HARSASHEN SO CHAPTER 12

HARSASHEN SO 
CHAPTER 12
Tsaye yake a jikin madubi bayan ya fito daga wanka, shiri yakeyi mai kyau da daukar hankali dan duk wani abu wanda yasan idan mace ta kalleshi hankalinta zai tashi yayi kokari wurin ganin ya tafi da imanin Shalele lokaci daya. Turare ya dauka ya feshe duk wasu gabobi najikinsa, gyara lallausan gashin kansa yayi yadan mikeshi tsaye yanda dai zai dauki hankalin Shalinsa. Yana gamawa ya dauki wayoyinsa ya fito, baibi takan Khadija ba ya fice, a lokacin har an fito mishi da motar da zai fita da ita kirar ‘Ferarri‘ motar tayiwa Mubarak kyau sosai kuma shine dama kadai ya dace da wannan zukekiyar mota shine ya dace da shiga cikinta dan ya fiddo martabar motar kyawunta da kuma tsadarta. Shiga yayi yaja yayi tafiyarsa shi daya dan ya lura na tare dashi munafikai ne, suna kallon shige da fitarsa ne don baban Mubarak yace su kula duk lokacin da sukaga Shalele su rike masa ita su kawota har wurinsa ranar zai nunawa Mansur baya da wayau. Tafiya yakeyi cikin natsuwa da kwanciyar hankali sai dan sautin kida dake tashi a motar wanda shi kadai yakejin abunsa dan koda akwai mutum a ciki ba lallai bane yaji. Shalele kuwa tunda tayi sallah la’asar tayi wanka amma furr mai gida yace babu gidan uwarda zataje idan hankalinta yayi dubu ya tashi banda kuka babu abinda takeyi ta hada mai gida da girman Allah amma yace bazata flta ba, Bata da yanda zatayi dole ta hakura ta koma dakinta amma taso taje kada Mubarak yaji babu dadi to bata da yanda zatayi mai gida shika zaiyi idan ta fita. Mubarak kuwa ya dade tun yana duba lokaci harya fara sikewa dan gajeran tsoki yayi tare da fltowa daga cikin motar duba hanya yayi sosai amma babu Shalele babu dalilinta dan haka ya dawo motarya zauna har zuwa wani lokaci. lyakar kulewa Mubarak ya kule kuma ya Shaka sosai wannan abu yayi masa ciwo dama saboda rainin hankali irin na mata yasa baya sabgar su  baya zuwa zance hasali ma bai taba ganin mace da kansa yaji tayi masa ba kota kwanta masa a rai ba, 
‘Dan gajeran tsoki yayi tare da kunna motarsa yai taflyarsa. Gudu yakeyi sosai a hanya tun a motar ya bugawa Khadija waya cewa ta shirya kafin ya iso, khadija ta tambayesa lafiya? Yace ba komai kawai zasuyi Tafiya ne, itama ‘taji dadi zasuyi taflya dan idan yana garin nan Hafsat tana ganinsa ita kuma ta tsani ko kallon Mubarak ayi a rayuwarta. Cike da fushi ya isa gidansa ko parking din kirki baiyi ba ya fice daga motar a hanzarce ya shiga ciki yana shiga dakinsa ya fara rage kayanjikinsa ya nufi toilet. Shawa ya kunnawa kansa ruwa yana tararowa tun daga saman kansa har kasan kafafuwansa cikin fushi yake kansa yana kallon kasa idanuwansa a rufe yana fItar da numfashin mai dauke da sirrika masu dama! 
Towel ya jawo bayan ya gama abinda yakeyi ya daura a kugunsa fuskarsa a daure ya fito jikin madubi ya tsaya ya kalli kansa saida ya shafa gashin kansa sannan yakai hannunsa daidai zu ciyarsa yace ina so na manta da ita kwata kwata a rayuwa‘a. Yana fadar haka ya matsa inda yake ajiye kayansa ya bude ya dauko, sakawa yayi tare da kara komawa jikin madubi yadan gyara gashin kansa turare ya shafa yana gamawa ya dauki wayoyinsa ya fice a dakin, 
‘Dakin Khadija ya nufa, ita kuma tana ganinsa cike da farin ciki tace na shirya ta karasa maganar tana murmushi. Murmushi Mubarak yayi tare da kallonta amma baice komai ba, Tana ganin ya juya da sauri ta dauka gyalenta dan tasan bazaice mata ta taho ba tafiyarsa zaiyi ya barta saida ta isko sa daga baya. 
Zuciyar Khadija dinke take da farin ciki kuma bata san dalilin wannan tafiya ba, shi kuwa Mubarak zuciya yasa shi zai bar garin Abuja zaiyi tafiyarsa zuwa kano ya kwana washe gari kuma ya tafi patercourt dan ya daukarwa ransa har abadan duniya ya manta da Shalele kuma ya manta da ita dan zuciya garesa mai zafi idan harya bawa abu baya ya barshi har abada kuma baiyi ma Shalele uziri ba, 
A bangaren Shalele kuwa tana ganin mai gida ya fita itama ta sulale tabar gidan, inda Mubarak yace su hadu a wurin taje tayi ta jira amma babu shi babu dalilinsa har dare yayi sosai Shalele tana wurin da sunan jiran Mubarak har gefen asubahi Shalele tana wurin amma Mubarak baizo ba kuma bai aiko ba, Cikin tashin hankali ta koma gida tare da addu”ar dai Allah yasa lafiya, koda ta koma gida babu wanda yaga shigarta harta shiga dakinta, zanen hoton Mubarak ta dauko tana kallo tare da tambayarsa miyasa ya saba alkawari ne? Ta karasa maganar tana mai digo da hawayenta a saman jikin hoton. 
Goge hawayen idonta tayi da bayan hannunta sannan taci gaba da cewa dakel fa na fito mai gida ya hanani fita ne, saida aka kira magrib ya fita daga gida sannan na samu na gudu ta kofar baya nazo harna kwana a inda kace amma ban ganka ba rashin ganinka yasa banji dadi ba. Miye laifina kuma miye ya shafi soyayyar da nake maka da kiyayya tsakanin “yan uwa guda biyu? Nidai kam koma dai miye ina sanka, sanka yana rayuwa ne a cikin sokar jikina yana girma duk bayan second daya yana yaduwa sosai a Cikin raina kamar yanda jini yake gudana a cikin gangarjikin dan adam, Duk lokacin da wani ko wata yayi gigin zukejinin jikina hakika azumi sattin zai hau kansa dan rabajini da jiki kisan kaine to haka yake raba Shalele da soyayyarka tamkar rabani ne da lumfashina, ina sanka, Shalele tana kaunarka, ta karasa maganar tana maiyin 
murmushi saida ta sunbaci jikin hoton sannan ta matsa daga wurin. 
Haka dai kwanaki suka ci gaba da shudewa abu kamar wasa karamar magana ta zama babba tashin hankali irin wanda Shalele ta shiga ita kanta bata san irinsa ba, ta kada ta raya babu labarin Mubarak bare dalilinsa, wannan tashin hankali yayi yawa don haka Shalele ta sidada taje har gidan Mubarak amma sai aka fada mata yabar kasa ma kwata kwata kuma gidan ya bayar dashi kyautawa wani yaronsa, Tashin hankali sosai ta shiga gashi bata da number wayar Mubarak kuma wayarta data siya ta ajiye numbersa a ciki mai gida ya dandaketa tas, ta fitittike ta zuke, gan’ln tashin hankali da Shalele ta shiga yasa mai gida shiga cikin matsanancin damuwa kuma ya tambayi Shalele abinda ya sameta tace masa babu komai. Yayi iyakar kokarinsa amma fur Shalele ta kafe kai da fata tace babu abinda ya sameta, mai gida ya tambayeta me ta nema ta rasa? Tace babu komai, ganin abu kullum kara tabarbarewa yake al’amura suna ta karaja baya yasa mai gida ya bada Shalele aka mayar da ita Katsina gidan wani amininsa mai suna Alhaji Abas saboda yana da “ya“ya mata waiko zata samu ta rage damuwa da tunani. Gidan Alhaji Abas babban gidane daya tara samari da “yan mata, gidane da aka kawata shi da ginin zamani an kashewa gidan naira anyi gini na daukar hankali da burgewa amma duk wannan abu baisa gidan nan ya burge Shalele ba ko daya, 
Zaune take ta zabgaga uban tagumi hawaye kuwa suna kwarara daga cikin idonta takardar da aka zana mata hoton Mubarak ta kurawa ido tana kallo ko kyaftawa batayi, Asma’u data Fito daga toilet tabi ta da kallo tare da tabe bakinta ta girgirza kanta tare da nemar mata sauki, ita kuwa Shalele batama san tanayi ba, har Asma’u ta gama shirinta ta fita, 
Har taje kasuwa ta dawo Shalele tana cikin wannan hali,yanzun kam sabbatu takeyi kamar wadda ciwon aljannu ya kama sai tayi magana saita kyalkyale da dariya sannan ta sake kai dubanta ga hoton Mubarak taci gaba da magana! ‘ Cikin tausayawa Asma’u ta kalli Shalele, zama tayi a kusa da ita sannan ta tabata, Shalele bata san Asma’u ta zauna ba haka kuma bataji ta tabata ba, har yanzun hawaye ne ke digowa daga cikin idonta kur idanuwanta kuwa a saman wannan dai takardar zanen hoton Mubarak yake Tana cikin wannan yanayi ne kawar Asma’u ta shigo da sallama, Asma’u ta dauke kallonta daga Shalele ta mayarda hankalinta inda taji muryar kawarta tare da amsa sallamar. Murmushi Asma’u tayi sannan tace Maryam sannu da zuwa yawwa wadda aka kira da maryam tace tare da ida shigowa da sauri cikin dakin tana cewa Asma’u bani garwashin wuta k’I gani da sauri, Me zakiyi da garwashi ne? Haba kedai bani ki gani maza maza, tashi Asma’u tayi taje ta kawo garwashin wutar ta bawa Maryam, a gabansu Maryam ta cire duk kayan jikinta ta mike tsaye tare da kallon yamma ta bawa gabas baya wani garin magani ta dauka ta zuba a cikin wutar hayaki ya fara tashi a cikin dakin sannan ta fara maganganu akan wani can wanda bamu san ko waye ba, Tari Shalele ta farayi dan dakin ya dauka sosai rufe idanuwanta ta farayi tare da kora iska da hannunta yanda dai mutum yakeyi idan yaji hayaki yana shigar idonsa‘ Wayar Maryam ta farayin ringing dan haka ta ajiye kaskon wutartare da daukar zaninta ta daura, matsawa tayi kusa da wayarta ta dauka dariya tayi sosai wanda hakan yasa Shalele ta kalleta, Maryam tace dan iska kaji matsi kenan tun kafin na gama har ka kirani bana fada maka aljanuna sunfi naka ba? ‘Daukar wayar tayi tare da cewa hallo! Daga dayan bangaren akayi magana wanda banji ba, Maryam tace yanzu ka sauko kenan? Tou zaka bayar da motar ko A, a,? Murmushi tayi sannan tace tou godiya nake zanzo na dauka Allah ya kara girma, tana fadar haka ta kashe wayana. 
Dariya Asma’u tayi tana cewa wallahi kidai ji tsoron Allah kin gama kwakwale Auwal yanzun kuma kin kamo wani wannan kuma waye shi? Dariya Maryam tayi tare da cewa mai sona ne, kallon Shalele tayi tace wannan itace mai cutar ciwon so? Asma”u tace itace,jinjina kai Maryam tayi tana ci gaba da cewa na tausaya miki Allah ya jikanki ai kuka yarinya yanzu kika fara shi. 
Asma’u tace haba bansan wulakanci fa, Maryam tace aini shi na iya, ni na tsani so haka kuma na tsani duk wasu masu soyayya naci uwar so tun tunin ni yanzun tsakani na da masu soyayya saida nayi musu jaje kinga naira ta Me min kwanciyar hankali miliyan dari biyu nake so na tara a account ina yanzun dai na tara biyar kinga kuwa soyayya ba tawa bace. 
Kallon Shalele tayi sannan ta matsa kusa da ita ta dafa ta kana tace yarinya wane ne yasa zuciyarki kunci? Waye ya shiga ya dabaibayeki? Wane marar imani ne? Gaki kyakkyawa ga siga diri asali sannan uwa uba zunzurutun kyau wane ne wannan dan iska n ……… ? Cikin bacin rai Shalele ta dago kanta fuska a murtuke ta rike makoshin Maryam ram sannan tayi magana cikin damuwa wanda Maryam kadai taji abinda tace. Murmushi 
Maryam tayi irin na “yan duniya sannan ta zaunar da Shalele a gefen gadon data mike tsaye. Tsugunawa tayi a gaban Shalele tace ke yarinya ce, Asma’u tambayi kanwarki shin a fada mata ko kuwa a barta duniya ta gaya mata ne? Asma”u tace fada mata ai kune duniyar duk wanda ya baro gidan iyayenshi idan dai har iyayensa suka ce masa jeka ka gani idan ya taho ku yake gani. Cikin natsuwa Maryam tace na tausayi miki Shalele kuma nayi niyar taimaka miki naji labarinki kaf domin Asma”u bata boye min komai ba, abinda kuwa yasa nace miki ke yarinya ce har yanzun baki da gogewa baki da wayewa sannan kuma baki da wani ilimi akan soyayya haka nan kikayi wankan tsarki kika dulmiya kanki a cikin halaka, 
Ada lokacin ina yarinya nima kinga irin abinda kika fadamin akan nace wane dan iska ne? Baki bari na karasa ba kika tashi kika rikemin wuya murmushi Maryam tayi tare da goge hawayen idonta tace lallai ina miki jaje. Domin a da idan naji an aibata kalmar ‘SO’ sai nayi yanda nasa mutum yaje umara a gidan yari, kin ganni nan na iya hada tuggu na iya makirci dan wallahi idan har na kullawa mutum sharri baya iya warwareshi harsai gobe kiyamar Allah, 
‘Dan gajeren murmushi Shalele tayi tare da cewa Allah yayi mana tsari daga kaidinki. Maryam taci gaba da cewa kuka tunani damuwa ya kare miki kina da naira dubu dari?…. Me za’ayi da dubu dari? Shalele ta tambayi Maryam, Maryam tace garinmu zanje na anso miki taimako wallahi sai Mubarak ya kawo kansa sai yazo da kafafuwansa ya durkusa a gabanki yana fada miki, Kalmar so Murmushi Shalele tayi sannan ta kalli Maryam tace a cikin miliyan biyar dinki ki ranta min idan haryazo a gabana zan biyaki, mikewa tsaye Maryam tayi tare da cewa haba yarinya an tabayin asiri da kudin rance? Shalele tace tou wasu ma naga da kudin bashi suke zuwa makka, kece kika ga dama zaki taimakamin tunda har na yadda ayi asiri wa wanda nake kauna ai ke bada bashi abu mai sauki ne a wurinki. Shiru Maryam tayi na wani lokaci sannan ta kalli Shalele tace babu damuwa nayi alkawari zan taimakeki harsai inda karfl na ya kare, murmushi Shalele tayi tare da cewa ina godiya, Bayan sati daya Maryam taje can garinsu Mubi ta kaso kudi sosai ta hadowa Shalele asiri anyo tsafe tsafe an bibbigi layoyi anyi saddabaru sosai ta hado masifa tayo katsina da ita. Shidai Alhaji Abas da matansa basu san wainar da ake toyawa ba tunda shiyyar yara mata 
daban ta yara maza daban suma iyaye suna tasu shiyar, Komai Maryam tayiwa Shalele bayani yanda zatayi amfani dashi amma tace ance sai tsakar dare lokacin Mubarak yayi bacci dan asiri yafl cin mutum a lokacin da yake bacci, godiya Shalele tayiwa Maryam sosai, tadan dade a gidan sannan daga baya ta tafi. ldon Shalele biyu har agogon dakinsu ta buga 2:40am wanda wannan lokaci yayi daidai da lokacin da Mubarak yake fara ibadarsa har sai yayi sallar asuba yake komawa bacci! 
Hmm nanfa akeyinta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *