HEEDAYA CHAPTER 43 BY By Khaleesat Haiydar
Heedayah tayi kamar bata ji abinda kaka ke ce mata ba xata bi wata kawarta dake jan ta su tafi su yi hoto da family
dinta, Ammi dake kallonta da mamaki tace “Are you deaf Heedayah? Ba magana kaka ke maki ba??” Heedayah ta
juyo da sauri kamar a lkcn ta ji tace “Ohh ban sani ba…” Sai kuma ta kalli kaka da ta saki baki tana kallonta tace
“Na’am kaka….” Ammi na kallon classmate din Heedayah tace “Let her finish snapping here xata je kin ji yan mata, ki jira sai ku tafi” yarinyar na murmushi tace “Ohk Ma” Kaka na kallon Heedayah tace “Idan xaki fita hanyar
kawaye ki fita tun wuri bbu ruwanki da su, meye yarinya xata yi ta makale maki tun shigowar mu nan, to cewa nayi
shi Shureen baxa kije ku yi hoton tare ba, tunda har Allah ya kawosa shi ma ai sai kiyi hoton da shi ba don halin sa
ba, ai ya ma kyauta tunda daga legas ya taho duk da bakin halinsa” Heedayah dai bata ce komai ba ta juya ta d’an
kalli direction din da Shuraim ke tsaye sanye da uniform dinsa holding both hands dinsa ta bayansa yana bin
kayatattcen makarantar dake dauke da manyan mutane da suka xo murnan Candy din ‘ya yansu da idanuwansa,
kowa na wajen mai kudin kansa ne, sae dai duk attention ya fi karkata gun Heedayah da Family dinta, Heedayah ta
d’an kalli Ammi dake kallonta fuska daure, a hankali ta mika ma Mami dake wajen tare da su Dinar da stepmum
dinta jakar hannunta ta nufesa tana tafiya kamar bata son yi tana dage doguwar readymade din rigarta sbda jan kasa
da yake, duk wanda ya kalli Heedayah sae ya sake kallonta don koman jikinta is unique, camera man na biye da ita
har suka isa gun Shuraim, Farida dake tsaye ta bi ta da ido, ba tare da tace masa komai ba ta tsaya daga side dinsa
leaving much distance between them tana gyara graduation cap dinta bbu ko d’an murmushi fuskarta, sai gyara
kayanta take kamar munafuka, ya d’an kalleta ya dauke kai, Mumy dake wajen da Sadiya dai sai kallonsu suke,
murya can kasa Sadiya tace “Lallai kam yar gwamna, dubi gwalagwalai ni Halimatu” Mumy dai ta kasa cewa komai
ta hadiye abu da kyar, a hankali Shuraim ya dawo kusa da Heedayah yana kallon camera man din, kamshin turarensa
ya cikata, ita dai bata yarda ta kallesa ba, nan mai hoton ya kashe masu hoto har biyar, ko second daya bata kara a
wajen ba ta koma gun su Mami da sauri, gaba daya attention din mutanen wajen na kan su Heedayah sbda presence
din Abbanta da ke da mukamin gwamna a yanxu, sojoji ne da police men ta ko ina a wajen sai wajen ya dawo kamar
Heedayah kadai ce ke candy, Mumy dai na rakube gefe da kawarta tana tsoron xuwa kusa da su kaka ta sha disgi,
kaka kam taje gun Mahaifin Heedayah dake wajen xagaye da sojoji ya fi a kirga sai wani daga kafada take a wajen
kamar boss, Kuma bbu me hanata xuwa kusa da shi tun tsige wani soja da tayi farkon shigowarsu wajen, presence
din Sudais wajen kadai ya sa Heedayah ta saki ranta don tun fara occasion din bata da walwala gaba daya a sanyaye
take, but seeing Sudais after 2 years kawai sai ta d’an sake, Abbanta da su Abba ne suka fara barin wajen ana kan
daukan hotuna, Sadiya ta kalli Mumy tace “Haba Maryam kije ku dau hoton ke ma mana, gashi kinga ana to hotuna,
kin sa na rakoki kuma kin ki sakin jiki” Mumy tayi kasa da murya tace “Wllh tsoron kar tsohuwar can ta disga ni
nake Sadiya” a d’an fusace Sadiya tace “Don Allah ki tafi ni dai, kin sa duk munyi tsamo tsamo a nan kamar wasu
marasa gaskiya, dubi Hajiya Amina da ba son Heedayar take ba ita ma can cikinsu ke kuma kin kawo mu gefe don
Allah” Mumy tace “Toh bari in je” sosai Mumy tayi gathering courage ta karasa gun da su Heedayah suke tana
murmushin karfin hali tace “Ba mu yi hoto ba Heedayah….” da sauri kaka ta juya ta kalleta tace “Meye kuma hoto?
Kawarta ta riga ki ma ai, ke Heedayah ki tafi can kawarki na jiran ki kuyi hoto, ‘yar wajen Bulasawa ce fa kawar aka
ce” Mami dai ta dauke kanta, Gaba daya sai Ammi bata ji dadi ba ta dinga kallon kaka, Yakumbo da ta hakikance
kan kujera a wajen tace “To ma hoton me xa suyi ana xaune qlau idan ba gulma ba, mu ma kanmu da kika ganmu
nan guda daddaya muka yi da ita, da mai girma Gwamna sai ubanta na kaduna ne kawai suka yi hotuna yayi biyar,
ita kanta uwarta ta amana Rahinah sau uku suka yi…” Mumy ta juya sum sum ta bar wajen, Ammi ta hade rai tana
kallon Heedayah tace “Follow her immediately and snap” Heedayah ta nufi Mumy me hoton ya bi bayanta, Kaka
tayi ma Ammi wani shegen kallo tace “Dole ki xagemu da turanci ai tunda kin samu yar ki da rai, da a mace kika
ganta ai baxa kice taje su yi hoto da Rakiya ba” Yakumbo tace “Dalla rabu da ita, makirarra ce ai da kike ganinta,
banda makirci mu xata gwale” Ammi dai bata kallesu ba, Yakumbo tace “Toh wai ni banga sirkin nawa ba” Kaka
tace “Toh shi Junaidu ai ba ya shiga mata, yana can yana neman na kansa….” Sai kusan Magrib Heedayah suka
koma can gidan Mami gaba daya da su Ammi da kaka da Yakumbo, tunda suka dawo bata sakko parlor ba har bayan
isha, Mami ta shigo dakin jin shirun yyi yawa ta sameta kwance, ta karasa gadon ta xauna kusa da ita tace “What’s
wrong Heedayah? You don’t look happy today, upon it’s a great day for you… ur parent, love ones and well wishers
are all here today because of you” Heedayah ta mike xaune bata ce komai ba, Mami tace “Talk to me dear, meye ke
damun ki?” Kuka ta fashe ma Mami, Mami ta dinga kallonta da mamaki tace “Meye haka?” Ta rungume Mami cikin
rawar murya tace “Mami he told me xai dawo ranan graduation dina kuma ban gansa ba” Mami tayi shiru, bayan
kusan second talatin ta dago ta a hankali tace “You mean Khaleel?” Heedayah ta gyada mata kai, Mami tayi kasa da
murya tace “But ae bai san yau graduation din naki ba ma….” Hawaye na sauka idon Heedayah tace “It’s a year and
3 months now kuma bai dawo ba, his line isn’t going through till today…” Mami ta share mata idonta tace “In sha
Allah he is fine dear, kuma xai dawo da yardar Allah, kullum ina addu’an Allah ya karesa da kariyarsa ya dafa
masa…” Heedayah ta gyada kai bata dai ce komai ba, Mami tace “Now kiyi sllh ki sakko downstairs, ur mum, step
mum, relatives are all here for you, Ko kina son su gane wani abu ne?” Heedayah ta girgixa mata kai, Mami tace
“Good, do as I say now” Heedayah ta sauka gadon a hankali ta wuce bandaki Mami ta bi ta da ido, tun da Khaleel ya
tafi yau shekara daya da watanni ita ma rana daddaya ne baya fado mata kuma kullum sai ta sa shi a addu’arta, kuma
tana jin tana kewarsa sosai, sai da Heedayah ta fito bandaki Mami ta mike ta fita dakin. Heedayah na xaune saman
darduma bayan ta idar da sllh ta jinginar da kanta jikin gado tayi nisa tunanin da take aka bude kofar dakin, F
arida
ce ta shigo, ta karaso inda take xaune ta xauna gefen gado tana kallonta, Heedayah ta daga kai ita ma tana kallonta, Farida tayi kasa da murya tace “Congrats Heedayah, Allah ya sanya alkhairi” Heedayah ta sakar mata murmushi tace
“Thank you Sis, ya lectures?” Farida tace “Alhmdllh” Shiru duk suka yi, Farida ta mike ta fita dakin Heedayah ta bi
ta da ido, bayan fitar Farida Heedayah ta sake lulawa duniyar tunanin da take, hawaye ya sakko idonta ta sa hannu ta
goge a hankali ta jawo wayarta ta sake dialing number Khaleel duk da ta san baxai shiga ba, hade kanta tayi da
gwiwa bayan ta kira bai shiga ba hawaye na ci gaba da sakko mata, gaba daya shekara dayan nan da watanni bata da
wani sukuni bata ta6a tunanin xata yi kewar Khaleel har haka ba, she so misses him, to yaushe xai dawo?? Knocking
kofar da aka yi yasa ta dago kai da sauri ta share hawayen idonta, jin an sake knocking ta mike a hankali ta nufi
kofar ta bude, Junaid ne tsaye, sosai gabanta yayi mugun faduwa don kawai a fixge sai ta gansa kamar Khaleel din a
gabanta, lkci daya ta sunkuyar da kanta da sauri, Junaid yayi kasa da murya yace “Congratulations Heedayah, Allah
ya sanya alkhairi” Ta dago kanta ta sakar masa da murmushin karfin hali tace “Thanks Yaya” yace “I’m sorry I
couldn’t make it to ur graduation” Tace “Ba komai, ya aiki?” Yace “Alhmdllh” murmushi ya sakar mata yace “Just to
say congratulations” ta gyada masa kai a hankali tace “Nagode” Har ya juya sai kuma ya sake juyowa yana kallonta
yace “Are you alright” Cikin sanyin murya tace “Sure….” Yace “Ohk then sai da safe” Daga haka ya juya ya bar
wajen ta rufe kofar ta tafi ta kwanta saman gado tana jin wasu hawayen na taruwa idonta. Mumy ce ta bude kofar
dakin Shuraim a hankali ganin tun da suka dawo bai fito ba gashi har karfe goma da rabi, xaune ta samesa gefen
gado ya rike kansa, ta karasa tace “What’s wrong Aliyu?” Bai dago ba kuma bai bata amsa ba, tace “Aliyu” nan ma
yyi mata shiru, tace “Wai ba magana nake bane, meye haka Aliyu” Bai dago ba still yace “I am fine” tace “You are
fine?” Ya gyada mata kai, tace “Toh me ya hanaka fitowa ka ci abinci?” Shiru yyi bai ce komai ba, tace “Aliyu??”
Still ya ki cewa komai, juyawa tayi ta fita daga dakin, ya dago kansa da idanuwansa da suka sauya kala ya hau
saman gadon ya kwanta ya rufa da blanket, bayan fitarta da minti biyu sai ga Abba ya shigo dakin yace “Shuraim”
Ya yaye duvet din jikinsa ya mike xaune yace “Na’am” Abba yace “Are you alright?” Yace “I am” Abba yace
“Sure?” Kai ya gyada masa, Abba yace “To fito ka ci abinci” yace “I’m not hungry” shiru Abba yyi yana kallonsa,
can yace “Meet me at my parlor” Shuraim bai ce komai ba, Abba ya fita dakin, bayan kusan minti biyar ya sauka
saman gadon da kyar ya bi bayansa, Mumy na xaune main parlor ta kasa cin abinci gabanta, tunda ya kalleta sau
daya ya dauke kai ya nufi parlon Abbansa ta bi sa da ido, Xaune ya tadda Abba a parlon, ya xauna nan kasa, ba tare
da ya dago kansa ba cikin sanyi yace “Gani Abba” Abba na kallonsa yace “Tell me, meye damuwar ka?” Shiru yyi
bai ce komai ba, Abba yace “Talk to me Shuraim” Lkci daya idonsa ya kada, da mamaki Abba ke kallonsa, can yace
“Are you okay?” Shuraim ya kasa dago kansa, sai ga hawaye without him preparing for it, kasa ce masa komai Abba
yyi yana kallonsa da mamaki, bayan few minutes Abba yyi karfin halin cewa “Talk to me son, what happened…”
Girgixa masa kai kawai Shuraim yyi, sai kuma yace “Xan kwanta Abba, I will be fine” Yana fadin haka ya mike ya
nufi kofa Abba ya bi sa da kallo, bakin kofa ya tadda Mumy labe bai kalleta ba ya wuce dakinsa yana shiga ya sa
makulli ya hau gado ya shige Duvet. Mumy ta shiga parlon Abba da har lkcn was surprise, da damuwa tace “Ya
gaya maka Barrister?” Girgixa mata kai kawai Abba yayi, ta fashe da kuka tace “To kuma ka bar sa ya fita, ni ban
ta6a ganin yayi haka ba, ko matsala ya samu gun aikin, dama ni tun da ya xo nagansa kamar yana tare da damuwa na
dai yi shiru ne, plss Barrister ka koma dakin ka samesa ka lallabasa ya fadi me ke damunsa” Abba dai bai ce mata
komai ba ya bude laptop dinsa ya ci gaba da abinda yake.