HEEDAYAH SHURIEM CHAPTER 16 BY Maryam sule koki {Maman khairiyya}

HEEDAYAH  SHURIEM CHAPTER 16 BY Maryam sule koki {Maman khairiyya}

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Iyace ta tamik’e da gudunta tabar falon sukuwa su Abba sukayi Kan Shuriem suna jijjiga shi.

Iyace yadawo da sauri d’auke da Goran ruwa b’alle murfin tayi ta Fara zazzagawa Shuriem A fuskarsa, Ajiyar zuciya yayi San nan ya Kama kallonmu d’aya baya d’aya.

Can ya hango Heedaya ta rab’e jikin kujera tana faman kuka Ahankali bakinsa ya Shiga furta Ni Shuriem Na saki Heedaya saki d’aya sakama kon tursa sani da’akayi.

ABBA ne yakwab’e Masa Baki yace” tashi ja irin banza dama hakane yadace da Kai kuma Sai na Aurawa Heedaya miji na nuwa sa’a.

Mikewa Shuriem yayi Yana dafa bango ya shige d’akin momy, iya dai Bata ji dad’in wan Nan lamariba ummy kuwa kamar ta zuba ruwa A k’asa Tasha saboda farin ciki.

Lallab’awa tayi tabar falon wayar ta ta Ciro gefen zaninta ta Dan nawa Haj. Laila Kira ta D’an jima tana ringing San nan ta d’aga ko sallama Babu ta labarta mata Abinda ya faru cikin Murna Maman Meerah Tace” saura k’iris bayyanar ciki kawai muke jira haka suka k’arashe wayar suna shirya makirce makircensu.

Ni kuwa zuciyata fes gwarama Daya sakeni yanzu Ina  da yan’ cin yin Abinda nakeso Momy kuwa Sai daddakemin takeyi ita me d’a Ina lura da ita har rubutu take karb’owa yaya saukar Alk’ur’ani kuwa Anyita ba’a dadi.

Nidai idone nawa gogan kuwa Ina lura dashi Sai Momy ta Matsa Masa yakeyin komai Anty Meerah ma yanzu part d’inmu take wuni ba ruwana da ita Sadiya ma Bata wani Shiga sabgarta kuma dama basa shiri da iya.

Saidai inta gaji da Zama ta wuce part d’in ummy can ne take sakewa.

Wani Abu da na kuma lura dashi shine Momy ta kwashe wasu kayanta ta Mai Dasu part d’in ABBA saboda bedroom 2 ne Acan da Wanda take Amfani dashi Dana ummy Dan ummy Akwai masifa shiyasa ya raba musu d’aki.

Shi kuwa D’an lelen nata Ad’akin yake wuni inbashi da Aiki in kuwa ranar Aikine Agunta yakeyin break fast ya fita in yadawo Anan zaici na dare Sai 10pm yake tafiya part d’insa.

Iya Kam tayiwa Momy Fad’a har tagaji, Ni dai idone nawa magana ma Bata had’a Ni dashi.

Kwana 2 wani irin sauyi nake ji da gani Ajikina nayi fari na fitar hankali gashi na D’an k’ara k’iba, ga wata kasala da nake ji, ga wani shegen kwad’ayi in inason Abu ji nake kamar Naci Babu Sai Ankawomin shi duk inda yake, banacin Abinci Sai kayan kwad’ayi haka iya takesa Yaya Taufi’k yasiya ya kawomin kullum dare Sai Naci balangu in kuwa banciba Akwai matsala haka zan Hana kowa bacci Sai Ankawo min.

ABBA ne yagaji da halayyar da nake Masa da kansa yasa Yaya ya dubani Momy CE tace” Shi Shuriem Ina yaga kayan gwaji A gida saidai suje Asibiti, ABBA dai ransa besoba yace”suje Amma in za’a tafi Aje da iya, haka muka tafi Asibiti Babu Mai magana Acikinmu.

Bayan munzo ne ya cewa iya ta jirashi Awaje saboda Akwai gwajin dazaimin, iya ta tubure ita bazata jiraba, Dr. Suhail ne ya fito suka gaisa da iya Nan iya ta washe Baki domin sun Saba dashi sosai.

Zolayarta ya kamayi Nan yaja ta office d’insa ya cika Mata gabanta da kayan ciya ciye, iya kuwa da taga banza banta tai taci tana Tai maisa Hira.

B’an garena kuwa muna Shiga office d’in da Yaya yawani had’e Rai kwanta ya nuna min gado, ya fad’a hankalinsa nakan scanning machine d’in.

Ad’arare na hau gadon wani Abu Naga ya D’auko kamar Mai San nan yace” janye rigarki” Bata reda ya kalleniba Ahankali na zame rigata.

Matsamin Abun yayi Akan cikina San nan ya Fara gogamin da wani Abu, har yanzu hankalinsa nakan machine d’in can Sai Naga ya mik’e zumbur tareda rungumeni tsam tsam, Yana cewa Allah nagode maka dawan Nan baiwa da kaimin, k’arfina natattaro na tureshi San nan nanu nashi da yatsa nace” Malami ya isheka haka ko A musulunci  yanzu Niba muharramarka bace Aure ya k’are tsakanina dakai.

Murmushin mugunta Yayi San nan yace” to malama yanzu kwanakin iddarki nawa ko kina k’ir gawa Murmushi nayi Wanda iya kacinsa Kan labb’ana San nan Nace” wata 2 cif cif.

Had’e Rai yayi yace” A shari’an ce  Mace Mai ciki ya yata keyin Tata iddar, Nima had’e Rai Nayi nace” daga Randa ta haihu tagama idda good girl ya fad’a Yana shafa D’an ficil ge munsa  nikuwa hakan da yayi bak’aramin  burgeni yayi ba Amma Sai na fuske.

Jim yayi kamar Yana Nazari San nan yace” daga yau Ni Shuriem Na maidake d’akinki, wani malolon bak’in ciki naji har wuyana, mik’ewa nayi Raina Ab’ace zanyi hanyar waje da sauri ya Sha gabana Ashe hannu yasa ta Baya ya kulle k’ofar Sai gani mukulli nayi Ahannunsa Yana karka d’awa.

Ciki tsawa nace” Malami ka bud’emin nafita Aikamarma Baya jina haka yadinga yimin wasu Abubuwa Masu wuyar fassara inaji Ina gani Yaya ya Mai maita Abinda yaymin ran Nan bayan ya Gama yaje yay wanka Nima yace” nayi bayan nafito ne Kai tsaye nayi hanyar fita, ji mana yan’ Mata yace Dani Ahankali na tsaya batareda na juyoba shikuwa Shuriem Murmushi yayi yace Aransa ta Fara kamuwa.

Gaba na yazo ya tsaya Yana kallona cikin Ido San nan yace” Ina da sharad’i guda 2 idan har naji Abin da nai Miki Abakin wani narantse da sarkin da ya busa min numfashi kullum Sai na biki d’akin iya nai Miki Abinda nai Miki yanzu, Sai dai ta bar Mana d’akin, sannan Kar naji cewa na maida ke yanzu A gurin kowa shi kuma innaji hukuncinsa shine kullum cikin dare saikin dawo part d’ina kin kwana tare, kuma kisake naji ga hanya Nan Nima kallansa nai cikin Ido nace Muzuba nida Kai Aga Wanda ze fasa, zagayeshi nayi na mrd’a  k’ofan ga mamakina naji ta bud’e da sauri na fita har Ina tun tub’e gaskiya naji jiki Agurin yaya, wai gya waige na kamayi inda zanga iya.

Can naji maganar Yaya Abayana Yana cewa Megadin Taki kike nema Bari nakirata Wucewa yayi yabarni Atsaye Araina nace lallai Yaya D’an Duniya ne, can Naga Yaya sun fito daga wani office shida iya da Dr. Suhail nikuma Ina ganinsu nai hanyar waje, Abud’e nasamu motar Dan haka na bud’e na shige, Sai gasu sun iso Suma Yaya ne yashiga itama iya tashiga se Hira takeyid da Dr. Suhail Sai wani washe Baki take kome suka Gaya Mata oho.

Dr. Suhail ne ya duk’o ta gefena yace” Ranki ya dad’e kidinga kula Mana da kanki wata harara na watsa mishi Yaya kuwa wani makirin murmushi Yayi da Alama ya sake shirya wata muguntar motar ya bawa wuta muka tafi.

Tafiya muke Amota bawanda yake magana can iya ta hango wani me balangu Nan kwa tatab’oni ta nuna min Ai kuwa kwad’ayina ya motsa haka na cewa Yaya lallai yatsaya ya saimin haka bayadda zaiyi yayi parking ya siya, bayan munje gidane muna fitowa daga mota saiga Anty Meerah ta fito daga part d’in Ummi.

Tana hango mu, Aikuwa da sauri ta nufomu ita kuwa iya harta shige ciki don ta gaji dayawa, zuwa Tai ranta Ab’ace tace” Shuriem me kuma ya had’aka da wan Nan yarinyar ko kallonta be ba yace” Abinda ya had’a Ni dake shine ya had’ani da ita.

Merah kuwa tazo iya wuya kallona tayi sama da k’asa tace” keeee me ya had’aki da mijina Araina nace Anzo gurin kallon Baki isaba nai Mata San nan nace” Abinda ke had’a ki da shi.kullum ko ban Isa bane na fad’a Ina wata jijjiga Aikuwa Meerah ta Gama kaiwa bango.

Hannu ta d’auka zata yarfan Mari yayane yay saurin rik’e Mata hannu San nan ya sa hannu ya wanke mata fuska da Maruka  har 4 San nan yace” karki sake Koda Wasa hannunki ya tab’a min jikin uwar ya’ya’ na domin Ayanzu zancen Dana ke tana d’auke da cikin yan’ 2 Dan haka idan kika kuskura kika tab’ata saina Yi Miki wulak’anci Dana ki tab’a  zata ba………….

         Meerah Ai najin maganar ciki Nan tasoma washe Baki, matsowa tayi kusa Dani ta dafa kafad’ata Tace” San nu Aibansan haka bane Allah dai ya saukeki lafiya musha suna.

Hannnu ta d’aga sama ta kuma cewa Allah nagode maka da k’asa zan ga D’ana nakaina Aduniya wuce ta nayi domin Naga Bata da Aikinyi Yaya kuwa tuni ya wuce yabarmu.

Tana sauke hannun duk ta nememu tarasa Kiran maman ta tashigayi Awaya harta katse Bata d’aga ba, part d’in ummy tayi Bata same ta da kowaba Nan Tai Mata Albishir D’in Abinda taji, Ummy saboda farin ciki har sark’ar gwal d’inta ta bawa Meerah.

Suna cikin Murnar samun cikin Heedaya saiga Maman Meerah ta Kira da sauri Meerah ta da’aga tana Yi Mata Albishir Mamanta kuwa harda gud’arta San nan tace” burinmu ya cika.

yanzu kashe Bari na kira ummy Akwai maganar da za muyi katse kiran tayi takira laying ummy cikin hanzari tad’aga, Nan suka Shiga Murna da farin ciki Ummy harda Yi Mata Alk’awarin cewa su zab’i gidan Abincin da yay musu yau da yamma suje har Haj. Amina duka zatasai musu saboda yau tana cikin nishad’i.

Falon Momy nashiga da sallama ganinsu nayi duk Azazzaune jinayi iya tace”  yar’ halak ga tanan ma ta iso Yaya ne ya gallawa iya wata harara, ABBA ne yacemin Heedaya zoki Zauna ya nunamin gefen k’afarsa zuwa nayi jiki A San yaye nazauna.

Shiru Yayi na D’an lokaci San nan yace” Heedaya kisaurare Ni da kyau kana takane Allah kuma yana ikonsa, ta Allah itace dai_dai, yanzu Shuriem yake cewa sakamakon gwajin da yaymiki kina d’auke da juna 2 har na tsawan sati 8 da kwanaki.

Duk da kowa Acikinmu yasan yadda Akai cikin Nan ya samu Amma Yaza muyi da k’addarar, zaraf nayi nace” Ni ABBA banasan cikin Nan Dan Allah Acire minshi.

 Wani mugun kallo Yaya yaymin Nima kuwa na harareshi, ABBA ne yay gyaran Murya San nan yacigaba da cewa kiyi hak’uri Heedaya Kinga Abinda yasamu Meerah da cikinta ya zube banaso hakq ta faru dake.

Zaraf nai nacewa ABBA maganar rabuwar mu kuma ABBA, D’azu yace” wai ya maidani Ni kuwa banyarda ba wallahi, kuma San nan yaymin, Ai ban k’arasaba Naga yatashi ya nufo ni gadan gadan fuskar nan tasa ba Alamun fara’a Ina ganin haka natashi nai hanyar d’akin iya da gudu, Ina zuwa bakin k’ofa natsaya wani tunani ne yazomin Ai gwanda nayi d’akin Momy Dan Yaya yarana iya, da gudu najuya nai d’akin Momy shikuwa ABBA murmushi Yayi irinnasu na manya San nan ya kalli Momy yace” Momy tashi kibisu wan Nan yaran ba hankali gareshi ba, Momy murmushin tayi tace” kodai Yar’ta kaba Kai bakaga Abinda tayiba ne, ABBA ne ya katseta da cewa to naji yanzu dai tashi kibisu,mikewa tayi  ta bisu  d’akin.

Ni kuwa Ina Shiga ya biyoni Gam naji ya rufe k’ofa ya zare mukullin zare Ido nakamayi nace” Masa Kai Wana irin Mara hankaline kamanta inane Nan to in kamanta Bari natuna maka Nan d’akin babatane, mezesa  ka biyoni Nan Aiko me nayi maka kabari nabar d’akin tukunna . Au Babar kice Ai ban saniba kuma.fad’a naji.

Ji Mukayi Ana buga k’ofa zuwa yay ya bud’e hanya Momy ta nuna Masa da hannu Alamun ya wuce, d’an Sosa Kai ya Shiga yi, had’e Rai tayi Tace” zo ka wuce nace Shuriem.

Haka ya wuce Simi Simi dashi Yana zuwa falo yatarar Sai iya kawai wata harara yadan k’ara Mata San nan yace” to iya ta Allah dai ba takiba Nasan Dama ke kike zuga ABBA da Momy tsohuwa da ke kina Shirin Shiga kabari kina wan Nan Aika Aika, ita kuwa iya babu Abinda yay Mata ciwo irin Daya ce zata mutu, ita iya ba Abinda ta tsana A Duniya irin Kai Mata zan can mutuwa.

Fashewa tayi da kuka kariris saiga ABBA ya fito da sauri Yana cewa” iyata lafiya waya tab’amin ke nuna Shuriem tayi da hannu saboda tak’ai cima yahanata magana.

ABBA kuwa yace” dawa Allah yad’ani in ba dakaiba Nan fa yay Mai tatas kuma yad’ora da cewa yanzu ragamar Auranka na hannun iya Inka bita kun Zauna lafiya kazauna da matarka.

Akasin haka kuwa gata nan gaka kasan sauran mik’e wa yay ya fice yabar falon shi kuwa Shuriem kallan iya yayi yay k’wafa San nan Shima ya fice.

Ni kuwa tsuru tsuru nayi Dan Nasan Momy bazata ragaminba shigowa tayi ta nemi gefen gado ta Zauna san nan tacemin nazo na Zauna kusa da ita jiki Asan yaye na  nataso nazauna A k’asa kusada k’afarta, “Heedaya ta Kira suna Amsawa nayi tareda k’ara yin k’asa da kaina.

Cigaba Momy tayi da magana ke wace irice da Baki da wayo shikenan ke kita hassala mijinki haka Ake rayuwa kintab’a gani nida Abbanku muna irin wan Nan Abun, kuma Akace Miki fad’anne bamayi Amma haka muke dannewa bama nunawa Agaban mutane.

Kina kallon kishiyarki kome za’ai Mata dannewa takeyi Bata nunawa kuma Akace Miki zafine bataji kawai wayo ta fiki.

Inzakiyi hankali ki Kama mijinki A hannunki ki Kama in kuma Zaki barma kishiya gaki Nan gata kina kallo wata Rana zaifi k’arfinki.

Bance karki hukunta Shuriem ba Amma kiyi Mai hukunci ta hanyar dasa Masa soyayyarki me zafi Aransa ta yadda se yazo ya Kama k’afafunki ya Baki hak’uri kuma Rashin kunya ba da taurin Kai da kafiya ba mafita bace.

A ruwan Sanyi Zaki dafa Shuriem Yanda inyaga wata macen ko k’urarta baze so ya kallaba kuma ki Zama me rik’e sirrin mijinki Abinda kikayi yanzu ba dai_dai bane Tona Asirin Miji kansa namiji ya tsani mace, Heedaya kije kiyi tunani Kan magan ganuna tashi kitafi Allah yay Miki Albarka” godiya na Shiga Yi Mata San nan nakoma d’akin iya jikina Asan yaye.

Tabbas magan ganun Momy sun shigeni to gaskiyafa da sake dole na canza taku tunda Yaya Shuriem baida wata makusa Abin Alfahari ne ga mace tasa meshi A Matsayin miji.

Yanzu Kam zan Soma Dan Nasan gaskiya Momy ta fad’amin Abinda kowace uwa ta gari yadace ta gayawa yar’ ta kenan.

Tashi nai nashiga na silla wanka nazo nazauna gaban dressing Mirror nasha kwalliyata na D’auko wata gown me kyau ta Atamfa nasaka nabaza turare kala kala Sai k’amshi nake kitcheen na wuce Kai tsaye na d’orawa Yaya Abinci tuwan shinkafa nai Masa miyar Agushi saboda Nasan Yana San sa, lemon gora na d’aukar Masa na had’a Masa da ruwa d’akin Momy na wuce na nuna Mata ita kanta ta yaba da Abinda nayi tace” na mayar da Abin cin kitcheen Nan da kamar minti 30 tasan zaizo cin Abinci ita kuma zata bar d’akin saina kawo Masa.

Haka kuwa Akayi bayan 30 Mnts na k’ara gyara kwalliyata na kuma fesa turare nad’auki Trey d’in nayi hanyar d’akin Momy Ahanya na had’u da Anty Meerah ta shigo galala ta tsaya tana kallona Ni kuwa kallanta na
yi harda D’an rissinawa nace” Ina wuni Anty Meerah banjira Amsarta ba nashige d’akin Momy d’auke da sallama Abakina.

Yaya na zaune Kan k’aramin kafet d’in dayake gaban gadon Momy Yana Amsa waya, tsugunnawa nayi na Ajiye Trey d’in tunda nashigo yake Bina da kallo Abincin nashiga zuba Masa bayan Naga ma naji sunyi sallama dawanda yake wayar yakashe.

Ina wuni Yaya na fad’a fuskata Asake badai fara’a nakeba kuma ban Sha kunu ba irin dai bayabo ba fallasa d’in Nan Amsawa yayi Acan k’asan Mak’oshin sa mik’ewa  nayi na canza salon tafiya nayi hanyar fita, Shikuwa Shuriem Aransa cewa yake dama yarinyar Nan haka take da kyau Ai ban tab’a k’are Mata kallo hakaba Ai da nabi shawarar ABBA Kam danayiwa kaina, wan Nan Ai saita kasheni da salon gayunta, harna murd’a k’ofa zan fita naji Anturo k’ofar da k’arfi Anty Meerah nagani Atsaye Abakin k’ofar…..⁷¹ ⁷²

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *