HARSASHEN SO CHAPTER 30

HARSASHEN SO 
CHAPTER 30
Kashe sigarin hannunsa yayi sannan yace idan kuma kina ganin kema wata jar wuya ce to ki tattara kibarmin gida, 
Cikin damuwa Shalele ta kakkabe baccin dake cikin idonta tace Mai gida duk me yayi zafi haka ne? Tunda kace bazan koma ba bazan koma ba, kuma ko bayan baka numfashi na gama auren Mubarak har abada ka kwantar da hankali. 
Mai gida yace karya kike mara zuciya, ke baki da zuciya kare ya cinye zuciyarki da irin zuciyata kika yo har abadan duniya da bakiji san abinda bana kauna ba a duniya. 
Shalele tace a baya kenan amma a yanzun ka saka ido ka gani,yanzu ba kowa ya tafi ya barka ba? Tou ni waka ga nabi? Banbi kowa ba Mai gida wurinka na tsaya nasan banda gata duniyar nan saikai, ina tare dakai nafi kowa sanin mahimmancinka,Allah ya huci zuciyarka. Tana kaiwa nan ta mike tabar dakin. 
Tana fita Mai gida ya tashi daga inda yake ya wuce ciki dan kwanciya, bakar zuciyarsa kuwa sai tafasa takeyi da jin bakin cikin Mubarak na raye, ayyana masa tayi kawai ya kashe 
Mubarak tunda dan Baba bashir daya ne ya gama takaitashi har abadan duniya, kuma baya tunanin zai kara aihuwa. 
Wannan Shawara tayiwa Mai gida daidai, duk lokacin daya rumshe idonsa ya hango Mubarak yanajin bakin ciki, gashi dai mai kyau dan gayu ajin farko, ga natsuwa ga ilimi komai dai yaji dan ba mace ba namiji ma Mubarak yana daukar masa hankalinsa. 
Tsaki yayi tare da cewa shege dan buzuwa, zamu gauraya dani dakai, zaka isko babarka a lahira, 
Shalele kuwa tana zuwa dakinta baccinta tayi dan ita kam a halin yanzun tasa doster ta goge Mubarak a zuciyarta, sai inda yake mata fatalwa, domin rubutun ya dade sosai a saman allon zuciyarta, to ta goge kuma rubutun ya goge amma har yanzun fatarwa yake mata. 
Bayan sati biyu, Mama dai bata dawo gidan Mai gida ba, shima kuma baije ba, har suka tattara suka tafi basuyiwa Mai gida bankwana ba sun koma can gidan wanda Mai gida ya siyar, dan tun a lokacin da Baba yaji labarin siyar da gida ya sake siyo abunsa, 
Anyi ma gidan gyara sosai ginin da zamani yake tafiya dashi, kuma ya siyi wasu gidaje 
anan bayansu da kuma gefensa dama da haggu ya hada a gidan, komai dai yayi sai san barka. 
Shima Mubarak bai dawo ba, kuma babu waya dama baya da wayar kowa a gidansu, yana can yaci gaba da huldan gabansa, 
Ganin haka yasa abun nan ya kara konawa Mai gida zuciya, dan haka ya kira Shalele ya zaunar da ita, cikin lumana yace Shalele mu biyu muka rage a garin nan daga ni saike, kuma kina kallo zaman duniya ya canja, idan kana dashi akeyi dakai, idan baka dashi ko uwarka bata saurarenka, don haka zan turaki wurin dangin mahaifiyarki, idan kinje kuma ba zama nace kiyi ba, kisa natsuwa a rayuwarki kiyi abinda zan turaki kinji ko Shalinina? 
Shalele tace to Mai gida, Mai gida yace kuma bance ki fadawa kowa inda kikeba, duk abinda yayi tsananin sauki yana bayansa, kiyi hakuri Shalele duk nine naja miki wannan bakar rayuwar kiyi hakuri ubangiji ya albarkaci rayuwarki, ina miki fatan alkairi kuma albarka tabi ki duk inda kika tafi. Shalele ta amsa da amin. 
A cikin yinin ranar Mai gida yasa Shalele ta tattara komai nata, duk abinda tasan zata bukata saida ta hada abinta, kudade masu yawa Mai gida ya bata yace koda zatayi wani abu, 
Haka aka jibga kayan Shalele a mota, tana kuka dajin kunci da dacin rabuwa da mahaifinta, rarrashinta Mai gida yakeyi haka ya lallabata har suka tafi, Shalele sai kallon kofar gidansu takeyi Mai gida tsaye yana daga musu hannu har suka bace, saida ta daina hango Mai gida sannan ta gyara zamanta a cikin mota ta kalli gabanta. 
Karar aman da Khadija ke kwararawa ya farkar da Mubarak daga baccin da yakeyi, rai a bace ya sauka daga saman gadon ya nufl toilet, a bakin kofa ya tsaya hannun haggunsa ya rike kugunsa damarsa kuwa ya dafa bango yana kallonta amma baiyi mata magana ba. 
Saida ta gama sharara amanta, sannan ta kuskure bakinta, tajuyo, wani kallon rainin hankali yayi mata tare da cewa ke ciki gareki k0? Khadija tace wane irin ciki kuma? Cikin bacin rai yace ina tambayarki kina tambaya na wannan tsantsar rainin hankali ne yarinya, ciki kikayi? Khadija tace ni banda ciki,jinjina kai yayi tare da cewa idan ma kinyi matsalarki dan tun kafin na aureke na fada miki, yana fadin haka ya juya. 
Fita yayi daga dakin cikin damuwa, saida ya zauna saman kujera sannan ya gane ma Khadija ta raina sa, shifa aure yayi sane dan samun natsuwa taya za’ayi ma saboda tsabar iskanci kawai ma matarsa ta haihu? Sai yanzun ya tuna da ya daina amfani da maganinsa 
kwana biyu. 
Innalillahi wa”inna ilaihir raji”un””” kallon kansa yayi cikin mamaki yace haba duka duka  nawa nake? Harda za‘azo a haifamin “ya”ya a cikamin gida da hayaniya gaskiya bazai yuwu ba, tashi yayi ya koma dakin, Khadija na rabe a gefen gado, ko inda take bai kalla ba ya shige toilet cikin bacin rai. 
Itama addu”ar ta daya Allah yasa ba ciki bane, dan ita tafi dangana abun ne da taci abinci ta kwanta shine take tunanin yasa tayi amai, amma bata tunanin tana da ciki, 
Shi kuwa harya fito wanka fuskarsa babu wasa, danshi dama tuni ya fita hakkinta baisa ta tayi planing ba da kansa yakeyin abunsa dan kar a samu matsala, kuma baisa ta tayi ba saboda kada ya cutawa rayuwarta, dan idan ta gaji da zama dashi koda sun rabu tayi aure a wani wuri saita aihuwarta amma shidai kam badai a gidansa ba, kai wannan yahudanci da yawa yakeyi. 
Shiryawa yayi harya gama bai mata magana ba sai hade rai, da zai fita yace karki dafa abinci dani sannan kuma komai naki ki tartara shi kibarmin dakina, sannan kuma saiki zaba raino na zaki yi ko rainon ciki? Yana fadin haka ya fice. Ba tare da ya bari yaji abinda Khadija zatace ba. 
A gajiye Shalele suka isa garin jos, gajiya takeji sosai a jikinta dan kwance take a baya, duk 
da bata kalli garin ba ga yanayin iskan da take shaka ya tabbatar mata da garin jos yana dadi. Tunani damfare sosai a zuciyarta har suka isa kofar gidan da zasuje,jin mota ta tsaya tana barara horn ya tabbatarwa da Shalele anzo inda za’azo, tashi tayl’ zaune kallo daya tayiwa barkeken get din gida wanda saida kwalwarta tajuya saboda yanda ya bude mata idonta. 
Gabanta kuwa saida ya fadi, ikon Allah haka kawai ta fada a daidai lokacin da aka bude get in gida, dakel ta tattare bakinta tare da washe dukan idanuwanta tana kallon ikon Allah, taflya mai nisa daga bakin get zuwa wurin da aka tanada don ajiye motoci, Sukayi
Bayan yayi parking ya fita ya budewa Shalele murfin mota ta fito, duk da dare ne amma zaka iya cewa same ce, domin an kwata gidan da wasu irin manyan fitulu masu haske da kuma burgewa, driven daya kawota yana gaba tana bayansa tana biye dashi cikin natsuwa, 
Wata hanya sukabi daban wadda Shalele take tunanin itace zata sadasu da inda mamallakan gidan suke, kana tafiya kana kallon hoton kanka, murmushi Shalele tayi cikin yanayin kauyanci ta karewa kanta kallo sannan taci gaba da tafiya, a ranta kuwa wani irin farin ciki takeji tazo gidan “yan gayu dadi taji sosai tare da godewa Allah ma da suka rabu da Mubarak zatayi rayuwa mai kyau itama ta waye ta zama “yar gayu, kuma zatayi addu”a Allah ya bata miji nagari. Addu’arta kuwa ta tsaya ne a daidai lokacin da suka shigo ciki, lumfashin Shalele nema yayi ya dauke, ta tsaya tsaye cak taki gaba taki baya, domin gani takeyi kamar a saman glashi take tafiya tsoro takeji kar ta fada kasa. Tsuguniya yayi drivern a gefe daya tare da nunawa Shalele kujera yace bisimillah, uhum dan karta bayar damu kauyawa yasa ta dage tayi tattaki zuwa inda ya nuna mata ta zauna, Shalele dai tace a fada muku kallon sai wanda ya gani, domin dai labari yana hannunta rubutu kawai na admin ne
An dade sosai da zamansu sannan suka farajin tafiya daga sama, da sauri Shalele ta daga kanta sama inda takejiyo karar takalmi, da sauri ta kakkaba idanuwanta tare da kallon inda take zaune sannan kuma ta sake kallon sama, rasa ta ina akeyin ‘afiyar tayi, domin dai a inda take tana kallon mai tahowar sama ma kuma tana kallo shin abinda take so ta sani ne ta kasa fahimta. 
Barka da fitowa hajiya,jin maganar drvr ya tabbatarwa da Shalele abinda take san gani 
yazo kusa da ita,juyawa tayi gaba dayanta takai dubanta wurin matar, kafin tayi magana har ta zauna kusa da ita tana cewa sannunku da zuwa, 
Shalele tace ina yini, lafiya lau ta fada tare dajinjina kanta, mikewa drvn yayi yana cewa hajiya bara na shiga ciki, ba tare data kalleshi ba tace a huta gajiya ina godiya. 
Fita yayi, ita kuma tacewa Shalele ta taso suje, ta inda ta sauko ta nan tabi da Shalele 
gaban Shalele sai faduwa yakeyi dabadan ta rike hannun Shalele ba tofa lallai da bazata bi ba, 
Ai Shalele gajiya tayi da wani kauyance kyauyance tabi hajiya suka wuce ciki,  wani balagaggen palo ne wanda yaci kudi kamar ba‘asan darajarsu ba, wani kyakkyawan matashi ne kwance a saman kujera 3siater ya kashe, kallo daya zakayi masa kasan shima din dai babban yaro ne, 
Hajiya tace Kamal ga Suleim tazo fa, dan tabe baki yayi cikin rainin wayau yace sannu Suleim, murmushi Shalele tayi ba tare da hakoranta sun fito waje ba, ta jinjina masa kanta alamar yawwa. 
Wucewa sukayi ciki, da sauri Kamal ya cire glashin idonshi, yace momy a sakace yayi maganar, daga ciki tace mene ne kuma kamal? Haba mom “yar aiki zakije da ita har cikin dakin baccinki, haka kike zuwa kije kiyi ta yo mana kwashe kwashe wallahi, shiru tayi hajiya batace komai ba dan tasan iskancin Kamal tunda ta fada masa da zuwan Shalele tace masa Ummu Suleim zata zo diyar kanwarta, amma saboda tsabar iskanci zaice wata “yar aiki. 
Wanka Shalele tayi, momy ta bata kaya ta saka, domin kayan da Shalele tazo dasu momy ta raina musu hankali a palon kasa ma aka barosu, Naja mai aiki ta kawowa Shalele abinci, kadan taci abincin ta kwanta, 
Duk girman wannan rusheshen dakin Shalele kadai ta kwana a cikinsa, ta wayi gari a cikin sabon gida, wani irin yanayi takeji mai dadi, tana makale da tunanin Mai gida a ranta, amma zance Mubarak kuwa ta barshi a kauye. 
Bayan tayi sallah asuba, ta sake komawa ta leme a bargo, rayuwa sabuwa, Shalele na daga kwance tana sararawa abunta. 
Mai gida kuwa tafiyar Shalele shima dan abinda zai bukata kadai ya tattara, bayan ya gama ya bawa Balaga takardar gidanshi da yake ciki yace yaje ya kaiwa Bashir idan yaje yace masa ga gidansa nan ya dawo masa da abunsa, shima Balagan daya je bai’ samu Baba Bashir ba, sai Sulaiman ya bawa sakon. 
Bayan Balaga ya dawo Mai gida yacewa sauran yaransa su koma can gidansu, tambaya sukayi ko lafiya Mai gida yace zai canza sheka ne, sunce zasu bishi Mai gida yace baya bukatar kowa sai Balaga suje zai dawo bada jimawa ba! 
Daga Mai gida sai Balaga kadai suka tafi, Balaga ne yake tukin Mai gida yana gefensa, suma suka barbadi hanya sauka lafi inda kuka nufa.
Baba Bashir kuwa bayan ya dawo Sulaiman ya bashi sakon Mai gida warware takardar yayi ya duba, sannan ya bude wata “yar karamar takarda a ciki mai dauke da rubutu kamar haka. 
Amincin Allah, yardar Allah wadatar zuci su tabbata a gareka dan uwana, da farko dai ina maka fatan alkairi, sannan kuma ina neman yafiyarka akan duk abubuwan da suka faru tsakanina dakai, ni na yafe maka, Shalele ma ta yafe maka kuma ta yafewa danka, wannan takardar gidanka ne na dawo maka dashi, ubangiji ya hada fuskokinmu da alkairi, na yafe maka kaima ka yafemin abinda ya faru tsakaninmu, manta da rayuwar baya mu fuskanci rayuwa, sannan ka yafewa Shalele akan duk abubuwan da tayi maka a lokacin kuruciya. Daga dan uwanka na har abada! Nagode!Yana gama karanta wasikaryayi gaba ba tare da yayi magana da kowa ba, Sulaiman ne kadai yabi bayansa,  tafiya suke saman kafafuwansu har suka isa gidan Mai gida, Baba Bashir yaji tashin hankali fiye da tunanin mai tunani domin dai gida ba kowa, kuma a gidan babu abinda Mai gida ya cire kujeru k0 gado ko tsintsiya bai dauka ba, cikin damuwa Baba Bashir yace ina amfanin wannan rayuwa, abinda ya kamata ace ni babba nayi karamin 
kanine dana bashi tazara da shekaru masu nisan gaske shi ya fini tunani? Ya nuna min cewa ya ajiye kayan yaki, yabarmin gidana  shida “yar sa, ina suka tafi ne ya karasa maganar cikin hayaniya har wanda yake waje yana jinsa, hawaye ne suka gangaro daga cikin idonsa, 
Cikin marainiyar murya yace Sulaiman kirawo Mubarak, kiran wayar Mubarak akayi amma bai dauka ba, an kirasa so da yawa amma baya dauka, haka nan Baba Bashir ya hakura suka koma gida. 
Satin Shalele daya a gidan momy ta saki jikinta tana huddodinta, hankalinta kwance bata tare da wata damuwa, karatu shine abinda Mai gida ya turo Shalele tayi a garin jos, kuma Momy itace ta roka alfarma wurin Mai gida tace ya kamata suma a kawo musu Suleim ta gansu, sai Mai gida yace dama yana so tayi karatu domin dai batayi karatu a garinsu ba, sai dan kalmomi daya nuna mata saboda rayuwa, tou a gida ta iya rubutawa ta iya karantawa. 
Kamaladdeen shine yakai Shalele makaranta, bayan an mata interview, suka ajiyeta prmry 4. Tun a mota Kamal yake mata dariya wai katuwa da ita an ajiyeta a cls din yara, ita kuwa Shalele ko kallon arziki bai isheta ba bare na tsiya. 
Suna dawowa gida kuwa kowa ya kama gabansa, dan Shalele ta lura kamal yana da rainin hankali, ita dai tana zaune a saman maganar Mai gida karatu shi yake so tayi kuma zatayi harsai yace ta barshi haka nan. 
Kullum Shalele tare suke tafiya da Kamal ya ajiyeta a sch shi kuma ya wuce Office, Shalele ta maida hankali sosai karatu takeyi babu kama hannun yaro, 
Mubarak kuwa bai samu kwancnyar hankali ba saida ya tabbatar da Khadlja bata da ciki sannan ya samu natsuwa, tun daga wannan lokacin ya rike cream dinsa da mutunci baya mantuwa haka kuma baya tsallake. 
Yaran Mai gida kuwa a gidan Baba suka koma, Mama taji tashin hankali da taji labarin guduwar danta, wannan abu ya tada hankalinta ta shiga damuwa da rudani sosai ta nemi wayarsa amma a kashe, dan haka ta birkice tace ita dai bata zama neman danta zata cikin duniya, Baba yace babu inda zataje neman sa wallahi tunda ba yaro bane idan yaji uwar bari ya dawo gida. 
Dole Mama ta hakura, amma duk Gwaggo ta fita shiga tashin hankali dan ta tsorata da Mai gida kada yaje ya halakar mata da “yarjika, kuma duka a cikinsu babu wanda ransa ya bashi cewa Mai gida basu tare da Shalele, 
Mubarak kuwa da Baba Bashir ya fada masa batun Shalele hankalinsa ya tashi, kuma ya tattaro ya dawo nigeria, inma banda an daukesa sakarai ya za’ayi ma ayi masa wasa da aure saboda tsabar raini. 
