HEEDAYA CHAPTER 12 BY By Khaleesat Haiydar
Hajiya Sadiya dake sauraren Mumy tace “To kin dauko cikin ruwan sanyi maidawan fa Maryam?” Mumy tace “Aa
ni maidawan ba wani damuwa ta bace, minti nawa ne, abinda dai ba makulli take sa wa a dakin ba….” Sadiya tace
“Toh shkkn, amma wajen bude maganin kiyi ta ynda fa baxa a gane ba, a nutse xaki yi komai” Mumy tace “Toh
shkkn sai mun yi waya Sadiya” Daga haka ta katse wayar ta fito, handbag dinta ta nufa ta bude ta binciko wani
kwalba irin na magani dake karkashin jakar ta ciro sannan ta rufe jakar, kokarin bude eye drop din ta dinga yi amma
ta kasa, tayi tayi amma ya ki buduwa, wuka ne ya fado mata ta Kalli agogo taga sha biyu saura, ta d’an yi murmushi
ta ajiye drops din a drawer ta nufi saman gado ta kwanta tana jiran karfe daya yyi don wnn lkcn ta tabbatar kowa na
gidan yyi bacci, tana ta kwance idonta kyar ko digon bacci bbu har agogo yyi struck din karfe daya dai dai, ta mike a
hankali ta saka hijab dinta har kasa sannan ta dau drops din da kwalbanta ta fita daga dakin, cikin Hijabin nata ta
boye hannunta me dauke da eye drops da kwalba, kitchen ta nufa direct ta kunna wutan, sannan ta juya baya ta ciro
abubuwan cikin hijab dinta ta dau wuka ta fara gwada bude eye drops din a nutse, she was so careful kar saman yyi
shaidar da xai sa a gane an bude, bude kofar kitchen din taji anyi, a rikice ta boye komai cikin Hijab, muryar
Shuraim taji yace “Baki kwanta ba Mumy, what are you doing” kin juyowa tayi ta dinga kawar da plate da cups din
karya duk a rude, amma lkci daya ta dake tace “Me ya hanaka bacci har war haka??” Yace “Shayi xan hada” Mumy
ta hade rai sosai tace “Wannan shan shayin dai ya xame maka jaraba, wani shayi ne baka sha ba tun wayewar garin
Allah sai tsakar dare kamar maita ka tashi wai xaka sha shayi? Shayin me? idan baka sha shayin ba mutuwa xaka yi
ko me da baxaka hakura ba tunda dare yyi” Shi dai bai ce mata komai ba, har sannan hannunta daya na boye hijab
dinta, ta nufi kofa a fusace ya bi ta da kallon gefen ido, cup ya dauka ya bude flask ya debi ruwan Lipton ya bude
kayan shayin xai hada, Mumy tayi still ganin kaka a parlor, lkci daya gabanta yyi mugun faduwa kaka ta karaso Inda
take tace “Amadu yyi bacci ne?” Cikin rawar baki Mumy tace “Lafiya Kaka, me ya faru?” Kaka tace “Ina fa lafiya, idonsa biyu ko yayi bacci?” Mumy da hankalin yyi mugun tashi don cikin d’aga murya kaka ke magana tace “Kaka
ban san ko yyi bacci ba daga kitchen….” Abba ne ya fito parlon jin muryar mahaifiyar tasa, Kaka na ganinsa tace
“Amadu wannan wani bala’in ka kawo wa mutane gida, ya xa a dinga shiga hakkina Ina bacci, to gata can ta hanani
bacci wai shayi xata sha, meye kuma shayi kamar buxuwa tsakar daren nan” Mumy bata san lkcn da ta sauke wani
bayyanannen ajiyar xuciya ba, Kaka tace “Ni dai ba ruwana, tun wayewar gari bata gama shaye shayen shayinta ba
sai ynxu bayin Allah na hutawa, kawai ta cuceni ta tasheni” Abba dai bai ce mata komai ba, kaka tace “Ga ta can
xaune kamar yar mage ta ki bacci wai shayi, to ni siyar da shayi nake xata tasheni ta dameni” Abba yace “Kiyi
hakuri, bari a maida ta gun Rahinah” Kaka ta kallesa da sauri tace “A maida ta kuma? A kan me? To sai kayi ta
maida ta din ae, daga tace xata sha shayi sai a maida ta gun Rahilah” Duk wnn abun Shuraim na tsaye rike da cup
din shayinsa yana kallonsu, Mumy tace “Kiyi hakuri kaka bari in hado mata shayin yanxu” Shuraim ya karaso cikin
parlon Kaka na kallonsa tace “Waye wnn kuma?” Mika mata cup din hannunsa yyi ta amsa tace “Toh ba shkkn ba
dai, amma xaka wani ce a maida ta gun Rakiya, meye hadinta da Rakiya, Kuma waye bai san yaro ba Allah na tuba”
Daga haka ta wuce dakinta rike da shayin, ta gefen ido Mumy ta dinga hararan Shuraim da ya juya ya wuce dakinsa
shi ma, Abba ya girgixa kai ya koma bangarensa. Mumy ta tabe baki don har yau ba wani shiri take da shi ba,
dakinta ta koma ta sa makulli ta ci gaba da aikinta, da kyar ta bude drops din ta wuce bandaki ta tattular da maganin
ciki ta dauraye empty container din da ruwa a nutse sannan ta dawo daki, kwalbanta ta bude ta xuba content din ciki
wanda kalansa shi ma fari ne a robobin eye drops din, snn ta rufe gam da murfi… Ta ajiye robobin su bushe a gaban
madubi tana yi tana kallon agogo, sai biyu da kusan minti goma ta kwashe magungunan ta bude kofarta a hankali ta
fito parlor, kwance ta ga mutum saman kujera yyi rub da ciki, duk da wutan parlon a kashe yake amma wutan
compound ya d’an haska har cikin parlon, ta yi still a Inda take don ta san baxai wuce Shuraim ba tunda ya saba
kwanciyar parlor, yawanci ma nan yake kwana, tana daga Inda take tsaye ta dinga leka fuskarsa a hankali taga bacci
yake, tayi tiptoeing har xuwa hanyar dakin kaka sannan ta bude kofar very careful don ma ko kadan kofar baya kara,
fridge ta nufa ta ajiye eye drops din ta juyo da sauri ta fita ta kulle kofar, sannan ta sauke ajiyar xuciya, tana isa cikin
parlor ta kara lekan Shuraim da ko motsawa bai yi ba, ta wuce dakinta hankali kwance tana gode ma Allah. Sbda
baccin da Mumy bata yi ba da wuri sai kusan karfe takwas na safe ta tashi duk da ta tashi sllhn asuba, taga har su
Khadijah sun wuce makaranta, bandaki ta fara shiga sannan ta fito ta tafi parlor, dai dai nan Kaka ta fito, Mumy na
murmushi tayi kasa tace “Sannu kaka, fatan kun tashi lfya?” Kaka tace “Wani lafiya an shigo an sace ma yarinya
magani, a kira min Amadu” Kasake Mumy tayi tana kallon kaka, kaka ta nufi bangaren Mami tana cewa “Bari inji
ko wnn matar ce ta shigo ta kwashe magungunan yarinya sbda ta nuna min ban isa da ita ba” Kaka ta shiga buga
kofar Mami, Mami na fitowa kaka tace “Rakiya Ina maganin da kika shigo kika kwashe?” Da mamaki Mami tace
“Magani kuma kaka?” Kaka ta saki salati tace “Toh wllh barawo ya shigo ya sace maganin da kika kawo jiya, ba a
kan friji nace ki ajiye ba??” Mami tace “Ehh nan kuma na ajiye” Kaka tace “Toh ko sama ko kasa, dakin na can na
hargitsa wai ko ma ya shige wani lungun ne amma wllh ban gani ba, Ina Amadu” Mumy dai ta kasa motsi inda take,
Mami ta kalleta na yan sakwanni sannan ta dauke kai, Kaka da kanta ta tafi ta kwankwasa ma Abba kofa yana fitowa
tace “Amadu barawo ya sace maganin Deedayah, wllh da shi muka kwanta muka tashi ba shi” Da mamaki Abba
yake kallonta, tace “Wllh ba xancen wasa ba kana kallona” Mumy dai fa an kasa motsin kirki sai imagining take to
ko dai cikin mafarki ta mayar da maganin bata mayar a xahiri ba, Shuraim ya sakko downstairs jin muryar Kaka ya
cika gidan, ya karaso yana kallonta yace “Me ya faru?” Kaka tace “Shureen maganin Deedayah aka rasa wanda ya
dauke, ni kuwa yau xan ga 6atar nono a kirjin budurwa….” Kallonta kawai Shuraim yake with surprise, can ya kalli
Mumy dake tsaye sai wurga ido take, Kaka tace “Al-qur’an kira xan yi in sa a ja min Yasin, in dai ba a fito min da
maganin yarinyata ba sai na kai kudi an ja min yasin” Abba dai bai ce komai ba, Mami na tsaye just watching
everybody, Kaka ta nemi kujera ta xauna tana hada xufa tace “Ka ji min dai, to wllh ba ruwana sai dai cikin mutum
ya kumbura, me Deedayan ta tsare maku da xa a dauke maganinta, ko uban wani ne ya siya mata maganin banda
Amadu???” Abba yace “Junaid ne ma ya siyo ba ni ba” Kaka ta mike da sauri tace “Au Junaidu ne ma, to dama idan
ba kai din ba ko shi wa gareta da xai siya mata, wllh Amadu ka ja su daki kayi masu magana cikin nutsuwa su fito
min da maganin yarinya kar abu ya baci tsakanina da su, xan fa mance sanin da na masu in sa a ja masu Yasin” Tana
fadin haka ta juya ta nufi dakinta fuska daure, Shuraim ya bi ta da kallon gefen ido, Cike da karfin hali Mumy tace
“Ikon Allah….” Mami ta ta6e baki ta juya ta koma dakinta, Mumy tace “To magani kafafuwa garesa da xa a nema a
rasa?? Anya kaka ta san Inda ta ajiye maganin kuwa?” Abba na kallon Shuraim yace “Xan sa Junaid ya tura maka
sunan eye drops din, sai na maka transfer ka tafi pharmacy ka siyo su” Shuraim yyi kasa da kai, Abba yace “Ko
baxa ka samu xuwa ba…” Kafin yace komai Mumy tace “Baxai samu ba mana, shi da yake fita aiki Barrister, Ina ji
fa ranan Baffa ke fadan baya wani xuwa aikin sai ya ga dama to idan ba matsala kke son ja masa gun Baffan nasa ba
ina xai je samo wani magani ynxu da safe” Tun da ta fara magana Abba ke kallonta keenly, can ya gyada kai ya
wuce bangarensa, Shuraim dai bai iya ya daga kansa ba, Mumy ta hade rai bayan tafiyar Abba murya can kasa tace
“Did you know anything about the missing eye drops Aliyu??” Ya daga kai da sauri yana kallonta yace “Ni kuma
Mumy, ni ban ma san da wani eye drops a gidan nan ba, I know nothing about it, ban ma san kalarsa ba” Mumy ta kauda kai tana naxari to wai ko dai mafarki tayi ta mayar da drops din dakin kaka?? Ganin Shuraim ya fara wucewa
ta kara daure fuska tace “Wait, ko da wasa kar ka fita gidan nan da sunan tafiya siyo ma tsinanniyar yarinyar nan
magani…. I’m instructing you not to do so” Da mamaki ya tsaya yana kallonta, can yace “Toh idan Abba ne yace in
je fa Mumy?” Rai bace Mumy tace “Ni kuma nace baxa ka je ba, ko tsallake maganata xaka yi??” Yace “Amma ai
baxan iya ce masa A’a ba kamar ynda kema baxan iya ce maki A’a ba” tace “Wannan ya rage naka kai da shi, ni dai
nace idan ka fita gidan nan siyo maganin makafi to ba da yawuna kayi hakan ba” Fitowar kaka ya sa ta ja bakinta
tayi shiru da sauri, Kaka dake sanye da hijab hannunta rike da Heedayah tace “Ga shi na fiddo dubu daya ta xan je
siyo maganin idon a kemist, daga can kuma xan tafi gun da xa a ja min yasin na tsakani da Allah….” Mumy tace
“Haba kaka yanxu fa nake cewa xan shiga a sake duba dakin da kyau ko….” Kaka ta katse ta a fusace tace “Tunda
kinga alamar na fara makancewa kamar Deedayah ba, wllh tllh baxan yi kaffara ba wani algungumin ne ya shiga ya
dauke maganin nan, to ni abinda har yanxu ban gane ba a nan shine, bakin ciki ake ma yarinyar kar idon ya warke
ko me?? Anya wasu xa su gama da duniya lafiya kuwa, Junaidu ya cire kudi domin Allah ya siyo mata magani
amma wani mara tsoron Allah ya bi dare ya sace, tunda nake ban ta6a ganin irin haka ba sai gidan Amadu, gidan
Umaru basa haka kwata kwata, in haka ne lauyancin karya Amadu ke yi kenan, lauyancin karya mana tunda ya kasa
kama wanda ya sace ma Deedayah magani, ita ma amaryar da naji ance lauya ce ashe ta karya ce, lauyoyi biyu a
gida a tafka wnn uban sata amma a kasa kama barawon har war haka?? Aa ba ruwana gwara inyi ta kai na, dubu
daya da dari biyar dina ya biya min bukata, dubu daya in bada a kemist su bani maganin guda biyu, dari biyar kuma
in tafi gidan Ta salla ta rakani inda xa a ja min yasin….” Shuraim was trying hard not to laugh sai sunkuyar da kansa
yake yana shafa gashin kansa, Fitowar Abba yasa ya daga kai yana kallon Abban nasa, Abba yace “Ina kuma xa ki
kaka?” Tace “Ina ne kuwa baxan je ba Amadu, Kai baka san wnn yar amana ce Allah ya baka ba xaka barta ta
walakanta a gidanka, wani axalumi ya sace mata magani kayi shiru” Abba yace “Xan je siyo maganin ai ynxu” Kaka
tace “A’a ai tunda nayi niyya sai na siya ga dubu dayana xan je kemist da ita ynxu” Abba ya tsaya kallon kaka kafin
yace “Ae ko wani daya ya kusa dubu ashirin da biyar” Kaka ta gwalo ido tace “Me din?” Abba yace “Bari ynxu
xanje in siyo in kawo maku” Shuraim dake kallonsa a hankali yace “Abba I will go…” Abba yace “Noo, Kar ka
damu” Shuraim yace “Amma kace I should get it” Yace “Ehh na canja shawara, you don’t worry” Daga haka Abba
ya fita, Shuraim ya bi sa da kallo, Mumy ta kyabe baki, Kaka na kallon Heedayah ta dunguri kanta tace “kin dai ji
nawa ake siyar da maganin d’an cikin roban nan, to idan ba tsoron Allah ba uban me muka hada da ke xa mu dinga
kashe maki kudi haka, kin ji fa wahalan da d’a na yake, dubu hamsin xai kashe da safen nan a kan lalurar ki, to wa
xai saka masa kuwa banda Allah? Ba dangin iya balle na Baaba fa” Mumy tace “Abinda ke damuna kenan kaka daga
karshe ma a saka ma mutum da sharri” Kaka ta kalleta tace “Toh Ina ruwan ki, kudin ki ko na Amadun??” Kaka na
fadin haka ta ja hannun Heedayah suka koma daki…. Mumy ta wuce nata dakin don duba drops din ko bata mayar da
gaske ba, Mumy ta tsaya da mugun mamaki a gaban madubinta tana naxarin to waye ya shiga dakin kaka ya dauke
maganin nan, kaf ta duba dakinta bbu, ita dai tana da yakinin ta mayar wajajen karfe biyu da wani abu na dare ba
wai mafarki ba, hankalinta yyi mugun tashi don gashi an kara wargaza wnn plan din ma, ta dau wayarta rai ba dadi
ta wuce bandaki. Har Mami ta gama shirin fita office hankalinta ya kasa kwanciya, she is so disturb, ko kadan bata ji
xuciyarta yyi na’am da komawar Heedayah gun kaka ba, ko ma waye ya dauke eye drops din nan yyi hakan ne da
wata manufa na cutarwa, cuta kuma me girma ba karami ba, bata san ta ina xata fara billowa kan a bar Heedayah
wajenta ba, gaba daya taji bata yi trusting kowa na gidan ba, they all look guilty, both mother and Son, sannan masu
aikin ma haka kawai taji hankalinta bai kwanta ba bata yrda da su ba, sannan Rabi’ah da Khadijah ma halin uwar
garesu bbu abinda suka mance nata, kaka kuma from many indications taga baxata cutar da Heedayah ba balle kuma
a je ga wanda yyi sanadin xuwanta gidan wato Abba, dauke Heedayah daga wajen kaka isn’t going to be easy but she
will try, ynda take jin Heedayah bata jin xata bada space a cuceta a gidan nan sai iya inda karfinta ya kare, da haka ta
fita xuwa parlon Abba sanin bai fita ba, Yana parlon nasa da Shuraim dake xaune kasa, Abba na kallonta yace “Xaki
tafi office….” Tace “Yes, but barrister har yanxu baka ce komai ba a kan the missing eye drops…. This is a very
serious issue to address to with immediate effect, Sannan nasan ka fini sanin koma wanene ya dauke eye drops din
nan ya dauke sa ne da manufa biyu xuwa uku which I won’t mention cos you know….” Abba dake kallonta yace
“Gaskiya ne, I will see to that” tace “And pls ko xaka yi ma kaka magana Heedayah ta komo wajen??” Abba ya d’an
yi shiru, sannan yace “Will see to that too” Mami tace “Alright thank you, sai na dawo” daga haka ta fita, Shuraim
ya bi ta da kallon gefen ido, dakin kaka Mami ta tafi, ta samu kaka ta hada ma Heedayah shayi me kauri ga ledan
bredi guda ta ajiye mata, Kaka tace “Har xa a fita kenan” Mami ta xauna kusa da Heedayah tace “Ehh kaka, Ina
kwana?” Kaka tace “Lafiya lau, kawai sai muka wayi gari da alhinin an sace maganin Deedayah” Mami tace “Allah
dai ya kyauta….” kaka tace “Ameen fahhh, ga dai sabo Amadu ya siyo ya kawo na boye, ita kanta Deedayan ma
baxan bari ta san Inda na boye ba balle wani” Mami tace “Yauwa gwara haka kaka” Kaka tace “Ni fa sai nake ga
kamar Maryam ce ta dauke, ke baki ga duk ta rude ba??” Mami ta d’an yi murmushi bata dai ce komai ba tana gyara
ma Heedayah gashinta, Kaka tace “Toh wllh sai dai ta cuci kanta ba dai Deedayah ba, me yar yarinyar ta tsare mata”
Mami na kallon Heedayah tace “Did you pray today?” Heedayah ta gyada mata kai, Kaka tace “Toh wai sauran kayan nata fa? Ko in tafi in kwasa da kai na ne?” Mami ta kalleta tace “Kayan wa?” Kaka tace “Deedayah mana, ko
kaya kala uku kadai xan dinga sa mata kamar fatararru?” Mami tayi shiru, kaka ta mike ta ci gaba da abinda take,
Mami tace “To sai dai na dawo kaka” daga haka ta fita dakin, Kaka ta ajiye tsumman hannunta tace “Anya wannan
Rakiyan na da saiti ma kuwa, ke dai ba don Amadu ba baxa ki san yarinyar nan ba, ke ba dangin iya tsakaninki da
yarinyar nan balle na Baba to don me xaki dinga nuna fin karfi a kanta??” Kaka ta xauna ta rike ha6a tace “Ha’an,
yau ga fitinanniyar mata ni Fatee, ko dai kanwar uwar Deedayah ce ita bamu da labari…..” Hango ledan da tayi a
gefen kofa ya sa ta mike tace “Ji ledan da gantalallen can ya kawo jiya ko meye a ciki….” Daga haka ta nufi ledan ta
dauka tana leka ciki….Kaka tace “To dama idan ba shi din ba waye xai siyo min Apple manya haka? Ai sai dai Shureen din” Heedayah tace
“Ni bai siyo min ba kaka?” Kaka ta kalleta tace “Ke kuma a wa? Ae sai dai in d’an yankar maki idan nayi niyya”
Karime ce tayi sallama bakin kofar parlon Mumy ta shiga ciki, Mumy tace “kulle kofar, Sajida ta ga tahowar ki?”
Karime ta kulle kofar tace “A’a wanka ta shiga” Mumy tace “Toh mu shiga daki, ba wani aiki bane linki xa kiyi min”
Karime tace “Toh Hajiya” Mumy ta shigar da ita bedroom dinta, ‘yan kaya ne da basu fi biyar kan makeken gadon
dakin, Mumy tace “Ga su nan basu da yawa” Karime ta fara linke kayan, Mumy ta nemi waje ta xauna tana latsa
wayarta, ganin Karime har ta kusa gamawa Mumy tace “Hajiyar ta fara sake maki kuwa?” Karime tace “Aa, yau ma
tace min tunda Heedayah ta koma gun kaka to idan na gama aikin da xan yi a bangarenta in yi wucewata can
dakinmu, ko don d’an kallon da taga Ina yi ne yasa ta fadi haka…” Mumy tace “To banda abun ki ba ga TV a nan ba
Karime, duk sanda kike son kallo ki shigo nan kawai, ae xuciyar daban ne, kowa da irin tasa….” Karime tace “Kuma
haka ne wllh, ke kam naki daban ne….” Mumy tayi shiru jin ringing din waya a parlonta, mikewa tayi da sauri ta fita
parlon, Shuraim ta gani tsaye yana kallon screen din wayarsa dake ring, ya daga ya kai kunne tare da sallama, Mumy
ta juya ta koma dakinta da sauri ya bi ta da ido still answering his phone call, alama tayi ma Karime da cewa kar ta
kuskura ta fito, sannan ta juyo ta kulle kofar ta dawo parlon ta xauna, Shuraim ya gama answer wayar da yake yace
“Mumy xan d’an fita in dawo” Tace “Toh Allah ya kiyaye, yanxu dai kai baxa ka dinga sa manyan kaya ba Aliyu,
wllh suna maka kyau amma baka so, even if it’s just once a week banda Fridays ka dinga sa wa” Bai ce komai ba ya
nufi bedroom dinta, bata san lkcn da ya nufa dakin ba kawai gani tayi ya bude xai shiga, ta mike da sauri tace “Me
xaka yi ciki Aliyu??” Tuni ya shiga suka yi ido hudu da Karime, sai a sannan ya juya ya kalli Mumy yace “Gaban
mirror xan je” Bai jira tace komai ba ya wuce ciki, Karime dake tsaye kamar munafuka ta risina tace “Ina kwana
yallabai” Ko kallonta bai yi ba ya nufi gaban mirror ya tsaya, Mumy dai na tsaye ta kasa bin bayansa, Karime ta fito
dakin kamar munafuka tace “Hajiya na gama” cikin daga Mumy tace “Toh dama wani linki ne tun daxu kamar warce
na sa kwalemar dakin gaba daya?” Karime ta nufi kofa da sauri ta fita, Shuraim ya fito daga dakin, Mumy ta hade rai
tace “Ajiya kayi min a dakin da ka shige min bbu excuse Shuraim??” Yace “Na bar comb dina a nan ai jiya” Yana
fadin hka ya nufi kofa, Tace “Shuraim Ina ga fa gwara in sallami mai aikin nan tawa kawai, bbu abinda take
tsinana min sai magana ma da take yawan sanya ni, dubi fa wnn yarinyar yaushe ta xo gidan amma na gwammace in
sa ta aiki a kan Sajida, cikin dadin rai xata maka komai fess fess, to ni kuma nayi ta kiranta kenan uwar dakinta tayi
wani tunanin daban? Yanxu ma nasan uwar dakin nata bata sani ba ta xo, tun safe na kira Sajida ta xo ta min gyaran nan ban ganta ba shine na kira ita wannan din, matsalar ta daya wnn bata da wani wayewa….” Shuraim dai bai ce
mata komai ba ya bude kofa yace “Sai na dawo” bin sa tayi da kallo har ya rufe kofar, ta xauna a hankali saman
kujera tana naxari…. Mumy ce xaune dakin Hajiya Sadiya, da Hajiya Baturiya, Mumy tace “Sadiya tunda kin sa6a
harka da Mutumin nan ki lallaba sa ya rage kudin wllh sun min yawa, duka duka nawa ne a acc din nawa ma tukun?
Gaskiya ki yi masa magana a min ragi” Hajiya Sadiya tace “Kinsan Allah, wllh da dubu dari uku da hamsin ma yace,
da kyar ya yrda dubu dari biyu da hamsin” Mumy tayi tagumi tace “A kan tsinanniyar yarinyar sai in dawo bbu ko
sisi a account dina” Hajiya Baturiya tace “In dai bukata xata biya ba shkkn ba, ke kin hana mu xuwa gun malam to
ba sai ki bari ayi me yiwuwa ba” Mumy tace “Toh shkkn, amma fa Ina tsoron kuma kar a xargeni ko da wasa a
gidan” Hajiya Sadiya tace “Haba bbu wannan xancen, kaf xa a yashe ki kema har a buge ki, kinga bbu wanda xai
xarge ki” Mumy tace “Toh shkkn sai mun yi waya, yamma yyi bari in wuce gida” Har bakin mota Hajiya Sadiya ta
raka ita da Hajiya Baturiya, ko wanne ya shiga motarsa suka bar gidan. Kaka na sharan dakinta, Heedayah kuma na
saman gado tayi rub da ciki tana sauraron xancen kaka, Kaka tace “Atoh, Shima Sudess din ai ba son yanda yake
ganina xaune gidan duniya yake ba, kawai dai bbu ynda ya iya ne tunda ba ubansa ya halitto ni ba, to abinda Allah
ba bacci yake ba, sai gashi cikin ruwan sanyi ya kawo min ke duk da dai ke makauniya ce baki da wani amfani
kuma bamu hada komai da ke ba, to ai dai yafi babu… Wai d’an agwai da bak’in d’a” Heedayah tace “Waye Sudess
din” Kaka tace “Oho haka na ji suna ce masa, jikana ne fa, ni haifi ubansa Umaru, amma cin haram a wajensa ba a
cewa komai, yanxun nan xaki ajiye hakkin ki a nan kan ki juyo ya handame, to ina dalili….” Bude kofar dakin aka yi
Sudais ya shigo da sallama, Kaka ta saki tsintsiyar hannunta ta mike tace “D’an Halak, yanxun nan nake xancen ka
wllh, nace to Sudais anya lafiya kuwa kwana biyu, ni bai ta6a min haka ba” Ya mata wani kallo yace “Ke dai fadi
gaskiya….” Heedayah tace “Kaka shine yake cin Haram din?” Juyawa kaka tayi tana kallon Heedayah baki bude,
Can ta nufeta ta dunguri kanta tace “A gidan uban wa muka yi haka da ke? Meye kuma Haram, a ina kika ta6a jin
wnn mugun kalmar” Sudais yace “Toh an ci Haram din, tunda ina tsoron Allah ai shkkn” Kaka ta juyo tana kallonsa
tace “To waye baya tsoron Allah” ya bude hannu yace “Oho, sannan ni bana cin naman mutane, bana gulman
mutane” Kaka ta xauna gefen gado ta fara matsar kwalla tana share idonta, ya daga Heedayah ta sauka kasa ya nufi
kofa, kaka tace “Dama kar ka sake maido min ita dakina xan koreta wllh, ga kayanta nan duk a fitar min ba ruwana,
maganin ciwon idon ma gashi nan na nannadesa da Sabuwar atamfata na saka kasan akwati, kowa ma ya xo ya duba
ya kwashe ba ruwana” Sudais ya fita da Heedayah yana dariya kasa kasa, sai bayan da suka fita Heedayah tace “Is
she crying??” Sudais ya fara dariya yace “Yess” Heedayah ta kwace hannunta kamar xata yi kuka tace “Ni ka kai ni
inje ince mata sannu” Dariya kawai Sudais yake yi, Dai dai nan Mumy ta shigo gidan, ya tsaida dariyar da yake ya
gaisheta tayi banxa da shi ta nufi bangarenta, Heedayah da har hawaye ya cika idonta tace “Ka kai ni ince mata
sannu mana pls” Ya ja hannunta xuwa parlon Mami yace “Kina xuwa xata maki duka ba ruwana” Shiru Heedayah
tayi jin abinda yace, Mami ta fito daga daki jin sallaman Sudais, suka gaisa, tace “Sai yau Sudais” yana murmushi
yace “Ina shirye shiryen komawa UK ne, in sha Allah weekend xan wuce” Tace “Ayya, toh Allah ya kai mu lafiya,
kaka ta yrda ka fito da Heedayah kenan” Dariya yyi, ya kai Heedayah gun Mami yace “Ehh ta yadda” Mami ta
jawota jikinta tace “How are you dear?” A hankali Heedayah tace “Fine, Mami a kai ni wajen kaka” Mami tace “Ohh
baki ma son xuwa wajena kenan” Heedayah ta girgixa mata kai, Mami na murmushi tace “Toh bari ku ci abinci,
gashi an gama” Kaka na xaune saman tabarma hannunta rike da wayarta tana tunanin wanda xata kai ma ya kira
mata Baffa taji dalilin da yasa Sudais ya xo ya dauki Heedayah suka fita, aka bude kofar Shuraim ya shigo da
sallama, Kaka ta fara matsar kwalla tace “Yana shigowa kawai ya dauketa bbu wani bayani suka fita, ni ban san Inda
ma ya kai ta ba” Shuraim ya tsaya yana kallonta yace “Wa ya dauketa?” Kaka tace “Shine nake son inji ko Umarun
ne ya aikosa ya ci min mutunci haka, tana fa kwance muna hira gwanin ban sha’awa ya dauketa ya fice bayan ya
gama min rashin kunya har da ce min bani da tsoron Allah ni munafuka ce” Shuraim ya d’an ta6e baki ya nemi waje
ya xauna yace “Ina yini?” Tace “Aa wllh ba lafiya ba, ya fi minti talatin fa da fitar min da Deedayah har ynxu shiru”
Yace “Toh amfanin me take maki idan tana nan din?” Kaka ta mike da sauri tace “A’a ka iya bakin ka, bata fi min ku
ba ma aka ce maka, duk da bata gani kuma bbu dangin iya balle na baba ta fiye min kai wllh” Yace “Toh sai me”
tace “Sai bakin ciki ya kashe ka” Junaid ne ya shigo parlon da sallama, Kaka ta washe baki tace “Sannu da xuwa
Junaidu, ashe kana hanya” yace “Ehh kaka” ta rike ha6a tace “Wannan zungureren babyn roban duk na Deedayah
ne?” Murmushi yyi ya ajiye ledan Babyn hannunsa, Kaka tace “Toh ai dama sai dai kai din, ko Amadu” Tunda
Shuraim ya Kalli ledan Babyn ya dauke kansa, Kaka tace “Wannan Mutumin fa na ce ya siyo mata amma kaga bai
siyo ba tunda ba wai yana da Imani bane” Shuraim ya mike ya fice daga dakin, Junaid ya bi sa da kallo, kaka tace
“Ae kaga irinta, bai siyo ba kuma yana hassada, da ka sani biyu ka siyo ka basa daya tunda bamu san ko bakin ciki
yake mata ba” Junaid yyi murmushi yana kallon kaka…… Bayan Magrib Shuraim ya shigo parlon Mumy don
rabonsa da ita tun da safe da ya fita gidan, bbu kowa parlon nata ya leka bedroom ya dai ji alamar tana bandaki ya
dawo parlon ya xauna ya fiddo wayarsa yana dannawa, wayarta dake jikin caji ne yyi haske alamar kira, ko vibrating
wayar bai yi ba sai haske, yana dai xaune har wayar ya katse, aka kara kira, sai da aka kira na hudu sannan ya mike
ya nufi Inda wayar yake ya duka ya dauka yana kallon me kiran nata, ya shiga text msg din dake saman wayar, cikin few minutes ya karanta content din, sai kuma ya ajiye wayar ya nufi kofa ya fita ya kulle kofar, a hanya ya hadu da
Rabi’ah tace “Ya Shuraim Mumy tana daki?” Yace “Ba daga nan nake ba” daga haka ya wuceta ya wuce bedroom
dinsa. Mumy na fitowa parlonta ta nufi wayarta da sauri ganin yana haske alamar ana kira, ta daga ta koma daki ta
kulle kofar tace “Yi hakuri wllh na shiga wanka ne, ya ake ciki?” Ta d’an yi shiru sannan ta Kalli agogo tace “Xuwa
dai karfe dayan dare shine dai dai” Tayi murmushi tace “Toh shkkn sai mun yi magana….” Daga haka ta katse wayar
ta xauna gefen gado tana wani murmushi…. Mami na xaune parlon Abba da Heedayah sai Rabi’ah da Khadijah, aka
bude kofar parlon Kaka ta shigo ba ko sallama tace “Ni fa har yanxu ba a shigo min da Deedayah ba lkcn baccinta
har ya wuce, idan kuma an canxa wajen kwananta ne sai a sanar min” Bata jira cewarsu ba ta daga Heedayah ta nufi
kofa tana kallonsu Rabi’ah tace “Ku kuma gantalallu ga fura can da Junaidu ya kawo min na rage maku” daga haka
ta fita, Mami gaba daya bata ji dadin xuwan da kaka tayi ta tafi da Heedayah ba, don ynxu goma ma yyi ta xata
kakan tayi bacci ne ta wuce da Heedayahn part dinta don tace xata sha tea, Abba yyi murmushi bai dai ce komai ba
amma ya gane Mami wasn’t happy, Mami ta mike tace “Toh sai da safe” Yace “Allah ya tashe mu lfya” Su Rabi’ah
ma suka yi mata sai da safe ta fita parlon…..