HANAN PART 1 BY MAMAN NOOR

     _Tsokaci_ 

*Wanan littafin kagagen labarine banyi shi dan cin zarafin wani ko wata ba in yayi dai'dai da rayuwarki kiyi hakuri Yar uwa domin akasi aka samu*

   _Warning_

Ban yarda wani ko wata ta ta juya min labari ba ko a canzata ta ko wata tsiga ba a kiyaye please
~Godiya~
Alhamdullilah godiya ta tabbata ga madaukakin sarki daya sake bani daman rabuta wanan littafin,sanan Ina godiya ga masoyana Wanda a kullum suke bani karfin guiwa da goyo min baya Ina son ku sani da bazarku Nike taka rawa Allah ya biyaku ya Baku duk abinda kuke Nima na alkhairi Amin ya rabbi

  Paid book ne 

🅿️1️⃣▶️2️⃣

Bismillahir Rahmanir Rahim

      Babban falo ne wanda ta ji kayan alatu da kayan more rayuwa 

Kallo d’aya zakawa falon ka Gane na masu hanun da shuni ne domin kuwa wanan falon Yana cikin daya daga cikin faloli dake gidan babban d’an Siyasar Nan ne me suna senator sani Bello Ndaman Wanda a yanzu Haka yake niman takarar shugaban kasa

    Tsayuwa a falon kadai ya Isa yasa me hankali tunanin mutuwa,domin kuwa in Kana ciki baka gane yanayi da ake ciki ko zafi ne ko sanyi ne ko Kuma damina,sanan Kuma baka sanin lokaci ko Rana ne ko darene ko Kuma safiya ne domin Yana bada yanayine na daban sai ka kalli agogo zaka Gane lokaci,duk wanan dukiyar da aka narkar anan din b'angaren amaryasa  ce watoh ba indiya wacce ya aurota a India,matar senata uku ta farkon hajiya Aisha cikakkiyar Yar Niger ce banufiya kamar inda shima senator ya kasance banufe ne tun kafin ya tafi jami'a akayi musu aure da Aisha had'in iyaye Kamar inda dai nufawan sukeyi kafin ka auri  wata yare sai ka Fara auren yarenka 

Aisha batayi karatu ba Dan ko aji Bata tab’a zuwa ba suna tare ya Shiga jami’a Yana gamawa ya Niki soja Allah ya dafa me ya samu ya dade a Nigeria army kafin daga baya yayi resign ya shiga politics

 Shigarsa siyasa yasa ya auro wata Yar maduguri hajiya Rabi wacce master ce da ita kyakyawar gaske wacce zai iya nunawa duniya ga matarsa domin akwai Jin turanci ga Kuma kyau duk wani harkokinsa na siyasa itace me tsaya masa,Amma ba Yana nufin yana wulakanta uwargidansa bane asalima duk wacce tace"zata Raina me Mata  zai rabu da ita kusan nufawa da kabilanci ai,ita Aisha ma kasancewar akwai Hutu ga kudi ba abinda ta rasa baka tab'a sanin batayi karatu ba Dan kuwa idanunta a bude yake akwai wayewa a tare da ita domin babu kasar da Bata zuwa in taso Kuma yanzu ma ta Kan picking wasu abubuwa a bokon Saidau turancin ne babu ya'yanta 6 da senator ita kuwa Rabi biyar kyawawa dukkninsu Amma duk basa kasar suna turai senater me kudi ne Dan shekaransa ashirin a Senate so biyar ana zabarsa kasancewar Yana zuba aiki a zone dinsa yanzu haka ma shine Senate president saidai kujeran shugaban kasa yake so....bayan auren Rabi da tayi haihuwa uku ya auro wata ba indiyiya Wanda a UK Suka had'u me suna Hanaz wacce ta tab'ayin miss word sun Fara soyayya da yike Yana da kudi ya aureta anan fah ta ture gwamnatin hajiya Rabi domin senater ya daina yayinta hanaz ce Kan komai ya' daya ta haihu dashi domin Yar gayu ce Bata son tayi haihuwa dayawa ya b'ata Mata shape,ranan suna Yar ta ci sunan mahaifiyarsa hauwa sai suke Mata alkunya da Hanan yanzu tana da shekara goma Sha tara,tana da shekara goma Sha biyu ta bar Nigeria zuwa karatu yanzu ta Gama ta dawo Kamar inda akeyi da ka Gama karatu zaka dawo  ya'yansa biyar Mata suna gidan miji uku na nnagi Aisha Kamar inda yaran gidan ke kiranta biyu na ummi watoh Rabi maza uku Suma sunyi aure Amma duk suna kasar waje da matansu domin a can suke aiki matan ma cikinsu akwai Wanda Suke kasar waje yanzu Yara uku ne a gidan Hanan ce auta 

    HANAN ba abinda ta baro na mahaifiyarta tana da Asia's look kana ganinta ka gan india,zamanta a kasar waje ba abinda ya tsinana Mata sai koyo rashin kunya da yawo clubs da Kuma abota da maza ba ruwanta,itace most popular and famous yar'sa a media domin ita media person ce me tarin followers a media shiyasa da tayi laifi kad'an za a buga a jarida harda kari,itace ciwon kan mahaifinta Dan ba zagin da Baya Sha ana cewa Wanda beyiwa yar'sa tarbiya ba bazai mulkesu ba politically tana janyo me matsifu shikuma baya son komai ya Shiga tsakaninsa da abinda yake so itako ko a jikinta wallahi harkarta takeyi ba ruwanta rayuwar turai take ko Niger garin kakaninta Bata son zuwa bare a Abuja suke Zama 

Itace ciwon idon hajiya Rabi ta tsani mahaifiyarta da ita kanta Hanan din domin su Suka ture gwamnatin ta a zuciyar senator shiyasa da Hanan ke misbehaving Dadi take ji mussaman in mahaifinta na mata fad’a Dan ma kwanaki cewa yayi zai tsine mata yayi disowning dinta hakan ya farantawa Rabi Rai Amma ita hanan din ba ruwanta da wanan,nnagi Aisha ce kadai me nuna Mata soyayyar gaskiya

__________

Cikin kuzarin da Allah ya hore Mata take saukowa daga stairs rike da makullin mota 

Sanye take cikin matsatsiyar cinos baki sai wata Yar Riga jumper iya cibiya flat tummy ta a waje ga kugun Nan ma Sha Allah hills ne kafarta me tsini sai tayi parking sumanta a tsakiyar Kai sai bakar gilashi da ta rufe rabin fuskarta ta fito a zazzafanta

    Saukowa take hade da gudu kamar ba hills tasa ba har ta Kama handle zata bude kofar taji muryar mahaifiyarta na cewa Ina Kuma zuwa???"

Juyawa tayi ta zubawa mahaifiyarta dake sanye cikin atamfa doguwar Riga tayi kyau sosai ta saki murmushi tace”kawata ce zatayi birthday shine zani mu Fara shiryawa da wuri Dan muna expecting guest daga kasashe duniya our old friends are cominb

 B'ata Rai mother tayi kamar inda take kiranta tace"no Hanan you are not going anyway wallahi na gaji Zaki fita ki d'auko min magana mahaifinki ya dawo Yana min matsifa Kuma fa karki manta rantsuwar da yayi miki akan duk Randa Kika sake jawo me magana zai aurar dake ga Maigadi and you know he meant I......"

Bata karasa ba Hanan ta karasa gun mother ta Kai Mata kiss a kumatu tace”sai na dawo “tana fadin hakan ta Kara sauri ta fita mother ta bita da kallon mamaki,ta rasa ya zatayi da yar’ta kullum cikin jawo mata magana take kishiyoyi na goranta mata ta rasa taya zata bullowa Hanan ta daina abubawan da takeyi

  __________

HANAN na fitowa gun motan ta tayi direct ta bude murffin ta shiga tayi Masa key Daman megadi na ganinta ya wangale gate Dan yasan halinta dukda Haka be tsira ba data fizgi motar saura kad’an ta kwashe shi yayi tsalle yayi gefe

 Gudu take shararawa abinta a titi kasancewar layout dinsu babu hayaniya tana kokarin fita a anguwan su wata mota ta fito daga wani gida tana reverse a ka'ida sai ta jira ya Gama sanan ta tafi tunda ya rigada ya danno Kai Kuma an rufe gidansu bazai yiwu ya koma ciki ba Amma saboda matsifa irin ta Hanan kin ja baya tayi ya samu wuri ya fita sai ma horn da tayi  ta Masa Kamar zata kashe Masa kunni 

Da mamaki ya kalli madubi Suka had’a Ido domin itama kallonsa take irin kallon raini abin sai ya bawa Habib mamaki ya Danna Mata horn itama horn ta Danna me fiye da nasa

  Tsaki yayi a fusace ya fito a mota,ganin Haka itama ta fito tana tafiya cikin taku 

Yace”keee miye Haka

Hayewa saman bunnet tayi tace"malam in kasan abinda yayi maka kyau shine ka koma ciki in wuce in ba Haka ba saidai muyi ta Zama wallahi Dan baka Kai in baka hanya ba 

Yace”Haka Kika ce??”

Tace”Haka nace

Yace”ok shikenan we shall see ai titin bana uban wani bane”

Tace”Amma ubana ne yayi titin Kuma kowa yasan duk layin Nan Babu Wanda ya kaisa kudi so ban gan abinda zaisa in baka hanya ba

In Banda rashin respect ka ganni ka nimi in baka hanya wallahi baka Isa ba

Tsaki yayi ya koma ya zauna a mota kafafunsa na waje ya dinga latse waya 

Itako ko a jikinta radio ta kunna na motarta tasa kida ta Fara rawa abinta

Tun Habib baya kallonta har ya Kai ga Yana

Maman Nur

👄👄👄👄👄👄
HANAN
💋💋💋💋💋💋
By maman noorul
Hudah

Paid book 

🅿️3️⃣▶️4️⃣

Bismillahir Rahmanir Rahim

Rawar da brick and lace sukayi a love is wicked take tana kad'an kugu yariyar  ta iya rawa

Satar kallonta yake Yana Jin haushinta a take yayi Mata kallon Mara kamun Kai,abinda ya tsana a rayuwarsa kenan ya gan mace Bata da kamun kai

Sun dade a Haka Allah ko yasa babu wata motar da ta Zo wucewa ganin fah ko kwana zasuyi ba tashi zatayi ba kawai sai yayi tsaki ya Kira megadi ya bude Masa gate yayi ciki Yana jiyota cikin gurb’atacciyar hausarta tana cewa ka taimaki kanka malam”sanan tayi cikin motar ta tayar ta bar unguwan shima ya fito ya fita

  Hotel din da za a shirya party tayi direct ta tarar da kawayenta Mata da Maza sai Suka hau shirya komai 

   Bàyan duk an Gama wata shirye shiryesu  inda Suka Kama domin a kusa da swimming pool zasuyi party suka Shiga ciki domin shiryawa  

  Fitowa tayi cikin bikini pant da bra ta saka wata katuwar hat da flat takalmi ga Kuma uban eye glass sai kamshi take 

 Lucy Yar minister da sukayi karatu tare a kasar waje itace me birthday din sai Suka kunna radio Suka Fara rawa 

 Hotona ake kashe musu dukda tasan Yan jarida ne da gulmarsu bata dameta ba she don't bloody care sunfi maida hankali akanta kodan saboda babanta na niman president ne oho 

Tana kwance a kujera Dake kusa da pool din tana waya sai ga abokansu na nesa sun Fara isowa ganin shalo wani best friend dinta ya sata mikewa ta saki wani irin ihuuuu tana cewa shalo Kaine a gari saukar yaushe 

Ya saki murmushi tare da cire gilashi idanunshi yace”babe kece Kika canza haka?”

Murmushi tayi ta juya me baya wanan pant din da Bata da maraba da babu bama abinda ta rufe saima raba duwawun da tayi ya shige ciki

Wani ihhuuu shalo yayi itako karasawa tayi ta rungumeshi ta Haye jikinsa yace"it been long babe kin Kara kayan Dadi 

 Fari tayi da Ida tayi  pecking dinsa hagu da dama sanan tayi kissing lips dinta dukk wanan abinda ake ana Mata video Kuma ta sani ba abinda ya dameta Bata b'oye hallayenta 

    Sauka tayi daga jikin shalo tayi kissing sauran friends dinta har mata
  Karasowa wani Dan jarida yayi kusa da ita yace"Hanan "

Ta juya tana me kallon banza,be damu ba yace”me Zaki ce akan wanan Shiga da kikayi kina Yar musulma Kuma Yar Dan takara shugaban kasa Wanda Kuma zai fad’a aji ayi koyi dashi “

     Cire hat din kanta tayi tace"while mahaifinah ke niman shugaban kasa bani ba, so kaje ka samesa I have a life to live that is what iam doing,iam  enjoying life to the fullest so kaje ka sameshi not me"

  Yace"ok,but Baki tunanin zai iya affecting dinsa mutane na Miki kallon Mara tarbiyya wacce Bata san darajar kanta ba dayawar mutane na cewa bazasu iya zaben Wanda beyiwa   ya'yansa tarbiyya  ba "

Tace” Ina da right nayi abinda na gan dama Dan mahaifinna na niman mukami ban gan dalilin da zaisa in kuntata kaina ba saboda wani tsoho can da beda godiyar Allah me wanan tsohon zai Nima a gurin allah,Yana da dukiyar da har generation100 bazasu Gama dashi ba, madadin ya koma gefe young generation su samu wuri no he want to hijack the public property,,i don’t know why this old men are greedy and selfish”ta fad’a tana yatmusa fuska ta maida fuskarta Kan wayar hanunta irin ko a jikinta dinan shiko d’an jarida yayi dip da alamu maganar ta Dake shi

Wani ne ya Zo ya rungumeta ta baya ta kyalkyale da dariya

Dan jarida yace”please Zaki iya min suratul fatiha?”
D’agowa tayi ta zuba me harara tace”suratul fatiha,suratul fatiha….Kai da ka ganni ka ga alamu Zan iya?”

Wani irin salati ya sake tayi tsaki ta bar wurin rungume da wani Abba ba shalo ba

    Daya daga cikin d'an jarida ya karasa inda ta zauna a cinyar Abbati zaiyi magana ta mike ta wanka me Mari tace"Wai Kuna da hankali kuwa ku barni in sarara Mana"

Rike kuncinsa yayi yace"Kika dake Ni?"

Ta jawo kwalbar wine din da suke Sha ta fasa a tebu zata Kai kansa shalo ya rike Mata hanun tare da dakawa dan jarida tsawa yace”live

Barin wurin yayi Yana juyawa Yana kallonta Yana tunanin irin rashin mutunci da zai Mata wallahi

   Bayan shalo ya lallasheta kawai sai ta kyalkyale da dariya ta fad'a ruwa sai Suka Fara shashacinsu,duk abinda take ana d'auka ta dade suna wanka da kawayenta har mazan kafin ta fito tayi cikin hotel din ta Shiga room dinta tayi wanka ta saka burshot da wata Yar vest ta fito suka cigaba da party 

A ranan Hanan Bata koma gida ba


Abba ne tsaye rike da newspaper tunda sanyi safiya ya shigo d’akin mother ya tashe ta ji yaje kamar yayi hauka saboda Hanan ta Gama dashi bashi da sauran kima a idon duniya

Mother data gan Bata fahimtar maganarsa ta lumshe Ido Bata son hayaniya tace”sweetheart calm down please explain in Gane abinda yake faruwa

Ya daka Mata tsawa yace 


   Maman Nur
👄👄👄👄👄👄
    *_HANAN*_
💋💋💋💋💋💋
_by maman noorul_
Hudah

🅿️5️⃣▶️6️⃣

Bismillahir Rahmanir Rahim

        Kaiwa da kawowa ya dingayi Rai a matukar b'ace Yana cewa Hanan has finish me, inallilahi wa innailahy rajiun what have I ever done to Hanan to deserve this ,

  Hankali mother ya mugun tashi tace"Dan Allah sweetheart ka fad'a min abinda tayi please"

A fusace yace"ke Baki gan inda media ta d'au zafi bane kowa maganar tsinanniyar yariyarki ake a media,yariyar ki can stoop so low as to have sex in public wallahi nayi regretting aurenki Hanaaz 

Hawaye mother ta goge ta karbi wayar hanunshi video data gani ya bala'in girgizata I mean tasan Hanan zata iya shiga da tafi wanan Muni but Bata tab'a tunanin rashin Jin Hanan ya Kai ta Fadi wa'yanan mugayen kalamai akan mahaifinta ba 

Komawa tayi d'abas ta zauna a bakin gado ta saki wani irin kuka tace"sweetheart Ni nasan bakin iyayena ne ke bibiyata bazai Bari inji dadin rayuwa ba,a baya sun gargade Ni da Kar in aureka in har na aureka suñ yanke alaka Dani Amma saboda soyayya da Nikeyi maka na yarda na aureka na baro komai nawa da kowa nawa Ina ganin Zan samu ingantanciyar rayuwa,na bar duk wata d'abiyu na na karbi musulunci da zuciya daya ina salloli biyar Ina azumi litinin da alhamis Ina Kuma azumin Ramadan ban tabawa  nufar wani ko wata da sharri ba ko Kuma inyiwa D'an wani fatan tabewa wallahi alhaji ban tab'a ba meyasa sai n.......Kuka ta fashe dashi me tsuma zuciya abinda Hanan keyi na ci Mata tuwo a kwarya...sai ta bawa Abba tausayi Dan a ganinshi shine sanadi, soyayyar da take me ne ya baro ta da kasarsu dukda Bata Saba ba ta yarda zata zauna cikin kishiyoyi.goge zufa yayi yace" Taya zanyi clearing  mess din Nan da ta jawo min baby baby Taya Zan kalli duniya yanzu jam'iya ta gargadeni da in d'auki mataki akanta Dan bazasu so su Fadi ba baby na gaji iam tired of her attitude ya zanyi yanzu Nan "

Karfin kukanta da ya karu dan da yasan zuciyarta da bazai dage tambayarta ba ganin har shidewa tanayi yasa shi Zama kusa da ita ya rungumeta Yana lallashinta yace"gidan television dayawa sun nimi su zauna Dani akan wanan maganar Hanan tayi crossing all limit wallahi 

    D'agowa mummy tayi tace"duk abinda ka gan ya dace ayi Mata I don't care ka hukuntata  ta duk wata hanyar da kake ganin ya dace  wallahi alhaji bani ke Sata duk abubuwan da takeyi ba wallahi bana iya bacci da wanan hallayen nata"

Abba ya ji tausayin mother ya rungumeta Dan tabbass Yana kaunarta yasan ko kad'an Hanan Bata biyo halaye Hanaaz ba 

Lallashinta yayi da k'yar tayi shiru ya zuba Mata Ido Yana kallonta.goge hawaye tayi tace"sweetheart ya zamuyi "

       Dukar da Kai yayi yace"I will give her another chance just for your sake in tayi failing iam sorry I have to disown her kafin ta kasheni wallahi Hanaaz na gaji,Hanan is not useful to herself bare Kuma to her society,at her age kinyi suna da har yau ana damawa Dake at 21 kinyi miss world meyasa hanan bazata gyara rayuwarta ba she has a good carrier a good  surgeon Wanda a Nigeria in Bata Zo na farko zata Zo  na biyu ko na uku na bude Mata asibiti but Bata zuwa,Dan Allah ku fad'a min ya ake da ya' a Ina nayi failing dinta as a father please tell me,duk wani d'an na cikina Yana girmamani yana bani  girma and they all sopport me Banda ni why Hanan yariyar Da nake jinta a zuciyata,I love her the most duk cikin ya'yana but....."kasa karasawa yayi hawaye ya cika idanunshi it hurt ya gan yarshi na misbehaving Haka, daga kayan da take sawa zuwa manners dinta abin na damunshi 
 
        Mother shiru tayi tana kallonsa  ita kanta she is feeling bad ta Kama hanunsa tace"may be it because ka aurenine da nasan bazan Zama maka alkhairi ba wallahi da ban yarda na aurek......"jawo ta yayi ya rungume yace*don't said that 

    Murmushi me ciwo tayi yace"don't worry call her please muji ko tana  lafiya "

Mother tace"ba lallai ta d'aga ba yace"then text her"

Tace"she won't response Kuma ba lallae ta dawo gida a satin nan ba "

Mikewa yayi yace"ok but dont get tired always check on her love"ta jinjina Kai tare da jawo wayarta ta dannawa Hanan Kira 

    Ringing take ba a d'auka ba tayi ta dialling ta kalli Abba tace"she is not pickin....."Bata karasa ba taji muryar namiji 

      Yace"hello"

Kallon Abba tayi shima yaji wani d'aci a ranshi Dan wayar na speaker hawaye ya Fara sintiri a idanunta ta goge da bàyan hanun tace"waye ne please"

          Ji sukayi ance me wayar yanzu ta shiga wanka zata fito ba dadewa ba mun kwana muna morewa ne"

Baya mother tayi ta saki wayar tana wani irin kuka 

    Abba ko fita yayi a d'akin Dan ji yake kamar an daki zuciyarsa ya haifi mazinaciya,inallilahi wa'inailahy rajiun ko iya shiga dakunan sauran matansa beyi ba yayi d'akinshi ya zauna bakin gado yayi tagumi ya rasa ya zaiyi da Hanan 


      ___________
HANAN ko bayan sun Sha rawarsu a gun pool akayi ciye ciye sanan Suka Koma hotel suka sake wani wanka sanan sukayi club....dawowar su kenan da safe Nan sukayi gidanta da ita kadai tasan dashi da friends dinta 

        Bayan kwana biyar ko waiwaiyar gida batayi ba Kuma duk  kasa ta d'auki cece kuce da akeyi akanta da furuncin da tayi akan mahaifinta, duk tana gani Dan Abu ne na social media wasu na Mata addu'a shiriya saidai mafi yawanci sunfi ganin laifin mahaifinta Kuma shi ake zagi 

      Yau tun  safe Bata fita ba ita kadai ce a gidanta su Lucy sun wuce 

     Juye juye take a gado da alamu yunwa take ji ta jawo wayarta domin Kiran wani boy dinta ya kawo Mata abinci sai ta gan text da dai kamar bazata bi ta kan text din ba sai Kuma ta bude ganin mother ne abinda ta gani shi yasata mikewa tana zare Ido a gurguje ta saka wata vest a saman bra dinta Daman guntuwa wando ne jikinta ta Kama sumanta ta d'au makullin motar ta fita a guje 


         ___________


Yau Kamar kullum Yana zaune kofar gidansu gindi wata bishiya Yana hutawa Dan duk yamma ya Kan yi haka

        Amal (kanwarsa) ce ta fito a cikin gida zata fita ta gaishesa ya amsa 

     Yace"Ina Zaki je Amal "

Yariya ce da bazata wuce Sha biyu ba tace"Yaya Deeni ne yace"in siyo Masa Kati ba network da zai siyi ta banki yace"ka duba min titi na gan Kuma ba motorci shiyasa na tafi"

          Yace"Maza Yi sauri je ki dawo "

     Amal juyawa tayi ta hau titi saidai from no where mota ta shigo layin a guje da mugun gudu habib  ya mike ganin Amal ma ta kasa tab'uka komai ta  hanun kawai takai  kunnuwanta ta toshe tana jiran mutuwarta  harta sadakar da yau ta Gama yawo sai ta ji an ja birki..Habib yayi saurin janyeta 

            Jikin Amal rawa yake ta mugun gigicewa ko Bude Ido ta kasayi saboda fargaba da rudewa 

   Fitowa tayi a motar cike da b'acin Rai tace"


Maman Nur

DOWNLOAD COMPLETE BELOW

Hanan part1