HEEDAYA CHAPTER 21 BY By Khaleesat Haiydar

HEEDAYA CHAPTER 21 BY By Khaleesat Haiydar

                 Www.bankinhausanovels.com.ng 

Kaka tace “Aa to ni tsorona kada a sace ta ne Amadu mu shiga uku” Abba yace “Aa lafiya lau, bbu wata matsala in 

sha Allah” Mikewa Shuraim yyi ya nufi kofa kansa a kasa, Mumy ta bi sa da wani irin kallo xuciyarta na tafarfasa, 

Mami na lura da kallon da uwartasa ke masa har ya fita parlon, Abba ya dau wayarsa dake ring ya mike yace “Bari 

in amsa kira in dawo Baaba” mikewa kaka tayi tace “Aa to ni kuma me xan tsaya in maka, dama shawara ce kawai 

na kawo, amma tunda bafillatanin d’an ka yace a kai ta makarantar kwana kuma ka amince ai shi kenan, amma a 

gaskiya idan wani abu ya sami yarinyar nan baxan yafe maka ba baxan yafe ma Shuraim ba, don da kai ka haifeta 

baxa ka yi mata sha’awar xuwa makaranta kwana ba, me yasa baka kai ‘ya yan cikin ka ba sai ita?? Shi dai rikon 

amana dama da wahala take sai wanda Allah ya ba…” bata jira cewarsa ba ta fice daga parlon, Mikewa Mami tayi ta 

nufi kofa Abba ya bi ta da ido har ta fita, Mumy ma ta mike ta fice daga parlon bacin ranta ya kasa boyuwa gaba 

daya, dakin Shuraim ta wuce direct ta samesa ya shimfida darduma ya dauko qur’ani ya xauna, cikin daga murya 

tace “Aliyu a kan uban me yasa kace a kai yarinyar makarantar boarding?” Shuraim dake kallonta yace “Aa, naga 

kamar ba wani son xamanta gidan ake ba….” Tayi masa wani tsawa tace “Uban waye yace maka baya son xamanta 

gidan?? Kai da wa ku ka yi haka?” Yace “No naji kaka ta ce ta fara rainata, so it’s better we shouldn’t let that go 

far…” A fusace Mumy tace “Toh kai Ina ruwanka da xancen da ka tsoma baki? Dangi uwa ko ta uba? Meye hadin ka 

da ita da har xaka bada shawara kan lamarin ta iyye? Meye damuwar ka da ita nace?” Yana bude qur’anin gabansa a 

hankali yace “Nima din ban fiye son ganinta a gidan bane shi yasa na kawo nawa shawarar for my own good” 

Mumy ta jefa masa wani shegen kallo tace “Sau da nawa da nawa kake xaman gidan idan ba gulma da munafurci ba 

Aliyu?? Sati da lahadin da kake dawowa yi a gidan ne xaka wani ce kai ma ba ganinta kke son yi ba? Uban ma me ta 

tsare maka tukun? To ynda ka kawo shawarar a kai ta makarantar kwana sai ka koma kace a sa ta a day, in har kana 

son wanyewa lafiya….” Da mamaki yake kallon Mumy yace “Toh Mumy ke kuwa meye na ki idan an kai ta 

makarantar kwana? Naga kema ba wani son xamanta kike a gidan ba fa, so it’s better she should stay away from this house completely, hankalin kowa xai fi kwanciya, ni na xata ma xaki fi kowa murna da shawarar da na bada, I see 

no reason da xa ki daga hankalin ki don ance xa a kai ta boarding, sai dai idan da akwai wani abun daban…” Mumy 

da ta bude baki tana kallonsa tayi shiru ta kasa cewa komai da farko, can ta dake tace “Akwai wani abun kamar me, 

ban fahimta ba?” yace “No nima ban sani ba, kawai dai nayi tunanin haka ne” Ta hadiye abu da kyar tace “To bari in 

fito maka a mutum yanxun tunda ba tsoron ka nake ba Aliyu, ban ga dalilin da xa a kai yar tsintuwa tsadadden 

makarantar kwana da ya fi makarantar da ‘ya yan masu gida ke xuwa ba, baxan laminta da hakan ba” wani 

murmushi Shuraim yyi kamar baxai ce komai ba sai kuma yace “But ke kika ce baki da ra’ayin a kai su Khadijah 

makarantar kwana lkcn da na kawo ma Abba shawaran haka few years back, amma in har yanxu kinga kina son su je, 

ni xan yi ma Abba magana baxai ki kai su ba su ma” Tsawa Mumy tayi masa tace “Wai ban gane alkiblar ka ba 

Aliyu, kare yar tsintuwar kake yi kke challenging dina ko kuma shawara da ban bukata daga gareka ba kke bani?” 

Ya girgixa kai yace “Aa ko daya” Tana nuna sa on a serious note tace “Toh tun wuri idan ba haduwa kake son yi da 

fushina da bala’i ba duk wani abu da ya shafi lamarin yar tsintuwar nan kada ka sake sa baki, nace kar ka sake, bbu 

ruwanka da duk wani lamari da ya dangance ta ko da kuwa Ubanka ya tambayi opinion dinka, just remain mute” A 

hankali yace “What if i am also trying to find a way out for my self, as in…. May be I am not comfortable living in

the same house with her also, Nima ina neman mafita….” Mumy tace “Toh sai ka tsiri cewa a kai ta makaranta me 

tsada, Ina aka kai makarantun gwamnati da xaka kira Turkish??” Yace “Sbda hakan kadai xai ba ma Abba karfin 

gwiwar kai ta, idan da na gwamnati nace a kai ta Abba baxai kai ta ba” Mumy tace “Toh ni ba ruwana da duk wnn, 

ni kawai ka san ynda kayi ka sa a fasa ma kai ta boarding din gaba daya” Yace “Toh” tace “Toh me??” Yace “Toh in 

sha Allah” Tace “I am serious Aliyu kada ka raina min hankali” yace “Ehh xan kara yi ma Abba magana in sha 

Allah” Juyawa tayi ta nufi kofa ya bi ta da kallo har xata fita ta juyo tace “Toh yau litinin me ya hanaka komawa 

Zarian ma?” Yace “Sai Wednesday in sha Allah” Mumy tace “Ba dai degree kake ba Masters ne, idan xaka tsaida 

hankalin ka gu daya ka tsaya kayi karatu tsakani da Allah ka tsayar, ni ban ma ga amfanin weekend da kke dawowa 

ba, Sudais idan ya tafi ba sai bayan watanni me yawa yake dawowa ba, kai kuwa kamar wanda ake mintsili ko kuma 

wanda yyi wani ajiya a gida yana dawowa dubawa a kai a kai” tana kai wa nan ta fita ta kulle kofar, mayar da 

dubansa yyi saman qur’anin gabansa ya d’an yi murmushi cikin cool voice dinsa ya fara karatu. Washegari da safe 

Mami na kitchen tare da Heedayah tana gwada mata yanda xata dinga hada shayi da kanta, A hankali Heedayah ke 

diban madaran kamar tana tsoronsa har wani rawa hannunta yake yi sai ta xuba a cup, Mami tace “Look, ki nutsu… 

Ko me xaki yi ki dinga yi gently don’t panick, now fetch the Milo also…” Heedayah ta kai cokalin cikin Milo din ta 

debo, yamutsa fuska tayi tace “Mami me yasa kalan shi haka? And…” Mami ta dakatar da ita tace “Deba nace ki na 

batan min lkci xan tafi in shirya” Sake debo milon tayi ta xuba a cup, Mami tace “Sugar kuma cube uku xaki dinga 

sawa” Heedayah ta kirga cube din sugar din ta xuba a cup din, Mami bata bari ta dau flask din da kanta ba don a cike 

yake, ta xuba mata ruwan xafin cikin cup din dake dauke da kayan shayin, Heedayah sai kallon tiririn dake tashi 

take ko kiftawa bbu, Mami ta dau bottle water ta karasa cike cup din tace “Idan baki son yyi maki xafi sosai sai ki 

kara ruwan sha a ciki” Mami ta rufe gwangwanayen madaran ta ajiye su gefe da sugar, daga kai Heedayah tayi suka 

yi ido hudu da Shuraim da ya bude kofar kitchen din, Mami ma ta juya, sauke kansa yyi yace “Ina kwana” Mami 

tace “Lafiya lau” ya juya xai fita Mami tace “We are not stopping you from doing what u came to do” Ya d’an tsaya 

kamar me contemplating ya fita ko ya shiga kitchen din, can dai ya shiga ya tafi gun da mug suke ajiye, Heedayah ta 

bi sa da kallo, ya dau daya ya dawo xuwa gun flask, a hankali Heedayah tace “Mami shima shayin xai yi ya sha?” 

Mami tace “Ina ruwanki??” Bin bayan Mami Heedayah tayi ganin xata fita kitchen din da cup din shayin, sai da 

suka isa kofa ta juya tana kallon Shuraim da ya bi ta da ido shi ma, hade rai tayi ta murguda masa baki har da juya 

manyan idanuwanta, sai kuma ta fita kitchen din da sauri tana bin bayan Mami. Mami na gama shiryawa, Ta tabbatar 

Heedayah ma ta gama shiryawa suka fito main parlor a tare ta kulle kofarta, Shuraim ne xaune parlon yana kallon 

wrestling, Heedayah na kallon Tvn tace “Mami me yasa basu sa kaya ba kamar mu, nima xan iya tsayawa haka??” 

Mami tace “Ehh tunda baki da hankali” Daga haka ta wuce dakin kaka, Heedayah na biye da ita kamar xata yi kuka, 

waigo Shuraim tayi ta turo baki ganin yana kallonta ta shiga dakin kaka, bayan Mami sun gaisa da kaka tace “Kaka 

xan tafi gun gidan Baffansu Junaid” Kaka tace “Au haba, can xa ki yini kenan yau?” Mami tace “In sha Allah” Kaka

na kallon Heedayah kafin ta ce komai Mami tace “Go down now and greet her” Heedayah ta durkusa kasa tace “Ina 

yini kaka” Kaka tace “Toh mu dai ba mu yini ba tukun, da safiyar Allah kice Ina yini?” Mami ta dago Heedayah tace 

“Toh bari mu je kaka” Kaka tace “Au tare xa ku?” Mami tace “Ehh tare xa mu tafi” Kaka tace “To Amadun ya sani 

kuwa, don naga bai fiye son ana fita da ita ba” Mami tace “Ya sani” Kaka tace “Toh ki dai kula da ita, ita kuma 

Hajiya Zuwaira kice Ina gaisheta, Allah yayi mata albarka, mata me mutunci, har na bar gidan girmama ni take ke 

kyace ni na haifeta, kayana kuwa kullum sai ta sa masu aiki sun wake sun goge min, to bata fiye min wasu ba ma ni, 

jira in dibar maki kaikayi koma kan mashekiya ki kai mata, kuma kice nace Allah ya mata albarka” Tuni Mami ta 

fita dakin bayan kaka ta kulle mata iccen hayaki a leda ta amsa, Heedayah dai sai waigo kaka take, kaka tace “Ni dai 

aniyar ki ta biki, ban gane kan kallon nan ba…” Suna shigowa main parlor Mami ta nufi kofar fita, Shuraim dake 

xaune har sannan yana kallon wrestling ganin sun hada ido da Mami yace “Allah ya tsare” tace “Ameen” Heedayah bata fasa waigo sa ba har suka isa kofar, ya dau wayarsa yyi kamar xai jefa mata ta fasa ihu ta rike Mami, tuni ya 

ajiye hannunsa ya maida dubansa kan TV yana kallo attentively, ko juyowa Mami bata yi ba suka fita parlon, 

Heedayah ta murguda masa baki kafin ta daina ganinsa. A cikin gidan Alhaji Imran Mami tayi parking suka shiga 

ciki da Heedayah, ta tadda Hajiya Zuwaira da Mai aikinta a parlor, bayan sun gaisa Hajiya Zuwaira tace “Baffa na 

parlon sa ku je ku gaisa…” Mami tace “Ohk, ku kadai gida yan makaranta na can makaranta” Hajiya Zuwaira tace 

“Ae kam suna makaranta, jiya Junaid ya je masu visiting gaba daya” Hajiya Zuwaira ta bi Heedayah da kallo don 

sosai yarinyar ke mata kyau, komai nata burgeta yake bari hancinta da d’an karamin bakinta, idonta kuwa har lkcn 

basu koma farare ba, Mami ta wuce sama xuwa parlon Baffa, bata fi minti goma sha biyar bs parlon nasa ba bayan 

sun gaisa ta fito tare da Heedayah, Bedroom din Junaid ta bude, ta gansa kwance yyi rub da ciki yana bacci, 

Heedayah ta wara manyan idonta ta cikin glasses dinta tace “Mami Yaya” Zame hannunta tayi a na Mami ta shiga 

dakin da sauri ta hau saman gadon ta xauna dab da fuskarsa a hankali tace “Yaya” Jin bai ce komai ba ta kai hannu 

dogon hancinsa ta ja, a hankali ya bude lumsassun idonsa, ya sake rufe idon murya can kasa yace “Cutie” Washe 

masa hakoranta tayi tace “Me kake yi?” Bai bude idon ba har sannan yace “Bacci” tace “Nima xan yii?” Bata jira 

cewarsa ba ta kwanta yanda ya kwanta kusa da shi tana facing dinsa, bude ido yyi, yyi murmushi har dimple dinsa 

ya nuna, ta kai finger dinta wajen ita ma tana murmushin, Ta mike xaune tana kallon Mami tace “Mami ni me yasa 

bani da irin nasa” Kumatunta ta nuna ma Mami nufinta me yasa bata da dimples, juyawa Junaid yyi da sauri ganin 

Mami ya mike xaune yace “Mami” Mami tace “Karfe goma saura you are still on bed” yace “Aa ban jima da 

shigowa ba, Ina kwana” Mami tace “Lafiya lau” kallon Heedayah tayi tace “To sakko mu tafi parlor” Tace “Aa 

Mami xan tsaya da Yaya plss” Mami tace “Ki tsaya kiyi masa me, sakko mu wuce my frnd” Sauka tayi daga kan 

gadon kamar xata yi kuka ta nufi kofa Junaid ya bi ta da kallo har suka fita, Bangaren Hajiya Zuwaira Mami ta shiga, 

ta tadda har Hajiya Zuwaira ta sa masu aiki sun hada mata kayan kari a parlonta, Mami tace “Ikon Allah, we just 

breakfasted before leaving home Hajiya” Hajiya Zuwaira tace “Sai ku kara ai” Murmushi kawai Mami tayi ta xauna, 

Heedayah ta xauna kasa kamar yanda Mami ta nuna mata ta dinga yi a ko ina, Hajiya Zuwaira ta hada mata shayi ta 

mika mata, Heedayah ta kalli Mami tace “Mami ai na sha tea” Mami tace “To ke kin ji, she’s full” Hajiya Zuwaira 

tace “Toh ai shkkn, ya kaka fa” Mami tace “Tana can” Hajiya Zuwaira tayi murmushi tace “Uhn kaka sai hakuri…. 

ga dai dadin xama ga kuma akasin haka” Mami ta girgixa kai tace “Kwanan ta nawa nan?” Hajiya Zuwaira tayi 

dariya sosai tace “Ranan da kuka koma ranan ta sa a maida ta gida” Mami tace “Bata dai baki wani matsala ba ko?” 

Hajiya Zuwaira tace “Toh ai duk Inda tsoho yake dama sai anyi hakuri da shi balle tsoho irin kaka, har da rikicin 

tsufa, ni fa har ta bar gidan nan bana gane gabas dinta balle yamma, ita dai ga ta Nan dai” A hankali Heedayah ta 

sulale ta fice daga dakin ba tare da ta bari sun lura ba, ta bi hanyar da suka bi xuwa dakin Junaid, bude kofar tayi ta 

leka ciki, xaune ta gansa gefen gado yana danna wayarsa, ta washe masa hakora ta shiga ciki tace “Yaya” Daga kai 

yyi yana kallonta har ta iso ta xauna kusa da shi tana kallon abinda yake yi a waya, yyi kasa da murya yace “Wa 

yace ki shigo dakina?” Tace “Ni ce na shigo da kaina, I want to be with you” Kallon bakinta yake, ta wara masa ido 

tace “Yaya yaushe xan ga Farida?” Ya dauke idonsa daga lips dinta yace “Ki tambayi Mami mana” Tace “Ce min 

xata yi bata sani ba, Yaya me yasa sai Shureen ya dinga min haka….” Wayarsa ta amsa a hannunsa ta gwada yanda 

Shuraim ke mata ta jefar da wayar xuwa bakin kofa, xaro ido yyi yana kallon wayar tasa ya mike da sauri yace “Kee 

wayana kika wurgar haka?” Tace “Aa haka Shureen ke min” Ya tafi ya dauko wayar yana duba screen din da ya 

fashe ya dawo ya hade rai yace “Sai nace ki gwada min da wayata?” tace “Toh nima idan ya min haka wayarsa xai 

fashe haka kenan?” Junaid ya xauna kusa da ita yana kallonta yace “Me yasa yake maki haka” ta bude hannu tace 

“Ban sani ba, sai ya dinga min haka kuma” kallon yanda ta xaro idonta Junaid ke yi, yace “Haka yake maki?” Ta 

gyada masa kai, Yace “Toh a ina kike haduwa da shi?” Ta gyara xama tace “A parlor ko a kitchen idan Mami xata 

bani shayi, sai ya min haka….” Da ido ta dinga bin dakin da kallo alamar haka yake bin ta da kallo, Junaid ya d’an 

tabe baki yace “Ki gaya ma Abba” Tace “Toh” bude kofar dakin aka yi duk suka juya da sauri, Mami ta hade rai tace 

“Wa yace ki shigo nan din” Heedayah ta sauka saman gadon da sauri tana nuna Junaid tace “Shi ne” Junaid ya xaro 

ido yace “Ni?” Tace “Eh” Mami tayi mata alamar da ta xo ta fita, ba musu ta nufi kofar ta fita kafin Mami ta rufe 

kofar Heedayah ta daga masa hannu suka wuce. Sai kusan yamma Mami ta bar gidan Baffa, tun da suka hau titi 

xuwa gida Heedayah ke ce mata Mami bamu ga Yaya ba muka tafi, Mami tace “Ai bai dawo ba, gobe xai xo” kamar 

xata yi kuka tace “Toh” karfe shidda saura Mami tayi parking a compound, Sai da ta sauka motar sannan Heedayah 

ta sauka, A balcony suka tadda Shuraim xaune yana operating laptop, Ya gaida Mami ta amsa ta shiga ciki, 

Heedayah ta bi sa da kallo kafin ta shiga ciki ya fixgota yace “Kallon me kike min?” A tsorace tace “Aa” ya daure 

fuska yace “Me yasa kike kallona nace??” Tace “Kai ma naga ai kana kallona da idonka” hada ido suka yi da Mami 

ya saketa ta nufi kofa da sauri ta juyo ta wani juya masa ido ta shige cikin parlon Mami ta rufe kofar…. Bayan isha 

Shuraim na parlon Abbansa kasancewar ya kirasa a waya yana neman sa, Abba ya gama abinda yake, sannan yana 

kallon Shuraim yace “Shuraim I am worried at sending Heedayah to boarding school as you suggested because, Ina 

son ta samu ilimin addini sosai, ba boko kawai ba, shi yasa ka ga then banyi supporting xuwansu Rabi’ah boarding 

din ba, karatun addini nake dubawa” Shuraim ya d’an yi shiru da farko, sai kuma yace “Abba a situation da ake ciki ynxu, boarding din is the best” Abba yace “Koh, then what about islamiyya?” Shuraim yace “Idan sun yi hutu sae ta 

dinga xuwa” Abba yace “Toh shkkn, but ajin da xa a sa ta fa?” Yace “Jss2.. or 1…” Bude kofar parlon aka yi Mumy 

ta shigo, Abba ya daga kai yana kallonta, mikewa Shuraim yyi yace “Sai anjima Abba” Abba yace “Alright” Mumy 

ta bi sa da kallon gefen ido har ya fita. Bayan sllhn asuba Shuraim ya shiga gaida Abbansa, bayan sun gaisa Abba 

yace “Jiya mun yi magana da Barrister tace min su Farida na kan yin third term exams ne ynxu…. So ynxu sae anyi 

hutu an koma za ayi enrolling Heedayah, but before then I will get a mu’allim for her da xai dinga mata karatun 

qur’ani da sauran abubuwan da ya kamata…” Shuraim yace “Mu’allima instead” Abba yace “Really?” Shuraim bai ce 

komai ba, Abba yace “To bbu damuwa, when are you going to Zaria?” Yace “Tomorrow” Abba yace “Allah ya kai 

mu” mikewa yyi ya ma Abba sallama ya fita parlon. Karfe sha daya na safe, Heedayah ta fito parlon Mami rike da 

cup din shayi da ta sha xata kai kitchen, Shuraim na kwance 3 seater yana kallon wani action movie da ake yi, Ta 

gefen ido ya bi ta da kallo, ita kuwa sai kallon dogon kafarsa take, yana lura da ita, idan ta kalli nasa sae ta kalli nata, 

bude kofar parlon aka yi ta daga kai Junaid ya shigo parlon da sallama, ajiye cup din hannunta tayi a kasa ta tafi da 

sauri ta rungumesa tace “Yaya ranan nan ban ganka ba muka wuce” Junaid na kallon kayan jikinta yace “Me yasa 

kika fito da kayan nan?” Ta kalli kayan tace “Mami tace in sa” Tuni Shuraim ya lumshe ido kmr me bacci, Junaid na 

rike da hannunta suka wuce parlon Mami, Junaid na kallon Mami yace “Mami kayan nan da ta sa ina ga kamar bai 

yi ba, she shouldn’t be wearing this out” Mami ta kalli wando da rigan dake jikin Heedayah tace “Meye rashin yin 

sa?” Bai ce komai ba, Mami tace “Hijab xan sa mata ta dinga yawo a gidan ko jallabiya?” Nan ma dai bai ce komai 

ba, Mami ta masa wani kallo ta ci gaba da abinda take yi, ya xauna ya gaisheta a hankali, ta amsa tace “To sai ka 

siyo mata jallabiyoyi ta dinga yawo da su” shi dai bai ce komai ba, can ya mike yace bari in je in gaida kaka, Tace 

“Ohk” fita yyi Heedayah ta bi sa da sauri, Bai tadda Shuraim a parlon ba kuma, ya shiga parlon kaka da sallama, 

hada kayanta ya sameta tana yi a katon akwatin ta, da mamaki yace “Ina kuma xa ki kaka?” Kamar jiran xuwansa 

take ta gyara xama ta fashe da kuka ta rike kai tace “Wai da barin garin xan yi Junaidu, in tafi can Inda Allah yayi” 

Ya xauna yace “Me ya faru kuma kaka?” Kaka na Shessheka tace “Ni dai ba fitinanniya bace ni kuma ba 

rigimammiya bace Junaidu, kaga tunda uwar ka ta dawo gidan nan ta daina sake min fuska, yau kwana biyu da 

dawowarsu Ina kirgawa, Deedayar ma ta rabata da shigowa nan gaba daya, me nayi mata Junaidu? Daga nace a ba 

Maryam Deedayah bata san duk haushin ba a tafi da ni India bne shine ta kullaceni, toh ko Karen hauka ya cijen ae 

bana bari Maryam ta rike Deedayah ba, Maryam axxaluma, ae kamar an ba kura nama ne, to tun daga sannan Rakiya 

ko ta shigo min minti daya kawai take, ita kuma Deedayar ganinta ma ba abu ne me sauki a wajena ynxu, duk 

wahalar da nayi da ita sae a rabamu haka kawai ba tsididi ba tsadada?” Junaid dake ta sauraronta yyi kasa da murya 

yace “Kiyi hakuri kaka, bbu Inda xa ki je” Kaka ta kara rushewa da kuka tace “Da ma kayi aurene sae ka kai ni 

gidanka in huta da jarabar kowa inyi ta kai na, Amma baka yi ba sai gantali kke, wnn shine rana xafi inuwa k’una, ni 

dai na gaji” Heedayah da ke tsaye bakin kofa ganin yanda kaka ke kuka ta fashe da kuka ta fita dakin da sauri, Kaka 

ta xaro ido tace “Kaga don Rakiya tayi xaton wani abun nayi mata in shiga uku in lalace ko?” Kuka sosai Heedayah 

ke yi bayan ta fito ta tafi can jikin kujera ta rakube har da Shessheka, Shuraim da ke xaune dining ya mike yana 

kallonta, ya kalli bangaren Mumy da gefen ido kafin ya nufeta…. Tsayawa Junaid yyi bakin kofar dakin kaka ya fasa 

fitowa ya bi Shuraim da ido.

Shuraim na tafiya xuwa gun inda Heedayah ke xaune tana rusa kuka kamar ance ya daga kai ya ga Junaid tsaye 
kofar dakin kaka ta jikin TV dake kashe a parlon, yyi saurin dauke idonsa ya wuce Heedayah ya karasa gun TVn ya 
kunna sannan ya dau remote ya koma saman kujera ya xauna ya shiga canxa channel, Junaid ya karasa fitowa parlon 
ya karasa gun Heedayah ya duka yace “Why are you crying?” Ta gefen ido Shuraim ke kallonsu yana canje canjen 
tasha, Ta goge idonta da bayan hannunta cikin rawar murya tace “Toh me yasa kaka take kuka ita ma?” Soft smile 
Junaid ya sakar mata ya dagata suka mike ya ciro handkerchief yana share mata idonta, Shuraim bai yarda ya sake 
satan kallonsu ba ya dinga kallon screen din Tv, a hankali Heedayah tace “Yaya bana son kaka ta yi kuka kuma, or is she sick?” Junaid ya kama hannunta yace “Mu je ki bata hakuri kice kar ta sake kuka…” Yana rike da ita suka nufi 
hanyar dakin kaka, Heedayah ta kalli Shuraim da yayi frowning face ya bi su da wani kallo, wani harara ya jefa mata, 
ta turo masa baki ta dauke kanta tana biye da Junaid xuwa dakin kaka. Kaka na kwashe tarkacen kayan 
magungunanta da ta jera gaban madubi tana xuba su cikin katon handbag dinta Junaid ya shigo da Heedayah, 
Heedayah ta rakube jikin kofa cikin sanyin murya tace “Kaka kiyi hakuri ki daina kuka kin ji?” Kaka ta juyo ta kara 
rushewa da wani sabon kukan tace “Atoh kaga yarinya kenan ma tana bani hakuri balle kattin matan da Amadu ya 
ajiye a gidan nan, ko sanin ina yi ma basu yi ba, bbu wanda yace min ci kanki har ynxu, haba jama’ah ynxu ace bare 
ya fi jin k’an ka a duniya a kan naka, me muka hada da Deedayah banda Amadu da ya jajubo mana ita a bakin titi 
tana galantoyi, amma ace ta damu da halin da ta gan ni a ciki a kan yan gidan nan, abinda su Rabi’ah basu ta6a min 
ba kenan, ko kuka nake ina birgima basa ce min komai sai ma mayar da ni fim da xasu yi” Junaid ya karasa cikin 
dakin, yyi kasa da murya yace “Yanxu dai kiyi hakuri kaka…” Kaka tace “Toh ni abinda nayi ma Rakiya ta fita 
harkata a gidan nan ne na kasa ganewa har ynxu, ka dubi Allah ka tafi ka tambayo min ita abinda nayi mata yanxun 
nan…” Junaid yace “Babu abinda kika yi mata kaka, kawai dai….” Kaka ta daga hannu sama tace “Aa ba ruwana ka 
tafi yanxu ka tambayo min ita kawai, ko gaisuwar kirki fa ta bar min a gidan nan, haka kawai gida duk ya min xafi 
kamar mayya, ko don an gan ni shiru shiru me hakuri bana son tashin hankali??” shiru Junaid yyi yana kallonta, sai 
kuma ya juya a hankali ya nufi kofa xai fita suka kusa cin karo da Salima, haka kawai gabansa ya fadi, hanya ya bata 
tana kallonsa, shi dai bai bari sun hada ido ba ya fice dakin, Heedayah dake tsaye har sannan cikin sanyin murya 
tace “Kinyi hakuri kaka?” Kaka ta kalleta tace “To uban wa nake takama da shi idan banyi hakuri ba Deedayah? 
Bani da kowa sai Allah sai ma’aikin Allah, ni a yanxu fa da ni da juya daya nake kallonmu don wa ennan ba ‘ya yan 
nuna ma duniya bane, Atoh in nuna su in ji kunya, bari dai Junaidu yyi aure wllh da kudinsu baxa su gan ni ba, 
abinda nafi kowa sanin kan iskanci….” Shiru tayi ganin Salima tace “Waye wannan?” Salima na murmushi ta karaso 
da ledan hannunta tace “Ni ce kaka, Kin dawo lafiya?” Kaka tace “Ke xan ce ma kin dawo lafiya ai Salima, ni da na 
samu labarin yau watan ki daya baki gidan nan?” Salima ta hade rai tace “In ji ubanwa? To ai gidanmu na koma” 
Kaka tace “Toh wani man kika samu yake neman kwale maki fuska kuma yanxu” Salima tayi mata wani kallo ta 
ajiye ledan hannunta tace “Ga fura na gani a hanya sabon yi me kyau na siyo maki” Kaka ta washe baki tace “Toh 
Allah yyi maki albarka, dama dai ke din ce me kawo min wa ennan abubuwan” Salima ta kalli Heedayah tace “Ita 
kuma wnn ido ya bude kenan?” Kaka tace “To da fa? Ae har ta fi ki gani yanxu, bbu abinda xa mu yi sai godiya ga 
Allah, ynxu ma ji nayi suna cewa boding xa su kai ta….” Bude kofar dakin aka yi Shuraim ya shigo, Kaka ta ajiye 
jakar hannunta tana nunasa tace “Kai kuma kana gidan nan ina gidan nan amma ka shigo ka gaisheni balle ka san 
halin da nake ciki kake ganin asara, ai abun kunya ne in nuna ma duniya kai ince jika na ne, ba gwara min Deedayah 
a kan ka ba….” Heedayah ta kalli Shuraim sannan ta kalli kaka a hankali tace “Kaka sunana Heedayah ba Deedayah 
ba” Kaka tace “Meye kuma Yeedaya?” Heedayah tayi stressing sunan tace “Heedayah…” Kaka tace “Ba ruwana da 
wnn, ba Amadun da kansa yace sunanki Deedayah ba, meye kuma laifina a nan, Kai Shureen ba Deedayah ake cewa 
ba dama??” Heedayah tace “Ae Shureen ma bai san sunana ba, Bai iya fada ba” Fixgota Shuraim yyi, Kaka ta taho 
da gudu tana cewa “Kul kar ka ta6ata wllh, kana ta6a ta watan barin ka gidan nan ya tsaya Shuraim… A kanta xan sa 
Amadu ya koreka ka tafi duk Inda xa ka” Kallonta Shuraim ya tsaya yi da mamaki, ta kwace Heedayah a hannunsa 
tace “Uban me ta hada da kai xaka Fincikota haka, dangin uwa ko na uba?? to wllh kar ka kuma, bbu ruwana da ko 
kai waye, xan mance sanin da na maka in ci maka mutunci a kanta, yarinyar da tun ba aje ko ina ba tana 
tausayina….” Shuraim na kallonta da kyau yace “Ki ci min mutunci a kanta??” A fusace kaka tace “Wllh tllh, har shi 
Amadun sai in 6ata masa a kanta balle kai karan kada miya, ba gwara min ita ba akan kai da Amadun, duk me 
damuwa da danuwarka ae shine naka bbu wani xancen jininka ynxu” Juyawa Shuraim yyi xai fita suka hadu da 
Junaid bakin kofar, ya basa hanya ya shiga snn yyi ficewarsa daga dakin, kaka tace “Kai ka ji min katon Mutumi ya 
finciko yar mutane xai duka daga tace bai san sunanta ba, shi Amadun ne ya sa shi wnn danyen aikin ko bala’i ke 
damunsa? Haka fa ya xuge uban wai su kai ta makarantar kwana sbda tsabar mugun hali” Junaid yace “Makarantar 
kwana kuma?” Kaka tace “Wllh tllh, Kai ka ga hakan ya kamata?” Junaid ya kalli Heedayah dake ta kallon kaka yyi 
murmushi yace “Ya kamata kaka, xata samu karatu sosai kuma xata yi wayo, ta iya xaman duniya a duk ynda ya xo 
mata” Salima dake ta kallon Junaid ta kashe murya tace “Ae kuwa gaskiya ka fada….” Ko kallonta Junaid bai yi ba, 
Kaka ta kalleta tace “Ki bar tsomo bakin ki a xancen manya Salima, har fa ynxu kin ki aure ko da yake bbu 
maneman ne ynxu, ke fa kusan sa’ar Shuraim ce, a haihuwar kaji kin haifi Heedayah fa” Mami ce ta shigo dakin da 
sallama, Kaka ta juya ta ci gaba da hade kayanta ta wani marairaice fuska, Mami ta xauna, Salima ta duka kasa tana 
kallon Mami tace “Ina yini” Mami ta kalleta tace “Lafiya lau ya kike?” Salima ta d’an yi murmushi tace “Alhmdllh, 
kun dawo lafiya ya masu jiki?” Mami tace “Alhmdllh mun gode Allah” Mami na kallon kaka tace “Kaka ynxu 
Junaid ya sameni da wata magana da ban fahimta ba” Kaka tace “Aa bbu abinda baki fahimta ba Rakiya, yau kwana 
biyu kenan bakya tanka ni a gidan nan ba kya kulani daga na bugi cikin Amadu in ga ko xai iya ba Maryam 
Deedayah, so nayi inga abinda ke xuciyarsa game da Deedayah dama, don har ynxu bamu san xuciyarsa ba gaskiya, 
amma shkkn kika kullaceni….” Murmushi kawai Mami tayi tace “Aa kaka, baki fahimce ni bane ni bbu komai a 
raina, amma kiyi hakuri idan ke haka kika yi tunani, shi babba ae ba a fushi da shi idan ana son wanyewa lafiya….” 
Kaka tace “Ka ji ki, kowa ma ai babba ne Rakiya, yanxu wa xai ce ke kika haifi Junaidu, duka duka nawa nake xa a 
dinga ce min babba kamar wata tsohuwa??” Mami tace “Toh ni dai kiyi hakuri baki fahimce ni bane kaka” Kaka tace 
“Ni komai ya wuce a gu na, amma fa ko shigo min nan Deedayar ta daina yi, ban san ko ke kika hanata ba” Mami 
tace “Toh xan dawo da kayanta nan din In sha Allah” Kaka tace “Ae dama a nan kayan suke tun xuwanta gidan nan 
kawoa shaidan ne ya shiga ya fita ya hada mu” mikewa Mami tayi tana murmushi tace “Ina d’an wani aiki ne kaka, 
bari in je in karasa” Kaka tace “Toh yi tafiyar ki, Allah yayi albarka” Mami ta fita parlon, kaka ta kalli Junaid tayi 
kasa da murya tace “Ae gwara haka dae mun tura mata aniyar ta ko?? Gashi ta shigo tana ta borin kunya, amma ae 
baxan nuna mata na gane ba” Murmushi kawai Junaid yyi yace “Xan je anjima in dawo kaka” Kaka tace “Toh Allah 
yyi maka albarka” Heedayah tace “Are you going with me Yaya?” Ya kalleta yace “No….” Bin sa tayi da kallo har ya 
fita dakin, Salima ta mike ta bi bayansa, Kaka ta bude baki ta bi su da ido can tace “Tabdiijam, toh me wnn yar 
duniyar ke nufi? Son Junaidun take Koko? Naga har kasa ta duka ta gaida Rakiya abinda ko Amadun bata ta6a 
dukawa kasa ta gaishesa ba balle ni da na haifesa” kaka ta ta6e baki tace “Toh sai mu xuba ido mu ga gudun ruwanta, 
karuwa ce fa, meye dalilin da xata makale ma Salihi irin Junaidu” ta kuma ta6e baki ta kalli Heedayah tace “Maxa 
tattara ledojin nan ki kai masu kitchen can ki watsar ki dawo ga sauran mantina na ajiye maki, yau xaki ga ynda 
nake wanke bandaki ciki da bai, ba a xuba maki ido ki lalace ba baki iya komai ba” Heedayah ta duka ta kwashe 
tarkacen ledojin Kaka ta fita da su, har lkcn Shuraim na xaune parlor sai dai bbu abinda yake, ta tafi bakin kofar 
kitchen ta watsar da ledan ta juyo suka hada ido da Shuraim, calmly yace “Koma ki kwashe su” Ta make kafada tace 
“Ae Kaka ce tace in ajiye a nan” tana fadin haka ta wuce abun ta, ya mike yace “Keee” tsayawa tayi tana kallon 
eyeballs dinsa, ya daure fuska sosai yace “Koma nace ki kwashe su” Ta wani xare masa ido tace “Ni baxan kwashe 
ba, ai kaka ce tace in wurgar a nan” Bude baki yyi yana kallonta, ta nufi dakin kaka tana waigosa har ta shige dakin, 
Kaka tace “Ga wasu nan ki tafi ki watsar” Kwashe sauran tayi ta nufi kofa xata fita suka ci karo da Shuraim, kamota 
yyi ta ji kawai ya tsula mata abu me xafi, ta fasa ihu a tsorace jin shegen xafi, kaka ta saki xanin gadon hannunta 
tace “Auxubillahi waye wnn?” Ko kallonta Shuraim bai yi ba ya juyo da Heedayah yana kallonta da kyau yace “Ki 
ka ce min baxa ki kwashe ba?” Bai jira amsar ta ba ya kara tsula mata dorinar hannunsa a jiki, ta fasa wani karan a 
rikice tana sosa wajen tana rusa kuka, Kaka ta fashe da kuka tace “Nace waye wannan??” Shuraim ya murda 
kunnenta ya sake xabga mata dorinar a jiki, fuskarsa a murtuke yace “Nace maki ina wasa da yara ne? Daga yau 
kika sake kallon Inda nake a gidan nan sai na fasa maki ido na cire su…” Yana fadin haka ya tura ta ya fita dakin, 
Heedayah ta kankame kaka tana kuka sosai tana kiran Mami, Mami ta fito xata wuce kitchen taji ihun Heedayah da 
sauri ta shiga dakin kaka, Kaka na ganinta ta kara rushewa da kuka tace “Hada mu yyi ya xane Rakiya, Ashe dama 
Shuraim d’an da6a ne bani da labari, dorina fa me baki biyar ya dauko yayi ta tsula ma yarinyar nan bata masa 
komai ba, har cewa yyi xai fasa idanuwanta ya kwakule to kungiyar yan shan jini ya shiga ne bamu sani ba??” Mami 
ta dinga kallon kafan Heedayah da shatin dorina ya kwanta, juyawa tayi ta fice daga dakin direct dakin Shuraim ta 
nufa, tsaye ta samesa dakin nasa, a takaice tace “Shuraim a kan wani dalilin ka doki Heedayah?” Bai ko juyo ba 
balle ya tanka ta, rai bace tace “Am I even supposed to ask why? How dare you? Ka fara hauka ne? Ko ka fara shaye 
shaye? To wllh daga yau ka sake gigin mata kallon banxa balle ka kai hannunka jikinta xaka sha mamaki na a gidan 
nan, Wait… Are you mad?” Daga kai yyi ya kalleta ta madubi jin yanda tayi stressing mad din, still bai ce komai ba 
dai, tace “To kayi na farko kayi na karshe wllh, ko me Heedayah xata yi a gidan nan naka kawai ido, kada ka sake 
kai min hannunka jikinta” tana fadin haka ta fice daga dakin, Can tsakar gida kaka ta kai ma Me gadi wayarta ya 
kira mata Abba taji ko kungiyar yan shan jini Shuraim ya shiga ba a da labari a gidan, daga karshe dai me gadi ya 
jogale waya fitina ya koma kansa ta tara masa mutan anguwa. Tun daga wnn ranan Heedayah ko fitowa tayi main 
parlor ta ga Shuraim sae ta koma daki da gudu, ko da kuwa tare da Mami take, wani irin tsoronsa na musamman ta 
fara yi a gidan, ko dakin kaka ya shigo idan ma a xaune take sai ta rufe ido wai tana bacci, idan a kwance take ma 
haka, ko karatu suke da mu’allimar da Abba ya dauko mata a waje tana ganinsa xata daburce kai kace mala’ikan 
mutuwa ga gani, Mumy kuwa kullum idan ta fita da safe sai yamma take dawowa kamar ma’aikaciya nan kuwa 
tuggunsu kawai suke hadawa da Hajiya Sadiya, kudi kuwa ta kashe ya kusa dubu dari biyu…. Kaka na xaune parlon 
Abba bayan isha, Abba yyi shiru yana sauraronta, Mumy kuma na hada masa fruit salad, Kaka tace “Toh shine nace 
bari in xo in ji dalilin hanata xuwa gidan nan da tayi bayan sun yi hutu…” Abba yace “Kaka ba ita xata hanata xuwa 
ba, sai dai Baffan nata yace ta xauna can gidan, kinsan duk makaranta daya suke tare da yaransa, to da aka daukosu 
daga makarantar dole can gidan xa a kai su ai….” Kaka tace “Toh shi Baffan wiwi ya sha da xai hanata xuwa gaida 
mahaifiyarta har ynxu? Ni sai in iya xuwa in samesa in gaya masa gaskiya, ko don Rakiyar bata magana? In dan ta 
nine ma Faridar ta dawo nan gaba daya kawai” Abba yace “Ni dai bbu ruwanki da wnn kaka, ai dole kafin su koma 
makaranta na san xa ta xo nan din, tunda hutun da saura har ynxu” Kaka tace “Idan an koma tare xa su koma da 
Deedayah kenan?” Mumy ta saci kallon Abba ta ji me xai ce, Abba yace “In sha Allah” kaka tace “Toh Allah dai ya 
kai mu lafiya, nafi son yarinyar ta xo nan ne su yi ta sabawa da wnn yaro….” Satan kallon Mumy kaka tayi sai kuma 
tayi shiru, Abba yace “Wani yaro?” Kaka tace “Su saba da Deedayar wai” Abba yace “Ohk” Abba yyi kasa da murya yace “Dama kuma Ina son xuwa in sanar maki kaka, Shuraim ya samu Soja….” Kaka ta dafe kirji tace “Sojaa???” 
Abba yace “Ehh” kaka ta saki salati tana tafe hannu tace “Naga abinda ya isheni, uban waye ya masa sha’awar soja 
ni Patuu, yyi ta harbe bayin Allah kenan basu ji ba basu gani ba? Yana xaune a mutum dinsa ma ya aka kare da shi 
balle ace an basa wani soja?” Kallonta kawai Abba yake, Mumy ta wani hade rai tana ci gaba da abinda take, Kaka 
tace “To waye ya samar masa Soja???” Abba yace “Abokina….” Kaka tace “Baka basa labarin bakin halinsa bane da 
mugunta, don duk mutum me shiru shiru mugu ne” Abba bai kuma ce mata komai ba, Kaka ta kyabe baki tace “Toh 
ni dai ba ruwana, shi massers din da yake fa” Abba yace “Xai ci gaba” Kaka tace “To ni dai ba ruwana, Shureen a 
khakin soja ai abu ya lalace kuma, taka mu kawai xai dinga yi yana wucewa wllh” Abba yace “Kaka an gaya maki 
ne domin kiyi masa addu’a Allah yasa hakan ne mafi alkhairi, duk wnn xancen da kike yi ba shi bane kaka” Kaka 
tace “Toh Allah ya sanya alkhairi, amma wllh ba ruwana wataran idan bamu yi hankali ba duk nuna mu xai yi da 
bindiga mu shiga uku, Abinda na fi kowa sanin halin d’an nan naka Shureen, kwanaki kana ji cewa yyi xai kwakule 
idon Deedayah ya kai kungiyar su amma ko mataki baka dauka ba, ni dai ina ta xuba ido in ji tace idonta na ciwo ko 
wani abu wllh a nan xan rufe ido mu tafi gidan yan sanda in gaya masu abinda Shureen yace” Tana kai wa nan ta 
fice daga parlon, Mumy dai ta cika kiris ya rage ta fashe sai dai bata tanka kaka tun asali dama, Abba ya sauke ajiyar 
xuciya ya girgixa kai shi ma bai ce komai ba… Yau Heedayah tana xaune dakin kaka tana kallon cartoon ta cikin 
glasses dinta dake mata kyau sosai kullum baya rabo da idonta, kaka ta yi mata maganan ta miko mata darduman 
kusa da ita yyi sau uku amma bata san tana yi ba, gaba daya hankalinta na kan kallon da take, aka bude kofar dakin 
Shuraim ya shigo, rufe ido tayi da sauri xuciyarta na bugawa, Kaka tace “Algungumar yarinya kawai sai wahala take 
bani Shureen, tun daxu fa nake mata magana tayi min banxa ta saka kallon jaraba da baxae mata gafara ba a gaba, ni 
dai wllh na gaji da yarinyar nan, ba ta da aiki fa sai kallon robobin nan da an mayar min tashar wa’axi sai ya canjo 
min na aljanu, gashi kaf gidan nn bbu wanda ta raina sama da ni, ynxu kuma daga ganinka ta runtse ido ba tsoron 
Allah, shi boding din har ynxu basu koma bane, naji labarin Farida sun yi hutu wajen Junaidu fa, kawai dai Uwar 
bata bari ta xo mana nan bane…” Bude kofar dakin aka yi sai ga Farida ta shigo tana kalle kallen Inda xata ga 
Heedayah, she looks so happy, ganin Heedayah ta saki jakar hannunta ta tafi da gudu ta tsallake Shuraim cike da 
murna ta rungume Heedayah gam tace “Didi na dawo, Didi I am happy you can see me….

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *