HOD’IJAM CHAPTER 1 BY NOORIEEYAH
Www.bankinhausanovels.com.ng
Kaduna,Nigeria.+
Sake sauke idanunta tayi bisa fuskar kyakkyawan jaririn a karo na barkatai tun bayyanuwar jaririn da mamamallakin jarin gaban ta, ko daga hauka ta warke ba zata kasa ganin kamanni na ban mamaki tsakanin rayukan biyu dake gabanta ba.
“Ina sake tambayarka a karo na uku kuma na qarshe, wallahi wallahi Mukhtar zanyi mugun sab’a maka matuqar kace wasa da hankali na zaka cigaba da yi”
Ta numfasa lokaci guda tana sake tamke fuskar ta tamau tace,
“Yaushe kazama mazinaci Mukhtar?Mazinacin da har ya gawurta wajen yi ma wata ciki?Shin wace iriyar muguwar rana ce wannan yau nake gani?”
Runtse idanuwanshi yayi a hankali, lokaci guda kuma ya sake bude su ya maida su bisa halittar dake rungume a hannun shi yana baccin shi cikin nutsuwa,lokaci guda yanajin soyayyar yaron na sake ninkuwa cikin zuciyar shi fiye da wanda yake ji a baya!har yanzu yakasa yadda cewar wai shi din ubane a yau!uba ba ta hanyar aure ba!uba kuma a shekaru masu qarancin yawa!
“Duk da haka, it was something wonderful that has ever happened to him.”
“Mammy na rantse maki da tsarkin mulkin Allah bantaba zinah ba!bantaba kusantar ta ba, hasalima kinsan abinda nafi kyamata kenan tun bansan muni da illarta ba!ku fahimceni Mammy, please.”1
Kallon banzar da take watso mashi ya sanyashi yin k’asa da kai, can kasan zuciyar shi kuwa tashin hankalin da yake makare cikinta yafi wannan da yake fuskanta, shin yaya zeyi da Ni’imah ne ta fahimceshi?
“Don ubanka toh tunda ba ta hanyar zina aka samu dan ba toh ta ina neh?ko aure kayi a american ba tare da sanin mu ba?”
Ba tasan meyasa ta riqa fatan Allah yasa ma auren yayi ba tare da sanin nasu ba, ko banza dai zata samu sassaucin zafin da kirjinta ke mata.
Girgiza kan da yake ya sanya sauran hope din da take dashi qarasa zubewa,shikenan ta tabbata dan gaba da fatiha Mukhtar ya kawo masu cikin ahali,Mukhtar yakawo mata shege cikin gida, Mukhtar yagama daga mutuncin gidan su ya tika shi da qasa!baabban takaicin ta shine, waima Mukhtar din kwata kwata nawa yake?Allahumma ajirni fi musibati,wa’akhlifni khairun minha!
“Mammy ni banyi aure ba tare da saninku ba wallahi,how could i even try that?haba Mammy ku fahimceni please.”
Zuwa yanzu tagama harzuqa, ta kuma kufula,hakan yasa cikin kakkausar murya tace,
“Don ubanka tashi ka dauki shegen yaronka kubar mun gida, bana buqatar sake sanyaka a idanuwana Mukhtar,i am highly disappointed in you if you must know.”
“Mammy nidai kiyi hakuri kiyafr mani,infact ni duk ba wannan ke damuna ba Mammy, yanzu wanda zai kula mani da babyn nan shine matsalata,amma ina neman alfarmar kitaimaka kibani aron Ni’imah ta tayani riqr babyn kafin nasama mashi Nanny, don Allah mamy don’t say no.”
“Lallai sai yanzu naqara tabbatar da shashanci da rashin wayau irin naka Mukhty,tuna mani shekarunka nawa yanzu ma?”
Ba tare da wata damuwa ba yace “24 Mammy,but age is just a number mana!”
K’arasawa tayi ta kifa mashi wani bahagon mari, marin da ita da tayi shi ita tafi jin jiki, tasani ba tun yau ba, ba tun yanzu ba Mukhtar jarumi ne, ko lokacin da yake qarami yafi qarfin a dokeshi yai kuka, mussaman a islamiyya gaban en matan ajin su, duk zafin bulala haka zai cije yya basar, ba don komi ba sai tsabaragen son girma da dauriya irin tashi.
“Tashi ku fita ku bar mani gida don ubanka,ba zan raini shege a gid…..”
“Mammy don Allah, don Allah na roqeki ki dena sheganta mani yaro, da uwar shi, nine kuma ubanshi!”
“La’ilaha’illahu Mukhy yau me nake gani a cikin gidan nan, ni kake yiwa tsawa Mukhtar?”
Dafe kanshi yayi cikin rashin madafa.
“Mammy ki fahimceni don ya rasulillahi”
“In fahimci ubanka?nace ubanka zan fahimta?shashasha sakarai, inbanda ka na so ka maidani sa’arka ta yaya zaka rika nema ka riqa mani yawo da hankali?Tunda ba ta zina aka samu yaron ba, kuma ba aure kayi ba, toh ta gidan ubanwa ka haifi d’a?dan mutum Mukhtar, dan mutum fa?gaya mani ta gidan ubanwa kasameshi?”
“Mummy zanyi maku bayani, bt as of now i want my son to settle down, kingan shi awowi goma da haihuwar shi babu komi a tumbin sa, ki rufa mani asiri Mammy asamo mani yanda zaayi, wlh Mammy bansan ya zanyi ba.”
Ya ida zancen kamar mai shirin fashewa da kuka, gaba daya kallo guda zakai mashi ka hango zallar ficewa hayyaci a tattare da shi, babu digon natsuwa ko misqala zarratin a ilahirin fuska da jikin shi,tamkar ba dan gayun Mukhtar dinnan ba dan kwalisa, duk ya fice daga hayyacin shi.
Mutsu mutsun da jaririn yafara ne ya sake d’aga wa Mukhtar din hankali,ko kadan ba yasa ya tuno da irin ihun kukan da yarika yanqara masu a cikin jirgi awanni kadan da suka shude, da kyar da ya Allahu aka samu yayi shiru, kiri kiri kuma baya da alamun amsar madarar da asibitin da aka haifeshi sukai recommending a riqa bashi.
Ganin duk ya rude yana faman jijjaga babyn ya sanya tausayin shi kamata, daga uba har d’an duk suka nemi su karyar mata da zuciya, mussaman jin yanda jaririn ke yanqara kuka babu ji babu gani.
“Toh wai ni don ubanka ina kabaro uwar d’an naka ne?yaro yabi ya cika mana kunnuwa da ihu.”
Ji yai qirjin shi na lugude a karo na biyu,duk dunia idan da tambayar da yafi tsana a yanzu, toh bata wuce ta sanin wacece mahaifiyar yaron shi ba, he can never ever expose that to any single soul, infact he rather die than doing so.!”
Zuwa yanzu Mammyn ta harzuqa har ta amshe babyn daga hannunshi, qamshin shi ya sanyata sake kallon fuskar shi, mussaman yanzu da yake kuka sai yakoma mata Mukhtar dinta sak a ranar da ta kawo shi dunia.
Sabashi tayi a kafada tana faman jijjiga shi, lokaci guda tana cigaba da jifar shi da tambayar da yakejin gara tayi ta marin shi da ita.
“Wai bazaka fadi inda kabaro uwar yyaron nan ba, kana da hankali kuwa Mukhy?Yunwa yaron nan ke ji ba sai na sake nanata maka ba, tashi kawuce kkataho da ita ai mai afkuwa ta riga da ta afku, yana iya.”
“Please Mammy na roqeki kibar maganar mahaifiyar shi, nima bansan inda take ba!” Ya ida zancen yayin da wasu hawayen takaici ke sulalo mashi.”
“What?Are you out of your senses Mukhtar?don ubanka ina uwar yaro take?yau nashiga uku ni Khaltume!”
“Mammy idan kika san uwar yaron nan dari zaki shiga ba talatin ba!”
Ya furta hakan a qasan zuciyar shi, yayi da yakejin kukan yaron da na mahaifiyar yaron na mashi amsa kuwwa a cikin kunnuwan shi!
“Ko da wannan kadai aka barshi, zai amshe su a matsayin punishment na zunubin da ya aikata!Astaghfrullah ya Allah!”
Ya furta a hankali.A hankali take toshe bakin ta don ganin tayi matuqar qoqarin ganin kukan nata bai samu ikon fitowa ba, she need to be strong, she really need to be strong despite her being shattered already, but still tana buqatar jajircewa, for herself and ofcourse for her little bundle of joy.+
Lamo ta sake yi a jikin qofar dakin, har a lokacin kunnuwanta ba su fasa dauko mata sautin kukan shi ba, kukan dake tafiya da duk wani bugun zuciyarta, tana jin tamkar zata zauce, tamkar ba zata iya ba, tamkar ta haqura, tamkar ta ruga taje ta amshe shi, ta ji dumin shi, ta sunsuna qamshin sa, ta kuma tabbatar mashi da cewar ita din ce mahaifiyar shi, mahaifiyar da ta zalunce shi, mahaifiyar da bata cancanci zama mahaifiyar shi ba, mahaifiyar da bazata tab’a yafewa kanta abinda tayi ba na sanadin samuwar shi a ban k’asa!
“She is that stupid mother, world really needs to verify her stupidity!”
Takun tafiyar da takeji na dumfaro d’akin ya sanya ta yin baya da sauri, can k’asan zuciyarta tanajin tamkar ta arce da gudu,No, nooo nooo please don’t come in…
Hannunta dafe da gefen cikin ta ta rarrafa domin shigewa makewayin dake manne da dakin,bata da k’arfin fuskantar Mammy a yanzu,she might break into pieces, already dama she is that fragile stranded girl, who is totally lost and doomed!
“Ni’imah?Wai kina ina ne?tun shigowarki kin mak’ale a daki, bayan kinsan da tashin hankalin da Mukhy ya qunso mana, kina ina ne?”
Sake lafewa tayi a bayin tana kokarin shanye kukan da take, da kyar ta saisaita kanta tace
“Mammy kiyi hakuri banajin dadin jikina ne,Ya Mukhy bai fad’a maki ancire mani appendix din bane?”
“Appendix kuma Ni’imah?oh ni Khaltume, wai dama da yace mani likita yace kina fama da appendix yayi qamari har haka?and kuma don sakarci irin naki shine baku qara maganar ba?kina nufin yanzu tiyata akai maki kenan bamu da labari?”
Bude qofar tayi a hankali ta fito, tasani sarai Mammyn na iya ci mata qaniya at any moment, mussaman yanda ta shige bandaki tana bata amsa.
Galala Mammy din tai da ido da baki tana qarewa Ni’imar kallo,duk da tasan cewa Niimar bata cikin sahun mutane masu rama, hakan bai hanata ganin wani girma na mussaman da taga ta qara ba, gaba d’aya sai taga ta dan canza mata,she look too pale and disturbed,tayi mamakin da bata lura da hakan ba tun dawowar su dazu ita da Mukhtar, qila hakan na da nasaba da tashin hankalin da shi Mukhtar din ya sanya ta.
“Haka kika koma Niimah?duk appendix dinne ya maidaki haka?ya jikin yanzu?i hope the operation was done successfully?”
“Eh Mammy im good now alhamdulillah,sai dai fatigue da rashin appattite yanzu kawai, and hopefully i will be good soon in sha Allah.”
“Toh we hope so, Allah yaqara sauqi,Kuma shi Mukhtar yasan a halin da kuka baro american amma shine yake ambatar ki taimaka mashi da rainon yaro,ni bama zan fara tambayarki garin yaya Mukhtar ya samo yaro ba, don nasan kece mutum ta qarshe a duniar da zaki iya sani, amma still inaa mamakin yaushe Mukhtar yai budewar idon da zaije ya dirka wa mace ciki a waje har a kawo mani shegen jika cikin gida na, uptill now nakasa comprehending laamarin nan Ni’ima, wallahi im still in shock.”
Damk’e hannayenta tayi guri guda tanajin luguden da kirjin ta ke faman maimaita wa, lokaci guda kuma sai ta riqa jin wani zafi a qirjin nata, can k’asan ranta kuma ta rik’a maimaita
“My baby is not a bastard Mammy, By Allah my baby is not a bastard!”6
“Ni’imah naji na kuwa?”
Firgigit tayi lokaci guda tana girgiza wa Mammyn kanta
“Afuwan Mammy me kika ce?”
“Yooo ni bansan ya zanyi da Mukhy da dan shegen da ya kawo mana cikin gida ba, yanzu haka gashi can yacika mana gida da ihun banza da wofi, haka kawai muna zaman zaman mu lafiya yaron nan ya jajibo mana musiba da rana tsaka, sannan don baqin iskanci yana gaya man wai baisan inda uwar yaron take ba, anya Niimah Mukhy bai fara shaye shaye ba a american nan kuwa ba?”
A hankali take girgiza kai, yayin da take hanzarin dauke hawayen dake ta zarya bisa kuncin ta.
“This woman had no idea who her son is.”
“Yanzu bari inje imkira Sameera, inyaso sai Mukhtar din yaje yakai mata yaron ta riqeshi a gurin ta kafin asama mashi Nanny, tunda dai kema ba lafiyar ce ta ish…..”
Maganar ta ce ta datse jin anturo k’ofar dakin Niiman,kukan jaririn ya tabbatar masu da ko waye.
Kallon Niiman ya riqa yi a fakaice, gaba d’aya kuma sai ya rika jin yarinyar na yi mashi kwarjinin da bai taba saninta da shi ba, lokaci guda kuma yanajin inama zata tausaya masu?inama zata dube su shi da yaron su, inama zata haqura ta janye qudirin ta, inama zata amsawa buqatar shi?da kuwa ba zai taba dena roqa mata mafi kyawun dunia da lahira har yakoma ga mahallicin sa,sai dai kuma yasani, yasani kwarai babu wadannan alfarmomin a tsakanin su a yanzu.
“Kai don sakarci kasan bata lafiya shine kuma kake demanding ta riqe maka d’a?halan kai dai har yanzu ba zaka dena wannan shegiyyar d’abi’ar taka ta son kanka kai kadai ba?”
“Mammy ba haka bane,naga ne da muna cikin flight tayi dukkan dabarun da tai mashi yadena kuka, shine nake roqon ko yanzun ma zata taimaka mana, don Allah ba don halina ba.”
Ya ida zancen yana satar kallon ta, she look disturbed a lokaci guda kuma babu wani emotion bayan wancan da zaka iya karantowa daga fuskar ta, she isnt even looking ta side din da suke tsaye shi da babyn shi da har yafara gajiya da kuka.
Cike da tausayi Mammyn take kallon Uba da d’an, lokaci guda tanajin wai wannan wace iriyar qaddara ce wannan ta fada masu?a asirce ta hanzarta yin istighfari, kana fuska cike da damuwa ta dubi Niiman dake zaune kanta a qasa.
“Nikam Niimah toh ko zaki daure ki sake gwada sa’arki may be yai shiru kafin yanzu naje na hada ruwan wankan shi,yunwa ce nasan ke damun bawan Allahn nan,inbanda daqiqanci irin na uwar yaron nan ta yaya zata bar d’anta a hannun namiji ta tafi hankalinta kwance?anya babu hauka a tattare da kowace er banzar yarinya ce wannan Niimah?shi dai wannan yaro ya more iyaye, daga uwa har uban taron sakarkaru ne.”
Bata da ikon musawa alfarmar ta Mammyn, mussamman ma yanda jiki da ruhinta ke muradin sake jin dumin babyn nata, she is dying to hug him in her arms.
“Sai ka miqo mata shi skaran banza kai tsaye kana binta da kallo kamar ita tasaka kaje kaiwa er mutane ciki, kai daai wlh Allah ya shiryaka Mukhy.”
Da sauri ya nufi Niiman da nufin dora mata babyn akan cinyarta, baya buqatar sanin me takeyiwa yaron yake samun nutsuwa, amma dai one thing he is sure of shine,no matter what she will never hurt their baby, despite what is going on between them, ko banza jinin shi da nata ne ke gudana cikin jinin babyn nasu.3
Ficewar Mammyn ne ya sanya ta daka mashi wata tsawar da har yanzu yana mamakin yaushe ta iya su.
“Don’t you ever touch me again,and regarding wannan abun”
Ta nuna yaron dake kan cinyarta yana bin fuskarta da kallo tamkar ya santa.
“Karka taba tunanin zan shayar dashi, and karka taba tunanin zan taba kallonshi a matsayin d’a, because this thing is nothing but a retar…..”
Mari ya dauke ta dashi,idanun nan jair ya nuna ta da manuniyar dan yatsanshi.
“Zan iya daukar komi, zan iya jure duk wani batancinki zuwa gareni ko da hakan na.nufin zakiyita duka nane,but one thing im so sure of shine ba zan dauki batanci ko cin zarafi zuwa ga yarona ba, ko da kuwa daga uwar da ta kawo mani shi duniya ne,ki kula.”
“And one more thing”
Yakoma gefenta ya zauna, lokaci guda yaana kokarin nesanta hada jikun su guri guda.
“One more thing, wallahi summa tallahi you must breastfeed my son,those things da kike yanga kike cika kina batsewa a kansu da ba wai ma sun cancanci su zama abincin yarona bane,must be fed to him!wether you like it or not!”
Ba tai mamaki ba, domin daga jiya zuwa yau mari na uku kenan tasha,meye laifinta?laifinta daya na kawo yaronshi dunia, ba tare da sani ko amincewarta ba!1
“Mukhtar Gaya will remain and forever ramain as that monster that has been hunting her since decades!”
“Fiddo ki bashi kafin ragowar hakurina ya qare!”
Muryarshi ta doki kunuwanta.Are you threatening me?”+
Ta tambayeshi cikin yanayi na sarewa.
Mikewa yai da nufin bar mata d’akin, kafin ya idasa ficewa sai kuma ya dakata, haka kuma bai damu da ya juyo ba yace,
“It might be a threath as of now, amma kinsani, kinsan halina, at any moment zan iya watsi da alkawarin da na daukar maki, ina ga kamar wannan ke sanya ki yi mani iya shegen da kika gadama.”
Ya numfasa, kana ya cigaba
“I don’t care if the world happened to know who the mother of my son is, ba damuwata bace kinsani, becauuse hadn’t been ina da wannan damuwar tun farko ma bazan amince wa shawar zuciyata ba in yi sanadin zuwan shi duniya!”
Daga haka ya sanya kai domin ficewa gaba daya, yasani, yasani kwarai yana da son kanshi da yawa,son kan nashi ne ma yakaishi ga aikata abinda ya aikata din, amma yaya ya iya?wannan hanyar din ita kadaice hanya daya tal da tayi mash saura a kafatanin duniyarshi!
“Zakayi danasanin sanina a rayuwar ka, ko ba dade ko ba jima, ka rubuta ka aje!”
Muryarta ta rakashi.
“You have no idea of how much im dying to witness that day Hayatiey.”
Yasan ba taji ba, kasantuwar ya dade da nisanta kanshi da bangaren ta, dama kuma ba damuwar shi bace jin nata, abu guda yasani, abu guda ne yanzu kuma a gabanshi,his SON!
“Yes he is that selfish!”
***
Tun bayan fitar shi tai hanzarin fadawa bathroom ta hada da sanya key, ba tare da wani second thought ba tai qoqarin zaro nonon da yake ta zuba ba tun yanzu ba,kana tai hanzarin sanya ruwan dumi ta dauraye bakin nonon nata,seat din toilet ta zauna ta bayan ta gyaara zaman babyn a hannunta, lokaci guda tana sake tariyo classes na parenting da ta riqa bi a you tube,mussaman domin lokaci irin na yanzu.
Tun bayan da ya cafki nonon take sake qare mashi kallo, wannan shine karo na biyu da ta shayar dashi tun wasu awanni masu qarancin yawa da suka shude bayan ta haife shi.
Tacigaba da kallon shi yayin da yake zuqar nonon a iya gwanancewa na iyawar sa,sai kuma ta riqa jin nutsuwa na shigarta, soyayyar shi ta rika bin lungu da saqo na jikin ta,lokaci guda wani qunci ya sake mamaye ruhinta, me yasa?me yasa qaddara irin wannan zata ziyarceta a qarancin shekaru irin nata?tana ganin tamkar bata isa fuskantaar qalubale irin wadannan ba a rayuwar ta ba?A hankali ta furta istighfari, tare da fatan samun sassauci cikin lamuranta.
Sun dauki kusan mintuna goma sha takwas tana shayar da shi, kallon da take mashi ya sanyata manta rabi da kwata na daga cikin kuncin da duniyar ta ke ciki,kama daga sama ta rik”a jin muryar Fareeda na faman kiranta, da sauri ta janye nonon ta maida cikin riga,sa a lokacin ta lura ma ashe yayi bacci, hakan yasa ta sab’oshi a kafada ta yo waje.
“Ashe kin dawo?tunda muka isa Mammy tace mani kinje gidan Aunty Sakeena.”
Da sauri Fareedan ta matso gaban Niiman, murya cike da zumudi take fadin
“Oh my Allah,i can’t believe what im seeing right now!oh my God.”
Gefe ta samu bakin gado ta zauna tana bin Fareedan da ido, a karkashin zuciyarta kuma ta rika fatan inama itake le da freedom din da kowa kedashi waajen nunawa babyn kauna.
“Babban bala’incan, wai Niimcy garin yaya haka ta faru?i mean how comes?like ta yaya Ya Mukhy yasamo wannan fine boy din?by Allah i cant believe this,dawowata kenan Mammy ke tarata da wannan labarin maras dadi ta wani fannin kuma mai dadi.”
STORY CONTINUES BELOW
Ita dai tagumi tayi tana cigaba da bin Fareedan da ido, dama itace age mate dinta a gidan, although ta dan bata shekara daya, tunda ita yanzu ne take shekara sha bakwai, while Fareedan tana sha takwas, amma ta fannin kkaratu dukkansu bana suka gama secondary school.
“Babe come and see something.”
Fareedan ta yafito Niiman da hannu,
“Dubi d’an yatsanshi, shima yana da cindo exactly irin na Yaa Mukhy,ko baki lura ba?”
Sai kuma tayi shiru bayan ta lura da yanayin na Niiman, da saauri ta matso gefenta ta rungumota.
“Oh im so sorry hun,Mammy tace mani ancire maki appendix din, was that the reason you look too disturbed?infact you look pale, are you alright?”
Girgiza mata kai tayi, lokaci guda tana mai hadawa da murmushi,Fareeda is like a sister to her, ta wuce qawa ko aminiya, tafi jin dadi in tana mata kallon er uwarta ta jini,she lean on her every damn time,but not this time around, coz shr has no idea of what is going on in her life right now!and tasani tasani kwarai babban kalubale ne a gareta.
“I’m okay Fariey, reason why ban faada maki za ai theater din ba kenan, banason damuwarki, kin sani kema baki iya damuwa akan abu ba.”
“Na fahimceki ai, i wish you a speedy recovery, BTW wai don ya rasulillahi garin yaya Yaa Mukhy yaje yai ma wata ciki har ta haihu?”
Qirjin ta ne yafara bugawa da sauri da sauri.
“I thought ya rantsewa Mammy bai taba Zina ba, and a iya sanin da mukai mishi munsani shi din mutum ne mai kyamatar Zina da duk abinda ya shafeta, ko kin manta intuna maki case dinmu da Sadiq Kurfi?”
Fareedan ce ta katseta ta hanyar bata fuska da nunaa alamun yaa isa batason a tada zancen.
“Toh kingani, ni ba kareshi nake ba kinsani Ya Mukhtar is the last person da zan iya bin baya a cikin gidan nan, bt still when it comes to fact,dole in fadi gaskia.”
Tabe baki Fareedan tayi alamun dai still bata gamsu ba.
“Toh wai ke Niima idan ba shege bane wannan yaron toh minene?ni dake da duk wani na duniyar nan munsan cewar Ya Mukhy baida aure, hasalima aure is the last thing on his to do list a yanzu,toh ta ina?kuma ta yaya zai samu yaro in ba ta waccan hanyar ba da yake ta faman rtantse rantse akai,just tell me don Allah? Ta yaya?”
Shiru Niiman tayi tana sake sake a zuciyarta, shin ta yaya Mukhtar zai fahimtar da dunia cewar ba Zina sukai suka samar da yaron nan ba?duk kuwa da cewar still ba ta Sunnar aka samar da shi ba?1
Muryar Mammy ta maido ta daga tunanin da take.
“Ikon Allah yayi shiru kuma ko Niimah?ko ya hakura ya amshi madaranne?”
In ina Niiman ta fara, gaba daya duk ta daburce kasantuwarta wacce bata saba da qarya ba
“Yayi shiru Mammy,nabashi, harda ruwa ma, nafi tunanin ma yafi jin qishi, coz sosai yasha ruwan ma.”
Ta ida zancen tana sosa kai.
“Toh, ikon Allah, shikuma wannan masoyin ruwa ne kenan?da alama babu rabon exclusive breastfeeding a tashi jarirantakar, ko da yake inama akaga ta exclusive tunda madara zai sha ya girma,bawan Allah kai kam iyayenka basu kyauta maka ba, ga dai ta hanyar da suka samar da kai, duk da munsan da cewar taka kaddarar kenan, amma na menene kuma za’aqi tsayawa a shayar da kai?anya zaluncin beyi yawa ba?”
Yanda take kallon babyn zaka rantse da Allah yasan me take cewa,while ita kuma Niiman ke jin tamkar shagube Mammyn ke mata, meyasa kuma takejin dagaske tamkar zaluncin yayi yawa?ga mari ga tsinka jaka,kai har abada ba zata dena tsinema Mukhtar ba, gaba daya yasamu nasarar turning duniyar ta upside down!
Batasan ya akai ba, ta dai ji Mammyn na umartar Fareeda da ta kwaso jerin trolleys guda hudu da Mukhtar din yace duka na kahan babyn nashi ne, itakuma zata je tai mashi wanka.
Cikin zuciyyarta Fareeda take ambaton lallai wannan yaron sosai aka shirya ma zuwanka!
Gyyara kwanciyarta tayi bayan fitar Fareedan, a ranta tana tunanin yanda zata rayu da jaririnta ba tare da wata mishkila ba.
“Ki gudu da shi.”
Wani shashe na zuciyarta garajen sanar da ita, batasan meyasa ba, bakuma tasan dalili ba, sai ta rika jin tamkar hakan ne kadai mafitar da tai mata saura a duniyar ta!
“Ba zan sake zaluntarka ba!this is the least i can do for you my son!”
Daga haka ta mike a hankali ta nufi bandaki domin gasa jikinta a ruwan zafi.
“She really needs to be strong!she need to!”1
***