HOD’IJAM CHAPTER 2 BY NOORIEEYAH

HOD’IJAM CHAPTER 2 BY NOORIEEYAH

                 Www.bankinhausanovels.com.ng 

Kimanin kwanaki biyar har yanzu she couldn’t figure out what to do, like she is just overthinking herself, sai dai me?a duk iya kwnakin nan bata tab’a fashin samun hanyar da zata shayar da babyn ba a boye, atleast sau biyu ko sau uku a rana, duk kuwa da cewar zuwa yanzu ansamo mashi wata nanny wacce ita dama aikinta kenan.

Yau alhamis ranar dake kamawa kwanaki shidda da zuwan Fawad duniya,sunan da uban ya qaqaba mashi as a nick name, a cewar shi solidarity ne toh his most closest friend, wanda kowa yasan da hakan a gidan, althou asalin sunan da yai mishi hudu ba dashi Abdallah ne.

Kamar kullum yau ma da Nannyn ta gama wankeshi, ta shiryashi ta kuma bashi madarar shi sai kinkime shi taje ta kai wa me shi, toh daga nan kuma fa sai Allah, in ya qwaqumeshi babu kuma mai amsar shi sai wani babban dalili, gaba daya son duniar nan ya dauka ya dora ma wannan yaro,al’amarin dake matuqar daurewa Mammyn kai da ma sauran yayyenshi gaba d’aya.

Yanzu haka Aunty Sakeena da Adddah Bilkisu ne a gidan,gaba dayansu zuwan nasu sunyi shi ne akan taka wa Mukhtar din burki, sakamakon dagewa da yake akan llallai sai anyi wa yaronshi taron suna kkamar yanada akeyi wa ko wane jariri a al’adance.

Sunfi awa guda da zuwa, amma gogan naku yaqi yafito daga dakin shi, yana can naniqe da yaro yana faman jijjiga shi, ganin cewa bacci ya kwashe shi sai ya sab’oshi a kafada yayo waje, a ranshi kuma ya riga da ya daura aniyar babu wanda ya isa ya hana taron suna dan shj, ai shima d’a ne kamar koowa, asalima shi din yafi ko wanne sa’a a dunia, kasancewar yasameshi a matsayin uba, inji kenan.

Tunda ya karyo kwanar falon Fareeda ta taso da saurin ta, ita dai duniya tana masifar son baby Fawad, tanajin ma kamar har ta so tafi uban jin shi a ranta, duk kuwa da cewar ita din ba mutum bace mai yawon son yara,amma this time around ansamu canjin feelings akan Abdallah Fawad.

Dakatar da ita yayi da hannu, ba tare kuma da ya dubi fuskar ta ba yace,

“Heyyy, no need thank you.”

Yai shigewar shi ya nemi guri kusa da Mammyn tashi ya zaauna,lokaci guda yana sake gyara zaman Fawad din bisa kirjin shi, bai kuma damu da kallon banzar da Adda Bilkisu ke watso mashi ba.

Ita kuwa Fareeda tsabar takaici batasan lokacin da ta fashe da kuka ba, tun yanzu har anfara masu gorin d’a?d’an da har yanzu ma baa san taqamaimain da wata kalma za’a dangantashi da ita ba, rai a bace ta dubi Mammy tace.

“Mammy don Allah ki amince iyayen Najeeb su zo neman aure na, ko nima Allah ya bani d’a a dena man wulaqanci,d’an ma mai asali, wanda duk duniya zata shaida cewar d’an Sunna neh.”

Shiru falon ya dauka tun bayan da ta fara maganarta rai a bace, bata lura da yanda ko wani mahaluqi dake zaune a falon shan jinin jikin shi ba, ciki kuwa harda Ni’ima dake saukowa daga upstairs.

Sun sani, sun sani kwarai wayene Mukhtar, duk da kasancewar shi d’a na hudu daga ahalin gidan,namiji kwaya d’aya tal kuma a cikin gidan nasu,hakan bai hana shakka da gudun zuciyar shi da duk wani mai numfashi na gidan ke yi ba, tun yana k’ankanin shi yaro ne mai tsananin fishi, yakan iya fishi da komi da kowa matuqar aka tabashi,ga shegen rik’o, halayen da Mammyn ke matuqar iya qoqarinta wajen ganin ta yakice a rayuuwar shi ba tun yanzu ba!

Bai ce komi ba, kamar yanda kowa ke tsammani, hasalima wani asirtaccen smirk ne ke subucewa daga gefen bakin shi, lokaci guda yana cigaba da jijjiga Fawad din a hankali, can k’asan ranshi yanajin daga rana irin ta yau, babu shi babu Fareedah, infact a shirye yake da ya rabu da duk jinsin da zai sake gigin sheganta mashi d’a.

“Fareeda baki da hankali ne?”

Aunty Sakeena tayi kokarin kauda awkwardness din da yai masu shigar burtu take yanke, sun sani cewar suna da right din da zasu dubi Fawad su dangantashi da kalmar shege, amma ba su san meyasa suke jin tamkkar kalmar ba ta dace da yaron ba, hasalima suna jin tamkar wani gagarumin laifi sukai matuqar suka cigaba da dangantashi da waccan kalmar.

Jiki a sanyaye, da kuma wani irin tsoro tattare da ita ta dubi sashen da Mukhtar din yake tace,

“Don Allah Yaa Mukhty ka yafe mani,wlh ba nufi na ba kenan,i utterd such out of anger,afuwan and find it in your heart to forgive me.”

Ta k’arasa zancen da wani irin nadama a tattare da ita.

Still be ce komi ba, and at the same time his face is clearly plane, baka isa ka karanto wani yanayi yake ciki ba, he has that effect on everyone.

“Wai baka ji bane Mukhy ka yafe mata, ai naga kowa yana mistake a rayuwar nan, hasalima kaima mistake din naka ne yai leading to hers, then why the stupid silence?banason wannan banzar dabi’ar taka kana ji na ko?”

“Mammy ya wuce, can we talk about the issue that unite us all here?Fawad want to rest please.”

“Toh rasa kunya beran tanka, gaya mana ka haihu kayi d’a.”

Cewar Adda Bilkisu da duk gidan yafi daga mata k’afa, kila hakan nada nasaba da shirin da suke matuqar yi ne.

“Toh ya za’ayi Addah am,You had no idea of how this handsome being change my whole world, i hope zaki riqe mani shi and fight every mother fucker that ever try ditching my son ko bayan ba raina, kinsan ke kadai nai trusting koh?”

Ai tuni Fareeda ta qara kasa da kanta, itakuma ia tabani ta lalace ta dauko ruwan dafa kanta, wai shin wane tsautsayi ne ma ya hau kanta har ta furta wadannan kalamen?ita har ga Allah ba da wata manufa tai wadannan zantuttukan ba.

“Why not Mukhtar?though ma you will in sha Allah live to raise your bundle of joy by yourself,all is well in sha Allah.”

D’aga mata hannu yayi cikin alamun jinjina.

“Ina yinki Sister, Allahumma amin.”

Dariya su Mammy sukai, sanin babu mai saurin sakko da gogan inba Bilkisun ba.

“Ai inaga kawai ayi taron sunan, sai a fadawa sauran en uwa da abokan arziqi cewar aure Mukhtar din yayi a america ba tare da saninmu ba, then after matar ta haihu Allah yai mata rasuwa, i think that would be better koh?”

Cewar Aunty Sakeena.

Niima da tun shigowarta take gefen Aunty Sakinan sunkuye da kai bata ce komi ba, deep inside her sai ta rika jin tamkar baayi mata daidai ba,meyasa zaa nemi a kasheta da ranta?tanajin kamar ba ai mata adalci ba, can kuma d’ayan gefen zuciyarta tai qoqarin tuna mata matsayin ta a bayyane.

“No please Maman Haneef a wani dalili zaa kashe mani uwar d’a?don’t you think he will feel insulted?i mean look at him staring at you,na tabbata yanajin ki, gaskia ba zaa kashe mashu uwa ba bayan da ranta.”

Ya ida zancen yayin dake kallon sashen da Niiman take qirjin ta na lugude, ba shakka ba zata taba yafewa Mukhtar ba matuqar ya tozarta ta a bainar jama’ah.

“Toh don ubanka tunda tana da rai tana ina?Nifa Mukhtar nafara gajia da wannan iya shegen naka wlh.”

Cewar Mammy tana harararshi.

“Mammy toh don mi zaa kashe mashi Uwar d’a bayan da ranta, gaskia its not fair at all.”

Cewar Fareeda, lokaci guda tana yaqe yayin da take kallon Mukhtar din, duk a cikin kokarin don ganin ta fita daga black list din shi,tafi dan dakon tasha sanin baqin halin shi.

