HIKIMA CHAPTER 3

HIKIMA






CHAPTER 3








*NEBRASKA*

A hankali matar dake tsaye gefen bed side drawer dake cikin katon spacious bedroom dinta, Tana Sanye da Jeans trouser se katuwar rigar sanyi wadda tsayinta Ya kai kusan gwiwarta Ko ma Ya zarta kadan, kanta hula ce ta saka wadda ta bawa gashinta damar fitowa, kafafunta ruf suke da indoor socks, hannunta rikeda wani karamin frame Wanda ta tsura mishi idanu dukda bata juyo ba amma kallon is so intense, kuma duk abinda akewa wannan kallon to tabbas abun me soyuwa ne cikin zuciyar me kallon, a hankali ta jiyo jin an bude kofar bedroom din an shigo, Hafsa ce, ta kara girma bawai kiba, A’a shekaru sun ja, tayi kyau me sanyi sede kana kallonta Kasan lallai dukda shekarun da aka dauka na batan Lulu bai Bar zuciyarta ba, bata taba tashi ta koma ga Allah ba tareda kukan rashin yarta ba, kullum abin tamkar Sabo Haka yake kara zuwar mata, batasan Har yaushe ne zata daina jin kewar rashin Lulu ba.

Idanunta na digar da hawaye Wanda Ya zame mata jiki, Wanda kullum ne se ta zubar dashi sede idan ranta ya dauke, amma wannan “K” yake constant kenan. Miss A’isha ta shigo wadda girma Ya sameta, ya kara kamata kasancewar shekaru da suke kara karuwa yau da kullum. Gaba daya ta kankance fuskarta da skin dinta duk wrinkles saboda yadda menopause yayi aikinshi. Cikin damuwa ganin yadda yarta ke cikin halin damuwa shekara da shekaru, da ace akwai abinda zata mata ta dauke mata damuwar da tayi amma Allah kadai Keda wannan Ikon. Hannunta tasa ta dafa ta tana kallonta cikeda damuwa da kuma tausayi tace

“Hafsa yaushe ne zaki yi hakuri ki manta komai? Forget your past and move on Hafsa, wannan kukan babu abinda Zaiyi miki banda Karin damuwa da tashin hankali. Haka kike son muyi ta zama kenan?”

Sosae Hafsa ta kara sautin kukanta Dan babu abinda ta tsana a duniya irin Mom tace ta manta past dinta, manta past dinta na nufin manta Lulu Wanda babu Uwar da zata manta danta koda mutuwa Yayi balle nata da jikinta yake bata tana da rai kawai nufar Haduwa ce Allah baiyi ba.

Mom ce ta zaunar da ita, sannan ta zauna tareda fadin

“Hafsa bansan yadda ake jin rashin da ba amma nasan pains din rashin grand daughter, babu yadda zaayi Ki manta da Zainab Nima I don’t hope so, idan nace bury your past Ina nufin kiyi hakuri ki daina kuka, ki dauka kaddarar Ku ce a Haka daga ke har Aminu da Zainab din, dole Ki tuna Zainab amma not this way Hafsa, it’s been long shekaru goma sha biyu ba wasa bane. Ki karba kaddara da hakan Allah zai miki sakayyya mafificiya”

A hankali Hafsa ta goge hawayen fuskata tace

“Mom hankalina kwatakwata yaki kwanciya, nasan shekaru goma sha biyu ba wasa bane, amma kullum ina tunanin ko a Wanne Hali take ciki? Ko wacce irin rayuwa take? ”

Hannunta tasa ta rufe fuskarta tana kara sakin wani matsanancin kukan, shafa bayanta Mom ta dinga yi tana fadin

“Allahu A’alam…. Allah kadai yasan a Ina take, wacce rayuwa take. Hafsa trust in Allah and in his doings bazamu sha wahala ba. ”

Kanta ta gyada Tana goge fuskarta, seda ta nutsu kafin Mom tace

Da sauri Hafsa ta kalla Mom wadda har ta isa kofa, tace

“Mom amma nace miki I don’t want to meet him ever again Ko? ”

Juyowa Mom tayi ta kalleta for some seconds kafin tace

“Then ki yadda ki koma gidan Aminu ”

Mikewa Hafsa tayi Idanunta har sun cicikko jin sunan abinda tafi kauna duk duniya, kallon Mom tayi tace

“I’m not, har Se ranar da na riko hannun Lulu zan koma gidanshi, Kice Bashir Ya tafi kawai” 

Dariya Mom tayi tace 

“That will be forever, as for Ambassador he’s waiting for you, ni ba yar aike bace”

Hawaye yana bin kuncin Hafsa tace. 

“Mom kin daina so na, as I can see”

Kai Mom ta girgiza kawai, Hafsa rigima halayenta suna nan babu abinda ya canza a halayenta se Wanda suka dadu, Ko shekara Batayi ba Aminu Ya gane Babban kuskuren daya tafka na sakinta, yayi ya kada amma taki komen da ya keso bawai Don ta daina sonshi ba A’a Se Dan kawai ta riga tasawa ranta ganin Lulu komenta gidan Aminu, idan kuma babu Lulu babu kome, kuma abin mamaki babu Wanda Ya shiga Maganar, kowa Aminu Ya samu da Maganar Se yace Kunyar Hafsa yake ji, Baa kyauta mata ba, Wanne pain ne bata jiba, batan Ya ga kuma saki na wulakanci to Haka suka shafe shekaru goma sha biyu babu Wanda Yayi aure a cikinsu, suna zaune sun zubawa sarautar Allah idanu. 

Cire jumper jikinta tayi, hakan ya fito da bakar top din dake jikinta, wardrobe ta bude ta dakko wata red Abaya wadda kasanta wani lacy kwalliya akai da hannaye, toilet ta shiga ta wanke fuskarta amma dukda hakan kana kallonta kaga wadda damuwa take kwance a kai, abayar ta zura ta gyara veil din sannan ta ziro wani flat shoe ta sakko kasa fuskarta a dinke tamkar wadda take jiran ganin mutuwa. 

Ambassador Bashir haifaffen Dan Hong ne dake Adamawa state Nigeria, bafulatani ne sosae, shi ne Jakadan Nigeria to American Embassy. Matarshi daya Hauwa da Yara hudu, Dukkansu Mata ne na karshen ne kawai Namiji, akwai Zahra itace Babba tana SS1 a highschool, Na’eeyla tana JSS 2 se Afaf a primary da autansu me shekara biyar Ahmad suna kiranshi Baby. 

Sun hadu da Hafsa shekaru biyu da suka wuce a Saudiyya taje Umra and it happens shima yaje da yaranshi banda Madam wadda ta tafi Nigeria, inda sukayi masauki duk hotel daya ne da Hafsa, se Yaran suke Dan lekawa gurinta musamman Afaf da Zahra saboda sun fi Naeeyla son mutane, Wasu lokutan Ko siyayya zaayi zasuje shopping Se Afaf ta nace Se anje da Hafsa wannan shi ne mafarin komai, Har suka gama suka koma. Ita ta wuce America su sukai Nigeria. Bayan sati tana kwance se wayrta ta Fara ringing, Tana dauka 

“Anty Hafsa yau Papa zai kawo mu California gurinki”

Kai Hafsa ta dafe Don tuni ta gane Zahra ce hakan yasa tace

“Zahra ai bamu gaisa ba, har Kun dawo daga Nigeria din? “

Kai Zahra ta gyada tace

“Dama Mamaa muka dakko.”

Kai Hafsa ta kada tace

“To ai bana California, Mom Dita Anyi mata transfer ta dawo Nebraska da aiki, ki fada masa Kinji. “

A muryar Zahra Hafsa tasan bataji dadi ba Haka sukai sallama tana ta nazarin dalilin wannan sudden ziyarar. Da daddare har ta kwanta Sega wata bakuwar number tana kiranta, da farko bata dauka ba se a Kira na biyu sannan ta dauka, Tana karawa a kunnenta sassanyar muryarshi me cikeda, manyantaka, mazantaka da kamala ta Fara mata sallama, a hankali ta gyara kwanciyarta tace

“Ina yini? “

Tamkar yana gabanta ya girgiza Kai yace 

“Bazan amsa ba, kin tafi kin barmu da kewarki, we wanted to visit you kince ba Haka ba”

Ita se taji Ya zake da yawa, dukda tasan shi ne amma Se tace

“I’m I think ban gane me magana ba”

Dariya ya danyi kadan memakon yaji haushi yace

“I’m sorry…. Papan Zahra, Naeeyla, Afaf da Baby ke magana. Ina fatan kin fahimta”

Gyara kwanciyarta tayi tare da sake sabuwar gaisuwa, cikin jin dadi ya amsa mata, sannan ya Dan jata da hira kafin daga karshe suka koma hira wadda shi yakeyi Hafsa ji take duk ya takurata, Se ta Fara hammar karya hakan yasa ya barta sukai sallama. 

Tun daga wannan ranar Bashir Ya shigo gadangadan cikin rayuwar Hafsa sede Aminu Yayi dashen da ko baya kusa babu Wanda Ya isa Ya tuge abinda ya shuka, Hafsa ta rayu da son Aminu cikin zuciyarta kuma Haka zata mutu dashi a ranta. 

Zuwan farko da AMB. Bashir Zaiyi, gaba daya da Yaran ya taho suka yini sannan suka tafi ranar ita kanta taji dadi tayi walwalar da ta jima Batayi irinta ba. Daga nan yake zuwa shi daya har ya Fara yada manufa da sakonshi amma ko daya Hafsa taki bashi Hadin Kai, hakan yasa yaga better yazo da yayan ko zata amince Don su. 

Tana shigowa dukkansu suka yo kanta suka Rungume, itama daya bayan daya ta bisu da hug da side kiss daga karshe ta dauki Baby ta daura cinyarta sannan ta zauna suka gaisa da Ambassador da dukkan hankalinshi ke kanta, tamkar zai zuketa da idanuwanshi Haka yake ji, wani irin so yake mata irin me zafin nan. Seda suka ci Abinci kafin Yaran suka tafi gurin Mom nan ta gyara zamanta Kamar yadda taga Ambassador yayi 

“Hafsa, Ya kamata zuwa ynzun Ki gane irin yadda kike cikin rayuwar mu nida yarana, muna sonki gaba daya amma kwatakwata baki gani “

Dan Murmushi Hafsa tayi kadan tace

“Ba Haka bane kawai Dan Allah kayi hakuri”

“Me kikai min? Ko korata kikeyi Hafsa? Baki bukatar mu a rayuwarki kenan?”

Gaba daya nauyin kallonshi tace bata sonshi tayi hakan yasa tayi Shiru, shima baice komai ba kawai yana nazarinta ne. Sun kusa mintina goma a Haka se shi yace

“Turo su zamu wuce”

A sanyaye ta mike har ta taka first step taji yace

“Hafsa! “

Juyowa tayi tana dubanshi, fuskarshi da walwala yace

“Ina sonki, just bear in mind apart or together. I love you! “

Juyawa kawai Tayi ta cigaba da Hawa, zuciyarta na mata wani irin bugawa da karfin gaske, Idanunta a lumshe tayi sallama cikin parlon ranta babu dadi kwatakwata, maganganun Ambassador sun tsaya mata amma she can’t help but to shun that love! 

Suna zaune parlon Mom sun baje sunata kallo, tareda hira jefijefi Don sun saba da ita sosae Dan zuwan da sukeyi. Zama tayi gefen Afaf tace

“Papa yace zaku tafi, kowa ya shirya”

Zahra ta turo bakinta tace

“Kai Anty mu kwana zamuyi

Hafsa da sauri ta rufe baki tace

“A’a other time dai amma Mamaa Tana jiranku”

Da sauri Naeeyla tace

“Mummy bata nan, taje Dubai kuma daga can Malaysia zata wuce”

Baki bude Hafsa tayi tana tunanin wacce iri ce matarnan, tunda Yaran ke zuwa kullum Uwar bata nan, is that why he desperately wants her to save the family? Ajiyar zuciya ta sauke tace

“Dukda hakan ku tashi muje yana jiranku. “

Afaf ranta a bace tace 

“Damage ba kya sonmu “

Dariya Hafsa kawai Tayi ta shige daki Ta hado musu kayan da zata basu Wanda babu fashi, Tana fitowa Zahra dake rolling veil dinta tace

“Anty kin siyo min Abayas din? “

Hafsa tace

“Good girl, gwara da kika tuna min na siyo miki, Afaf jeki wardrobe kofar karshe ki dakko wata brown paper bag a ciki kayan suke”

Wucewa tayi dakin nan Mom ta fito dasu chocolates da wafers cikin wata paper bag ta basu sunata godiya suka sauka kasa inda yake jiransu. Yana tsaye Ya harde hannayesnshi a kirji yana kallon idanun Hafsa wadda tuni tayi kasa da nata Kan. 

“Papa kalla gowns din da Anty ta siya min”

Zahra ta fada tana Mika masa paper bag din, baby ya taho yacr

“Nima play ship ta siya min”

Afaf ta Mika masa Wasu set na dankunne Se Naeeyla ta ciro veils. Sosae yaji dadi yana fadin 

“Hafsa I’m very grateful darling “

Murmushi tayi, kafin tayi magana Zahra tace

“Papa kaje se jibi kazo ka dauke mu”

Kallonta Yayi yacr

“Zahra rigima, kada ku takurwa Antyn taku mana”

Ya fada yana kallon Hafsa dake wasa da gashin Afaf, Murmushi tayi tace 

“Ka barsu Se kazo next week ku tafi”

Kanshi Ya gyada tareda fadin 

“If that’s the case, I’ll leave now”

Sallama sukai mishi suka koma ciki Se murna suke abinsu. Ranar Hafsa taji dadin kasancewa dasu, idan suna abu se tana ayyana idan da yarta Tana nan tabbas da tuni tafi Afaf bata Kai Naeeyla ba. 

Bayan kwanaki uku Hafsa ta ware sosae, da Yamma ta shirya Yaran suka tafi strolling sannan zasu karasa wani ice-cream parlor suka sha hade da fish roll. Suna dawowa tunda ta Kalli Mom tasan tabbas akwai damuwa Dan Se zirga zirga take a parlor, suna shiga Mom ta iso tana fadin

“Thank God, you guys are back”

“Me Ya faru? “

Hafsa ta tambaya tana kokarin zama, yayinda Yaran sukai Shiru suma

“We’re flying to Nigeria ASAP”

“Nigeria Mom?! Inace nace Bazan taba komawa ba”

Zama Mom tayi tace 

“It’s urgent we’ve to go, goben nan dan komai is in place”

Dauke Kai Hafsa tayi tareda fadin

“Mom please no I’m going nowhere”

“Dole ne Hafsa don an kama Cynthia tana under police custody a Jos”

Wata zabura Hafsa tayi tareda………. 

“Mom Tana tareda Lulu ne?” 

Kai Mom ta girgiza tace 

“I can’t tell gaskia, abinda babanki yace na fada miki kenan” 

Da sauri Hafsa ta Mike ta wuce dakinta ta bar Yaran dukkansu Sunyi Shiru babu me fadin wani abu, Tana shiga dakin Ta dakko wayarta ta Fara neman layin Ambassador, shi dinma kokarin dialing number ta yake zai sanar da ita yanxun zai taho daukar Yaran se gashi ta rigashi. Ko sallama batai mishi ba tace 

“If you are free kazo ka dauke su Zahra, by 3am zamu bi flight zuwa Nigeria” 

Yadda take Maganar baki daya ta hautsina shi don yasan babu lafiya daga sautin muryarta, amma bai Ko tambayeta ba se cewa Yayi 

“Inshaaa Allah” 

Daga Haka ya katse kiran ya fito, Hafsa mikewa tayi jikinta a bala’in sanyaye ta shiga harhadawa Yaran kayansu tsaf ta kammalla kuma har lokacin Ko daya a cikinsu babu Wadda ta biyo ta, suna tareda Mom Tana basu labarin batan Lulu dukkansu seda sukai hawaye saboda tausayinta da na yarinyar, shiyasa suka ga she need space. 

Misalin hudu na yamma Ambassador Ya kira Hafsa akan yana jiranta a downstairs, mikewa tayi daga Kan praying carpet din da tunda ta hada kayan ta dana Yaran ta hau Tana Kai kukanta ga mahallici akan ya sassauta mata ya bata Ikon yarda da rungumar abinda zata tarar a Nigeria, Haka kurum jikinta ke bata Lulu is not together with Cynthia Dan tasan da tuni Aminu Ya fada mata, Se kawai ta saki kuka hannunta rikeda carpet din, wani irin matsanancin Tsoro yana addabar zuciyarta, bakinta nata maimaita kalmomin neman dauki daga Allah Har ta samu kukan Ya tsaya amma hawaye bai dauke ba, kafarta ta bude ta shiga fito da kayansu Zahra, Idanunta Sunyi jawur saboda tsabar kukan da tayi, a hankali ta shiga dakin Mom tace dasu 

“Papa yazo yana downstairs” 

Bata kuma fadar wani abu ba tayi kasa Janye da trolley dinsu, yana jiyo footsteps dinta ya mike tsaye tareda tsurewa benen idanu Har zuwa lokacinda ta bayyana gabanshi, fuskarta kusan rabi a rife take da veil din da ta yafo, idanu ya tsura mata gaba daya yanayinshi Ya canja daga murmushin da yake zuwa wata irin fuska me cikeda alhini. 

Bata zauna ba kuma ta kasa bude baki balle tayi mishi magana Don data bude to tabbas kuka ne zai kubce mata and ita kuma abinda bata so kenan, kuka a gaban mutane. 

Bayanshi tabi ganin Yayi hanyar barin parlon, jikin matarshi ta Embassy yake tsaye hakan yasa ta tsaya bayan an loda kayan a booth din motar, cikin sanyin murya yace 

“Antyn Zahra kiyi hakuri, rayuwa tana zuwar mana yadda bama expecting Dan ba kowanne so ne yake zama samu ba. Kiyi hakuri Allah yana sane dake. ” 

AI yana rufe bakinshi Hafsa ta kara fashewa da kuka don ita daya tasan abinda takeji cikin zuciyarta, tayi kuka sosae bai hanata ba don yasan shi ne kadai saukin da zataji. Seda ta gama dake ya rigada yasan labarinta hakan yasa tace

“Dazun Alhaji yace mu taho Nigeria an kama Cynthia amma inajin a jikina Lulu is not with her” 

Tana fada ta Kara kifa kanta jikin motar Tana sheshekar kuka, yayinda Ya dinga kwantar mata da hankali cikin tattausan kalami, a ranshi yana raya da ya halasta babu abinda zai hanashi rungumeta ya rarrasheta in the best of way amma hakan bazai yiwu ba sede da kalaman kawai. Seda ta nutsu sannan su Zahra suka fito suka rungumeta suna mata adduar Allah Ya kiyaye hanya. 

Misalin uku na dare jirginsu Ya tashi zuwa Nigeria inda Zaiyi trans in a Egypt kafin ya karasa Birnin Lagos. Tunda sukai boarding flight din Hafsa take Karatun qurani cikin wata iPad dinta, Mom na gefenta Tana bacci, har seda gari yayi haske kafin Hafsa ta rufe iPad din ta runtse idonta, gabadaya tunanin abinda zata tarar take, bakinta banda Innalillahi wa Inna ilahil rajiun babu abinda yake maimaitawa, a hankali wani bacci yazo Ya saceta ba ita ta farka ba seda suka sauka a airport dake Egypt, awanni goma sha biyu zasui kafin su tafi hakan yasa suka nufi hotel suka huta, sukaci Abinci da sallaoli sannan sukai wanka. 

Basu suka isa Lagos ba se bakwai na yamma, nanma kwana suka kara yi Wanda Hafsa gani take tamkar da gayya hakan ke faruwa, Don ta kagu ta ganta a Kano, inda a man aka kama Cynthia, maimakon a maidata Abuja kasancewar sune asalin masu case din se kawai akai transferring case din Kano. 

Washegari da wurwuri suka wuce airport, jirgin da ya Fara tashi daga Lagos zuwa Kano suna cikin passengers din. Suna isa airport akai komai daya kamata suka fito. Mom ce ta Fara hango Aminu tsaye jikin motarshi Baka, Da dukkan alamu ya Dan jima Don se kallon hanya yake, Girma Ya fara kamashi Don a shekaru Arbain da doriya kadan ne babu, yana sanye da kubta kalar brown an zuba mata hand embroidery design coffee, kanshi hula ce ta asalin maiduguri, kafafunshi cikin wani ubansun Mister half cover, hannunshi dake rikeda wayarshi daure da wani agogo me igiya coffee na kamfanin Invicta. Kallo daya zakai mishi Kasan tabbas asiri a rufe yake, dukiya an Tara ta Don a lokacin yana matsayin Head of marketing and sales na bankin First bank na gaba daya Nigeria. Sede komai Yayi yadda akeso amma babu mata balle da, mutane Sunyi Sunyi Yayi aure amma yaki Dan ganinshi Hafsa na Raye wacce Macen zai zauna da kuma, ai sede idan Hafsa bata numfashi. 

Tunda Alhajin sama ya sanar dashi shi zaije dakko Hafsa wadda ya manta rabonshi da ita, shidai abinda zai tuna tunda ta bar Nigeria bayan Ya saketa bata kara dawowa ba, Anyi rasuwa, Anyi bikukkuwa, Anyi suna amma Hafsa sede a waya, duk yadda Hafsa take da Salima sau biyu a shekarun Salima na haihuwa amma bata zo ba. Shiyasa guilt ke damunshi Har yakan samu kanshi da tantamar anya shidin yana son Hafsar? Tunda ya kasa zama da ita lokacinda take bukatar shi the most, dukda yana ganin hakan shi ne kadai saukin su amma baiyi tunanin hakan zata kasance ba Dan Yayi yunkurin maida aurensu sede Hafsa Sam taki bashi Hadin Kai. 

Suna zuwa inda yake tsaye gaba daya Hafsa dashi kanshi Aminu dukkansu sakin baki sukai suna kallon junansu, wata irin kewa, wani irin bege, wata irin kauna wadda suka daskare gaba daya lokaci daya suka taso musu, wani yanayi me wuyar a fassarashi dukkansu suka shiga, babu bakin magana amma idanunsu kadai ya isa zama Dan Aiken. 

“Mom barka da zuwa, how was d flight?” 

Kanta ta gyada masa tana fadin 

“Tiring, but Alhamdulillah! ” 

Kanshi Ya gyada tareda bude mata baya ta shiga sannan ya zagayo ya budewa Hafsa gefenshi, babu musu ta shiga ta zauna har lokacin kuka take, kukan kewa, bege da kuma farin cikin ganin abinda zuciya ke muradi shekara da shekaru, a wannan takin ita kanta Hafsa ta manta dalilin zuwanta Nigeria saboda farin gani da tayi, seda Aminu Ya fara driving sannan yace da ita cikin barbarci 

“Se yaushe Zaki daina kuka ne” 

Juyowa tayi a hankali ta kalleshi sannan tace itama cikin barbarci Dan Mom ba fahimta take ba, iya zamanta a maiduguri basics din kawai ta iya amma bata iya yarawa sosae ba. 

“Bansani ba nima, may be se ranar da dukkan bururruka na suka cika, ranar zan daina kuka” 

Kanshi Ya gyada yace 

“Inshaaa Allah ranar ta kusa zuwa. It’s been long da muka hadu dake, kullum zuciya na kukan rashinki, eyes are longing to see you Hafcy, every night da kyar bacci ke daukata saboda rashinki, Hafcy yaushe zaki bamu abinda muke so? Yaushe Zaki bar zuciyoyinmu su huta? Yaushe zaki?…..
 

Kukan da Hafsa ta keyi yasa dole yayi Shiru, se taji Kamar an bubbude mata duk Wasu channel na jikinta, a hankali son nan nashi da ya daskare ya fara narkewa yana bin circulation dinta, kafin mintuna ya zagaye ko ina cikin jini, tsoka da dukkan komai na jikinta. 
*Hello readers! How are you doing, I’m so sorry for the sluggish post, kunsan jiki da jini se a Sannu. I noticed something that I wanted to clear some people’s doubt a little. About Assisted conception babu inda na rubuta Artificial insemination Haramun ne, babu idan kuma akwai pls notify me ASAP! Kafin na rubuta HIKMAH I made sure nayi bincike kafin na rubuta, Abu daya nake son mu fahimta a rayuwar Hafsa da Aminu, hakuri, neman yardar Allah da kuma shawara. Babu abu daya dasu Hafsa sukai. In life, we need to understand not all desires are best for us, Kamar haihuwar Lulu a ynzun babu alkhairi sede may be Ko nan gaba…… Ina fatan kun fahimceni* 

Mom dai dakko wayarta tayi ta Fara neman layin Alhajin sama, dukda cewar ba Wai tana jin dukkan abinda suke cewa ba, amma tana Dan tsintar Wasu abubuwan. Suna gama wayar ta Kira sunan Aminu Wanda Ya shagala sosae wajen kwantar da kai yana lallamin Hafsa tareda kara kasheta da harshen shi. Seda Mom ta kira shi sau biyu sannan a dan rikice yace 

“Mo….Mom” 

Dan Murmushi kawai Tayi sannan tace 

“Alhaji yace ka wuce station don su sun rigada sun je” 

“To Mom” 

Ya fada Yana kallon Hafsa wadda tayi laushi matuka dan Aminu Ya riga ya gama da ita, kalamanshi sinking kawai suke cikin zuciyarta suna Kara bin circulation pump. 

A Bompai anan aka kulle Cynthia da mukarrabanta, suna isa Mom ta kira Alhaji ta sanar dashi isowarshi, Ko mintina hudu basu cika ba sega shi ya fito, bayanshi Wasu guards ne rike da bindigogi duk wani motsinshi akan idanunsu, Da gudu Hafsa ta isa gareshi ta rungumeshi tana jin wani sanyi na ratsata, shima rungumeta Yayi yana patting bayanta yana fadin 

“Is ok Hafsa na, everything will be ok ” 

Kanta ta cigaba da gyadawa yayinda hawaye suka cigaba da sakko mata babu kakkautawa, hannunta ya kama suna gaisawa da Mom sannan yana fadawa Aminu 

“Ku shigo ciki Dan already commissioner of police ya iso” 

Gaba daya ciki suka dunguma, mutane nata gaishe da Alhaji kasancewarsa a Yanzun shi ne Deputy governor Borno state, a wani katon hall suke zazzaune, yana shigowa kowa ya mike har seda ya zauna sannan suka zazzauna suma, Hafsa se rarraba idanu take don ganin Cynthia amma ina babu ita babu dalilin ta, a gurin Alhaji Bukar Mahaifin Aminu, Dada, Nafi’u, Salima, Habibu, se CP da police officers guda uku. 

Ko gaisawa basu samu Anyi ba, CP da kanshi ya ciro file din case din da akai compiling aka turo daga Abuja, kallon Hafsa yayi wadda itama shi take kallo, baice mata komai ba se umarni da ya bayar akan a shigo da Rebecca. 

“Rebecca? ” 

Hafsa ta furta a hankali cikin tantamar abinda ke faruwa, jin footsteps yasa Hafsa Juyawa nan da nan ta Mike a hanzarce ganin Cynthia Anyi handcuffing dinta, dukda alamu sun nuna cewar tabbas rayuwa ta canza mata amma ko tsufa Cynthia tayi Hafsa zata ganeta, ta rame tayi baki, fuskarta a daddauje da alamun duka taci a hannun police officers din Don kowa yasan yadda Nigerian police suke idan ka shiga hannu tamkar zaki yaga Nama Haka suke. 

Tunda suka hada ido da Hafsa Cynthia ta Fara kuka Tana hade hannayenta guda biyu Kamar me rokon gafara, rokon gafarar take don Tun ranar da ta gudu da Lulu hankalinta kullum a tashe yake, kullum da Hafsa take kwana da ita take tashi a zuciyarta tasan bata kyauta ba, tasan batai yiwa wannan couples din adalci ba, matsayin Wanda suka dinga neman haihuwa idanu rufe suka samu kuma ta rabasu da sanyin idaniyarta. 

“Cynthia shi ne sunan da nayi amfani dashi lokacinda muka hadu dake Anty, asalin sunana shi ne Rebecca, ban taba zuwa Abuja ba Kamar yadda nayi miki karyar ni din yar Abujan ce, bani da hadi, asalina ma ni Inyamura  ce a jihar Edo. Tunda aka haifeni na tashi na tsinci Kaina as a cultist, a Haka na tashi kuma na girma akai. Fuskata tana masifar taimakona saboda Inada fuskar da kana kalla zaka fada trap dina, mutane da dama suna nuna min tausayi amma ni ba abar tausayi bace. ” 

Shiru tayi tareda share hawayen dake fuskarta da bayan hannunta, Babu Wanda ta taba bawa labarinta idan ba yau ba shima tasan babu kufcewa bata isa tayi meddling da mutanen ba, she never taught they’re that powerful ba se Yanzun. 

“Matar da ta kawo ni gurinki aiki nake mata, duk yadda nake tunanin a tsaye nake to tafi ni, hakan yasa ban taba samun space da zanyi wani abu ba, dalilin da na Fara neman hanyar guduwa Dan lokacin sacrifice Ya kusa kumatu ina bukatar yaron da zan Kai. Se kawai naji tana neman yarinyar da zata zame miki Nanny, naji tana bawa kanwar mijinta labarin baku taba haihuwa ba se wannan Shekarar, anan na tuna offering din da zan bayar has to be a precious child, Wanda iyayensa suke matukar so, wannan yasa nace tunda ni tasan halina why not ta barni Nazo gurinki, bata wani ja ba as if tasan manufata ta baki ni, a cewar ta dama anyiwa mata transfer aiki zuwa Ibadan kuma bata son takura ni. ” 

“Farkon abinda na Fara lura a rayuwarku shi ne matsanancin son da kuke yiwa Lulu, kuna sonta kuma kuna son junanku, sede inda na Fara samun gap shi ne a gurin Anty she’s some how careless dukda yadda nake nuna mata ni abar tausayi ce amma a zahiri na fita gatan dukiya, mijinta Wato Abban Lulu kullum na kalleshi Se naga rashin yarda Dani a idanunshi, he always give me a suspicious look.” 

“Na hada dukkan yadda zan fita da Lulu amma na kasa samun wannan damar, kwatsam naji suna rigima akan birthday Lulu, I was super excited Haka na harhada plan dina nayi parking komai against wannan ranar. Ranar tana zuwa Tun safe da kika aikeni karbo cake na fita da kayyayaki na amma saboda hidimar da kike ciki baki Ankara ba. Inata fakon ki har aka gama party babu wani space na hakan seda cikin sauki kika bani ita nayi mata wanka anan ko dakin ban koma ba na fice da ita. ” 

Babu abinda ke tashi gurin banda kukan Hafsa wadda ta daura kanta akan kafadar Dada Se kuma Uhmmmm, lallai da zantukan na zaune. 

“Muna fita dake komai cikin shiri yake ana jirana a Suleja, Mota na samu na hau cikin saa Lulu tayi bacci nako goyata a bayana har muka isa. Ina sauka Yan kungiyarmu nata murna an samu yarinyar offering. A ka’ida kafin akaiwa dodon Tsafi sacrifice Se an Kai offering asibiti an duba lafiyar sa. Washegari muka isa Jos cikin plateau state inda anan muke komai kuma nasan nayi nisan da Bazaa kama ni ba. Seda muka kwana biu dake Lulu ta saba dani kukan da take kadan ne. Ranar da muka kwana biu muka shirya mukaje asibiti inda akai running test da exrays komai normal sede kafarta ta hagu is deformed babu yadda zaayi offering da ita. Hankalinnu dukka ya tashi tunda ga samu ga rashi, munata controversy akan yadda Zamui tackling abin. ” 

“Muna nan muna tunanin yadda zaayi, a Haka Har dare yayi muka kwanta, abinda Bazan taba Mantawa ba muka tashi da safe da tunanin yadda zamu tackling Maganar da yadda zamu samu replacement din Lulu.” 

Se ta Kara saka hannayenta Tana wani irin kuka me tsuma zuciya, officer ne ya daka mata tsawa yace 

“Useless fellow, bazaki cigaba ba” 

A firgice Rebecca ta cigaba da fadin 

“We walk up and couldn’t find Lulu, she got missing” 

“Miss what? ” 

Aminu Ya fada a firgice yana mikewa tsaye, wani wawan Mari dayan police din Ya bata hakan yasa tace 

“Wallahi I said nothing but the truth, iya gaskiya na fada muku. ” 

Shiru gaba daya gurin aka dauka Har lokacin babu Wanda ya iya furta komai saboda su kansu sun San gaskiya ta fada kuma da gaske alama ce ta Allah Ya kubtar da ita daga mugun hannu. 

*_Never employ a nanny whose house you don’t know, some of them might be human traffickers_*

Dukkansu a wannan ranar suka baro Kano suka nufi maiduguri, to me yayi saura? Babu shi tunda itama Rebecca bata san inda Lulu take ba. Hafsa Tasha kuka Har seda Idanunta suka daina budewa, Aminu dake namiji ne babu kuka sede idanunshi kadai zaka kalla Kasan Tashin hankalin da yake ciki yafi na Hafsa, tunda at least nata akwai rangwami ta iya yin kuka amma shi fa? Ji yake tamkar zuciyarshi zata biyo makogaronshi ta fito Haka yake ji amma babu Hali. 

Flight suka bi zuwa Maid, securities duk sun iso suna jiran isowar deputy governor da famylinshi. Yana landing motoci suka zo suka shiga motoci amma Alhaji bai saki hannun Hafsa ba even for a second, Idanunta a runtse dukda ta kasance Baka amma fuskarta ta nuna tsabar kukan da tayi. 

Suna isa gida, ta nufi dakin Dada ta kwanta batareda sanin halin da take ciki ba, can kuma ta Mike ta shiga wanka sannan ta shimfida carpets ta hau sallah Don samun nutsuwa, Aikuwa Ta samu. Tana cikin karatun qurani wayarta ta Fara ringing seda ta kai aya sannan ta janyo wayar da dazun zuwansu airport ta saka SIM dinta na MTN, tana kallon number tasan Ambassador ne, she remembers kafin ta taho daga America ta bawa Zahra number, ganin kiranshi se zuciyarta ta Kara karyewa Dan tasan zatai masa abinda bazai taba so ba shi ne bazata koma America ba, auren Aminu zata koma yafi mata sauki and zuciyarta na gaya mata Aminun shi ne alkhairin kawai. Tana kallon call din Ya katse ta kasa dauka a Haka wani ya kara shigowa se lokacin Tayi ta maza ta dauka, muryar ta acan kasa suka gaisa yace 

“Baa ganta ba? ” 

Hawaye masu dumi suka gangaro mata ta gyada kanta tareda fadin 

“She’s still missing, I pray wherever she’s, she’s safe. ” 

Kanshi Ya gyada da damuwa yace 

“Amin Amin, kiyi mata addua Allah zai amsa. ” 

Itama kanta ta gyada Kamar yana tsaye sannan tace 

“Kayi hakuri, dama nasha fada maka idan Allah Yayi zan aureka it will be, amma….. ” 

Se tayi Shiru ta kasa karasawa, jikinsa a matukar sanyaye ya mike daga Kan kujerar dining din da suke breakfast da Yaran gaba daya, bedroom dinshi Ya shige Zahra da Naeeyla suka bishi da ido jikinsu a sanyaye suma . 

“Zaki koma gidan tsohon mijinki ne Haf? ” 

Shiru tayi har seda yace 

“Ba wani abin bane ba fa Hafsa, it’s normal a kada mutum a fagen soyayya amma hakan yana da kyau tsohuwar zuma ita ke nagani Haka Hausawa sukace. Ina fatan zumuncinmu zai daure har a aljanna. ” 

Sosae kalamansa suka taba ta amma taji dadi daya fahimce ta, Ya gane abinda take nufi, a Haka sukai sallama dukkansu kowa jiki a sanyaye, wayar ta dauka ta turawa Aminu da Alhaji text sannan ta kwanta bacci, kuma har lokacin babu Wanda ya shigo gurinta. 

Lokacinda text din Hafsa ya shigo wayar Aminu yana zaune ya gama shan coffee Wanda yake sha kowanne dare kafin bacci, kwatakwata baya cikin farin ciki amma ya Zaiyi Haka Allah ya hukunta musu, coffee dinma ji yake Kamar extra daci aka kara masa, Hakanan yake sha babu yadda Zaiyi. Yana nan zaune yaji beep na wayarshi alamar shigowar text. Yasan bazai wuce Yan jaje ba hakan yasa ya share seda ya kammalla dukkan abinda yake, zuciyarshi na kwaidata masa son ganin fuskar Hafcy dinshi amma ya hakura don gani yake ba sauararenshi zatayi ba Kamar yadda takeyi kowanne lokaci. 

Yana Hawa gado ya janyo wayarshi se ganin text dinta yayi, jikinshi har Bari yake wajen budewa, wani kuzari yazo mishi Yayi wani durowa daga gadon tareda kai goshinsa kasa yayi sujudus shukr yana godiya ga Allah iyakar iyawarshi, yana dago kanshi ya zaro wayar ya fito tsakar gida, Alhajin sama da Babanshi ya gani a tsaye alamar suna magana ne. Har ya juya zai koma yaji Babanshi yace 

Story continues below


“Aminu” 

“Alhaji barkanku da dare” 

“Barka dai Aminu. Hafsa ta turon text akan zata koma dakinta, me kace?” 

Bakinshi kamar zai yage don Murmushi yace 

“She texted me also” 

Dariya Alhaji Yayi ganin madaukakin farin cikin da Dan nasu ke ciki 

“Amsa zaka maida ita ko A’a? ” 

Wani kallo Aminu yabi Alhaji dashi unconsciously, Eh ko A’a wannan is more of a silly question, Murmushi yayi yace 

“Zan maida ta babu damuwa” 

Dukkansu seda sukai dariyar jin tone din da yayi using. Sunsan da gangan sukai mishi wannan tambayar. 

HIKMAH 

Idar da sallah ta kenan amma ban ma tashi akan praying mat din ba a kalla inason inyi tilawar karatun da mukai kafin gobe naje na kakare, Malam ya samu Nama. Na kai wajen shafi daya naji sallamar Mama, hanzartawa nayi na kai aya sannan na juyo ina fadin 

“Mama zakuyi yamma fa idan baku tafi ba” 

Kanta ta gyada alamar ta yarda da abinda nace sannan tace 

“Taso muje kasuwar, bana son barinki a gidannan ke kadai” 

Mikewa nayi na nufi wardrobe bayan na amsa mata na canja kayana sannan na biyo bayanta. Ina zuwa parlor na iske su Mama da Anty Fadila da alamun ni kawai suke jira, Har na Fara shirin zama Mama tace 

“Karki zauna mana, ke muke jira” 

Tare muka fita zuwa motar Hamma Mustapha shi ne zai kaimu, zamuje kwari hado lefen Anty Fadila Don sati uku kawai ya rage bikinsu. Kusan yadda nake da rawar kai, gashi ina son Anty Fadila bana son ganinta a damuwa Ko kadan, tunda aka sanar mata auren tabi ta lalace idan na tambayeta Se tace min Hamma Mussadiq ne hakan yasa naje Har daki wani yammaci yana zaune system dinshi a gabanshi alamun data analysis yake Dan naji yana ta fada akan Wasu basu aiko da data dinsu ba cikin waya. Seda ya kammalla kafin na zauna tareda sunkuyar da kaina saboda irin kallon da yake bina dashi, Nidai bana sonshi saboda jikina Se Inji wani yam! Amma Haka na daure na zauna cushion din dake kallonshi, 

“Hamma Sannu da aiki” 

Lumshe idonshi Yayi Kamar me shirin bacci sannan ya budesu tar a Kaina tareda fadin 

“Ya akai?” 

Dan kallonshi nayi nayi Murmushi sannan nace 

“Hamma, Dama….. ” 

Se nayi Shiru, I dunno why Se naji Yau nauyinshi nakeji, ture system din yayi tareda bani full attention dinsa, Se na kara gyara zama na nace 

“Dama I wanted to congratulate you” 

Murmushi yayi sannan yace 

“About? ” 

Dan turo baki nayi nace 

“Dama Mama tace zaka auri Anty Fadila, amma kullum tana kukan wai Baka sonta.” 

Tsira min idanu Yayi yana kallona irin intense gaze and piercing one, inajin effect din kallon hakan yasa na Mike Don fita amma ya kamo hannuna, cikin sauri na kalleshi. Quite sure nasan muna having body contact sosae amma na rasa me yasa na wannann ranar was different, abinda naji is beyond comment. 

“Sit ” 

Ya fada da wata murya me bada umarni, zama nayi sannan ya saken hannu sannan yace 

“Da gaske bana son auren, akwai wadda nake so amma Kamar Bazan sameta ba. HIKMAH kinada hikima sosae bani shawara kanwata. ” 

Gyara zama nayi nace 

“Hamma Kasan akwai abubuwa dake pulling dinmu back, lack of gratitude. We’re never grateful da abinda muke dashi, Anty Fadila is an uncut priceless gem, na zauna da ita nasan Wacece ita kuma idan ka aurenta zakasan kayi aure. Just open your heart and let things flow naturally!!! Give my words a thought please” 

Ina gama fadar Haka na Mike na fice, da mamaki yake bina da ido saboda maganganun da nayi are beyond shekaru na amma nasan effect din karatun littafin Hausa ne. Tun daga wannan ranar Anty Fadila bata kara kukan Hamma Mussadiq ba, ta dai cemin ya daina abinda yakeyi mata, ta rasa dalili ko waye yayi mishi magana? Bance ni nayi ba amma naji dadi yaji magana ta. 

A kwari duk inda muka shiga Mama ta dinga takura mata ta zaba kaya amma taki Wai kunya, Se ni ce nake zabar mata Dan nasan me take so, Munyi siyayya ta ban mamaki kafin muka koma gida a mugun gajiye. Muna dawowa gida aka shiga bubbude kayan, ni dai bana hangowa Dan zaki na zaune a gurin Se harara yake Wulla min. Muna zaune Mama tace 

“Hikma jeki dakina a can Kasan trolley sama ki dakko min Wasu ledoji farare. ” 

“Meye Haka Mus’ab, Tana sane zata taka ka? ” 

Mama ta fada cikin daga murya don takaicin abinda yamin. Ga mamakin kowa ko kuka banyi ba, fuskata dai ta nuna rashin jin dadi amma banga dalilin kukan nawa ba, a rayuwata na rasa abinda na tsarewa Hamma Mus’ab nasan ya tsaneni tsana sosae tunda har fada yake bai jin Ko Kunyar idanuna. Wucewa nayi dakin Mama dakko mata sakon naji yana bawa Mama amsar 

“Ita mahaukaciyar inace ? Bata gani wallahi watarana karya ta zanyi a gidannan” 

Ina shiga dakin Mama na taka bedside drawer na janyo trolley din, Ina budewa idanuna yaci karo da wani karamin board Kamar kwali an saka wata paper pink an lullube shi, ga wata chain a hade dashi ya hade da bracelet wadda size din Yaran Yan shekara zuwa shekaru biyu. Wani bakin calligraphy lettering akai a jiki 

_Lulu, my Zainab, our first love that was born 9th September 1996, today is her first birthday……….we so much love you baby_ 

Abinda aka rubuta a jiki kenan daga kasa an rubuta 

AminHafcy 

Shiru nayi na kurawa rubutun idanu, nasan ni ce, Dani ake to me Aminhafcy ke nufi? Duk yadda nayi tunanin kasa ganewa nayi hakan yasa naji gabana nata faduwa….. 
Bude kofar bedroom din da akai yasa nayi saurin maida board din na aje, Kamar marar gaskiya Haka na juyo, Mama ce ta shigo fuskarta blank babu wani expression da zan iya karanta, tsira min idanu tayi tana kallona Har ta karaso sannan tace 

“Menene? ” 

Da sauri na girgiza mata Kai na ba tareda na iya furta Kalma Ko daya ba, nayi waje. Shiru tayi na lokaci kafin ta maida trolleyn ta rufe don bashi take nufi ba, kuma tunaninta bai taba kawo mata zanga wannan board ba. Ina zuwa dakina na zauna gefen gado tareda zabga tagumi, gaba daya kaina a cunkushe yake I dunno what to think of, sede tambaya daya ce su waye Hafsa da Aminu? Mama da Baffa ba iyayena bane? 

Cikin sauri zuciyata ta kwabe ni akan abinda nake tunani, saboda tunanin hakan seda naji kunya ta lullubeni, babu wani gap da aka Bari da zai nuna cewar su ba iyayena bane, Babu wani abu, bayan hakan jikin board Zainab is written amma Meye Lulu? Jin Kaina na barazanar tarwatsewa Se na sulale na kwanta a gurin gaba daya hankalina ya tafi akan abinda na karanta. 

Haka muka cigaba da Hada lefen Anty Fadila, kullum Se mun fita wani lokacin Har dashi kanshi angon. Ana saura kwanaki uku a fara biki na shirya zan tafi islamiyya, na gama saka uniform dina na fito, Anty Fadila tana zaune an kawo gowns dinta da Sauran kayan fitar biki daga gurin dinki, once na ganta Tana ta magana cikeda jin dadi don tunda aka Fara shirin bikin ta dinke bakinta especially idan Mama na gurin ,gaba daya surukuta take da ita. 

“Na zata se an gama biki zaki koma makaranta” 

Bude baki nayi nace 

“Kada Mama ta jiki tace ni nace ki fada. AI daga yau Se bayan biki” 

Dan Murmushi tayi tace 

“Allah Ya kiyaye ” 

“Amin Amin ” 

“Lafiya…. Lafiya… Lau… Yanmata ” 

Ko kallon Arziki zaki baimin ba, na wuce Abuna ina jin yana dannawa abokinshi zagi Wai 

Sauri na kara saboda bansan abinda zai fada next ba, saboda bana son zuciyata ta tsaneshi amma Naga alamar zata kaimu ga Haka, don har na Fara jin wani irin yanayi inhar na ganshi, bana son ganin shi idan kuma muka hadu to gabana Se ya fadi, se naji gaba daya raina ya baci. 

Nayi gaba sosae Kamar daga sama naji ance 

“Beautiful Zainab” 

Ba kowa yasan sunana ba Zainab balle a kirani harda beauty, hakan yasa na kara sauri ina kokarin shan kwana Naga mutum a gabana, seda na tsorata Har na ja da baya se Naga yana Murmushi yace 

“Matsoraciya kawai, makaranta zaki je? ” 

Da sauri na gyada Kaina Ko leben bakina ban bude ba saboda tsoron kar wani ya ganmu tare da Abdallah, ganin yadda nake ta waigewaige yasa yayi dariya yace 

“Jeki yi tafiyarki, Allah Ya bada saa” 

“Amin” 

Na amsa sannan na gebare shi na wuce. Har na shiga class gabana bai daina faduwa ba, duk Tsoro nakeji. Ina zama Malam ya shigo mukai tilawa sannan ya Fara karbar hadda, ni ce ta ukun karshe Don haka ina bada Haddar na ciro invitation card nasu Hamma Mussadiq na bashi, seda ya karanta sannan yace 

Story continues below


“To Allah Ya sanya alkhairi, Se Monday kenan” 

Nayi Murmushi ganin ya fahimci inda Maganar take nace 

“Eh malam” 

Daga Haka na koma gurin zama na muna hira da ta kusa dani Naja’atu, Kawata ce sosae sede unguwarmu ba daya bace shiyasa kawancen a class kadai ake yinshi, amma Hatta a school ga seat dinta ga nawa Haka muke. Kowa ya bada hadda sannan muaki hadisi lokacin tashi Yayi mukai addua sannan muka tashi. 

“Allah Naja bazaki zo ba? ” 

Dan Murmushi tayi tace 

“Ni nace Bazan zo ba, to in fada miki Har dasu Anty zamu zo” 

Cikeda jin dadi nace 

“Allah? ” 

“Da gaske nake. Harda Yaya Nazir” 

Kallonta Nayi tareda jan Tsaki nace 

“Kede bakida zance Se na wannan Yaya Nazirun, Allah Ya kawo shi na ganshi” 

Dariya tayi tace 

“Hikma kenan, ai ke yarinya ce tunda har Yanzun baki San Meye soyayya ba, kinga kina ruwa Har kai” 

Juyawa nayi Dan tafiya gida, se ji nayi ance 

“Ouch! Kafata ” 

Cikin sauri na daga Kaina nan take idanuna suka shige cikin na Abdallah Wanda ke faman yarfa hannu shi a dole na taka shi, bata rai nayi tareda sunkuyar da kaina amma babu wani yunkuri da nayi na tafiya, hakan yasa yace 

“See this girl, kin taka ni instead Ki bani hakuri shi ne kike bata rai?” 

Bakina na turo gaba alamun naji haushi nace 

“Baka kallon gabanka ne?” 

Baki a hangame cikeda mamaki yace 

“Dama kina magana?” 

Banza nayi mishi tareda pouting face dina na Fara kokarin wuceshi, a hankali ya saki dariya wadda tafi kama da chuckling, Juyawa nayi na kalleshi, Haka kurum se na saki Murmushi saboda yadda Abdallah yayi kyau da dariyar. A hankali cikin nutsuwa muka cigaba da tafiya babu Wanda yake magana a cikinmu, amma kowannenmu wannan yanayin na mishi dadi. Seda mukaje kofar gidansu sannan ya tsaya hannayensa harde a kirjinshi yana kallona a nutse yace 

“Se gobe? ” 

Kaina na gyada nace 

“Allah Ya kaimu” 

Daga Haka na juya na cigaba da tafiya, na danyi nisa kadan naji Ya bude muryarshi yace 

“Zainab!” 

Juyowa nayi a hankali, wink Yayi min tareda Murmushi me tsayawa a rai Har seda naji cikina yana Kara, da sauri na juya Se gani a gida Ina maida Ajiyar zuciya. Kamar wadda kwai ya fashewa a ciki haka na karasa cikin gida. Babu abinda idanuna ke hango min banda kayataccen Murmushin Abdallah. 

A hankali ya daidaita parking din matarshi, tsakanin Wasu 206 guda biyu, fitowa Yayi hannunsa rikeda wayarshi kirar Blackberry Q10, cikeda nutsuwa ya shiga gidan, yawanci jikokina a gidan kasancewar weekends ne, sunzo da iyayensu dadin dadawa kuma jiya jumaa aka maida auren Aminu da Hafsa, taro kam anyishi don Kamar wannan ne aurensu na fari. 

A parlor Ya gaida iyayenshi da kamkanin shi, inda Ammiey ke zaune ya nufa, Tana ta faman surutu baki abin magana, shi kanshi mamakin irin yadda Ammiey da Ma suke coping da Maganar, Yan hayaniya ne. Tun yaro yasan Haka to har Yanzun bata canza zani ba. 

“Maina” 

Ta fada lokacinda ya iso gefenta 

“Naam Ammiey, ina Ma? ” 

Dan Murmushi tayi tace 

“Tana dakin Dada” 

Bai kuma magana ba yayi hanyar fita, yana jin wata kanwar Hajja Yakura (Kakarshi) Tana fadin 

“Ka gama miskilancin ka, aure dai babu fashi, ja’iri kawai” 

“Ma! Bakice Dani zaki dawo Nigeria ba, kika barni a Wata kasar bayan Uwata ta dawo gida. ” 

Murmushi Hafsa tayi tace 

“Da na fada maka bazaka zauna ba and Nima unexpected trip ne? Ya exams din? ” 

Kanshi Ya shafa Wanda akai saisaiye babu wata suma me yawa akai, amma da dukkan alamu da mace ne shi tabbas Zaiyi gashi Don eyelashes dinsa kawai abin kallo ne balle azo ga fuskarshi. 

“It was fine Alhamdulillah” 

Cikeda jin dadi Hafsa tace 

“My son is now a cardiologist (likitan zuciya) ” 

Kanshi Ya gyada cikeda jin dadi, se lokacin ya amsa gaisuwar su Zahra Wanda suke ta kallonshi ganin kyakyawar mu’amular dake tsakaninshi da babarsu, sun gane waye Don ko Baa fada ba yana kama da Salima. 

“Kaci Abinci kuwa? ” 

Kanshi Ya girgiza Yana Kara duban agogon hannunshi Wanda Ya kwanta luf a jikin damtsenshi, mikewa yayi yace 

“Ma, lemme pray first, zan dawo naci abincin” 

Kanta ta gyada shi kuma yayi waje hannhnsa rikeda na Baby da yace zai bishi massallaci, kafin ya dawo tuni Hafsa tasa an gama Jera masa abincin da tasan yafi so, komai in place, yana shigowa su Zahra na shirin tafiya Don haka seda yayi nisa da cin Abincin sannan Hafsa ta dawo daga rakiyarsu. Seda ya gama cin Abinci ya wanke hannunshi Har yana kokarin kwashewa ta dakatar dashi akan Zaa kwashe. Zamanshi ya gyara yace 

“Ma abinda ya faru kenan da Cynthia” 

Murmushin takaici Hafsa tayi tace 

“wallahi kua son, jiya ma akai hanging dinsu dukda nace a kyaleta Allah zai saka mana amma sunki” 

Kanshi Ya girgiza cikeda rashin jin dadi yace 

“Allah Ya rufa asiri” 

“Amin” Hafsa ta furta kafin tace “Son karatun Ya isa Haka, Ina ganin is high time daya kamata kayi aure kayi settling” 

Kokarin ya hadiye yawun daya taru bakinshi he ended up kwarewa hakan yasa ya Fara tari sosae har seda Hafsa ta taimaka masa da ruwa kafin ya tsaya, idanunshi tuni sukai ja, jikinshi a mace yace 

“Haba Ma! Kin manta ke kikai min alkawarin aura min Lulu? ” 

Cikeda damuwa Hafsa tace 

“Ni nayi, amma Maina Lulu is in the past, Yanzun shekaru goma sha hudu kenan Ko trace dinta babu, babu Wanda yasan Ko ina take? Tana da rai ko ta mutu? Allah masani” 

A hankali Idanunta suka cicikko amma Haka ta maidasu Dan kukan Ya isa Haka, she’s cried enough. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *