HEEDAYA CHAPTER 1 BY By Khaleesat Haiydar

HEEDAYA CHAPTER 1 BY By Khaleesat Haiydar

               Www.bankinhausanovels.com.ng 

Wani d’an matsakaicin daki ne da aka xagaye da tsadaddun labulaye, dakin na dauke da katifa babba, sai kayan kallo 

daga gefe, sai cushion tsadadde guda daya, Dattijuwar da baxata haura hamsin da biyar ba dake xaune dakin tayi 

tagumi tace “Toh mu dai baxa mu gaji da addu’a ba, Allah ubangiji ya bata lafiya, watan gobe kenan dai ake sa ran 

komai xai yi dai dai koh?” Matashiyar matar dake gefenta ta d’an yi murmushi tace “Haka dai likitocin suka ce in 

sha Allah, sai dai kinsan kana naka ne Allah na nasa, amma wnn aikin shine na karshe da xa ayi mata idan Allah ya 

yrda, sai kuma fatan Allah ya sa a dace” Yakumbo tace “In sha Allahu xa a dace, abinda kullum gaya ma Allah muke, 

kaf dangi bbu mai irin laluran nan balle ace ko gado ne, sam bbu shi a danginmu gaba daya, ko ke akwai a naku??” 

Dariya matar tayi tace “A’a Yakumbo” Yakumbo tace “Atoh, Allah dai ya raba bawa da wahala ke ma kuma Allah ya Www.bankinhausanovels.com.ng 

sauke ki lafiya, Indiyan xa a kara komawa kenan ayi aikin?” Matar tace “Ameen, ehh can xa mu je” Yakumbo tace 

“Toh in sha Allahu karshen wahalan kenan” Matar tace “Allah ya sa” agogo Yakumbo ta kalla tace “Anya tafiyar 

nan taku na nan yau kuwa Amina, shiru shiru har yanxu Umar din bai xo ba” Amina ta kalli agogon ita ma tace 

“Kuma na kirasa daxu ban samesa ba, ina jin meeting suka shiga, kila sai gobe dama na cire rai yau” Yakumbo tace 

“Atoh, ku bari kawai sai gobe yamma yayi, sai kace wa inda ake kora, ga hanyar nan da ba kyau gari ya xama 

abinda ya xama mucuta ta ko ina….” Amina tace “Haka ne” Yakumbo tace “Naji wai matar Salihu na ta neman ki da 

fada ko? Kar ki kuskura ki kulata gayyar mayu ne, har ita Asama’un ma ki bar kulawa duk haushin ki suke ji suna 

ganin kin fi su walawa gidan miji, ba su san Allah ne ya baki ba” Amina tayi murmushi bata ce komai ba, Yakumbo 

ta kara da cewa “Kuma wai sai kiyi ta boye yarinya kar su gani, wai haka?” Amina ta kalleta tace “Aa ba gaskiya 

bane, ke kanki shaida ce Yakumbo tun tana yar yarinya ba a fiye fito da ita cikin jama’ah ba, a ko da yaushe tana 

daki tare da ni ko mai kula da ita, ko malamarta, har yau ‘yan anguwa basu wani san kalan Heedayah ba, da kyar ki 

xo gidan ki ganta a parlor, to sau tari idan anyi baki har su tafi ma baxa su ganta ba shine ake ganin kamar boye ta www.bankinhausanovels.com.ng 

muke kar a ganta” Yakumbo tace “Toh ai gwara haka, haka kawai baka san bakin wani ba, ayi ta sa ma yarinya baki, 

gaskiya kun yi dubara, ki rabu da su suce duk abinda xa su ce, lafiyan yarinya shine gaba kan komai” Amina dai bata 

ce komai ba, Yakumbo tace “Har bokon ma a gida ake mata kenan?” Amina tace “Ehh har islamiyya” Yakumbo tace 

“To madalla, ae gwara hakan, Ke leko yar mutane naji shirun yyi yawa, Allah ya sa dai gantalallun yaran makotan 

nan nawa ba shigowa suka yi suka yi waje da ita ba” Da sauri Amina ta mike tana leka tsakar gidan tace 

“Heedayah??” Jin shiru ta fito tsakar gidan, Katon Babyn robanta da take combing gashinta kadai ne kan tabarma da 

comb din sai hularta amma babu ita, Yakumbo ta mike tace “Ni da nasan sai sun shigo sun ja ta, Amma wa ennan 

yara iyayensu sun haifi jaraba kawai, yara kauyawa bbu kamun kai kawai malam…” Dawowa Amina tayi dakin ta 

dau Hijab dinta sannan ta fita waje, Yakumbo na biye da ita tana cewa “Ni dai Allah ka rufa min asiri ba rafi suka ja 

ta suka kai ta ba in shiga uku, yarinya dai ba ido ba, daga kawo min ziyara shaidan ya fake ta nan yayi abinda ya ga 

dama tawa ta sameni ina xaman xamana….” Tun Mahaifiyar Heedayah na daurewa ana shiga bukkokin makota duba Heedayah a kauyen har taji hankalinta ya fara tashi sosai ganin babu alamar yar tata…. Yakumbo dai sai salati take www.bankinhausanovels.com.ng 

xabgawa a rikice tana yafa gyalen da ya ki xama tana cewa “Toh me xance ma kanina Umaru jama’ah?? Ina xan ce 

yar sa ta shiga?” Wata mata ce tace “Daxu fa naga sun yi hanyar kasuwa da su Hinde da Bibalo, har da fatu, kusan 

dai su shidda suna rike da hannun ita yarinyar” Yakumbo ta saki salati tace “Toh kuwa wllh Ubanta a Habuja yake 

kuma duk iyayensu xae sa a daure idan abu ya samu yar sa, ita fa kadai garesa sae ynxu da uwar ke da sabon ciki, 

shekararta goma sha biyu, kuma ba idanuwa gareta ba, to a kan me gantalallun yara xasu ja ta su tafi da ita kasuwa, 

uwayensu xa su siya mata a kasuwar? Tun shekaranjiya da suka xo kauyen nn nake ja ma ja’iran yaran nan kunne 

ganin ynda suke makale mata har da masu wasa da gashin kanta nake ce masu su fita harkarta, ita dai ba fuskarsu 

take gani ba balle ace, to wannan wani irin bala’i ne, hanyar kasuwan nan da babu kyau sace sace yyi yawa, haba 

jama’ah??” Tuni duk aka watse aka dau hanyar kasuwa aka bar Yakumbo tsaye ita kadai tana kumfar baki, can dai ta www.bankinhausanovels.com.ng 

bi su da sauri ganin sun yi nisa. Yara ne duk mata kusan su biyar karkashin bishiyar mangwaro sai mata biyu dake 

saman bishiyar suna tsinkar nunannun mango suna jefowa kasa matan dake kasa suna kwasa suna xubawa a karamin 

buhu, wata yarinya ce warce duk baxata wuce sa’aninsu ba tana durkushe hannunta rike da mango tana sha, daya 

hannunta kuma na rike da rigar fatuu don ita ke mata jagora, fara ce sosai, kana ganinta kasan jinin Fulani ce don 

gashinta dake bude ko hula babu ma ya shaida haka, idanuwanta farare ne kal kamar Madara tana kifta su a hankali 

kai kace ras take ganin kowa a wajen, sai dai babu abinda take gani banda duhu, wajen duk ya kauraye da surutun 

yaran dake tsinkar mangwaro xa su kai kasuwa su siyar, wata bakar mota ce ta ja tayi parking a wajen, duk suka juya 

yaran, lkci daya kattin maxaje biyu suka fito motar da sauri, gudu yaran suka yi har da Fatuu da ta warce rigarta 

daga hannun Heedayah, na saman bishiyar ma duk suka diro suka ruga aguje, Heedayah ta saki mango din hannunta 

ta dinga waige waige a tsorace, maxan suka bi bayan yaran suka samu kamo uku daga cikinsu, Heedayah ta mike ita 

ma suka daga ta suka saka cikin motar, kan kace me driver ya ja motar da gudu suka bar wajen. Gaba daya ihu yaran www.bankinhausanovels.com.ng 

ke yi cikin motar har da Heedayah dake ta kwala ma Mahaifiyarta kira tana cewa “Ammina….” Wanda ke xaune a 

baya ya ciro bindiga yana nuna masu da jajayen idonsa fuskarsa a murtuke ya daura hannu a lebbansa alamar su yi 

shiru, lkci daya su ladi duk suka yi shiru sai rawa jikinsu yake, Zulai har da sakin fitsari a gun, Heedayah ce kadai 

bata fasa ihun da take ba, Mutumin ya shake wuyarta yana nuna mata bindigar yace “Ohh ke baxa ki rufe mana baki 

ba koh?” Jikin Ladi na 6ari tace “Bata gani” Mutumin ya shiga kare mata kallo sannan ya gyada kai yace “Kuma duk 

yanxu xaku daina gani” yana fadin haka duk ya rufe ma sauran ido da kyalle, Heedayah da ta ki yin shiru kuma ya 

dinga buge mata baki yana marinta, hakan kuma bai hanata ci gaba da ihu ba tana lalube laluben inda xata fita, daga 

karshe jin taki shiru wanda ke xaune gaba ya miko masa wani leda yace “Bada mata a fuska” hakan kuwa aka yi, 

nan da nan kuwa ko ina yyi tsit a motar, a hankali Heedayah ta fada jikinsu Ladi. A hanya mutan kauyen suka hadu 

da su Hinde da sauran matan da suka samu guduwa, Nan su Hinde na kuka da ihu suka fada masu abinda ya faru, da 

hanxari wasu mata biyu suka rike Ammin Heedayah dake neman sulalewa nan kasa, ta fada jikinsu a sume. 

Yakumbo ta saki wani salati da karfi ko ina na jikinta na rawa, cikin kidimewa ta dinga cewa “Ai shkkn tawa ta kare, 

na shiga uku na lalace, kar ace min yan kinnaping ne ko yan yankan kai suka dauke Heedayah, me xance ma kanina www.bankinhausanovels.com.ng 

jama’ah???” Ta fashe da matsananin kuka xata fadi kasa ita ma aka rikota, ana ta salati iyayen sauran yaran da aka 

dauke ma suka dinga kuka suka bi bayan maxan da suka nufi gun da abun ya faru. Tafiyar kusan awa daya mutanen 

suka yi da su Heedayah a mota kafin su fita hanyar kauyen gaba daya kasancewar hanyar bbu kyau, sannan suka yi 

parking gefen jaji don tafiyar minti ashirin kawai xasu kara su isa wani checking point a gaba, wasu mutane ne suka 

fito daga dajin bbu kyan gani kana ganinsu kaga axxalumai, Mutumin dake bayan mota ya sakko da sauri ya fiddo 

su Ladi aka tasa keyansu cikin dajin bayan an kunce kyallen idonsu, daya daga busassun mutanen da suka fito daga 

dajin na kallon Heedayah yace “Wannan fa” Mutumin na kokarin fiddota yace “Daukarta xa ku yi, xata daga mana 

hankali muka badata da powder” busasshen Mutumin yace “Ai baxai yiwu bane, wnn uban tafiya xaka ce a dauketa, 

ku kashe ta kawai a jefar a nan, mu yi wucewar mu” A fusace Mutumin yace “Mu kasheta bayan yara goma muka yi 

alkawari yau, duk bbu sa’a sannan mun samu yara hudu kace mu kashe daya…. Kuma dole dai ku dauketa don 

makauniya ce wai” Yana fadin haka ya direta kasa ya shige motar driver ya ja suka bar gun a guje” tsaki Mutumin 

yyi ya dau Heedayah kai kace dabba ce irin daukan da yyi mata suka shige dajin dake da manyan torns, ga duhu don 

Magrib ya gabato……

Bayan tafiya that seems endless da kafa suka bullo ta wani titi inda wata mota ke jiransu, nan suka shiga aka ci gaba 

da tafiya, gaba daya yaran kana ganinsu kasan sun gaji sosai, Heedayah dai har lkcn dabata farka ba, sai kusan goma 

suka iso wani karamin Uncompleted building, mata da maza ne sun kusa 6 yashe a wani daki da bbu hasken kirki 

sbda karamin window ne a dakin daga can sama, Nan aka tura su ladi da Heedayah da ta fadi kasa ko motsi bata yi, www.bankinhausanovels.com.ng 

Wani wanda da alamar shine babba cikin yan bindigan dake wajen yana rike da bindigarsa ya kalli wanda ke gadin 

mutanen shi ma da bindigarsa a hannu yace “Ya ku ka yi da mutanan wancan Mutumin a waya?” Ya kalli wanda 

yake nuna masa yace “Ae kawai bbu alamar xasu bada kudaden nan, sun ma daina daga kiran” Bai rufe baki ba ogan 

nasu ya harbe Mutumin da ake magana a kai, hakan ya kidimar da mutanen da ke xaxxaune gun, barin matan, sound 

din harbin ya farkar da Heedayah ta fasa wani ihu tana kokarin mikewa tsaye wata mace dake xaune kusa da ita ta 

jawota da sauri ta rufe bakinta a jikinta, Ogan ya dinga ma Heedayah wani kallo sannan ya kalli Mutumin gefensa 

yace “Is she among the kidnapped?” Mutumin ya girgixa kai da sauri yace “Aa yan kauye ne, su hudu muka dauko a 

kauyen jiya, ba kace ana son body parts ba” Mutumin ya karasa gun Heedayah ya dagota daga jikin matar yana kare 

mata kallo da kyau, ya girgixa kai yace “Yar wani babba ce wnn, it will have been good she’s kidnapped, but anyway, 

ana bukatan parts din ma” Yana fadin haka ya turata ta fadi kasa, janye gawar Mutumin ogan yasa aka yi aka fitar 

waje, sannan duk Yan bindigan suka fita aka garkame kofar. Ladi ta kankame Zulai ta dinga rusa kuka tana kiran 

sunan Babarta, wata mata ta mike ta nufesu ita ma tana hawayen, nan ta shiga lallashin su tana kwantar masu da 

hankali da sauran mutanen wajen, kai kana gani kasan duk karfin halin lallashin nasu suke yi. Matar dake kusa da 

Heedayah sai kokarin daga Heedayah take ganin kamar suma tayi….. Sai kusan asuba Heedayah ta kuma farkawa, ta 

mike xaune da kyar tana laluban inda take tace “Ammi??” Jin shiru bbu muryar Mahaifiyarta kamar ko da yaushe sai 

mutane a kwance tana ta6a su ta janye hannunta da sauri, muryar Zulai taji a hankali tace “Kiyi shiru yar birni yan www.bankinhausanovels.com.ng 

yankan kai ne suka sace mu, kiyi shiru kar su shigo” Tsit Heedayah tayi da farko, sai kuma ta fasa ihu tana kwala 

kiran Ammi, wani da ke sallah ya sallame ya taho kusa da ita da sauri gudun kar mutanen su shigo don babu abinda 

suka tsana irin a dinga masu ihu, karamin aikinsu ne su kasheta in har suka shigo, lallashinta ya dinga yi yana ce 

mata xata koma gida in sha Allah, ita kuwa sai cewa take “Aa ni a kai ni gun Ammina da Abbana yanxu….” Nan dai 

ta tada wa enda suka samu bacci aka dinga hiaikin lallashinta a d’an dakin, Cikin kuka take ce masu xata yi fitsari, 

aka nuna mata wani karamin kofa dake cikin dakin, Ladi tace “Yo ai bata gani” furucin Ladi ya sa duk aka tsaya 

kallon Heedayah, wata mata ta mike a sanyaye ta kama hannunta ta kai ta bayin. Har aka yi asuba gari ya waye 

Heedayah shesshekar kuka take a hankali, can ya ta6a matar dake kusa da ita cikin kuka tace “Aunty yunwa nake ji” 

Matar ta kuma jawota jikinta cikin sanyin murya tace “Yanxu xa a kawo abincin idan Allah ya yrda” sai karfe goma 

aka bude kofar dakin, duk kowa yyi tsuru tsuru ana addu’a a xuciya, Mutane uku suka shigo ko wanne ya saita 

bindiga, kamar ko da yaushe facemask na fuskarsu, sai wani mutum da shi ma fuskar tasa ke a rufe dake rike da 

babban leda me dauke da kananun bread, daga inda yake tsaye ya dinga jefa ma kowa da ledan pure wata daya, ya 

jefa ma Heedayah dake ta bin duk inda ta ji sound din faduwar bread da ido, Zulai ta mike xata dauka ta bata ya 

mata wani mugun kallo ta cikin mask din fuskarsa da ke nuna idonsa kadai, jiki na rawa tace “Yo ai bata gani ne” 

kallon Heedayah ya sake yi, gashi dai fararen idanuwanta a kansa kuma ace bata gani, wani tsawa ya mata yace “Sa 

hannunki ki dauka da kanki” Heedayah da tayi mugun tsorata ta fara laluben inda xata ga bread din amma bata gani 

ba don bayanta yake, karasowa yyi cikin dakin bindigar sa a hannu, duk occupant din dakin suka rike numfashi 

ganin ya nufo Heedayah da ta hakura da laluben inda bread yake ta sunkuyar da kai, dukawa yyi ya dau bread din ya www.bankinhausanovels.com.ng 

mika mata yace amsa, tana laluban inda yake, ya kamo hannunta ya sa mata bread din, tana kallon direction din da ta 

ji hannunsa idanuwanta cike da kwalla a hankali tace “Thank you” ajiye mata ledan ruwa daya yyi ya bar sauran 

bread din ya mike ya fice daga dakin sauran yan uwansa suka bi sa sannan suka garkame kofar, matar dake kusa 

da Heedayah ta rungumota hawaye na zuba idonta ita ma, ta amshi bread din ta kunce mata ledan ta mika mata. 

Zulai da Ladi dai tuni suka handame bread din suna zare ido. Ammi ce kwance gadon asibiti da drip a hannunta, da 

ido kawai take bin mutanen dake cikin ward din, she looks so sick, Yakumbo na can wani gefe xaune kan kujera tayi 

tagumi idanuwanta duk a kumbure, wani matsanancin kuka ta saki tace “Innalillahi wa Inna ilaihi raji’una, Allah kai 

kasan yanda xaka yi da axxaluman bayin nan naka, Ya Allah ka rufa min asiri ‘yar Dan uwana ta dawo cikin koshin lafiya, wllh Ita kenan garemu…” Kanwar Ammi dake Ward din ita ma ta fashe da kuka sosai, haka ma sauran 

mutanen ciki, Mahaifin Heedayah dai na xaune kusa da Ammi yana rike da hannunta, shi ma ko kadan tashin 

hankali bai boyu a fuskarsa ba, kawai ta maxa yake, Yakumbo ta mike tana hade hanya ta fice ward din kamar xata 

shide don kuka tana cewa “Shkkn ni dai tamu ta kare, ita kenan gare d’an uwana fa, na cikin ma anyi barinsa sbda 

wnn tashin hankali, wannan wani irin xalunci ne ake yi haka a duniya ni Khadijah, Allah ka tsine ma duk wanda ya 

raba mu da Heedayah, Allah ka isar mana, ka dawo mana da ita cikin aminci….” Kanin Abban Heedayah ya mike ya 

bi bayanta shi ma dai trying hard to control his tears. Kusan la’asar aka bude kofan dakin da su Heedayah ke ciki, ja 

baya kowa ya dinga yi a tsorace, Heedayah ta mike xaune daga kwancen da take tana kallon inda taji karan budewar 

kofa, su hudu suka shigo, ko wanne da bindiga, Ogansu na nuna wani matashi yace “Kai taso xaman ka ya xo karshe 

a nan, Yan uwanka sun yi abinda ake bukata” tashi yyi da sauri yana hamdala sauran mutanen wajen sai hawaye, www.bankinhausanovels.com.ng 

haka aka fitar da shi, ogan na nuna wani a cikin sauran yace “Kai yan uwanka na raina mana hankali, xuwa gobe 

idan basu yi complying ba xa mu aika ka barzahu kowa ya huta….” Yana fadin haka ya kalli wanda ke gefensa yace 

“Cikin yaran nan ka fito da guda daya a cire abinda ake bukata, me siya na kan hanya anjima, gobe da yamma ma 

akwai me xuwa zai siya” yana fadin haka ya fice, sauran suka bi bayansa, Mutumin daxu da ya kawo masu bredi ne 

kawai bai fita ba sai wanda aka sa ya dauko yarinya daya ya dinga bin yaran da kallo, Mutumi dai mai bredi ya nufi 

Zulai ya dagata ya fice tana ihu tana sakar masa fitsari, d’an uwansa ya bi bayansa ya garkame kofar, bbu abinda 

mutanen cikin dakin ke yi banda hawayen tashin hankali, Heedayah ta dinga waige waige jin ihun Zulai, matar dake 

kusa da ita ta rungume ta tana kuka sosai, cikin kuka ita ma tace “Aunty ina xa su kai ta??” Matar dai bata ce mata 

komai ba sai kuka. Washegari har kusan yamma basu samu an kawo masu bredin ma da ake kawo masu ba, 

Heedayah ta fada ma matar kusa da ita tana jin yunwa ya fi a kirga tun matar na ce mata xa a kawo abinci har ta gaji 

ita ma tayi shiru, kusan la’asar aka bude kofar wajen, mutumin da ke basu bread ne ya shigo da buhun bread da ruwa, 

nan duk ya jefa ma kowa, har bread din ya kare amma bai ba Heedayah ba, matar dake kusa da ita har xata yankar 

mata nata, Mutumin ya karasa ya daga Heedayah cikin kaushin murya yace “Mu je ki amshi naki” cikin rawan baki 

matar tace “A’a ko in yankar mata a nawa ba cinyewa xan iya yi ba, baxan ma ci ba….” Wani mugun kallo ya dinga 

mata hakan yasa tayi tsit jikinta na rawa, juyawwa yyi ya nufi kofa da Heedayah dake ihu tana kiran Ammi tana 

gatsa masa cixo a hannu, bayan ya fita ya rufe kofar, ya toshe bakinta yace “Ke xan halbe ki yanxu idan baki rufe 

min baki ba” Tsit tayi ko ina na jikinta na rawa tana kallonsa kamar dai tana ganin fuskarsa, xagawa yyi ya canxa 

hanya yanda sauran yan uwansa dake xaune a baya baxa su gansa ba, cikin hanxari ya karasa bayan wani karamin 

bukka da suke ajiye makamansu ya ajiyeta bayan Bukkar ya durkusa yana kallonta yace “You don’t move, ki tsaya www.bankinhausanovels.com.ng 

nan har in dawo idan ba haka ba, I have gun….” Kai kawai take gyada masa a tsorace tana komawa baya, ya mike da 

sauri ya koma inda Yan uwansa ke xaxxaune ana xuke xuke ana buga karta, Makullin mashin dake rataye jikin 

bishiya ya dauka yace “Xan je amso ruwa in dawo yanxu….” Wani daga cikinsu ya kallesa yace “Oga na hanya da 

customer fa” yace “Ehh yanxu xan dawo ai” har ya nufi gun da suke ajiye babur dinsu sai kuma ya juya da sauri ya 

sake komawa dakin da ya dauko Heedayah ya bude ya shiga yana masu wani kallo yace “Ko da an tambayi yarinyar 

nan kuce ta mutu an fitar da ita….” Tsuru tsuru suka yi suna kallonsa ya juya ya fita ya kulle kofar. Daga haka ya 

nufi machine ya hau ya tada, a guje ya bar wajen, dai dai inda ya ajiye Heedayah ya tsaya, sai xare ido take tana 

kalle kalle, ya daga ta ya daura gaban machine din yyi speed off, gudu kawai yake a dajin kamar mai race din 

motorcycle, tafiyar kusan awa daya da rabi suka yi suka shigo cikin gari sosai, a hankali yake tafiya yana kalle 

kallen jama’ah dake ta kokarin rufe wajajen sana’arsu kasancewar Magrib ya gabato, sai kuma ya tsayar da machine www.bankinhausanovels.com.ng 

din ya kashe, sauke Heedayah da tashin ta bacci kenan yyi, ya ajiyeta nan gefen hanya yana kallonta, laluba wajen ta 

shiga yi, jin ya sake kunna bike din da sauri tace “Noo, Are you leaving me??” juyar da Machine dinsa yyi ya dau 

hanyar da ya fito with speed, ta fashe da kuka sosai tace “Noo”

 _Heedayah_ 

_By Khaleesat Haiydar_ 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *