HEEDAYA CHAPTER 11 BY By Khaleesat Haiydar
Www.bankinhausanovels.com.ng
Mumy tace “Toh ki tafi ki hada shayin, kayan shayin na can kitchen, bredi kuma na parlona su Rabi’ah sun bar sa a
can” cikin rawan jiki Karime tace “Toh ngdd Hajiya, nagode” Mumy ta kuma kai idonta kan eye drops din sannan ta
fita Karime ta bi bayanta da sauri cike da jin dadi, main parlor Mumy ta xauna tana girgixa kafa, Karime kuma ta
wuce bangarenta dauko bread, Mumy ta bi ta da kallo har ta shiga ciki, dai dai nan kuma aka bude kofar parlon
Mumy ta juya don ganin wanda xai shigo, Kaka ce ta shigo parlon tana sakale da wani karamin jaka me kama da
handbag, Mai gadi na biye da ita a baya rike da wani tikeken akwati, Mumy ta bude baki ta mike da sauri tace
“Lafiya Kaka? Me ya faru??” Kaka bata ko saurareta ba ta nufi wani spare room dake nan cikin parlon tana cewa
“Ina fa lafiya? Meye kuma baxai faru ba? Sai kace dai Umaru kadai na haifa a duniya, ga dai gidan Amadu me
dakuna ta ko ina….” Har ta bude kofar sai kuma ta dawo tace “Wllh Maryam wani kwai suka soya min yau xar karni,
to ga dai albasa an cika amma ni dai naji yana karni na bala’i, ina laifin su d’an yanyanka min yar tafarnuwa su watsa
a ciki, wnn ba alamomin an gaji da kai bane a waje? Jiya sai bayan magariba suka kawo min abincin dare, tuwo da
wani miya sun cika naman kasuwa, to ca masu nayi yunwan nama nake?? abinda mu xamaninmu karfe biyar duk
mun ci abincin dare munyi wanke wanke kowa ya manta, mata kawai suna neman kashe ni kuma sai in xauna kamar
uwata tace min je ki kya gani, A’a wllh, to me gidan Amadu yake da baxan lallaba in dawo ba??” Mumy da ta ji
kamar ta kurma ihu cike da karfin hali tace “Haba kaka, Haba kaka, haba kaka, wllh hakuri ake a ko ina, ko ina
mutum yake sai yyi hakuri, rayuwar ma gaba daya d’an hakuri ne, ni ba gashi an min kishiya ba nayi hakuri muna
xaune lafiya? me yyi xafi xaki tattaro kayanki ki dawo nan ai baxa su ji dadi ba Kaka, gaskiya bari in dauko
makullin mota mu koma, baxa su ji dadi ba wllh barin Baffa, gani xai kamar baki gode kokarinsa a kanki” Kaka tace
“Koh??” Mumy tace “Wllh tllh, ai ba xamansu kike ba da xa ki bar masu gidan kaka, sun ma ci riba kenan, bari in
dauko makullin mota” Kaka tace “Toh, idan fita xa ki yi ga mai adaidaita can ki biyasa dari biyunsa kar ya mana
ihun 6arayi a unguwa yana can yana jira ban basa ko sisi na ba, dama kuma ban masu sallama ba ta baya na bar
masu gidansu, kya iya xuwa ynxu ki ce masu na dawo nan da xama, duk me nemana Ina nan gidan d’ana Amadu….”
Kaka na kai wa nan ta shige daki… Mumy ta xauna saman kujera tayi tagumi tana furta innalillahi wa Inna ilaihi
raji’un a xuciyarta, Mai gadi da ya ajiye kayan Kaka a parlan har ya tafi ya dawo yace “Hajiya D’an sahu na can yana
jira fa….” Cikin bacin rai Hajiya tace “Kai da d’an sahun sai na ci kaza kazanku idan baka fita idona ba, na hau
adaidaita ne da xa ka xo kace min d’an sahu na jirana???” Mai gadin ya juya ya bar bakin kofar… Shuraim da ya
dawo daga kai Abba office yana kallon Mai adaidaitan da ya gyara parking don basa hanya ya sauke glass yace “wa
kake jira malam?” Mai adaidaitan yace “Wata tsohuwa na kawo nan ta shiga wai xa a kawo min kudi to har yanxu
dai ina ta jira” Shuraim yace “Nawa ne?” Yace “Dari biyu ne kudin” Shuraim ya ciro dubu daya ya mika masa, D’an
sahun yace “Amma bani da canji wllh” Shuraim yace “To je ka” D’an sahun ya dinga yi masa godiya, Shuraim ya
gyada masa kai kawai ya ja motarsa xuwa ciki don Mai gadi ya bude masa gate, parking yyi ya sauka ya rufe
motarsa ya wuce ciki… Mumy ya tadda a parlor tayi tagumi ga tashin hankali karara a fuskarta, ya isa kusa da ita ya
xauna a hankali yace “Mumy lafiya” Mumy tace “Ina fa lafiya Aliyu, don Allah ka shiga ka lallaba tsohuwar nan ka
mayar da ita gida, kalli uban akwatin da ta kawo wai ta dawo nan, ta dawo wajen wa? Ta dawo tayi mana me? Don
Allah ka shiga ka lallaba ta ka maida ta inda ta fito….” Shuraim dake ta kallon Mahaifiyar tasa yace “Mumy amma ai
ba laifi bane don ta xo nan, Kuma ai….” A mugun fusace Mumy tace “Rufe min baki gantalalle kawai, dama ina
kuwa xaka san laifi ne dawowarta nan???” Lkci daya Mumy tayi tsit ganin Kaka ta fito har ta cire Hijabin ta, Kaka
tace “Kin sallami d’an sahun ko kuwa kin barsa yana can yana min kallon macuciya barauniya??” Shuraim ya mike
yace “Na sallamesa” Kaka tace “Atoh, Kai baka je aikin bane yau?” Yace “Sai da yamma, ina kwana?” Tace “Lafiya
lau, Shureen ni dai na dawo nan gaskiya, matan Umaru kasheni suka so yi Allah bai yi ba, yau wani kwai suka ban
da ya kusa kai ni lahira, shayin kuma sun cika masa kayan kamshi kamar dai buzaye… To ina dalili ga dai gidan
Amadu” Shuraim dai bai ce komai ba, Kaka tace “Ka shigar min da akwatina daki dukiya ne a ciki, jama’ah Ina Deedayah, ga bredi na taho mata da shi da kwai….” Shuraim ya dau akwatin nata ya shigar da shi ciki, Mumy dai
karfin hali kawai take don kiris ya rage hawaye ya xubo mata, kaka tace “Maryam tambaya nake Ina Deedayah?”
Mumy ta dake tace “Wacece kuma Deedayah?” Kaka tace “Sabuwar ‘yar Amadu mana….” Mumy ta wani tabe baki
tace “Ayyo makauniya wai?” Kaka tace “Aa wannan kuma isgilanci kike ma ubangiji ba ruwana, ke kika halicceta
da xaki kirata da makauniya, meye kuma makauniya idan ba isgilanci ba, ko ita ta xabar ma kanta makantar? Ni
yanxu Ina take??” Duk wannan abun Karime na tsaye sai kallon kaka take, Mumy ta nuna mata Karime tace “Ga me
kula da ita can” Kaka ta kalli Karime tace “Wacece kuma wnn sai naso take, ta kula da ita ko ta sa mata cuta, bakya
wanka ne baiwar Allah?” Karime ta kasa cewa komai, Shuraim dai yyi murmushi ya nufi dakinsa, Kaka na kallon
Karime tace “wa ya daukeki ki dinga kula da ita, Amadu ko wa? Tunda ita uwar rikon tata na samu labarin har ta
fara fita aiki, Amadu ya fita ita ma ta fita….” Karime ta girgixa kai tace “Aa, Hajiyar ce ta daukeni…” kaka tace “Toh
kuma sai kiyi ta kazanta kina naso, ba kya tashi da safe ki sa ruwa kiyi wanka ki dauko yar atamfar ki ko da kodadde
ne ki saka kiyi fess da ke.. yanxu Ina yarinyar take?” Karime tace “Tana can daki kwance,” Kaka tace “Wannan
xama da ke ai sai cuta ya kama ‘yar mutane…” Daga haka kaka ta nufi part din Mami tana cewa “Ita kuma mata daga
tarewa sai fara fita aiki kamar auren banxa aka daura mata, ni ba ruwana” Zaune kaka ta ga Heedayah saman gado ta
tashi tana mitsika ido, Kaka ta washe baki tace “Deedayah… Kin tashi” Heedayah ta juya da sauri tana duban Inda ta
ji muryarta tace “Kaka” Kaka ta karaso tace “Ehh ni ce Deedayah, kin ga na dawo nan yanxu, kwai suka bani duk
karni, kinji dalilin barin gidansu da nayi” Sakko mu je ga bredi da kwan na kawo maki kema ki ci ki ji, Heedayah ta
sauka saman gadon kaka ta kama hannunta suka fita tana cewa “Ita dama ashe ba don ta kula da ke aka aurota ba,
xata barma katuwar mata kazama ta sa maki wani cutan Amadu ya shiga uku….” Heedayah tace “Kaka tafiya xa ki yi
da ni can gidanku?” Kaka tace “Wani gida? Ai na dawo nan sai kuma wani ikon Allah, abincin banxa fa suke bani a
can gidan wllh Deedayah….” Mumy ta bi su da kallon gefen ido, Kaka ta tsaya tana rike da hannun Heedayah tace
“Maryam ban fa karya ba, Kuma ni ba shayi xan sha ba gaskiya, ko me aka samu ni dai a bani in ci fisabilillahi”
daga haka ta shige dakin da ta sauka tare da Heedayah, Mumy ta mike ta wuce bangarenta da sauri ta dau wayarta ta
shiga Kiran Hajiya Sadiya, Hajiya Sadiya na dagawa Mumy ta sakar mata Kuka tace “Sadiya wllh shirinmu na ta
rugujewa, yau dai ga wnn tsohuwa ta diro da katon akwati, ynxu haka ta dauke yarinyar ta shige da ita dakin da ta
sauka, wato bbu ma ranan komawarta ne don sai kinga akwatin da ta kawo, ni dai wllh Sadiya hakurina ya fara
karewa ji nake kamar in kashe yarinyar nan a gaban kowa a daureni kawai in huta, wnn yarinya har in mutu xan
mance da ita kuwa a rayuwata, ta janyo min dariya a duniya, Duk fa dariya ake min a boye Sadiya” Sadiya tace “Ki
kasheta kuma a daure ki Maryam, me aka yi kenan? Ke ina gaya maki gaggawa na shaidan ne kin kasa fahimta ko,
meye na gaggawa abinda dai ana tare….” Mumy tace “Toh ke kina ga wnn tsohuwar da ta diro mana gida ynxu
baxata kawo mana wani cikas ba?” Hajiya Sadiya tace “To ke meye ruwanki da ita? Wajenta yarinyar take da xai
dame ki, Kinga xa mu yi waya anjima nayi bakuwa” daga haka ta katse wayar, Mumy ta xauna gefen gado tayi
tagumi hawaye na sauka idonta…. Karime da Sajida tasa suka girka ma kaka shinkafa da miya ko damuwa da ynda
suka yi girkin bata yi ba… Kaka na kallon Heedayah dake kwance gefenta tace “Toh sai kuma a siya maki?”
Heedayah tace “Ehh mana, har kitso Ina yi ma gashin babyn nawa….” Kaka ta rike ha6a tace “A makancen?”
Heedayah tace “Na’am” kaka tace “Toh yanxu a nan wani gantalalle ne xai siya maki wani baby ana xaune kalau??”
Heedayah tace “Abba mana” Kaka ta ja kunnenta tace “Ke ce gantalalliya ba d’a na ba, shi Abban ne gantalalle?”
Heedayah tace “Aa ai Mami ma xata siya min” Kaka tace “Atoh sai dai ita din, Amadu ba gantalalle bne…” Bude
kofar dakin aka yi Shuraim ya shigo da sallama, kaka tace “Ko kuma Shureen ya siyo maki ba?” Heedayah tace
“Waye shureen?” Kaka tace “Aa nima haka naji suna ce masa amma sunansa Aliyu…” Heedayah tace “Ae ban san
shi ba” Kaka tace “Toh ai sanin nasa bashi da amfani don bashi da kyakkyawan alaka da mutane, mugun hali ne da
shi, kin ga ai tun daxu da na xo bai shigo gaisheni ba sai ynxu…” Heedayah tace “Shi ma a nan gidan yake?” Kaka
tace “To Ina xa sa? Ai gidan Ubansa ne nan din… da dai yyi aurene sai ya bar gidan, ni da Allah xai fito masa da
mata ma yyi auren kowa ya huta don wannan shiru shirun da yake yi idan xamaninmu ne cewa xa ayi aure yake so”
Shuraim dake tsaye bakin kofa ya hade rai yana kallon kaka da Heedayah bai dai ce masu komai ba, Heedayah tace
“To ki ce masa ya siya min babyn Kaka, babba nake so” Kaka ta kalli Shuraim tace “Kaji kai Shuraim ko ba mai
tsada bane ka dubi maraicinta ka siya mata domin Allah, ya fi tayi ta xama shiruuu kamar kurma…” Yace “Toh sai ta
xo ta kwata ai” Heedayah na jin muryarsa ta matsa kusa da kaka a hankali bata kuma cewa komai ba, Kaka tace
“Atoh, tunda ba ajiya ta ba mutane ba ai sai ta hakura da Babyn dama” Tsaki Shuraim yyi ya juya ya fita ya rufe
dakin, murya can kasa Heedayah tace “Kaka ya wuce?” Kaka tace “To me xai min dama, ya wuce” Heedayah ta turo
baki tace “Ni bana son sa” Har aka yi azahar Kaka na dakinta tare da Heedayah, bbu irin labarin da bata ba
Heedayah ba wanda kwakwalwarta xai dauka da wanda ma baxai dauka ba, Tun tulin shinkafa da miyan da aka
kawo mata da safe ba a sake kawo mata wani abincin ba…. Karfe uku da yan mintuna Mami ta dawo gida daga
office, Karime na xaune kasan carpet a main parlor tana kallo, tun kiran da Mumy tayi mata dakinta bayan sun gama
yi ma Kaka girki ita da Sajida sai lkcn ta sauko kasa ganin lkcn dawowar Mami yyi, ta mike da sauri daga xaunen da
take tana yi ma Mami sannu da xuwa xata amshi jakar hannunta, Mami ta ki bata jakar tace “Ina Heedayan take?” Karime tace “Ai kina fita Hajiya sai ga wata da naji suna ce ma kaka ta xo gidan, to tun safe da ta shigo ta fita da ita
xuwa wancan dakin bata yadda na je gunsu ba ma, ynxu haka suna ciki” Mami tace “Kaka?” Karime tace “Ehh haka
naji suka kirata, kuma Sajida tace min Baabar Alhaji ce” Mami ta nufi dakin da kaka take ta yi sallama sannan ta
bude ta shiga, Heedayah na xaune tana cin shinkafar da kaka ta xuba mata, ita kuma kaka na kara gyara kayan
akwatinta don a birkice ta jerasu sbda sauri, Mami ta xauna nan kasa da murmushi fuskarta tace “Sannu Kaka” kaka
tace “Yauwa sai yanxu kike dawowa kenan” Mami tace “Ehh yanxu na dawo” Kaka tace “Toh sannu da xuwa….”
Heedayah dake washe baki jin muryar Mami tace “Mami kin siyo min Babyn” Kaka tace “Wani baby? Ki samu ma a
samu lkcn kula da ke ba wani shegen baby ba, ke yanxu fisabilillahi Rakiya da kika hadata da wannan yar aiki duk
wari ta kula da ita idan cuta ya kamata wa aka kai aka baro??” Mami bata ce komai ba tayi shiru tana kallonta, kaka
tace “Kice min Amadu, to wllh xuwa nayi na samu mai aikin duk wari wai ita ce me kula da Deedayah, ki fa bar
ganinta makauniya ki xata bata da galihu Rakiya, ke kina ganin fatan jikinta kinsan ba daga cikin wahala ta fito ba,
gashi har abincin banxa na ga bata yrda ta ci sai na yan gayu, jikinta kwata kwata bai son wahala, wa ya sani ma ko
daga kasar waje wani axxalumin ya sato ta ya wullota nan Nigeria da mugun abu yyi yawa?? Allah kadai yasan me
yasa ya hadata da Amadu a titi, kema gashi ta albarkacin ta ya aure ki, wa yasani ko kin dade kina jin son sa a
xuciyar ki sai gashi ta dalilin Deedayah ya aure ki…” Mami dai tayi murmushi tace “Ai nayi mata komai kafin in fita
kaka, abincin rana kawai take bata sai abinda ba ka rasa ba, kuma baxai yiwu in dinga fita da ita aiki bane da tare xa
mu dinga xuwa” Kaka tace “Toh ni dai na dawo da ita nan ba ruwana, sai in ga uban da xai dinga cutarta, mace duk
wari kice ita xata kula da cin ta da shan ta, kishiyar ki kuma tun xuwana da safe har ynxu ban ga keyarta ba, duk
wannan bai dameni ba tunda ke kin shigo, ynxu abinda nake so dake ga wayata ki kira min Junaidu don mun yi da
shi xai xo yau kar yaje can bana nan, ba komai yasa na bar gidan ba sai kwai da suka kawo min duk karni” Mami ta
amshi wayarta ta sa number Junaid sannan ta kira sa ta mika ma kaka, kaka na jin ya dauka ta washe baki tace
“Junaidu… to yau dai gidan Amadu xaka taho na tattaro gaba daya na dawo nan” Junaid ya gaisheta yace “Toh shkkn
kaka sai na xo” tace “Allah ya maka albarka ya kare ka sharrin makiya, ni ai ka fi min kowa” Murmushi kawai
Junaid yyi ya amsa da Ameen sannan yyi mata sallama ya katse wayar, Mami na kallon Heedayah ta kama hannunta
tace “Mu je ki canxa kaya” Kaka ta kalleta da sauri amma bata ce komai ba, Mami ta mike rike da Heedayah tace
“Sai na shigo anjima kaka” Kaka ta bi su da kallo a hankali tace “Yauwa” Suna fita kaka ta mike ta fita ita ma ta nufi
dakin Shuraim da sauri, yana fesa turare ta samesa a dakinsa da yake a gyara kamar dakin mace, ko ina fesss sai
sanyin Ac, kaka ta xauna gefen gado ta fashe da kuka sosai, ya juya yana kallonta da mamaki, ganin irin kukan da
take ya nufeta yace “Lafiya kaka? Me ya faru” Tana Shessheka tace “Mata ki fita tun safe ki bar yarinya Ina wahala
da ita daga dawowa sai ki dauketa, Halan ita ta tsinto ma Amadu ita bani da labari ko kuma kanwar uwar yarinyar ce
ita bamu sani ba, Yarinya muna xaune lafiya banda hira babu abinda muke yi tun safe ba irin labarin da bata bani ba,
bbu irin labarin da ban bata ba kawai mata ta xo ta dauketa su wuce sbda bakin ciki….” Ta fashe da wani sabon
kukan tana mika masa wayarta tace “Kira min Junaidu….”Shuraim ya dauke kai ya juya ya koma gaban mirror ya dau makullin motarsa, Kaka ta mike tace “Baxa ka kira min
shi bane Shureen?” Ba tare da ya juyo ba yace “Ehh baxa a kira ba, waye kuma wani Junaid….” A fusace Kaka tace
“Aa wllh kar ka xagar min shi don in ka xagesa ni ka zaga, kar ma ka fara wllh, ance maka bai fiye min kai ba sau
dubu, Ina ruwana da kai dama idan ba kaddaran na haifi uban ka ba, wllh Junaidu ya gama min komai, kana xagin sa
xaka xago ma kanka fitina, don ni ka xaga….” Ta koma ta xauna ta fashe da wani sabon kukan, bude kofa Shuraim
yyi ya fice daga dakin ya kulle, kaka ta tsaida kukan da take a hankali tace “Ehh lallai d’an Amadu ya ci ganye…”
Mikewa tayi ta bi bayansa fa fita. Mumy ce tsaye ta wajen flowers dake bayan gida, sbda shuke shuken flowers din
wajen sai ya fi kama da garden, waya ne kare kunnenta cike da damuwa tace “Wllh kuwa Baffa, ni dai nayi ta bata
hakuri ina kwantar mata da hankali, to kaga bbu ddi idan ban kira ka na sanar maka ba tunda cewa tayi kai ma ba
son xamanta kake a gidan ba, kuma idan anyi duniya don manzon Allah ita da gidan har abada tunda xaman dole ku
ke da ita, har mayar da ita na yi niyyar yi tace ta koma a wani matsayin?? Tunda har ynxu bbu wanda ya biyo ta ko
ya kirata ya bata hakuri yace ta tashi su koma, to shine nake ga gwara ka taho da kanka ka kara bata hakuri sannan
ku tafi don wllh ta dau xafi sosai, ni ban ma ta6a ganin bacin ranta irin na yau ba, kuka kuwa ta sha shi har ta gode
Allah, xan kira barrister in sanar masa ta hanani wai ita xaman garin ma duk ya fita a kanta, gidan nawa ma ba xama
xata yi ba, wai xa a iya wayan gari a ga bbu ita ta bar garin, to shine naga gwara in kira ka…” Baffa dake ta
sauraranta ya sauke ajiyar xuciya yace “Shkkn Maryam nagode, sai na shigo anjima” Mumy tace “Babu komai,
amma don Allah kar kace ni na kira ka, idan ma kace mata ni na kira ka kara baci ranta xai yi tace wato ma sai da na
kiraka ka xo, da ban kira ba baxa ka xo ba, kuma idan xaka xo sai ka d’an taho mata da abinda kasan ta fi so” Baffa
yace “In sha Allah, sai na xo” daga haka suka yi sallama, Mumy ta katse wayar tana wani murmushi, lkci daya ta
sauke ajiyar xuciya, cikin compound din ta koma dai dai shigowar Junaid, har xata hade rai ganinsa ko me ta tuna
kuma sai ta sake fuska sosai, ya gaisheta da ladabi ta amsa tace “Sannu da xuwa junaid, kwana biyu baka shigo ba”
yace “Ehh naje Zaria ne” Mumy tace “Kuna da ‘yan uwa can kenan” yace “Aa, naje wani uxuri ne a can” tace
“Ayyo… To sannu da xuwa” yyi mata godiya sannan ya nufi entrance din shiga gidan, ta bi sa da wani kallo har ya
shiga parlor… Sajida ce ke ta share share a parlor, ta mike tana gaishesa ya amsa yace “Wani dakin Kaka take?”
Sajida ta nuna masa hanyar dakin, can ya nufa, yyi sallama bakin kofar, Kaka ta amsa da karfin ta, ya bude kofar ya
shiga, kaka na xaune ta daura kafa daya kan daya, Khadijah na jera mata tarkacenta na tsofaffi a gaban madubi,
kofar bathroom a bude Karime na ciki tana ta faman wankewa, Junaid ya xauna nan kasan carpet yace “Sannu kaka,
Ina yini” tana washe baki tace “Lfya lau Junaidu, sai ynxu??” Yace “Ehh kaka, ashe kin dawo nan…” Ta gyara xama
tayi narai narai da ido tace “Baxan dawo ba Junaidu, kwai suka soya min duk karni gashi fari fatt sai uban albasa to
hakan ba alamar an gaji da kai bne, to shine naga tun kafin sun barbadamin shinkafar bera gwara in gudu, ynxu hka
ba wanda ya san ina nan, kilan suna can hankali tashe sun kai rahotu gidan ‘yan sanda” Junaid da kansa ke kasa yana
murmushi yace “Da dai kinyi hakuri Kaka….” Shiru tayi tana kallonsa can tace “Aa kar ka xama gantalalle kai ma
mana, ae in kowa ya gaya min wnn mugun magana kai bai kamata ka gayan ba, inyi hakuri su cuceni su kasheni a
banxa, sae kace Umaru kadai na haifa, ga dai Amadu, Aa ba ruwana, ni duk wanda yace in koma can gidan ma
haushi na kawai yake ji ya tsaneni” Junaid ya ajiye ledan hannunsa yace “Allah ya sa hakan shine mafi alkhairi”
Kaka tace “Toh ka ga ynxu kayi magana, Kuma in sha Allahu alkhairin ne dama” murmushi kawai yake yi, kaka tayi
kasa da murya tace “kana ji Junaidu, dama uwarka haka take ban sani ba?” Junaid ya daga kai yana kallonta, kaf ta
kwashe labarin abinda Mami tayi mata ta sanar masa tana matsar kwalla, tace “A gantale fa ta barta gun mai aiki
dake naso uwa an tuttula mata jarkan man gyada, ynxu hka fa ga Mai aikin can na sa ta wanke bandaki na, kuma ban
amince ta shiga bandaki na ba sai da tayi wanka wllh, to mata daga dawowa kuma sai ki dauke min yarinya haka
kawai, yini fa muka yi tare da yarinyar bbu wanda ya ji kanmu, muna ta hira fa in gaya maka” Junaid yace “Gaskiya
bai kamata…..” Kaka tace “Allah ya maka albarka, daga shigowa gida sai ta fara fito da mugun halinta da wuri wuri
hka tun ba aje ko ina ba, ni sai nayi tunanin ma ko tasan uwar yarinyar ne wnn isa haka da ta nuna min….” Junaid ya
d’an yi murmushi yace “Xan je in dauko maki ita ynxu kaka” kaka tace “Amma fa kar kace nace maka komai, ba
ruwana kar ta kullaceni, kawai dai kayi mata nasiha ta canxa halinta, wannan ba halin xaman gidan miji bane…” Ya
mike still smiling yace “In sha Allah kaka, bari in je in dawo” Kaka tace “Allah maka albarka, ni dai gwara min kai a
kan kowa ma a gidan nan” Kaka ta kalli Khadijah da sauri tace “Ke ‘yar banxa kin gaishe sa ma kuwa da ya shigo?
Ku dai ‘ya yan Amadu baku da hali tirrr” turo baki Khadijah tayi tana ci gaba da abinda take, shi dai Junaid tuni ya
fita ya rufe mata kofa, part din Mami ya nufa ya sameta xaune parlor ta daura kan Heedayah a cinyarta tana mata
gyaran gashi, Heedayah ta mike xaune da sauri jin muryarsa, ya xauna saman kujera ya gaida Mami, Mami ta amsa
tace “Na xata da Farida xa ku xo” yana kallon Heedayah yace “Aa, Uncle said she should stay” Mami tace “Okay,
how are you” yace “Alhmdllh, ya aiki” tace “Mun gode Allah” Ya mike ya koma kujeran da suke ya xauna gefen
Heedayah yana kallonta yace “How are you Heedayah” Ta wara ido tace “Fine, me yasa baka xo ba jiya har da
shekaranjiya” Yace “Ae gani na xo yanxu” Ta laluba fuskarsa tace “To ka dinga xuwa kullum ka ji?” Mami dai ta
tabe baki tana harhada kayan gyaran gashinta, Junaid na murmushi yace “Mami kaka tace a maido mata da
Heedayah” Mami na kallonsa kafin tace komai ya kara da cewa “She wants her to be staying with her, bata ji dadin xuwa da kika yi kika dauketa ba daxu” Mami ta rike ha6a tace “Tohhh, ikon Allah” Junaid yace “Yess allow her ta
koma wajen ta Mami, since ita ta bukata” Mami tace “Toh ai naga kamar wani nauyin Heedayah xata xame mata,
baxata iya da tsirfan Heedayah ba” Junaid tace “Tunda ita ke son hakan ki bar mata kawai Mami” Mami tace “kai
yaushe ta gaya maka haka?” Yace “Yanxu, har da kukan ta” Mami ta bude ido tace “Ahh to dauketa ka kai mata ita”
Heedayah dake jin su tace “Mami wajen kaka xai kai ni?” Mami tace “Ehh” Heedayah tace “Amma xan dawo koh?”
Mami tace “Ehh xa ki dawo” Junaid ya mike ya kama hannunta suka fita parlon, Mami ta bi su da kallo…. Mumy
dake xaune parlor kamar dai ko da yaushe ta bi su da kallon gefen ido har suka wuce dakin kaka, Kaka na ganin
Heedayah ta washe baki tace “Deedayah, ga kaza Junaidu ya kawo min, ai kin iya cin kai da kafar kaza koh?”
Heedayah tace “A’a ni lap na iya ci” Kaka ta kalli Junaid tace “Meye lam kuma?” Yyi yar dariya yace “Cinya” Kaka
ta kalli Heedayah da sauri tace “To sai ki kwata ai, ka ji min dai” Ya xaunar da ita gefen kaka yace “Kaka xan je
Masallaci in dawo” Kaka tace “Toh yi maxa gashi can an fara kira” a hankali Heedayah tace “Are you coming
back?” Ya juya yana kallonta yace “Yess” Yana fadin haka ya juya ya fita, Kaka tace “Toh ko wnn lafiyayyen
turancin da kike ai ya ci kowa ma ya san ba daga gidan gantalallu kika fito ba, da kyar idan baki fi Shureen iya
turancin ba don ni tunda nake ban ta6a jin ma yyi turancin ba, ga dai makaranta me tsada uban ya sa shi yana karami
amma bai jin turanci, ko wnn kwam din da kowa ya sani baya ji” Heedayah ta kyalkyale da dariya tace “Kaka to sai
in dinga koya masa mana” Kaka tace “Atoh, bari dai Allah ya shigo da shi mu ga ko xai yadda” Heedayah tace
“Kaman ni yake?” Kaka tace “Ka ji ki wannan a haihuwar kaji ai yyi jika da ke, Shureen fa nace maki” Heedayah
tace “Ni ban san shi ba” Kaka tace “Idan ya shigo xan Kai ki ki tattabasa ki ji” Heedayah tace “Toh” Tare Junaid ya
shigo cikin gidan da Baffa, Baffa ya xauna parlor shi kuma ya shiga wajen kaka yace “Kaka Baffa ya xo” Kaka tace
“Waye kuma Baffa, uban wa yace masa Ina nan, Kai ni dai gaskiya ana shiga hakkina, to me ya xo min kuma kamar
dai wata yar karamar yarinya” Junaid na murmushi yace “Ya xo ne ya tabbatar nan din kika xo” Kaka ta tabe baki
tace “Ni dai ba ruwana wllh” Bude kofar dakin aka yi sai ga Hajiya Amina da Hajiya Hauwa sun shigo da sallama,
Kaka tace “Su waye wannan kuma” Hajiya Hauwa tace “Sannu kaka” Kaka tace “Yauwa, daga ina haka kamar an
koro ku, ko daga anguwa ku ke?” Hajiya Amina tace “Daga gida muke kaka, mun xo biko….” Kaka tace “Yaji
Maryam din ta kara yi ina gidan bani da labari??” Hajiya Hauwa tayi dariya tace “A’a kaka, kawai sai mu ka ga ba ki
a gida” dai dai nan Mumy ta shigo dakin, kaka tace “Wllh na so shiga in maku sallama amma sai nayi tunanin bacci
ku ke don na San ku da baccin safe, tashi nayi yau da tunanin Amadu a raina shine nace bari dai in je shi ma ya sami
lada na….” Baffa ne ya shigo da sallama, kaka tace “Ikon Allah, har da kai Umaru, to me ya faru ne wai? Ba fa kai
kadai na haifa ba da xanyi ta xama gidanka, shkkn kuma shi Amadu ba mutum bne da baxan dinga xuwa nasa gidan
ba, Kar ka xama me son kanka mana Umaru, ka so ma d’an uwanka abinda kake so ma kanka, shima ka barsa ya
dinga samun ladan uwarsa” Baffa yace “Nayi tunanin ko an 6ata maki rai ne ai Baaba” Da sauri kaka tace “Aa wllh,
baku ta6a min komai ba, idan nace ma kun mun sai Allah ya kamani, matan ka ai mutanen kirki ne tun ma ba Mai
jidda ba, tamkar ynda xa su yi ma iyayen su suke min, to sae in masu sharri ince sun min wani abu?? Aa kawai ni dai
na xo gidan Amadu ne shi ma ya samu lada….” Kallonta kawai junaid yake with surprise, Mumy da hawaye ya cika
idonta tace “Amma fa kaka cewa kika yi kwai suka soya maki duk karni sannan basa baki abinci da wuri kawai sun
gaji da ke ne….” Kaka ta saki salati tace “Yau naga abinda ya isheni jama’a, Maryam ke da wa ku ka yi haka???
Lalacewar ta ki ta kai haka bani da labari? To ke ina ruwanki ko danyen kwai suka kawo min, ba gwara su sun kawo
min kwan duk karni ba, ke me barina da yunwa fa??” Baffa yace “Toh kaka tunda dai bbu wani matsala shkkn sai
dai mun yi waya” Kaka tace “Bbu ko wani matsala Umaru Allah yyi ma kai da matanka albarka…” Baffa ya amsa da
Ameen ya fita….Mumy dai hawaye ya ki tsaya mata, Hajiya Hauwa sai danne dariyar ta take, daga karshe ita ma tayi
ma Kaka sallama ta fita haka ma Hajiya Amina, Mumy ta bi bayansu xuciyarta na tafarfasa, Junaid dai kansa na kasa,
kaka tace “Ka ji min mata dai xata min sharri da rai na” Tuwo da miyar egusi Sajida ta kawo ma kaka, Kaka tace “To
ba gwara ke ba kan wannan mata da Rakiya ta dauka aiki duk wari…. Tafi ki kawo min flet da cokali” Mai aikin ta
fita sae gashi ta dawo, Kaka ta amsa ta bude warmer din tuwon ta diba, ta ajiye ma Junaid, Junaid yace “Kaka ni fa a
koshe nake” Kaka tace “Aa ni ba ruwana gashi nan ka ci, kana da Inda xaka je ka ci abinci ne da ya fi nan….” Ta
kalli Heedayah tace “In xuba maki kema” Heedayah tace “Na koshi” Kaka tace “To wlh baxan baki Kai da kafar
Kazan ba ma” Heedayah ta mike xaune kamar xata yi kuka tace “Toh in ci da Yaya” Kaka ta kalli junaid, Tashi yyi
ya koma kusa da ita da plate din tuwon yace “Toh mu ci” Kaka ta ta6e baki tana xuba nata, Heedayah ta d’an fincili
tuwon bayan ta laluba plate din ta kai baki, Kaka tace “Wllh haramta maka tuwon xata yi, meye kuma na mintsilin
tuwo kamar kaza??” Dariya junaid yyi ya deba a cokali kadan ya tabbatar ya huce sannan ya kai bakin Heedayah,
Jin cokali a lips dinta ta bude bakin ta amshi tuwon, a haka suka dinga cin tuwon, aka bude kofa sai ga Shuraim ya
shigo, kaka tace “Shureen wai xaka dinga koyon turanci gun Deedayah” Shuraim ya kalli Heedayah da ta tankwashe
kafa a gaban Junaid, ajiye ledan hannunsa yyi nan gefe ya fita dakin, kaka ta kalli Junaid tace “Kila kunya ya ji, da
ban masa magana a gabanka ba” Dariya sosai Junaid yyi… Sai kusan karfe tara yayi ma Kaka sallama Heedayah har
da kukanta wai xata bi sa, ya samu dai ya lallabata ya fita, Kaka tayi tagumi tace “Toh wai a gidan ubanwa kika ta6a
sanin Junaidun idan ba gulma ba?? Sai kace shine Amadu? Ai ni da Amadu ne dolen ki…” Wajen karfe sha daya Mami ta shigo da eye drops din Heedayah, Kaka da har ta kashe wuta tace “Kinga Rakiya, abinda xai faru ba sai kin
dinga ba kanki wahalan shigo mana tsakar dare ba mun fara bacci, kawai ki nuna min ynda xan dinga sa mata a idon,
Amadu fa ya fi awa daya a dakin nan sannan ya fita, tun daxu ya kamata ki xo ai, ni na xata kin gaji kin kwanta ne”
Mami tace “Aa ban kwanta ba” kaka tace “To nuna min ynda abun yake in dinga yi mata da kai na” Mami ta nuna
ma kaka ta tabbatar ta gane din tana kuma tsaye ta diga ma Heedayah dake bacci drops din dare sannan tayi masu sai
da safe ta fita… Har kaka ta kashe wuta aka sake bude kofa, Mumy ce ta shigo kaka ta kunna wuta tace “Amma dai
bakwa tsoron Allah matan gidan nan, bakin cikin baccin ake mani cikin daren ma” Mumy tace “Yi hakuri kaka, naga
baki bacci da wuri ne ban san kin kwanta ba, kankana na yanka ma Barrister shine na dibar maki” kaka tace “Ki sa
min a firiji, amma wnn ae shiga hakki ne, meye kuma kankana tsakar dare jama’ah kamar ana yunwa” Mumy ta bude
fridge dake dakin ta ajiye tana kallon eye drops dake ajiye saman fridge din, lkci daya ta kwashe su tace “Toh sae da
safe kaka” bata jira cewarta ba ta fice daga dakin, kaka ta ja tsaki ta kashe switch din wutan…. Har wani murmushi
Mumy take ta wuce dakinta da sauri, bandaki ta shiga da wayarta ta doka ma Sadiya kira, Sadiya na dagawa tace
“Toh ga dai eye drops din na samo Sadiya… Kin yarda Allah na tare da ni?? Wllh cikin ruwan sanyi na samu, ban
ta6a xaton hka ba….