He dont even bother to show some remors, hasalima ko kallon ta beyi ba ya cigaba da maganar shi da sauran mutanen falon,kowa ya lura da hakan, mussaman yanda suka ga Fareedan tayi lakwas, ga idanuwanta da sukai rau rau kamar zata sake tsagewa da kuka.

“Toh uwar wacece uwar d’an naka?wannan shine karo na k’arshe da zan tambayeka, billahillazi kaji na rantse.”

Wani smirk ne bayyane a fuskar shi, lokaci guda ya maida kacokan din kallon shi zuwa sashen da Niima ke zaune gefen Aunty Sakeena sunkuye da kanta, qarqashin zuciyarta tanajin wani irin bugu da qirjin ta ke faman yi, she isnt ready for a day like this, a moment like this!

“Don Allah, Don Allah, Don Allah Yaa Mukhy stick to your promise, kar ka karya mani alqawari, shine alfarma ta qarshe da zakai mani.”

Ta riqa ambatar hakan a qasan ranta, yayin da zufa ke ta faman keto mata ta cikin hijabin ta, lokaci guda ta rika jin tamkar qarshen ta ne yazo yau!

Ku dakace ni.Duk da bata d’ago ba, bakumua ta damu da ta d’ago kan nata ba, amma sosai har cikin jikinta take jin saukar idanuwan mutane da dama a kanta,ta riga da ta sani, ta sani ranar tozarta ta zo,watan jin kunyarta ya tsaya, shin tun farko mi ya hanata bin shawarar da zuciarta ke bata ba tun yau ba?+

“Ni’imah lafiya jikin ki ke rawa?ko baki lafiya ne?”

Muryar Aunty Sakeena ta doki kunnuwanta, hakan yasa jikin nata ya sake daukar rawan da bata da control akan shi,gaba d’ayanta ta daburce a kallo naa farko da zaka iya yi mata.

“Ko Niimah bata ji ne?”

Wannan karon muryar Mummy ce, cikin yanayi na qarfin hali tai qoqarin sakaya tashin hankalinta da wani marayan murmushi, murya a sarqe tace

“Mammy banajin dadi ne, har yanzu banajin qarfin jiki na.”

Bata damu da komawa baya da yayi ba yana wata iriyar dariya a hankali,damuwarta guda ce, damuwar ta d’aya ce, damuwar ta itace kar ya ambaci sunanta a lokaci irin wannan, bata shirya mashi ba, ba kuma tajin jaririyar zuciyarta zata iya jure babban qalubale irin wannan.

“She is that fragile being one could ever meet.”

“Inace jiya kuka koma asibiti?”

Sai kuma ta maida kallonta zuwa Mukhtar din

“I thought kace mani Doctor Nabeel yace babu wata matsala?operation din na improving yandaa ake so?”

Bai fasa kallon Niiman ba, haka kuma bai fasa yin dariyar shi ba a kaikaice.

“Mammy duk abinda na fada maku hakane, sai dai kuma may be she has another hidden issue da mu kanmu bamu da masaniya akai,ko ba haka ba Hayatiey?”

Tsaki Mammyn tayi, lokaci guda tana mai sakar mashi daquwa, ba tare kuma da ta qara bi ta kanshi ba tacewa Niiman ta tashi takoma daki ta kwanta, amma kafin nan ta tabbatar da tasha magungunanta.

Jiki a salube ta mike a hankali da niyyar bin umarnin Mammyn, ko banza Mammyn ta fiddata daga masifar da Mukhtar din ke niyyar jefata, duk kuwa da tasan dalilin Mammyn na yin hakan, Kalmar Hayatie da Mukhtar din ke kiranta dashi, kowa da kowa na gidan yasan yanda Mammy ke adawa da sunan, asalima don bata da yanda zatai da Mukhtar dinne akan qaqaba wa Niimar sunan, ta rabu da shine mussaman saboda nuna mata da yai cewar shi ya tsani Niiman as a name, shiyasa ya zabi ya riqa kiranta da Hayatie, a cewar shi its far way better to think of her positively,than ya riqa resenting din ta saboda wancan sunan da baya so.

Har ta kusa ficewa daga falon ta tsinkayo muryar shi na kiranta, ta so taciga da tafiya tamkar bata ji ba, sai dai bata da hurumin yin hakan, mussaman a idanun Mammyn, hakan yasa ta dawo ta tsaya a gefen shi kanta a k’asa.

