GIMBIYA SA’ADIYA
CHAPTER 27
A hankali Cikin sanyin murya mai martaba ya karbi lasifika, bayan yayi gyaran murya sannan yace, “Da farko dai ina mai ba al’ummar wannan masarauta hakuri bisa ga wannan al ‘amari da yake faruwa. Sannan bayan nan, Ina mai umurtar kowa da yanzu yanzun nan idan mun tashi daga nan kowa ya watse, ya cigaba da harkargabanshi. Sannan magana ta karshe, ba na sonjin duk wasu kananan maganganu don Allah, idan har naji kuwa zan zantar da hukunci mai tsanani ga duk wanda na kama, ko kuma naji Iabarin wata magana ta fito daga bakinshi.” Ya ajje sifukar. Da sauri dogarawa suka iso gare shi, suka zagaye shiya mike tare da bin bayanshi suka isa farfajiyarshi.
Da sauri Asiya da Dago suka iso ga Salbiyya, isowarsu tayi daidaida isowar Adnan da Anwar. Su duka hudun suka hau kanta, suna ambatarbsunanta. “Goggoji.”Amma babu ko alamun motsi a tattare da ita. Adnan ya runtse idanuwanshi yanajin wasu irin zafafan hawaye na kwaranya. Kunyata Salbiyya da aka yi a wurin kadaiya ishe su, to kuma saiga wannan sumar da tayi, kuma mai martaba ya nuna halin ko ‘inkula a gare ta. Da iya karfinshi ya ciccibe ta, yana tafiya suna biye da shi har suka isa bangarenta. A bisa gado ya dire ta. Anwar kuma ya nufu deep freezer dinta ya dauko ruwa mai sanyi, a hankali suka hau yayyafa mata har suka yi nasarar farfadowarta.
Nannauyar ajiyarzuciya ta sauke wanda yayi daidai da saukar ruwan hawayenta mai tsananin gumi. Ta hau gyada kanta bayan ta runtse idanuwan, “Wallahi sharri Tabawa tayi mini.” Shi ne kadai abin da ta iya furtawa.
Cikin kuka Asiya tace, “Duk wanda yaso gaskiya ya san kazafi aka yi miki Goggoji. Wanda duk ya dauki al’amarin nan a matsayin gaskiya to ya sone. Domin kuwa a bayyane komai yake. Babu komai, akwai AlIah.”
Dago ta share kwallarta, ta ce, “maganarki gaskia ce Asiya. Duk zantukan nan da Tabawa ta fada ya faru nega Kursiyya. Domin kuwa ba zan taba mantawa ba ta taba nemana da aikata mummunan aikiga Goggoji. Allah ya sani, kuma shizaizama shaidata, bana taba tunanin akwai ranar da za a hada baki dani a cuci Goggoji. Tayi min gatan da har in koma ga mahaliccina ba zan taba mantawa da ita ba. Ba kuma ni kadai ba, da dama ma daga Cikin mutanen masarautar nan. Dagajin komai an san tsari ne. Allah baya gyangyadi, yana sane da dukkanin komai.” ’
Har sannan Salbiyya idanuwanta a runtse suke. Damuwa kunshe a kasan ruhinta. Tana jin karar taku, kamshin turarensa ya daki hancin ta ta yi saurin bude idonta, ta dora suga mai martaba da fuskarshi ko kadan babu annuri a cikin ta. Da sauri Asiya da Dago suka fice, suka bar Adnan da Anwar gaban mahaifiyarsu kowanne damuwa fal a fuskarshi.
Bayan ya nemi wuri ya zauna, ya dan tauni Iebonsa kafin a hankali yace, “Salbiyya kin ga yadda reshe kejuyewa da mujiya k0?”
Ta bude nannauyan idanuwanta ta kalle shi. Sam bata yi mamakin kalaminshi ba, sai dai ta
tsura masa Idanuwa tana son sanin madosar kalaman nashi.
“Ba mutuncin Kursiyya kadai kika so kici ba, nawa mutuncin kika so ci. Yau kin nunar wa mutane cewa ni ban isa da gidana ba. Kin bayyana musu cewa ba ki dauke ni a bakin komai ba, tun da ba zaki iya tinkara ta da damuwarki ba har sai kin hada taron gaggawa.”
Da karfi ta matse idanuwanta, sauran dan hawayen da suka rage suka karisa tsiyayowa,
labbanta na rawa ta furta “Amma mai martaba…”
“Kar kice mini komai Salbiyya. Ba ki da bakin da zaki kare kanki. Kursiyya kuwa kainuwa ce dashen Allah. Wanda dukya nemija da ita sai dai shiya kwana ciki. Kin gani dana Hausawa sun ce idan zaka gina ramin mugunta ka gina shi dan karami, gudun karkai ka afka a cikinsa.”
Taso ta daure a wannan gabar, ta so ta kwakkwafi zuciyarta, taso .ace bakinta karya motsa, sai dai ta kasa, ba tajin zata iya daure wa kalaman mai martaba masu tsanann daci, cikin bacin rai tace, “Gaskiya mai martaba kabani mamaki. Kalaman da suke fitowa daga bakinka sun daure min kai. Ya da girmanka zaka rinka abu babu tunani? Meyasa ba zaka yi bincike ba kai tsaye ka zantar da hukunci? Adalci bai ce haka ba. Ba ka aikata abin da ya dace ba. Kana neman yanke hukunci a cikin duhu, irin wanda addininmu ya hane mu. Kana neman tafka babbar dana sani wacce za ka dade kana nazartar ta. ”
Cike da mamaki yake kallon ta. “Salbiyya, yau ni ne kike dakawa tsawa haka? Ni ne kike
jifa da wannan munanan kalaman?”
Shiru tayi ba tace komai ba sai sauke ajiyar zuciya da take yi. Tana kallon shiya taka ya bar dakin damuwa bayyane a saman fuskarshi.
Kaman ance ya fita ta kuma barkewa da wani kukan. Adnan da Anwar da kamar an dasu su suka yi saurin share mata kwallarta. “Goggo kiyi hakuri ki daina kukan nan. Da izinin Allah
gaskiya zata bayyana. Allah yana ganin kowa da kuma komai.”
Ta gyada kanta, ‘abwar kenan. Yanzu har kana tunanin akwai ranarda kuskuren Kursiyya
zai fito? Akwai ranar da asirinta zai tonu kowa ya gane halinta?” Murmushin takaici Adnan yayi, “K0 ba dade k0 bajima akwai ranar da kaidinta zaiyanke. Kullinta ya Ialace. Asirinta ya tonu. Rayuwarta ta gurguntaka daga ita har magoya bayanta. Addu’a itace tamu, karmu gajiya duk runtsi duk wuya. Shiya sa tun sadda kika ce za ki hada taron nan na hana ki, don na san makirci da kulle kullen masarautar nan. Gashi nan kuwa, kinaji kina gani an juyar da komaiya dawo gare ki.”
Daga haka suka cigaba da rarrashin mahaifiyarsu har suka yi nasara tayi shiru. A nan suka cigaba da zama tare da ita har dare ya yi sannan suka tafi. Suna tafiya suka ci karo da Kursiyya da Zabbau sun dawo daga wurin boka Fartsi. Ko kallon su ba suyi ba. Kursiyya ta saki murmushin zalunci sannan suka nufi bangarenta.
“Zabbau kin ga dole sai an samu naman tattabara an hada da wannan maganin. Saboda haka aikin ba zaiyiwu yau kadai ba, tun da dai maimartaba a dakina yake. Amma ban sani ba k0 zaki iya
Zabbau ta kalli Kursiyya da murmushi a fuskarta, “Me zai hana ni iyawa ranki shi dade? Ki
bani umurni kawai, yau-yau din nan mai martaba zai sallame ta ita da kodaddun yaran can nata.”
A cikin daren Zabbau ta aikata duk abin da boka Fartsiya umurce su. Tayi riarfesun tattabara hade da maganin. Tattabarar ma sai da aka murde mata wuya sannan aka fige aka dafa. Da murmushinta ta iso dakin Kursiyya. Bata tsammani iske ta a daidai Iokacin ba, amma tana zuwa ta same ta zaune da waya a hannunta. Ta rusuna girmamawa hade da mika mata ‘yarlangar farfesun. Kursiyya ta karba da murmushi kunshe a saman fuskarta. “Shiya sa nake dada kaunarki a kodayaushe Zabbau. Sannu da kokari. ”
“Nakanji dadi a duk sadda zan saka ki farin ciki. Ina mai miki albishiri da cewa Salbiyya ba
zata kwana a gidan nan ba. Ki karisa aikin, ni zanje inci abinci.”
Kursiyya ta karbi Iangar, “K0 a haka fa mai martaba ranshi a bace yake sosai, to ina ga an kammala wannan aikin? Tsananin bacin rai har niyau ban samu sakin fuska na sosai daga wurinshi ba. Shiya sa ma na fasa kwana a turakarshi.”
“Haka nake sonji uwargijiyata. Bari in tafi Sai munji Iabari.”
Zabbau na ficewa Kursiyya ta dauki langar farfesun ta shiga asurtaccen bandakin nan nata, tana shiga ta jawo shi ta rufe. Ta dauki tsawon lokaci kafin ta fito sai hada zufa take yi. Kimanin mintiashirin da zamanta ta dan farajiyo hayaniya sama-sama. Ko data saurara sai tajiyo muryoyin Anwar da Adnan da kuma kukan Salbiyya. A hankali ta rangada guda. Cikin farin ciki “Yau dai burina ya gama cika. Su Salbiyya za a yi tafiyar har abada.” Ta mike a bisa kafafu wanta. Mayafi ta yafa hade da ficewa daga dakin. A daidai kofa taci kara da Zabbau data taho da sassarfa don ta shaida mata halin da ake ciki.
Hannu taba Zabbau suka kashe da karfi, sannan suka kallijuna da murmushi a saman
Fuskokinsu. Tun daga nesa Kursiyya ke fadin “Lafiya nake tajin hayaniya? Me yake Ihruwa ne?”
Tana kallon yadda Salbiyya ke kuka sosai tamkar ranta zai fita. “Kiyi shiru Goggo. Allah ba azzalumin bayinsa bane. Kuma ba dole sai a cikin gidan nan bane zamu iya cigaba da rayuwa ba Don ya kore mu bashi bane zaizama karshen numfashinmu ba. Babu komai. Muje gidan su Abdul mu kwana, gobe da sassafe mu koma inda muka fito. Ni dama can nafi
jin dadin rayuwata a can. Zama a cikin kasar nan ba komai bane ba face zallar tashin hankali.”
Anwar ya dafaa kafadar Adnan, “Gaskiya ne dan uwana. Kuma Goggo ki gode wa Allah daya baki mu. Inda ace baki da mu shine za kiyi kuka. In shaa Allahu mu zamu share miki wannan hawayen naki. Zamu mantar dake duk wata rayuwa ta cikin wannan kasar mai cike da kunci da radadin zuciya. ” A hankaliya taka ya isa gaban Kursiyya dake ta binsu da kallo. Ya mata kallon sama da kasa sannan yace, “Fulani, ga masarautar Bilbah nan mun bar miki, ki cigaba dacin duniyarki yadda kike so. Sai dai ina so ki sani, akwai ranar kin dillanci. Sannan ki tuna, akwai mutuwa akwai hisabi. Akwai wuta akwai aljannah. Sannan kuma, tsafinki zai kare k0 ba dade ko bajima. Ga sako ki fadawa Abba. Don Allah duk ranar da asirin da kika masa
karye, ya dawo cikin hayyacinsa, ki shaida masa injimu mun yi dana sanin fitowa daga tsatsonshi. Tsatson da asiri ke saurin yin tasirigare shi. Sannan duk daren dadewa karya neme mu. Kamar yadda ya kore mu tare da mahaifiyarmu, mun tafi harabada babu mu babu shi. Barin masarautar nan ya fiye mana a kan zama a nan, irin rayuwar da Gimbiya sa’adiyya tayi. A haka yarinyar nan ta mutu cike da takaici.
Yana gama fadin haka ya koma ga Salblyya da dan uwanshi. Basu ko tsaya daukar kaya ba kawai suka yi ficewarsu.
Sosai ran Kursiyya ya sosu da kalaman da Anwar ya fada mata. Sai dai komaiya zo da sauki tun da dai tafiya zasu yi kwata-kwata su bargidan. Takaicin nata dai da a gaban al’umma sosai yayi maganar. Sai kowa suke ta kallon-kallo. Sum-sum-sum ta bar wurin Zabbau biye da ita. Zukatansu cike dajin dadi.
Cikin sanyin jlki ya Iatsa kiran Sarki Sani. A ranshi yana tunanm sam bai kyauta mishl ba. Zai dauke shi tamkar ya yi mishi karanta. Ya saka tafin hannunshi na dama ya gage zufar da
ta tsattsafo bisa goshinshi.
Jin Sarki Sani ya daga wayar da sallama kunshe a bakinshi yasa shi sauke nannauyar Ajiyar zuciya, wacce shi kanshi Sarki Sanin sai da ya tsorata. Sarki Abdurrahmanu ya amsa
sallanar tare da kirkiro guntun murmushi. “Mai’martaba barka da wannan lokaci. ” Da fara,a sosai Sarki Saniyace, “Barkanmu aminina. Da fatan Iyali kowa Iafiya.”
“Kowa lafiya Iau ranka ya dade. Wani mummunan Iabari ne kunshe a bakina. Ina fatan ba za ka dauki hakan a bakin komai ba, kar kayi mini kallon wani mutumi wanda ya saba maka alkawari… ”
Da sauri Sarki Saniya tari numfashinshi. “Don AlIah ka tofar da yawunka mai martaba. Baka da wani abu da zai faru wanda zai sa na maka wannan kallon. Tunma kafin ka fadi k0
me ka kira ni domin shi, na yafe maka wallahi da zuciya daya.” ‘
Sarkin Kubaisu ya gyada kanshi. “Na gode sosai aminina. Game da auratayyar da zamu hada ne tsakanin yaran nan. Kasan kana naka Allah na nashi. Sannan kuma yaron yanzu ba shi da tabbas. Kanaji kana gani yake bada maka kasa a idanuwa. Mun zauna ni da Abu Sufyanu, babu yadda ban yi dashi ba game da auren Hafsatu amma ya kekashe kasa ya kiye mini. Wallahi ba karamin kunyata ni ya yiba. Yau kwana biyu ke kan ina tunanin ta yadda zan tinkare ka da maganar amma na kasa. To kuma dai bani da wani zabin daya wuce in fada maka din. Shi yasa na daure nake fada maka. Amma…”
“Kar kaji komai aminina. Dan Yerima Abu Sufyan yace baya son Hafsa k0 kadan ba zan ga Iaifinshi ba, Abun dubawa shi ne, yaron nan yayi ladabi da farko, ya amince ma auren Gimbiya Sa’adiyya duk da cewa hada su aka yi. Bai kiba, ya aminta har aka saka musu rana, Allah bai nufi abin ba ta tafi gidanta na gaskiya. Ke nan sai mu dubi alkhairinsa na baya, muyi masa uzuri a wannan karon, domin kuwa dan adam ajizi ne. Ba mu isa mu yi masa dole ba. Sai mu dage dayi musu addua daga shi har ita din, Allah yaba su abokan zama nagari.”
Wani irin farin ciki Sarkin Kubaisu yajiya mamaye zuciyarshi. Dama yasan amininshi mai fahimta ne, zai fahimce shi. Kawai daiyaji nauyi ne na tinkararshi da zancen, a ganinshi
babban abun kunya ne.
“Ganin haka yasa na rantse sai na hada zuria da kai. Na nemi ta jin Yerima Bukar, kuma ya amince zai aure ta. Sai dai ban saniba a bangarenka, da daman yaran sarauta ba,a cika hada su zama da kishiya ba. Ga shi shi kuma yana da mata. Ya kake gani?”
Bayyanannen murmushi Sarki Saniyayi, “Wannan mai sauki ne ranka ya dade. Hafsa yarka
ce. Duk hukuncin da zaka yanke a kanta ba zan tabaja dashi ba. Ka aurar da Hafsa ga duk
wanda kaga dama sam bazan ga aibunka ba. Yadda take ‘yata haka take ‘yarka. Ka fitar da ranar da za kuzo daurin aure. ”
Tun daga wannan maganar da Sarki Sani ya yi sai suka koma tattauna batun daurin aure.
Suka tsayar da rana nan da mako daya za a daura sannan suka yanke wayoyin.
Sarki Sani ya dafe kanshi, Yana tuna alkawarinsa da Kursiyya kan nema wa Hafsa auren
Yerima Abu Sufyan. Bai ma san ta inda zai bullo ma al,amarin ba.
Haka kawai wata zuciyar ta kitsa masa kawaiya yi shiru da bakinshi karya fada musu ainahin wanda zai aura ma Hafsa. Sai bayan anyi auren ta ga ko waye, ai dai ba ta isa tace bata son shi ba, saboda matsawar da Kursiyya tayi sai anyi auren. Sai kuma yaji sam bai kyauta ba idan yayi haka. Ya zama karamin mutum. K0 ma daiyaya ne Hafsa ‘yarshi ce.
Yana da damar tilasta mata idan ta bijire. Ya zabga tagumi yana tunanin mafita. A take Gimbiya Sa’adiyya ta fado mishi a rai Idan ita ce ya tabbata ba zata ki maganarshi ba, za ta
karba da hannu bibbiyu duk kuwa yadda bata son abun. Amma ga Hafsa shakkun ma
tinkaran ta da batun yake yi. A karshe daiya tsayar ma zuciyarsa cewa ba zai fada mata ko waye zata aura ba. Zaiyi shiru kawai a matsayin Yerima Abu Sufyan ne angonta, har sai an
daura aure sannan zata sani, daga ita har Kursiyyar.
Hannunshi na dama yasa ya share ruwan hawayen dake sauka bisa kumatunshi. Tun sadda abin ya faru ya shiga tsananin damuwa. Sosai mahaifinshiya canza mishi. Idan ma ya gaishe shi kasa-kasa yake amsa wa. Yaga yadda suka kulle sosai da Yerima Bukar har
suna wasa da dariya, sabanin da, da k0 gaisuwarshi sai yaga dama yake amsa wa.
Yana cikin wannan dogon tunanin Fulani Maryama ta shigo dakinshi cikin shiga ta alfarma. Ta yi sallama kusan sau uku amma Yerima Abu Sufyan sam bai san tana yi ba. A karshe ta
shigo dakin kawai ta nemi wuri ta zauna.
A hankali ta bubbuga mishi kafada, ya dago kanshiya kalle ta. Runtse idanuwanshiya yi, sauran hawayen da suka rage suka karisa saukowa.
“Yerimana.” Ta furta cikin sanyin murya, tana kallon yadda idanuwanshi suka rine tsabar kuka.
“Ka mika dukkanin lamurranka ga Allah. Ka kai kokenka wurinshi, shi kadai zai fitar da kai. Ka cire damuwa daga zuciyarka gudun kar ka illata.” Ta sake kwantar da murya, “Ina
kaunarka, kuma har abada ba zan taba gudunka ba.”
Ya gyada kanshi, wasu hawayen na kuma sauka. “Fulani ya zan yi da rayuwata? Ya zan yi idan maimartaba bai daina fushi da niba.?”
“Hakuri.” Ta fada tana kallan shi. “Hakuri shine magani Yerima. Lokaci na zuwa da komai zaizamto tamkar ba ayi ba.”
“Fulani, zuciyata tana zafi a duk Iokacin da na je gaishe da maimartaba yaki kulani kuma naga ya mayar da hankalinshiga Yaya Bukan Ba zanjurigani ba, na yanke shawarar barin kasar nan, zan koma Italy in cigaba da karatuna kamaryadda na tsara daga farko.”
Zaro idanuwa Fulani Maryama ta yi. “Yanzu Yerima saboda wannan abun ne zaka tafi ka bar ni? Me yasa kake son nisanta kanka da ni bayan irin kaunar da nake maka? Haba Yerimana. ”
Yayi kneel down cikin kuka yace, “Ki gafarta min Fulani. Don Allah ki yarje min in tafi ko zan samu sassauci a zuciyata. Abun biyu ya hade min, ga mutuwar Gimbiya Sa’adiyya da haryanzu nakejin ta sabuwa dal, ga kuma wannan da ke matukar damu na.”
Mikewa tayi ta iso gare shi, da hannuwanta biyu tasa ta tallabo shiya karisa biyota. “Tashi
ka zauna dana. Na amince maka ka tafi Italy in dai hakan zaiyi silar kwanciyar hankalinka.
Ka shirya maza-maza ka Iafi, da izinina. Adduata tana tare da kai. Allah ya taimaka ya maka jagora.”
A karo na farko na rayuwarshivya rungumo mahaifiyarshi cike da tsananin kaunarta.
“Nagode kwarai Fulani, na gode da dukkan komai. ”
“Kayi hakuri da abin daya faru maimartaba. Banji dadi ba sam, na sani Abin da Salbiyya tayi ko kadan bata kyauta ba. Sai dai shi abu idan ya faru baka da maganinshi. Don kunya
kam naji ta sosai. ” Ta saka kukan munafurci.
“Kin san dai yadda na tsani zubar hawayenki Kursiyya. Kiyi hakuri, komaiya wuce. Na kuma bada izinin duk wanda aka kama a masarautar nan ya tashi wata magana a hukunta shi. Bana tunanin za .a kara yin maganar. Komaiya wuce. Kema ina son ki manta komai, a tari gaba. ”
“To shi ke nan mai martaba. Naji dadi sosai tayadda ka goyi bayana. Allah ya kara mana sonvjunanmu.”
“Ameen ameen. Mun yi magana da Sarkin Kubaisu, mun tsayar da rana nan da mako biyu za,a yi auren Hafsa ‘yarbaba.”
Don murna bata san sadda ta rangada guda ba. Sam ba tayi tunanin tambayarshi yadda aka yi Yerima Abu Sufyan ya amince ba. Sai kawai ta fara hango Hafsa ta zama amaryar Yerima Abu Sufyan, dan lelen Sarki Abdurrahmanu.
“Sai a fara shirye-shirye. Za a yi bikin ’yargatan maimartaba.” Ya fada duk don ya faranta ran Kursiyya. Ai kuwa sosaiya faranta din. Dan yadda taji dadin wannan al’amari ji take kamar tajawo maka biyun. Ta tabbata ran Hafsa zaiyi fari, zata auri abun kaunarta. Finally, burin ta zai cika.
“Maimartaba ka bani izinin inma Hafsatutuna albishir.”
Murmushiya mata hade da nuna mata hanya da hannuwanshi guda biyu. Kamarza tayi gudu ta fice, ta nufi dakin Hafsa.
Ta same ta kwance da hoto a hannunta tana kallo. Tanajin motsinta tayi saurin boye hoton hade da kirkiro murmushi. Cikin saurin magana Kursiyya tace “Yata, ranar da muke
tsumaye yau dai tazo.” Tashi tayi zaune Hafsa, cikin mamaki ta kalli Kursiyya tana son sanin madosar zancenta. “Nan da mako guda za,a daura miki aure ke da muradin zuciyarki, Yerima Abu Sufyanu…”
Tun bata kai aya a zancen nata ba Hafsa ta gaggauta rungumarta tana sakin ihun murna. Tajanye jikinta daga na Kursiyyar tana mai sake kallon ta. “Umma da gaske ko da wasa?
Garin yaya haka ta faru? Ya sauko kenan yaji zai aure ni? Wayyo zan mutu don murna.”
Lallai fa akwai rikici