HARSASHEN SO
CHAPTER 33
Daurewa Shalele tayi taje ta samu Mai gida cikin kuka tace Mai gida kanajin Mubarak zaiyi tafiya don girman Allah kayi hakuri ka anso min yaran nan don Allah Mai gida, ta karasa maganar tana daga hannayenta duka biyun.
Gyara zama Mai gida yayi sannan yace Shalele kiyi hakuri, ki tattara al’murranki duka ki barwa Allah, banyi haka dan na wulakantaki ba, nayi haka domin na nema miki mutuncinki a wurin Mubarak.
Kinga yaron nan, san da kike masa wallahi baya miki wanda kike masa, ko aurenki da yayi saboda wata manufa tasa ta daban, to Allah ya kaddara akwai aure tsakanin ke dashi,
Boka ya fadamin babu aure tsakaninki da Mubarak amma ubangiji ya nuna ikonsa domin musan shine Allah, ya rubuta haka kuma kikayi aure da Mubarak, Allah ya nuna ikonsa ya baki ciki kuma shi Mubarak baya san aihuwa,
Duk duniyar nan baki da kowa daga Allah saini, duk ranar da na kwanta na mutu zaki shiga gararin rayuwa, wani saboda idona yake raga miki, daga ranar da kasa ta lullube fuskata a ranar zaki gane ina da muhimmaci.
Baki da uwa, baki samu soyayyar miji ba yanda ya kamata, ga “ya”ya kin haifa, kika tashi haihuwa domin ya wulakanta ki ya nuna miki baki da matsayi baki kai mace ba a wurinsa, ko pampers bai siyawajarirai ba, ba dan baya da kudin ba domin Mubarak yana da kudi yanda hankali baya dauka, kudinsa sun wuce dukyanda tunani yake zato, haka kuma kika tashi aihuwa yace bazaje asibiti ba,
Da kika sake masa magana yace idan kikaje ma bai yafe miki ba, kinga idan kin mutu baya da asara, da yana sanki zaiji tausayinki yakaiki koda kuwa baya san abinda zaki aifa, shin rayuwa zata yuwu haka? Ke a wulakance “ya “ganki a wulakance yaushe zakiji dadin rayuwa Eye? Ki barshi da “ya “yan
Shiru Shalele tayi batayi magana ba, Mai gida hakuri ya kara bata tare da nuna mata ta cire komai a ranta taje kawai taci gaba da karatunta wata rana sai labari,
Mubarak kuwa ya yanke shawarar dauko mai kula da yara amma wani abokinsa ya tsoratar dashi ta hanyar fada masa masu aiki dukan yaran sukeyi suyi ta gana musu azaba, idan kuwa ya dauko za’ayi ta azabtar masa da yara har ciwon zuciya ya kamasu suna yaransu.
Ciro wayarsa yayi ya nuna masa wata mai aiki dake dukan wani dan jariri sai kuka yaron yake, ta matse masa hanci tana mummurde masa hannu sai ihu yaron yakeyi ya hada zufa sai majina ke fita daga hancinsa, da sauri Mubarak ya dauke idonsa tare da kallon “ya “yansa yace wallahi duk wanda yayi ma “ya “yana wannan iskanci saina kasheshi.
Aidai an cuceka, Mubarak yace gaskiya Allah ya kyauta, sun dade suna fira daga baya abokin ya tashi ya tafi, Mubarak yana zaune a wurin cikin bacin rai, tsaki yayi sannan ya dauki wayarsa ya kira Shalele amma tanaji tana gani taki ta dauka.
Baiyi zuciya ba ya sake kiranta amma ko kallon wayar batayi ba, sako Mubarak ya tura mata cewa‘ kin bata wayanki, baki da girma sainajiki, baki da tunani Suleim kinsan Allah yaran nan barinsu zanyi can ma idan sun mutu babu abinda ya dameni,
Tana gani ko reply batayi ba, tashi yayi ya matsa kusa da yaran ya cire musu kayan jikinsu
suna wani irin kuka yayi musu video ya turawa Shalele don ya tada mata hankali, hankalinta kuwa ya tashi domin uwa da da sai Allah, hankalinta ya tashi sosai amma bata bawa Mubarak amsa ba.
Mubarak yace ya kika ga “ya “yanki ne Eye? Nasan kinji damuwa zuciyarki tana nan dauke da bakin ciki, yau nasan bacci saiya gagari idanun wata yarinya. .
Hawaye Shalele ta farayi amma bata bawa Mubarak amsa ba, shi kuma dariya yayi sosai tare da ajiye wayarsa ya tashi, wanka yayiwa yara ya saka musu kayansu sannan ya basu madara suka sha, saida sukayi bacci sannan ya sake dawowa wurin Shalele.
_Wata mata tana neman “ya “ya nace mata tazo ga “yan biyu_ _Hahaha, tace min bata da abin basu nace ta rika dura musu koko_ _Shiru_
Sai tace min bata da koko, ni kuma dai nace ko tuwo ne ya samu ta basu dan taimakawa
rayuwarsu_ _Shiru_ _Suna kuka suna witsilniya na kamo su kamar yanda ake kamo kifi na dankawa matar_
Kukan Shalele ya kara yawa, saida ta goge hawaye sannan taci gaba da kallon abinda
Mubarak yake rubutawa.
_ldan kin shirya zaki ansa yaranki kimin magana in baki adireshin matar,shin ko wane
kauye ne ma matar nan take?_‘
_Oh bara dai na tambayi Mai nasara shine yakai su, ni addu”a daya nakeyi ma Allah yasa
kada a rika basu kiwon shanu idan sun girma_ . Cikin bacin rai Shalele ta rubuta, _lna abinda ya dameka? Koma noma zasuyi karewar kiwon shanu._ Wata irin dariya Mubarak yayi sosai dan yasan ya latsowa Shalele inda zai mata ciwo, _Oho dai bara inyi sallah yarinya, tunda dai baki san “ya “ya anbawa masu mabukata._ Tashi yayi yaje yayi alwallah don bada farali.
Shalele kuwa fadawa Mai gida abinda Mubarak yace tayi, Mai gida yace manta dashi
karya yakeyi, ta nuna masa vidion yaran suna kuka duk da yaji babu dadi a ransa amma saiya danne zuciyarsa yace karya yakeyi ba kuka sukeyi ba, saida dai Mai gida ya samu ya kekashe zuciyar Shalele hankalinsa ya kwanta.
Bayan chat dinsu da Shalele da kwana biyu Mubarak yabar nigeria dashi da yaransa dan zuwa kasar hollond, duk wanda yaga Mubarak da yara sai yayi dariya, dashi da Mai nasara suka tafi dan ya rika kama masa.
Hotuna Mubarak yayiwa yaran ya turawa Shalele cewa gasu nan suna miki bye na tafi dasu in bada su sadaka a can,
Murmushi Shalele tayi dan taji dadin ganin yaranta cikin kyakyawan rayuwa, da ganinsu yaran suna cikin koshin lafiya, kuma an musu gaye Mubarak ya zuge yaransa cikin kayan sanyi sunyi kyau sosai.
Saida Shalele ta nunawa Mai gida cikin farin ciki, shima yaji dadi amma bai nunawa Shalele,ba saiya bata wayar yace da kyau, ansar wayarta tayi ta koma daki ta nunawa Momy, itama taji dadi su Shalele sai babarniya akeyi an kasa zama wuri daya saboda farin ciki.
Haka rayuwa taci gaba da tafiya, kwanci tashi babu wuya a wurin Allah, Shalele ta gama wanka lafiya, ita kuma Momy ta fara shirin tafiya dan tace Shalele na gama wanka zata tafl,
Shalele taji dacin rabuwa da momy sosai, Mai gida da kansa dashi da Shalele da Balaga suka kai Momy gidansu Mama, Mai gida yayi godiya sosai kuma ya cika Momy da sha tara ta arziki,
Mama tacewa Mai gida yabar Shalele tayi musu kwana biyu amma yace sam baisan labarin ba, a gidan suka yini harda Baba bashir kowa dai yana kallon kowa amma babu gaisuwa a cikinsu,
Saida su Mai gida sukayi magrib sannan suka bar gidansu Mama, amma har suka taho basu hadu da Baba ba.
Mubarak kuwa tun ranar daya turawa Shalele hoton yara bai sake chat da ita ba, amma yana tunani kamaryayi aure saboda yaran nan, ita kuma Khadija taki ta biyosa juyin duniya yayi tace wallahi baza taje ba kukan yara ya hanata bacci babu dalili.
Shalele kuwa ta koma makaranta, mate dinsu da sukayi j s c e tare yanxun suna ss2 amma ita a ss1 aka ajiyeta, anan abuja take karatunta Balaga yake kaita ya daukota,
Itama tanajin damuwa rashin chat da Abak, dan tana so taji lafIyar su Al’ Hassan kullum
dai Clki duba status dinsa takeyi shima saboda ya kona mata rai yakeyin status da yaran. Sun girma sunyi wayau sosai, haka nan zai musu dan vidio mai burgewa yayi status dasu,
Yauma yayi status dasu ya saka daga kasan vidion da yayi status ya rubuta ranar koyon zama, irin tangal tangal da yaro yakeyi idan bai iya zama ba ya fadi kasa kurum, dariyar Mubarak taji a cikin vidion amma bataji maganar da yayi ba status din ya kare,
Download tayi itama tayi status, status dinta yana hawa Mubarak ya gani vidio daya saka ne ta saka bai duba ba, amma har a ransa yaji farin ciki kuma haka ya tabbatar masa har yanzu Shalele tana sansa tunda har tanayin abinda yakeyi.
A gajiye ta dawo daga sch, wanka tayi taci abinci sannan ta dauki wayarta ta hau online, tana hawa ta fara dubawa ko Abak yayi sabon status, yakoyi yau hadashi a cikin dan vidion da yakeyi, daga shi haryara suna cikin farin ciki, kara dauka tayi itama tayi status, murmushi Mubarak yayi tare dayin alkawari a ransa bazai sake saka status ba.
Tashi yayi domin yara sunajin yunwa, madara ya basu suka sha yayi musu wanka, suka kwanta bacci.
Tun daga wannan ranar Mubarak bai sake saka status dinshi da yara ba, yama daina saka komai kwata kwata, saidai Shalele tahau idan taga yana online hankalinta yana kwanciya tasan dai lafiyarsa qalau tunda har ya samu lokacin chat.
Haka dai Mubarak yaci azaba wurin kula dasu Al ” Hassan, da kansa ya koya musu zama har suka iya, watansu bakwai suka fara tashi tsaye domin suna da wadata kuma suna samun kyakywan kulawa, kuma haryanzun bai dawo ba, saima gaba yake karawa.
Khadija kuwa ta gaji da jiran zuwan Mubarak dan itama kanta yanzu bata san inda yake ba, bata waya dashi kwata kwata kuma ko tayi masa magana a chat baya bata amsa, saboda abinda tayi masa dashi da yaransa ya kona masa zuciya, ashe da Shalele mutuwa tayi da bazata rike masa yaransa ba,
lta kuma Shalele baiga laifinta ba, domin yasan bayinta bane yin Mai gida ne, kuma bai wani rike abin a ransa ba, kuma yayi alkawari duk ranar da yazo nigeria zai kaiwa Mai gida yaran idan sun yadda su kwana dan wani tashen kiuya sukeyi basu yadda da kowa sai Mubarak domin tunda suka bude ido shi suka sani sai kuma Mai nasara, amma shi yana dawowa nigeria lokaci lokaci,
Wani irin katon daji ne babu abinda ke cikinsa sai namun daji masu halakarwa, da gudu Shalele ta taho Mubarak baisan abinda takewa gudu ba amma yabi bayanta da gudu yana kiran sunanta,
Gudu takeyi sosai Mubarak yana cewa ki tsaya zaki fada a rami fa, tuntube tayi ta fada cikin wannan katon ramin da Mubarak yake magana, da sauri ta rikejijiyar wani icce tana kuka, cikin tashin hankali Mubarak ya riko hannunta da sauri dayan hannun kuma ya rike wata igiya dashi dake daure a jikin wannan itaciyarda Shalele ta rike jijiyarsa.
Sulbewa Shalele tayi daga rikon da Mubarak yayi mata tayi kasa, wani irin ihu Mubarak yayi tare da fizgo igiyar daya rike yabi Shalele,tatafi sosai sannan kuma wani icce ya sake tallabeta, a daidai nan ya igiyar da Mubarak yajawo ta tsaya,
Cikin wahala yace Shalele rike kafata kinji karki fada mutuwa zakiyi, kin kallonsa tayi kuma bata rike kafarsa ba, cikin damuwa yace kawo hannunki ya sadda kansa kasa yana kallon Shalele, cewa yakeyi ki kama hannuna nace k0? Shalele taki ta rike Mubarak,
Zabkewa lccen yayi saboda sun masa nauhi, Shalele ta sake tafiya….luuuuuu, salati Mubarak yayi tare da sakin igiyar yabi Shalele, saida ya rikota hankalinsa ya kwanta amma hannunsa yana rike ajikin iccen daya gagara daukarsu.
Kuka Shalele takeyi, cikin damuwa Mubarak yace miye ne? Shalele tace yunwa nakeji, Mubarak yace yunwa a wannan lokacin? ‘Daga masa kai tayi cikin yanayin wahaltuwa, dan lumshe idanuwa Mubarak yayi cikinjigata ya saka hannunsa a aljihun wandonsa dakel ya ciro biscuit ya mikawa Shalele, ansa tayi ko taunawa batayi taci gaba da hadiyewa biscuit Din tana ku ka.
Kallonta Mubarak yayi tana makale a jikinsa ga icce sai lilo yakeyi saura kadan ya kare su fada ciki su mutu, murmushi Mubarak yayi sannan yace wa Shalele toki daina kuka mana, shiru Shalele tayi, Mubarak yace in kara miki zaki kara cin biscuit din ne?
Jin iccen ya kara kasa sosai yasa Mubarak yin karfin hali ya riko wannan igiyar daya saki daga farko, a wahalce yake hawowa sama dan fitowa daga cikin ramin, kukan Al “Hussan ya farkar da Mubarak daga wannan mummunan mafarki da yakeyi, salati Mubarak yayi tare da goge zufar dake tsiyaya daga goshinsa,
Awahalce ya sauka daga saman gadon ya nuFI toilet saida yayo alwallah sannan ya fito sauko dashi yayi daga saman gado yaja hannunsa ya nufi toilet dashi wanka yayi masa sannan suka futo,
Tea ya hada masa ya ajiye masa a gabansa yace yi sauri kasha zanje inyi sallah, bata fuska yayi yana kallon Mubarak kamar zaiyi kuka, murmushi Abak yayi tare da dan turo lebonsa na kasa, yace bazan dade ba yanzun nan zan dawo kaji ko? Jinjina kai Al” Hussen yayi Mubarak ya wuce da sauri,
Harya kusa fita yajuyo yace kada kayi banna fa idan ka gama kayi zaman ka a wurin nan kaji ko? Kara daga kansa yayi cikin gamsuwa,
Fita Mubarak yayi cikin damuwa, saida yaje yayi sallah sannan ya fara kiran wayar Shalele domin dai yana cikin tashin hankali saboda mafarkin da yayi da ita gab da asuba.
Yayi mata kira yafi a kirga amma Shalele bata dauka ba, saboda bata kusa da waya. Baba Bashirya kira shima bai dauki wayarba baya kusa da wayar
Kai tsaye ya kira Mai gida, babu wani bata lokaci ya dauka! Gaisawa sukayi dashi sannan yace dan Allah k0 Shalele tana kusa? Mai gida yace bata nan tana makaranta, Mubarak kallon agogonsa dake daure a tsintsiyar hannunsa yayi sannan yace don Allah Baba idan ta dawo don Allah don Annabi ta kirani, Mai gida yace to babu damuwa, godiya Mubarak yayi sannan yace su Al” Hassan suna gaishe ka, Mai gida yace ina godiya nima ina gaishe su.
Godiya Mubarak yayi sannan ya ajiye waya, da sauri ya nufl gida dan ya lallaba Al” Hussen ya koma bacci kada ya tashi dayan su dameshi.
Lokacin da Mubarak ya koma gida har ya gama shan tea inshi ya koma saman gado ya kwanta amma baiyi bacci ba, Mubarak yace ba nace kada ka tashi a wurin ba saina dawo,
kallon Mubarak yayi yana murmushi,
Shima Mubarak murmushin yayi tare da hawa saman gadon yace don Allah kayi bacci kaji k0? Ya karasa maganar yana jawosa cikin jikinsa, gwaranci Al ” Hussen ya farayiwa Mubarak, dariya Mubarak yayi tare da cewa to naji yi bacci.
Lumshe idanuwa yayi alamun bacci, riritashi Mubarak yaci gaba dayi har bacci ya dauke sa. Shima yanajin bacci sosai amma saboda damuwa ya kasa komawa.
Tunanin mafarkin da yayi yaci gaba dayi abun ya tsaya masa a zuciya lallai cikin satin nan saiya koma nigeria duk ma abinda za’ayi saidai ayi amma wallahi dawowar Shalele gidansa ya zama dole saidai duk masifar da za”ayi ayi kuma ya shirya ma duk ma abinda zai faru.
Kila ma Shalele tana cikin damuwa shi yasa yayi mafarkinta, k0 kuwa wasa takeyi da aurensa shi yasa zata fada rami ta mutu? Wata zuciyar tace masa A, a, Shalele ba zatayi haka ba, to yunwar me ‘takeji ne Eye? A gigice yayi ta fassara mafarkin wanda baisan abinda yake nufl ba, yadai dauka alkawari a satin nan zai koma nigeria in Allah ya yadda kuma zaije ya taho da matarsa, idanma saboda yara yasa Baba Mansurya tafi da ita zaici gaba da kula da yaransa amma babu wani maganar ta sake haihuwa wannan ma mamarsa tayi.
Shalele kuwa bayan ta dawo makaranta Mai gida yace ta kirawo Mubarak, tace Mai gida kuma kace na daina kiransa na daina daukar wayarsa idan ya kirani, Mai gida yace Eh amma yanzu nace ki kirasa, Shalele tace to, “
Saida tayi wanka taci abinci sannan ta fara kiran wayar Mai gida Abak. Saida wayar tayi ringing ta gama sannan ya kirata, dauka tayi suka gaisa, Mubarak yace ya karatu? Alhamdulillah, Mubarak yace kina so in dawo k0? Shalele tace A, a, Mubarak yace to amma ai kinayin mafarki na?
Shalele tace ni bana mafarkinka kuma banso ka dawo dan rayuwa tafimin dadi a haka idan baka nan, tunda na dawo gidanmu na manta da bacin rai sabanin lokacin ina tare dakai, Mubarak yace nine nake baki damuwa? Shalele tace sosai kam, Mubarak yace to kiyi hakuri in Allah ya yadda zan zamar miki garkuwa,
Nayi alkawari babu ke babu sake shiga damuwa matsawar ina numfashi kiyi hakuri nayi miki rainon yaranki suna tafiya ma, kuma kullum sai sunce Mama, ai kin gode ba?
Shiru Shalele tayi Mubarak yaci gaba da cewa kiyi hakuri don Allah
Shalinina …………. insha Allah cikin satin nan zan dawo nasan zakiji dadi idan kika ganni k0?
Murmushi Shalele tayi amma batayi magana ba,
Mubarak yaci gaba da cewa, kice wani abu mana kin banni sai surutu nakeyi kamar wani sakarai. Kashe wayarta tayi ba tare data sake cewa komai ba, shima bai sake kiranta ba ya
fita daga wannan lamarin.
Shalele kuwa fadawa Mai gida yanda sukayi da Abak tayi, Mai gida yace to kinga wannan yaran har abadan duniya sun zauna a cikin ran Mubarak saboda yayi shakuwa dasu kamar yanda uwa take shakuwa da danta, sun shiga ransa sun zauna sosai baya san kukansu baya san bacin ransu, sunci tare sun sha tare yayi musu wanka yasan fushinsu yasan farin cikinsu, yanda uwa bata san bacin ran danta haka zakiga bazai so bacin ransu ba.
Amma a da yace baya san haihuwa, da kina tare da yaran haka zaiyi ta kuntata muku dake dasu, yasan her a bada bazasu shiga gararin rayuwa ba saboda suna tare da uwa, ita uwa tana iya tsotse ko wane dafi saboda farin cikin “ya“yanta, amma tsabanin haka saiya fiki jin bakin ciki idan suna cikin damuwa saboda shine ya rayu dasu, kiga wane dalili yasa bai bayar da yaran gidan raino ba ya rikesu a hannunsa?
Mai gida yace saboda yana sansu, kuma karki kuskura ki koma gidansa saikin fada masa kina san ki haifa yara domin ke kadai kike a wurin babanki kina san ki samu dangi, idan kuma bai yadda ba sai kice to ba komai ya sakeki Allah ya hada kowa da rabonsa na alkairi.
Shalele tace to, Mai gida yaci gaba da cewa karki wani ji tsoro sannan kuma kar kiyi fargaba kinji k0? Idan kuwa kika tsaya sakarci da san zuciya kika biyewa soyayya haka zaki tsufa ki mutu ba tare da kinbar wanda zasuyi miki addu”a a rayuwa ba,
Shalele tace to, haka Mai gida yayi ta mata lissafl yanda zata fadawa Abak idan ya dawo, tace to babu komai in Allah ya yadda.
Yaune ranar da Mubarak zai dawo nigeria, dan haka tunda safe ya tashi yayiwa yara wanka sukayi kalaci ya shiryasu cikin shiga mai kyau da daukar hankali, saida ya game musu sannan yace to ku natsu zanyi wanka duk wanda ya tashi anan bazan tafi dashi ba,
Bin Mubarak sukayi da ido duka fuskokinsu kamar zasuyi kuka, Mubarak yace miye to? Dukansu kara bata fuska sukayi sosai suna kallonsa, murmushi Mubarak yayi ba tare da yayi magana ba yayi gaba dan ya kusa makara jirgin 9 zasu tafi.
Babu wani dadewa yayi wanka ya fito, a gaggauce ya shirya shima cikin shiga mai daukar hankali ya fito gwanin burgewa, palo ya fito inda suke zaune, kusa dasu ya zauna yace kozo muyi hoto.
Duk iya shege yaran nan sun iya, sun koyi fi”ili na hoto, suna cikin nishadi suka dauki hoton, Mubarak ya turawa Shalele yace kiyi nana addu”a zamu taho.
Yana tura mata ya kira Khadija ya fada mata cewa zai taho, a ciki ciki tace Allah ya kiyaye, godiya yayi tare da kashe layin, tashi yayi yace musu ku tashi mu tafi,
Saukowa sukayi suka biyo bayan Mubarak yana gaba suna biye bayansa, dugwi dugwi suna tafe cikin burgewa gwanin sha’awa! Saida yaje bakin mota ya tsaya dan jiransu su iso,
saida ya saka su mota sannan ya bude ya shiga suka nufi filinjirgi.
A fllin jirgi ma haka yayi ta daukarsu hoto, ajirgi ma haka, saida ya gama ya tattara duka hotunan ya turawa Shalele shidai komai yanayi dan ya burge Shalele amma idan ta gani saita basartana daijin dadi sosai a ranta yara gaba daya da babansu suke kama basu wani yi kama da Shalele ba, shi kuwa Mai gida haushi yakeji da “ya “yan suka biyo ruwan buzaye.
Karfe 9:15am jirginsu Abak ya dago dan dawowa gida, Shalele kuwa yau tana cikin farin ciki ko ba komai zata ga “ya “yanta amma ta boye taki yadda Mai gida ya gano tana murna.
Baba Bashir kuwa tunda Mubarak ya fada masa zasu taho ya bugawa Baba waya cewa gaskiya asan abinyi idan Mubarak ya dawo lallai a zauna a mayar masa da matarsa shi kenan ayi hakuri komai ya wuce, Baba yace to Allah yasa ya dawo lafiya. Baba Bashir ya amsa da amin.
Shalele kuwa ko a makaranta ranta dauke yake da farin ciki, sai kara duba hotunan da Mubarak ya tura mata takeyi, amma idonta yafi zama a saman hoton Abak wai hausawa sunce so hana ganin laifi duk abinda kake so da gaskiya baka taba ganin aibunsa.
Hmm