“Oyaa daukeshi, and ki tabbata kin bashi dukkan kulawar da yake buqata, when i said kulawa, ina nufin kulawa of the highest order,i hope kin fahimceni?”

The moment yai emphasizing kulawar ta gano inda ya dosa,sosai take son ci mashi mutunci, sosai take son gasa mashi maganar da duk tazo maqoshin ta, sosai take son kawo karshen wannan mulkin mallakar nashi, sai dai kuma sosai take da yaqinin cewa yin hakan a gaban Mammy tamkar k’arawa wuta fetur ne, domin kuwa ta sani, tafi kowa sanin me zai biyo baya.

“Haba baban baby,yanzu fa kaji Mammy tace taje ta sha magani ta kwanta,ko ba yanzu ake maganar rashin jin dadin ta ba a gaban ka,haba, wai yaushe kazama maras tausayi ne?”

Fareeda kam ji take kamar zuciyarta zata yo waje don haushi, ita wallahi ta tsani yanda Ya Mukhtar ke treating Niiman, ko banza ai itama er uwarshi ce inda kara, although laifin ba na kowa bane sai na Mammy.

Kunnen uwar shegu yayi da Aunty Sakeenan da ke faman b’ab’atu, ba tare kuma da ya damu da idanuwan mutanen falon ba ya sukuya don yi mata rad’a a kunne

“Make sure you breastfeed him to his ultimate satisfaction,inajin ya cancanci hakan ko Hayatiey?”

Da tana da iko da dago wannan kyakkyawar fuskar tashi da yake taqama da ita zatai ta wanke da mari, mari ba sau d’aya ba, ba sau biyu ba, ba sau uku ba,in son samu ne tayi ta marin shi to her on satisfaction,daga nan kuma sai ta bugi k’irji ta nunawa duniya shi din wani irin mutum ne, kwarai dagaske duniya na buqatar sanin mugayen mutane irin Mukhtar Gaya.

Sai dai me?bata da iko, ko hurumin aikata ko abu guda a guri irin wannan!abu guda take da ikon yi yanzu shine amsa wa buqatar shi,shine tsirarta.

A hankali ta juya rungume da jaririn, k’asan ranta tana jin anya haka be isa ba?anya ba zata samawa kanta ‘yanci ba?it has been ages since yaro da uwa ke gara rayuwarta yanda su ke so, duk da qarancin shekaru irin nata, ta fahimci gajiyawarta, ba tun yanzu ba,ba tun yau ba, lallai she need to move, she need to, she have to!ai tanajin kamar haka ya isa koh?

Tana qoqarin billewa ta jiyo muryar Mammyn na bambami.

“Don ubanka kabini a hankali Mukhy, wai bance ka riqa nesa nesa da Niimah bane?meyasa ka rainani ne?”

Shiru yayi yana qara had’a rai, har gobe yakasa comprehending wannan lamari na Mammy,tanason Niimah da dukkan iyawarta, abu guda ne ta tsana, take kuma adawa dashi tun shekaru uku da dawowar Niimar gidan su daga america bayan rasuwar iyayenta, abu guda ne tal!ta tsani ko kallo irin na en uwantaka Mukhtar din yai wa Niiman, ta tsani taga yana bin ta da kallo irin na so, ta tsani duk wata mu’amala daka iya hada Mukhtar din da Niima, bata kaunar ko a mafarki Mukhtar din yai gigin fara qaunar Niiman, qauna irin ta aure, ba don komi ba sai don sanin ainihin wacece Niimahn!

Ta sani,ta sani kwarai,Niimahn bata da laifi ko kwaya d’aya na daga hanyar da aka sameta, laifin ta d’aya shine samar da ita da ita da iyayenta sukayi ba ta hanyar da addini ya hukunta ba,duk da cewar ba zaka dubeta kai tsaye ka kirata da shegiya ba, at the same time kuma ba zaka dubeta kai tsaye ka danganta ta da diyar sunna ba!4

Laifin ta kenan kwaya d’aya tal!laifin da ita kanta bata san dashi ba, batasan da kwatankwacin shi ba, abinda tasani shine ta rayu da mama da babanta cikin so da qauna, da kumma dukkan kulawa da gatan da yaro zai iya samu daga iyayen shi, kafin rana d’aya, lokaci daya Allah ya dauke mata iyayen da har ta koma ga mahallicinta ba zata dena kuka da maraicin su ba.

A dalilin hakan she faces alot of challanges a mafi qarancin shekaru irin nata!

“Na dai fada maka babu kai babu Niimah ko bayan raina,ba tun yanzu baa anga alamar ba jin gargadi na kake ba.”

“Haba Mammy wai don Allah meyasa kike haka?kuma ma naga Mukhtar din bai taba cewa yanason Niimah ba, besides lets assume ma yace yanason nata?menene a ciki?duk ba jin dadin mu bane gaba daya?”

Cewar Adda Bilkisu da tun dazu bata ce komi ba.

“Nidai nagama magana,ko bayan ba raina ban amince wata alaqa ta shiga tsakanin shi da Niimah ba,I’m done talking.”

D’age kanshi sama yayi gamida rufe idanuwan shi a hankali, kana daga can k’asan makoshin shi ya furta

“I’m so sorry Mammy, i have failed you completely.”

Lokaci guda yana jin son ta na qara girma a zuciyar shi,she is the reason why he is still functioning, his happiness and his sadness!

Ya sani he cant choose her over his own mother, at the same time kuma ba zai iya hakura da ita ba, she is his body and his soul, zuciyar shi na bugawa ne da soyayyarta, wacce yake jin ba zai dena ba sai bayan tsayuwar numfashin shi.

Is that even enough word to say how much he loves her? She perfectly complete him!yanason ta da dukkan ruhin shi!son nata ne ma yakaishi ga aikata abinda ya aikata din, infact shine option na qarshe da yakejin zai taimaka mashi wajen samunta.

“Hayatiey.”

Ya furta daga k’asan maqoshin shi.Lexington Avenue,USA.+

Za ta kira shi,za ta sake kiranshi, infact she will keep on calling him even if yin hakan zai qarar da duk sauran dignity da pride din ta a matsayin ta na ‘ya mace, she don’t care, she never do care da duk wani abu da zaa iya danganta ta dashi indai akan Mukhtar neh,he is the reason why she is still holding on to life, tana yi mashi son da ba tai wa kanta!

Duk kuwa da sanin da tayi na cewar itace halitta ta k’arshe da zai iya d’aga ido ya kalla da sunan so!Har gobe ta kasa gane ta ina ta gaza, ta ina ta kasa, ko kuwa da me Ni’imah ta fita,ta dade tana zana surar Niiman a fuskar ta, ta dade tana son sanya idanunta bisa fuskar yarinya Niimah, ta dade tana son sanin me take da shi har haka da ya d’auke hankalin Mukhy daga kan duk wasu jinsi na ‘ya’ya mata!She really is dying to see this bitchhh.

“Najma zanje gidan su Mukhtar,i cant hold it anymore!”

“Kina ganin Ra’is zai baki duk wani clue da kike nema?”

Bata bata amsa ba, sai bayan tagama nada brown vail din akan ta mai dauke da yalwataccen gashi mai tarin yawa da cika, a kallo guda da zaka iya mata kai tsaye zaka iya danganta ta da irin larabawan somali dinnan,she just defines the word beautiful!

“I don’t think Ra’is zai iya watsa mani k’asa a ido, kinsani, kinfi kowa sanin waye shi, and how he always worship me, ba zai bani matsala ba ina tunanin hakan.”

“Altight then,inafatan ki samu abinda kika je nema, you take care.”

“I will surely do that, especially for Mukhtar’s sake.”

Murmushi Najman tayi, yayin da can qasan zuciyarta haushi gami da tausayin k’awar tata rufeta kamar koda yaushe,ta kan rasa wannan musiba da Allah ya dorawa Fadwah,ita kumaa tata qaddarar kenan!

“Allah ya sauqaqa maki Fadwah”

Ta furta hakan a k’asan ranta,yayin da take sake maida hankalinta kan littafin gaban ta, in few coming weeks zasu fara rubuta final exams din su a medical school, but look at Fadwa,she just dont give a damn,karo na biyu kenan da qila za ai mata repeating,ba wai mussamman don diqiqanci ko gazawar ta ba,ah ah sai don sakaci da kuma qalubale da kuma gallafiri da qaunar Mukhtar din ke sanya ta!

***

Madison Avenue

New york city, USA.

Yacigaba da kallonta cike da tausayi, har gobe yanai mata uzuri, sosai yake mata uzuri, mussamman don sanin ainihin abinda ke kokarin zauta ta, shin sai yaushe Fadwa zata baiwa zuciyarta hakuri?sai yaushe zata fahimci tarin baiwa da mai duka yayi mata?sai yaushe zata fahimci cewar duniyar fadi ne da ita?duniyar na da matuqar fad’i da girma,sai yaushe zata fuskanci alkibla, ta gane cewar in wani ya qika da wuni, to fa wani da kwana zai so ka, ta yaya zai samu yafahimtar da ita hakan?

“He is tired of trying!”

Dafe kanshi yayi cike da sarewa da lamarin, sosai yake jin sautin kukan nata har cikin jiki da b’argon shi, sai yake jin kuma inama shi ke da ikon kokawa, dama zai samu wannan damar,kila da hakan yataimakeshi wajen rage nauyin da yake ji a tashi zuciyar.

“Look at me Fadwah.”

Ya sake maimaitawa a karo na uku,wannan karon ya samu sa’ah, domin kuwa ta d’ago d’in, hawaye shabe shabe bisa kyakkywar fuskar ta mai sanya shi jin duk dunia babu mai kyawu da tsaruwar ta,meyasa har yanzu wacce yake fama da dakon son ta tun ranar da yafara dora kwayar idanun shi a kanta kasa fahimtar hakan?asalima a ranar ita kuma qaddarar qaunar aminin shi dirar mata, dirar da har yau ke dawainiya da duk farin cikinta, domin kuwa daidai da rana d’aya bata taba samun ko da mafi qanqantar kulawa bane daga Mukhtar din ba, its sad, so sad.

STORY CONTINUES BELOW

“Zaki iya yin komi domin mallakar Mukhtar?”

Kallon shi take da dan guntun mamaki a fuskarta, ai tana jin ta wuce wannan matakin a k’aunar da take wa Mukhtar.

“Ofcourse zata iya yin komi akan Mukhtar, ko da hakan na nufin b’atawa dubban mutane ne, ko da hakan na nufin subucewar farin cikin wasu, ko da hakan na nufin zubewar mutuncin ta ne, ko da hakan na nufin qarshen duniya ne,yes she can be this selfish, indai a kan son da take wa Mukhtar Gaya ne.”

Yasani, yasani kwarai, Fadwa can do anything just to win Mukhtar all by herself, matsalar guda daya ce, bata da masaniya akan abinda zata yi din, amma shi yana tunanin yana da masaniya akan hakan!kuma yanajin he can also do anything for her, not to win her, but to make her happy, to complete her by giving her what she desires, ko da hakan na nufin cin amanar abokin shi ne, bai damu ba, ba kuma zai damu din ba, as long as Fadwa will be happy!farin cikin ta shine babban priority din shi a yanzu.

“So be it.”

***

Kaduna Nigeria.

“Nagaji da maimaita magana d’aya a cikin gidan nan Mukhy,sau nawa zan fada maka banason yawan takurawa Niimah da kake a cikin gidan nan?Shin minene amfanin Nannyn da aka samo da kullum baka da aiki sai zaryar zuwa dakin ta?kabi ka takurawa yarinyar mutane, kamar ita tasanyaka samo yaro a kwararo.”

Yariga da ya fahimci inda ta dosa, yakuma san dalilin fad’anta, rabi da kwata ta rinjaya ga shigewa Niiman da take tunanin ya na yi, amma bata fito kai tsaye a yanzu ta nuna hakan ba, kila sabida ta fahimci yagaji da ji ne, ko kuma ita kanta ta fahimci zaqalqalewarta a kan lamarin,duk kuwa da tabbacin da take tunanin tana da shi akan cewar Mukhtar ba zai taba son Niimah ba, tana matuqar son ganin ta gasgata hakan, kwarai kwarai dagaske, sai dai wani sashe na zuciyarta na gargadin ta da haakan.

“Mammy sau nawa zan fada maku natsuwa da yaron nan yake samu wajen Niiman ne babban dalilin dake sa ina zarya dakin ta,Mammy sai yaushe zaku gane farin cikin Fawad a yanzu shine abu na farko dake gabana,he needs to survive,he have to, mussaman domin ni da kuma mahaifiyar shi, mu ke nan abinda ta mallaka a kafatanin duniyar ta, sai yaushe zaku gane hakan Mammy?”

“Ba zan gane hakan ba har saai ka gaya mani wacece mahaifiyar wannan yaron a yau ba sai gobe ba,Mukhtar har ka kawo qarfin da zaka kalleni ka rika gaya mani maganganu akan yaron da aka sameshi ba ta hanyar aure ba?shin saboda nayi maka rangwame kasantuwar alakar dake tsakaninmu, rangwamen da ban taba tunanin zan iya yin shi ba ga ko waye a cikin gidan nan ba Mukhtar?”

Ta nunfasa, kana cike da bayyanannen bacin rai ta cigaba.

“Banaso,kuma ina adawa da abinda zuciyata ke faman kitsa mani ba tun yau ba, banaso na yarda da hakan,banaso na yarje wa kaina abinda na fara zargi game da wannan yaron da kai, da kuma Niimah, a yanzu ba anjima ba nake son sanin wacece uwar wannan yaron,gazawar hakan na nufin zareka daga cikin ahalina a yanzu ba sai anjima ba.”

Ji yai wani abu na taso mashi daga qasan shi har kwakwalwar shi, baisan zai iya tsintar kanshi cikin tashin hankali irin wannan a wayewar garin na yau ba, ba kuma hakan nada nasaba da maganganun Mammyn tashi bane, No!sai dai hakan nada nasaba ne da girman son da yake wa Ni’imah, yasani, yafi dan dakon tasha sanin wacece Mammy, rabi da kwata na daga halayenshi nata ne, she can be sweet and a lokaci guda she can be tough fiye da tunanin mai tunani, mace ce mai tsayuwa a kan ra’ayin ta.

“Kai nake sauraro, nabaka mintuna uku ka fada man uwar yaron nan, gazawar hakan na nufin debeku daga zuri’ahta, ina nufin kai da shegen d’anka.

Ba don mahaifiyar shi bace, da babu abinda zai hana ya barta kwance, duk kuwa da sanin rashin dacewar hakan, mussaman kasancewar ta mace!bayajin zai yafewa duk mahaluqin da ya qara sheganta mashi d’a.

” Yaa Mukhtar,ka rike man alkkawari,duk wuya duk wuya, duk dadi, duk runtsi, duk musiba, duk tashin hankali,ba zaka taba gayawa duniya nice uwar babyn nan ba.”

Ya rika tuna kalamenta a gadon asibiti, bayan anciro mashi ajiyar shi dake kwance a mahaifarta na tsawon watanni tara!

Al’amuranta masu girma ne a wajen shi, alkawarinta abin qanqamewa ne, koda hakan na nufin lalacewar shi, ko da hakan na nufin salwantar nashi farin cikin ne, ko da hakan na nufin rabuwa da mahaifiyar shi ne, rabuwa ta har abada kuwa, ba zai taba karya alqawarin ta ba!alkwarin ta a gareshi lullube yake da so da kaunarta masu tarin qarfi da girma!kwarai ya zabi dukkan qalubale na duniya, yazabi hakan indai shine farin cikin ta.1

“Hayatiey!!”

Ya furta daga karkashin zuciyar shi.

“Assalamu alaikum.”

Muryar baba mai gadi ta katse Mammy daga niyyarta na baiwa Muktar din umarnin tashi yabar mata gida.

“Yaya akayi Baba Maigadi?”

Ta dubi tsohon cike da kulawa, lokaci guda tana sakaye bacin ranta da murmushi.

“Hajia dama wata baiwar Allah ce a bakin gate ke neman izinin shigowa, shine nace bari inzo in sanar dake.”

“Toh ikon Allah, wacece wannan?nasan dai baquwa ce tunda har take neman iso daga gareni,wa tace maka?”

“Gaskia kam Hajia nafi tunanin bakuwa ce, asalima banajin er k’asar nan ce, domin kuwa tafi kama da jinsin larabawa ko indiyawa.”

Baba maigadi yafada cike da ladabi, kuma bilhaqqi da gaskia.

Cikin dariya Hajiya tace yaje ya shigo da ita, har ya juya sai kuma yadawo da sauri.

“Af Hajiya tace in tabbatar da na sanar dake Sunan ta.”

“Kai nake sauraro toh baba.”

“Tace a ce maki Sunanta Fadwa Hisham,wai itace mahaifiyar jaririn yallab’ai Mukhtar.”5

A tare suka mik’e

“Whatttt?”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *