HEEDAYA CHAPTER 6 BY By Khaleesat Haiydar
Www.bankinhausanovels.com.ng
Parking Junaid yyi kofar gidan Baffa ya kashe motar sa ya bude ya sauka, sanye yake da kananun kaya, walking
calmly ya isa gate suka gaisa da Mai gadi sannan ya shiga gidan, baya bukatar tambayar entrance don tuni ya hango,
yana isa bakin kofar yayi knocking, bbu bata lkci aka bude kofar, kanwar Sudais ce ta bude kofar, yana kallonta da
murmushi fuskarsa yace “Good evening” tana kallonsa irin kallon rashin sanin tace “Welcome…” Muryar Abba suka
ji yace “Is that Junaid” Junaid yayi kasa da kai yace “Ina yini Abba” Abba yace “Lfya lau, Zainab ki kai sa bangaren Kaka” Zainab na kallon Junaid tace “Toh” bin bayanta yyi suka nufi parlon kaka, Abba kuma ya fita rike da makullin
motarsa, da sallama Junaid ya shiga parlon kaka, Mami dake tsaye rike da jakarta alamar xata wuce ta juya tana
kallonsa, Kaka ta kalli Junaid sannan ta kalli Mami tace “wannan ne d’an naki?” Mami tayi murmushi tace “Eh
Mama” kaka tace “Ahh ba shakka… Kyakkyawan bafillatani da shi wllh, ya ma fi ki kyau ai, da ganin ubansa ya
yo….” Mami dai na murmushi tace “To sai na shigo da daddare kaka, bari in je” kaka tace “A’a ki yi xaman ki kar ki
wani wahal da kanki ba gashi ina kula da ita ba tsakanina da Allah….” Mami tace “Toh shkkn mama” Daga haka ta
fita parlon, Kaka na kallon Junaid dake tsaye har sannan tace “To kai ko ka xauna mana d’an nan” ya xauna smiling
broadly, with respect yace “Ina yini” Kaka na washe baki tace “Lafiya lau, ya sunan naka?” Yace “Junaid Muhd…”
Tace “Junaidu sai kaji kuma wai yarinya ta gurde koh? To ni kai na ban san yanda akayi wnn bala’i ya faru ba, amma
dai na gode Allah tunda ba karyewa tayi ba….” Junaid yace “Allah ya kara kiyaye gaba” Kaka tace “Ameen kai dai….
Don ma uwarka na da fahimta na lura ita ta lallaba Amadu bai dau abun da xafi ba, kasan sa da xuciya, Kuma kasan
shi ya tsinto makauniyar a titin kano tana galantoyi….” Junaid dai bai ce komai ba, kaka tace “To ka leka ta tana
bacci can uwar daka ka duba ta, amma ta fiye son jiki yarinyar, d’an bugewa fa kafar yyi amma duk makota bbu
wanda bai shigo gidan nan ba, ke Zainab kai sa ya ganta, kuma bance ki tsaya kusa da kumbo na ba, kinfi kowa min
sace sace a gidan nan” kasa motsi Zainab tayi, shi dai junaid kansa na kasa, kaka ta ja tsaki ta mike tace “Haka nan
suke min ban isa in sa su aiki ba, ae dai kaga taki kai ka, to ba ruwana ba biyesu nake ba, tunda ‘ya yana na min
biyayya ae shkkn” har dakinta ta kai Junaid tace “To ka ganta….” Junaid na tafiya a hankali ya isa gefen gadon kaka
yana kallon Heedayah dake bacci, kaka ta juya ta fita, durkusawa yyi yana kallon kafarta ya kai hannu kneel dinta,
kwace kafar tayi tana turo baki alamar ta ji xafi, ta juya masa baya ta ci gaba da baccin ta, mikewa yyi walking
gently ya koma dai dai fuskarta ya durkusa, bayan seconds kusan goma yace “Ina ke maki ciwo?” Bude fararen idon
tayi a hankali kamar irin xata gansa din nan tayi shiru staring into space bata dai ce komai ba, lkci daya kuma ta
mike xaune tace “Ina Abba” Bai ce mata komai ba, ya dau ledan da ya gani gefenta dauke da drugs yana dubawa,
bude kofar dakin aka yi junaid ya juya, Sudais ne tsaye bakin kofar yana kallonsu, Junaid ya mike shi ma yana
kallonsa, Sudais ya karasa ya basa hannu nan suka gaisa, sannan ya isa kusa da Heedayah yace “Me ya kai ki wajen
wanke wanke har kika fadi?” Heedayah na kallon inda ta ji muryar tace “Ita ce ta kai ni wajen tace sai inyi wanke
wanke” Sudais yace “To ina ke maki ciwo yanxu?” Kafarta na hagu ta nuna masa tace “But…” Yace “But what?” A
hankali tace “Don’t touch it” kallonsu kawai Junaid yake yi, Sudais ya duka yana kallon kafar sosai yace “Ohkk…”
Hannu ta kai tana laluba wajen don taga ta inda yake, ta ta6a kirjinsa, shi dai kallonta kawai yake, Bude 32 set of
white teeth dinta tayi tace “Wannan sweet din naka ya kare ko?” Ya buda ido yace “Kina so ne?” Ta gyada masa kai
tace “Um” yace “Ohk to bari in kawo maki” tace “Har da short bread??” Juyawa Junaid yyi ya fita daga dakin ya
rufe kofar, Sudais ya kalli kofar sannan ya kalleta yace “Who is he?” Ta d’an yi shiru sannan tace “Shine ya bar ni a
middle of road wai in wuce cikin gida da kai na bayan yasan bana gani, I don’t like him” da mamaki Sudais yace “A
ina kenan?” Tace “A gidansu mana, kuma ina shan strawberry ya dauke min plate din, wai baya son in sha…” Tana
fadin haka ta turo baki, Murmushi Sudais yyi ya mike yace “Toh bari in kawo maki sweet din in dawo” ta kara bude
hakoranta tace “Toh” ya isa kofar ya bude ya fita, xaune ya tadda Junaid a parlor tare da kaka, kaka na nuna sa tace
“To ka gansa, sai dai idan ban ajiye abu ba wllh, shi kuma wancan axxalumin ko magana baya wani yi, sae dai yyi ta
kallon ka yana fama da mugun abu a xuciya, shureen naji suna kiransa ko wa, shi ma dai Aliyun ne, amma gaskiya
xan gaya maka xuciyarsa bbu kyau yau na sake gaskata hakan daxu, to dai duk sunan Mai gidana ne da yayi hatsari
ya rasu” ko kallonta Sudais bai yi ba ya nufi kofa xai fita, kaka tace “Kuma wannan da kake gani yan matansa sun
kusa dozin har na gaji da xuwan da suke gaisheni, yau fara ta xo, gobe baka, jibi mummuna, kai gasu nan dai, ni dai
na gaya ma daya a ciki yaudaran ta kawai yake, to ita ce ta goma xuwa gaisheni, to naga tana da hankali tana ta min
aiki da goge goge” Sudais ya mata wani kallo ya fita ya kulle kofar. Junaid ya d’an yi murmushi yace “To ni xan
koma…” Kaka tace “Da wuri haka har ina murna na samu abokin hira?” Yace “Xan dawo da daddare” tace “Ahh to
shikenan, in ajiye maka abinci kenan?” Wani murmushin da ya bayyana dimples dinsa yyi yace “Toh sai na xo in sha
Allah” tace “Toh Allah ya kawo ka, amma kaddai ka ki xuwa ka bar min abincina yyi kwantai” yace “A’a xan xo”
mikewa yyi tace “Toh ka leka ko ta tashi yarinyar” yace “Toh” daga haka ya shiga dakin, xaune ya same Heedayah,
ya karasa kusa da ita ya kai hannu ya dunguri forehead dinta yace “Kina ji ina maki magana kika min shiru daxu
koh” turo baki tayi bata ce komai ba, yace “Sai na yanke wannan bakin” Tana jin haka ta 6ata fuska lkci daya ta fara
Shesshekar kuka, xaro ido yyi ya xauna gefenta ya jawota jikinsa yace “Ke wasa nake maki fa” Cikin rawar murya
tace “Toh shine xaka ce xaka cire min baki?” Yace “A’a baxan cire ba, sorry” tace “Toh ina Farida?” Yana kallon Eye
balls dinta yace “Ta je Abuja” da sauri ta dago kai tace “Nan ne garinmu mu ma ai” Yana kallonta yace “Where in
Abuja?” ta bude hannu alamar bata sani ba, sai kuma tace “Yaushe xata dawo?” Yace “Soon” saketa yyi ya mike
yace “I’m going” tace “To ni baxan sake xuwa wajen Mami ba kuma, ni ina tsoron wannan matar” Junaid ya buda
ido yace “Me yasa” ta marairaice tace “Tana ma kowa masifa, kuma tana aikana bana ganin hanya” Murmushi yyi
sosai yace “Mami xata xo ta tafi da ke” Shiru tayi bata ce komai ba, yace “Anjima xan xo da daddare” ta gyada masa
kai alamar to, sannan ya juya ya fita dakin. Da daddare Junaid ya xo gidan Baffa kamar yanda yyi ma kaka alkawari, Kaka na can uwar daka, Heedayah kuma na xaune parlon da plate din tuwo a gabanta, Da sauri kaka ta fito jin an
bude kofa, ganin Junaid ta washe baki tace “Ka zo ashe Junaidu” gaisheta yyi ta amsa tana washe baki tace “Bari in
gama gyaran gadon in fito duk ta yamutsa xanin gadon” daga haka ta juya ta koma ciki, Junaid ya ajiye ledan
hannunsa ya koma inda Heedayah take tace “Me yasa ba ki cin abincin?” Kamar jira take ta fashe da kuka a hankali
tace “Ni ban iya ci ba” xaro ido yyi yana kallon tuwo da assorted miyar veg din gabanta, yace “To me xa ki ci?” Tace
“I want to take tea” ya kara wara ido, bude kofar parlon aka yi ya juya, wani dogon matashi ne just his mate ya shigo
parlon, sanye yake da 3 qtr da polo, Shuraim ya karasa cikin parlon waving at him without much interest yyi xaman
sa kan kujera, kaka ta leko don ganin waye, tana ganin Shuraim ta hade rai sosai tace “Dawowa kayi ka kashe mu
lkcn mu bai yi ba ko ya aka yi??” Dauke idonsa yyi daga kallonta ya fiddo wayarsa ya maida dubansa kai, kaka tace
“To idan ma mun mutu bayan ka tafi Junaidu na shaida, ehe” daga haka ta koma ciki, ba a dau wani lkci ba sai ga ta
tafito tana washe baki tace “Sannu Junaidu bari in kawo maka abincin na ka” Junaid yayi murmushi yace “To ngd” a
gabansa ta jera masa abincin, shi dai bai ce komai ba duk da a koshe yake, xata wuce ta gaban Shuraim kamar ana
forcing dinsa yace “Ina yini” tayi kamar bata ji sa ba, sai ga ta ta dawo tace “Toh ka ci abincin mana Junaidu” Junaid
na murmushi yace “Toh” sauka yyi ya bude warmer din ya ga shinkafa ce da lafiyayyen Miya da ya ji nama, sai ga
wani bowl da aka yanyanka kayan ganye, kallon Heedayah yyi da plate din tuwon gabanta, sannan ya kalli kaka
dake kokarin share bakin kofar ta, matsawa yyi kusa da Heedayah murya can kasa yace “Xa ki ci shinkafa?” Da
sauri ta gyada masa kai, Ta gefen ido Shuraim ke kallonsu, Junaid ya dau plate ya diba shinkafar da Miya da nama,
ya dauke tuwon da ta fara kacalcalawa ya ajiye mata shinkafar, a kan idon kaka da ta saki tsintsiyar hannunta ta
mike da sauri tace “La la la kar ka bata, gantalalliya ce wai bata iya cin tuwo ba, to uwar me xa a bata, ko gidan
Amadun da ya tsinto ta ma ai ana tuwo balle nan, mu ba wasu masu kudi bane da xata ce bata cin tuwo har da
hawayenta, shinkafar kuma iya cikinka nayi nima tuwon na ci, idan aka ce xa a biyeta ai sai ta lalace Allah ya
tambayemu….” Heedayah dai sai xare ido take kamar xata yi kuka ta dafe plate din shinkafar don kar ma a dauke,
Junaid yace “Kaka ni na fi son tuwon ne shi yasa” Kaka ta saki baki tace “Allah?” Yana murmushi yace “Ehh” ta
tabe baki tace “Toh Allah ya raba bawa da wahala don ko na wahala gun neman shinkafar nan da miya, to ai sai ka ci
tuwon ita kuma sai ta karata da shinkafar duk da ni dai ban bata ba, kaji min yarinya dai da mugun hali” tuni
Heedayah ta fara cin shinkafar, idan akwai abinda junaid ya fi tsana rayuwarsa tuwo, sai kallon tuwon yake yana
tunanin ta wani side din xai fara ci, da cokali ya debi tuwon ya kai baki yana ci da kyar, mikewa Shuraim yyi ya
maida wayarsa aljihu ya nufi kofa ya bi ta gefen kaka ya fita, kaka ta mike tace “Ka dai ga ko? Mugun hali har tsiro
sai da yyi a jikinsa, tirrr Amadu dai bai yi sa’a ba ya haifi jaraban duniya kawai, to ba gwara min Sudess ba ni dai”
sake bin kofar Junaid yyi da kallo don ya dai ga Shuraim na kama da Abba amma bai yi tunanin son dinsa bane.
Hajiya Maryam ce xaune parlonta kai kace rasuwa aka yi mata, duk ta fita hayyacinta, idon nan nata duk a kumbure
ga su Hajiya Sadiya, Hajiya kyauta, har da Hajiya Amina da dai kawayenta gaba daya sun kusa 7 sai Yan uwanta
uku, Hajiya Zaliha tace “Ban da ma dodewar tunani da kwakwalwa ke har kya dau shawarar wannan tsohuwar da
shekara da shekara kuna dauki ba dadi da ita, to duk gari kowa cewa yake ita ce ma karfin auren barristern, ita ta
matso da auren ma aka yi da wuri wuri” Mumy ta fashe da matsanancin kukan takaici amma ta kasa cewa komai,
Hajiya safara’u tace “Toh Kuma meyasa duk tsawon lkcn nan kika ki kunna waya fisabilillahi” cikin rawar murya
Mumy tace “Ita ta sa in kashe wayar wai sai na basa wahala kafin ya gano inda nake da yara, kuma kusan kullum sai
mun yi waya da ita, tayi ta shirga ni wai Ahmad na nan duk ya daga hankali ana ta nemana gari gari, har rahotu ya
kai ma yan sanda, ko abincin kirki baya ci, da mun gama wayar kuma sai ta ce in kashe da sauri” Mutanen parlon
suka kwashe da dariya ciki har da Hajiya Amina, Mumy ta hade rai tana bin su da kallo, Hajiya Sadiya na
kyakyatawa tace “Ban ta6a ganin makiran tsohuwa irin matan nan ba, gaskiya ta sha ki da yawa, lkci daya ta rama
duk abubuwan da kika dinga mata tana xaune gidan nan” Mumy ta mike tace “To bari ku ji wani abu, ba don ba ni
da abinda xan iya yi bane kan tsinannen auren da barrister yyi ya sa nake kuka ko hankalina ya tashi, A’a kuka nake
saboda takaicin da yarintata ba a min kishiya ba sai yanxu, kuka nake sbda boasting da na dinga yi cikin mutane
Barrister baxai ta6a min kishiya ba, kuka nake sbda makircin da annamimiyar tsohuwar nan ta hada min, ita kuma
wnn mata da tayi kuskuren auren mijina ina jiran shigowarta gidan nan, wllh sai ta gwammace bata ta6a sanin
Barrister ba, ita kuma wnn yarinya da aka min kishiya ta dalilinta….” Wani murmushi Mumy tayi tace “Da farko
xamanta gidan nan kirgagge ne, sannan kafin ta tafi sai na tabbatar da shaida xata bar gidan wanda har girmanta
baxata manta ba, sannan a makantan ta xata tsaya har karshen rayuwarta, wllh wllh bana wani jin kishiyar da aka
min kamar yanda nake jin yarinyar nan a rai na, ita ce sillar rugujewar duk wani farin ciki nawa….” Hajiya kyauta
tace “Toh nan dai da kwana biyu xa su tare da uwar rikon tata, ke dai gashi kin samu an sauya maki komai na
bangaren ki kamar ke ce amaryar, amma ni tunda nake ban taba ganin irin haka ba, anya ba aljana barrister ya kwaso
ba me son ta tarwatsa maki gida, gashi ma tana kan yin haka tunda ta sa an rangada maki kishiya yar boko yar gayu”
Mumy tace “Za mu ga wanda xai tarwatsa wani ni da ita, na fa ce maku ynxu ni ba ma da kishiyar xan goga ba….Baffa ne ya bude kofar parlon Kaka da sauri jin ihun da Heedayah ke yi ya shiga, shi ma shigowarsa gidan kenan
daga masallaci an idar da isha, Kaka ce ta danneta sai shafa mata wani magani kamar rub take a kafan da ke ciwo,
Baffa ya bude baki yace “Meye haka kuma Baaba?” Kaka dake ta hada xufa tace “Toh sai a biye mata tana dingishi
baxa a san na yi ba, so ake ta dawo gurguwa ga makanta abun ya taru ya ma d’a na yawa? da wanne ake son ya ji, a
hankali fa nake mata amma da yake munafuka ce algunguma dubi tonan asirin da take min kamar warce nake
yankawa” Baffa yace “Don Allah ki kyaleta Baaba, ba tana shan magani ba, a hankali xai bar mata ciwon ai” a
fusace Kaka tace “Maganin banxa maganin bature, ka san daga wani kasa aka kawo min wnn din da nake shafa mata,
ku dinga kallona kamar ban san me nake yi ba, toh naki kyaletan sai ka kwace ta ai” Ita dai Heedayah bata fasa ihun
da take tana kiran Abba ba, aka bude kofa Sudais ya shigo parlon da sauri shi ma daga masallacin yake, Bude baki
yyi yana kallon kakar tasa, tace “Kai ka ji ubanka da wani magana Sudess, daga taimako fa xai min rashin kunya, ita
kuma yar banxan magani fa nake shafa mata….” Sudais yace “Toh kaka ba ke kika sa ta wanke wanken ba, ai sai bari
har lkcn da kafar yyi niyyar warkewa ya warke da kansa, ynxu hakan da kike mata idan kika sake ji mata wani
ciwon fa?” Kaka ta tura Heedayah a fusace tace “Ni dai Allah ya isa wllh, ya xa a dinga cewa ni na sa ta wanke
wanke, ga yarinya dai da bakinta ko bata da ido ai sai ku tambayeta ta fadi gaskiya mana, kawai kawai an mayar da
ni karamar mutum a gidan nan sbda ana bani abinci a kwano…. Ban da xalunci me xai sa in sa makauniya wanke
wanke idan ba ita ta bukaci yin hakan ba da kanta??” Juyawa Baffa yyi ya fita daga parlon, Sudais ya jira har ya rufe
kofar sannan yana nunata yace “Ke dai kawai baki son gaskiya, ki yarda kawai kin kusa karya yar mutane kin sa ta
wanke wanken da kika tara an kwana biyar….” Kaka ta fashe da matsanancin kuka tana jawo dankwalinta xata yi
hankici da shi, Sudais ya daga Heedayah suka fita parlon ya kulle mata kofarta yana murmushi, Heedayah dake
dingishi tashin hankali a fuskarta tace “Plss ka wuce da ni wajen Abba kar ka dawo da ni nan” kallonta yake bai ce
komai ba har ya isa stairs, daukarta yyi ya wuce sama, dai dai xai ajiyeta sai ga Ummarsa ta fito daga part dinta,
tsaye tayi tana kallonsa da mamaki fuskarta, yace “Sannu da gida Umma…” Bata amsa ba tace “Ka sameni a parlona
yanxun nan” daga haka tayi wucewar ta, bangaren Aunty ya shiga yana rike da Heedayah, Aunty dake xaune saman
darduma ta idar da sllh tace “Ta ya kaka ta yrda ka fito da ita, daxu da rana kiri kiri taki yarda in fita da ita, wai ba
ruwanta yar amana…” Sudais yyi dariya yace “Ae tana can na barota tana kuka” Aunty tace “Kai dai baka gudun
abun magana koh Aliyu?” Ya xaunar da Heedayah saman kujera yace “Danneta fa tayi tana ta ihu wai magani take
shafa mata a kafar” Dariya Aunty tayi ya juya yace “Ina xuwa Umma na kirana…” Tace “Amma xaka dawo ai” yace
“Ehh xan dawo” daga haka ya fita, Dawowar da bai yi ba kenan har sha biyun dare yyi, Heedayah har ta gaji da
tambayar Aunty ko ya dawo, Aunty ta kai ta bathroom dinta tayi fitsari sannan ta kwantar da ita saman gadonta nan
da nan bacci ya dauketa, yaranta kuma suna dakinsu dama… Aunty na kwance har ta fara bacci ta ji ana kwankwasa
kofar bedroom dinta, ta mike ta kunna wutan dakin tana kallon agogo ta isa kofar ta bude, Baffa ta gani tsaye kafin
ta ce komai yace “Yarinyar nan na nan ne?” Da mamaki Aunty tace “Tana nan har tayi….” Hango kaka da tayi tsaye
bakin kofar parlor tayi kicin kicin da fuska ya sa tayi shiru, Baffa yace “to fito da ita” Aunty bata ce komai ba ta juya
ta koma dakin, sai a sannan ta girgixa kai ta shiga tada Heedayah, tana rike da hannunta har sannan tana magagin
bacci suka fito parlon, Kaka tace “A bani amana sbda ance maku ban san girman amana ba xa ku cuceni ku dauketa,
to uban me xata maki a nan din banda gulma Hauwa? wllh Umaru kasa bacci nayi, gani nake kawai Allah na fushi
da ni, idan Amadu ya ji wnn me ku ke son ya daukeni? To ba ruwana a maido min da abata….” Baffa dai bai ce
komai ba, Kaka ta warce hannun Heedayah a na Aunty ta fice daga parlon Heedayah da har baccin ya fice a idonta
jin muryar kaka ta dinga bin ta kamar xata yi kuka, Baffa ya girgixa kai yana kallon Aunty yace “Toh Allah ya
kyauta” dariya tayi tace “Halan har ka fara bacci” yace “Nayi bacci mana dama” daga haka yyi mata sai da safe ya
fita. Kaka na shiga bangarenta ta kulle kofar tace “Gantalallen yaro kawai in sake ganinsa a parlona idan ban ja
Allah ya isa ba” furan da ta rage ma Heedayah ta dauko mata ta ajiye gabanta tace “Gashi nan baxan shanye ban
baki ba kar Allah ya tambayeni, duk da mugun halin ki” Heedayah ta ta6a cup din a hankali ta kai baki ta fara shan
furan kamar xata yi kuka. Washegari juma’ah da safe Mami ta xo tafiya da Heedayah, Kaka ta kwaso kayanta da ta
wanke ta linke su fesss tace “Sai kin sa ido sosai kan yar nan, shegen son jiki ne da ita kamar mage, baxa a fake da
makanta ba a cuceta….” Mami tace “Toh mama” Kaka tace “Toh har yanxu baki saka ranan tarewar bane ke kuma?
Ba a fa wasa da igiyar aure” Mami tace “Yanxu haka can gidan xa mu wuce gaba daya” Kaka tace “Toh alhmdllh,
kin dai ji duk nasihar da na maki ranan ai ko, yanxu haka matar na can ta dawo, bbu ke bbu ita” Mami tayi
murmushi tace “In sha Allah” sai kusan sha daya suka bar part din Kaka tare da Heedayah….. Horn Mami tayi dai
dai gate din gidan Barrister Ahmad, mai gadi ya bude gate din ta ja motar xuwa cikin gidan tayi Parking a space din
yin hakan, Da taimakon ta Heedayah ta fito a motar, tana rike da hannunta suka nufi entrance din shiga main parlor,
Shuraim ne xaune balcony din da system a gabansa, tun daga nisa da ya kallesu ya dauke kai ya ci gaba da abinda
yake a laptop har suka iso balcony din, Mami bata kallesa ba tace “Take off ur shoes Heedayah” Heedayah ta fara
cire takalmin kafarta, Mami ta ajiye su gefe, ita kam dama bata cire nata ba da shi ta shiga tana bude jakarta don
fiddo wayarta dake ring, ta daga ta kai kunne, Hajiya Amina mahaifiyar Sudais ce parlon da Mumy sai Hajiya
Sadiya da Hajiya kyauta, kallo daya Mami tayi masu ta cikin siririn glasses din idonta still holding Heedayah’s hand
ta nufi bangarenta tana cewa “Ai court ma baxata bada bail dinsu ba, their case is different, baxai yiwu ba ma, so kar
ku ji komai, pls hold on I will call you later” tana fadin haka ta katse wayar ta fiddo makullinta don bude bangarenta
wanda aminiyarta da sister dinta suka xo tun jiya suka yi gyare gyaren da ya kamata, tana shiga ciki rike da
Heedayah ta kulle kofar. a hankali Hajiya Sadiya tace “Tabdijam, lallai kina da aiki babba a gabanki Maryam, idan
baki yi hankali ba wnn farar matar dai kwace maki gida ta shigo yi, ke kin ji wani kamshi da take xubawa kuwa,
kalli fa ko kallon arxiki bata mana ba sai xancen kotu da bail take, da takalmi ma ta shigo parlon don rainin wayo…”
Hajiya Maryam da taji kamar xuciyarta xai fashe don kishi bata dai ce komai ba nan ko naxari iri iri take yi a
xuciyarta tana tunanin ta ina kenan xata fara….