HEEDAYA CHAPTER 45 BY By Khaleesat Haiydar

HEEDAYA CHAPTER 45 BY By Khaleesat Haiydar

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Mami ta mike tana rike da hannun twins din xata sauka kasa ita ma suka yi ido hudu da shi, tsaye tayi tana kallonsa, 

lkci daya Heedayah ta ji hawaye ya kawo idonta, yana murmushi ya karaso wajen walking slowly, yyi kasa da kai 

with respect ya gaida Mami, Mami ta sauke wani ajiyar xuciya tace “All this while bbu kira Khaleel? Sannan tafiya 

babu sallama” Ya kasa kallonta yace “Kiyi hakuri ban tafi da sim din da nake da numbers bane” Mami tace “To ka 

dawo lafiya?” Yace “Alhmdllh Ummi, ya gida” tace “Lafiya lau, ka shiga ciki, xan je Supermarket in dawo yanxu” 

yace “Toh in ajiye ku?” Tayi masa murmushi tace “Aa xan yi driving, motar ma na waje, kar ka damu ka shiga ciki” 

Yace “Toh Allah ya tsare” Mami ta kalli Heedayah da ta sauke kanta kasa tace “I will be back soon Heedayah, you 

stay back” Heedayah tayi shiru bata ce komai ba, Mami ta kama hannun girls din ta wuce, Heedayah bata yarda ta 

kallesa ba ta juya ta koma ciki, ya bi bayanta yana kallonta. Babu kowa parlon ya xauna saman kujera still looking 

directly at her, ita dai ta ki yarda su hada ido, yyi kasa da murya yace “Heedayah” ta kauda kanta ta wani daure fuska, 

mikewa yyi ya dawo kujeran dake kusa da ita yana kallonta a hankali yace “Ain’t you happy seeing me?” Hawaye ya 

kawo idonta ta rufe fuskarta da kujeran, yyi shiru yana kallonta, can yace “To kiyi hakuri, idan baki son ganina I will 

go now” Ta dago tana kallonsa cikin rawar murya tace “You just left, no calls, no text….” Ya kwantar da murya ce 

“But I told you before leaving Heedayah, kuma ni ban tafi da wayata ba…” ta goge hawayen idonta da ya ki tsayawa, 

cikin sanyin murya yace “But I missed you with every second, I think of you everyday….” Ta d’an kallesa, sai a snn 

taga irin ramar da yyi, ya sakar mata cute smile dinsa yace “I missed you Heedayah” Bata iya tace komai ba, shima 

yyi shiru, bayan few seconds yace “Kuma ai jiya ku ka yi graduation dinku, i kept to my promise…” Tace “How did 

you know jiya ne graduation dinmu?” Yyi murmushi yace “I knew because I care Heedayah, nayi kewar ki fiye da 

yanda kike xato, I had no choice but to stay far away…” Yakumbo ce ta shigo parlon tana kallon Heedayah tace “Aa 

fasa tafiya tayi da ke Rahinar?” Heedayah tace “Uhm sun tafi” Yakumbo na kallon Khaleel a hankali tace “Auu, 

dama Rahinah na da wani d’an bayan Junaidu, ahh ba shakka” Heedayah ta kalli Khaleel dake kallon Yakumbo shi 

ma, cikin ladabi ya gaisheta ta amsa tace “Toh ya aka yi baka xo shagalullukan jiya ba, sannan ni bata ce min tana da 

babban d’a haka ba….” Ya d’an yi shiru sai kuma yace “Nayi tafiya ne yau na dawo…” Yakumbo tace “Ba shakka, to 

ya sunan naka” ya sauke idonsa kasa yace “Khaleel” Yakumbo tace “Ba shakka, ita dai Rahinah Allah ya bata 

kyawawan yara maa sha Allah” lkci daya Yakumbo tayi tsit tana kallonsa da kyau tace “Aa wnn ai kamar na ta6a 

ganin ka ma…” Shi dai Khaleel bai ce komai ba don bai mance abinda tayi masa a gidansu Heedayah a Abuja ba, 

Yakumbo tace “Wllh sai fuskar yyi min kamar na ta6a ganinsa, toh shi Junaidu ba kullum yake dawowa gida bane, 

naga kullum ba a ganinsa a gida” Heedayah dai bata tanka ta ba ta mike ta tafi kitchen ta dauko masa ruwa da drink 

ta daura glass cup a tray din ta dawo parlon ta ajiye kusa da shi tana kallonsa, Yakumbo dai tayi wucewarta sama 

amma fa tana son tuna inda ta ta6a ganin Khaleel, Khaleel na kallon Heedayah murya can kasa yace “Ina kama da su 

Ummi ne?” Ta kallesa ta d’an yi murmushi tace “Aa, just the dimples” Shiru yyi yana kallonta, ta dau drink din ta 

mika masa, suka yi direct contact na ido, sosai gabanta ya fadi, shi ya fara sauke idonsa ya karbi drink din cikin 

sanyin murya yace “No matter the circumstances do not leave me plss Heedayah, idan kowa ma ya gujeni ke kar ki 

gujeni, I don’t know what will become of me…” Cikin breaking voice ya fadi haka, lkci daya taji jikinta yyi sanyi 

tace “Me yasa kake yawan fada min haka, kana tunanin akwai abinda xai raba mu ne?” Ya gyada mata kai a hankali 

yace “Sure Heedayah, amma kar ki bari hakan ya raba mu…” Sakkowa kasa yyi kasa a hankali kneeling down right 

in front of her, ta ja baya ta xauna tana kallonsa da mamaki, cikin sanyin yace “I have never fell in love sai da na 

sake haduwa dake 1 year and some months back Heedayah, ban san meye soyayya ba, ban san ya yake ba, I was raised with a strong harsh heart, sai dai ban bari hakan yayi fatali da tausayina ba, Ina da tausayi sosai duk da 

dakakkiyar xuciyata…” Shiru yyi yana kallonta da lumsassun idonsa, ita kuma taki dago kanta tana ta naxarin abinda 

ya fada, can ta dago tana kallonsa tace “Sai da ka sake haduwa da ni? Dama mun ta6a haduwa ne?” Ya sauke idonsa 

kasa yace “Ehh mun hadu a lkcn da bakya gani, a lkcn da baki da sauran gata… Naji tausayin ki sosai, wanda 

tausayin yasa nayi maki abinda na maki” Kallonsa take ko kiftawa babu, can tace “Ban gane ba, meye ka min?” Yayi 

kasa da murya ce “Ni ne na dauke ki a den din Kidnapper na fito da ke a kan Motorcycle na ajiye ki gefen hanya 

Heedayah, and your words to me then were ‘Are you leaving me?’ Ban kuma ce maki komai ba nayi wucewata na 

barki, kin tuna??” A tsorace Heedayah ke kallonsa da manyan idanuwanta, can ta fara ja baya tace “Kai Kidnapper

ne?” Ya girgixa mata kai da sauri as confused as he is yace “Noo Heedayah, kawai na kubutar da ke ne daga wajensu 

sbda tausayin ki da naji” Kallonsa take ko kiftawa bbu xuciyarta na bugawa, cikin sanyin murya yace “Ni ba su bane 

Heedayah, na dai taimakeki ne sbda kashe ki xa su yi” Ta hadiye abu da kyar tace “To ya aka yi kasan ina wajen, I 

was thinking daji ne, me ya kai ka wajen har ka san da ni??” Ya girgixa kai da sauri, da farko ya rasa abun cewa, sai 

kuma yyi saurin cewa “Na xo wucewa ne da Bike dina shine na dauke ki….” Bata kuma cewa komai ba ta sauke 

idonta kasa, lkci daya jikinsa yyi sanyi sosai don ya san bai gamsar da ita ba, bata gamsu da bayaninsa ba, gaba daya 

kuma ya rasa me xai ce mata, can a hankali yace “Heedayah” ta dago da sauri ta kallesa yace “Tunanin me kike?” Ta 

girgixa masa kai ta mike tace “Aa ba komai, xan karasa wanke wanken da nake yi a kitchen” bata jira cewarsa ba ta 

wuce kitchen din da sauri, ya bi ta da kallo xuciyarsa na bugawa, Heedayah na shiga kitchen ta kulle kofar ta jingina 

jiki gabanta na wani irin faduwa flashback din shekaru shidda da suka wuce da muryarsa na sake dawo mata, sai 

yanxu ta tuna inda ta ta6a jin muryarsa, shi ne wanda ya kama hannunta ya saka mata bread bayan an sanar masa 

bata gani a lkcb, snn shi ya xo ya dauketa ya sa ta a bike ta tuna ihun da ta dinga yi and he told her he have gun 

wanda haka
n ya tsoratata sosai a lkcn, yess muryarsa ce, ji tayi gaba daya jikinta ya dau rawa kafafuwanta sun kasa 

daukarta, ta fi minti biyar a haka can ta bude kofar kitchen din a hankali ta fito parlon, yana durkushe yanda ta bar sa, 

jin an bude kofar kitchen din ya juya ganinta yace “Heedayah….” Bata ko kallesa ba ta wuce sama da gudu xuciyarta 

na bugawa, ya bi ta da ido… Sai kuma ya dafe kansa da yyi masa nauyi lkci daya, a haka Mami ta shigo parlon ta 

samesa, ya dago da sauri, tace “Lafiya Khaleel??” yyi murmushin karfin hali yace “Aa ba komai, sannu da dawowa” 

Tace “Yauwa, ina Heedayar?” Yace “Ta wuce sama yanxu” Mami ta sake hannunsu su Ashnaah ta nuna masu sama 

duk suka wuce, ta xauna tana kallon Khaleel tace “Is everything okay?” Ya sauke idonsa kasa ya xauna nan kasa 

yace “In sha Allah” Tace “Baka sha lemon ba?” Ya kalli drink din da Heedayah ta ajiye masa yace “Xan sha” tace 

“Ko a kawo maka abinci?” Ya girgixa mata kai yace “Alhmdllh na ci abinci” Ita dai sai kallonsa take, bayan few 

seconds yace “Dama ina jiran ki dawo ne, xan wuce” tace “To xaka shigo anjima” ya gyada mata kai yace “In sha 

Allah” ta mike tace “Toh shkkn Khaleel, bari a kira Heedayar” da sauri yace “Aa mun yi sallama da ita” Mami ta 

juya tana kallonsa ya mike yace “Nagode Ummi, sai anjima” daga haka ya nufi kofa ta bi sa da kallo har ya fita, ta 

koma ta xauna a hankali, ko kadan bata gane feeling din da xuciyarta ke samu idan taga wnn bawan Allah, muryar 

Yakumbo taji tana cewa “Rahinah ashe kina da babban d’a dama bani da labari, wnn ma har ya fi Junaidun nutsuwa 

da kunya naga” Mami ta kalleta tace “Wa kenan?” Yakumbo tace “Au har ya tafi kenan, nan na samesa tare da 

Heedayah” Mami tayi shiru, can tace “Aa ba d’a na bane, ya xo gaisheni ne” Yakumbo tace “Toh ai d’an d’an uwanka 

ko yar uwarka naka ne, jini ai ba wasa bane, ga kamanninku nan tare da shi kuma kice ba d’an ki bane, kuma ko ba 

komai suna yanayi da Junaidu sosai, ke kanki ma idanunku iri daya ne da nashi, to ita kuma Aisha bata da niyyar 

dawowa ne ta debi sojoji suna gadinta tana xaga gari don neman suna, kai samun waje ma dai bai yi ba wllh, tun 

safe an shanya mu ba alamar wucewarmu fisabilillahi, ita kuma wancan tsohuwar me gilla karya har yanxu bata iso 

ba ta kuma ce min da sassafe xata xo, Amadi dai yace a taho da ita, Kar mu je bbu ita ya kullace mu tunda ta nace 

sai ta bi mu” Mami dai bata ce komai ba don abinda ya dameta ya tsaya mata a xuciya daban. Farida ta rufe laptop 

dinta tana kallon kofar bathroom don kusan minti talatin kenan da shigan Heedayah har yanxu bata fito ba, har 

lekowa Mami tayi daxu tana tambayar Heedayar tace mata tana bayi, kuma ita bata ji alamar wanka take ba, mikewa 

tayi ta isa bakin kofar ta kwankwasa, jin bata amsa ba ta bude kofar bathroom din, durkushe ta ganta bandakin ta 

hade kanta da gwiwa, da mamaki Farida ta karasa ciki ta dago kanta tace “What’s wrong Heedayah” hawaye ta gani 

sha6e sha6e fuskarta, Farida ta buda ido tace “Subhanallah, me ya faru? What happened?” Heedayah ta fashe da 

kuka a hankali, Farida ta dagota hankali tashe tace “Ki gaya min me ya faru Heedayah, me aka maki?” Heedayah ta 

rungumeta tana kuka sosai amma ta kasa cewa komai, Farida ta fito da ita daga bandakin ta xaunar da ita gefen gado 

tace “Don Allah ki gaya min menene? An maki wani abu ne” cikin rawar murya Heedayah tace “I don’t want to say 

anything about it Farida…” Sai kuma ta fashe da kuka sosai, cike da damuwa Farida tace “Don’t you trust me 

Heedayah, talk to me plss” Heedayah ta runtse ido trying hard not to burst out again tace “Khaleel” Farida ta bude 

ido tace “What about him? Is he back??” Da kyar tace “Am thinking….” Sai kuma tayi shiru wasu hawayen na 

taruwa idonta, Farida tace “What are you thinking?” Rungume Farida tayi cikin kuka sosai tace “He is a kidnapper 

Farida, wllh kidnapper ne” Still Farida tayi jin abinda Heedayah tace, can ta dagota with so much shock tace “How 

did you know?? who told you that?” Heedayah tace “Shine ya fito da ni daga wajen kidnappers ya ajiye ni bakin titi years back” Heedayah bata kai Farida tsorata ba, Banda xare ido bbu abinda Farida ke yi kamar warce tayi ma sarki 

karya, cike da karfin hali tace “Who told you all this Heedayah?” Hawaye na sakko ma Heedayah tayi ma Farida 

bayanin komai, Farida da tayi mugun tsorata tace “Is he still in this house?” Heedayah ta buda mata hannu alamar 

bata sani ba hawaye me xafi na sakko mata, Farida xata mike Heedayah ta rikota tace “Promise me this will be a 

secret between us, don girman Allah kar ki gaya ma kowa not even Mami” hawaye ya kawo idon Farida ta koma ta 

xauna tace “Why secret Heedayah? Xa ki ci gaba da alaka da d’an kidnapper ne? What will be our faith?” Heedayah 

ta fashe da kuka tace “Not at all, baxan ci gaba ba, amma….” Farida tace “Amma me?” A hankali Heedayah tace 

“Yasa na fara sonsa, I don’t know how that happened all of a sudden, ya cuceni ya sa min sonsa” Farida ta xaro ido 

tace “So xa ki ci gaba da sonsa kenan???” Da sauri Heedayah ta girgixa kanta tace “I hate everything about him now, 

he is disgusting, I now understand why I saw gun with him a gidansa ranan da daddare, I now understand why he is 

this rich with so many cars and houses, I now understand me yasa baya son daga kiransa a gabana, I now understand 

why yake yawan ce min I shouldn’t leave him no matter the circumstances, but I have to leave him, kuma na bar sa 

har abada, na tsani komai nasa, nayi da na sanin sake haduwa da shi da kulasa da nayi, dama shi ya rabani da 

iyayena tun ban san kaina ba, ya kuma maida ni wajensu after many years sbda selfish interest dinsa” kuka take 

sosai tana girgixa kanta, Farida ta kamo hannunta amma ta rasa abinda xata ce mata, ita ma hawayen take sosai don 

tun ba yau ba tasan Heedayah ta fada son wnn mutumi, Mikewa Heedayah tayi ta tafi gun kayanta ta fara hadawa 

tace “I will be leaving with Ammi today….” Jikin Farida yyi sanyi sosai sai a snn ta gane sbda Khaleel Heedayah 

tace baxata koma Kano da Amminta ba after her graduation, sbda tana anticipating dawowarsa. Da ido kaka ta dinga 

bin Shuraim da ya gama saka kayansa a jaka tace “Yau naga jaraba ina ta magana mutumi ya mayar da ni 

mahakuciya, dubi fa yanda ka zabge kamar me wata cutar can warce bamu sani ba, tunda iyayenka gantalallu ne ai 

ni ba gantalalliya bace baxan bari ka cutu ba, idan ma wani abun ke damun ka sai ka gaya min in san nayi tun wuri, 

bbu wajen wani shegen aiki da xaka koma, to banda kai wa ke gareni a duniyar yanxu, dama ni da kai nafi sabawa a 

kan su Amadu ma, kawai shaidan ne ya shiga tsakaninmu, shekarunka nawa a wajena kafin algungumar uwarka ta 

amshe ka ta karfi da yaji” Shuraim ya juya yana kallonta yace “Ba abinda ke damuna, bana jin dadi ne kawai, Amma 

yanxu Alhmdllh, xan koma bakin aikina” ta mike tace “Allah ya tsine ma aikin, idan ma xaka bini in kaika asibiti ka 

bini wllh, tunda shi Umaru bai daga kirana ba shi yasani, shi kuma Amadu xai ga barbadin bala’i yanxun nan kuwa” 

daga haka ta fice daga dakin, xaunawa Shuraim yyi gefen gado jin kansa na juya masa ya dafe kan xuciyarsa na 

bugawa, kaka na shiga parlon Abba ta samesa ya gama shiryawa xai wuce aiki, cike da bala’i tace “Amadu ba gwara 

abu ya sameka ba da ya samar min Shureen, uban me ka ta6a tsinana min tunda na haifeka dama, wato bakin ciki da 

rayuwar da Shureen ke yi a duniya kake yi ban sani ba, ban da bakin ciki ya xa ayi d’an ka bashi da lafiya amma ko 

a jikinka ka wani shirya xaka fi
ta inda ku ke giggilla karyar ku…” Abba dai kallonta yake kafin yace “Baaba 

Shuraim ba yaro bane, idan yana ga barin damuwarsa a xuciyarsa ne mafi alkhairi garesa ba sai a kyalesa ba” Kaka 

tace “To anki kyalesan, kuma aniyarka ya bika wllh, in sha Allah bbu abinda xai samar min shi….” Abba ya d’an yi 

murmushi bai dai ce komai ba, sarai yasan meye damuwar son din nasa, ta juya ta fice daga parlon ta koma dakin 

Shuraim, Mumy dai na ta xaune main parlor tana ta addu’ar Allah ya sa son Heedayah ne ya sa shi damuwar nan, 

kuma Allah ya sa ya sanar ma kaka komai ya xo cikin sauki kenan. Zayyad ne durkushe an daure hannunsa da igiya 

ta baya, oganninsu ne tsaye kansa ko wanne na nuna sa da bindiga, Zayyad ya kalli sauran colleague dinsa dake 

tsaye gaba daya a katon parlon, Oga Manga ya karasa gaban Zayyad da katon muryarsa yace “Brainiac ya sauka 

kasar nan jiya, yana ina??? We are asking you this for the last time Zayyad” Zayyad ya juya da jajayen idonsa yana 

ma Salim wani irin kallo, Oga Arne ya kai masa kyakkyawan naushi a fuska cikin tsawa yace “Baxa ka bamu amsa 

ba??” Zayyad yace “Ni bamu hadu da shi ba har yanxu Oga, na gaya maku kun ki yarda” Oga Bala na nuna masa 

wayarsa yace “Amma kun yi waya ko….” Zayyad ya kalli wayarsa da Ogan nasa ke nuna masa yace “Ehh” Oga 

Manga yace “Ina yace maka yake?” Zayyad yace “Naje gidansa kamar yanda ku ma ku ka je, ban samesa ba gidan a 

kulle yake” Salim yace “Amma a waya daxu yace maka xai je gidan budurwar tasa” Zayyad ya sake jefa masa wani 

kallo, Oga Arne ya hauresa yace “True or false??” Zayyad yace “Ai ban san gidan ba nima” Oga Arne yyi wani 

dariya ya koma kan mighty chair dinsa ya xauna ya daura kafa daya kan daya yace “Ku tafi da shi ku tabbatar ya 

fadi inda gidan yake, snn a tafi a dauko mana mahaifiyar ita yarinyar yau din nan” Wani kara Zayyad yyi ya buga 

tsalle ya dawo da hannunsa dake daure ta baya gaba, ya haure Oga Arne dake kan kujera da kafarsa snn yyi hanyar 

bedroom da gudu ya bude wani daki ya shiga ya sa makulli yana huci, da sauri ya tafi gaban mirror ya fiddo karamar 

wayarsa ya shiga dialing number din Khaleel, yana jin suna kokarin balle kofar gaba dayansu, har wayar ya katse 

Khaleel bai dauka ba, gaba daya Zayyad ya hada xufa, ya sake kira praying hard Allah ya sa Khaleel ya dauka sai 

gashi ya dauka, da sauri Zayyad yace “Brainiac ka dauke Barrister din nan a gidanta with every other person, su Oga 

Arne xa su je gidan yanxun nan, I am giving them the address nowwww…..” yana fadin haka ya katse wayar ya 

kashe gaba daya ya jefar ta bayan mirror ya durkusa a dakin ya sunkuyar da kansa kasa, suna 6alla kofar Zayyad ya 

dago da sauri nan ya zayyano masu full address din gidan Mami ya kara da cewa “Xan iya kai ku gidan ynxu ma….

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *