HEEDAYA CHAPTER 25 BY By Khaleesat Haiydar
Tsaye suke su biyu jikin mota a bakin wani katon hotel, alamar dai wani suke jira, wanda ba shi da tsayi sosai ya
ta6a me tsayin gefensa dake waya yana sanar ma wanda suke jira a hotel din xa su wuce idan baxai fito ba, Juyowa
yyi yana kallonsa da alamar tambaya amma bai ce komai ba, Mutumin yyi kasa da murya yace “Babaa kaga wasu
fine chicks kuwa, dogaye farare…..” Tsaki yyi ya ci gaba da wayarsa ba tare da ya kalli direction din da abokin
tsayuwar nasa ke nuna masa ba, Gajeran ya kara tabosa ganin su Farida sun kusa inda suke yace “Dallah ka sallami
idanuwanka malam, just look at them, kyawawa ne fa” Dogon Mutumin dake waya a mugun fusace yace “Hey pls
ka daina nuna min ‘yan mata idan muna tare, stop that pls, I don’t have any business with ladies, ba su ke gabana ba,
just planning on how to get….” Dai dai nan su Farida suka iso inda suke tsaye, Wanda hakan yasa Mutumin bai
karasa abinda xai fada ba ya makale a bakinsa ya bi Heedayah da kallo ko kiftawa babu, gajeran kusa da shi ya
kyalkyale da wani shegen dariya yace “Ya dai Genius? Ya da wnn kallon??” Mutumin ya kifta ido ya sake bin
Heedayah da kallo, bai san lkcn da ya bi bayansu ba da sauri, Guntun Mutumin sae dariya yake har da kyakyatawa,
can kuma ya dakatar da dariyan yyi shiru ya bi abokin nasa da kallo, coz like seriously bai ta6a ganin Genius ya kula
mace ba, komin komin kyanta kuwa, and it’s not as if basa haduwa da kyawawan mata wanda ma suka fi wa ennan
da suka wuce ynxu, ga dai tsadaddun yan matan Abuja da kullum suke gani iri iri don sun fi harkarsu a can… Tsaye
yyi gabansu ya cire bakin glasses din idonsa yana kallon Heedayah, Heedayah suka kalli juna da Farida, duk sai
suka gansu wasu marasu tsayi a kusa da shi, da mamaki Farida tace “Meye haka malam??” Ya cire p cap din kansa
yana kallonsu da dara daran idonsa yyi kasa da murya yace “I’m Sorry” kallonsa kawai Heedayah ke yi almost not
blinking, Farida ta wani daure fuska ta kama hannun Heedayah xa su bar wajen yace “Amm Pls… Can… can I drop
you both…. home” Bluntly Farida tace “Capital NO, Tafiyar ta fi mana, shi sa ma ka ganmu da kafafuwan mu, isn’t
not as if ba mu da kudin motar, you need not to drop us home, thanks for the solidarity” slowly yace “But I’m sorry
Madam, ba da ke nake ba” Farida ta ja wani tsaki ta ja Heedayah suka bar wajen, bin ta kawai Heedayah ke yi sai
kuma ta waigo tana kallon Mutumin da ya bi su da ido, karasowa gajeran Mutumin yyi gun abokin nasa with much
surprise yace “But this is odd Genuis, tun da muke da kai ban ta6a ganin ka tare mace ba sai yau, don hka ko sun ki
ko sun so wllh sae sun saurare ka, ka kyaleni da su, idan Maska ya fito ku tafi xan same ku a joint….” yana fadin
haka ya bar sa gun a tsaye ya bi bayan su Heedayah da suka yi nisa sbda saurin da Farida ke yi, ita dai Heedayah bin
ta kawai take, adaidaita farida ta tsayar masu don ta fasa trekking din, gajeran Mutumin da ya bi su ya tsayar da
wani napep din yace “Ka bi min adaidaitan gabanka, kannina na ciki ina son sanin inda xa su je” Farida ta hade rai
cikin napep din bayan sun fara tafiya tace “Wai meye naga mood din ki haka Heedayah?” Heedayah ta kalleta, a
hankali tace “His voice sounds familiar” Farida ta buda ido sosai tace “Da gaske?” Heedayah ta gyada mata kai a
hankali, Farida tace “Ikon Allah, then where did you know him??” Heedayah tace “I am still thinking” Farida ta
marairaice tace “Toh ae da kin gaya min tun a can sai mu kulasa mu ji waye, to kin yi shiru kawai, kuma tsayawa da
yyi gabanmu ai rainin hankali ne tunda mu ba gantalallu bane shi sa nayi masa haka” Heedayah bata kuma cewa
komai ba har suka isa gida wajen sha biyu da rabi, Farida ta sauka ta ba Mai adaidaitan kudi, Heedayah ma ta sauka,
Murmushi Mutumin dake cikin napep din nesa da su yyi yana kallonsu har suka shiga gidan da yake tunanin nasu ne
sannan yace ma Mai adaidaitan su wuce. Babu kowa parlor Farida ta kai kayan da suka siyo kitchen suka wuce sama
dakin Mami da Heedayah, Mami tace “Kuna fita su Jamila suka xo” Farida tace “Wacce Jamila?” Mami tace “Ke
baxa ki wani sansu ba amma ita Heedayah ta san su, yaran Baffansu Rabi’ah ne” Heedayah tace “Ayya, ita kadai ta
xo?” Mami tace “Aa su uku suka xo, sun kawo IV” Heedayah tace “Waye xai yi aure?” Mami tace “Kannin Sudais
biyu” Heedayah tace “Ohk su Aunty Safiya” cike da murna Farida tace “Dama kwana biyu ban je biki ba wllh,
yaushe ne bikin Mami?” Mami ta galla mata wani kallo tace “To Amara” dariya Farida tayi tace “Pls Mami saura
kwana nawa?” Mami tace “Saura 10 days” Heedayah tace “Allah ya kai mu” Mami tace “Ameen, xuwa gobe sai ku
shiga kasuwa ku siyi anko, na bata number Farida xata turo mata sample din ankon ta WhatsApp” Farida tace “Toh shkkn Mami” Heedayah suka fito da Farida xuwa dakinsu, har sannan muryar Mutumin daxu ke dawo mata a kai, ita
dai ta san ta ta6a jin muryar nan, ta nemi gefen gado still thinking hard, tun da tayi regaining sight dinta wani lkcn
tuno abu ke d’an bata wahala, which is very unusual, Amma idan ta damu brain dinta ta kan tuno kuma, Farida dake
kallonta tace “Ya aka yi Heedayah?” Heedayah ta juyo tayi murmushi tace “Nothing wanka xanyi” daga haka ta
mike ta fara cire kayanta xata shiga Bathroom. Da daddare Heedayah na xaune dinning da Farida suna cin abinci
Mami na dakinta, Heedayah tayi kasa da murya tace “Wai ina Mami ta ajiye chocolate dinmu da tayi seizing when
we came back from schl Faree?” Farida tace “I don’t know, kila ma ta xubar a shara, that’s a simple act for her”
Heedayah ta marairaice bata ce komai ba, ranan da xa su dawo daga makaranta suka shiga supermarket din cikin
makarantar suka siya chocolates har na dubu uku, mistakenly Mami ta gani ta dauke, Heedayah tace “I am craving
for it wllh” Farida tace “May be it’s because kina period, kuma idan kika sha cikin ki ciwo xai fara maki ba ruwana”
Heedayah tace “Just one fa” Farida tace “Toh ki dau wayata ki kira Yaya ki gaya masa ya siya maki idan yana
dawowa” Heedayah ta turo baki don hide and seek take yi da shi tun incident din daren jiya, Heedayah tace “Kafin a
karasa bakin titi ba akwai wani karamin supermarket ba, xan je in siyo a can” Farida tace “Then u will have to sneak
out kenan, don Mami won’t let you, and ni baxan fita in rakaki ba ynxu na cire kaya” Heedayah ta mike tace “Sure”
Daki ta tafi ta dauko dubu daya cikin ragowar kudin da suka dawo da shi daga makaranta ta sa Hijab dinta ta fita
gidan, bbu kowa layin nasu ta isa shagon a kusa da bakin hanya, ta xabi chocolate din da take so ya kama dari biyar
ta basa dubu dayan, yana bata canji wata mota ta shigo layin, kauda ka
i tayi sbda haska ta da fitilar motar ke yi, ana
bata canjinta ta fara wucewa da sauri, tsayawa taga motar yyi bayan ya wuceta a can gaba, ita dai tafiyarta kawai
take har ta isa dai dai motar ta ga an bude kofar motar, sosai gabanta ya fadi, Mutumin daxu ta gani ya sauko motar
yana kallonta, from all indications ya rasa abinda xai ce, coz he looks speechless, ta wucesa da sauri, bin bayanta yyi
walking fast har ya jera da ita yyi kasa da murya yace “Good evening” Tsaya tayi ta juyo ta hade rai tace “Why are
you following me?” Ya fara kalle kalle, looking for what to say, a lkci daya yace “Naga kamar na san ki ne” Shiru
tayi tana kallonsa, can tace “A ina ka san ni?” Ya sauke idonsa yace “I don’t really know, but I know na san ki” Ta
dauke kanta, kamar baxata ce komai ba, can tace “And I also know ur voice” Ya buda ido yace “Really?” Tace
“Yess” yace “May be a mafarki muka san juna… ” Ta hade rai tace “Ba a mafarki bane” Xai yi magana wani mota ya
shigo layin, xaro ido tayi ta koma bayansa da sauri tace “Na shiga uku yayanmu ne, kar ya gan ni” Kafin yace komai
ta durkusa kasa gabanta na faduwa, Ya bi motar da ya wucesu da ido yana kallon guy din dake ciki, sai da motar ya
shiga compound bayan mai gadi ya bude gate sannan Heedayah ta mike har lkcn gabanta na faduwa, ya juya yana
kallonta kafin yace komai tayi saurin cewa “Good night” ta fara tafiya, yace “Wait…” Ta juyo ya nufeta yace “Ki
bani number ki, I will figure out where we know each other sai in gaya maki” Ta 6ata fuska tace “Don’t worry about
that, may be illusion ne kawai amma bamu san juna ba, not anywhere” A hankali yace “Billah na san ki, na ta6a
ganin ki, har mun ta6a magana….” tayi shiru tana kallonsa ko kiftawa bbu, yace “Bani lambar ki” ta girgixa kai tace
“Ba ni da waya” Hannu ya sa a aljihunsa ya ciro tsadadden wayarsa ya mika mata yace “I will call you…” Tace
“Noo….” Yace “Amsa nace, I will call and tell you where I know you” K’in amsan wayar tayi ya kama hannunta,
sosai gabanta ya fadi jin hannunsa a nata, ya saka wayarsa a ciki sannan a hankali yace “I am Khaleel…” Tayi shiru
tana kallonsa, yace “And you?” Ta sauke idonta kasa tace “Heedayah” tana fadin haka ta juya ta fara tafiya ya bi ta
da ido har ta isa gate din gida ta shiga. Heedayah ta fi minti biyar tsaye bakin kofa tana tsoron shiga parlon kar a ce
Mami ta sakko downstairs, a hankali ta bude kofar daga karshe ta shiga, Farida ce kadai parlon, Farida tayi mata
alamar ta wuce sama da sauri, hanyar stairs ta nufa taji ance “Where are you coming from?” Farida ta saci kallon
direction din kitchen taga junaid ya fito, Heedayah da gabanta ya shiga faduwa sbda wayar dake hannunta a cikin
hijab tace “Naje siyan abu ne” karasowa parlon yyi yace “Me kika je siya?” Ganin ya nufota ta wuce sama da gudu
ta shige dakinsu ta sa makulli, Farida dai sai kallon tv take attentively kamar bata san suna yi ba, Junaid ya juya ya
hade rai yana kallonta yace “Me taje siyowa?” Farida tace “Ba wani abu bane Yaya, chocolate ta je siyowa a shago
bata son Mami ta sani kuma” Heedayah na shiga dakinsu ta dinga kallon hoton dake jikin screen din waya kirar
Samsung da ya bata, shine jikin screen din wayar, hoton yyi kyau ba kadan ba ya jingina da pillar din wani ubansun
gida ga motoci ya kusa bakwai a katon compound din, bata samu access din shiga wayar ba don a lock yake,
knocking aka yi ta juya da sauri ta tafi gun handbag dinta ta saka wayar ciki sannan tace “Waye?” Farida tace “It’s
me, open” Heedayah ta bude kofar Farida ta shigo ta sake sa makulli, Farida tace “Me yasa kika dade, ina ta tsoron
kar Mami ta sakko taga bakya nan” Heedayah tace “I met people buying stuffs there” Dai dai ta raba chocolate din ta
ba Farida rabi, ta dau rabi… Farida ta ajiye nata a jaka sannan ta kwanta tana danna wayarta, sai kusan sha biyu
Farida tayi bacci, Heedayah dai na ta kwance tayi kamar me bacci amma idonta biyu, can da ta ji alamar Farida tayi
bacci ta sauka daga kan gadon ta tafi jakarta ta bude a hankali ta dau wayar dake ciki, miss call ta gani guda biyu,
tana ta kallon wayar sai ga shi kira ya kara shigowa ta ga an sa “KH” kallon Farida tayi sannan ta shige bathroom ta
rufe ta daga kiran, sallama yyi daga daya side din, sai da ya kara yin sallama sannan ta amsa, yace “Baki yi bacci
ba?” Tace “Ehh, and where did you say u know me?” Ya d’an yi shiru sannan yace “I can’t remember but I will
remember soon, ya kike?” Tace “Ohk then, anytime you remember we will talk, sai da safe” Da sauri yace “Noo
o wait Heedayah…” tace “But I can speak comfortable with a stranger” yyi kasa da murya yace “But I am not a
stranger” Tace “Xan kwanta ne” ya d’an yi shiru sannan yace “Toh sai da safe, I will spend the night thinking of inda
na ta6a sanin ki, sleep tight” Bata ce komai ba ya katse kiran, ta dinga kallon screen din sannan ta juya a hankali ta
fita ta saka wayar a jaka sannan tayi addu’ar bacci ta kwanta. Washegari Saturday da safe Farida suka gama shirin
tafiya islamiyya kamar yanda dai suke yi idan suna hutu, Sunan tsaye jikin mota suna jiran fitowar Driver Junaid ya
shigo gidan daga gym, duk suka gaishesa ya amsa, Heedayah dai ta dauke kai don bata son ma su hada ido har ya
wuce, driver na isowa suka shiga motar suka bar gidan. Heedayah na aji taji vibration din waya a jakarta ta kalli
Farida dake xaune gabanta sannan ta mike ta saka jakar a hijab ta nemi ixinin malamin su ta fita, Farida ta girgixa
kai don a tunaninta xuwa xata yi ta sake duba ko tayi stain tunda aikinta kenan tun da suka shigo, can bayan wani
building Heedayah ta tsaya ta fiddo wayar ta daga, Khaleel yace “Good morning” tace “Ina kwana?” Yace “Lafiya
lau, how are you?” Tace “Fine, why did you call?” Shiru ta ji yyi, sai kuma yace “To check on you” tace “Toh bana
so, stop it… I want your call to be meaningful, like… you telling me where you know me, how and when” Yace “Sure
duk xan gaya maki amma idan mun hadu…. Where will that be? I mean wajen da xa mu hadu?” Heedayah ta wani
hade rai kamar yana ganinta tace “A wani dalilin xan hadu da kai, besides meye ma sanin ka xai kareni da, nothing
of course…” Cikin cool voice yace “Do not judge that, kilan ynxu haka akwai abinda kike buri a rayuwarki, they are
wishes you are wishing…. I might make those wishes come true, you never can tell” shiru tayi tana sauraron sa, yace
“Anyway, naji kamar baki gida, sai later” Bai jira cewarta ba ya katse wayar, Heedayah ta jingina da bango tana
naxarin maganganunsa, wishes she is wishing? Sure she have wish, and her biggest wish in life now is to meet with
her Mother, a da hakan baya damunta ko kadan don har mantawa take ba Mami da Abba suka haifeta ba, amma daga
farkon shekaran nan sai take yawan jin abun a ranta, ta kara kallon wayar hannunta sannan ta saka a jaka a hankali ta
bar wajen duk jikinta a sanyaye, but how did he know she have wishes a mind dinta…. Karfe uku saura Farida da
Heedayah suka bar gida xuwa kasuwa don siyo ankon Safiya da Nafisa, kusan dubu sittin suka kashe a kasuwan don
lace ne me kyau sosai da atamfa kala biyu, Farida tace “Kawai mu tafi plazan da nake bada dinki mu bada kafin mu
wuce gida” hakan suka yi sai da suka fara kai dinkin sannan suka fito suka samu adaidaita xuwa gida don Mami tace
baxasu je da driver ba su basa wahala ya rasa gun ajiye mota a kasuwa, throughout ranan Heedayah na ta jiran kiran
Khaleel amma bai kira ba har washegari, gashi wayar da lock balle tace ko xata kirasa,
har bayan kwana biyu bai
kirata ba, ta shiga damuwar da ta rasa dalilinsa sai dai ko da wasa bata yrda kowa ya gane halin da take ciki ba, bini
bini xata duba wayar a jaka amma bbu miss call, ranan talata ta dawo islamiyya tana wanke uniform dinsu da na
Farida da yamma a bakin tap a waje aka bude gate, juyawa tayi Sudais ya shigo gidan tare da Shuraim, ta dauke
kanta ta ci gaba da wankin da take, Sudais ya karaso Inda take ba tare da ta dago ba tace “Good evening” yana
murmushi yace “Evening cutie ya kike?” Tace “Lafiya lau” yace “Ya hutu?” Tace “Alhmdllh” satan kallon Shuraim
tayi suka hada ido don kallonta yake, tayi saurin sunkuyar da kanta tace “Ina yini” Can ciki taji yace “Lafiya” Sudais
yace “Mami na ciki kuwa?” Heedayah tace “Aa bata dawo ba” yace “Ohh really” gyada masa kai tayi, yace “Toh
shkkn anjima da daddare xa mu dawo” Heedayah tace “Toh Allah ya kai mu” yace “Farida fa?” Tace “Tana kitchen
da Sis Zainab” Sudais yace “Alright sai yaushe xaku taho can gida?” Heedayah tace “Sai Mami tace mu tafi” Yace
“Toh shkkn, let get going” daga haka ya bi bayan Shuraim da ya fara tafiya, ganin tafiyar da Shuraim ke yi kamar
bai son yi Sudais yyi overtaking dinsa nan ko bai san intentionally yyi hakan ba, Shuraim ya d’an juya bayan Sudais
ya shiga gabansa suka hada ido da Heedayah da ta bi su da kallo, da sauri ta dauke idonta ta ci gaba da wankinta shi
kuma ya fice gate din as if ana koransa. Shirye shiryen biki kawai ake a gidan Baffa ba kama kafar yaro, ana biki
saura kwana biyu aka kawo lefe hakan yasa Mami taje gidan tare da Farida da Heedayah shima sbda kiran da kaka
ke tayi mata don bata yi niyyar xuwa ba sai ranan bikin, Junaid ne ya kai su gidan bikin a motarsa, yawanci dama shi
ba kullum xaka samesa a gida ba may be twice in a week ko thrice kadai yake kwana a gida yafi tsayawa gidan
Baffan sa, yana parking Mami ta sauka motar tace “Sai yaushe?” Yana magana yana kallon Heedayah ta madubi
yace “Gobe in sha Allah” Mami tace “Allah ya kai mu” daga haka ta nufi cikin gidan, Farida ta sauka motar haka
Heedayah, Farida tace “Sae anjima Yaya” ya gyada mata kai, Heedayah tace “Sae anjima” alama yyi mata da ta xo
da hannunsa, ta 6ata fuska ta kalli gate din gidan sae kuma ta karasa ta tsaya tana kallonsa yace “Me yasa kika sa
mayafi Heedayah? Baya maki kyau” a hankali tace “Mami ce tace in sa Yaya” yyi shiru yana kallonta, can yace
“Alright” ta daga masa hannu ta nufi cikin gidan. Yan uwa da abokan arxiki har sun fara cika gidan biki ana ta shiri,
Mami ta shiga parlon da sallama girls dinta da suka yi anko na atamfa me tsada na biye da ita a baya, sosai kayan ya
amshi Heedayah da ta sakale gyalen gefen shoulder dinta, tayi wani sanyayyan kyau duk da bata yi kwalliya ba sai
eye pencil da ta saka idonta da chappet da ta goga lips dinta, Mumy ce xaune parlor da kawarta Hajiya Sadiya, sai
Hajiya Amina mahaifiyar Sudais da step mother dinsa, sun dai kusa goma sha biyu a parlon duk dai ana tsara yanda
abubuwa xa su kasance, masu tafiya kasuwa na shirin tafiya, Tunda Mami ta shigo Mumy da ta yi ture ka ga tsiya ga
daham dinta a wuya ke kallonta, farin ciki ba na wasa ba Mumy tayi don ta wani hakikance kan kujera sai kace
sarauniya, Lkci daya murnan Mumy ya koma ciki ido hudu da tayi da Heedayah dake bayan Mumy, Heedayah dai ta
xama cikakkiyar budurwa don idan ka ganta ma baxa kace she is just 16 ba, Doguwa ce fara sosai kuma siririyahancinta is worth noticing ko da kuwa daga nisa take, ga karamin bakinta me xagaye da jan labbe, gaba daya ta
sauya daga lkcn da take 13 don idan ba saninta kayi sosai ba baxa kace ita ba ce, Mumy ta hadiye abu da kyar ta
kalli Hajiya Sadiya dake kallon Heedayah ita ma ba ko kiftawa, Heedayah da Farida suka durkusa suka gaida
Mutanen parlon, ita Mum din Sudais dama ko ganeta bata yi ba Hajiya Hauwa ce kadai ta ganeta don sai kallonta
take tana murmushi, Mami tayi hanyar dakin kaka don ta gama gaisawa da occupant din parlon, mikewa Heedayah
da Farida suka yi suka bi bayan Mamin tasu, Mumy tayi kasa da ido ta bi Heedayah da kallo har suka shiga dakin
kaka, da mayafinta ta share d’an guntun xufan da taji ya keto mata.