaici Zabbau ta bardakin. Kai tsaye ta nufi bangaren Kursiyya. Murmushin takaici tayi bayan ta ajje kayan a kusa da Kursiyya.
”Ranki shi dade, kin ga wasan da kike yi da yarinyar nan yana neman saka wa ta raina ki k0?”
“Ki daina daga murya a saman kaina Zabbau. Kin san bana so.” Wani irin kallo tama Kursiyya. irin ta bata haushi amma bata da yadda za tayi da ita.
“Bana son ana kura mini ido, kin sani sarai. Kuma ki fada mini abin da ya faru ba nason tsawaita zance.‘
Zabbau ta kwashe abin da akayi da wanda ba a yi ba duk ta fada wa Kursiyya. A karshe tace,
”Gaskiya Fulaniya kamata kidaukar ma yarinyar nan mataki. Rainin wayan ya isa haka nan… “Ya isa ” Kursiyya ta furta da murmushi kunshe a fuskarta.
“Sai me don ta fara raina ni? Karki manta da batun mu da Boka Fartsi. Kwana nawa yayi mata saura? Dole ne na lallaba Halimatu ko ina so ko bana so, matukar
muna son Cikar burinmu. K0 kin manta cewa da kafafuwanta boka yace mu kaita?” Kai sunkuye Zabbau tace, “Haka ne kam.”
“To kin gani? Dole mujure komai zaijeya dawo. A karsheza mu washe baki, ina mai baki wannan tabbacin. Ki daure kiyi hakuri kamar yadda nidin ma nayi.”
Zabbau tayi murmushi bayan ta dago kanta.
”Tabbas wannan maganar haka take. Halima ki saurari karshenki, domin kuwa ba zaiyi kyau ba.”
Karar kararrawar dake bugawa ne ya dakatar dasu daga hirar da sukeyi. “Sun iso kenan?” Kursuyya ta furta hade da karkace kanta. “Babu makawa su ne. ” “Tashi kije.” Zabbau ta mike hade da barin dakin.
Kusan duk al’ummar masarautar bakunansu a bude suke sanadiyyar isowar su Uwargida Salbiyya. Daga masu zubewa kasa suna kwasar gaisuwa sai masu rusuna wa da murmushi a saman fuskokinsu. Wasu daga cikin kuyangun Salbiyya na fadin, “Ranki shi dade barkanku da zuwa. Allah dai ya sa kun dawo ke nan.” Salbiyya tayi murmushi, cike da soyayya a saman fuskarta tace, “Hakan nake tunanin in sha Allahu. Kunji dadin dawawar tawa ne?” Har hada baki sukeyi wurin amsa mata. “ “Kar ku damu. Na dawo kenan ba zan sake barin ku ba.”
Da haka har suka isa bangaren ta, jama ’a da yawa biye da su. Tsaf-tsaf ta samu dakin nata, ga sassanyan kamshi na fita da sanyin AC suna ratsa hancinta. ‘Gida mai dadi.’ Ta riya a ranta.
“Naji dadin ganin dukkaninku. Ya kuke ya bayan rabuwa?” Hajjo ta ce, “Komai lafiya ranki shi dade. Wallahi ba kiji yadda nakejin dadi ba. Tamkar in dauke ki in goya haka nakeji. Don Allah kar ki sake barinmu.” Salbiyya ta kama hannun Hajjo, “Ba zan barku ba Hajara. Ina alfahari daku duka, inajinjina yadda kuke kaunata, kuke son kasancewa tare dani a koda yaushe.”
Raha sosai suke yi a tsakaninsu. Sai dai duk abin nan dake faruwa Tabawa na kalIon inda Salbiyya ta zauna, tana fatan ta tashi daga nan ta koma kan kujerar da ta saba zama duk sadda take nan.
Sai bayan ishai Salbiyya ta samu jama’ar nata suka tartafi, ba wai dan sun gaji da gaisawa da ita ba, sai don suna so ta samu ta huta, kafin ta isa farfajiyar mai martaba.
Cike dajin haushi Tabawa ma ta tafi. Sai dai tayi alwashin duk ma yadda za tayi sai tabi don ganin Salbiyya ta zauna bisa kujerar nan tata, ko don ta samu kyakkyawar kyautar da Kursiyya ta mata akawari.
Wanka ta sake yi ta feshe jikinta da turarukan oud, a daidai lokacin Kursiyya da Hafsa suka shigo.
Hmm