HEEDAYA CHAPTER 4 BY By Khaleesat Haiydar
Www.bankinhausanovels.com.ng
Sudais na tsaye compound din gidan nasu Abba ya fito rike da hannun Heedayah, Sudais ya nufe sa ya gaishesa da
ladabi, Abba yace “Lafiya Aliyu, ya weekend?” Sudais yace “Alhmdllh sir….” Yana kallon Heedayah ya kai hannu
kanta yace “How are you?” Shiru tayi bata ce komai ba, Abba yace “Talk to him Heedayah” tana rike da hannun
Abba a hankali tace “I am fine” Sudais ya mata murmushi yace “Good girl….” ya kalli Abba yace “Allah ya bayyana
iyayenta” Abba yace “Ameen My son” jin taku a bayansu Sudais ya juya, Shuraim ne ke tahowa yana tafiyar kamar
bai son yi, wani kallo Abba yyi masa ya kalli Shuraim yace “Xan wuce gida ynxu, anjima ka taho can gidan ka
sameni” Sudais yace “In sha Allah….” Daga haka Abba ya bar wajen xuwa gun motarsa tare da Heedayah, Sudais na
kallon Shuraim da ya bi Abbansa da ido yace “Kai ma baka bada goyon bayan taimakon yarinyar da Abba ke son yi
ba kenan, coz naga kallon da ya maka” Shuraim ya bude hannu yace “But…. She’s blind, ta ina xa a fara kula da ita,
is it even possible….” Sake baki Sudais yyi yana kallonsa a bit shock, can ya juya da sauri ya kalli parking space
yaga Abba is helping her Into the car, ya kara kallon Shuraim yace “Blind? How is that?? Who told you that, ban
gane ba” Shuraim ya shafa kansa yace “Yes makauniya ce…” Yana fadin haka ya juya ya koma ciki ya bar Sudais a
wajen baki bude, Sudais ya kara satan kallon motar Abba har ya fita compound din…. A hankali Abba ke driving
yana yi yana waigen Heedayah dake shan yoghurt da ya siya mata, muryar ta ya ji tace “Abba gida xa mu je ynxu
wajen Ammina?” Ya gyada mata kai kamar tana ganinsa yace “In sha Allah” wani babban eatery ya shiga yyi
parking yana kallon agogon wrist dinsa da ke nuna karfe sha biyu saura, wayarsa ya dauka yyi dialing number ya kai
kunne, bayan few seconds yace “Hope you aren’t going to keep me waiting Barrister” bin motar da ya shigo eatery
din a dai dai lkcn yyi da kallo sannan ya katse wayar, Heedayah tace “Abba mun kai gida?” Ya shafa kanta yace “A’a,
I want to see a frnd now, xa ki jirani har in dawo koh?” Ta gyada masa kai a hankali, kamo hannunta yyi yana
murmushi ganin she looks sad and insecure, kamar dai tafiya xai yi ya barta din nan, mika mata wayarsa yyi yace
“Ki rike min wayata har in dawo ynxu, kin ji?” Ta kara gyada masa kai, ya bude motar ya sauka sannan ya rufe ya
nufi entrance din eatery din, Table din dake dauke da wata mata that is in her early fifty ya nufa, kana ganinta kaga
well educated bafillatana cikin shiga ta kamala, ya ja kujera ya xauna yace “Good morning Barrister” Ta ajiye wayar
hannunta da take operating tana kallonsa ta cikin siririn glass din idonta tace “Morning, ya family, ya weekend?” ya
gyada kai yace “Alhmdllh mun gode Allah” tace “Hope ba aiki xaka hadani da shi ba kace xaka yi tafiya, coz nima
tafiyan xanyi gobe in sha Allah” yayi ‘yar dariya yace “Not at all, how are the children?” Tace “They are all alhmdllh,
ya su Rabi’ah?” yace “Lfya lau” tace “Toh Maa sha Allah” shiru ne ya biyo baya, bayan few seconds ya kalleta yace
“Ba aiki xan baki ba, na dai xo maki da magana mai muhimmanci ne Hajiya Rahinah…” kallonsa tayi ita ma tace
“Ohk Am all ears in sha Allah barrister, Allah kuma yasa dai lafiya” yace “Sai alkhairi, Hajiya Rahinah na gayyatoki
nan ne…. To ask for ur hand in marriage” Da wani irin mamaki take kallonsa wanda hakan bai bata damar iya ce
masa komai ba, yyi kasa da murya yace “Yes nasan xa ki yi mamaki but ba abun mamaki bane, I want to marry
you…” Ta yi wani yake tace “Haba Barrister, do you even know what u are saying, ni ynxu auren me xan kuma yi?
Me nake nema a rayuwa….” Ya katse ta yace “Aure shine rufin asirinki let me tell you idan baki sani ba, idan kika yi
aure kimarki da darajar ki xai fi haka a gun jama’ah, I have known you for more than 15 years now tun mijin ki na
da rai….” Bude handbag dinta tayi ta ciro tissue don nan da nan har hawaye ya kawo idonta, ya girgixa kai yace “I
don’t mean to hurt you ko in fama maki ciwon xuciyar ki Rahinah, kar ki manta tun ba yanxu ba na sha baki
shawaran kiyi aure sai ki ce min sai kinyi shawara, to yanxu na yanke shawarar auren ki for 3 reasons, which I will
let you know ko ba yanxu ba” tace “I am sorry Ahmad bana tunanin xan yi aure har karshen rayuwata, rabuwan
tashin hankali nayi da mijina ba wai normal rabuwa, bana da ra’ayin aure har abada” ya katse ta ya d’an buga table
din gabansu yace “Stop this nonsense Rahinah…” A d’an fusace tace “In koma gida ince ma yarana xan yi aure? Me
ye nake nema a duniya a yanxu? Me yarana suka rage ni da shi da xai sa inji ina sha’awar yin aure? Plss come off
this barrister” Ya lumshe ido ya bude yace “Noo Rahinah, ba don kin rasa komai xaki yi aure ba sai don auren shine
suturar ya mace….” Tana goge hawayen idonta tace “Idan ma sbda tafiye tafiyen da nake yi ne ko sbda Aikina ni naji
xan ajiye in xauna gidana dama Junaid ya fi son haka, tun ba yau ba yake son in daina aikina coz ban rasa komai
daga garesu ba, ni kuma xaman kadaici ne dama bana so” Kallonta kawai yake, ya sauke boyayyen ajiyar xuciya
yace “I’m sorry I am making you cry this much, I’m sorry Rahinah” tayi murmushin karfin hali tace “It’s okay….” A
hankali yace “Xa mu ci gaba da magana amma ba ynxu ba, it’s almost time for zuhur, but….” Jin yyi shiru ta kallesa
tace “But?” Ya sakar mata murmushi yace “Ban hakura ba, anyway that aside xan baki yarinya ki tafi da ita, for now
marainiya ce bata da kowa….” Da mamaki take kallonsa tace “Ban gane ba, a ina ka samo ta…” Briefly ya 6ata
labarin Heedayah, wanda hakan yasa jikinta yyi sanyi tace “Allah sarki, Allah ya bayyana iyayenta, I will go with
her in sha Allah” yace “Yes I know u will Rahinah, sai dai I didn’t made mention of her blindness to you, she’s blind”
xaro ido tayi tace “Blind??” A hankali ya gyada mata kai, tace “Innalillahi wa Inna ilaihi raji’un” yace “Tana mota ita
kadai, mu tafi ki ganta” a tare suka fita eatery din, sai da suka kusa motarsa a hankali tace “Matar ka tace baxata
riketa ba kenan?” Ya juya ya kalleta ya d’an yi murmushi yace “Ehh” Ta girgixa kai tace “Toh Allah ya kyauta” yace
“Ameen, amma a gidana Heedayah xata xauna, she will stay with u just for few days let me settle down things”
Bude mota yyi Heedayah ta juya direction din da sauri fuskarta duk hawaye tace “Abba” ya kamo hannunta yace
“Kuka kike yi daughter” cikin rawar murya tace “Naga baka dawo ba” ya share mata ido yace “I’m back dear, xaki bi
Maminki gida yanxu kin ji?” Tace “Abba ina xaka je?” Yace “Xan je in siyo maki sabbin kaya ko baki so” tayi shiru
bata ce komai ba, Hajiya Rahinah dake ta kallon Heedayah da tausayi tace “Ba dadewa xai yi ba baby, mu je gida
kafin ya kawo maki kayan” daga haka ta sauketa a motar, ya kalleta yana murmushi yace “Thanks Barrister, sai na
xo anjima” ta gyada masa kai ta nufi motarta da Heedayah, sai da ya ga fitansu sannan ya ja motarsa ya bar Haraban
eatery din shi ma. Hajiya Rahinah na parking a parking space ta bude motar ta fito, wata yarinya da baxata haura sha
hudu ba ta iso gun motar tace “Mami sannu da dawowa” Tana mika mata handbag dinta tace “Thanks dear, har kin
gama assignment din?” Tace “Ehh na gama” Mami ta xaga xuwa side din Heedayah tace “Junaid ya xo kuwa?”
Yarinyar ta girgixa kai tace “A’a..” bude motar tayi ta sakko da Heedayah, xaro ido yarinyar nata tayi tace “Mami
who is she?” Mami tace “Bakuwa” daga haka ta rufe motar tana rike da hannun Heedayah ta nufi entrance din shiga
cikin gidan ‘yar ta Farida na biye da ita a baya…
Hajiya Rahinah na xaune parlonta watching a movie, almost absentminded, lkci lkci take kallon Heedayah da ke
xaune kasan lallausan carpet dake tsakar parlon, Short bread ne hannunta tana ci a hankali, irin kallon da take ma
kofar kitchen sai kace tana ganin kofar ne da idanuwanta, Hajiya Rahinah ta sauke ajiyar xuciya for the countless
time ta girgixa kai, ba karamin tausayin Heedayah take ba har ranta, text ne ya shigo wayarta ta dauka sanin baxai
wuce Barrister ba, dai dai nan kuma aka yi knocking kofar parlon, Farida dake xaune dining tana shan cornflakes ta
mike ta nufi kofar, bude kofar tayi wani matashi dake tsaye bakin kofar yana kallonta yace “Baki je islamiyya ba?”
Ta langwabar da kai tace “Mami tace I should stay behind xata fita ynxu” Xai yi magana ganin Mahaifiyarsa xaune
parlon ya shiga ciki da sallama, Farida ta rufe kofar ta koma dining, xaunawa yyi kujeran dake kusa da na mum din
tasa yace “Ina yini Mami” tana danna wayarta tace “Lfya lau, jiya baka xo ba Why?” Ya shafa kansa a hankali yace
“Mami Uncle ne ya bani aiki, amma kin manta ne nace maki baxan dawo ba” Tace “Ohk, ka kai ma Salma sakonta
kuwa” yace “Eh daga can nake, har xan kawo maki Fadil wai xai biyo ni na fasa, kar ya xo yyi ta mana kuka” Tace
“Gobe ma Monday akwai aiki ai” Yana kallon Farida yace “Mami wai ke kika ce kar ta tafi islamiyya?” Da sauri
Junaid ya dauke kafarsa xai mike jin abu na ta6a sa, bai kai ga cewa komai ba ya ga Heedayah rakube jikin kujeran
da yake xaune, Kuri tayi ma kafarsa da ido, ya mike ya dinga kallonta, Mami tayi dariya tace “Kai dai ka fiye tsoro
kamar mace” Yace “Mami wacece wnn kuma?” Mami tace “Bakuwa nayi daxu” hade fuska yyi ya canxa kujera ya
xauna, Mami ta mike tana kallon Farida tace “Ki dawo nan parlor ki xauna, yanxu xan fita, you make sure baki bar
ta ita kadai ba, I will be back soon, kasuwa xan je” Farida ta mike ta dawo parlon, Mami ta nufi Heedayah ta duka
tana kallonta ta shafa kanta tace “Kina son wani abu dear?” Gyada kai tayi tace “Xan sha ruwa” Mami tace “Farida
ki kawo mata ruwa” Farida ta tafi fridge dauko ruwa, Mami ta kalli Junaid tace “Sai na dawo, I am not staying
long” ya mike yace “Ni ma ai wucewa xan yi Mami” tace “Aa ka jira ni, I said I am not staying long” daga haka ta
nufi kofa, da kallo ya bi ta har ta fita, sannan ya koma ya xauna yana kallon Farida yace “Who is she? I mean the
girl” Farida ta bude hannu tace “Mami came back with her earlier this afternoon” Ya buda ido sosai yace “From
where?” Farida tace “I don’t know” girgixa kai yyi ya kara satan kallon Heedayah, direction dinsa take kallo, ya d’an
hade rai calmly yace “Kin san ni ne kike kallona?” Laluben kasa ta shiga yi tana neman murfin bottle water cikin
sanyin muryarta tace “Ni ba kallon ka nake ba” yace “Hoto kike daukata da idon ki idan ba kallona kike ba kenan”
Ta d’an turo baki bata ce masa komai ba tana ci gaba da lalube lalubenta, Farida ta koma kusa da shi da sauri ta kai
bakinta kunnensa cikin rada tace “Yaya she is blind fa!!!” irin yanda ya yo waje da ido yana kara kallon Heedayah
yasa Farida tayi dariya bata shirya ba, ta dinga dariya har da kyakyatawa da saukowa saman kujera, Shi kam kallon Heedayah kawai yake da mamaki ya ma kasa cewa komai, bai ankara ba sai ganin hawaye na sauka fararen
idanuwanta yyi, Bai san lkcn da ya mike ba, Farida ma ta hadiye dariyar da take tana kallonta, ya nufeta ya duka
kusa da ita yace “Me yasa kike kuka??” Shessheka ta fara yi tace “Xan tafi gun Abba” Farida ta dawo kusa da ita da
sauri tace “Yanxu fa Mami xata dawo” Junaid ya kai mata rankwashi a kai yace “She thought u are laughing at her…
What’s making u laugh that loud at the first place” Farida tace “Kiyi hakuri, ba dake nayi dariya ba wllh” Ita dai
Heedayah sai juya biscuit din hannunta take hawaye na xuba idonta, Junaid yace “Kin ji ta baki hakuri, kiyi hakuri
kin ji” Shiru tayi masu, ya dafa goshinta yana goge mata hawayen da hannunsa yace “Kin hakura?” gyada masa kai
kawai tayi, nan kuma ta daina hawayen, mikewa yyi ya koma kujera ya xauna so relieved ganin ta daina kukan, shi
dai fa har sannan ya kasa yrda bata gani don gashi sai kallonsu take tana kifta fararen idanuwan, Farida ta rufe bottle
water din ta mike ta koma kan kujera ita ma, Junaid ya dau wayarsa ya shiga gun msg yyi typing kamar haka, “Da
gaske bata gani? Don’t joke with me” mika ma Farida wayar yyi, Farida na karantawa ta kallesa tayi masa alamar
rantsuwa cewar Heedayah bata gani, kara kallon Heedayah yyi da shock, can ya mike ya wuce sama yana kara
waigo ta. Farida ta canxa tasha ta maida hankalinta kan movie din da ake yi, bayan kusan awa daya taji muryar
Junaid ya sakko kasa yace “Why don’t you tell her to lie down Farida?” Farida ta juya da sauri tana kallon Heedayah
da ta kwantar da kanta saman kujera tana bacci daga xaunen da take, Farida ta mike tace “Ban sani ba” nufenta tayi
ta ta6a ta tace “Ki tashi in raka ki daki” Heedayah ta bude ido da sauri tace “Aa” Farida tace “To hau kan kujera”
mikewa tayi ta fara laluben kujeran, shi dai Junaid kallonta kawai yake, Farida ta sa ta kwanta kan kujeran sannan ta
koma ta xauna. Shidda da yan Mintuna Mami ta shigo gidan da ledoji manya manya, Farida dake parlon har sannan
ta mike tana mata sannu da xuwa ta amshi ledojin, Mami da hankalin ta na kan Heedayah tace “Me yasa kika bari
tayi bacci ta yamman nan?” Farida tace “Ina son in tasheta daxu yaya yace in bar ta” Mami tace “Ina yayan?” Kafin
Farida tace komai sai gashi nan sakkowa, Mami ta nufi Heedayah ta dafa kanta tace “Dear” bude ido tayi da sauri,
Mami tace “Yamma yayi tashi kar ki yi sake bacci” Heedayah tace “Abbana fa?” Mami tace “Ga kaya nan Abban ki
yace a kawo maki…” Heedayah ta katse ta tace “A’a ina son in je wajensa” Mami tayi murmushi tace “To yana jiran
ki a waje” kallon Junaid Mami tayi tace “Take her outside, xaka ga mota a waje, ka kai ta motar” shiru yyi yana
kallon mum din tasa, ganin ko kallonsa bata yi ba sai bude ledojin da Farida ta ajiye take, ya karaso cikin parlon
yace “But Mami I thought she’s blind how will I take her outside” Mami ta hade rai tace “Kama hannunta xaka yi ku
tafi, ko in kai ta da kai na?” Ya girgixa kai yace “Aa” ya nufi gun Heedayah, Farida sai dariya take kasa kasa, ya
kamo hannun ta jin haka ta sakko daga saman kujeran, kamar me counting steps dinsa ya nufi kofar fita yana rike da
hannunta, Farida ta bi su da kallo tana danne dariyar ta, sai da suka fita parlon, Heedayah dake ta bin sa tace “Ha’an
da sauri kake tafiya xan je in fadi” kallonta yyi sannan yace “To ba sai ki fadi ba” Bata ce masa komai ba har suka
fita gate, ya nufi motar da ya gani a bakin gate din, Bude motar aka yi barrister ya fito, ganinsa Junaid ya yi kasa da
kai ya gaishesa da ladabi, Abba ya amsa da fara’a yace “How are you doing Junaid?” Yace “I’m fine sir” Abba yace
“Ashe ka dawo, kuna hutu ne?” Junaid yace “Ehh Abba mun yi hutu” Abba yace “To maa Sha Allah, Allah ya
taimaka son” Junaid yace “Ameen nagode” Heedayah sai murmushi take jin muryar Abba, ta fara lalube lalube xata
ta6a sa, Murmushi yyi ya duka kusa da ita ya kamo hannunta yace “How are you my dear?” Ta fada jikinsa a hankai
tace “I am fine Abba, are you taking me with you now??” ta gefen ido Junaid ya dinga kallonta, nan kuwa he is
trying to vividly recall weda he said anything bad daxu da turanci da yyi magana da Farida…. Abba yace “No, xaki
tsaya tare da Mami kinga ni xan tafi aiki ne” tayi shiru bata ce komai ba, amma gaba daya mood dinta har ya canxa,
yace “Ga kaya Mami ta siya maki da yawa sai ki ce mata thank you idan kun koma ciki” a hankali tace “Ohk” yayi
patting kanta yace “Good girl” cikin sanyin murya tace “Abba yaushe xan koma gun Ammina da Abbuna?” Tana
magana har hawaye ya kawo idonta, Shiru yyi yana kallonta, can yace “Soon daughter, in sha Allah soon xa ki koma
wajensu” mikewa yyi yana kallon Junaid yace “Ku koma ciki Junaid” Junaid ya kama hannunta yace “Toh Abba
Allah ya kiyaye hanya” Abba yace “Ameen” Sai da suka shiga gate sannan Junaid ya kalleta yace “Ina Ammin taki
da Abban ki???” shiru tayi bata ce komai ba, yace “Baki ji na ne?” A takaice tace masa “Ehh” tsayawa yyi da
mamaki yana kallonta, can ya saketa ya koma gefe ya tsaya yace “To ai sai ki kai kanki ciki”Da asuba bayan an idar da sllh a masallaci da kusan minti sha biyar Shuraim ya mike ganin Abbansa xai fita
masallacin don dama shi yake jira, sai da suka fita masallacin ya isa gun Abban nasa, ya d’an risina yace “Barka da
asuba Abba” Abba ya kallesa ba tare da ya tsaya ba yana ci gaba da tafiya yace “Yauwa….” Shuraim na biye da shi
yace “Abba dama ina son baka hakuri ne kan abubuwan dake faruwa….” Abba ya katse sa yace “A’a kaje dai ka ba
babarka hakuri, ita ta fi daukan abun da xafi, sannan kuma dama a bayanta kake as always” Ya girgixa kai yace “A’a
Abba, ba wai ina bayanta bane, just that muna tsoron abinda xai je ya dawo ne a kan lamarin….” Abba yyi murmushi
yace “Ehh gaskiya ne Ali, barin ma da ya kasance cewar duk abinda yaro ya hango ba lallai babba ya hango ba”
Shuraim yace “A’a ba haka bne” Abba yace “No haka ne” Shiru Shuraim yyi yana dai biye da Abban nasa, can yace
“Toh Abba tana ina yarinyar ynxu?” Abba ya tsaya ya juya yana kallonsa yace “Do you have any problem with
that?” Bai iya yace komai ba, Abba ya watsa masa wani kallo ya ci gaba da tafiyarsa, Har suka shiga gida babu
abinda Shuraim ya sake ce masa. Reaction din Abban nasa bai hanasa bin sa har cikin parlonsa ba, Abba ya xauna
saman kujera ya dau remote xai powering TV, Shuraim ya xauna kasa daga gefensa, a hankali yace “Kayi hakuri
Abba, ni ban ga aibun abinda kayi ba haka ma ban ga aibun abinda Mumy tayi ba, she’s right in many ways”
kallonsa kawai Mahaifin nasa yake, can ya girgixa kai yace “Baxa ka ta6a yin alkibla ba dama, look… Ur mother
like it or not dole gidan nan Heedayah xata xauna har sai naga she’s back to her parent, idan ku ka ga Heedayah bata
dawo gidan nan ba to iyayenta ne Allah ya bayyanar, amma I mean it, bbu abinda xae hana hakan, kuma tare xata
dawo gidan nan da matar da xan aura ta kula da ita, ur mother can do whatever she want bbu wanda ya isa canxa
ra’ayina” Shuraim dake kallonsa da wani expression yace “Abba aure?? I’m sorry to say… you want to spoil ur home
because of a mere little girl da baka san ma me ya rabata da iyayenta ba, baka san daga inda ta fito ba, think about it
plss Abba, this is wrong” Abba yyi wani murmushi yace “It’s my home not urs, ko da wasa ai baxa ka gaya ma
uwarka irin wannan maganar da kake gaya min ba yanxu, ni kuma ga abokin rainin ka, check out pls my frnd”
Mikewa Shuraim yyi kamar baxai ce komai ba sai kuma yace “Kayi hakuri” daga haka ya fice daga parlon, lkci daya
ya hade rai bayan ya fita ya nufi dakinsa, who the hell is this forsaken girl that’s trying to cause confusion in their
home…. Muryar Mumy yaji tace “Ya aka yi Shuraim? What’s wrong?” Tsayawa yyi ya juyo bbu walwala yace “Ina
kwana Mumy” tace “Lafiya lau, ya naga ranka a bace haka?” Yyi kasa da kai yace “Nothing mum, xan shirya ne
yanxu” daga haka ya juya ya shige dakinsa, sarai tasan daga parlon Abbansa ya fito, ta d’an yi jim kamar me naxari
sannan tayi murmushi ta juya ta nufi dakinta a ranta tace Idan barrister ya san wata bai san wata ba ai…. Karfe sha
biyu saura na safiyar ranan barrister ya isa gidan Yayansa Dr Umar, yana shiga main parlor bangaren Mahaifiyarsu
ya nufa, ya bude kofar parlon tare da sallama, a guje kaka ke kokarin boye bowl din gabanta tana cewa “Naga fitina
waye kuma wannan” d’an murmushi yyi ya karasa cikin parlon, tace “Au ashe Amadu ne, wllh na xata yaran nan ne
masu halayyar bera, to idan na ajiye d’an nama na da cin cin sai su bi dare su yashe….” Abba yace “Ina yini Baaba?”
Kaka tace “Lfya lau Amadu, ya aikin” yace “Alhmdllh, ke daya ce gidan kenan” Da sauri tace “To da fa?? Ai
Kullum a haka suke bari na, kar fa kayi xaton basu gidan, duk suna nan wllh, dama wannan yaro Aliyu ne me shigo
min, shi ma kuma na koresa gaskiya, don raini ya shiga tsakanin mu” Abba yace “Daga gun aiki nake nace bari in xo
mu gaisa” Kaka tace “To ae ka kyauta, Allah yyi maka albarka, Wai ya maganar da kayi ranan na cewa xaka kara
aure ne naji shiru” yace “Ehh dama xan gaya maki maganan na nan in sha Allah…” Kaka na washe baki tace “Toh
Alhmdllh, yar ina ce?” Yace “Nan kaduna” kaka tace “Abu me sauki, to ni dai Allah ya sa ta kirki ce, don Maryam ta
gasa mana Aya a hannu gaskiya, to ta amince xata rike yar makauniyar??” Abba yace “Ehh ba matsala” kaka tace
“Atoh ita da ke tsoron Allah kenan, Maryam ae shaidaniya ce sanye da kaya irin na mutane” Abba ya mike yace
“Bari in je kaka sai na shigo ko gobe” Kaka tace “Toh, ni dai haka nn nake sae bin yara nake ina rokon hamsin, dari,
suna xagina suna ba ni” Abba ya juya yana kallonta da sauri, ta tsuke fuska tace “A’a kai ba ubana bne da xaka min
kallon tuhuma Amadu, idan gantalalliyar dubu ashirin din ka ce ta shekaranjiya to ta kare tun jiya wllh” Bai ce
komai ba ya nufi kofa ya bude yace “Sae anjima” Daga haka ya fita. Hajiya Rahinah ce xaune tare da Barrister kan
kujerun dake karkashin inuwar bishiyar tsakar gidanta, barrister ya ajiye wayar hannunsa yace “Sae kuma kika yi
shiru” Sae a sannan ta kallesa tace “Ehh shirun naga xai fi, barrister in dae har sbda wannan yarinyar kke son aurena,
ina nufin indan sbda in riketa ne to kar ka damu ni me iya rike little girl din ne har bayyanar iyayenta idan Allah ya
yrda, ina hada ka da Allah ka rabani da xancen auren ka, bbu aure a tsarin rayuwata ynxu….” Shiru yyi yana kallonta,
sannan ya d’an yi murmushi yace “Sae dai fa kiyi hakuri Rahinah, you can’t stop me from marrying you, Heedayah
kuma gidana nake son ta xauna ba wani waje daban ba” Mami ta tabe baki sae dai bata ce komai ba, Budewar gate
ya sa duk suka juya, Junaid ne ya shigo compound din hannunsa rike da Makullin mota, har ya isa inda suke ya fara
gaida Abba sannan ya gaida Maminsa, Abba yace “Kana aiki ne Junaid?” Yace “Ehh ina aiki tare da Uncle dina a
hospital dinsa” Abba yace “To that’s good ya fi ka xauna, Allah ya taimaka” Yace “Ameen” daga haka ya wuce ciki,
Abba ya kalli Mami yace “Ya kusa gama masters din nasa ne?” Mami tace “Ehh months suka rage masa idan Allah
ya yrda” Abba yace “Allah ya taimaka” Junaid na shiga parlor ya ga Heedayah ce kadai parlon kwance saman kujera tana bacci, ya dauke idonsa ya wuce sama xuwa bedroom dinsa. Sae kusan la’asar Abba ya bar gidan har sannan
kuma bai yi convincing Hajiya Rahinah ba dake kan bakanta na cewa bbu aure a gabanta. Yau dai har sha daya saura
na dare Hajiya Maryam na xaune parlor tana jiran ganin lkcn da barrister dake compound yana ta waya xai shigo,
yau kwana biyu kenan da ta lura da hakan duk da kasancewar ta mai bacci da wuri yau kam coffee me kauri ta sha
tayi xamanta a parlor tana jiran ganin ikon Allah, lkci lkci take tashi ta leka waje ta dawo, lekawar da tayi na karshe
ne taga ya gama wayar xai shigo ciki, da sauri ta shige kitchen ta kulle don ma kar ya san idonta biyu, sae da taji ya
wuce part dinsa sannan ta fito ta dinga xaga parlor tana jiran ya kwanta sanin bashi da wuyar bacci, a haka Shuraim
ya sakko downstairs ya sameta, ganinta da mamaki yace “Mum baki kwanta ba” Tace “Ehh yanxu dai xan je in
kwanta na gama kallon wani film ne” Bai ce komai ba ta wuce sama shi kuma ya shiga kitchen, sae da taji Shuraim
ya shiga dakinsa ta fito ta nufi part din mai gidan nata, a hankali ta bude kofar parlonsa ganin wuta a kashe ta gane
ya kwanta, ta lallaba ta nufi daki tana tafiya a hankali, tana shiga duk da wutan a kashe yake tasan yyi bacci ta tafi
inda tasan yana ajiye wayarsa ta dauka ta fita daga dakin, bangarenta ta koma ta bude wayar ta shiga call log dinsa,
Number da aka yi saving da Great barrister taga last call dinsa, nan ta duba taga yana yawan kiran number, msg ta
shiga tayi scrolling har xuwa farko, hankalin ta ya fara kwanciya ganin kawai text ne da ya shafi aiki, a hankali ta
fara gwalo ido bayan tayi nisa ganin salon message din ya fara sauyawa har ta kai karshe, xufa ne ya karyo mata ta
ajiye wayar ta rasa tunanin da xata yi, can ta dau wayarta ta kwashe number tas sannan tayi dialing, sae da ya kusa
katsewa aka daga, daga daya bangaren Mami tayi sallama, shiru Hajiya Maryam tayi xuciyar ta na bugawa jin
muryar mace, kawai ta katse ji tayi kamar ta daura hannu a ka tayi ta ihu, ta xauna gefen gado tana furta innalillahi,
kallon wayarta tayi, sae kuma ta shiga call log tayi dialing wani lamba, yana fara ring aka dauka, Ta hadiye abu da
kyar tace “Sadiya wllh da gaske Barrister neman aure yake, Ashe da gaske yake wllh, gashi ynxu na bincike wayarsa
kaff har na samu lambar warce yake nema da aure, na shiga ukuna Sadiya, da yarinta ta ba a min kishiya ba sai
yanxu a kan wata shegiyar yar tsintuwa makauniya….” Ta fashe da matsanancin kuka tace “In dai Alhaji yyi auren
nan ai tawa ta kare, dariya xa ayi min a gari ki bani shawara don Allah kawata, wllh dariya makiyana xa su min”
Hajiya Sadiya dake saurarenta baki bude tace “Aure fa kika ce Maryam?? Ke sai ki yrda ki barsa yyi auren? Toh
ynxu dai ae sai ki wanke kafarki mu tafi inda kike ikirarin bbu abinda xai kai ki” Hajiya Maryam tace “Ina???”
Hajiya Sadiya ta kyalkyale da dariya tace “Wa enda kike raina taimakonsu mana….” A fusace Hajiya Maryam tace
“Allah shi kiyaye, tun da can da kuruciyata ban ta6a xuwa ba sai ynxu a kan yar yarinyar da na haifa?? Yar cikina?
Ni nan da kike gani na ishi kowa wllh, Kuma muna nan dake auren nan baxae ta6a yiwuwa ba ni nasan me xan yi,
ke dai kawai ki xo gobe don Allah, sae da safe” daga haka ta katse wayar, ta kusa awa daya xaune kafin ta iya tashi
ta mayar masa da wayarsa ta dawo dakinta, daren ranan bata yi baccin kirki ba, Wai ita barrister xai ma kishiya sbda
taki rike makauniya??? Tayi kwafa ta juya tana jiran dai gari ya waye. Mami na xaune tana ma Heedayah gyaran
dogon gashinta dake ta kyalli, yau ma dai bata je aikin ba don har lkcn bata samu wanda xai kulan mata da
Heedayah ba, Farida kuwa na boko daga safe har 6, wayarta ne ya fara ring ta dauka ta kai kunne, sallama aka yi
mata daga daya bangaren ta amsa, Hajiya Maryam dake xaune dakinta da Hajiya Sadiya da wata kawarsu Hajiya
kyauta tace “Don Allah da barrister nake magana” Mami tace “Yes, wacece ke magana?” Hajiya Maryam ta gyara
xama tace “Toh Barrister wata yar matsala ce wllh ta taso mana muna neman lawyer, shine wani abokin aikina ya
bani lambar ki, yyi assuring dina you can help…” Mami tace “Allah sarki sai dai na dau hutu baxan yi aiki ba cikin
satin nan gaba daya” Hajiya Maryam ta gwalo ido tace “Don Allah ki taimaka barrister, ya gaya min irin kirkin ki da
taimakon ki, ke kadai xaki iya rufa mana asiri kan lamarin nan, don Allah barrister ki dubi girman Allah ki
sauraremu, wllh muna cikin tashin hankali sosai” Mami tace “Kar ki damu malama xan hada ki da wani barrister, he
is also good xama ki ji dadin nasa aikin fiye da nawa, I can send you his number now” da sauri Hajiya Sadiya tayi
ma Hajiya Maryam alamar tace mata to ta turo… Hajiya Maryam tace “Toh ngd Barrister, Allah ya saka, ina jiran
lambar” Mami tace “Kar ki damu, let me send you” daga hka ta katse wayar, cikin few seconds ta tura ma Hajiya
Maryam number Barrister Ahmad, Hajiya Maryam da ta ji kmr xuciyarta ya fashe cikin tashin hankali tace “Na
shiga uku, kun ga lambar mijina ta turo min dai koh???” Hajiya Sadiya tace “Toh sake kiranta” hannu na rawa ta
sake kira, Hajiya Sadiya ta amshe wayar tace “Ki dubi girman Allah Barrister ki bamu lkcn ki ki saurari matsalar mu,
an ce mana ke ce maganin kukan mu, wllh ko nawa kika bukata xa mu biyaki domin Allah ki taimake mu…” Da
mamaki Mami tace “Wnn barristern da na tura maki numbersa ya ma fini iya aiki, xae saurare ku fiye da ynda ni xan
saurare ku” da kyar da kyar suka shawo kan Mami kan ta amshi case dinsu, Mami ta girgixa kai tace “Gaskiya baxan
fita gidana ba ynxu, sae dai ko ke ki xo ki sameni” Hajiya Maryam tace “Wnn ae ba matsala bane, bari in taho ynxu
ma, Allah ya kara girma da daukaka Barrister, ki turo min address din plss” Mami tace “Ameen, xan tura maki ynxu”
daga hka ta katse wayar, ta tura address din nata, Hajiya Maryam tayi wani murmushi ta mike ta dau mayafi da
Makullin mota jikinta har wani 6ari yake tace “Ku mu je” fita duk suka yi suka bar gidan a motarta. Gane gidan
Hajiya Rahinah bai masu wahala ba, suka yi parking a waje bayan sun sanar ma Mai gadi Hajiya Rahinah suke nema
kuma ta san da xuwansu ya bar su suka shiga cikin gidan. Har entrance din shiga gidan suka nufa suka tsaya, Hajiya
Sadiya ta danna bell, Mami da ta saka Heedayah gaba tana mata tambayoyin ynda aka yi har ta fito gida…. exactly labarin da Heedayah ta bada a station ta sake ba Mami, ta kare da cewa sai taji ana tafiya da ita a bicycle kawai sai
ya wuce ya bar ta bai kai ta gun Amminta ba kuma, tana fadin haka ta fara hawaye, Mami dake ta naxarin d’an
labarin ta gane daga all indication kidnapping yarinyar aka yi sai kuma Allah ya kubutar da ita, mikewa tayi jin an
sake danna bell for the third time ta nufi kofa ta bude tana kallonsu Hajiya Maryam, Hajiya Maryam ta kirkiro
murmushi tace “Sannu fatan ke ce barristern?” Mami tace “Oh, okay ga kujeru can bari in fito yanxu, ku jirani a
can” Hajiya Maryam ta saka kai ta raba ta gefenta ta shiga ciki, tace “A’a xai fi daga cikin dai barrister, tonon asiri ai
ba dadi” sauran ma duk suka shige ta gefenta, kallonsu Mami tayi da d’an mamaki, Hajiya Maryam ta isa tsakiyar
parlon tana kallon Heedayah da wani expression, sauran kawayenta ma duk suka tsaya kusa da ita suna kallon
Heedayar, Kasancewar Mami lawyerr yasa lkci daya ta gane abinda ya kawo matan nn gidanta ba abinda suka ce
bane, Hajiya Maryam tace “Toh kinyi tsaye bakin kofa ae sai ki karaso ki ji case din mu koh barrister?” Heedayah
dake xaune saman kujera da apple a hannunta ta mike da sauri don in dai ta ta6a jin murya to baya ta6a bacewa a
sense of hearing dinta, ko da kuwa an dau lkci sosai sai ta gane muryar duk inda taji, Mami ta karaso parlon tace
“Bana bukatar jin case din ku, domin bana hulda da Yan tasha, ku kai case din ku wani wurin, and ku fitar min a gida
immediately now….” Hajiya Maryam tayi wani dariyar rainin hankali tace “Koh?? To sai ki fitar da mu ta karfi Mai
gida, bari ki ji….. ba barrister ba, ko judge ce ke na xo ne in yankar maki lafiyayyen wani ki fita hanyar mijina
Barrister Ahmad, shi ba gantalalle bane irin ki, kin gama xaga duniya kinyi yawon karuwancinki shine xaki wani
makale masa ya aure ki sbda baki da tunani ko? To wllh kin yi kadan, mijina ba sa’an auren ki bane, Ashe ke ya
kawo wa shegiyar yarinyar nan kika karba kika rike tunda dama kina sonsa da aure, to don kaza kazan ki nace baki
isa ba, mijina ni kadai ne shi din, baxan hada shi da karuwa ba yar boko da ke yawon duniya don ma kiji, don haka
tun wuri ki san inda dare yyi maki” Tunda ta fara Mami ke kallonta, duk da maganganun sun ma Heedayah girma ba
duka xata iya ganewa ba hakan bai hanata dinga kuka ba tana kiran Mami, Mami ta nufi gun wayarta ta dauka cikin
few seconds tayi dialing number Abba, yana fara ringing kuwa ya daga ta sa hands free tace “Ahmad kana ji na?”
Yace “Yeah ina ji my barrister, ya gidan?” Tace “Alhmdllh, dama nace ne you can come forward with ur pride price
to my elders ko gobe, na karbi tayin auren ka idan Allah ya yrda” Yace “Da gaske kike barrister, pls don’t joke with
me” farin ciki ne sosai tare da words dinsa, Mami tace “I’m not joking barrister, na baka go ahead, we will talk later
in sha Allah” daga haka ta katse wayar, Hajiya Maryam da wani xaxxafan xufa ya keto mata ta dinga kallon Mami
so speechless, Mami ta isa gabanta ta tsaya tace “xa mu shigo gidan barrister Ahmad tare da wannan yar yarinyar
nan da sati daya, sai dai ciwon xuciya ya kashe ki a banxa, sannan wnn yarinyar da kike gani ita xata xamar maki
nightmares dinki kafin ni…. Lastly kin ci sa’ar mijinki na da k’ima da daraja a idona sannan ga soyayyar da nake
masa, wllh da yau bbu abinda xai hana ke da mahaukatan kawayen ki kwanan cell kuma in ga uban da xai bada bail
dinki, amma soyayyar mijin ki baxai bar ni inyi hakan ba…” Tana fadin haka ta ja hannun Heedayah suka fita xuwa
gun mai gadi tace “Salisu ka tattaro abokanan ka masu gadi ka fitar min da wasu mashaya da suka shigo min gida,
and from henceforth duk wanda ya xo ka fara sanar min kafin ya shigo” da sauri ya fita yin yanda tace.⁸