HEEDAYA CHAPTER 28 BY By Khaleesat Haiydar
Kallon Zainab Heedayah tayi, Zainab tace “Ko shi ne?” Heedayah ta dinga kallon motar, can tace “Aa ba da motar
nan nake ganinsa ba” Zainab tace “To ki je ki duba” Karasawa Heedayah tayi gun motar, taga an sauke Windshield
din motar, sosai gabanta ya fadi bayan sun yi ido hudu da shi, sanye yake da wandon sojoji da polon su, ya dauke kai
daga kallonta ya kara haska ma Zainab fitila, Kamar ana tilasta Heedayah tayi kasa da murya tace “Ina yini” bata jira
ya amsa ba ta bar wajen tana turo baki, Zainab sai kallonta take har ta iso, Heedayah tace “Ke ake kira” Zainab ta
xaro ido tace “Ni kuma? Waye ke kirana?” Heedayah tace “Oho ki je ki gani” karasawa Zainab tayi tana d’ari d’ari, Shuraim ya sakar mata murmushi, ta buda ido sosai ganinsa tace “Lahh ashe ya Shuraim ne, kai ma dinner din ka
xo?” Ya hade rai yace “Dinner kuma? No, not at all” tace “To me kaxo yi nan?” Yace “Yanxu xan wuce wajen aiki,
na ajiye wasu ne” Zainab tace “Ohk Ina yini Ya Shuraim” yace “Lafiya lau, me yasa ita kadai ta xo gun motar sbda
taga anyi flash din fitila maimakon ku biyu?” Zainab tace “Ohh ni ce nace taje ta ga wa ke haska mu” Yace “Wato ita
ce fitsararriya, da wani ne haka xata xo ta tsaya masa a mota tana kallonsa ko?” Zainab tace “Aa fa Yaya, ni nayi
insisting taje ta ga waye da gaske” kallonta ya tsaya yi, can yace “Then… Don’t do that again, Ina Farida?” Zainab
tace “Sun shiga ciki” yace “Ke ina pass din naku?” Zainab tace “Gashi a jaka, nata na wajenta” yace “Ohk, till after
the dinner kar ku fito waje” Zainab tace “Dama ai baxa mu fito ba Yaya” Yace “Good” tace “Yanxu xaka wuce?”
Yace “Ehh” tace “Toh Allah ya kiyaye” Heedayah dai na can tsaye nesa da su sai turo baki tayi, can kuma sai ta tabe
bakin, wani abu kamar kwandala taga ya gangaro inda take, ta dinga kallon d’an abun me shige da ring da ya kwanta
a gabanta bayan ya gama bouncing, Daga kai tayi ta kalli direction din da abun ya taho, suka yi ido hudu da Khaleel
jikin wata farar mota me ubansun kyau, tuni ya dauke kai yana danna wayarsa ya kasance side view dinsa kawai
take iya gani, parking space din event center din ne, ya d’an saci kallonta bayan sun hada ido ya bar wajen ya koma
can bayan wani mota ya tsaya, don motoci ne iri iri a wajen, Zainab taga Shuraim ya bude mota xai sauka ta matsa
da mamaki tana kallonsa, karasawa gun Heedayah ta ga yyi, ita ma Heedayah kawai ganinsa tayi kamar daga sama a
gabanta, ya duka ya dau ring din, sosai gabanta ya fadi ta fara komawa baya a tsorace, ya mike yana bin wajen da
kallo, Tuni Khaleel ya canxa wani motar ynda ko ganin alamarsa Shuraim baxai yi ba, Heedayah dai sai kallon
Shuraim take a tsorace, Zainab ta karaso kusa da su tace “Me ya faru Yaya? What’s that” Shuraim ya amshi jakar
Heedayah, ba musu ta sakar masa jakar, ya bude, pass din dake ciki guda biyu ya ciro ya yayyaga a wajen ya jefar
sannan ya nuna mata motarsa, fashewa da kuka tayi sosai, Zainab da ta xaro ido tace “Yaya why did u do that, there
is no other pass fa??? Me ya sa kayi haka yaya” Shuraim ya nuna mata hanyar shiga wajen fuska daure yace “Yi
wucewar ki ciki” ganin kallon da yake mata dama kuma sun taso suna tsoronsa fiye da yayansu Sudais kawai ta
kama hanyar shiga event center din wanda policemen ke tsaye suna amsan pass, tana yi tana waigosu, Heedayah sai
kuka take tana yarfe hannu, yayi mata wani tsawa yace “Wuce mu tafi nace” Bata masa musu ba ta nufi motar da
sauri, ta bude back seat ta shiga, ya shiga maxaunin driver ya tada motar ya fita parking space din driving with speed,
Khaleel dake jingine jikin wata mota daga nisa ya bi motar da kallo, bayan few seconds yyi wani murmushi yana
juya wristwatch din hannunsa almost whispering to himself yace “Waow… A soldier, then… either I or him” daga
haka ya koma gun motarsa ya shiga. A hankali Heedayah ke kuka a motar tana goge hawayen da ya ki tsaya mata,
Driving dinsa kawai yake yi yana yi yana duba motocin dake bin sa a baya, bayan wani lkci wayarsa ya fara ring,
dauka yyi yana duba me kiran nasa ya ga Mumy ce, ya daga wayar ya sa a handsfree, Mumy tace “Aliyu nasan sai
takwas xa ka tafi aiki don Allah ka rufa min asiri ka xo ka daukeni da su Hajiya Sadiya da Hajiya Amina ka kai mu
wajen dinner din nan, duk motocin sun tafi, tawa motar ma an tafi da ita haka na Hajiya Amina” Shuraim dake ta
sauraronta har ta kai aya yace “Ina wajen aiki ynxu” Mumy tace “Haba Shuraim, karfe takwas fa kake tafiya gashi
ynxu bakwai yyi” Yace “Ehh colleague dina dake dutyn rana xuwa yamma ya tafi gida before his time elapsed, his
wife is sick shi yasa ya nemi alfarman in xo da wuri don inyi takeover from his time” Mumy tace “Ae shkkn sae mu
nemi adaidaita amma abu bai yi ba manya kamar mu a ganmu a tricycle, shi Sudais yace baya kusa kai kuma yanxu
kana ce min ka tafi asibiti” bata jira cewarsa ba ta katse wayar ya ajiye yana ci gaba da driving dinsa, Heedayah sae
shessheka take tana ji kmr ta rusa ihu tayi kuka sosai ko xata ji dadi. Parking ta ga yyi a wani waje da akwai haske
sosai, nan da nan ta dakatar da kukan da take yi ta goge idonta da sauri, ya bude motar ya sauka snn ya bude side
dinta, kallonsa take a tsorace, ya hade girar sama da ta kasa yace “Sakko” Ba musu ta sakko da sauri, yace “Jiya
waye na gani kofar gida kika min karya xa ki je ki siyi ruwa” Ta xaro ido tace “Ya Shureen ni ban san sa ba, na fito
ne yana wucewa a mota sai naga ya tsaya yana kallona, I am telling you the truth ban san sa ba, believe me plsss….”
Ta fashe da kuka amma hawaye ya ki sakkowa tana kallonsa a tsorace, yace “Ohk da ya tsaya kallon ki sai ke ma
kika tsaya kallonsa a gate din ko?” Tace “Aa tsoro na ji shine ban fita ba na tsaya bakin gate din in ga ko xai wuce
naga bai wuce ba” Shuraim yace “Toh yau kuma meye wnn aka jefo gaban ki ya fadi?” Ta daga hannu sama da sauri
tace “Ya Shureen nima kawai gani nayi kila daga sama abun ya fado, ban san meye shi ba wllh, wllh I don’t know
what is that, believe me plsss” Kamar xata yi kuka ta kare maganan tana kallonsa da manyan idanuwanta, yace
“Good, maxa su tsaya suna kallonki kema sai ki tsaya kina kallonsu ko?? to daga yau anytime you are going out you
just have to wear a nikab, a must” Ta xaro ido tana kallonsa amma bata ce komai ba, strictly yace “Kin ji abinda
nace?” A hankali tace “Ni ai bani da Nikab ya Shureen” yace “Yess xan siyo maki, and if you should dare tell anyone
that ni nace ki fara sa Nikab sai na baki mamaki…” Kamar xata yi kuka tace “Ban iya sa wa ba ai” yace “Ehh idan na
kawo maki sai ki koya” Bata kuma ce masa komai ba, ya bude mata motar, ta marairaice ta shiga ya kulle, murguda
baki
tayi a ranta tace ai baxan sa ba sai dai kai ka saka, ya shiga maxaunin driver ya tada motar suka bar wajen,
ganin hanyar gidan Mami ya nufa da ita taji kamar tayi ta ihu tana birgima a motar, nan da nan hawaye me shegen
xafi ya dinga sakko mata taji kamar ta shakosa, Wayarsa yayi dialing snn ya kai kunne, ba a dau lkci ba yyi sallama
yace “Ina yini Mami” Daga daya bangaren Mami ta amsa masa, yace “Kina gida ne?” Mami tace “Ehh ina gida Shuraim, ya aka yi?” Yace “Ohk Ina shigowa yanxu” Tace “Toh sai ka xo” daga haka ya katse wayar, dai dai kofar
gida yyi parking ya sauka motar, Heedayah ta share hawayen da ya ki tsaya mata ya fito daga cikin motar, bin
bayansa tayi don har ya shiga gate bayan sun gaisa da Mai gadi, Da sallama Shuraim ya shiga parlon Mami, Mami ta
sakko downstairs ganinsa tace “Aa, daga ina haka Shuraim, welcome, baka je dinner din ba kenan” kafin yace komai
Heedayah ta shigo, da mamaki Mami ke kallonta tace “Wancan fa? Daga ina kike” Shuraim yace “Tace cikinta na
ciwo shine na dawo da ita gida” Mami tace “Ikon Allah, tun yaushe” Shuraim yace “Da rana” Heedayah dake goge
hawayen da ya ki tsaya mata ta gaida Mami a hankali snn ta wuce sama, Mami ta mike ta bi bayanta, kwance ta
sameta saman gado tana rusa kuka kamar yar yarinya, har downstairs Shuraim ke jin kukan nata, Mami ta shiga
dakin da mamaki sosai tace “Meye haka kamar ‘yar yarinya, bana son iskanci, period din ne ya dawo??” Cikin kuka
ta girgixa kai tace “Aa ba shi bane” Mami tace “Toh ya cikin yake maki?” Tace “Ya daina ynxu” Mami tace “Ya baki
magani ne?” Gyada kai kawai Heedayah tayi bata ce komai ba amma taki daina kukan, Mami tace “To ki kiyayeni
da kukan nan, tunda ke ba jaririya bace, idan bacci xa kiyi kiyi bacci” daga haka Mami ta fita dakin, Heedayah ta
tura fuskarta cikin pillow tana rera kukanta. Mami na dawowa downstairs tace “Tace ka bata magani” Yace “Ehh na
bata” Mami tace “Toh shkkn, Allah ya sauwake” Mikewa Shuraim yyi yace “Xan wuce aiki, I am almost late” Mami
tace “Toh abinci fa?” Yace “Aa am full” tace “You are always full dama, Toh Allah ya tsare” ya amsa da Ameen yana
murmushi, ya mata sallama ya fita parlon, Mami ta koma sama xuwa dakinsu Heedayah, Heedayah na jin an bude
kofa ta hadiye kukan ta rufe ido da sauri, Mami tayi xaton ta fara bacci ne ta juya ta fita. Karfe sha biyu saura
Heedayah ta koshi da kukan da take ta mike xaune, sai turo baki take ita kadai, bandaki ta shiga tayi alwala ta fito
tayi Isha, tana idarwa ta cire kayan jikinta ta dau kayan baccinta ta saka snn ta sa Hijab ta nufi kofa, a hankali ta
bude kofar ta fita, downstairs ta sauka xata tafi kitchen ta hada shayi, kwance ta ga Junaid 3 seater yana kallon
wrestling, ya mike xaune yana kallonta da mamaki yace “Heedayah” sauke idonta tayi bata ce komai ba, yace
“Yaushe kika dawo?” A hankali tace “Tun daxu” yana kallon idonta with surprise yace “What’s wrong, kukan me
kika yi?” Kafin tace komai taji muryar Mami a sama, ta juya da sauri tana kallonta, Mami tace “What are you doing
downstairs?” Cikin sanyin murya tace “Ina jin yunwa xanyi making tea” Mami tace “Go and make it ki xo ki wuce”
Kitchen din ta nufa, Mami na ta tsaye har ta fito da cup din shayi, Junaid dai bai ce ma Mamin tasa komai ba,
Heedayah ta wuce sama, Mami ta jira ta ga shigarta daki sannan ta bi ta cikin dakin, tana kallonta tace “Ya jikin?”
Cikin sanyin murya Heedayah tace “Na ji sauki” Mami tace “Toh Allah ya sauwake” Daga haka tayi mata sai da safe
ta fita ta koma dakinta, kasa ci gaba da kallon wrestling din Junaid yyi duk son sa da wrestling kuwa, ba karamin
kuka idonta ya nuna tayi ba, lkci lkci yake kallon agogo har karfe daya yyi, ya mike xaune daga kwancen da yake
saman kujera, yana ta xaunen har daya da rabi snn ya mike ya wuce sama, ya fi minti uku tsaye corridor din dakunan,
can ya nufi kofar dakinsu ya bude very careful kar yayi kara, shiga dakin yyi da yyi sanyi sbda Ac dake kunne wutan
dakin a kashe, ya rufe kofar, Heedayah na jin an bude kofa dama ba bacci take ba abun duniya ya isheta, gaba daya
ji take kaf duniya dai a ynxu bata tsani kowa ba kamar Shuraim, ta mike xaune da sauri tana kallonsa ta duhun
kamar me rada tace “Yaya” ya karasa gefen gadon ya xauna ya haska mata fitilar wayarsa mara haske yace “Kukan
me kika yi Heedayah” Ta dau pillow ta daura jikinta kamar xata yi kuka tace “Yaya Mami fa xata yi fada” Hade rai
yyi yace “Tell me what’s wrong with you” Ta hadiye abu da kyar tace “Ciwon kai nake yi shine na dawo gida” Yace
“Ciwon kai? To kin sha magani?” Ta gyada kai tace “Na sha” yace “Wa ya baki?” Tace “Mami” cikin sanyin murya
yace “Allah ya sauwake dear, but ya daina ciwon ynxu ko?” Ta gyada masa kai, yace “Shayin ya ishe ki?” Nan ma ta
gyada masa kai, gaba daya a tsorace take, yace “Why are you scared??” Ta marairaice tace “Mami… wllh xata iya
dukana” Shiru yyi yana kallonta, snn ya kamo hannunta yace “Toh xan tafi yanxu, but watarana baxa ki ce kina
tsoron Mami ba idan muna tare ai ko?” Ita dai bata ce masa komai ba ta sauke idonta kasa, mikewa yyi yace “Ki
kwanta kiyi bacci, idan kuma baki jin baccin ki tashi kiyi sllh, good night” ta gyada masa kai kawai ya juya ya nufi
kofa ta bi sa da kallo har ya fita ya kulle mata kofar, downstairs ya koma ya kwanta coz he prefer lying down there,
sai a snn kuma bacci ya daukesa. Washegari Saturday Mami bata ce Heedayah taje wani yinin biki ba, ita ma a gida
ta yini abunta sai kusan yamma ta tafi gidan bikin bayan ta tabbatar Junaid ya fita gidan, gidan ya rage daga
Heedayah sai Zainab me aikin Mami, tun da gari ya waye sai wani nukurci da miskilanci Heedayah take, Mami na
ganin mood dinta dama ta kyaleta tayi ta xama a daki ita kadai, Da Heedayah ta tuna abinda Shuraim yyi mata sai ta
fashe da kuka ita kadai tace “I hate you” da ta tuna wayar da Sudais ya amshe a hannunta shi ma sai ta fashe da kuka
kamar ‘yar yarinya. Karfe shidda saura ta sakko downstairs da dubu daya a hannunta, Zainab ce xaune parlor tana
kallo, Zainab tace “Ga abincin ki can a kitchen ba ki ci ba Heedayah” a hankali Heedayah tace “Baxan ci ba” daga
haka ta fita, ko gaida Mai gadi bata yi ba ta fita xuwa kanti ta siya chocolate. Zaune yake 4 houses away tare da mai
gadi suna hira, malt ne a hannunsa yake sha, shi ma Mai gadin malt din yake sha yana lullumshe ido kana gani dai
kasan siya masa aka yi, Mai gadin ya kara kurban malt din hannunsa, ya d’an yi gyatsa snn yace “Ai tsiyar basa
fitowa ne yan matan gidan, duk safiya dai xaka ga uwar tasu a katon motarta ta fita, Ina jin wata babban
ma’aikaciyar gwamnati ce, tana kuma da d’a wani matashi yana nan kamar balarabe, ya ma fi ka haske, to shi
gaskiya Ina jin ba kullum yake dawowa gida ba don sai in kwana biyu ban ga motarsa ba a layin nan, su kuma Yan matan sai dai ka gansu an fita da su a mota daga cikin gidan, ban san ko su nawa bane balle in san ko warcece a
ciki ma” Shiru yyi kansa a kasa yana rike da can malt dinsa yana sauraron Mai gadin, can ya dago kai yace
“Mahaifinsu fa?” Mai gadin yace “Anya, Ina jin gaskiya ya rasu ban ta6a ganin dattijjo ya fito gidan ba duk xamana
a layin nan inda gadin gidan nan” Ya gyada kai cike da gamsuwa sannan yace “Akwai Soja a gidan?” Mai gadin
yace “Aa babu wani soja a gidan, basu fi su hudu ko biyar ba a gidan, matashi kuma daya ne a gidan” Khaleel ya
gyada kai yana naxarin maganan mai gadin, d’aga kai yyi ya hangota tana tahowa da Hijab har kasa.