HEEDAYA CHAPTER 5 BY By Khaleesat Haiydar
Www.bankinhausanovels.com.ng
Tun da Hajiya Maryam suka dawo gida da kawayenta take kuka kamar ranta xai fita, ji take kamar ta bude ido taga
cewar duk mafarki take, ya xa ayi Barrister ya mata kishiya bata mutu ba?? Hajiya kyauta tace “Ke Maryam bari ki
ji in gaya maki, idan xaki share hawayen ki ki san nayi ki share, don 6ata lkcn ki kawai kike, wllh wannan kukan
baxai fisshe ki ba, wajen nan dai da baki son xuwa dolen ki nan xa aje da ke yau a san nayi, don wnn mata ni dai da
kamar wuya mijin ki ya fasa aurenta duk haukan ki kuwa, na farko in dai kyau ne baxa ki nuna mata komai ba, ke
diplomar ma da ya kika kare? Ita kuwa lawyer ce fa me xaman kanta, kinga kenan ta kure karatu, ga shi da gani dai
kin san ba cikin wahala take ba tana da kudin ta, ke dake buga buga ki raruma gun miji fa?? ni wllh ba karamin
kwarjini matar ta min ba ma, da ba ku fito ba dama ni wucewata xan yi kar ta sa a daure mu kamar yanda tace”
Hajiya Maryam ta katse ta a fusace tace “Ni fa da ku ke gani nan babu abinda ya isa kai ni gun malami a duniyar nan,
ku dai ku bar ni inyi ta kai na kawai idan baxa ku bani shawara ba, ni kadai raina na ishi kowa, wllh karuwar nan
baxata shigo min gida a matsayin kishiya ba, muna nan da ku kuma xa ku ce na fada, ita kuma wnn makauniyar
dama sai dai ta kara shiga duniya wani ya tsince ta a wani garin amma ba mijina ba….” Tana kai wa nan ta mike ta
dau gyalenta tana share idonta, Hajiya Sadiya tayi wani dariya tana kallon kyauta tace “Bar ta, xata dawo ta same
mu ne ai” Ficewa Hajiya Maryam tayi daga dakin rike da makullin motar ta….. Direct gidan Dr Umar ta nufa, yau
dai ko shiga bangaren matan gidan bata yi ba ta nufi gun kaka, da sallama ta bude kofar parlon kaka dake uwar daka
ta fito da sauri tana cewa “huuu Ko waye don Allah ya share kafarsa ga tsumma na ajiye bakin kofa, wllh kazamai
ne matan gidan ko sharan kirki basa yi a makeken parlon nan nasu sai a tattako a xo a yasar min a nawa parlon….”
Hajiya Maryam ta dinga goge kafarta a tsummar kamar an aikota, kaka tace “Aa Maryam daga ina haka da sassafe
kuma” Ta karasa cikin parlon ta xauna kasa cikin sanyin murya tace “Daga gida kaka, ina kwana” Kaka ta xauna
tace “Lafiya dai naga idonki a kukkumbure ko Balaraba ce ta rasu??” Ta fashe da matsanancin kuka tace “Ba lafiya
ba wllh kaka….” Kaka tace “Ikon Allah me ke faruwa Kuma? Ni dai jiya Amadu ya shigo min da rana wai ya xo
gaisheni a nan kuma yake ce min wai aure xai kara har ya samu matar yar kaduna ce, ni dai nace masa ba ruwana,
ana xaune lafiya fitina ya shigo ciki, to daga haka ni bai ce min ga abinda ke faruwa a gidansa ba….” Cikin kuka
sosai Mumy tace “Abinda ya kawo ni kenan ma kaka, wai aure fa xai kara….” Kaka ta saki salati tana tafe hannu
tace “Ohh ni na ga abinda ya isheni ni Rahamar ubangiji, me Amadu ke nema a duniya da xai kara aure ana xaune
qlau, ni dai yana gaya min ce mashi nayi ba ruwana, don bn san kan xancen ba….” Mumy ta share idonta tace “Idan
ma sbda wnn baiwar Allahn ce ya kawota kawai xan riketa na amince” iyakar wnn furucin da Mumy tayi bakinta,
don kuwa ta sha alwashin ko an fasa auren aka kawo mata Heedayah sai ta sake lulawa da ita wani duniyar daban,
duniyar ma na kauye, can xata sa aje a wurgar da ita don ma kada mistakenly wani me rufin asiri ya dauketa har ya
taimaka mata, a yanxu dai duniya bbu wanda taji tana tsana kamar wnn yar yarinyar, har ta mance rabon ta xubda
hawaye ta shiga tashin hankali da xai hanata bacci sai a dalilin Heedayah, Kaka tace “Aa ni ya kawo min ita ma nan
kawai xan riketa, kar a ja maki kaffara kina xaman xamanki, dama bbu me min wanke wanke da shara tsigalallun
yaran nan duk ba kulasu nake ba ta kaina nake” Mumy tace “Makauniya ce fa kaka” kaka tace “To makafi basa
wanke wanke da shara aka ce maki Maryam, ai dai naga ba kuturwa bace, sai in kada mata kumfar in sa mata ruwan
dauraya in ajiye mata kwanukan in xaunar da ita ta wanke min su tass” Mumy tace “Aa kaka wahala kawai xata baki,
ni din dai xan riketa, ai d’a na kowa ne” Kaka tace “Atoh dai, ki kwantar da hankalin ki kawai, bbu wani xancen kara
aure in dai da raina tunda xaki riketa, to idan ba toxarci Amadu ke son mana ba meye kuma karin aure ana xaune
kalau, wannan ne kuma bai haifu ba gaskiya don baxan yrda ba” Mumy taji hankalinta ya d’an kwanta, tana share
idonta tace “Toh shkkn kaka nagode” Kaka tace “Haba godiyar me kuma, ai yi ma kai ne, yanxu shawarar da xan
baki a nan shine ki dau kayan ki kala daya ko biyu ki tafi gidanku, idan ba haka kika yi ba Amadu baxai dawo
hankalinsa ba, ki tafi da fitsararrun ‘ya yan nan naki ki bar masa gidan ba kowa sae kujerunsa da tv, nan xaki ga ya
shiga taitayinsa wllh, kaddai ki gaya ma wnn dunkum din d’an naki kudurin ki don wllh hana ki xai yi ya cuce ki, ki
bar masu gidan shi da ubansa kawai” Mumy da ke kallon kaka tana jinjina shawarar ta a ranta, tayi murmushi tace
“Gaskiya ne kaka, hakan xan yi in sha Allahu ina komawa kuwa” Kaka tace “Atoh maxa tashi ki tafi tun yanxu ki
hada hada kayan, ai mu xamaninmu haka muke yi, idan miji ya musguna maka ka hada kayanka ka bar masa gidan
sa, xo ki ga yanda hankalinsa xai tashi kuwa….” Mumy ta mike tace “Toh sai anjima kaka, nagode sosai, Allah ya
kara girma, sai mun yi waya” daga haka ta fita, kaka ta bi ta da kallo har ta rufe kofa sannan ta ta6e baki ta juya ta
koma cikin dakinta tana cewa “To ai idan Amadu ya fasa auren nan ma ni sai naji dalili wllh, da kaina xan kai
sadakin auren, huuu wai ba kunya ba tsoron Allah matar da ke bari na da yunwa me saka min nama tsoka daya ce
wannan fa jama’ah, Ehh lallai duniya ya lalace…..” Da yammacin ranan Abba ya tafi gidan Barrister Rahinah don
sake tabbatar da abinda ta gaya masa a waya da safe, nan ta nuna masa she is serious, ko da wasa bata sanar masa
cewar Hajiya Maryam ta xo gidanta ba, yana murmushi yace “Toh nagode Rahinah, in sha Allah gobe xa mu je can
gun kawun ki…” Mami tace “Allah ya kai mu….” Basu wani jima ba ta koma cikin gida don tace masa girki take, shi
kuma ya wuce. Mumy na komawa gida dama ta hada kayanta ynda Kaka tace mata, ta hada har da na su Khadijah da
Rabi’ah ta bar gidan, makarantar su ta fara biyawa ta sanar masu inda xasu sameta idan an tashi sannan ta wuce
gidan kanwar Mahaifiyarta dake nan kaduna. Mami ce xaune study area dinta tana kallon files din gabanta, gaba daya mood dinta isn’t okay, ta kasa gane ko she is making the right decision marrying barrister, har xuciyarta tana
son taimakon Heedayah amma ba irin taimakon da xai kai ta ga aure ba at this stage, ta jinginar da kanta da kujera
tana tunanin ta ina xata fara sanar ma yaranta wannan xance me girma, amma kuma ai idan bata Aure Barrister ba ta
6ar matarsa ta ci bulus kenan, ta shigo har gida ta yi mata cin mutunci sannan ta bar ta haka nan, muryar junaid taji
yace “Mami aiki kike?” Ta daga kai da sauri ta kallesa don bata ji shigowansa ba ma, ta mayar da glass din da ta
sakko idonta tace “Sure, ka shigo kenan” yace “Nayi sallama naji shiru” ya ja kujera ya xauna yace “Mami this two
days naga kamar kina da damuwa, meye matsalar ki gaya min” shiru tayi kuma bata daga kai ta kallesa ba, yace
“Talk to me Mami” ta sauke ajiyar xuciya tace “Junaid barrister ne ya xo min da xancen da ya saka ni cikin damuwa
kwarai, I don’t know I am really confuse junaid….” Yana kallonta sosai yace “Me ya faru Mami?” Ta kuma yin shiru,
bayan few seconds taga bbu wani amfanin boye boye kuma, nan ta sanar ma d’an nata intention din Barrister Ahmad
a kanta, junaid bai iya ya ce komai ba na kusan second talatin, can dai yyi gathering courage ba tare da ya kalleta ba
yace “Toh, idan hankalin ki ya kwanta da hakan Mami, Allah ya sa shine mafi alkhairi a gare mu baki daya” kallonsa
kawai take bata ce komai ba, ya mike yace “Na xo daukan system dina ne” daga haka ya wuce sama ta bi sa da ido,
dakin Farida ya bude, ya ga Heedayah kwance edge din gadon tana bacci, riga ne da wando jikinta kamar dai ‘yar
turawa, he wondered if she is neva tired of sleeping, karasawa cikin dakin yyi walking slowly ya isa kusa da gadon
yana kallonta, a hankali ya mayar da ita tsakiyar gadon ya gyara mata dogon gashinta dake rufe idonta, jin an bude
kofar dakin ya mike tsaye da sauri, kafin Mami tace komai yace “A gefen gadon na sameta….” Mami ta gyada masa
kai kawai, ya juya ya fita dakin…. Da daddare Barrister ya tafi gidan Yayansa, bayan sun gaisa da kaka yace “Na je
can gida na tarar Maryam ta kwashe yara sun bar gidan Baaba” Kaka tace “Kila ganin gida taje….” Shiru yyi yana
kallon mahaifiyar tasa, kaka tace “Toh ina dama xata je idan ba ganin gida ba, ai ta kwan biyu bata je ba, kaga kai
kuma kafin ta dawo sai amaryarka tayi kokari ta tare xuwa nan da ranan juma’ah tunda yau talata, wannan makeken
bangaren da nake sauka sai ka sa a gyara ma amaryar ayi fenti da komai da komai kawai, ita kuma Maryam ban ce
ka kirata ba balle kace xaka mata fada, uwarta taje gani….” shigowar Baffa ya sa Kaka tayi gum, ta sauya xancenta.
Ranan juma’ah aka daura auren Barrister Ahmad da Barrister Rahinah, though they did it in a confidential way, bbu
wani gayya, duk abubuwan nan dake faruwa Hajiya Maryam na can ta lula xuwa gidan wata childhood frnd dinta a
Zaria tare da su Rabi’ah wai kar barrister ya biyota gidan kanwar mamarta, ita a dole sai ta basa wahala, Shuraim
kadai take kira don samun update, sai dai me? Shi ma bai san da auren ba sai a ranan juma’ar, shi ma kuma da asuba
Abban nasa ya sanar masa a masallaci da suka hadu, he was so shock ya ma kasa cewa Abban nasa komai, haka nan
Abba ya wuce ya bar sa wajen a tsaye, ita kanta Hajiya Amina mum din su Sudais ranan ta ji xancen daurin auren
daga bakin Baffa da safe, nan tayi ta kiran Hajiya Maryam amma wayarta a kashe, bata fasa kira ba har sai da aka
daura wnn aure amma bata samu Mumy ba….. Washegarin ranan da ya kasance Saturday Mami xata koma can gidan
Barrister Ahmad, shopping suka tafi tare da Heedayah, Farida da First daughter dinta Amira dake aure a Abuja, su
dai sun yi farin ciki da auren mahaifiyar tasu kilan hakan ya rage mata damuwa sosai, don duk sun san barrister
Ahmad, A cikin mota Amira tace “Kinga yanxu Mami sai ki bar ni mu tafi da Farida sai ta dinga xuwa maki hutu
kawai ko” Mami dake ta tunanin makomar autar tata tun bayan da aka daura aure don bata ta6a jin tafiya da ita gidan
barrister ba, baxai ma yiwu bane, ta kalli Amira tace “Alright dear” Amira na dariya tace “Kinga cikin ruwan sanyi
kin bani ita” Babban shopping mall Mami tayi parking suka fita, Amira na rike da hannun Heedayah suka shiga ciki
gaba daya, shopping sosai Mami tayi, yaranta na taya ta, Mami da ta lura Heedayah ta gaji da jan ta da ake ta yi, duk
ta yi wani laushi, kana ganinta kasan ko kadan bata sa6a da wahala ba koma wani iri, Mami tayi murmushi ta samu
kujera nan kusa da counter ta xaunar da ita sannan ta koma gun yaranta, a kan idon wani mutumi dake tsaye shelf
din turare yana diba, ya cire glasses dinsa yana kallon Heedayah sannan ya kalli Mami da ta sha corner xuwa gun su
Amira….Mutumin ya ajiye turaren hannunsa ya isa gun Heedayah ya tsaya dab da ita yana kallonta bayan yyi make sure bbu
me kallonsu yace “How are you?” Juyowa Heedayah tayi da sauri, lkci daya ta mike tana waige waige, shi dai bai
sake cewa komai ba yana kallonta, kamar xata yi kuka tace “ka dawo xaka kai ni gun Ammina ne?” Jin shiru, ta kai
hannu to see if he is still there, komawa gefe yyi yace “Ina Ammin taki take?” Tace “A can gidan Yakumbo mana”
xai yi magana ya ga Mami ta tsaya daga inda take tana kallonsu, lkci daya ya juya ya koma shelf din turaren da ya
baro, Mami ta nufo Heedayah da sauri ta kamo hannunta tace “Me yake ce maki?” Heedayah da ta 6ata fuska xata yi
kuka tace “shine ya sa ni a bicycle muka tafi…” Mami ta juya wajen da taga Mutumin ya tafi taga wajen wayam, da
ido duk ta bi wajen amma bata ga alamarsa ba, Heedayah da hawaye ya cika idonta tace “Baya son inje wajen
Ammina” kama hannunta Mami tayi suka bar wajen har sannan tana kalle kallen mall din ko xata ga wannan
mutumi, sai da suka biya abubuwan da suka siya sannan suka tafi mota, Mami na kallon Heedayah tace “But ya
akayi kika san shi ne?” Tace “Na ji voice dinsa, shine….” Mami bata kuma cewa komai ba har suka bar shopping
mall din. Bayan Magrib Shuraim ya iso gida, rabonsa da gidan tun jiya juma’ah da safe, dama ko wajen daurin auren
Abban nasa ma bai je ba, sau daya ya kalli motar Abban nasa dake parking space ya dauke kai, ya fita motarsa ya
rufe ya wuce xuwa entrance din gidan, bbu kowa parlon, ya tafi parlon Abbansa, sallama yyi still standing at the
door, Abba dake rike da makullin mota alamar xai fita ne, ya amsa masa sallama sannan ya bude kofar ya shiga,
Heedayah ce xaune parlon kan lallausan carpet da plate din watermelon a gabanta tana sha, kasa karasawa parlon yyi
tun da ya ga Heedayah, sai da Abba ya daga kai ya kallesa sannan cike da kasaita ya karasa ciki, gaba daya bbu wani
annuri a fuskarsa, can gefe ya duka yace “Ina yini Abba” Abba yace “Lafiya lau” mikewa yyi ya nufi kofa Abba ya
bi sa da ido har ya fita, a compound Abba ya samesa xaune shi dai bai ce masa komai ba ya fita da motarsa da nufin
maida Heedayah can gidan Mami. Washegari lahadi Abba ya tafi can gidan Mami don ranan xasu tafi gidan Baffa
Mami su gaisa da kaka, Abba ne ke driving Mami na gaban motar Heedayah kuma na baya a xaune, jifa jifa suke
magana da ya shafi field din aikinsu, Mami dake danna wayarta ta kalli barrister tace “Hope ba dadewa xa mu yi ba
wajen mama coz xa mu yi sallama da Amira nan da sha biyu xa su wuce” Abba ya d’an yi shiru kafin yace “I mean it
Rahinah… Farida baxata je Abuja ba, are you trying to show ni ban isa riketa ba” Mami tace “A’a ae hutu xata je, in
sha Allah xata dawo soon…” Yace “Wani hutun?” tace “Mid term….” Yace “Am damn serious baxata xauna Abuja
ba” Mami tayi murmushi tace “To shkkn” a haka suka isa gidan Baffa, bayan Abba yyi parking ya juya yana kallon
Heedayah da tayi lamo jikin motar, yace “Heedayah” ta xauna da kyau da sauri tace “Abba” murmushi yyi yace
“Hope
ba bacci xa ki yi ba” ta girgixa kai tace “A’a” Ya kalli Mami da ke kallonta ita ma, Mami tayi murmushi tace
“Heedayah is more than lazy, tafi son tayi ta bacci” Shiru Abba yyi bayan few seconds yyi kasa da murya yace
“Look Rahinah… my mother can be very weird at times kin san ynda tsoffi suke, I know she will welcome you
wholeheartedly but…. Akwai halin tsufa dai, so get prepared Mamin Heedayah and Farida….” murmushi kawai tayi,
ya bude motar ya fita, ita ma ta fita ta sakko da Heedayah, main parlor Mami ta xauna tana amsa gaisuwan da Yan
matan gidan ke mata, Hajiya Hauwa dake kitchen ta fito don ganin su waye, ganin Abba tace “Sannu da xuwa
barrister” yace “Sannu Hajiya Jiddah ya gidan” tace “Gida Alhmdllh” da fara’a tana kallon Mami tace “Sannu da
xuwa Hajiya, sannun ku da xuwa” Mami na murmushi tace “Yauwa sannu, fatan mun same ku lafiya” Hajiya Hauwa
tace “Alhmdllh, you are welcome to the family” murmushi Mami tayi tace “Thank you” Hajiya Hauwa ta tafi dauko
ruwa, Abba ya mike ya nufi bangaren Mahaifiyarsu, Hajiya Amina ce ta sakko bayan yaranta sun tafi sun kai mata
rahotu sama, tun daga step take kallon Mami har ta kusa faduwa, ta shigo parlon idonta kyar kan Mami tace “A’a
Sannun da xuwa Bakuwa, lale marhaba, sannu amarya” Mami ta kalleta ta gefen ido jin salon maganan nata tace
“Yauwa sannu” tana fadin haka ta mike tana kallon Hajiya Hauwa da ta ajiye mata ruwa da lemo tace “Hajiya ina ne
bangaren mama?” Hajiya Hauwa tace “Mu je in raka ki” tana rike da hannun Heedayah ta bi bayan Hajiya Hauwa,
Hajiya Amina ta bi ta da kallo har suka shiga parlon kaka sannan ta koma sama da sauri. Mami na shiga parlon Kaka
ta xauna saman babban darduman dake shimfide tace “Sannu Mama” Kaka dake kallonta tace “Yauwa sannu ‘yar
nan, sannun ku da xuwa” Mami tayi kasa da kai tace “Ina kwana” Kaka tace “Lafiya qlau, kinga ynxun nan na gama
karyawa, yau dai ba laifi sun ga daman kawo min karin kumallon da safe, kinsan uwa idan ba taka ba” Murmushi
Mami tayi, Abba ya dauke kai daga kallon kaka da yake, Mami tace “To Allah ya rufa asiri Mama” Kaka tace “Atoh,
Ameen dai, ni da so nayi ma su bar ni in dinga kayana da kaina tunda ina da karamin kitchen amma Amadu da
wansa Umaru sun ki yarda, Kuma fa idan na ci abincin sae inyi ta tashin xuciya tsabar kazantar Yan gidan….” Ba dai
wanda yace ma kaka komai, kaka tace “Toh ya sunan naki, kuma yaranki nawa?” Mami ta kalleta tace “Sunana
Rahinah, yarana uku” kaka tace “To yaran me ya hanasu xuwa gaisheni bayan an riga an xama daya kuma??” Kafin
Mami tace komai Abba yyi saurin cewa “Heedayah You didn’t greet grandma” Mami ta daga Heedayah ta maido ta kusa da kaka tace “Greet her” a hankali Heedayah tace “Ina kwana” Kaka da ta saki baki tana kallonta tace “To wnn
kuma wani irin kaya ne aka sa mata kamar ‘yar anna, abu duk a d’angale jama’ah? Rahilah kike ko wa? Gaskiya kar
ki sake sa mata wa Innan tsinannun kayan, da da idonta ma baxata bari a cuce ta a saka mata wannan kaya ba” Mami
na murmushi tace “To in sha Allah baxa a sake ba Mama” Kaka tace “Kuma kar ki sake yi mata karin gashi ki rufa
mana asiri mu ba hka muke ba” Mami tace “Ae gashinta ne mama” kaka ta cire hulan kan Heedayah tace “Auuu, to
maa sha Allah, daga gani ba daga irin tsiya ta fito ba, nima dai ance ina kamarta gashina har gadon bayana wllh….”
Abba ya mike yace “Baaba xa mu je, ana jirana ne” Kaka tace “Ko dai har ta tare bani da labari?” Yace “Aa tukunna”
Kaka tace “To sai yaushe?” Abba xai yi magana kaka tace “A’a ni ba ruwana, ita bata da baki sae kai, ni da ita nake
ba da kai ba ae koh” Mami tayi murmushi tace “Ko nan da sati kaka” Kaka tace “Toh dai kiyi ki tare kafin matar tasa
ta dawo, kinsan tana d’an tabin hankali, ko da yake dai gadonsu ne, ga shi kuma ya hade da an mata kishiya, ke dai
ba ruwanki da ita kiyi ta kanki ki kula da marainiya tsakanin ki da Allah, parlon ki na nan tikeke da uwar daka har da
bandaki ba ruwanki da fitinanniyar, kitchen kuma ya fi parlon nan nawa da kike gani girma, komai kike son xubawa
naki ki xuba duk xai cinye wllh….” Abba yace “To bari mu je Baaba” Mami dake ta murmushi kawai ta duka xata
daga Heedayah, Kaka tayi saurin cewa “Kai ku ji mata ba yini ku ka kawota ta min ba dama, kinsan ynda muke da
ita ne? D’a na fa ya tsinto ta tana galantoyi a titi” Mami ta mike tace “To shkkn mama, sae anjima” kaka tace “Ko
anjima da daddare ba sai ki xo ki tafi da ita ba” Abba tuni ya fita, Mami tayi ma kaka sallama ita ma ta fita. Kaka na
kallon Heedayah da jikinta yyi sanyi jin an tafi an barta tace “To sun baki abincin ma kuwa, don naga Amadu har
wani rawa kansa yake shi a dole yyi amarya” Heedayah ta gyada mata kai kawai, kaka ta mike tace “Ni dai ba
ruwana don ba barinsu Allah xai yi ba idan suka bar ki da yunwa” cup ta dauko a inda take jera su ta dawo ta bude
flask ta debi ruwan xafi, shayi me kauri sosai ta hada a cup din ta bude bread ta dau slice biyu ta daura a plate ta
debo dambun nama da tsoka uku na nama ta watsa kan plate din ta ajiye ma Heedayah a gabanta tace “gashi nan
maxa ki cinye ki bani kwanuka na, duk cikin ki ya hade da bayanki kice min kin koshi” tana fadin haka ta mike ta
koma daki tana cewa “Haka matar ta xo tsiya tsiya ba komai, kamar ta baxata kawo d’an lemonta ko ma dai turare ba
tace gashi kaka” tabe baki tayi ta ci gaba da linkin da take. Heedayah dae na xaune da shayi a gabanta don ba yunwa
take ji ba, ita din ba wata me cin abinci bace sosai, bude kofar parlon aka yi a hankali, Sudais ya shigo, direct inda
ya hango turarensa da kaka ta dauke jiya ya nufa don dama abinda ya kawo sa kenan, ya duka xai dauka kenan ya ga
Heedayah dake xaune, mikewa yyi tsaye yana kallonta sannan ya nufeta ya duka gabanta, she looks so sad, shi dai
ya kasa yarda da abinda Shuraim yace masa wai fararen idon nan nata basa gani, hannu ya kai har kusa da idon ya
ga bata motsa ba, ya sauke hannunsa a hankali, murya can kasa yace “How are you?” Juyawa tayi da sauri jin murya
kusa da ita, Amma kuma tayi shiru tayi tana kallonsa directly in the eye, yace “How are you?” a hankali tace “Fine”
yace “To ki sha shayin ki….” Tace “Na koshi” hannu ya sa aljihunsa ya fiddo chocolate biyu ya kamo hannunta yace
“Toh ga chocolate ki sha, ko in bude maki?” Ta gyada masa kai, ya bude guda daya ya saka mata a hannunta, xai yi
magana sae ga kaka ta fito, tana ganinsa tace “Ni dai wllh ba ruwana idan baki na ya bi ka Aliyu, nace kar ka sake
xuwa min nan xan ja Allah ya isa, Kuma wllh na ja a raina tun ranan” Yace “Tunda ke ba Baffa bace kuma ba Umma
bace me xai dameni, Allah ya isan ki iyakarsa lebenki” ko kadan bata ma san me yake cewa ba, don bude baki tayi
kawai tana kallon shayin gaban Heedayah, can tace “Naga ikon Allah, Ke baki sha shayin bne har ynxu kika bar shi
a walakance?” Heedayah ta marairaice tace “Na koshi” kaka tace “Amma ke dai muguwa ce, kina kallo ina hada
shayi duk na yi barna da madarata da banvita kiyi shiru ki kyaleni sbda mugunta??” Sudais yace “To da idon ki taga
kina hada shayin ta maki shiru kaka” Kaka tace “Ba ruwana da wnn, ance maka haka Allah ya bar su, duk suna sane
da komai ke faruwa a inda suke, kawai tayi niyyar walakanta ni ne, amma tana sane lkcn da nake kada shayin”
Sudais ya dau cup din shayin yace “Toh bari in Shan…..” Kaka tace “Haram…. Ban baka ba har xuciyata, Amadu ne
ya siyo min kayan shayin ba Umaru ba” dariya yyi yace “Toh shi din ba Abbana bne, Kuma ae dama abincin Haram
dadi ne da shi” kaka ta fashe da kuka ta nemi kujera ta xauna, sai da ya shanye shayin ya ajiye mata cup yyi
ficewarsa….. Hajiya Hauwa ce ta kawo abincin rana bayan azahar, Heedayah na xaune kan darduman da Kaka ta
shimfida mata wai tayi sllh, Hajiya Hauwa da suke ce ma Aunty a gidan, ta gaida kaka tace “Ga abinci kaka” kaka
tace “Toh yau dai kun bar yunwar ta gigitani gaskiya, Amma bbu komai Allah yyi albarka, amma fa ni dai nasa yar
nan tayi sllh bn san ko ba musulma bace” dariya sosai Aunty tayi tace “Musulma ce mana kaka” kaka tace “Atohh
naga dae ta iya alwalar…” Aunty tayi murmushi tana kallon Heedayah ta isa kusa da ita ta kai hannu kanta tace “Bari
in kawo maki naki abincin kin ji daughter?” Heedayah ta gyada mata kai kawai, Aunty ta juya ta fita, sae ga ta ta
dawo da plate din shinkafa da miya da salad a gefe sae neman kaza ta ajiye gaban Heedayah tace “Ki jira ya huce
sae ki ci, kaka xata baki ruwa idan kika ci” daga haka ta fita, kaka na kallon Heedayah tace “To me kika yi ma
iyayen naki suka sallama ma duniya ke d’a na ya kwaso ki?” Heedayah dai bata ce komai ba don Hausan ya mata
girma, kaka ta tabe baki tace “Toh, Allah shi yasan dai dai, mu dai gashi mun kwaso ki bbu dangin iya balle na
Baaba, muna neman lada wajen Allah” Bayan la’asar Kaka ta kwashe Yan wanke wankenta ta bude wani kofa da xae
fitar da ita bayan gidan, inda aka yi mata pamponta ta kada kumfa ta ajiye ruwan dauraya ta dawo ta daga Heedayah
dake bacci tace “Taso ke ma a dinga cin amfanin ki ba wai ki ci ki sha kiyi kashi kiyi ta bacci ba, tun xuwan ki kike bacci” a haka ta kai ta bakin tap ta xaunar da ita kan kujeran tsugunno dake wajen tace “Maxa kiyi ta lalubawa kina
daukan kwanukan kina wankewa ga ruwa a gefen ki, mace kike gidan wani kuma xa ki” daga haka kaka ta wuce ciki
ta bar ta, tunda Heedayah take bata ta6a wanke wanke ba, bata ma san meye shi ba, hka ta dinga daukan kwanukan
tana tsoma su cikin ruwa tana fitarwa, har taji bbu wani nan kuwa duk suna gefe daya a ajiye, mikewa tayi pink
wandon jikinta da ya wuce gwiwarta a jike jagab, kofa taji an bude a tunaninta kaka ce tace “Na gama” duk a tsorace
take hannunta rike da plate biyu da cup daya, Shuraim ne tsaye bakin kofar alamar shigowansa kenan gidan a
tunaninsa kaka ce backyard din, hannu Heedayah ta sa tana laluba wajen xata wuce ta ci tuntube da kujeran da ta
tashi daga kai, cikin few seconds komai ya faru, duk da effort din Shuraim kuma jikinsa ta fada hakan bai hanata
buge kneels dinta a kasa ba, shirun da Shuraim ya ji tayi ya sa yyi saurin daga kanta yana kallon fuskarta, sae a
sannan ta wara ido ta fasa wani ihu da ya raxana shi, lkci daya ta kankamesa tana cewa wayyo kafanaa, kaka ta saki
flask din ruwan xafin hannunta ta taho a guje tana cewa “Innalillahi wa Inna ilaihi raji’un, yar mutane ta mutu a
gidana, na shiga uku na banu, me xance ma Amadu” Shuraim ya kalli kafan nata yana kokarin dagata ta rirrikesa
cikin kuka tana cewa “Wayyo a kai ni wajen Abba, wayyo Abba ya xo….” kin fitowa kaka tayi ta dinga lekowa
jikinta na rawa, Shuraim ya hade rai, ganin Heedayah ta ki tsayawa yace “Baxa ki tsaya ba sae na mare ki?” Kuka
sosai take yi tace “Baxan iya ba kafan yana min ciwo…” Daukarta yyi ya shiga parlon kaka da ita ya kwantar da ita
saman kujera yana kallon kafar, cikin rawar murya Kaka tace “Kaddai karyewa kafar yyi Ali?” Ta gefen ido Shuraim
ya kalleta kafin ya mike yace “Ni na sani…” Kofa ya nufa zai fita ta cafkosa ta fashe da kuka tace “Don Allah ka rufa
min asiri ka duba mata kafar tun da kai ma likita ne, Kar Amadu ya kullaceni, wllh sai in iya tattara kayana in gudu
ba ruwana da bacin ran Amadu, ya takarkare ya tsinto yarinya kuma ace a gidana ta karye….” Heedayah dai sai kuka
take tana kiran Abba, kaka ta xauna kasa ta saki matsanancin kuka tace “Ka ji algungumar wai Abba ko??” Shuraim
ya hade rai yace “To ina xuwa in dauko abu a mota” daga haka yyi ficewarsa, dawowar da bai sake yi ba kenan.
Abba ne tsaye kan Heedayah dake bacci saman gadon kaka, Mami kuma na xaune gefenta tana rike da hannunta,
Aunty da Baffa da Umma ma duk suna dakin, kowa yyi jigum, can na hango kaka rakube jikin kofar bandakinta ko
ganinta bata son a dinga yi sosai, Baffa yace “Toh wai ma ina aka ta6a sa mara ido aiki fisabilillahi??” Kaka tace
“A’a ni dai kar a min sharri ita tace xata yi, tana ganin na hada kayan wanke wanken tace Kaka kawo in taimaka
maki, to sai in hanata sbda mugun hali ko me? Kuma da kke wnn maganar so kke Allah ya tambayemu tarbiyar da
muka mata? Don tana makauniya shkkn sae a fake da haka a ki bari ta ta6uka komai??” Baffa yace “Ta ina makaho
xai iya wanke wanke kaka???” Kaka tace “Ni dai kar a min rashin kunya ba ruwana, Kuma flask din ruwan xafi na
da ya gamu da ajalinsa daxu da plet dina da suka fashe guda biyu duk a biyani kayana, hatta kujerar tsungunnon ma
yyi targade ba ita kadai ba, targade mana tunda kafa daya ya karye, Kai kuma Amadu wllh jidali ka haifar ma kanka
kana tunanin d’a ne, sam xuciyar wnn yaro naka shuree yake ko wa, bashi da kyau, xuciyarsa bakikirin yake, ni
Yaron ma idan ba tsoro yake bani ba shegiya nake, mugu ne axxalumi na bugawa a jarida, wllh yarinyar nan na tsala
ihun axaba gwanin ban tausayi ya tsallake da shegen idanuwansa kamar naka yyi wucewarsa ko ta mutu ko tayi rai
oho, tsaf xai iya kashe mutum har ya kai sa makwancinsa, ni abun hannunsa ma na daina ci daga yau, inda Sudess ya
fi sa kenan, shi dai bar shi da cin Haram amma xuciyarsa fari ne fatt wllh” Abba dai bai ce komai ba kuma bai kalli
mahaifiyar tasa ba…