HARSASHEN SO THEND

HARSASHEN SO 





CHAPTER 34 THEND




Suna tashi sch bata tsaya wani bata lokaci ba ta wuce gida, 
Lokacin data koma babu kowa a gidan sai Balaga, 
Saida tayi wanka taci abinci sannan ta tambayi Balaga inda Mai gida yaje, Balaga yace yana gida kuma yace idan kin dawo ki sameshi a gidan. 
Shalele tace to bara na gama abinda nakeyi saika ajiyeni, Balaga yace to. 
Komawa tayi ciki taci gaba da uzirinta, saida ta gama sannan ta fito, Balaga ya dauketa dan 
zuwa gidan Baba. 
A bakin get ya ajiyeta ya wuce, ita kuma ta shiga ciki, dakin gwaggo ta fara zuwa suka gaisa, 
sannan ta nufi dakin Mama. 
Da sallama ta shiga, Mama tayi mata sannu. Shalele ta amsa, wuri ta samu ta zauna tana 
cewa Mama ina Mai gida ne? Mama tace baizo nan ba. 
Shalele tace kuma Balaga yace Mai gida yana nan shine ma yace min Mai gida yace inzo 
nan idan na dawo daga makaranta. 
Mama tace to zaizo din ki jirashi, Shalele tace kai ni gaskiya bazan wanijira ba tafiyana 
zanyi idan sun dawo na dawo. 
Murmushi Mama tayi sannan tace ki kiyi hakuri fa, Shalele tace kai wallahi bazan jira ba, ta 
karasa maganar tana mikewa tsaye. Mama tace ki gaida gida, Shalele tace to ta fice daga gidan, napep tahau ta koma gidansu, 
Mai gida kuwa bai dawo ba saida dare sosai sannan ya dawo dan a lokacin ma har Shalele 
tayi bacci, zama yayi a palo yasha sigarinsa sannan yaje ya kwanta. 
Da safe kuwa bayan Mai gida ya dawo daga masallaci sallah asuba, waya yayiwa Shalele 
cewa idan ta gama abinda takeyi ta Shirya ta samesa a palo. 
Babu wani dadewa ta gama ta fito, a pale ta samesa yana kalaci itama kalacin ta zauna 
tayi, Mai gida ya rigata gamawa yace idan kin gama ki sameni a waje. 
Tana gamawa dakinta ta koma ta dauko wayarta da hijabi ta fita, a mota ta samu Mai gida dashi da Balaga itama ta shiga Balaga yaja suka tafi. 
Tafiye suke a mota a cikinsu babu mai magana kowa yayi jigum babu mai cewa wani abu har suka isa gidan. 
Motoci ne sosai aka ajiyesu masu kyau da tsada bawai wani parking din kirki akayi ba kamar dai an ajiyesu irin ana sauri haka, ganin motocin nan ya tabbatarwa da Shalele Mubarak ne a gidan. Harta kagara su shiga dan ta gansa, amma Mai gida sai wani bata 
lokaci yakeyi yana gaisawa da mutane. 
Ya dade yana gaisuwar tare da jawo fira ta daban, saida ya gama sannan ya wuce, Mai gida 
yana gaba Shalele tana biye a bayansa, Balaga kuwa yana mota bai fito ba. 
Palon Baba suka nufa, Baba Bashir, Mubarak, twins, Mama, Gwaggo sune a palon sai Mai 
gida da Shalele da suka shiga yanzun, 
, tunda suka shiga palon Mubarak yake kallon Shalele da wutsiyar 
idonsa waishi a dole sai ya nuna shi yana da aji. 
Suma wuri suka samu suka zauna kamar yanda suka ga kowa ya gurfana a kasa Baba ne 
kadai zaune a saman kujera, amma dukansu kowa a kasa yake kamar masu neman gafara. 
Mama ina kwana, Shalele ce take gaisheta, amsawa Mama tayi sannan ta gaishe da Gwaggo, ta gaishe da Baba sannan ta gaishe da Baba bashir, ya amsa cikin jin dadi amma bata gaishe da Abak ba. 
Mai gida kuwa Baba da Mama da gwaggo kawai ya gaishe , amma bai gaishe da Baba bashir ba, bayan ya gama gaisuwa Mubarak ya gaishe shi ya amsa dai sama sama. 
Gyara murya Baba yayi sannan ya fara magana kamar haka, Mubarak meke tsakaninka da Shalele ne? Mubarak yace babu komai gata nan ka tambayeta, kallon Shalele yayi tare da 
cewa ke nayi miki wani abu ne? Ko inda yake bata kalla ba sannan kuma batayi magana ba. 
Baba yace kana santa kuma zakaci gaba da zama da ita a matsayin matarka ne? Mubarak yace Ey, Baba yace to idan dai kana santa ka dauki matarka ka tafi”: da ita, sannan kuma idan har kuna san zaman lafiya ku manta da matsalar iyayenku domln dai ‘tun kafin fitinarsu tayi girma nayi kokari wurin ganin na dakatarda wannan matsalar amma abun ya fassakara. 
Gyara zama Shalele tayi amma batace komai ba, Baba yaci gaba da nasiha wa Mubarak saida ya game tas sannan Mai gida yace to Baba ai itama Shalele a tambayeta ko tana ra’ayinsa kuma tanasan ta sake zama da Mubarak? Kada a shiga hakkinta. 
Mama tace tana sansa kaima ka sani ni na sani kowa ma yasan haka, Mai gida yace Mamana babu ruwanki a maganar nan so nawa kake san abu kuma kazo ka daina sansa 
kika sani yanzun ko ta canja sheka ne? Ke Shalele kiyi magana kar a cuci ki mana. 
Gyara baki Shalele tayi amma batayi magana ba, daga idonta tayi ta kalli Murbarak, kyakyawan murmushi yayi mata amma baice komai ba, dauke kanta tayi daga kallonsa sannan ta kalli Mai gida, hade rai Mai gida yayi kamar yaga bala’i, murmushi Shalele tayi da 
gefen bakinta sannan tace Mai gida gaskiya ka fada, 
Ni na soke aure a tsarin rayuwata, kuma koma ina san aure a yanzu badai da wanda kuke magana ba, ni banma san saboda shi aka tara mu anan ba ai da banzo ba na batawa kaina lokaci ba. 
Baba yace wane dalili yasa haka ne Eye? Shalele tace saboda ni a yanzun nafi jin dadin rayuwa ni daya, a da kuma nayi yarinta ne shi yasa nayi ta hauka sai yanzun da hankali yazo na gane ashe nayi kuskure saboda yanzun na gane shi Mubarak ba irin tsarin namijin da nake so bane, 
Murmushi Mubarak yayi ba tare daya kalli Shalele ba kuma baice komai ba, amma yasan Shalele taci masa fuska, Baba yace to mu sasanci kadai ne namu, maganar rashin tsarinsa bai mlki ba wannan tsakaninku ne, idan yaji yana iya sahale miki aurensa dake saman 
kanki sai ya warware kije ki sami irin tsarin namijin da kike so. 
Mai gida yace to gaskiya dama auren aka kwance ina tu nanin hakan zaifi kwanciyar hankali ga zuciyoyin kowa kuma kwance auren nake ganin shine zai kawo zaman lafiya kamar yanda ka roka a shekarun baya. 
Faduwa gaban Mubarak yayi amma baiyi magana ba yana dai kallon Shalele da gefen idonsa, Baba Bashir yace Baba ka bar Mansur wannan maganar ba tasa bace kuma nima ba tawa bace, Mubarak da Shalele kakeyi wa magana dan haka kowa ya cire bakinsa a ciki. 
Mai gida yace kai da Allah rufewa mutane baki sakaran banza. tunda ka samu danka yana 
tacin zalin diyata ba dole zakace kowa ya cire bakinsa ba tunda kasan danka yake zalintar ta. 
Baba Bashir yace kai saurara ba dakai nake magana ba, banza sakarai akwai wani dakiki bayan kai? Jaki marartunani, Mai gida yace duk abinda ka fada a kaina kaine marartunani 
diyar tawa wani ya haifarmin ba nine na haifa abata ba? 
Baba bashir yace nima dan nawa wani dakiki ya haifarmin bani ne na haifa abana ba. idan an raba auren sai akace zai fasa rayuwa ne,juyawa yayi ya kalli Mubarak cikin bacin rai yace da Allah sakar masa diyarsa sai wace tsiya? Yau idan ya rabu da diyarka akwai mata dubu a duniya suna neman mai aurensu, kama samu ya aureta harzakayiwa mutane rashin kunya, 
Sakarta Mubarak, yau din nan ba wata rana ba saina auro masa mata guda ukku kuma duka sai sunfi diyarka, Baba yace Bashir saurara haka nan, tsaki Baba bashir yayi sannan yaja hannun Mubarak dansu fita, 
Twins na ganin anja Babansu suma suka tashi suna kuka sukabi bayansu Baba bashir, Baba yace Bashir dawo. Cikin bacin rai Baba bashir yace Baba babu ranar da zaman lafiya zaiyiwu a tsakanin nida Mansur ina ganin rabuwar yaran nan nake tunanin shine zaisa a zauna Iafiya. 
Mama tace Bashir dawo, komawa yayi ciki yana maijin bacin rai a zuciyarsa, ya rasa dalilin da yasa Mansuryake kyamatar dansa yake nuna masa hiyananci, dukansu suna tsaye babu wanda ya zauna, Baba yace kai Mubarak dauki matarka ku tafi, 
Mubarak yace idan na tafi tazo daga baya, danni yanzu ba gida na nufa ba, Shalele kuwa tana san tayi maganar da Mai gida yasata ta rashin haihuwar da Mubarak baya so amma dole ta hakura tunda taga zuciyoyin kowa sunzo kusa da makoshi ita kanta gabanta faduwa yakeyi addu”a ce kadai dauke a bakinta Allah yasa kada Abak ya warware aurensa dake kanta, Nan yabar yaran yayi tafiyarsa, sai kuka sukeyi dan basu saba da kowa ba sai Babansu, duk wanda ya riko su dan rarrashinsu sai su fizge hannunsu suyi ta kuka, idan kuma hannunka ya taba fatar jikinsu sai sun goge wurin sannan suci gaba da kuka. Baba Bashir ne ya tattarasu ya zaunar dasu a kusa dashi yana lallashinsu, sai kuka sukeyi 
kasa kasa amma sunki suyi hakuri sun kurawa kofa ido ko babansu zai dawo. 
Baba kuma nasiha yayiwa Baba bashir domin shi yafi Mai gida saukakakkiyar zuciya, saida 
ya gama masa nasiha sannan yace ya mayar da Shalele gidanta, 
Baba yace ma Shalele ta tashi su tafi. kallon idon Mai gida tayi amma ko inda take bai kalla 
ba, Baba bashir ya lura da Shalele tana Cikin fargaba da tsoron mahaifinta, murmushin 
karfin hali yayi tare da cewa zoki mu tafl. 
Rusuna kai kasa tayi tace kayi hakuri Baba ni bazan koma ba, cikin rarrashi Baba bashir yace mi yasa ne? Shalele tace haka nan, Baba b yace ni nace ki taso idan har nima mahaifinki ne to ki zama mai biyayya a gareni, 
Saidata sake kallon idon Mai gida sannan ta tashi tabi bayan Baba b suka fita, Sulaiman ne 
yake tuki Baba na gaba Shalele da yaranta suna baya. 
Saida Baba bashir yakai Shalele dakinta da kansa, yayi mata nasiha mai ratsa jiki ya nuna mata girman hakuri da kuma darajar miji a wurin matarsa, kudi ya bata sannan kuma yace duk abinda takeso ta fada masa, idan kuma Mubarak yayi mata wani abu wanda bataji dadi ba ta fada masa karta fadawa kowa, Shalele tace insha Allah, ya dade yana mata nasiha sannan ya tafi, gidansa ya nufa ba tare daya sake komawa gidansu ba. 
Bayan tafiyar Baba Shalele tabi yaranta da kallo wanda basu santa ba kuma basu san wace ce ita ba a wurinsu, sun samu wuri sun zauna sai Shashshekar kuka sukeyi. 
Baba kuwa ya zaunar da Mai gida yayi masa fada sosai amma duka abinda Baba ya fada ta gefen kunnesa yabi ya wuce, amma yayi ladabi a gaban Baba kamar da gaskiya yanajin 
nasihar, saida Baba ya gama sannan Mai gida yayi musu sallama shima ya wuce gidansa. ‘ 
Mubarak kuwa bai koma gida ba sai bayan sallah isha’i, a gajiye ya koma gida, wurin Khadija ya fara zuwa ya dade sosai sannan yace taje dakin Shalele ta taho masa da twins, babu wani damuwa taje ta taho dasu itama Shalele batayi wata magana ba tana gani ta tattara yaran ta tafi dasu amma ko inda take bata kalla ba, Dakinsa ya tafi dasu bayan Khadija ta kawosu, wanka yayi musu sannan ya basu abinci sukaci suka kwanta bacci, saida sukayi bacci sannan shima yayi wanka ya kwanta dan hutawa rayuwarsa. 
Fitarsu Khadija Shalele tayiwa Mai gida waya, gaisheshi tayi bayan ya dauka, bayan gaisuwa Shalele tace a bada sch uniform inta da schbg inta Balaga ya kawo mata. Mai gida yace to amma tayi hakuri saida safe idan yazo saiya ajiyeta makarantar ma, godiya Shalele tayi sannan ta ajiye waya, gyara kwanciyarta tayi taci gaba da bacci cikin kwanciyar hankali. 
Da safe wurin 7:07am Balaga yazo, yana kofar gida yayiwa Mai gida waya ya iso, Mai gida ya kira Shalele ya fada mata Balaga yana waje yana jiranta, hijabinta ta saka taje ta anso kayanta ta dawo ta shirya sannan ta fita dan tafiya makaranta, 
Da Mubarak suka hadu zai wuce, rabawa yayi itama ta karkata ta wuce babu wanda yayi ma 
wani magana, ita bataji fushi ba dan baiyi mata magana ba, amma shi’ abin yayi masa ciwo, 
har shi Shalele zata gani tayi kamar bata san Allah ya ajiyeshi ba. yaji haushin hakan da tayi 
sosai da yayi niyar ya bita wata zuciyar ta hanasa. 
Tana fita Balaga ya dauketa suka wuce abunsu, yinin ranar nan Mubarak cikin bacin rai ya yini mamakin abinda Shalele tayi masa kawai yake kartar masa zuciya amma zata dawo ta sameshi, saboda ma ta raina sa harta fita bada izinin sa ba, makarantar ma bata kara zuwa tazo ta zauna gidan su zuba dashi da ita. 
Koda aka tashi sch Balaga ya daukota, yanzun ma a waje yayi parking ta fita shi kuma ya 
wuce ita kuma ta shiga gida, 
Mubarak yaso ya hanata zuwa makaranta amma ya kyaleta kuma idan zasu hadu kofar allura Shalele bata masa magana bata gaisheshi ko kallonsa batayi kwata kwata, kuma fitarta takeyi hankallnta kwance bare tambayarsa babu abinda ya dameta rayuwarta takeyi cikin jin dadi dan duk watan duniya Baba bashiryana aiko mata da kudi masu yawa ya mayarda abin kamar albashi. 
Yau ya kama asabar Shalele tana gida bata zuwa makaranta, tana baccin gajiya wanda bata samu yinsa ba ranar da take zuwa sch, tunda tayi sallah asuba ta koma bacci dan hutar da gajiyar data tara a cikin ranaku biyar.
Mubarak kuwa tattara yaran yayi ya tafi dakin Shalele dasu, yanayin yanda tayi kwanciyar ya tabbatarwa Mubarak a gajiye take, dan haka ya dawo palo ya zauna, yara sai yahaniya sukeyi suna “yan koken yunwa, murmushi yayi cikin sigar mugunta yace duk wanda yafi yin kuka da yawa, ya fiddo wani abu a aljihunsa yace shi zai bawa. 
Kukansu ya karu kowa yana cewa nashi ne, shi kuma sai dariya yakeyi, mikewa yayi tsaye yace to kuzo zan ajiye a wani wuri ku dauka, cikin bedroom ya shiga ya dora abun daidai 
kunne Shalele yace to ku hawo ku dauko. 
Shi kuma ya koma saman bedsite ya zauna yana dariya,da gudu suka hau saman gado, Mubarak yace Yeyy, suma ihunsu karuwa yayi suka fara kokowar daukowa, wurin kokowar dauka suka cakulo idon Shalele wanda tunda suka fara abunsu tana jinsu tayi musu shiru, kama idon da aka mata yasa ta tashi cikin bacin rai ta mari Al “Hassan domin shine ya kwakwalo idon Shalele, a gigice ya sauko daga saman gadon yana kuka ya nufi wurin Mubarak dan tunda yake ba’a taba dukansa ba, ‘Daure fuska Mubarak yayi sannan yace kika marar min da ko? Shalele tace na maresa bakai ka koma gefe ka zauna kana dariya ba, su kuma sun taho Yeyy zasu tasheni daga bacci kai kuma kanajin farin ciki, 
Jinjma kai Mubarak yayi tare da rumgumesa a jikinsa yana rarrashinsa, sauka Shalele tayi daga saman gado ta nufi toilet, Mubarak kuwa sauke Al ” Hassan yayi daga jikinsa yabi Shalele toilet, ganin ya taho yasa tayi sauri ta rufe kofar da key, Tsaki Mubarak yayi sannan ya fita daga dakin suka bi bayansa suna mita, kicin din Shalele ya shiga dan nema musu abinda zasuci, shi kuma dalilin kawo su wurin Shalele yana so su saba da ita ne. Shine saboda danyen iskanci ta mari Hassan kuma wallahi bazai yadda ba saiya rama masa marinsa. Ita kuma kin fitowa tayi saboda ranta ya bata Mubarak zai mata wani abu, tana ciki tana 
jiran taji fitarsu amma yaki ya fita,jin basu fita ba yasa ta hakura ta fito, 
Mubarak yanajin fitowarta yace tazo, fita tayi ta nufi palon tana dan bata fuska, kallonta 
Mubarak yayi sannan yace kije kiyiwa yaran nan wanka, da gudu Al ” Hassan ya shigejikin 
Mubarak ba zaije wurin Shalele ba, 
Mlkewa Mubarak yayi dashi ajikinsa yace suje, hannun Al “Hussan yasa ta rike suka nufl toilet tare, ita tayiwa Al “Hussen wanka shi kuma yayiwa Al ” Hassan, bayan sun gama suka fito dasu. 
Mubarak yana dauke da Hassan ita kuma tana jan Hussen, Mubarak yace dauko shi mu tafi, babu gardama ta daukeshi suka nufi”: dakin Mubarak, a saman gado Mubarak ya sauke Hassan yace ka tsaya ta saka maka kaya idan ba haka zan bata dakai. ’ 
‘Bata fuska yayi yana kallon Shalele sannan ya kalli Mubarak, kayansu ya dauko ya kawowa Shalele kafin ya ajiye yacewa Shalele kinsa Allah saina rama masa marinsa, yi tayi kamar bataji sa ba taci gaba da shafa musu mai, ta gama ta saka musu kayansu. Sannan tayi tafiyarta, Mubarak yace ku bita gani nan zanzo idan nayi wanka. 
Kin tafiya sukayi suna tsaye a wurin, Mubarak yace ku tafi gani nan zanzo nace ko? Kowa wuri ya samu ya zauna, ganin bazasu tafi ba yasa Mubarak ya hakura yaje yayi wankasa, saida ya fito ya shirya sannan yaja su suka koma dakin Shalele, 
Acan suka yini, idan Mubarak zai tafi sallah sai yace yanzun zan dawo idan zakuci abinci ga Mama zata baku ku fada mata kunji ko? To haka suka ce kawai. 
Tunda Mubarak ya sulbe bai dawo ba, su kuma sunyi kukansu sun gaji sunyi shiru, Shalele itace ta dafa musu abinci ta basu da kanta, har dare Mubarak bai dawo ba, Shalele tana zaune ta tisa “ya “ya gaba tana kallosu, 
AI” Hussen ne ya kalli Shalele yana cire kayansa, Shalele tace mene ne kuma? Wanka haka kawai ya fada, tashi Shalele tayi ta nufi ciki suka biyo bayanta, wanka tayi musu tana gama musu suka haye gado sai bacci, 
Shi kuwa Mubarak koda ya dawo baizo dakin Shalele ba, tunda safe zaiyi tafiyarsa huddodin gabansa, baya dawowa sai dare. haka yayi tayi har tsawon wata daya Shalele bata sake ganin Mubarak ba, suma yara tun suna kukan Baba har suka hakura suka daina, tun 
sunaja baya da Shalele har suka saki jikinsu. 
Shalele kuwa ta daina zuwa makaranta saboda idan zata fita yara kuka sukeyi bata da inda zata ajiyesu idan ta kira Mubarak kuma baya daukar wayarta,ta kira Mai gida ta fada masa yace to tayi hakuri harta samu inda zata ajiye yaran taci gaba da zuwa makaranta. 
Dole ta hakura, taci gaba da kula da yara amma duk iya kokarinta na taga Mubarak har yanzun sunki haduwa, amma yau tace ko gari zai waye sai taga Mubarak, tanayi wa yara wanka sukayi bacci ta nufi”: dakin Mubarak. 
Bedroom ta shiga ta kwanta tanajiran dawowarsa har baccin ya dauketa bau dawo ba, kuma koda ya dawo dakin Khadija ya sauka acan yayi wanka yayi kwanciyarsa shi baisan Shalele tana dakinsa ba, 
Da safe ma yana shiryawa baibi ta dakinsa ba ya fice abunsa, ita kuwa Shalele tana tashi 
taga babu Mubarak ta nufi dakinta, wanka tayi tayiwa yara sukayi kalaci, 
Tana ganin abun kamar wasa karamar magana ta zama babba ta shafe kwanaki masu yawa babu Mubarak ita a tunaninta ma kila baya nan, amma yana gari itace dai bata ganinsa. 
Yau kam a zuri’arsu Shalele sun tashi da wani irin tashin hankali, domin Baba ne ya tura Mai gida da Baba bashir gaisuwar wani abokinsa a kano, shi bayajin dadi yace suje, haka sukayi tafiyar cikin rashinjituwa kowa ya dauke kansa, 
Sunje kano Iafiya sukayi gaisuwa kamar yanda Baba yace suka taho tafia dan dawowa gida, sun kusa shiga Abuja barayi suka taresu, kudi suka bukata Mai gida yace baza a bayar ba, wulakanci cike da cikinsa yaci gaba da musu rashin kunya. Yace idan da a yankinsa suka hadu Mai gida yace dasai na ciccira naman jikinku na bawa karnuka na sun cinye, Baba B yace Mansur bari, kuyi hakuri bara a baku kudi, Mai gida yace 
alkawarin Allah baza a bayar ba, 
Baba b yace to kudinka ne ba nawa ba? Mai gida yace ba nawa bane najikokina ne,sai an tattara kudin an bata sannan kuma idan ka mutu su kuma su rayu cikin wahala? 
Cikin barayin wani yace kai zaka bari a bamu ko kuwa sai mun farka kane Eye? Dariya Mai gida yayi tare da cewa kai kila baka taba farkawa ba ni na yanka na harbe na badda na halakar wannan kudin kudinjikokina ne wallahi babu ubanda zai bayardasu su suyi rayuwar kunci. 
Cikin bacin rai barawon ya daga bindiga da niyar harbin Mai gida, Baba b da sauri ya shiga gaban Mai gida suka harbesa a kafada, suka kara sakin harsashen ya kara sauka a kafadarsa kara saitawa sukayi da niyar harbin zuciyarsa cikin tashin hankali Mai gida ya janyesa wani irin tashin hankali yaji wai shi za’a harba amma Bashir ya karesa saboda baya so ya mutu, 
Da sauri ya daga rigarsa ya fiddo bindigarsa sukaci gaba da masayar wuta, ga Baba b a kasa sume cikin jini, ganin Mai gida yana da bindiga kuma yana da saiti yasa sukayi cikin daji da 
gudu suka watsu, Mai glda ya bisu amma bai samu ko daya ba, 
Cikin tashin hankali ya dawo hawaye na duga daga cikin gurbin idonsa, dakel ya saka Baba bashir mota yaja suka tafi, yana shigowa Abuja asibiti ya wuce dashi haryanzun kuka yakeyi, 
Taimakon gaggawa aka bawa Baba b kuma likitoci sunyi nasarar flta da harsashen daga jikinsa, amma Mai gida ya kasa fadawa kowa saida Baba bashir ya kwana sannan ya sanar da Baba abinda ya faru dasu, kamin kace mi asibitln ta cika, sai “yan koke koke akeyi, 
Mai gida da kansa yasa Balaga ya dauko Shalele domin yaga Mubarak kuma yaga Khadija amma babu Shalele, itama cikin tashin hankali ta iso tana kuka dan Baba b ya duba mata sosai, 2wins ganin mamarsu tana kuka suma suka ci gaba da kuka,
Mai gida ma yana cikin damuwa sosai addu”arsa daya Allah yasa kada Bashir ya rasu, shi baisan irin san da dan uwansa yake masa ba, irin wannan soyayyar yake nuna masa tun yana karami har yanzu kuma babu abinda ya ragu daga zuciyarsa na kaunar da yake masa. Tun jiya Mai gida yake kuka har yanzun ya kasa tsayar da kukansa, Baba da kansa yake rarrashin Mai gida amma yaki saurarawa tsakanin jiya da yau Mai gida ya rame kamar ya 
kwana yana amai da zawo. 
Mubarak kuwa ganin Shalele tana cikin damuwa yasa ya koma wurinta abun ya mata yawa ga kukan da Babanta yakeyi tana tayasa ga yara sun sakata a gaba sai kuka sukeyi, 
hannunta yaja su ka fita waje. 
Binta yaran sukayi suma suna kuka, moto ya bude ya shigar da ita ba tare daya shiga ba yaja yaran suka koma ciki, saida ya samu wuri ya zauna sannan yace kowa yayi min shiru, shiru sukayi suna kallon kwayar idonsa, Mubarak yace ku zauna anan zan dawo. 
Kai suka daga masa alamar to fita Mubarak yayi ya koma wurin Shalele har yanzun kuka takeyi, shiga motar yayi shima ya zauna, a hankali ya jawota zuwa cikinjikinsa yace miye 
kike kuka ne? Shiru tayi batayi masa magana ba, Mubarak yace baza kiyi magana ba ne Eye? Cikin kuka tace ba komai, Mubarak yace saboda jin dadi kikeyi k0? Shalele tace A, a, Mubarak yace tou ki daina kuka kinji ko? Tace tou, Mubarak yace ko zakici abinci ne? A, a, ta fada, Mubarak yace tou ki daina kuka ni banajin dadl idan kinayin kuka ko kina so nima inyi ne? A, a, murmushi Mubarak yayi tare da cewa tou yi murmushi kema, dan yake tayi wanda bai kai a zuciyarTa ba, Mubarak yace to muje. Fita tayi daga motar shima ya flta suka koma ciki, 
Mai gida yaci gaba da kula da Baba bashir harya samu sauki, satinsa daya aka sallamesu, bayan sun koma gida ma 3 gidan Baba bashir ya zauna yana kula da lafiyarsa. kuma ya bashi hakuri akan abinda ya wuce kuma ya kara neman yafiyarsa. 
Baba bashir yace babu wani damuwa danshi dama bai wani rike sa a zuciyarsa ba, nasiha sosai Baba ya karayiwa Mai gida haka Mama, shi kuwa Mai gida cewa yayi aiki ba’a fada 
masa ba yasan Yaya ya mishi halakci da babu shi da yanzun yana can barzahu. A bangaren su Shalele kuwa, tana zamanta lafnya amma yanzun kudin da Babe Bashlr yake kawowa harda Khadija ake bawa kuma suna zaman laflya a tsakaninsu, amma har yanzun 
Mubarak ya zauna saman kudarinsa na rashin san haihuwa. 
Wannan dalilin yake hadasu fada da Shalele dan duk lokacin da zai kwanta da ita idan yayi amfani da wannan maganin ita bata ma kwana dakinsa tafiyarta takeyi, baya wani jin damuwa sai yayi baccinsa, dama ita tazo idan kuma ta tafi ita tajiyo tunda dama itace ta 
iskosa. 
lta kuwa Khadija ba abinda ya dameta dan dama sun daddale magana babu haihuwa kuma tace taji ta gani ta yadda, ita kuwa Shalele tace bata yadda da haka ba aurenta kawai Mubarak yakeyi amma babu wani abinda yake shiga tsakaninsu domin dai ita tace bazata yadda ayi wannan shafashafen iskanci a kwanta da ita ba, shi kuma baya bari dan haka sun 
raba jaha. ldan ya dade bai ganta ba kuwa zaije dakinta ne dan ya ganta, amma koya shiga dakin zaiyi wasa da yara ne kawai ya flce abunsa, babu wani ruwan kowa da kowa, haka dai sukeyin 
rayuwar kowa yanajln haushin kowa, lta Lanajin haushinsa saboda wannan abun da yakeyi, shi kuma yanajin haushinta saboda bata zuwa dakinsa, 
Kuma idan zaiyi tatiya da Khadija yake taflya abinsa, idan ya mm sai yayi wata biyar bai dawo ba, kuma babu waya tun abin bai damunta harya fara tada mata hankali, amma ta yanke hukunci idan ya dawo kawai zata yadda a yadda yake so dan su samu zaman latiya kuma taki fadawa kowa halm da take ciki, 
K0 bikin Asma”u da ya tashi Shalele taso taje amma Mubarak ya hanata, taji damuwa sosai da kamar ta fadawa Baba b amma ta fasa saboda a cikin nasiharta da Baba bashir yayi mata ya nuna mata muhimmacin hakuri dan haka ta hakura bata kai masa karar Mubarak 
Khadija kuwa ana makela da miji dama haka akeso, a zamansu da Mubarak ta roki Mubarak alfarma da ya taimaka mata don itama tayi ciki ko so daya ne tunda Shalele itama ta aihu, 
Kuma Allah ya taimaketa ya yadda amma yace bazaiyi planing na sati biyu ba idan ta samu ciki a lokacin tou idan bata samu ba kawai baya da wani damuwa. 
Tace ta yadda, haka kuwa akayi ya daina planing har na tsawon wata daya, amma Khadija shiru, ita da sukayi sati biyu amma anyi wata babu wani bayani, hankalinta ya tashi ta kara rokar Mubarak don girman Allah ya taimaka mata yayi hakuri ta samu ciki sannan, yace to, 
Har suka dawo Mubarak ya daina planing amma Khadlja babu ciki, lokacin da suka dawo tacewa Mubarak yaci gaba da using cream dinsa, abinda yasa tayi haka kuwa saboda kada Shalele ta samu ciki, shi kuma bai kawo komai a ransa ba yaci gaba, ita kuma Shalele a haka ta hakura amma ranta baya so. Yauma tana dakinsa kwance sai kuka takeyi, shi kuma ya fito daga wanka, yana tafiya dan matsawa inda zai saka kayansa yace me kike ma kuka ne? 
Cikin kuka Shalele tace nida ka sakeni. saida kwalbar turaren dake hannunsa ta fadi kasa saboda maganar da ta flto daga bakin Shalele cikin bacin rai ya juyo yace wannan wace irin magana kikeyi ne? Cikin kuka Shalele tace ni gaskiya ina so zan aihu tunda kai kuma baka 
san aihuwa ka sawakemin sai inje in auri wanda yake son aihuwa sai muyi aurenmu, 
Mubarak yace ba kin aihu ba, yara biyu sun isheki kiyi hakuri Shalele ya dawo kusa da ita ya Zauna, da hannunsa yake nuna mata yace ga abin tausayi ma Khadija itafa bata taba aihuwa ba, ke kuma fa? Yara biyu idan kin tara yara me zakiyi dasu? Tsufar dake zasuyi, 
Shalele tace Eh nidai ina so na tsufar, Mubarak yace har yara nawa kike so kiyi duniya? 
Shalele tace bakwai, murmushi Mubarak yayi sannan yace haba Shalele sai kace wata akuya “ya “ya bakwai duk me zasuyi miki ne? Saida ta goge hawayen idonta sannan tace nidai ina so haka nan, 
Shiru Mubarak yayi yana nazari sannan yace tou zanyi shawara, Shalele tace da waye zakayi Shawara? Kallonta yayi sannan yace dani da Khadija, Shalele tace ni ban isa kayi shawara dani ba? Ta karasa maganar hawaye yana digowa daga cikin idonta, dagota Mubarak ya rungumeta ajikinsa yace kin isa har kinyi yawa, yanzun dai aihuwa k0? Shalele tace Ey Mubarak yace insha Allah zaki kara aihuwa, amma nidai bana san “ya “ya bakwai don girman Allah, Khadija tayi biyu ki kara daya. cikin kuka Shalele tace ni gaskiya ba ukku ba, 
Shiru Mubarak yayi har yanzun Shalele tana jlkinsa tana kuka, hakuri Mubarak ya bata tare da mama alkawarin zata ci gaba da aihuwa insha Allah k0 so nawa zata aihu ya yadda, dadi taji sosai sannan ta ma daga jikinsa da gudu ta ma ta nufl dakinta, 
Bayanta Mubarak yabi da kallo harta flta, murmushi yayi tare da tashi ya dauko cream din yaje yajefar a cikin shara, kwalbar turaren daya fasa ya tattara yana juyowa yaga Khadija tsaye, yana taflya yace ke kuma ya akayi ne? Ina shigowa naga maganinka a Shara miyasa ka yadar dashi ne? Mubarak yace Shalele tace idan bazan aihu da ita da yawa ba saida na saketa. 
Khadija tace tou ni gaskiya ban yadda ba dole aci gaba da amfani da magani, Mubarak yace tou ki ajiye a dakinki ranar da kike aiki idan zaki zo sai ki taho dashi, Khadija tace ni daya zaka nka amfani dashi, Mubarak yace Ey ai saboda kece kike so, Khadija race wallahi baya 
yuwuwa dole kowa sai an masa dashi, 
Mubarak yace wallahi bazanyi ba, tunda tace bata so bazan mata ba, ko so kikeyi muzo kuma mu samu matsala ni Baba yace nine banda gaskiya? Khadija tace ni da kamin fa? Mubarak yace saboda kince kin yadda ita kuma a lokacin da na aureta ban fada mata haka ba, 
Khadija tace tou idan dai baza kayi amfani dashl ba tou saika sakeni. Mubarak yace aini na 
fada miki bana sakin aure amma idan kece kika saki kanki sai inyi miki sign, 
Khadija tace haka ne? Mubarak yace sosai ma, cikin bacin rai ta matsa ta dauki paper da biro, Mubarak yace kiyi tunani kafin kiyi abinda zuciya ta sakaki idan har na saki mace na gama da ita har abadan duniya ko wace ce kuma duk san da nake mata bana sake zama da ita, ina bata ji kira ba domin shedan ya doka mata ganga. 
_Ni Mubarak Bashir Abak na saki matata Khadija saki 1 saboda nace na daina amfani da maganin planing. Tace bata yadda ba shine ta bukaci na saketa._ 
Tana gamawa ta mikowa Mubarak tace ka saka hannu, ansa yayi yai mata sign ya mika mata, Khadija tace baka burgeni ba da baka saka saki goma ba, Mubarak yace idan nayi 
miki goma ai na zama mahaukaci dayanma ya isheki, 
‘Daukar takardartayi fuuuu ta fice daga dakin, shi kuma turare yadan matsa ya dauki abinda zai dauka yabar gidan. 
Bayan shekara biyar, Shalele ta kara haihuwar yara biyu, mace daya wanda aka sawa Hauwa”u wato sunan Maman Mubarak suna kiranta da Afnan, sai namiji wanda suka aka sakawa sunan Mai gida wato Mansur, suna kiransa da Affan, yara hudu kenan ukku maza mace daya, daga haka aihuwa ta tsayawa Mubarak saboda amfani da yayi tayi da maganin hana daukar ciki, 
lta kuwa Shalele tace gani takeyi kamar wata hanya ta daban ya canja kuma shi ba haka bane iyakar gaskiyarsa kenan, yayi mata rantsuwa amma taki ta yadda, kyaleta yayi saboda baisan abinda zaice mata ba. 
Momy kuwa tana zuwa wurin Shalele lokaci lokaci, ltama Shalele tana zuwa ko bikin Kamal da ita akayi amma bata tafl da yaro ko daya ba ta barsuwa wurin Abak sati daya tayi tadawo, ‘ 
Baba kuwa ya natsawa su Mai gida suyi aure dolensu, shidai Mai gida ya auri tsohuwal budurwarsa wanda ya bawa kyautar motar Baba, shi kuma Baba b “yar uwar matarsa ya 
aura wato “yar uwar Maman Mubarak, a gida daya suke zama da Baba bashir da Mai gida. 
Zaman lafia sukeyi, sosai Mai gida yake kyautatawa dan uwansa wato Baba b, kuma 
matansu ma zaman Iafiya sukeyi sosai, Shakara daya Mubarak ya kwashesu su dukansu suka je saudiya dan sauke farali, shidai Baba bashir dama yaje, Mubarak ma, bakin alhazai a ciki, Shalele, Mai gida, Balaga, 
Sulaiman, Mama, Baba, Gwaggo. Mai nasara, sai matan da iyayensa suka auro, 
Yara aka barsu jos a wurin Momy, sukaje aikin hajjinsu [aflya suka dawo qalau, Asma’u tazo sannu da zuwa, Momy ma tazo ita da yara ta dawo dasu, 
Bobo mai napep ma yayi kokori ya gano Shalele ya hada zuminci da matarsa ana ta 
gaisawar mutu nci sosai, 
AlhaJi Abas baban Asma’u shima sun shlrya da Mai gida, kuma duka yaransu suna zaune a wuri daya amma duk a karkashin Mubarak suka koma domin shine mai kayan gabar wato kudi, albashi yake musu mai waya wanda duk wanda ka gani a cikinsu zaka sha wani 
hamshaki ne, domin dai Abak ya fiddo su ya mayar dasu mutane. 
Mubarak kuwa ya tattara iyallnsa ya koma inda ya rayuwa amma bawai kwata kwata ba, dan yayi alkawari yanda baiyi karatu nigeria ba duka yaransa baza su karatu nigeria ba, 
amma lokaci lokaci yana zuwa nigeria dan saiya zo sau biyar Shalele batazo so daya ba. 
Yaranta sun taso cikin kulawa sosai suna samun gata yanda ya kamata amma haka bai 
hanasu bawa “ya”yansu tarbiyya ba, 
Mai gida da Baba bashir suma suna zuwa lokaci lokaci suna kaiwa “ya “yansu ziyara, kuma suma su Shalele idan sun samu hutu suna dawowa gida idan hutu ya kare su koma, shi kuma Mubarak baya zama wuri daya saboda abubuwa sun masa yawa mai neman kudi 
baya zama, an tara amma anki a daina nemansu haka nan. 
Khadija kuwa sai yanzu ta gane ta jibga babban kuskure, domin yanzun dai Mubarak yayi 
mata zurfi ganinsa ma wahala yake mata, amma tana masa waya idan yaga dama ya dauka idan kuma yaga haggu ya basar, dan shi wani iri hali garesa imma Shalele hakuri takeyi amma tasan yana santa,
Dan ko ita ta kirasa yaga dama ya basar da ita, amma yaransa na kiransa zai dauki waya 
idan yana wani abu zaice inayin kaza idan na gama zan kiraka, 
Yauma tun safe daya flce daga gida bai dawo ba, kuma duk wayoyinsa ta kira baya tafiya, saida ta hau online tayi masa magana wai yana ina ne ? tun safe, ya gani ya barta, amma 
saiya kira Hassan yace kacewa Mamanku levnon, yace torn, 
Mama, Dady yace yayi taflya Al ” Hassan ya fadawa Shalele bayan ya gama waya da Abak. Shalele tace shidai ya sani, zai sake magana tace da Allah kuje kuyi bacci nima kaina ciwo yakeyi. 
Tashi sukayi suka nufi dakinsu danyi bacci, Afnan ta tashi tabi bayansu, Shalele tace dan ubanki ina zakije nan ne? Ban gama Home work ina ba, daka mata sawa tayi cewa kije ki 
kwanta nace idan na tashi wallahi saina farfasa mikijiki, 
Ajiye littafln tayi ta wuce ciki da gudu tana kuka dan idan da sabo sun saba dan dasun ji 
tana masifa Babansu ya bata mata rai, itama cikin bacin rai ta tashi ta nufl dakinta, 
Tulin miss calls Mubarak yayi mata amma bata bi kiransa ba, Hussen ya kira yace ya kaiwa mamansu waya, amma sai yace wa Mubarak dady tace mull bacci, murmushi Mubarak yayi 
tare da cewa tou yayi saida safe, saida safe Hussen ya fada tare da kashe wayarsa. 
Sako ya turawa Shalele cewa, kidaiji tsoron Allah na hanani wannan halin baza ki bari ba k0? Wallahi saboda kina takurawa ” ya “yana zaki hadu da fushi na wallahi, saboda zalinci sai kisa yara baccin dole, wannan ai daukar alhakine da cin zalin, ke baccin dole nake sakaki kiyi ne? Zan dawo zakiyi baccin dole kiji idan da dadi, kuma kada ki dauki wayar, 
idan kin dauka ban gode ba mtswwwww, 
Tsoki tayi bayan ta gama karantawa bate bashi amsa ba, Mubarak kuwa jin shiru bata dawo da amsa ba yasa ya sake kiranta, kin dauka Shalele tayi, sake rubuta mata sako yayi cewa 
yi hakuri na gano lain na dan na tafi ban fada miki ba, kIyI hakuri msha Allah ijI zan dawo dauki waya muyi magana. 
Sake kiranta yayi amma Shalele taki daukarwaya, ajiyar zuciya ya sauketare da kara kiran wayar Shalele yayi amma tayi kunnen uwar shegu dashi bata dauka ba, Hassan ya kira yace yaje ya kaiwa Mamansu waya, tashi yayi ya nufl dakin Shalele cikin fargaba, da sallama ya shiga, cikin tsoro yace dady zaiyi magana dake, 10 ka kawomin wayar da sauri ya juya dan 
yasan yana matsawa rikesa zatayi tayi ta dukansa, u 
Saida ya ma yace Dady wallahi dukana zatayi, Mubarak yacejeka ka bata ta dakenka ai zan dawo, komawa yayi dakin yaje har gabanta yace Mama kiyi hakuri don Allah Dady bayajln dadi, Mubarak yace yawwa fada mata dai, Hassan yace Dady bata ansa ba, Mubarak yace sa H free, sakawa yayi sannan yace na saka Dady, Mubarak yace tou ajiye ka ma, ajiye wayar yayi ya flta daga dakin, 
Mubarak yace Shalele ni kike ma wannan abun ko? Rayuwar da kika koyawa kanki rayuwa mai kyauce haka kenan? Shiru tayi batayi magana, munnushi mai sauti Mubarak yayi sannan yace na yafe miki amma ki daina, shiru tayi batayi magana, Mubarak yace saida safe Allah yayi miki albarka ngode, 
Shalele dai batayi magana ba, Mubarak yace ‘ou ki kashe wayar mana nace saida safe k0, idan kaga dama ka kashe tunda kaine ka kira, dariya Mubarak yayi tare da cewa tou saida safe, kuma bai kashe wayar ba, bayan wani lokaci yace Shalinina nace saida safe, banza tayi masa, 
Saida aka kara daukar lokaci mai tsawo sannan yayi dan gajeran tsoki yace swry wallahi nadan fara bacci ne, saida safe kashe wayar don glrman Allah bacci nakeji wallahi zan kashe waya inyi bacci, saida safe ta fada sannan ta kashe wayar dan tasan idan zasu kwana a haka shi baya ta kashe mata waya idan dai ba itace ta kashe ba. 
Tana kashe wayar ya kashe wayoyinsa yaci gaba da bacci, 
Mubarak kuwa bai dawo ba saida yayi wata daya, kuma ranar da zai dawo bai fadawa Shalele zai dawo ba sai a bakin yaran taji suna cewa yau Dady zai dawo, wannan abu da Mubarak yake mata yana mata ciwo a da tana iya boye damuwa amma banda yanzu ita 
kanta ta rasa dalili tana dai addu”a ubangiji ya yaye mata wannan damuwa. 
Koda Mubarak ya dawo yara kadai sukayi ta ihunsu banda Shalele, kuma ko abinci bata 
ajiye masa ba saidai Affan ya dafa masa lipton yasha, bayan ya gama yayi wanka ya the, 
Saida yara sukayi bacci sannan Mubarak ya dawo gida, fada sosai yayiwa Shalele kamar zai daketa yace wannan halin banza bazai dauka ba idan kuwa ba haka ba dukanta zai tayi 
harsal (a gene bata da wayau, ye are da cewa banda km aukem sakaral k0 yaron gldankn ne ni ina miki aiki nayi tafIya na dawo ai zakimin sannu da zuwa, amma saboda tsabar iskanci na dawo gida babu sannu da zuwa, abinci ma bakl‘ ajiye min ha a gabanki nacewa Affan ya dafa min tea amma sai kika tashi kika dawo daki, kuma wallahi daga yau idan kika sake dukanmin yara saina zane mikijiki a gidan nan dabi”u irin na kidahuman matajahilai wanda basu san darajar miji ba, daka mata sawa yayi tare da cewa ki tashi kije ki bani 
abinci yunwa nakeji, 
Simi simi ta tashi ta flta tana kuka, biyo bayanta yayi yana cewa ni zan miki magana ki flto kina min kuka ko? Tou kici gaba zan kamaki, cikin bacin rai ta sama masa abinda zaici ta dauko cikin fushi ta taho, a wulakance ta ajiye abinci ta wuce, tana kokarin flta daga dakin 
yace ke zo nan, dawowa tayi tazo tayi masa tsaye a saman kai. 
Jawo hannunta yayi ya zagayo da ita gabansa, cikin rarrashi yace wai mene? Har yanzun kuka takeyi, riketa yayi a jikinsa cikin tattausar murya yace baki da latiya ne? Cikin kuka (ace laflyata qalau, Mubarak yace tou kinajin yunwa ne A, a, ta fada, Mubarak yace na bata 
miki rai ne? Eh, 
Mubarak yace tou me nayi miki ne? lea bananan dawowa ne kenan, Shalele tace sai ka tafl baka fadamin zakayi tat’Iya, sannan idan na kiraka sai kaga dama ka dauka waya, kuma da zaka dawo baka fadamin ba, ina zaune a pale kace Affan ya dafa maka tea, 9 
Kara nketa yayi sosai ajikinsa sannan tace tou kiyi hakuri insha Allah na daina, kinyi hakuri k0? Ey ta fada, Mubarakyace xou zakici ablnci kema? A, a ta fada, Mubarak yace tou zauna 
bara na gama, kuma ki bani Iabari. 
Murmushi tayi sannan ta kwanta ta dora kanta saman cinyarsa ta fara bashi Iabari. wani 
yayi dariya wani kuma yayi murmushi wani kuma yace tou pha harya gama cin abincinsa. 
Gyara zamansa yayi tare da cewa Shalele dan tashi tsaye na gani, kallonsa tayi tare da cewa in tashi kuma, ba tare daya kalleta ba yace Ey mana ai kema kinsan sai kin tashi, tashi 
tayi tsaye dan dama idan yayi taftya ya dawo haka yake cewa tayi wai yaga idan tayi rama, 
Kallonta yayi sosai sannan yace tou juya, juyawa tayi sannan yace to na gani zoki ki kwanca, dawowa tayi ta kwanta bata dade da kwanciya ba bacci ya dauketa. Saida tayi bacci sannan ya sauketa daga jikinsa, pillown kujera ya dauko ya dora mata kanta, 
Shi kuma toilet ya nufa yayi alwalla ya futo, sallah. 
Haka dai rayuwarsu taci gaba da ‘af‘lya dan tun daga wannan ranar da Mubarak yacewa Shalele ta daina hali irin na jakan mata ta daina, kuma shima ya daina tatiya bai fadawa 
Shalele ba kuma idan zai dawo yana fada mata, 
Zaman su laflya sukeyi kuma Mubarak ya hanata dukan masa yara yace idan sunyi laifl ta fada masa, Mubarak yana jin Shalele sosai har a akin ransa baya san damuwarta haka 
kuma baya barin ta shiga damuwa, rayuwa ce sukeyi mai tsafta tare da nunawajuna kauna, 
Mai gida kuwa ya daina harkar boka ya gane boka mushiriki ne, suna kuma zama na 
lumana da kwanciyar hankali dashi da Baba Bashir. 

Alhamdulillah 

Mu tara a wani book din

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *