HEEDAYA CHAPTER 59 BY By Khaleesat Haiydar
Washegari da sassafe Mami da su Heedayah suka gama shiryawa xuwa Nigerian Army Reference Hospital Kaduna,
Mami na tsaye parking space da Heedayah Khaleel ya karaso tare da Farida, Mami tace “Ba lallai a barmu mu shiga
gaba daya ba, ka dauko makullin motar Junaid kai da Heedayah ku tafi tare, ni kuma i will go with Farida” Yace
“Alright” daga haka ya juya ya koma ciki, Mami ta jira har ya dawo da makullin motar snn ta bude tata mota da ke a
kunne ta shiga Farida ta shiga front seat, suka bar compound din, Khaleel ya shiga motar Junaid ya kunna yana
warming din motar, Heedayah dai na tsaye fuskarta bbu walwala, ko kadan bata ji dadin wucewar da Mami suka yi
suka bar ta ba, ya d’an daga kai ya kalleta suka hada ido, sauke idonsa yyi yace “Are you waiting for me to help you
in?” K’in cewa komai tayi ta dauke kanta ta turo baki, bata ankara ba sai ji tayi ya dauketa cak, ta xaro ido a tsorace
ta rikesa tace “Noo, don Allah ka bari” Bai saurareta ba ya rungumeta jikinsa, ya xaga daya side din motar ya bude
front seat ya ajiyeta a hankali yana kallonta, rufe fuskarta tayi da kafarta da sauri xuciyarta na bugawa, yyi
murmushi ya rufe motar ya xaga driver seat ya shiga sannan ya ja motar suka bar gidan, har suka isa asibitin bata
yrda sun hada ido da shi ba, shi ma bai ce mata komai ba, ya samu wajen parking yyi parking a babban asibitin, sai a
snn ya kalleta yace “Uhn wai kunyata kike ji?” Ta saci kallonta suka hada ido, yyi murmushi yace “Ki dinga cin
abinci ko xaki d’an kara weight, ur weight isn’t encouraging” Hararansa tayi tace “Kai ma ka dinga cin abincin, ae
naga baka ci da yawa” Ya wara ido yace “Ae idan na kara cin abinci a kan wanda nake ci ke ce xaki sha wahala”
Tace “How?” Ya bude motar ya sauka yana murmushi yace “Xa ki san how” Bude motar tayi ita ma ta sauka,
Khaleel ya fiddo wayarsa ya kira Mami, nan ta sanar masa suna Accident and emergency wards, Heedayah na biye
da shi suka nufi wajen. Mami na xaune tare da Hajiya Amina da Hajiya Hauwa, ko wannensu yyi tagumi, sai su
Rabi’ah da suka ci kuka suka gode Allah, Khaleel ya gaida su Hajiya Amina da ladabi, Heedayah ma ta gaishesu,
duk suka amsa, Khaleel yace “Ya mai jiki?” Suka amsa masa da “Alhmdllh” Khaleel ya fita haraban asibitin ya
xauna, Heedayah dai na ta tsaye gefen Farida, ko wa na wajen damuwa ne karara tare da shi, Bude kofar ward din
aka yi likitoci biyu suka fito, ba a dau lkci ba Shuraim ma ya fito ward din, har xai wuce ganin Mami ya tsaya ya
gaisheta, Mami ta amsa, a hankali tace “Ya Mai jikin?” Yace “Alhmdllh” da damuwa tace “Baxa a bari a shiga ba
ko?” Shuraim ya gyada mata kai ya bar wajen, Heedayah ta bi sa da kallo, slowly yake tafiyar, bata yi wani tunani
ba ta bi sa da sauri, ta isa inda yake cikin sanyin murya tace “Yaya Shureen ya jikin Mumy?” Ya d’an kalleta yana
tafiya still yace “Da sauki…” Bin sa tayi har suka fito ya xauna kan Concrete bench, ta xauna gefensa tana kallonsa,
she could see how disturb he is, a hankali tace “Ya Shureen is it that serious?” Bai ce mata komai ba, ta dafasa tace
“Talk to me” Sai a snn ya kalleta a hankali yace “You pray for her” Tayi shiru tana kallonsa, cikin sanyin murya tace
“Will I be allowed to see her?” Ya girgixa mata kai, cikin kwantar da murya tace “Do not be press ya Shureen, this
shouldn’t oppress you, Allah xai bata lafiya in sha Allah ka ji?” Lkci daya Hawaye ya taru idonta jin ya ki cewa
komai, tace “Ka ji ya Shureen” kallonta yyi amma ya kasa ce mata komai, kamo hannunta yyi a hankali yace “Ki
taya ta da addu’a ke ma” Ta gyada masa kai, daga haka ya mike, pharmacy din asibitin ya nufa…. Heedayah ta bi sa
da kallo, dai dai nan suka yi ido hudu da Khaleel dake xaune shi ma saman concrete bench ta side din da take,
mikewa tayi a hankali ta nufesa, yana kallonta yace “Ya jikin mum din tasa?” Ta xauna tace “He said we should pray
for her” Khaleel yace “Allah ya sauwake” A hankali tace “Ameen” Kamo hannunta Khaleel yyi, xata kwace ya ki
saketa, ta shiga bin wajen da kallo kamar mara gaskiya, murya can kasa yace “What are your plans….” Tace “What
plans?” Yace “For ur wedding” sunkuyar da kanta tayi bata ce komai ba, yana kallonta ta gefen ido yace “Kinyi
shiru” A hankali tace “To ai ban sani ba, sai abinda Aunty ta ce” Yace “Ohk, jiya sai kika barni ni kadai a parlor
ko….” Tace “Mami ce tace in je in kwanta” Murmushi yyi bai ce komai ba. Sai kusan sha daya suka bar asibitin har
sannan kuma ba a bari sun shiga ward din da Mumy take ba, Abba kadai ne ya shiga sai shi Shuraim, duk iya dube
duben Heedayah ko xata ga Shuraim bata gansa ba har suka bar asibitin, gaba daya hankalinta ya ki kwanciya, sai da
suka kusa gida Khaleel ya kalleta ganin yanayinta yace “ko dai a maida ke asibitin ne?” Ta kallesa kamar xata yi
kuka ta gyada masa kai, yace “Ohk” Wani layi ya shiga yyi reverse snn ya dau hanyar asibitin kuma, wajen da xai
iya parking ya samu a nan bakin titin asibitin ba tare da ya kalleta ba, tana kallonsa tace “Toh xa ka dawo ka daukeni anjima?” Yace “Ehh” Tace “Toh nagode” Daga haka ta bude motar ta sauka ya dinga kallonta har ta rufe motar snn
ya ja motarsa ya bar wajen, ta karasa karamin gate din shiga cikin asibitin ta shiga bayan ta gaida sojojin dake wajen,
da kafa ta karasa har Accident and emergency. Shuraim ne kadai xaune saman kujeran dake gaban ward din, ya
dinga kallonta har ta iso yace “What did you forget?” Ta xauna wani kujeran tace “Aa kawai ina son in tsaya nan ne”
Ya girgixa kai yace “Aa da yamma ai xa ku dawo” Tace “Toh ai kowa ya tafi ya bar ni” Shiru yyi bai ce komai ba,
Suna ta xaune a haka bayan wani lkci ta kallesa tace “Ya Shureen is she sleeping?” Ya girgixa kai yace “She is still
unconscious” Da damuwa tace “Ta ji ciwo ne?” ya girgixa kai yace “Aa, may be internally” Lkci daya jikin
Heedayah yyi sanyi sosai, a hankali tace “Toh yanxu wani treatment ake yi?” Yace “Still on scanning, kafin a gano
inda matsalar yake idan akwai sai a dau mataki, Ana jiran wasu results din” Cikin sanyin murya Heedayah tace
“Allah ya bata lafiya” Shuraim yace “Ameen” Suna ta xaune a haka har kusan sha biyu da wani abu, Heedayah ta
kallesa ganin baya daukan phone calls dinsa yace “Why ain’t you picking?” Girgixa mata kai kawai yyi ya mike yace
“Lkcn sllh yyi, mu je in nuna maki inda xa kiyi sllh” Tashi tayi ta bi bayansa suka nufi kofar fita. Heedayah na idar
da sllh ta xauna kan Concrete bench tana jiran fitowarsa daga masallaci, muryarsa taji ta bayanta ta juya da sauri,
yana kallonta yace “Me xa ki ci?”
Ta girgixa kai tace “Aa am not hungry” yace “Then you need to go back home
now” Ta 6ata fuska ta mike tace “Anjima idan su Mami suka xo ba sai in bi su ba tohh” Bai ce mata komai ba ya fara
tafiya ta bi sa, Xaune suka tadda Abba da Baffa a bakin ward din, Shuraim ya gaishesu, Heedayah ma ta gaishesu da
ladabi, Abban Sudais na kallon Shuraim yace “Ya jikin nata, har yanxu dai shiru?” Shuraim yace “Ehh, duk scans
din da suka fito bbu matsala saura uku yanxu ake jira” Baffa yace “Toh Allah ubangiji ya tashi kafadunta” Shuraim
yace “Ameen” Shi dai Abba bai iya yace komai ba, Baffa yace “Sun dai ki barin a shiga a ganta” Shuraim yace “Ehh
amma in sha Allah idan ta farfado shkkn” Baffa yace “Toh Allah ubangiji ya tashi kafadunta ya bata lafiya” Shuraim
yace “Ameen” Sai karfe daya su Baffa suka bar wajen. Karfe biyu da ‘yan mintuna Shuraim ya mike daga inda yake
xaune ya kalli Heedayah yace “Nace ki tafi gida kin ki tafiya…. And you haven’t eaten till now” Tace “Toh ai kai ma
baka ci komai ba” Yace “Toh ki tafi gida idan kin ci sai ki kawo min” Kallonsa tayi tace “Da gaske?” Yace “Ehh”
Tace “Toh xan iya ganinta kafin in wuce?” Ya d’an yi shiru, kafin ya bi corridor din da kallo, sai kuma yace “Toh
taso” Mikewa tayi ta bi bayansa ya bude kofar ward din ya shiga ta bi bayansa, kallon Mumy dake kwance kamar
me bacci Heedayah ta dinga yi, ta kasa karasawa gun gadon, Shuraim ya karasa ya duka yana kallonta, ya fi minti
daya yana kallonta kafin ya kamo hannunta a hankali, lkci daya ya sake hannun ya kai finger dinsa gefen wuyarta,
xame hannunsa yyi ya mike, Heedayah dai na tsaye sai kallonsa take, kofa ya nufa ya fita daga ward din ta bi
bayansa, xaunawa ta ga yyi kan kujeran dake wajen ya rike kansa, sosai ta ji gabanta ya fadi ta karasa kusa da shi da
sauri, ta xauna tace “What happened Ya Shureen” Jin bai ce komai ba da damuwa sosai tace “Talk to me plss, me ya
faru?” A hankali ya dago kansa hawayen dake idonsa ya sauko….