Gaba daya Mubarak yabi ya tada hankalin kakaf zuri’arsu, duk wani wanda yake da alaka dasu Mubarak ya tada hankali ya hana gidansu Mama zaman lafiya ya ruda kowa ya hana 
kowa zaman lafiya da kwanciyar hankali, wai kamarshi nan da kansa matarsa, sirrinsa, wai shi matarsa za’a gudar masa da ita saboda tsabar iskanci. 
Duk inda ake tunanin za’a ga Shalele babu labarinta, kuma babu wanda tunanin sa da hankalinsa ya taba zaton tana jos, Mubarak yaji dacin wannan abu dan gani yakeyi kawai wulakanci yasa akayi masa haka. 
Mai gida babu inda ya sauke shekarsa sai a small london wato calaver, nan ya yada 
zangonsa kuma yaci gaba da huddodinsa daga shi sai Balaga hankalinsa kwance bayajin wata damuwa. 
Haka dai rayuwa taci gaba da tafiya, kowa yana huddodin gabansa, amma Shalele tana cikin damuwa ita dai ta gaji da zaman jos din nan haka, kuma tayi waya da Mai gida tace masa ta dawo? Mai gida yace A, a, 
lta dai zaman gidan baya mata dadi kwata kwata, ita momy bata da “yaya mata dama biyu ne kuma duk sunyi aurensu, kuma momy ba mazauniya bace ba daga ita har mijinta, 
saidai a barta gida ita da masu aiki maza da mata, sai kuma Kamal daya raina mutane, 
Yanxun gashi tayi j, s, c, e, da tana zuwa sch tana dan rage kewa amma yanzun kuma babu, islamiya ma sunyi hutu, tana kwance saman kujera tana game Kamal ya shigo da sallama shima ya kwanta a saman kujerar dake kallon Shalele. Shima wayarsa ya fiddO yana latsawa, yana kallon wayar yace Shalele kina facebook ne? Itama bata kallesa ba tace A, a, yace whatsapp fa? Banayi ta fada a takaice, gyara kwanciyarsa yayi sannan yace kinayin instagram ne? Shalele tace kai bana komai sai game, 
Dariya Kamal yayi tare da cewa yarinya kawo wayarki in kankaro miki girmanki, murmushi Shalele tayi tare da cewa karka karkaromin girman nan barni a haka, Kamal yace yarinya kawo kin samu saukin kadaici idan na tafi Office, Shalele tace na rika raka ka 
Office din, kallonta Kamal yayi sannan yace A, a, gaskiya bazanje dake Office dinmu ba, 
Shalele tace miyasa? Kamal yace haka nan, Shalele tace tou naji, daga haka babu wanda ya sake magana wa wani, kowa ya mayarda hankalinsa a wayarsa. 
Bayan wani lokaci Kamal ya mike yana cewa kafaryawo ta samu zakije ne? Da sauri Shalele ta ajiye wayarta tace zanje wallahi, dariya yayi yace tou ki shirya amma fa ba yau ba,jibi idan Allah ya kaimu amma wallahi hajiyata ki dauki wanka mai aji domin kinsan Allah gidan ubangida nane, 
Washe baki Shalele tayi tare da gyara zama dan Kamal yana zuwa da ita wurare sosai danta bude idonta, cikin zakuwa tace Allah ya biya Yayana karka damu saina kankaro maka kimarka, Kamal yace tou ki shirya da kyau yarinya, Shalele tace baka da damuwa. Fita Kamal yayi Shalele taci gaba da jin farin ciki sosai. 
Farin ciki sosai Shalele takeji, tana sakawa Kamal albarka, dan shine kawarta itace take rakasa anguwa, wani lokaci har zance idan zaije da ita yake tafiya tunda ta tabayin korafi wa momy tace dama kamal macene da taga gari sun rika fita yawo tare, tun daga wannan Iokacin yake tafiya da ita wasu wurare, momy tana da “ya “yanta biyu mata amma 
duksuna gidan aurensu. 
Washe gari da marece Kamal a gajiye ya dawo daga Office, yana shigowa palo zai wuce dakinsa Shalele tace Yaya zokaga kayan da zan saka gobe idan sunyi, ta karasa maganar tana murmushi, shima murmushin yayi tare da cewa dauko kizo nan in gani na gaji wallahi, 
Cikin kyarmarjiki ta koma daki ta dauko kayan ta kawo masa yana kwance ta ajiye a gabansa, a gajiye ya kalli kayan yace haba karki bani kunya mana, Shalele tace basuyi ba? Kamal yace ina sukayi fa? 
Cikin fushi Shalele tace to nidai sune karshe, Kamal yace bazai yuwu ba, yarinya so nake ki shako mana wuyan wani alhaji a wurin domin manyan zakakurai ne za”a tara a wurin wallahi nake fada miki, Shalele tace me akeyi ne? Kamal yace ina fada miki jirage biyu ya siya shine matar sa ta hada lafiyayen party dan tayasa murna, 
ldanuwa Shalele ta zaro tacejirgi biyu? A lokaci daya? Kamal yace ai a wurin akwai manyan mafiyoyin da suka fi shi, dan idanma suna wurin shi dan karamin kwaro ne, kedai Allah yasa wanda nake miki hasashe yace yana sanki yarinya kin warke, 
Tsaki Shalele tayi tare da daukar kayanta tana tafiya tana cewa ni wallahi nasha ma partyn aure ne, sai in mi a cikin taron maza inta raba idanuwa kamar nayiwa sarki karya? To na goben dai bazanje ba a tari gaba, Kamal yace wallahi karya kike sai kinje tunda kinyi niyya, fita daga dakin Shalele tayi tana gunguni. 
Da safe kuwa Kamal yana dawowa daga masallaci palo ya zauna yana kiran Shalele tana jinsa amma tayi mishi shiru, dan gajeran murmushi yayi tare da cewa zaki nemeni ai, da kanki zakice kina zuwa wani wuri wallahi idan dai bakije min taya mai gidana murna ba bazan sake zuwa dake ko ina ba saidai ki samu wani abokin badai kamal ba. 
Murmushi tayi tare dayin gyaran murya, sannan tace sallah fa nakeyi kaima dai Yaya, Kamal yace na dauka kina jinina kika kyaleni, tace haba na isa? Zanje insha Allah, yace tou Allah ya kaimu kina gama sallah isha‘i ki tabbatar kinyi wankanki da kinyi alwallah, kina gama sallah ki shirya. 
Shalele tace in Allah ya yadda, komawa tayi daki dan sararawa da baccin safe, Kamal 
kuma anan ya mike yaci gaba da baccinsa cikin natsuwa domin yau babu zuwa Office 
Shalele dai sai 11:04am ta farka bacci, Kamal kuwa tuni ya tashi ya fantsama gari zaije ya leko gidan Ogansa yaga abinda yake tafiya, ita kuma Shalele lokacin data tashi tuni an gyara gidan k0 ina fes sai kamshin “yan gayu ke tashi, kalaci tayi sannan ta kamawa Naja sukayi girkin abincin rana. 
Bayan sun gama suka gyara inda suka bata, Naja tayi wanke wanke, Shalele ta koma daki ta watse dukan kayanta domin neman fitaccin kaya, banda fitinar Kamal itafa duk a 
kayanta babu na banza domin dai momy komai mai aji take siyo mata da burgewa. 
Haka dai ta shiga ta fita ta zaliko kayan da zata saka tasan zasu burge idan ta shige a cikinsu, kuma zatayi kokari ta fentu komai zatayi sa cikin aji da kuma gogewa. 
Sai bayan magrib Kamal ya dawo a gigice domin ya gano zakunan kasa, a palo ya tsaya ya fara kiran Shalelejin bazata fito ba yasa ya shige Cikin dakin, cikin rudewa yace kai Shalele mutane suna da kudi a duniya, mutane suna fariya Shalele duniya kowa yayi kudi ina nan an manta dani, 
Shalele tace haba Yaya miye haka? Ka godewa Allah, Kamal yace wallahi kullum cikin godiyar Allah muke Shalele wani matashi na gani ya bude min idonauwa ya kada min gabana ya firgitani ya gigitani ya rudani, Shalele baki ga shegen yaron nan ba, yarone sosai amma kudi sunmishi shigar sauri, kai tsakanina da Allah yasa min ciwon dimuwa dakel na gano hanyar gidan, 
In gaya miki Shalele wallahl ko su taron abokan nasu sunsan Shl ubansu ne, yana taflya yana dire dire karkice dire dire irin na yara, ina miki nufin kudi ke ingizashi, kai Allah ka bamu sa‘ar rayuwa, motocinsa kawai kika kalla kinsan shi ba sakarai bane, ke yarinya dan gayu ne sosai yana zuwa wurin duk wani maroki ya koma wurinsa, tunda rana yake aman kudi har yanzun bai dakata ba wannan inajin aljani ne Shalele. 
Girgiza kansa yayi tare da cewa tashi kiyi wanka yarinya mata nacan suna baza duniyarsu Allah yasa da rabonmu, dariya Shalele tayi sosai dan Kamal ya bata dariya tace Yaya ka iya bada labari yace na anjima kece zaki fadawa momy ni nan iyakar abinda na gano kenan na dawo gida, idan ma muka koma dake kada ki nuna kin sanni yarinya dan wallahi kashe miki kasuwa zanyi, Shalele ta sake shekewa da dariya, amma batayi magana ba. Fita Kamal yayi daga dakin tare da cewa don Allah kiyi sauri kijijjika ki fito, Saida tayi sallahr isha’i sannan tayi addu’o’i ta shafa, cire kayanta tayi taje tayi wanka, amma tunda ta flto daga wanka gabanta ke faduwa, haka nan taji tana jin tsoron zuwa wurin amma a daskare takeyin shiri dan kar Kamal yace ta masa ba daidai ba, “yar kwalliyarta tayi bawai irin wannan mai mayar da mutane dodo ba, 
Mai pawder sai kwalli ta zirara a cikin idonta, sai dan man baki ta shafa, bata bukatar komai domin itama yanzun ta faso a cikin sahun boters, kayanta ta saka ta daura kallabinta daidai da zamani, takalminta ta saka sannan ta dauka jakarta da gyalenta ta fito palo, 
Cikin sauri Kamal ya fito yana balle maballin hannun rigarsa, ansar gyalen Shalele yayi yace kawo a nuna miki yanda “yan gayu sukeyi, wani iskanci yayi mata da gyalen yace mu tafi, Shalele tace haba Yaya sai kace diyar inyamurai? Kamal yace keych….wai da haka kike? Har yanzun dai kyauyen na nan cikin kanki, dan gajeran tsaki yayi tare da cewa da Allah malama ki bari, mu mune birni, mune idon gari, kuma mune kafar kare, haka ake yayi kuma haka zakiyi wallahi inba haka ba ince ban zuwa dake. 
Batayi magana ba sai tayi gaba Kamal yabi bayanta yana cewa Naja ki dafamin lipton karki manta, Naja tace to a dawo lafiya, basu bata amsa ba suka sauka. Ko a mota Kamal sai kara gargadin Shalele yake saura taje taga mutane ta gigice, ita dai tayi shiru bata bashi amsa, sai nuna mata yakeyi yanda zata rika magana kuma karta kuskura ta rika yawan dariya dan yawan dariya barar da girman mace yake, cewa yake Shalele ki rike sosai ki samu ki shako mana wannan yaron da nake baki labari dan wallahi duk wurin nidai shi kadai yafi burgeni Allah ma yasa bai tafi ba. 
Faduwar gaban Shalele ya karu sosai a daidai lokacin da suka iso wurin, motoci ne na 
tashin hankali gasu nan kwance a saman kamar fari a lokacin sanyi. 
Cikin zumudi Kamal ya fito tare da cewa fito Shalele, fita tayi Kamal yace uhum kalli wayayyin mata duk babu gyaluluwa suke ta harkokinsu, Shalele tace na gani, Kamal yace kai Allah wadaran naka ya lallace muje, Shalele tace nice lalatattar Yaya? Yace haba badake nake ba, tafiya suke amma Kamal sai sauri yake dan ya sake gani mutumin dazu. 
Shalele tace ka tsayani tou, ba tare daya tsaya ba yace ba nace idan munzo ba karki nuna kin sani ba, yana fadin haka yayi gaba abunsa, Shalele tabi bayansa da sauri, 
Katon hall ne wanda ya hadiye dubban mutane, an kawata wurin sosai da furanni masu burgewa da daukar hankali, an haska wurin da fararen fitilu sun haska wurin sosai kamar safiya, mutane ne da yawa a cikin hall ne maza da mata kowa yana huddodin gabansa. 
lta kuwa Shalele bayan Kamal tayi tabi da sauri tana tutture mutane, shi kuma kutsawa yake itama kara shigewa takeyi sosai, shi kuma burinsa kawai yakai gaban mutumin daya gigitashi dazu da rana. 
Fita sukayi daga cikin mutane suka gangare wata hanya daban shidai Kamal baisan Shalele tana biye dashi ba tafiyarsa kawai yake har suka isa wani katon palo inda a nan ne manyan mafiyoyin suke kamar yanda Kamal yake fada. 
Saida ya saita kansa sannan ya tura kofarya shiga, Shalele babu abinda ya dameta itama budewa tayi ta shige, cikin natsuwa ta rufe kofar bayan ta shiga, gyara gyalenta tayi daya rike a jikin kofa sannan ta juyo, Idanuwa ta zaro sosai iyakar ganinta, a lokacin da idonta ya sauka a kansa, yadan gicce saman kujera irin dai zaman nasu namasu kudi, murmushi yayi kadan a lokacin da idonta ya shiga a cikin idanuwansa,jikinta har kyarma yakeyi saboda tsoro da sauri ta juya ta bude kofarta fita da gudu har wayarta ta fadi amma bataji ba, Ehum Mubarak yace tare da tashi da sauri ya fito, 
Harta fara hawa saman step din data biyo taji babu wayarta, dan haka ta sauko da sauri dan dubawa, da tasan zata ga Mubarak da bata zoba, bayan tayiwa Mai gida alkawari idan kuma ya sake ganinsu a tare ya zatayi ne? 
Da gudu ta taho tana kuka, shima da saurinsa ya taho yana dubawa ta ina tabi ne? Jin ana tahowa yasa ta samu wuri ta boye, da sauri ya wuce yana waige waige, yana wucewa ta fita da gudu taje ta duba wayarta ta dauko, cikin sauri ta taho a daidai lokacin da Mubarak yake saukowa shi kuma, wannan karon kowa yaga kowa amma a tunanin Shalele bai ganta ba ta sake boyewa. ‘Dan gajeran tsaki yayi hade da murmushi, saida yazo daidai wurin yace taso, ba tare daya kalli wurin da take boye ba yadai mika hannunsa ne, shiru tayi kuma bata tashin ba, kallon wurin da take yayi sannan ya sake cewa taso nace mana. 
Kin tashi tayi, matsawa yayi yajawota daga wurin, cikin hargowa tace da Allah malam cikamin hannu, Mubarak yace bazan cikadin ba, kiciniya ta farayi Mubarak yace saurara me kikeyi haka? Ni kasarmin hannu, Mubarak yace wallahi bazan sakeki ba, ashe baki da 
hankali saboda dodewar lissafi kika zo jos da izinin wa kika zo ma? 
Jinjina kansa yayi cikin bacin rai yace muje, muje wallahi yau zakiji ajikinki sai kinsan kin tafi da aure na shekara biyar saboda kin daukeni dan iska, cizon hannun sa Shalele tayi sosai harsai da kanta ya rika kyarma dan tabbatar da Mubarak ya cizu, Mubarak yace duk kiyi damarki ta yanzu ce,janta yayi suka koma ciki, wayoyinsa kawai ya dauka yace musu saida safe. 
Kamal cikin tashin hankali ya tambayi uban gidansa me kanwarsa tayi ne? Ya tambayar masa Mubarak kafin ya fita, kallon Kamal yayi tare da cewa kayi hakuri yana zuciye yanzun idan wani yayi masa magana komai zai iya faruwa. Tashi Kamal yayi da gudu yabiyo Mubarak domin shine mutumin da yake bawa Shalele labari ya kuma abu zaizo da 
cimimiya haka? 
Da gudu ya biyosu a lokacin har sun isa bakin mota, Kamal yace Shalele,juyowa tayi amma batayi magana ba domin itama ranta a bace yake, cikin daburcewa yace ina zakije ne? yana maganar ne cikin nuna tsoro, ko saurarensa Mubarak baiyi ba ya kurmusa Shalele 
mota, shima ya zagaya ya shiga yaja suka tafi. 
Kamal baisan yanda zaiyi ba dole ya hakura ya koma wurin mai gidansa amma yana cikin tashin hankali wane bayani zaiyiwa momynsa game da Shalele?. Oho, 
Dukansu su biyun zuciyoyin kowa ajagule, amma ran Mubarak yafina Shalele baci wato yana mata ma magana saboda tsabar rashin kunya waishi take cizo,jinjina kansa yayi tare da cewa wallahi saina rama.  kika cijeni ko? Zan miki yanda kikai min kiji idan da dadi. 
A bakin get din gida ya tsaya, saida yayi horn sannan ya kama hannu Shalele yayi mata cizo irin wanda tayi masa, a daidai lokacin da aka bude get din ya shiga, yace wallahi yau 
zakiji azabar da naji bayan bakinan. 
Shalele kukan cizon ta farayi, Mubarak yaceji rashin kunya nida kika cijeni’ kuka nayi? Ai tunda dai kina shawa’ar kuka yau zakiyi shi harsai kinyi baccin wahala, 
A kofar palo yayi parking sannan ya kashe motar, wayoyinsa yace ta daukar masa, kai tsaye tace bata dauka, yace tou bari in dauka fita muje ko a mota zaki kwana? Shiru tayi ta 
fita, fita yayi shima ya wuce ciki, bayanshi tabi tana gunguni. Murmushin mugunta yayi tare da cewa duk lokacinki ne zamu hadu a ciki, palo taja tayi tsaye, ba tare daya juyo ba yace taho, kin tafiya tayi, haryanzun bai juyo ba yace idan kika kuskura na sake dawowa wallahi bazakiji dadi ba gara ki taho kila ma in miki hakuri bazan 
miki azaba ba, a daidai lokacin daya turo kofa ya shige, 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *