HEEDAYA CHAPTER 57 BY By Khaleesat Haiydar

HEEDAYA CHAPTER 57 BY By Khaleesat Haiydar

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Murmushi Shuraim yyi yace “Toh sae da safe” Heedayah tace “Ko kana yi?” Yace “Mene?” Tace “Soyayyan mana” 

ya girgixa kai yace “Aa sai ke” Tace “Tohm byee” katse wayar ta ji yyi, ta kalla sannan ta ajiye a hankali ta juya ta 

kwanta. Washegari da safe Heedayah ta samu Mami a parlon Amminta, bayan ta gaisheta a hankali tace “Mami don 

Allah ina son in bi ku….” Mami tace “Ki bi mu ina?” Heedayah tace “Kaduna” Mami tace “Yaushe kika xo xaki ce 

xaki koma Kaduna?” Shiru Heedayah tayi, Mami tace “Look Heedayah gidan ku ne nan idan xaki saki jiki ki saki 

jiki, bana son gulma” Ita dai Heedayah bata ce komai ba, Shigowar Ammi ya sa ta mike ta fita, a ranan karfe goma 

da rabi Heedayah na tsaye sai kallon Khaleel dake xaune gaban motar da xai kai su Kaduna take, Mami ta shiga 

bayan motar bayan ta gama sallama da Ammi da Mom Islam, a hankali Heedayah ta daga mata hannu, Sannan ta 

daga ma Khaleel ma, murmushi ya sakar mata ta juya ta koma ciki kar hawayen dake makale idonta ya gangaro. 

maid dinsu Amina ce ta kwankwasa dakinta bayan Magrib, Heedayah dake xaune saman darduma ta mike ta bude 

kofar tana kallonta, Amina tace “Baaba Yakumbo na kiran ki” Heedayah bata ce mata komai ba Maid din ta juya ta 

bar wajen, Heedayah ta koma ta dau wayarta ta fita dakin, gaba daya a sanyaye take, sosai take jin tana missing din 

Khaleel, a hankali ta bude kofar parlon Yakumbo bayan ta isa, Yakumbo ce xaune parlon da kaka da tayi tagumi, 

Shuraim ma na xaune parlorn, ta karasa ta durkusa saman lallausan carpet dake parlon ta kalli Shuraim tace “Ina yini 

Ya Shureen” Yace “Lafiya” Ta kalli su kaka ma ta gaishesu, bbu wanda ya amsa mata cikinsu, Bayan few seconds 

tace “Gani” Kaka ta saki kuka tace “Yanxu fisabilillahi Deedayah ki rasa wanda xaki ce ma iyayenki kina so sai d’an 

kinnafin? Ke ko me ya sameki haka kika xabar ma kanki mutumin nan ni Patuu??” Tuni Heedayah ta hade rai tace 

“Shi ba Kidnapper bane” Kaka tace “Aa toh wllh kin karyata ubanki, Mutumin da tun kina ficiciyar ki ya daukeki ya 

raba ki da iyayenki, sbda addu’ar da ake jefa sa da shi ya rasa sukuni ya fito dake daga garkensu ya yasar dake gefen 

titi shine xaki bude baki kice mana ba kinnafa bane???” Hawaye ya kawo idon Heedayah tace “Ni dai ba Kidnapper 

bane, ku daina kiransa haka” Yakumbo na kallonta da kyau tace “Toh bari kiji wllh indai da raina bbu wanda ya isa 

ya nuna ni yace ga surkar kinnafa, tun wuri kiyi maxa ki sauya shegen tunanin ki, kaf xuri’ar mu bbu me abun fadi 

da ya bar ma jika, don haka baxa ki bar mana abun fade ba, har gobe mutumin nan kinnafa ne a idona, ba komai 

bane mu ma ya kwamushe mu wataran” Kaka tace “Toh da fa?? Ai ynxu da kyar idan bai lallabo ya dawo nan ba yyi 

abinda xuciyarsa ke raya masa, ni ban yrda ya wani koma kaduna ba, yana nan makale a kano xai dawo tsakar dare, 

sannan wlh banda ina kunyar uwarsa ni rufe ido xanyi in gaya masa abinda ke raina, to meye hadina da shi??” 

Heedayah ta fashe da kuka sosai tace “Ni dai ba Kidnapper bane….” Yakumbo ta dau pillon da ke gefenta ta jefa 

mata a fusace tace “Kin karyata uwarki, wllh in dai ina numfashi baxa ki auri katon D’an ta’addan nan ba” Kaka ta 

kalli Shuraim dake danna wayarsa tace “Kai kuma an kiraka ka xo ka yi mana shari’a kayi shiru kana kallonta tana 

mana fitsara” Ya dago kai yace “Toh Kaka ku xa ku xauna mata da shi?” Bude baki Yakumbo tayi tana kallonsa, 

yace “Ita xata xauna da abun ta, kuma Kidnapper da ku ke ce masa ya ta6a kidnapping din ku ne?” Yakumbo tace 

“Naga abinda ya isheni….” Kaka tace “Toh tashi ka fita, na mance halinka ne ya sa na kiraka, Allah yayi maka yanda 

kayi mana yanxu” mikewa yyi ya maida wayarsa aljihu ya nufi kofa, Yakumbo tace “Kai xaka yrda kanwarka ta auri 

tatattcen tsohon d’an kinnafin idan ba mugunta ba, ashe haka xuciyarka take ban sani ba, toh aniyarka ta bika wllh” 

Kaka tace “Gantalalle ne fa, ni ba na mance waye shi ba na gayyatosa, ai fadan gaskiya karara sai Sudess Dan 

arxiki” Mikewa Heedayah tayi ta fita tana goge hawayen da ya ki tsaya mata, tsaye ta ga Shuraim bakin stairs, ta 

fashe da wani sabon kukan, yana kallonta yace “Toh meye na kuka? Ba dai Abbanki ya amince ba haka ma 

Amminki?” Ta hade kanta da bango tana kuka sosai tace “Toh shine xa a dinga ce masa Kidnapper bayan ya 

daina???” Yace “Haka yace maki?” Juyowa tayi da sauri tana kallonsa, yace “Suna nufin idan ku ka yi aure da shi, ce 

maki xa a dinga yi matar tsohon Kidnapper” Tace “Ehh na yarda” daga haka ta bi gefensa xata wuce ya riko 

hannunta, kin juyowa tayi hawaye na sauka idonta, ya juyo da ita yace “Toh kiyi hakuri idan ma sun kiraki kar ki 

sake xuwa” ita dai bata ce komai ba, yace “Mu je ki amshi wayarki ki bani nawa” Ba musu ta bi sa downstairs. 

Mami ce xaune bedroom dinta tare da Junaid dake sauraron abinda xata fada masa don kiransa tayi a waya, Mami na 

kallonsa tace “Da farko na so ka da Shaheedah ka kawo excuses which I had no option then to let you stick to ur 

choice, kace kai Heedayah kake so, fine ka je gun iyayenta without me even knowing kuma sun nuna sun baka ita, 

weeks back ana da intention din kai kudi gidansu, sai abubuwa suka faru wanda ya sa aka daga, to har yanxu naji 

kayi shiru kan xancen baka cewa komai ba, da akwai wani abun a ranka ne??” Tunda Mami ta fara magana Junaid 

ke kallonta, can ya sauke idonsa kasa yace “Na hakura da ita ne kawai Mami” Mami na kallonsa tace “Ko saboda 

me?” Yace “Saboda yayana, I will welcome anything that will make him happy, he deserves to be happy bayan duk 

abubuwan da yyi passing a rayuwa, I over heard conversation dinku the other night, a wannan daren kuma na cire 

Heedayah a raina, bbu aure tsakanina da ita, na bar ma Ya Khaleel, Allah ubangiji ya sa rabonsa ce ita” Mami ta kasa 

cewa komai don tunda Khaleel ya gaya mata Heedayah yake so bata da wani kwanciyar hankali, har ranta take son 

duk abinda xai faranta ma first son din nata, amma kuma bata sanar ma Junaid xancen ba sbda bata son ya ga kamar ta fifita Khaleel a kansa, amma furucin Junaid yau ya sa taji hankalinta ya kwanta, Rasa ma abinda xata ce masa 

tayi, Junaid ya mike ya fita daga dakin.

3 months later….

Heedayah na parlon Stepmum dinta dake tsefe mata kitson da tayi mata duk da satin kitson daya bbu abinda yyi, 

Mom Islam ce ke ta surutun ta ita kadai Heedayah bata cewa komai, can Mom Islam tace “Are you okay 

Heedayah?” Da sauri Heedayah ta dawo daga duniyar tunanin da ta afka, Mom Islam tace “Tunanin me kike?” shiru 

Heedayah tayi, Mom Islam tace “Talk to me” A hankali Heedayah tace “Nothing aunt” Murmushi Mom Islam tayi
 

tace “Sa ranan da aka maki yau ne ya sa kike ta tunani tun daxu” Lkci daya hawaye ya kawo idonta amma bata ce 

komai ba, Mom Islam tace “Toh ki kwantar da hankalin ki dear, kowa ma haka ya ji yanda kike ji, amma naki shirun 

yyi yawa, you are suppose to be happy….” Heedayah tace “I am not sad” Mom Islam tace “Ko ranan da aka sa yayi 

maki kusa?” Heedayah ta dago ta kalleta kamar xata yi kuka tace “Ehh” Mom Islam tayi murmushi tace “Wata dayan 

ne yyi kusa?” Hawaye na sauka idonta tace “Aunty just four week fa, yar karamar yarinya da ni?” Dariya sosai 

stepmom dinta tayi tace “Ehh lallai kam yar karamar yarinya, to ni a ranan da Abbanki ya kai kudi ranan ma aka 

daura auren, kinsan Ammin ki ce ta hada mu dama” Heedayah dai tayi shiru bata ce komai ba, Mom Islam tace 

“Washegari kuma aka kai ni dakina, kinga ke ai an maki gata sosai har sati hudu” Heedayah ta share hawayen idonta 

a hankali, Mom Islam tace “Ki kwantar da hankalin ki kin ji my daughter, ba dai kina son mijin ki ba” Heedayah ta 

gyada mata kai, sai kuma a hankali tace “Amma ni tsoronsa nake” Dariya sosai Mum Islam tayi tace “Tsoron me?” 

Heedayah dai bata ce komai ba, Mom Islam tace “Shi yasa jiya kika ki dadewa da kika fita wajensa?” Heedayah ta 

turo baki tace “Aa shine yace min yana jin bacci” Mom Islam tace “Ayya, ya koma Kadunan shi?” Heedayah ta 

gyada mata kai, Mom Islam tace “Allah sarki, ni dai nutsuwarsa na burgeni kuma naji dadi da ba a samu matsala 

shari’ar da aka yi ba, Allah ya dubesa da yake xaluntarsa aka yi” Heedayah dai bata ce komai ba, Mom Islam ta ci 

gaba da kwantar mata da hankali har suka gama tsifan ta hau sharce mata dogon gashin nata kafin ta wanke. Sai 

bayan awa kusan biyu Heedayah ta koma bangaren Amminta bayan Step mum dinta ta gama gyara mata gashinta, 

Amminta ta bi ta da wani kallo tace “Kumbure kumburen uban me kike?” Heedayah ta girgixa kai tace “Ba komai” 

Ammi ta ci gaba da abinda take, juyawa Heedayah tayi ta fita ta koma bangarenta. Mumy ce xaune parlon Hajiya 

Sadiya hawaye na sauka idonta tace “Ni shkkn dai a tutar bbu na tashi wllh….” Tana fadin haka ta fashe da 

matsanancin kuka, Hajiya Sadiya dai ta ma rasa abun cewa, cikin rawar Mumy tace “Dama nace asirin nan bai ci 

Shuraim ba ku ka ce ina na fito, Salima ta sa ina ta kashe kudi a Iska, ga dai yarinya yau an sa mata rana da d’an 

gidan Rahinah, kamar fa almara labarin ya xo min, ban ta6a kawowa hakan xai faru ba, kuma tunda na ji kullum sai 

Shuraim yaje government house na xata saboda ita yake xuwa ina ta murna sun shaku yanxu ashe ashe ba haka bane, 

Wai ina kwance Barrister ya shigo ya sanar min xa su kai kudi da safe….” wani sabon kuka ne ya kubce mata, a 

hankali Hajiya Sadiya tace “Shuraim yana da tsari duk ynda aka yi, tunda bake kadai Mutumin nan ya ma aiki ba, ni 

da mutumin ya min aiki kan surajo ba gashi yayi ba, ko sati ba ayi ba ya saki matar saki uku ya auri warce nake 

so…..” Mumy na share hawayenta tace “Kuma haka ne wllh, yanda dai kika fada haka ne Shuraim na da tsari, kinsan 

Kakar ma ba wai barin su haka tayi ba” Hajiya Sadiya tace “Toh wata nawa aka saka ranan yanxu?” Da damuwa 

Mumy tace “Wata daya kacal Sadiya” Hajiya Sadiya ta bude baki tace “Toh sai dai in Heedayar xa a asirce tace ta 

fasa kawai ko?” Hawaye na taruwa idon Mumy tace “Ta yaya? Shi wnn mutumi sai yace a barbada a abinci ko abun 

sha, to ina xa mu ga wata Heedayah tana gidan iyayenta, Kadunan ma ko ta xo kwana biyu take yi ta koma, balle ma 

tunda aka sa mata rana ma shkkn ba lallai ta xo kwana kusa ba sai bayan bikin” Sadiya tace “Wai tsaya ba d’an 

fashin nan bane d’an Rahinar da aka sa mata rana da?” Mumy tace “Shine dai wllh, in gaya maki sun shiga sun fita 

sai da suka tabbatar sun wankesa tass, su kuma abokan huldarsa duk an masu daurin rai da rai a gidan yari haka naji, 

lkcn shari’ar kuwa ko baccin kirki Barrister baya yi, su kusan biyar suka hada kai aka wanke Mutumin nan me laifi 

kiri kiri gashi a bayyane, kuma wllh gagarumin d’an Kidnapping ne fa aka ce” Sadiya da ta saki baki tace “Ikon 

Allah, to ya aka yi da dukiyoyin jama’ah da ya tara da mutanen da ya kashe???” Mumy tace “A karyansu wai bai 

ta6a kisa ba, dukiyoyin jama’ah kuma an kai gidan Marayu, ke kiji daure ma karya….” Sadiya tace “Lallai yana da 

masu tsaya masa ne” Mumy tace “Da fa, ance kanin ubansa wani babba ne a Gombe, snn autarsu ubansa ma wani 

babba take aure a gomben, snn ga danginsu Junaid su ma kinsan an sansu, uwa uba ga gwamnan kano dake tunanin 

xai xama surkinsa, kinga kuwa ai ba karamin wanki xa ayi masa ba” Sadiya ta rike ha6a tace “Ikon Allah” Mumy 

tace “Ni dai mu koma abinda ya dameni, yanxu Sadiya ya xan yi??” Sadiya tace “Asiri kawai xa mu je ayi ma 

Heedayar idan ma magani ya bada wanda ake son ta ci sai ki wanke kafa ki tafi government house ai bbu wanda xai 

ce maki don me, bbu wanda xai koreki, da ba don mijinki ba da yanxu kilan bbu Heedayah a doron kasa, kina sauka 

kano sai Shuraim ya shigar da ke government house din kawai” A hankali Mumy tace “Toh hakan xa ayi, tunda da 

sauran lkci tashi mu tafi gun Mutumin Sadiya” Kallon Mumy kawai Abba ke yi har ta gama maganan da take sannan 

yace “Ki dai gaya min me xa ki je yi a kano Maryam” Tayi masa wani kallo tace “Me xanje yi kamar Yaya? Kana 

nufin karya nayi maka kenan ko me? Nace xanje gaida kaka kace min me xanje yi a kano” Abba yace “Sati me xuwa kaka xata dawo ba sai kin je ba, bbu inda xaki je” Mumy tace “Toh wllh wllh sai naje ko da gobe xata dawo kuwa” 

bata jira me xai ce ba ta fice daga dakinsa xata je hada kayanta ya bi ta da kallo keenly. A ranan da safe Heedayah na 

babban parlon Abbanta xata yi masa sallama, ya gama wayar da yake yana kallonta yace “Kwana nawa Ammin ki 

tace kiyi?” A hankali Heedayah tace “Biyu” Abba yace “Toh Allah ya kiyaye hanya, xa ku je tare da Shuraim….” 

Heedayah tace “Ammi ta gaya min” mikewa tayi ta fita daga parlon, step mum dinta ce ta rakota gun wata 

rantsantsiyar mota ta shiga baya ita kadai sai driver dake gaba, step mum dinta na kallonta a hankali tace “Ki kula da 

kanki kinji daughter?” Heedayah ta gyada mata kai tace “Toh Aunty” Mom Islam ta daga mata hannu Heedayah ta 

daga mata ita ma, Kalle kallen wajen Mom islam ke yi tace “Toh ina Shuraim din” Heedayah ta bude hannu alamar 

bata sani ba, can Mom Islam ta hangosa cikin daya daga motar da xasu yi masu escort, Mom Islam na tsaye har 

motocin suka fara fita…..

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *