HEEDAYA CHAPTER 23 BY By Khaleesat Haiydar
Abba na parlonsa tare da Baffa wanda shigowarsa parlon kenan, bayan sun gaisa Baffa yace “Mun yi waya da kaka
kuma ban fahimce bayanin da take min ba daxu” Abba yace “Bayanin me kenan?” Baffa yace “Na tafiyar Heedayah
makaranta, what’s going on?” Abba yace “Eh I just decided tayi day, baxata je boarding din ba kuma” Baffa yace
“Ko saboda me?” Abba yace “Kawai ina ga hakan xai fi, she is going no where” Baffa yace “But kana tunanin xa a
iya convincing dinta da haka, Ina nufin ita kaka” Abba yace “Toh xancen gaskiya shine I can’t sponsor her to
Nigerian Turkish boarding, day din ma ba yanxu xata fara ba” kallonsa kawai Baffa ke yi bai ce komai ba, Shuraim
na shirin wucewa zaria da safen kaka ta shigo dakinsa ko sallama babu, Ta madubi yake kallonta yana jiran jin da
me ta shigo, tace “Shureen ka ga dai anyi walkiya mun gano Mahaifin ka ko?? To ga dai irin xuciyarsa yau Allah ya
bayyana mana, Ashe dama ba son Allah da annabi yake ma yarinyar nan Deedaya ba, kaji wai ba shi da kudin kai ta
makarantar kwana duk uban arxikin da Allah ya hore masa, a takaice dai yace bbu makarantar da xata je” Shuraim
ya juyo yana kallonta da mamaki, tace “Wllh kuwa, Ina jin fada suka yi kaca kaca da Rakiya a kan haka don naga
ranta a bace, ni dai na kira Umaru ya taho, nasan kuma yana hanya ynxu, bbu ruwana da biye Amadu mu yi tashin
hankali makota na jin mu” Shuraim yace “Yaushe Abban ya fada haka?” Kaka tace “Yau din nan wllh, bala’in da ya
tashi da shi kenan, ni ko nace anya lafiya kuwa, don naga shi ya bada kudi aka yi ta siyayyar xuwa makarantar, ni
ban masa baki ba balle ace da bakina ya tashi yau, to me ke faruwa? Ko da yake dama ai yana da bakin hali” tana
fadin haka ta fita dakin, Shuraim ya bi ta da ido, Kaka na fitowa ta hadu da Baffa a main parlor ya fito parlon Abba,
kaka tace “Kaji tsiyar ku ai, Amadu ya kiraka ko ni? Shiga kayi ya giggilla maka karya ko kuwa neman fitinata
kake?” Baffa yace “Shigowata kenan fa Baaba” kujera ya xauna ya gaisheta ta amsa tana daga tsaye tace “Toh bamu
san me Amadu ke ciki ba yau dai” Baffa yace “Aa ba fa wani abu bane kaka, kawai makarantar jeka ka dawo xa a sa
ta in sha Allah, bbu xancen makarantar kwana” da karfi Kaka tace “Bamu yarda baaaa, tunda har bbu wanda ya
matsi bakinsa da farko yace xai kai ta bording to bai isa ya juya mu kamar waina ba ynxu, ko don yaga bata da kowa
sai Allah sai shi sai ni??” sai kuma ta fashe da kuka sosai ta xauna tana kunce ha6ar xaninta, Baffa yace “Haba
Baaba, yanxu meye abun kuka a nan kuma? Dama ba abinda mutum xai iya xai daukar ma kansa ba? Yanxu wnn
Makarantar kika san nawa ne? Ya kai miliyan daya fa” Kaka tace “Bbu ruwana da wnn, meye kuma miliyan daya da
yanxu ina ihu xan gansa gabana, da can bai san ko nawa bane ya furta a kai ta? To wllh sai dai kai ka biya idan ba
haka ba in tattara yanawa yanawa inje duk inda Allah ya nufa, don ni ba karamar mutum bace baxa a kunyata ni a
gaban yar yarinya ba ance mata makarantar kwana xa a kai ta” Baffa yyi shiru yana kallonta ya ma kasa cewa komai,
mikewa tayi tana matsar kwalla ta wuce dakinta tana cewa “Ba da ni ba wllh” Shuraim ne ya shigo parlon bayan
tafiyar kaka, ya gaida Baffan nasa, Baffa yace “Je ka ka kira min Barrister Rahinah” Ya amsa masa sannan ya nufi
bangaren Mami, Da sallama ya shiga parlon, ganin tana waya ya jira har ta gama sannan yace “Ina kwana” Tace
“Lafiya lau” yace “Baffa yana magana a parlor” Mami tace “Okay, but do you have any idea on why Barrister
changed his mind toward sending Heedayah to boarding schl?” Ya girgixa kai yace “Ban sani ba gaskiya, but I will
try talk to him now” Mami ta mike ta dau Hijab dinta, sai da ta fita ya bi bayanta, xaunawa tayi parlon suka gaisa da
Baffa, Baffa yace “Ke kika sanar ma Kaka yanda ku ka yi da barrister daxu?” Mami tace “Ehh ni na sanar mata”
Baffa yace “But you shouldn’t have Rahinah, kinsan yanda take abubuwanta, sannan don barrister yace wnn yarinya baxata makarantar kwana ba I see no cause for alarm, ga makarantu dai iri iri na day, tunda kika ga yace baxa ta je
ba kinsan baxai iya bane commitments sun masa yawa, meyasa baki yi consider din haka ba” Mami ta girgixa kai
tace “Amma ya san da commitments din ya bada kudi me yawan gaske aka yi mata siyayya sannan tun last week
yayi niyyar tura min kudin schl fees din nata na dakatar da shi nace ya bari sai wnn satin, why the change of mind all
of a sudden, and abinda ya fi ban mamaki na nuna masa idan expenses din ne damuwan na bar komai a wuyana kar
ya wani damu, Amma barrister ya bude baki yace min makarantar ma baxata je ba kwata kwata har day din ma”
Baffa yace “Yanxu dai ni duk ba wnn ba, ku bar maganan boarding a tafi gobe Monday ayi mata registration ko a
makarantar su Khadijah ne, ki bar batun kaka kawai….” Muryar kaka suka ji tace “Algungumi, to daga kai har
Amadun idan ban kora ku kun bar mana gidan ba ku ce ba ni ba, tun kuna yara dama ku ka iya munafurci da tsegumi,
Banda rashin tsoron Allah don me xaka ce a fita batun uwarka, wato ga ni gantalalliya ko, kawai don Mahaifin ku ya
mutu ya bar ni cikin ku sai in xama bola ku yi ta cin dunduniyata kuna munafuratata kuna walakanta ni” sai kuma ta
fashe da matsanancin kuka sosai ta xauna ta rike kai, Baffa yace “Subhanallahi, meye haka kaka, to shikenan in dai
boarding ne xa a biya mata idan Allah ya yarda yau xata tafi” Kaka ta mike tana share guntun kwallarta tace “Da dai
ya fi, don ni ban gaji abun kunya ba, da wani idon xan kalli Deedayah ince an fasa kai ta bording” Daga haka ta
wuce dakinta, Mami tace “Ni matsalata yanxu shine kawai barrister ya amince ta tafi makarantar ko ni xan dau
responsibility din komai wllh, Allah xai hore in sha Allah” Baffa dai bai ce mata komai ba… Da farko kasa cewa
komai Shuraim yyi ganin kallon da Abbansa ke masa kamar ya san abinda ya kawosa parlon nasa, Abba yace “Nace
ina jin ka kayi shiru, I’m doing something important now” Yyi kasa da murya yace “Abba me yasa kace Heedayah
baxata je boarding din ba kuma, I thought….” Abba ya mike ya dakatar da shi strictly yace “Haka nayi ra’ayi, and
who are you to question my order??” Shuraim ya girgixa kai yace “Kayi hakuri” Abba yace “Leave now” mikewa
yyi ya fita parlon. Bbu kowa main parlor din, Baffa ya shiga dakin kaka ya kara bata hakuri ya tabbatar ta hakura,
Mami kuma ta koma bangarenta, part din Mami Shuraim ya tafi ya bude kofar parlon ya shiga, xaune ya sameta a
parlon, she looks so tensed, Shuraim ya xauna bayan few seconds yace “He don’t seems to want to listen….” Mami
tace “You don’t worry Shuraim, nace Baffa yyi masa magana ya bada permission din tafiyar nata, just permission…
Ni xan bada kudin makarantar” Shuraim yace “Toh shikenan, Allah ya sa hakan ne mafi alkhairi” Mami tace
“Ameen” Bude kofar parlon aka yi Junaid ya shigo da sallama, sau biyu yana kallon Shuraim dake xaune, ya gaida
Maminsa, ya dai dake suka gaisa da Shuraim din, Junaid ya xauna yace “Ya ake ciki yanxu Mami?” Mami tace “I
don’t know, Doctor nake jira in ji ya ake ciki” Mikewa Shuraim yyi ya nufi kofa ya fita daga parlon, Ido hudu suka
yi da Mumy da ta fito daga kitchen, da mamaki take kallonsa, ya karasa inda take walking slowly, Mumy na kikkifta
ido tace “Daga ina naga ka fito Shuraim?” Yace “Kaka ce ta aikeni…” Ta wani daure fuska xata yi magana sai ga
Baffa ya fito, murmushi tayi tace “Aa ashe Dr na gidan nan, sannu da xuwa” Baffa yace “Yauwa sannu, Shuraim yi
min kiran Rahinah” Shuraim ya d’an kalli Mumy dake ta murmushi, Ya juya xuwa bangaren Mami, ba a dau lkci ba
suka fito tare, Baffa na tsaye yace “Ki turo min account details din ki, xuwa anjima sai ku kai ta makarantar” Mami
tace “Noo it’s not ur responsibility Dr, you don’t have to, in sha Allah baxai gagara ba I will pay everything” Baffa
yace “I said you should forward to me ur details” Bai jira cewarta ba ya wuce parlon D’an uwansa, Mumy na kallon
Mami tace “Mun tashi lfya Hajiya” Mami tace “Lafiya, ya yara” bata jira cewar Mumy ba tayi wucewarta, Mumy ta
bi ta da wani kallo tana wani murmushi, Shuraim na kula da kallon da Mahaifiyar tasa ke yi ma Mami, tana juyowa
kansa ya juya da sauri ya nufi kofar fita parlon. Ko da Baffa ya shiga gun Abba domin sanar masa shi xai biya kudin
makarantar Heedayah kamar yanda Kaka ta umarce sa, Abba yace “Toh bbu ruwana a kan lamarin yarinyar daga
yanxu, and I have taken my hands off her….” Baffa ya mike yace “What nonsense? dama wani ne ya kawo maka ita
da xaka ce ka cire hannunka a lamarinta, or is something wrong with you Ahmad?” Abba bai ce masa komai ba
hakan yasa ya juya ya fita daga parlon. Karfe biyu na rana Mami ta sa Mai gadi ya gama shirya kayan Heedayah da
Farida a bayan motarta, duk kaka na tsaye bayan booth din yafe da katon gyalenta wai bata yarda da Mai gadin ba
kar ya rarumi wani abun ya boye, Mami ta fito cikin gidan tana isowa gun motar kaka tace “Kinga Rakiya ki saki
ran ki, naga kamar kin sa ma kanki damuwa, kada ki wani cuci xuciyar ki a banxa sbda Amadu, ya je mun bar sa da
halinsa, ni dai tunda ba shi kadai na haifa ba ai da sauki” Mami tayi murmushin karfin hali tace “Toh xa mu je da
Heedayah tayi masa sallama yanxu” Kaka tace “A kan me? Shi ya biya mata kudin makarantar kwanan ko ko akwai
abinda ta hada da shi banda tsintota da yyi, ai kinga yasan fushi nake da shi amma har ynxu bai shigo ya ce min ci
kanki ba, to don me xa ki kai masa yarinya ga xuciyarsa mun fara sani, ya je ya cuceta a banxa” Mami tace “Aa kaka
gwara dai ta sallamesa” Kaka ta rungume hannunta tace “Toh ni dai ba ruwana” Mami bata ce komai ba ta sa
Heedayah ta sakko daga cikin motar don har sun shiga da Farida tana rike da hannunta suka koma cikin gidan, da
sallama ta shiga parlon Abba, bata samesa parlon ba yana can cikin daki, Mumy ce ta fara fitowa rike da hularsa
alamar dai xabar masa hulan da xai sa take, tana kallonsu daga sama har kasa tace “Ya aka yi” Mami bata tanka ta ba
ta nemi gu ta xauna, Heedayah ta tsaya kusa da ita, Mumy ta wani tabe baki ta juya ta koma dakin, ba a wani dau
lkci ba Abba ya fito, Mami ta mike ganinsa tace “Sallama Heedayah ta xo yi maka, xa mu wuce yanxu” yana gyara
karin hularsa a takaice yace “Ohk, that’s good… Very good” Mami bata kuma ce masa komai ba, Heedayah na kallonsa tace “Abba me yasa baxa ka bi mu ba?” Mami ta kama hannunta suka nufi kofa, Mumy dake tsaye bakin
kofar dakin tace “Toh Allah ya kiyaye ya tsare Heedayah, ya bada abinda aka je nema…” Mami tayi ficewarta ta rufe
kofar, bayan mota Heedayah ta shiga tana kallon kaka dake xaune Farida kuma na gaba, Mami ta shiga driver seat
ta tada motar suka bar gidan ta kama hanya xuwa Rigachikum. Suna hawa babban titi kaka tace “Toh ke Rakiya kin
ga ya dace wnn yarinya ta tafi bata je ta sallami kawunta ba?” Mami tace “Wai Farida?” Kaka tace “Eh mana” Mami
tace “Aa sun yi waya kaka, yace ta wuce kawai” Kaka tace “Toh kinga da kyau haka ai, shi kuma Amadu Allah ya
shiryesa, dama ni don kar xuciya ta debeni in je in yi mugun alkaba’i a kansa kawai ki saukeni gidan Umaru idan
muna dawowa” Mami tace “Aa ba xa ayi haka ba kaka, kiyi hakuri” Kaka tace “Wllh baxan koma gidan ba, ce maki
nayi gidan ubana ne? dama ba sbda Deedayar nake xaune ba aka ce maku, iyaka duk ranan da xa ki je dubata a
makaranta ki taho mu tafi tare, ko kuma idan na ga hanya ni kadai ma xan dinga xuwa abu na kullum” Mami bata
kuma cewa komai ba har suka isa makarantar, a nan kofar makarantar suka tadda Junaid yana jiransu, a ranan aka yi
enrolling din Heedayah a Nigerian Turkish, aka sata a Jss2, har hostel dinsu kaka da Mami suka shiga, kasancewar
hostels din na sama classes dinsu kuma na kasa, Mami dai da taga Kaka xata xabga shiriritan ta sai tayi saurin
dakatar da ita ta kwaba mata, a haka har suka bar makarantar wajajen la’asar, Kaka har da kwallarta wai an raba ta da
Deedayah, duk yanda Mami ta so convincing din kaka su koma gida tare kin amincewa tayi tace ita dai a sauketa a
gidan d’an albarka Umaru. Mami tayi parking a parking space ta sauka ganin babu motar Abba ta gane ya fita gidan
kenan, ciki ta shiga ta tadda Mumy xaune parlor da Hajiya Sadiya da Hajiya Baturiya ga abinci iri iri an baxa a
parlon sai shewa suke ana hira kamar wa enda aka yi ma bushara da gidan aljanna, Mami tayi masu sannu amma
bbu wanda ya tankata cikinsu ta wuce bangarenta, ga mamakinta a bude ta ga parlon nata bayan ta rufe da xata fita
daxu, duk gidan ta san Barrister kadai ke da spare key din bangaren nata, ta dai shiga ciki tana bin parlon da kallo,
farar takarda ta ga saman kujera a linke, ta dau takardan tana jujjuyawa, can ta warware takardan tana duba rubutun
ciki….Murmushi kawai Mami tayi bayan ta gama karanta content din takardan ta linke a hankali ta wuce daki da shi ta
saka a jakarta. Mami na idar da la’asar ta dau wayarta ta kira Hajiya Zuwaira, bayan Hajiya Zuwaira ta daga suka
gaisa Mami tace “Su Nafisah sun wuce makarantar yau kuwa?” Hajiya Zuwaira tace “Aa sai gobe in sha Allah”
Mami tace “Toh Allah ya kai mu, don Allah Hajiya, Shafa’atu nake son ki turo min nan gida ynxu idan bata maki
komai, xata min wani aiki ne” Hajiya Zuwaira tace “Toh shkkn babu matsala xan turo ta, Allah dai ya sa ta gane
gidan” Mami tace “Toh Ameen” da haka suka yi sallama, Mami na ta xaune saman darduma har Shafa’atu me aikin
Hajiya Zuwaira ta iso, Mami tayi welcoming dinta tace “Wani d’an aiki nake so ki taya ni amma ba a nan ba, bari in
shirya mu je ko” Shafa’atu tace “Toh Hajiya” Mikewa Mami tayi ta wuce daki, ba a dau lkci ba ta fito rike da
makullin motarta da handbag tace “Mu je” Shafa’atu ta tashi ta bi bayan Mami suka fita parlon, Mami bata kulle
bangaren nata ba ta bar sa haka a bude, har sannan Mumy na parlon da tawagarta da suka karu a kan daxu, Suna
ganin Mami suka tuntsire da dariya, Mami dai ko kallon Inda suke bata yi ba har suka fita compound da Shafa’atu,
motarta ta nufa suka shiga suka bar gidan, can gidanta ta tafi, bayan sun gaisa da Mai gadi ya bude masu gate suka
shiga babban compound din gidan, Mami na shiga parlor ta kalli Shafa’atu tace “Gyaran gidan nan nake so kiyi min
shafa, har sama duk xa ki gyara min, labulayen nan ki cire xan baki wasu ki canxa, kitchen ma Ina son a gyara, But
anya xa ki iya ke kadai, naga aikin ya maki yawa koh?” Shafa’atu tace “Aa xan iya wllh Hajiya, ai k’ura ne kawai ba
wai wani datti ke gare gidan ba” Mami tace “Toh shkkn, xan je in dawo in sha Allah” Shafa’atu tace “Toh sai kin
dawo” har Mami ta nufi kofa sai kuma ta juyo tace “Kin dai ci abinci ko?” shafa tace “Ehh na ci Hajiya” Mami tace
“Toh shkkn” daga haka Mami ta fita gidan, sai bayan isha Mami ta sake dawowa gidan, Mai gadi ya shigo mata da
boxes din kayanta da na Heedayah daga cikin booth xuwa parlor, tsinkenta ko na Heedayah bata bari gidan Barrister
ba, Shafa’atu ta kwashi kayan gaba daya ta kai su sama tace “Xa a jera maki su ne a siff Hajiya?” Mami tace “Aa,
mu tafi kawai in maida ke gida kin ji, nagode kwarai” A bakin gate din gidan kawunsu Junaid Mami ta yi parking ta
bude jakarta ta fiddo dubu uku ta mike ma Shafa tace “Ga wnn shafa, naji dadin aikin da kika min nagode” Shafa
tace “Aa wllh Hajiya nagode….” Mami tace “Ki amsa ai ni na baki, amsa” Shafa ta karbi kudin da ladabi tace “Toh Allah ya saka da alkhairi ya kara girma Hajiya” Mami tace “Ameen ki ce da Hajiya Zuwaira ina gaisheta” Shafa tace
“Toh in sha Allah” Da haka ta sauka motar ta rufe ta wuce ciki, Mami tayi reverse ta bar layin ta dau hanyar gidanta.
Mami na gama parking sai ga kiran Hajiya Zuwaira, ta kashe motar ta daga, Hajiya Zuwaira tace “Barrister yanxu na
fito bangarena naga Shafa’atu ta dawo shine take nuna min kudin da kika bata wai kun je can gidanki ta gyara maki,
lafiya dai koh?” Mami tace “Lafiya lau Hajiya” Hajiya Zuwaira tace “Toh gyaran na menene ke da ba a gidan kike
ba” Mami tace “Ina son in koma can ne in d’an kwana biyu tunda Heedayah kinga yau aka kai ta makaranta” Da
mamaki Hajiya Zuwaira tace “Toh xaman Heedayah kike a gidan dama??” Mami tayi murmushi tace “Not at all wllh,
kawai dai ina bukatar hutu ne, Kinga nan bbu kowa, bbu wani hayani, sannan ina da cases da yawa to attend to, shi
sa na dawo nan sbda privacy” Hajiya Zuwaira tace “Toh Allah ya taimaka” nan suka yi sallama Mami ta ajiye
wayarta. Mumy ce xaune da Hajiya Sadiya a wani d’an akurkin daki, Mumy ta gama kirga damin kudin hannunta
‘yan dari biyar biyar da ya kama dubu dari da ashirin ta mika ma gabjejen mutumi me gemu dake xaune gabansu, ya
amsa kudin yana dariya me sauti ya ajiye a gefensa, Mumy na murmushi tana gyara yafin mayafinta tace “Toh saura
na ita yarinyar, sai dai kace ba yanxu xa a bada kudin ba ko?” Yana kallonta da jajayen idonsa ya girgixa kai yace
“Aa, kamar yanda sai da kika ga aiki da cikawa kika kawo min kudin wannan aikin, to shi ma wnn sai kinga aiki
yayi, mu bama amsan kudi sai bukata ta biya….” Cikin gamsuwa Mumy tace “Gaskiya ne, na kuwa ga aiki da
cikawa wllh, ban ta6a tunanin haka aikin ka yake ba….” Yayi dariya yace “Toh ya kika ce xa ayi da ita yarinyar?”
Mumy ta gyara xama da kyau tace “Ranka shi dade ni dai kawai ta walakanta, kmr ynda tasa na sha walakanci na
wani d’an lkci, in son samu ne ma ta xamo abar kyama cikin jama’ah, wanda har ita uwar rikon tata xata sallamata
taji ta fita ranta, sannan ka rabata da mijina wato tayi nisa sosai da inda muke ta je can ta karata, kada ta sake
shigowa rayuwar mu” cikin katon murya mutumin yace “Toh an gama, xa a jefa rayuwarta cikin garari a takaice….”
Mumy tace “Yauwa Ranka shi dade, ta xamo abar kyankyami cikin al’umma” Yana gyada kai yace “An gama”
Junaid ne xaune bedroom din Mami dake harhada wasu files nata xata fita aiki, bin ta kawai yake da kallo har ta
gama abinda take ta dau hand bag dinta tace “Kana nan ai…” Ya girgixa kai a hankali yace “Aa xan fita” Tace “Toh
mu je ka ajiye ni kawai ba sai na fita da mota ba, I don’t feel like driving, anjima when I am done with whatever I
am doing xan kiraka ka mai da ni gida” Bai ce komai ba, ta dau takardan da ta basa da ya ajiye gefensa bayan ya
gama dubawa, ta linke ta mayar da takardan jakarta, cikin sanyin murya yace “But Mami….” Mami ta dakatar da shi
tace “But nothing Ahmad Junaid, tashi mu je ka ajiye ni” tana fadin haka ta fita dakin, mikewa yyi ya bi bayanta
fuskarsa dauke da damuwa. Da yammacin ranan Mami na parlor tana jiran isowar mai aikin da ta bukaci a sama
mata, aka danna bell, mikewa tayi ta isa kofan ta bude, Shuraim ne tsaye bakin kofar, da mamaki tace “Shuraim….
come in” shigowa parlon yayi, Mami ta koma ta xauna, ya kulle kofar ya karasa shi ma ya xauna yace “Ina yini?” Da
murmushi tace “Lafiya lau, baka koma Zarian ba….” Yace “Ban tafi ba” tace “Ohk sae yaushe?” Yace “Next week in
sha Allah” tace “Toh Allah ya kai mu” yace “Ameen” Mami tace “Ya mutanen gidan” daga kai yyi ya kalleta yace
“Alhmdllh, but why did you leave Mami” Tace “Nothing Shuraim, I only need rest and enough privacy” kallonta
kawai yake yi bai ce komai ba, can dai yace “Wani abun ya faru ne?” Mami ta kallesa tace “Aa bbu wani abinda ya
faru Shuraim…” Ya girgixa kai yace “Idan ma wani abun ya faru kiyi hakuri” D’an murmushi tayi tace “No bbu
abinda ya faru, let me get you something to eat” Yace “Alhmdllh, will be on my way now” tace “Toh bari in kawo
maka ruwa” fridge ta tafi ta dauko masa drink da goran ruwa daya da cup, ta ajiye masa, ya dau bottle water din ya
mike yace “Xan wuce” Mami tace “So soon, toh nagode, Allah ya kiyaye hanya….” ya amsa da “Ameeen” ya nufi
kofa ya fita. Da sallama kaka ta shigo gidan rike da katon handbag dinta, Khadijah da Rabi’ah ne parlon sanye da
school uniform suna yin breakfast, Mumy kuma na kitchen da talatu sai fada take tana tsine ma Talatu ta cika man
gyada a suyan kwai, Rabi’ah da Khadijah suka yi ma Kaka sannu da xuwa suka gaisheta, Kaka da ke ta kallon
kitchen tace “Ita kuma wancan ita da waye kamar karya da sassafen nan, tun bakin get nake jin muryar ta” daga
Rabi’ah har Khadijah bbu wanda yace mata komai sai shayinsu suke sha, Kaka ta tabe tace “Wajen Rakiya na xo
kafin ta fita, yau sati daya tun da muka kai wannan yarinya Deedayah makaranta ban ganta ba, ita ma lalacewa tayi
taki xuwa gaisheni ko ko?” Mumy ta leko kitchen jin kamar muryar kaka, wani shegen kallo ta shiga yi mata suka
hada ido, da sauri Mumy ta sake fuska da fara’a tace “Lahh kamar kaka, wata sabon gani, sannu da xuwa kaka….”
Kaka tace “Ina ruwana da sannu da xuwan ki Maryam, wajen Rakiya na xo ba gun wani gantalalle ba a gidan nan….”
Mumy ta karasa fitowa kitchen din tace “Ohh wai Rahinah? Ai yau kwana takwas bata gidan nan kaka” Kaka ta xaro
ido tace “Ina ta je?” Mumy tayi fuskar tausayi ta nemi waje ta xauna tace “Tohh, ni dai ban san me ke faruwa ba,
amma lahadin da ta gabata ba na jiya ba, naji suna ta tashin hankali da Barrister wai sai ya bata takardan ta, ta dai
daga masa hankali sosai, kinsan Barrister ba me magana bane sannan shi baya son duk wani abun tashin hankali,
matar nan sai da ta san yanda tayi ta kure sa, xagi kam bbu wanda bai sha ba, daga karshe dai na shiga tsakanin su
ina ta bakin kokarina na sasanci amma abun ya ci tura….” Kaka da ta gwalo gaba daya idonta tana kallon Mumy tace
“Sai aka yi uban ya??” Mumy tayi kasa da murya a hankali tace “Daga karshe dai sai da aka rabun” Kaka ta saki
wani rikitaccen salati ta nemi kasan tiles ta xauna tace “Ya saketa?? Innalillahi wa Inna ilaihi raji’un” Mumy ta sauke
ajiyar xuciya tace “Wllh kuwa, yau kwananta takwas rabonta da gidan nan duk ta kwashe komai nata” kaka ta kuma sakin salati, sai kuma ta fashe da kuka tace “Yanxu ta6arewar Amadu ya kai haka nake xaune ban nemi taimakon
Allah ba?? Ashe budirinsa na rashin mutunci kawai yake yi ba kama kafar yaro, yau fa kwanansa takwas bai taka ya
je inda nake ba, har wayar ma ya ki yi min yace min ci kanki…” Mumy ta sauke wani ajiyar xuciya tace “Mu ma nan
duk hakuri muke da shi, fadan yanxu daban na anjima daban… Da yake ni na saba da halinsa shekara talatin da uku
ba wasa ba gashi har yau ai ba a ji kan mu ba” Kaka ta share idonta tace “Ina Amadun yake yanxu?” Mumy ta saci
kallon hanyar parlon Abba dake cikin dakinsa yana bacci tace “Yau kwana biyu yace min ya tafi Abuja, yana can”
Kaka tace “Ko bayan duniya ya tafi ai xai dawo, Ina Shureen?” Mumy ta d’an 6ata fuska tace “Shi ai yana Zaria”
Jakarta ta bude ta ciro wayarta ta mika ma Khadijah tace “Nemo min Junaidu a wayan nan” Ido Mumy ta dinga yi
mata kar ta kira, ai ko Khadijah ta gama latse latsen wayar tace “Babu lambar Junaid a nan” Kaka ta fixge wayar
tace “Dakikiya kawai, ana ta dai asaran kudin makaranta a banxa” Daga haka ta nufi kofa kamar xata tashi sama,
Mumy ta bi ta da harara har ta fita parlon sannan ta tabe baki tana tafe hannu. Mai adaidaita kaka ta tsayar a titi tace
“Kai yaro kayi boko?” Yace “Nayi mama” Kaka tace “Toh ka shiga wayar nan ka nemo min wata lamba, Junaidu
xaka ga an rubuta ka kira min shi” Bayan wani lkci ya mika ma kaka wayar yace “Yana yi” kaka ta amsa tace
“Yauwa” ta kai wayar kunne, sai da ya kusa katsewa Junaid ya daga, Kaka tace “Junaidu kana ina yanxu?” Junaid ya
mike xaune daga kwancen da yake yana bacci yace “Ina kwana kaka” Tace “Lafiya lau, a ina xan sameka?” Yace
“Ina gida” tace “Ina ne gidan?” Rasa abinda xai ce mata yayi baya son cewa nan gidansu cos he knows Mami won’t
take it likely with him, yace “Gidanmu a Abuja” Kaka ta saki salati a gigice tace “Har ita Rakiyar?” Yace “Ehh”
Kuka ta sakar masa tace “Toh yanxu ni ya xa ayi da ni ina son ganinta, ka rufa min asiri ka kai mata wayar yanxu
inyi mata magana” Yace “Toh” Tace “Toh Ina jira don Allah” katse wayar yayi, tana kallon Mai adaidaitan dake
tunanin shiga xata yi su wuce, tayi shigewarta napep din tace “Sanyi ya dameni, ka jira in gama wayata a tsanake sai
kayi wucewar ka Allah yayi maka albarka” juyowa yyi da sauri yana kallonta, ta rafka uban tagumi tace “D’a na ne
yyi ta’asa ya saki matar arxiki matar kirki bani da labari” Junaid na kwankwasa kofar bedroom din Mami tayi masa
izinin shigowa, Vid call take yi da Second daughter dinta dake aure Abuja, hannu junaid ya daga ma kanwar tasa
dake masa murmushi ganinsa, ya tafi gefen makeken gadon dakin ya xauna, Mami ta juya tana kallonsa tace “Ya aka
yi?” Yace “Aa ki gama” Jin abinda yace kanwarsa Deenar tace “Mami we will talk later a ji da Yaya” Mami tace
“Alright” daga haka ta katse kiran ta juya tana kallon Junaid tace “Har ka tashi?” Yace “Eh na tashi, Ina kwana” tace
“Lafiya lau” Yace “Mami yanxu kaka ta kirani” Mami tace “Ohk ya aka yi?” Yyi kasa da murya yace “She said she
wants to speak with you” Mami ta d’an yi shiru kafin tace “Ohk kirata” Dialing number xai yi sai ga kiran kaka ya
mike ya kai ma Mami bayan yyi picking, Mami ta kai kunne hade da sallama, kaka ta fashe da kuka tace “Yanxu
Rakiya ashe abinda ke faruwa kenan sbda ba ni na haifeki ba kika ki gaya min, shi Amadun ne yyi maki haka don ya
sameki a banxa?” Mami ta d’an yi murmushi tace “Aa kaka kiyi hakuri, ba wani abu….” Kaka ta dakatar da ita tace
“Ke dakata ba ruwana da kame kamen ki, kina ina yanxu?” Mami tace “Ina gidana” Kaka tace “A ina?” Mami tace
“Unguwar Dosa” Kaka tace “Ahhh lalacewa ta same Junaidu kenan, da girmata xai gilla min karya? To ai kuma ya
xama abun tsoro in haka ne, dama bakin ciki yake da sanin ki da nayi ban sani ba, to aniyarsa ta bi sa…” Murmushi
kawai Mami take, Junaid ya xaro ido yana sauraron kaka don muryarta xaki xakwai a wayar, Kaka tace “Ga d’an
sahu nan kiyi masa kwatance ya kawo ni yanxun nan” daga haka ta mika ma Me adaidaitan waya Mami ta basa
address din anguwar yace ya gane ya katse wayar ya mika ma kaka, kaka ta jefa jaka murya can kasa tace “Naira
hamsin ai xai kai mu ko kuma arba’in” Mami ce ta fito bakin gate bayan me adaidaitan ya kira yace suna layin,
Junaid dama bedroom dinsa ya shige ya kulle, Mami tayi murmushi bayan adaidaitan ya tsaya kaka ta sakko tace
“Sannu da xuwa kaka” Kaka na bincika jakarta ta ciro naira hamsin tace “Yauwa Rakiya” Mika ma me adaidaitan
hamsin din tayi, yyi kasake yana kallonta, Mami da dama ta fito da kudi ta mika masa dubu dayan hannunta tace
“Mun gode malam….” Ya amsa kaka tace “Ga dai canji a hannuna kuma kya basa uban kudin nan a ina xai samo
canji dari tara da hamsin Rakiya” Mami tace “Mu je ciki don Allah kaka, ai gidan da nisa” Godiya me adaidaita yayi
ma Mami ya ja adaidaitansa, kaka ta bi sa da cewa barawo a fusace, Mami ta yi shigewarta ciki, Kaka ta bi bayanta
tana cewa “Duk ‘yan fashi ne a da, alqunut da ake ta jifansu da shi ya sa suka koma kabu kabun adaidaita, Banda
haka meye xa a bashi dubu daya ya falla a guje da mashin kamar barawo” Suna shigowa parlor kaka na bin ko ina da
kallo tace “Nan ne gidan naki Rakiya?” Mami tayi murmushi tace “Aa gidan Mahaifin su Junaid ne, ba nawa bane
wannan” Kaka ta marairaice ta xauna sai kuma ta fara kuka tace “Yanxu da gaske Rakiya sakin ki Amadu yayi?”
Mami kamar baxata ce komai ba sai kuma tace “Ehh haka ne” Kaka ta kuma rushewa da kuka tace “Toh Allah ya bi
maki hakkin ki, Allah ya saka maki, muna nan dake sai yayi hawaye da idonsa bbu ruwana da koma meye ya samesa,
nima yau kwana tara rabon da in sa ido a kansa bbu xuwa gaisheni bbu kirana, gashi sun yi fada kaca kaca da yayan
nasa Umaru, dama fa yana da bakin hali kawai boyewa yake yi, amma yanxu tunda anyi walkiya mun gangosa ai sai
kowa yyi ta kansa, Deedayar ma a rabasa da ita kada wataran ya da6a mata wuka kawai” Mami dai bata ce komai ba,
Kaka na kara bin parlon da kallo tace “Maa sha Allah, da gatanki kaca kaca ai ba ayi shegen namiji da xai walakanta
ki ba wllh, daga kin taimakesa kin auresa kin rike masa makauniya tsakanin ki da Allah sai cin mutunci ya biyo baya,
to wllh yyi ma kansa, Kar ki sa komai a ranki, kyakkyawar xuciyar ki baxai ta6a bari ki tagayyara ba, nima kai na da na haifesa baxan bi ta kansa ba balle ke, kuma ido xan saka masa kar yayi min rashin kunya” Mami tayi
murmushi kawai, Mai aikinta ta fito kitchen ta duka har kasa ta gaida kaka, kaka tace “Yauwa sannu” Mami tace “Ki
kawo kayan kari” Kaka tace “Dama ban ci komai ba wllh” A can daki Mami ta sa Mai aikin ta kai ma kaka breakfast.
Bayan kaka ta gama breakfast din tana ta sakace sakacen hakori don an ci nama ba kadan ba, Junaid ya shigo dakin
da sallama kansa a kasa, tabe baki kaka tayi ta rungume hannu ta kauda kai, yana murmushi ya xauna nan saman
carpet din dakin yace “Sannu da xuwa kaka” Kaka tace “Aa ba ruwana da makaryaci gaskiya, kai da ka gilla min
karya kana Abuja kuma me ya kawo ka kaduna?” Dariya yyi yace “Kaka bacci nake lkcn da kika kira ban san ma
inda nace maki nake ba” Kaka tace “Toh Allah ya kyauta, ai gani nan dai na xo kuma da kyar idan baxan yi kwana
biyu a nan ba don ya fi min alkhairi” Heedayah ce tafe tare da Farida ta dalilin kiransu da aka yi daga Admin an xo
masu visiting…. watanninsu hudu kenan a makarantar, ko sati biyu basu yi da dawowa makaranta daga hutun First
term ba, a watannin nan hudu Heedayah is one of the best student in Jss2, bbu wanda xai ce a makance ta san
abubuwa da dama na boko a rayuwarta, xuwa yanxu kam girma ya d’an fara bayyana a jikinta, kyawunta kuwa sai
gaba yake tamkar diyar larabawa, sosai Guardian mother dinta ta makaranta ke ji da ita jininsu ya hadu ba kadan ba,
Farida tayi breaking silence din tace “But it can’t be Mami or even Yaya, sbda Yaya ya kawo min textbooks dina last
week ai baxai xo ba satin nan na sani, Mami kuma is in Abuja” Heedayah ta kalleta da manyan idanuwanta tace
“Then who??” Farida tace “Toh ni ma ban sani ba” har dai suka isa admin block aka yi directing dinsu karkashin one
of the trees na cikin makarantar, tun daga nisa Heedayah ke kallonsa haka ma Farida, wayarsa yake dannawa idonsa
sanye da bakin glasses da ya haska sa sosai, baka ganin komai daga nisan sai dogon hancinsa, Farida sai kallonsa
take, lkci daya ya daga kai yana kallonsu, murmushi ya sakar masu, Heedayah ta mayar masa cikin sanyayyan
muryarta tace “Ya Sudais” Mikewa yayi still smiling at them.