HEEDAYA CHAPTER 20 BY By Khaleesat Haiydar

HEEDAYA CHAPTER 20 BY By Khaleesat Haiydar

                 Www.bankinhausanovels.com.ng 

Mami na xaune office din likita a ranan da aka sallamesu asibiti yana bata conditions na kula da idanuwan Heedayah 

idan sun koma gida, do’s and don’t kawai yake xayyane mata, sosai Mami ke sauraronsa don ko kadan bata son a 

samu wani matsalan, da turanci take tambayarsa ko har kwana Heedayah xata dinga yi da Glasses din nata da aka 

bata, ya amsa mata da A’a, amma…. throughout the day the glasses should be on her eyes ko bandaki xata shiga, nan 

ya kara sanar ma Mami after wata shidda xa su dawo for check up yana nan rubuce takardan da aka bata, godiya 

Mami tayi masa sosai sannan ta fita office din, dole hotel xa su koma don sai dare jirgin Nigeria xai tashi, A cikin 

Tricycle din da xai kai su hotel din Heedayah ta rufe idonta jikin Mami don duk Inda ta kalla mutane ne in group 

kuma hakan na rikitar da ita ba kadan ba ga kuma Haske da yyi mata yawa sosai wanda tun asibiti hakan ke sa mata 

ciwon kai, Bayan sun shiga dakin hotel din Heedayah na kallon Sudais tace “Ya Sudais why are some people black 

and others White in color??” Mami dai tayi dariya bata ce komai ba, Sudais ya dawo kusa da ita ya duka yace “The 

black are the Africans, and the white may be indians or Americans….” Shiru tayi tana kallonsa, can ta kalli Mami 

tace “Is Mami an Indian also?” Junaid dake tsaye jikin window yana danna waya bai ko kallesu ba, ya d’an yi 

murmushi amma bai dago ba still, Mami tayi dariya tana jiran jin me Sudais xai ce mata, Heedayah ta kalli hannunta 

tace “And I am also white, does this mean I am an indian?” Sudais ya d’an juya manyan idonsa yace “Noo Neither 

Mami nor you are Indians….” With confusion Heedayah tace “But how, we are white also” Sudais yace “Ohk let me 

explain to you better, but ur brain is small to understand my explanation…” Heedayah ta xaro ido tace “Ohk wait… is 

yours big?” Dariya Sudais yyi yana kallonta yace “Yess” tace “shi sa kanka kato ne, nawa karami?” Ya gyada mata 

kai yana murmushi, tace “To idan nawa ya kai kmr naka sae ka min explanation din?” Sudais yace “Yess dear” Kofa 

Junaid ya nufa, Mami ta bi da sa kallo tace “Where to?” Yace “I will be back soon Mami, I want to get something” 

Heedayah tace “Yaya should I accompany you?” Juyawa yyi yana kallonta bluntly yace “Noo” Ta wani tabe baki ta 

juya masa idanuwanta tace “Just pulling ur legs, I am going no where” Bude kofar yyi ya fita, Sudais dai yyi 

murmushi kawai, Mami ta kamo hannunta tace “Heedayah yayanki ne fa kike masa rashin kunya” Heedayah tace 

“Mami shi ma fa ya min rashin kunyan, daxu da safe he even pinched me, Sudais yace “Idan kina yi masa haka zae xaneki ne one day, and bbu ruwana” Heedayah tayi shiru sai kuma tace “Shi ma Mami xata zanesa ae” karfe bakwai 

da few minutes jirginsu ya tashi daga india xuwa Nigeria… Ganin ynda Heedayah ke bin kowa na cikin jirgin da 

kallo Mami ta jawota jikinta tace “Kiyi baccin ki” tace “Mami su ma duk gidanmu xa su je wajen Abba?” Mami bata 

san lkcn da tayi dariya ba tace “Nooo dear, but we are all going to Nigeria that’s our country” Heedayah tace “Toh 

Ina xa su je su” Mami tace “Nigeria is a very large County with 36 states ba kin sani ba??” Heedayah ta gyada mata 

kai, Mami tace “Toh everyone u are seeing inside this plane is going to various state, some Kaduna, other kano, and 

so on” Heedayah tace “Jirgin ne xai kai mu gida wajen Abba?” Mami tace “Noo mota xa a kawo airport sai mu shiga 

a kai mu gida” A Hankali Heedayah tace “Ohk” daga haka tayi lamo jikin Mami nan da nan bacci ya dauketa, Sudais 

da Junaid na xaune daga bayansu, sai da suka sauka Abuja Nigeria da asuba Mami ta tada Heedayah suka sauka

jirgin tana rike da hannunta, sai makalewa take jikin Mami don bata son kowa ma ya ta6a ta cikin masu saukowa 

kallon dodo take masu, ta dinga bin ko ina da kallo bayan sun sauka jirgin tace “Mami babu Light a Nigeria din 

dama?” junaid ya kalleta kafin yace komai Mami tace “Noo, asuba ne har yanxu ai, anjima xaki ga haske ko ina 

dear” ta kalli Junaid xata yi magana sai kuma tace “Ohh not you, Yaya Sudais a nan xa mu bar jirgin mu tafi?” 

Junaid yace “Aa xa a daura maki a kai ne ki kai gida” Ta kalli Mami tace “Mami kin gansa ko? Nice xan iya daukan 

jirgin a kai na?” Mami tace “Aa sai dai shi a daura masa a nasa kan” Heedayah tace “Toh Mami ai shi ma baxai iya 

ba, naga kato ne ai jirgin” Sudais ne ya samar masu Taxi cab yana kallon Mami yace “Train station din xa mu 

wuce?” Mami tace “No this 4 am, mu tafi gidan sister na, xuwa biyar da rabi sai mu wuce station din” yace “Ohk” 

cikin mintuna kadan suka isa gidan Hajiya Asiya, sosai matar ita ma tayi murnar ganin anyi sa’ar aikin duk da suna 

chatting da Mami tun a India Mami ta sanar mata Heedayah ta warke, wanka kawai suka yi a gidan suka yi breakfast 

shi ma da kyar don Hajiya Asiya ta damu su yi, duk suka yi sharp sharp sbda su samu train going to Kaduna da safen, 

Driver din Hajiya Asiya ya kai su train station din…. Karfe tara da wani abu suka isa train station na Kaduna, duk 

suka sauka train din…. Mami na kallon Sudais yace “Sun taho daga gidan ne?” Sudais yace “Ehh ya turo min text ya 

iso” a wajen station din suka ga motar Shuraim a Parke, Bude motar yayi ya sakko Heedayah ta dinga kallonsa irin 

na sanka din nan har ya iso Inda suke, ya gaida Mami, Mami ta amsa, hannu ya mika ma Sudais sannan junaid da ya 

dinga danna waya ya ki dagowa har sai da Sudais ya d’an bugesa, sai a snn ya dago kansa ya amshi hannun Junaid, 

Heedayah dai sai binsu take da ido ganin abinda suke yi da hannu, ganin Shuraim xai juya ta mika nata hannun tace 

“Ni fa?” Very serious tayi maganan, hakan ya ba Mami dariya sosai Sudais na tayata, Shi dai Junaid murmushi 

kawai yyi still pressing his phone, Ko kallonta Shuraim bai yi ba ya nufi motarsa, a hankali Heedayah tace “Mami 

me yasa ni bai min ba?” Mami tace “Maxa ne kawai suke yin haka” Tace “Mami na ta6a ganinsa ranan nan” Mami 

tace “That’s Shuraim” Da sauri Heedayah ta kalleta tace “Shureen?” Mami tace “Yes” back seat Mami ta shiga da 

Heedayah dake ta kallon Shuraim, Sudais da Junaid suka gama saka kayan a mota, Junaid ya shiga back seat, Sudais 

ya shiga gaba, Shuraim ya tada motar suka dau hanyar gida… Bbu me magana cikin motar sai Heedayah da ta kafe 

idonta jikin windscreen komai ta gani sai ta tambayi Mami, Mami kuma ta bata amsa, lkci lkci Shuraim ke kallonta 

ta madubin gaba, hada idon da suka yi da Junaid ya sa bai sake kallon Madubin ba, bayan tafiyar kusan minti ashirin 

suka iso, gida Mai gadi ya bude gate Shuraim ya shiga da motar, Mami ta kalli Heedayah da ta kura ma gate ido tace 

“We are home” Heedayah ta juyo da sauri tace “Xan ga Abba yanxu?” Mami tace “Yess of course” Bude motar 

Sudais yyi ya fita, Junaid ma ya fita sannan ya xaga ya bude ma Mami bangarensu, Mami tace “Sauketa” Da sauri 

Heedayah dakatar da shi ta hanyar daga masa hannu tace “No xan sauka da kai na” Tana fadin haka ta lallaba a 

hankali ta sauka tana kallon interlock din gidan, Mami tayi murmushi ta fito Junaid ya rufe motar, Abba ne ya fito 

balcony ya sakko yana kallonsu gaba daya, Mami ta xagayo da Heedayah tana murmushi ta nuna mata Abba tace 

“There…” Heedayah ta kalli Mami tace “Abba?” Mami tace “Yes, go to him” tafiya ta fara ya a hankali, Abba dake 

murmushi ya bude mata hannunsa, hakan ya sa ta tafi da gudu, ya rungumeta tace “Abba I can see everything now, I 

can see you also” tana magana tana ta6a fuskarsa Abba yace “Alhmdllh daughter, now say Alhmdllh Ya Allah” 

Heedayah tace “Alhmdllh Ya Allah” Junaid da Sudais dai na tsaye suna kallonsu, Abba ya daga kai ya kalli Mami 

dake tsaye tana kallonsu ita ma, karasawa wajensu yyi yana rike da hannun Heedayah, Yyi patting shoulder dinsu 

yana murmushi yace “Allah yayi maku albarka my boys, I am so proud of you two…” Duk suka amsa masa da 

Ameen smiling back at him, Kallon Mami yyi ya nufeta, still smiling yyi mata side hug, karaf a kan idon Mumy da 

ta makale jikin window a parlon sama tana lekosu tun shigowar motan gidan, ji tayi ta kasa tsayuwa ga wani abu da 

taji ya soketa a xuciya, bata san lkcn da ta fashe da kuka ba ta sake labulen da sauri, Abba na kallon Mami softly 

yace “Welcome back Dear Rahinah, Allah yyi albarka, I will for ever be grateful to you…. Knowing you is one of the 

sweetest thing I can admit to in life, I am so proud of you wife” Mami dai sai murmushi take, tuni Shuraim yyi 

wucewarsa ciki, Abba na rike da Heedayah tare da Mami suka wuce cikin gidan, ko Abba bai fadi ba you can see 

how happy he is, ita kanta Heedayah lkci lkci sai ta kalli Abba ta sakar masa murmushi, sai bayan da suka shiga 

parlor ta dinga bin parlon da kallo kamar munafuka, Rabi’ah da Khadijah na tsaye duk suna jiran shigowar 

Heedayah, Abba ya nuna mata su yace “Ur sisters” a hankali tace “Hi” ganin yanda Abba ke kallonsu duk suka ce 

“Hello” Heedayah ta kalli Abba tace “Abba kaka fa?” Abba yace “Anjima xata dawo in sha Allah” Mami na kallon Abba tace “Let me go and freshen up barrister” yace “You need to dear, Allah ya huce gajiya, sai na shigo” Ta amsa 

da Ameen ta nufi part dinta, Heedayah ta kwace hannunta a na Abba tace “Mami are you leaving me” Mami ta juyo 

tace “No dear, stay with Abba a little” Abba yace “Mu je ki gaida Mumy” Heedayah bata ce komai ba yana rike da 

hannunta suka wuce bangaren Mumy. Mumy na bedroom dinta tana waya da Sadiya tana sanar mata ai sun dawo, 

ynda take kukan a wayan kai kace mutuwarta aka nuna mata, Sadiya tace “Toh wai ke meye na kukan, dama ba jiran 

dawowarsu ake ba ne, ae ke abun farin ciki ne ma a gare ki da suka dawo yanxu” Cikin kuka tace “Baxa ki gane ba 

Sadiya dole inyi kuka, dole inyi kuka, rungumeta fa naga Barrister yyi tana wani murmushin kissa, ko kunya bbu a 

gaban yaran gaba daya ya rungumeta wllh” Sadiya tace “Ita Rahinar?” Mumy tace “Wllh, runguma fa sosai, yaushe 

rabon ya kama hannuna ni balle ya rungume ni a kan idon wani, a fa tsakar gida ya rungumeta” Sadiya tace “Bbu 

komai ki kwantar da hankalin ki, da ba mu da mafita ne shine xa ki yi kuka, Amma ga mafita iri iri dai, abu tun 

yaushe muke baxa idon dawowarsu kuma gashi Allah ya dawo da su lfya” Jin an bude kofa Mumy tayi saurin cewa 

“Xan kira ki anjima, an shigo parlona” Daga haka ta katse wayar tace “Waye?” Jin shiru ta mike tana kara goge 

idonta sosai ta fita, Abba ne tsaye yana rike da Heedayah, Mumy ta sake fuska tace “A’a, mutan India har an iso 

kenan, toh kun sha kabo, Alhamdulillah, Sannun ku da dawowa” Heedayah dai sai kallonta take a tsorace jin 

muryarta, Abba ya sake hannunta yace “Go and greet her” a hankali Heedayah ta nufi Mumy dake kirkiran 

murmushin karfin hali Mumy ta jawota jikinta sosai ta rungumeta tace “Alhamdulillah ido ya bude, Alhamdulillah 

mun gode Allah” Murya can kasa Heedayah tace “Good morning” Mumy ta dago kanta tace “Good morning ya kike, 

Ina Mamin ta ki?” Heedayah ta nuna mata hanyar waje, Mumy tace “To maa sha Allah, Allah ya huce gajiya” Abba 

yace “Sai ki samu ki tafi kiyi ma Rahinar sannu da xuwa” Mumy tace “A’a ba abinda xai hana haka ai” Mumy ta 

xaunar da Heedayah kan kujera tace “Kun yi breakfast kuwa?” Heedayah ta girgixa mata kai, Mumy tace “To bari a 

hado maki shayi” ganin haka Abba ya fita ya bar Heedayah a parlon, Mumy ta bi sa da kallon gefen ido, can ta kalli 

Heedayah tace “Kar fa ki fita, Ina xuwa in kawo maki shayi, xa ki ci har da bredi Koh?” Heedayah ta gyada mata kai, 

Mumy ta nufi kofa ta bude kafin ta fita sai da ta sake kallonta tace “Kar fa ki fita, Ina xuwa yanxun nan in kawo 

maki kin ji” Heedayah ta kara gyada mata kai, Mumy ta fita da sauri, Mumy na fita da few minutes aka bude kofar 

sai ga Shuraim ya shigo, Kallonta ya dinga yi daga Inda take xaune with surprise, can ya kalli kofar dakin Mumy ya 

karasa ya leka ciki bai ganta ba, dawowa yyi ya bude kofar parlon yana kallon Heedayah dake ta bin sa da kallo ya 

nuna mata kofar alamar ta fita, Tace “Mami tace min door ne… It’s a door” ya wani daure fuska, da sauri ta dauke 

kanta, Ya dake yace “Xo ki fita nace….” Mikewa tayi tsaye da sauri tana kallonsa don ranan ya fara mata magana, 

kamar munafuka tace “Tea xa a bani da bread” Ya kara daure fuska yace “Fita na ce” da sauri ta karasa gun kofar ta 

bi ta gefensa ta fita tana waigosa, ganin inda xata bi ya bi bayanta da sauri, ya gwada mata hanya da finger dinsa, 

part din Mami da ya nuna mata ta nufa, da tayi tafiya kadan sai ta juya taga yana tsaye yana kallonta, sai da ta d’an 

yi nisa sannan ta juyo ta tsaya tana kallonsa ita ma, ya xare mata ido yace “Baxa ki wuce ba” 6ata fuska tayi ta juya 

ta nufi kofar shiga parlon Mami hawaye cike idonta tana isa kofar ta kara juyowa ta tsaya tana kallonsa, sun fi minti 

daya a haka yana kallonta tana kallonsa…. Daukar remote da ke kan kujera yyi, yyi kamar xai jefa mata ta fasa ihu ta 

durkusa a wajen, da sauri ya juya ya wuce dakinsa, Mami ta bude kofarta jin muryar Heedayah tana kallonta tace 

“What happened?” Kamar xata yi kuka tace “Wannan da kika ce min Shureen ne, I heard his voice, xai min doka 

wai” Mami na bin parlon da kallo tace “Ina yake?” Heedayah tace “Ya gudu” kama hannunta Mami tayi suka shiga 

ciki, Mumy ta fito kitchen rike da cup din shayi da bredi da nama a plate ta wuce parlonta, turus ta tsaya ganin bbu 

kowa parlon, can ta nufi daki nan ma bbu kowa, ta dake tace “Heedayah?” Nan ma shiru, Ficewa tayi dakin ta wuce 

parlon Abba, ta samesa dakinsa, rai bace tace “Kai da ka bar yarinyar nan a parlona baka san abinda kke yi bne 

barrister, Wai daga in je in hado mata kayan kari shine har an shiga an dauketa…” Abba ya dakatar da ita yace “Aa, 

ta dai fita, wa xai shiga ya dauketa” Mumy tace “Wllh wllh shiga aka yi aka dauketa don na jadadda mata kada ta 

fita tace min toh, wllh dauketa aka yi” Yace “To wa xai dauketa??” Tace “Oho na sani” yace “To sae ki kai mata can 

parlon” tace “Baxan je ba wllh, ikon dai da ake nunawa bani da shi a kanta a ci gaba” daga hka ta fice daga dakin rai 

bace…. Jin shiru shiru Mami bata ga junaid da Sudais ba ya sa ta kira Junaid, nan ya sanar mata wucewa suka yi, fita 

tayi parlonta ta tafi dakin masu aiki ta bude tana kiran Sajida, wata mata ce ta mike tace “Aa ni ce, Ina kwana” Mami 

tace “Lafiya lau, Ina Sajidar?” Matar tace “Ni ce sabuwar mai aikin ynxu” Mami tace “Tohhh, to Sannun ki” daga 

haka ta juya ta wuce xuwa kitchen ta hada ma Heedayah da ita kanta shayi.Da yamma Mami na xaune main parlor da Hajiya Amina da Hajiya Hauwa, sai colleagues dinta su shidda duk sun 

xo yi mata sannu da xuwa da gaida Heedayah, drinks da ruwa ne da snacks iri iri a gabansu sannan ga lafiyayyen 

jollof da isasshen kaza sai coslow a gefe, Mumy dai na xaune parlon ita ma sai kirkiran murmushi take, lkci lkci take 

jefa nata hirar a hiran da suke, Heedayah na xaune kasa kusa da Mami duk tana kallonsu hannunta rike da roban 

Fanta, daya hannunta kuma cup cake, bude kofar parlon aka yi Kaka ta shigo sakale da daya dayan handbag dinta da 

xa a iya saka karamin jariri a ciki, ta sha yafin mayafinta, ko takalmin kafarta bata cire ba ta shigo parlon, biye da ita 

a baya Hajiya Zuwaira ce matar Baffan Junaid da kawarta sai kanwarta Maimuna, Mami na ganin kaka tayi 

murmushi ta mike tace “Sannun ku da isowa kaka” A dakile kaka tace “Ehe” Heedayah sai kallon warce taji an 

kira da kaka take kamar idanuwanta xa su yi magana, sauran matan parlon duk suka shiga yi ma Kaka sannu da 

xuwa ciki har da Mumy, duk da “Ehe” kaka ta amsa su tayi wucewarta dakinta bayan ta saci kallon Heedayah da ta 

bi ta da kallo, Mami suka gaisa da su Hajiya Zuwaira da fara’a tana masu sannu da xuwa, kasancewar parlon is 

occupied tace “Bari mu je can parlon kawai” Sai da ta sanar ma bakinta gaba daya cewar tana xuwa sannan ta kai 

Hajiya Zuwaira da kawarta da kanwarta parlonta, mikewa Heedayah tayi da sauri ta bi bayanta, Mumy ta bi ta da 

wani kallo ta gefen ido, Mami ta ciro ma bak’in nata ruwa da lemo a fridge ta ajiye masu tace “Tunda ku na gida ne 

bari in sallami bakin parlor, abokan aikina ne da matan yayan Barrister, Ina xuwa yanxun Hajiya” Hajiya Zulaiha 

tace “Ba damuwa Rahinah, mu kam na gida ne” Mami ta fita Heedayah ta bi bayanta da sauri duk da kiranta da 

Hajiya Zuwaira ke yi, Mami ta kalleta tace “C’mon je ana kiran ki my frnd” a hankali ta juya ta koma cikin parlon ta 

nufi gun Hajiya Zuwaira, Mami tayi wucewarta… Mami na dawowa main parlor Hajiya Hauwa tace “Kinga ki shiga 

ki gaida Kaka tana iya cewa ai kin ganta kin shareta, kinsan halin abar tamu….” Dariya Mami tayi tace “Ae kuwa” 

Mumy tace “Ae haka ma kawai xata ce” Mami tace “Bari in je in dawo” daga haka ta nufi hanyar dakin kaka, dakin 

masu aiki ta fara shiga, tana kallon sabuwar mai aikin me suna Talatu tace “Don Allah ki debi abinci da su samosa 

da cake ki kai can parlona akwai baki guda uku” Talatu ta mike da sauri tace “Toh Hajiya” Mami ta juya ta fita ta 

wuce dakin kaka, kaka na share windanta da tsintsiya bayan ta cire duk labulayen dakin da ma xanin gado Mami ta 

shigo da sallama, Da fara’a tace “Sannu da isowa kaka, fatan mun same ku lafiya” Kaka ta ajiye tsintsiyar hannunta 

tace “Ita Deedayar bata da labarin ni na haifi Amadu da ya biya kudin gyaran idon nata ne da har yanxu bata shigo ta 

gaisheni ba? Kinga Amadu fa bai ta6a sanin yarinyar nan ba wllh, bbu dangin iya balle na baba, to kuma ya ina 

mahaifiyarsa baxata xo ta gaisheni ba sbda idonta ya budu, to ni da nasan haka ne xai faru da nace ma Amadu ba da 

yawuna ba idan aka gyara mata idon, ace tun dawowar ku ba ki xaunar da ita kin sanar mata wacece ni da abinda ya 

kamata tayi idan ta gan ni ba, kin ga rashin gaskiyar jama’ah ko? To ni dai ba ruwana, ai ba wani ya haifar min 

Amadun ba, kwanana uku ina nakudar sa wllh” Mami da ke ta kallon kaka tace “Toh kiyi hakuri, kuma Heedayah 

har yanxu ba wai ta gama sakin jikinta da mutane bane, Kar ki manta kaka tun da aka haifeta makauniya ce ita, 

Kinga da girmanta ta fara ganin duk wani halitta, to banda ynxu da ta fara sakewa ai da ko mutum ta gani ta dingi 

ihu kenan tana tsoro” Kaka ta daga hannu tace “Toh ni ina ruwana, ni dai ba ni ce na haifi wanda ya tsintota yyi silar 

gyaran idonta ba, Taimakonta Allah Taimakonta Amadu a duniyar nan, don haka ai ban cancanci raini wajenta ba, 

baki ga kallon rainin hankalin da naga tana min ba, ni a gaskiya da na sani da an barta a makancen ma kawai tayi ta 

ma mutane ladabi a hakan” Mami bata kuma ce mata komai ba ta juya ta fita don ranta ya gama baci, Sai bayan da ta 

fita kaka tace “Wa ya sani ma ko ‘yar ta ce ta makala ma Amadu don kawai ya aureta, mutane dai bbu gaskiya” 

Mami na fitowa ta wuce parlonta, Tayi ma su Hajiya Zuwaira sannu sannan tace “Heedayah taso mu je” Mikewa 

Heedayah tayi ta bi bayanta suka fita, Mami ta wuce da ita dakin kaka suna isa kofar ta juyo tana kallonta tace “Idan 

mun shiga ki xauna a kasa ki gaisheta, ita ce kaka” Heedayah ta gyada mata kai sannan Mami ta bude kofar suka 

shiga dakin, a bakin kofa Heedayah ta xauna tace “Ina wuni” Kaka dake share bangon dakinta ta juyo ta kalleta ta ajiye tsintsiyar tace “Toh ki gode ma Allah ki gode ma d’a na Amadu, kuma ni nan nice kaka ni na haifi Amadun da 

yyi silar gyaran idonki, ko iyayenki na da rai yau basu da iko a kanki kamar yanda Amadu ke da iko a kanki amma 

ya xa ayi in shigo kina xaune rike da goran panta da kenk ki kasa ce min komai kin ji kowa na min sannu da xuwa 

kaka” Heedayah dai sai kallon kaka take, duk Inda ta bi da hannu sai ta kalla kai kace TV ta samu, Kaka ta kalli 

Mami dake jira ta fitar da Heedayah daga dakin tace “Kin gani ko Rakiya, hararata fa take” Mami tace “Wani harara 

kuma kaka, ance maki yarinyar har yanxu bata gama sabawa da komai ba, yaushe ma ta fara ganin ki idan ba yanxu 

ba, sai fa a hankali xata saki jiki da kowa ta dawo kamar ko wani mutum, ynxu haka da xa ki kawo mata mage ko 

tsuntsu bata san su ba bata ta6a ganinsu ba, sae dai sunansa, to kinga kuwa dole ayi ma mutum uxuri, ranan da 

idonta ya bude tsoron kowa ta dinga yi, kuna hada ido xata fasa ihu, sbda duk rayuwarta a duhu yake banda ynxu da 

Allah ya yaye mata” Kaka tace “Haka abun yake?” Mami ta daga Heedayah dake ta xaune tana kallon kaka tace “Sai 

hakuri kaka, ni xan tafi in ji da mutane” Daga haka ta fita da Heedayah dake waigo kaka… Fitowa kaka tayi tana 

kallon mutan parlon ganin Mumy tace “Xo Maryam” Mumy ta mike ganin kaka ta nufi nata bangaren ta bi bayanta 

har suka shige parlon Mumy, Kaka ta xauna saman kujera ta fashe da kuka tace “Rakiya ce ta shigo ta min wankin 

babban bargo bbu abinda ta mance bata gaya min ba, a takaice dai a baibai kirana tayi da fitinanniya, ni dai ina tsaye 

bance mata uffan ba ta ja hannun makauniyar da Amadu ya kashe kudi ya warkar suka fita” tana kai wa nan ta fashe 

da matsanancin kuka, Mumy tace “Ikon Allah, to ke me kika yi xata maki haka daga dawowarki” kaka tace “Wllh 

Maryam daga nace mata Deedayah lafiya bata shigo ta gaisheni ba naga kamar ma hararata take da na shigo ko bata 

gane ni bane ta min irin wnn kallon, Kar ki d’a d’a kar ki raga, Rakiya ta hau ni da bala’i wai ni bana yi ma mutane 

uxuri, ai Deedayah a duhu take ynxu Allah ya fito da ita Amadu ya fito da ita haske, Kuma ai dole ta ji tsorona tunda 

ita ma ta ji tsoronta da suke asibiti, to idan Rakiya na da hankali da tunani sai ta hada kanta da ni? Ni fa na haifi 

Wanda yayi silar warkewar Deedayan” Mumy ta hade rai tace “Gaskiya wnn raini ta maki, bata kyauta ba, gani take 

ta fi kowa Iko da yarinyar a gidan nan daxu fa daga Barrister ya kawota parlona na fita kitchen hada mata shayi 

matar nan ta shigo ta dauke ta” kaka tace “To kuwa ta ci kanta, Kuma sai na sa an karbe Deedayan hannunta in ga ta 

tsiya, idan ma Amadu baxai bani ita ba ke ya baki ki rike, abinda ma xai faru kenan wllh wllh, a ina take da iko da 

yarinya bayan ita ma makalewa tayi aka aurota dalilin yarinyar, da ba don yarinyar ba mu muka san wata Rakiya” 

Mumy tace “Ae shine, ni wllh a bani ita dama lkcn can shaidan ne ya shiga xuciyata ya hanani amsar ta amma wllh 

tllh ynxu xuciyata daya xan amsheta in riketa kmr yanda xan rike d’an cikina, abinda yarinyar har ta fara sabawa da 

ni da suka dawo har ta kusa awa biyu a parlona” Kaka tace “Toh kin ga dai, bari Amadun ya dawo shi ma gantalalle, 

xan ji ko maganan Rakiya xai dauka ko tawa” Mumy tace “Atoh dai” mikewa kaka tayi ta fita parlon, Mumy tayi 

wani murmushi ta xauna tana kara naxarin maganganun Kaka. Kafin Magrib duk bakin gidan suka watse har ma da 

makota da suka shigo duk da basu wani san Mami ba sai Mumy, suka yi mata sannu da xuwa suna ma Heedayah 

barka suka fita, Mami da kanta ta taimaka ma Talatu gyaran gidan don kai kace wani karamin walima aka yi a gidan, 

Mumy kuwa ta shige bangarenta da yaranta ta kulle kofa don ma kar su dauke ko da cup, Duk inda Mami tayi 

Heedayah na makale da ita, Mami har ta gaji da ce mata taje ta xauna ta kyaleta, Mami na kitchen suna gyaran 

kitchen din aka yi Magrib, sai da Mami ta tabbatar ko ina ya dawo fess ta fito parlor tare da Heedayah ta bar talatu ta 

karasa wanke wanken, Kaka ce ta fito dakinta, Mami tace “Sannu kaka, abincin ya ishe ku ai koh?” Can ciki kaka ta 

amsa tace “Ya Isa…” Daga haka ta nufi bangaren Mumy tana rike da wayarta tana cewa “Ina Maryam ta kira min 

Junaidu shiru ni ban gansa ba, ko a indiyar suka baro sa” Mami dai bata ce mata komai ba har ta shiga bangaren 

Mumy, Mami ta wuce nata bangaren da Heedayah. Bayan isha Abba na parlonsa tare da Shuraim sai su Rabi’ah da 

Khadijah, Mami ta shigo ciki da sallama holding Heedayah’s hand, Gun Abba Heedayah ta nufa ta xauna tace “Abba 

sannu da dawowa” Yyi murmushi yace “Yauwa daughter, hope kinyi bacci da yawa daxu” ta gyada masa kai, Abba 

ya maida dubansa kan su Khadijah on a serious note yace “As I was saying, today should be the last day da yayanku 

xai maku fada ko ya doke ku ku je ku gaya ma Mamarku” Rabi’ah tace “Abba ba mu muka gaya mata ba fa, she just 

came in” Abba yace “Whatever…. Na gaya maku ni dai….” Abba ya kalli Shuraim yace “And you Shuraim duk ranan 

da suka kara fashin makaranta you do what ever you wish to them, don’t think twice before punishing them” ya 

girgixa kai kamar baxai ce komai ba sai kuma yace “Abba it will be good idan Mumy tayi hakan, ni babu ruwana da 

lamarinsu a gidan nan, beside she said I should take my hands off their issues” Abba yace “And I am instructing you 

to keep on disciplining them, ko ban isa?” Bai kuma cewa komai ba, Mami na kallonsu tace “Ku kuma sai kace 

wasu yara xuwa islamiyyar ne ku ke fashi, amma ai ban ga kuna fashin boko ba” Basu ce mata komai ba, tace 

“That’s bad, you two should stop that” Abba yace “Nan da one week Heedayah will join them also, kafin sati dayan

an nuna mata abubuwan da ya kamata ta sani facially since ta san karatu gani ne kawai bata ta6a yi ba” Mami tace 

“Allah ya kai mu” Bude kofar parlon aka yi, kaka ta shigo, Ko gaisuwan da ake mata bata amsa ba tace “Amadu 

baka san na dawo bane baka shigo ba? Tun fa yamma nake gidan nan” Abba yace “Aa dama Ina kokarin shigowa ne, 

Ina son in gama da su” tace “To ai dai nice dolen ka ba su ba koh?” Wani kallo Shuraim ya watsa mata, Abba dai bai 

ce komai ba, ta nemi waje ta xauna, Mami tace “Sannu kaka” kaka tace “Ehe” Abba yace “Ina yini Baaba” tace 

“Lafiya lau, Ina son magana da kai ne Amadu” Abba ya kalli su Rabi’ah yace “To na gama da ku” mikewa Mami tayi Heedayah na ganin haka ita ma ta tashi daga kusa da Abba, Kaka tace “Aa Ina kuma xa ki Rakiya koma ki xauna” 

Rabi’ah da Khadijah xa su fita kaka tace “Kai ku kira min Maryam idan kun fita” Abba dai sai kallon kaka yake, can 

yace “Lafiya dai ko kaka?” Tace “Eh lafiya lau” Bai kuma cewa komai ba sai ga Mumy ta shigo da sallama, ta nemi 

waje ta xauna tayi ma kaka sannu sannan tace “Ga ni kaka” Kaka tace “Toh Amadu shawara na xo baka idan kana 

son xaman lafiya a gidan ka….” Abba yace “Shawarar me fa?” Kaka tace “To wai me yasa baxa ayi ma Maryam kara 

ba a bar mata Deedayah wajenta tunda dai ta nutsu tayi hankali, ita Rakiya ba xama take ba aiki safe, rana, yamma, 

Ina jin har dare ma wani lkcn, to ni kuma a ynda nake ganin wnn Deedayar fitsararriya ce naga alama, don daxu bata 

san ina lura da ita ba ta harareni, kaga kuwa idan nace ta xauna wajena idan Rakiya ta fita kasuwancinta ai xagi na 

yarinyar xata dinga yi wataran in shiga uku, jikokina basu ta6a xagina ba ita ta xageni….” Da mamaki Abba ke 

kallonta, Mami dai bata ce komai ba kuma bata kalli direction dinsu ba, kaka ta ci gaba tace “Tunda dai ita Maryam 

xaman kashe xani take a gida bbu aikin fari balle na baki ba gwara a bar yarinyar gun ta ba sbda tarbiya, ni dai tun 

ba aje ko ina ba naga ta rainani balle ace ta xauna gu na” Mumy tace “To ai bbu komai ko ma gun wa ta xauna kaka, 

in ma gu na in ma gun Rahinar…” Kaka tace “Oh oh ai Rakiya aiki take fita kullum, ke dai me xaman banxa ya 

kamata a baki ki sa ido kan lamarin ta don naga yarinyar na bukatar sa ido, sakakkiya ce, ta xata a duhu take har 

ynxu” Shuraim dake sauraron kaka yace “Xai fi idan aka kai ta boarding a can xa a koya mata ladabi, xa kuma ta 

gane cewar ba a duhu take ba yanxu” Da sauri Mumy ta juya ta kallesa, Abba yace “Ehh in sha Allah boarding xata 

fara kamar yanda Shuraim yace” Kaka tace “Meye kuma boding?” Shuraim na kallonta yace “Makarantar kwana” 

Kaka tace “Amma kai axxalumi ne Shureen, me Deedayar ta tsare maka a gidan da kake son a kai ta makarantar 

kwana, Kai da aka ta6a kai ka kana yaro ka xauna?? Ba gudowa ka yi ba, to meye kuma xaka ce a kai marainiya??” 

Mumy tace “Toh makarantar kwanan da ake kwashe yara ma, wnn ae gurguwar shawara ce” Shuraim yace “Ae ba na 

gwamnati xa a kai ta ba” Kaka tace “Ni dai ba ruwana da muguntar ka na fulani, me xa mu ce ma Allah idan aka 

kwamushe ‘yar mutane” Abba yace “Makarantar da Farida take ynxu xa a sa ta in sha Allah, boarding ce me kyau

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *