HOD’IJAM CHAPTER 8 BY NOORIEEYAH

HOD’IJAM CHAPTER 8 BY NOORIEEYAH

                    Www.bankinhausanovels.com.ng 

. Ta aje wayar a lokacin da zuciyar ta ke sake nutsuwa da samun Kabeer din a matsayin wani bigire dake taka muhimmiyar rawa cikin duniyarta,tana son shi,tana mashi son da ba taiwa kanta!ba kuma ta tabajin ko sau daya cewar hakan son kai bane,ah ah!hasalima tana ganin shi din ya cancanci dukkan so da qaunarta,kai harma da dukkan yardar ta da tausayin ta,mussamman tausayin,duba da irin sadaukarwarshi a gare ta,da kuma abin alfaharin ta a dukkan duniyar ta watau Fawwad.+

“A karo na barkatai,zan sake jaddada maki cewar bantaba jin nagaji da jiranki ba,ballantana har sonki ya ragu daga zuciyata,hasalima tazarar dake tsakanin cikar burinmu na taka muhimmiyar rawa wajen sake nutsa zuciyata cikin sonki,zankuma cigaba da lallashin zuciyata wajen jure zafin rashinki da takeyi a tare da ita kulli yaumin har zuwa lokacin da Allah zai amsa adduah ta Ni’imatah.”

Ta sake lumshe idanunta a yayin da take sake jin nauyin qirjin ta na qaruwa,kalamen Kabeer a kullum su ke qara qarfafa mata guiwar shi din nata,itama kuma ta shi ce,mataki kadan suke jira su isa ga matakin da suke buri suke fata,duk kuwa da irin tarin qalubalen da hakan ke da shi garesu,mussaman ma dai a gare ta,ta sani ta sani qwarai Mama ba zata rusuna ba kamar yanda yake a fili cewar ita din macece a tsaye wacce babu alamar ranqwafawa daga gareta,duk kuwa duba da tsawon shekarun da aka diba ana abu daya.

Sau da dama ta kan gaza ganin laifin Maman da ta tsaya kai da fata akan cewa Kabeer din sai dai in ya mutu babu aure,amma ko sama da qasa zata hade ba zai auri bazawara ba,bugu da qari kuma bazawarar da baa san asalinta ba,dukkan wannan qudirin nata ya sake samun gindin zama ne tun bayan rasuwar Alhajin wata takwas da bayyanuwar Niiman gidan shi.kwarai hakan ya sake bata ikon shimfida rashin kirki iri iri duk don ganin ta hana tabbatuwar  yiwuwar a tsakanin su.

Ammy dama bata sanya a ka ba,a wancen lokacin ita kanta har ga Allah dama ba ta ganin yiwuwar faruwar hakan a tun wancan lokacin ba don komi ba sai qudurin da ke ranta na tabbatar da ganin ta jajirce wajen inganta rayuwar Ni’iman da ta danta,tana ganin ilimi shine abu na farko da ta fi buqata ba soyayya ba,mussamman domin rayuwarta ta inganta a duk wani sarqaqiya da rayuwa kan iya jefa ta.

Hakan yasa itama ba tai qasa a guiwa ba wajen shimfida tata dokar tamkar yanda mahaifiyar Kabeer din tayi,sai dai dokokon nasu maabota bambanci ne,ita nata beyi tsauri ba,beyi tsaurin da zai sanya masoyan jin tamkar duniyar batayi da su ba,ko banza suna da hope daga bangarenta,tunda lokaci ta bada,lokacin da suke ganin a kwana a tashi zasu cimmashi,duk da yanga da yake masu na qin tafiya a kan kari,amma a ganin su kenan,mussamn in akai duba da cewar shekaru biyar ba wata biyar bane ba,ko kuma satittika biyar ko kwana biyar,shekaru ake magana,ninkuwar kwanaki zuwa satittika,satittika zuwa watanni,watanni kuma su ta da shekara,har shekaru biyar!!!Kai kamar zaa dauki dogon zango,a ganin su kenan a wancen lokacin.

Domin a yanzun ancinye shekaru biyar din kamar wasa harma ana shirin tasarwa cinye rabin zango na daga cikin shakera ta shidda ba tare da su din sun ankara ba,a tunanin su lokaci da zamani zai iya sauya qaddarar zantukan Maman,sai dai kamar yanda zamani ke shudewa haka qudirin Mama ke sake sabunta kanshi,kamar yanda bata ranqwafa ba akan bakanta,haka shima dan nata yafi mil tsayuwa,domin kuwa yanda tasha alwashin ba zai auri Ni’imah ba muddin tana raye haka shima ya lashi takobin sai dai ya mutu ba aure matuqar bata amince mashi ya auri abar son sa ba Ni’imah.

Sai dai gaba d’ayan su sun manta cewa qaddara da akalar rayukansu duk baa hannun su suke ba.

***

Muryar Fawad ce tai nasarar tada ta daga baccin wahalar da ya danyi nasarar kwasheta,baccin da a duk lokacin da zata zauna tunanin mafitar rayuwar ta yake kasadar dauketa ba tare da ta samu zaren kamawa ba,sai dai kamar ko da yaushe ne zasu cigaba da adduah,adduar da basu fidda ran ranar amsuwarta ba.

STORY CONTINUES BELOW

“Fawad bana hanaka tayar dani in ina bacci bane ba?”

Ta jefi yaron da yarigama ya haue gadon da take yana qoqarin lalubo wayarta dake qarqashin pilllow,haka kuma ba tare da alamun jin fadan Niiman ba ya riqa qoqarin janyo wayar fuskarshi da bayyanannen farin ciki.

“Bani nan,sai bayan Maghreeb zai kira kuyi magana.”

Ta amshe wayar da har ya janyota zaifara dannawa,ba ta damu da yanda ya daquna fuska ba yana shirin yage baki,hasalima idanunta ta sanya cikin nashi tana mai hade girar ta,ba shakka bata son wannan tabarar ta Fawad,abun da bai kai yakawo ba ma ba kuka yake mashi,zata iya rantsewa duk girman gidan nan ita kadai yake shakka kadan,sai ko Mama da ko hanyar apartment din ta baya kalla tun wani zana da tai mashi sakamakom rotsa mata tangamemiyar plasma din falon ta da ya taba yi,cire tausai tayi ta sanya wayar caza ta zaneshi son ranta,ba tare da ta duba qanqantar shekarun shi ba na dan shekaru hudu da doriya a lokacin,a cewar ta tunda har yaro dan shekaru kusan biyar zai yi babbar barna irin wannan,toh kuwa bata ga dalilin da zaisa ta taqi hukun ta shi ba,hukuncin da yai nasarar bata ran Kabeer fiye da kowa,domin kuwa ma iya cewa shine yazama tamkar mahaifi ga Fawad din,domin har gobe Fawad din bai san kowa a matsayin mahaifi ba face shi din,alamarin dake qara assasa wutar tsanar Niiman a zuciyar Maaman.

“Ann ni ki kila man Daddy na.”

Muryarshi mai kama da ta masu son yin kuka ta doki kunnuwanta a lokacin d atake sanya hular kanta da ta zama garin bacci,hararar shi tayi kana ta zuro qafafunta qasa da shirin tashi ta shiga wanka,ta ga six na neman yi,gashi yau night shift zata fara,da yake wata uku kenan da fara bautar qasarta a a nan asibitin FMC dake katsina,tun bayan nasarar   karbar takardar shaidar kammala digiri a Nursing da tayi a watannin baya kadan.

Kwarai karatun yataka muhimmiyar rawa wajen sauqaqa lamuranta na cikin gida,sai dai ta dayan bangaren kwarai ba tafiya bace mai sauqi ta aiwatar ba,domin kuwa sosai batayi wasa ba wajen ganin ta jajirce ta yi karatu bilhaqqi da gaskia don ganin ba ta baiwa Ammyn kunya ba,sosai tayi karatun cikin tarin nutsuwa da kuma wasu qalubale na yau da kullum da soyayyar Kabeer din ta ja mata,soyayyar da ke shayar da ita dadi hade da zafi,wanda tai nasarar jure su da taimakon Allah da kuma shi kanshi uban gayyar,ta wani bangare kuma Ammy da duk abinda ya shafeta,ba shakka bazata iya cewa ga daidai da rana daya da tai maraicin uwa ko uba ba,domin Ammyn ta riqe alqawarin ta gamgam wajen ganin ta zame mata uwa harma da uban da ta rasa,haka zalika ta zama wa danta kakannin d aya rasa,ta yalwata su da tarin farin ciki da tarin alkairai marasa iyaka,ba shakka bazata taba biyan ta ba,sai dai kama ynda take fada ne kullum babu abinda baza ta iya yi wa Ammyn ba a duk duniyar nan,sai dai in yafi qarfin ta ne.

“Ann please,ki kira mani Daddy,yace innadawo daga tahfeez zamui waya.”

Wannan karon tsaki tayi tana jinjina wannan naci na Fawad,zata iya rantsewa yau ko wayar kirki basui da Kabeer din ba duk don Fawad din da yai magajiya da wayar wai shi nan hirar school yake ma Daddyn nashi,bayan tafiyarshi islamiyyan kuma sunfara magana kenan wani abu yataso daga bangarenshi d ayasa dole suka haqura da wayar.

“Toh bari ingama wanka inzo inkira maka shi kaji Fawady na?kaga yanzu Maghreeb yayi,yanzu Daddy yaje massallaci yana sallah,kaima maza kaje toilet din Ammy kayi alwala kuyi sallah da Ammyn,idan kun idar da sallan kaga nima by then nagama shiryawa sai onkira maka shi ku dora a inda kuka tsaya ko?”

Ta qarasa maganar tana dan shafa kumatun shi masu sulbi da kyau,sau da dama infana kallonshi sai yariqa rikide mata zuwa fuskar mutumin da bata fata ko da a lahira ne Allah yahadata da shi,sai dai tasani ba shakka Allahn yariga da ya hadata dashi,mussamman da ya qadararta tsananin kamar Mukhtar din da Fawad din,kama ce da a zahiri take,duk da qanqantar shi a yanzu,hatta tafiyar shi irin ta Mukhtar din ce,baa maganar yanayin da fuskar shi takeyi in yayi shiru,tattarewar fatar gaban goshin shi tamakr dai Mukhtar din yayi kaki ya aje.

STORY CONTINUES BELOW

Daalama yaji lallashin,domin da gudu ya sauka daga gadon yai hanyar fita daga dakin,dama da biyu tace yaje yai alwala,don tasan dunia ba bu abinda yafi dauke mashi hankali irin yaganshi dauke da buta yana alwala tamkar yanda yaga anayi,mussaman ba don komi ba sai don yai wasa da ruwa.Bin shi da kallo tayi tana sake jin son shi na sake bullawo kullum cikin ranta,harma ta kan ji sassucin jin haushin Mukhtar din a lokuta irin haka,ko banza ya daukaka darajarta zuwa uwa,uwar da ke alfahari da dan da ta ke ma kallon da ne kamar kowa,in aka cire alaqar jini kuwa,da ne da take yi ma kallon  wani jinsi da aka samar  daidai da yanda aka samar da ita,a duk lokacin da wannan tunanin ya riske ta,zuciyarta kan dunqule a qirjinta,tai mata wani irin nauyin,nauyin da take da tabbacin da shi zata koma ga mahalliccin ta!

Ba shakka wasu qaddarorin basa canzuwa,a mafi lokuta da yawa sukan riga fata ne.

***

Da misalin qarfe bakwai da minti arba’in da bakwai ta kammala shirin ta na tafiya asibitin,a lokacin da take qoaqrin daukar jakar da zata fita da ita ne wayarta ta dauki qara,murmushin da kan subuce mata ne a duk lokacin da ta ji kalar sautin kiran shine ya subuce yanzun ma,tana girmama bawan Allahn nan,tana daraja shi,a lokaci guda kuma ta kan tausaya mashi fiye da kanta,ba shakka shi din abun tausayi ne.

“My Baby Mamaa”

Ta sake yin murmushi bayan jin sautin muryarshi daga cikin wayar,tun shekarun baya ya liqa mata sunan,har abada kuma tana da tabbacin sunan ya bita kenan,mussaman a lokutan da yake cikin nishadi,itama narkar da murya ta yi cikin salon muryar da take da yaqinin sake samawa sonta gurbin zama cikin zuciyar shi tace,

“Daddy for how long?you kept us waiting,tun bayan laasar fa nake jiran wayan ka,har nai bacci natashi,infact Fawad ma bai dade dagama rigiman sai na kiraka mashi kai ba,amma dai na lallabashi yaje yai sallah tukunna.”

Tana jiyo yanda ya nutsu yake saurarenta,duk da a waya ne kuwa,ta sanshi,ta sanshi kamar yunwar cikinta,yana bata mahimmancin da yakan iya baiwa duk wani abu mai daraja da girma da ya shafeshi,a yanzunma ta kan hasko yanda zai nutsu ya amshi korafinta,ya kuma tabbatar da ya miqo mata uzurin da ya sa har hakan ya faru,ta kuma amshe su ta rungumesu da dukkan yardar ta,domin haqiqah qarya bata daya daga cikin abinda suka gina soyayyar su da ita,shi din mai gaskia,akai saa itama dinma qarya ko son burgewa basa daya daga cikin ababen da ta iya,she is very blunt and straightforward person mussaman yanzu da girma ya sake cinmata akan lokutan baya,she is 22,shekarun sun tafi ne da qara inganta kyawun d’abi’unta,tana da hakuri da kawaici,amma ta kanji Kabeer na cewa kafiyarta har tsoro ta ke bashi,amma ai shi dinma kafiyar gareshi,zamu iya cewa ta wani fannin ma ya doketa,domin dai ita ko banza mace ce,tana da tarin rauni a lokuta da yawa.

“Afuwan Ni’imatah,i met an old friend,it’s been long da na hadu dashi,toh kinga akwai yiwuwar doguwar gaisuwa a tsakaninmu,and afterwards nabari nai sallar maghreeb ne,because i know kema kina shirin tafiya asibiti,reason why nabari sai yanzun na kira,ayi wa bawan Allah hakuri ba don halin shi ba.”

Tana dariya a hankali take bashi amsar ya qaddara an dade da yi mashi hakuri dama,qorafin dama dai anayi mashi ne domin a saurari ban hakurin shi,ta dayan bangaren ta jiyo shi yana mitan missing din su da yake,gaskia zai gudo yabaro masu seminar su,abu kusan sati biyu yaqi ci yaqi cinyewa!

“Daddy saura fa kwana uku,ka jure wadancan kwanakin wadannan ne ba zaka jure ba?don Allah ni dai kayi hakuri ka qarasa.”

Ta ida cikin sigar lallashi,shi dinma cikin bayanannen gajiwa yace mata,

“Allah i am badly missing you,mussaman yaro na,amma dai not bad tunda zanqara samo kudin da zan riqeku da kyau har iya lokacin da Allah ya ara mani a ban qasa,so it’s a win after all.”

STORY CONTINUES BELOW

Ta zumburo baki gaba kamar yanda takeyi a duk lokacin da zai kwatanta zance makamanciyar wannan,take kuma ta jefa mashi amsar da ta kan bashi a irin lokacin tana mai hararar wayar tamkar yana gabanta.

“Zaka fara ko?kai kullum baa magana daya biyu uku da kai sai ka soko zancen da mutum baya so,Allah zan hadaka da Ammy inkana man haka.”

Dariya yayi a hankali kamar yanda yasaba,yariga yasan yanda taqi jinin yai zancen mutuwa ko da kuwa bata shafe shi kanshi ba,ita dai kawai bata so yake kawo maganar mutuwa,a cewar ta in sha Allahu ba yanzu zasu mutu ba,sai sun yi aure sun tara zuriar da za sui alfahari da ita,sannan bayan sun tsufa sai su mutu,mutuwar ma kuma tana fatan ta daukesu a tare,da fatan cewa in sunje lahira su daura daga inda suka tsaya a aljanna in Allah yaso.

Sai dai sau da dama ba yanda mu ke so muke samu ba,wasu qaddarorin sun riga fata.

***

Ranar da zai baro Abujan yayi daidai da day off dinta,hakan yabata damar zagewa wajen shirya mashi kala kalan abincin da yafi so,tafi kowa sanin gwanin nata masoyin abinci ne,qwarai inkana so kaga bacin ranshi to iskeshi a lokacin da yake jin yunwa,ba shakka karma ka kusanto shi da duk wani abu da ka iya tunzura shi,yanzun nan zai huce haushin shi akan ka,duk kuwa da kasancewar shi cikin mutane masu sauqin hali da barkwanci a mafi yawa na lokutan rayuwar shi.

Shigowar Ammy dakinta ya dakatar da ita daga daure tumulin gashinta da yasha gyara da ribbon,ta maido dukkan hankalinta kan Ammyn mussamman ganin yanda Ammyn ta nemi guri ta zauna a bakin gadon ta.

“Ya iso ne?”

Ta jefawa ma ta tambayar duk da tana da tabbacin cewa Kabeer ba zai iso gidan nan ba tare da ya fara isowa part din su ba,duk kuwa da sanin abinda hakan ke janyo mashi a bangaren mahaifiyar shi.

“No Ammy bai riga ya qaraso ba,yace mani zaifara branching a bank din su kafin ya qaraso,i think akwai abinda zeyi.”

“Toh shikenan,dama so nake ince maki idan ya isa kungaisa banason doguwar hira,ya wuce yaje yagana da mahaifiyar shi inyaso daga baya yazo yaci abincin,tun safe nake lura da take taken Mamar,banajin yau din tana neman zaman lfya,kin fahimceni ko?”

Jikinta a dan sanyaye ta ce “Na fahimta Ammy,in sha Allah zaki sameni mai kiyayewa.”

“Yawwa toh Allah yai maku albarka,yakawo mafita cikin lamarin.”

Da murmushi a saman kumatun ta tace “Amin Ammynmu”

“Idan Yusrah ta tashi daga shegen baccin na nata,kice nace ta tabbatar taje ta amso mani saqona gidan Hajia Altine,ni ba don dawowar Kabeer ba ai ke zakije man ma aiken nan Ni’imah,aiken Yusra ko shiririta.”

Tai tsaki yayin da take idasa ficewa daga dakin,ita kuma Ni’imahn tana mai binta da kalmar ban haquri a madadin Yusran tana dariya,inda sabo yaci ace ansaba da shegiyar shiririta da son jiki irin na Yusran,haka kuma yana qara samo asali ne da sangarta da take qara samu daga bangaren Daada,ga kuma Chicago daga gefe,da a kullum yake mitan a qyaleta yarinta ce zata dena,sangamemiyar budurwar da take neman shiga shekaru ashirin da uku ita ake kirawa yarinta,al’amarin da kansa Ammyn yin tsaki cike da takaicin halin na Yusrah,ga shi babu damar ka tanka yanzun nan tsohuwar nan sai ta nemi tada hankulan duk mutan gidan.

***

Tun daga dakin ta take jiyo surutun Fawad din ya cika falon,baka jin komi sai tashin muryarshi mai dankaren zaqi,ya dage iyakar iyawarshi yana baiwa Daddyn nashi labarin abubuwan da akai masu a school da baya nan,shikuma Kabeer din ya tattara hankalin shi gaba daya yana biye mashi ta hanyar jefo mashi tambayoyin da suka shafi abinda Fawad din ke fada.

Babu kowa a falon bayan Yusrah can kan dining area tana tsakurar abinci,rabin hankalinta kuma yana kan hirar Fawad din da Kabeer tana tiqar dariya,ta wani fannin kuma tana gwasale Fawad din duk don ganin ta saka shi kuka,dama dai duk gidan daga shi sai ita a tabara,shiyasa suke gabzawa kusan ko da yaushe.

Qamshinta mai matuqar sauqin ji ya sinsino,hakan ya tabbatr mashi da isowarta cikin falon,a hankali yadago kanshi fuskar shi dauke da bayyanannen annuri yana jifanta da idanuwanshi masu sanyata ta sake narkewa cikin son shi,meyasa yake da matuqar kyau ne duk da kasancewarshi cikin jinsin mutane masu duhuwar kalla?kyakkyawan Sajen shi da yake kwance saman fuskar shi yaqara taimakawa wajen sake fidda kyawu da tsarin fuskar shi,ta kan rasa nutsuwar ta a duk lokacin da idanuwansu sukai nasarar haduwa,akwai wani sanyi sanyi da kan ziyarce ta a duk wata kalma daka iya fita daga labbanshi,komi nashi me kyau ne,tun daga tsarin halittar shi har qalqashin zuciyar shi. Ba shakka tana son shi,tana son shi fiye da tunanin mai tunani.

“Hello Beautiful.”

Ya jefeta da kalmar lokacin da ta ke samun matsuguni kusa da shi,yayin da Fawad yake a tsakiyar su,har a lokacin bai janye ganin shi daga kanta ba,duk da ba wata shahararriyar kwalliya ta yi wa fuskar ta ba,amma tai mashi kyau,tai mashi kyawun da kullum yakan rasa da yaushe da yaushe ne tafi kyau?Daga randa yafara dora idanuwanshi a kanta,a duk rana ta Allah qara mashi kyau take,kyawunta mai sanyi ne,lokuta da dama yakan nemi nutsuwar shi ya rasa in idanuwansu suka gamu,shiasa bai fiye bari suna making eye contact sosai ba,qwarai da gaske jikin shi na gaya mashi ba kadan ba,daalama yau dinma jikin shi zai gaya mashin.

“Anya mahaifiyar shi na qaunarshi kuwa?domin ita kadai tazama katanga daga samuwar farin cikin shi,har yanzu kuma yarasa sai yaushe ne zata sakko daga dokin naqin ta ta agaza wa rayuwar shi ko zai samu salama,ai yanajin shima mutum ne kamar kowa ko?kuma yana da ‘yancin samun nutsuwa tamkar ko wani dan adam!”

“Daddy ya hanya?kaga yanda kayi qiba?me suke baka a Abujan nan ne har haka?”

Muryarta mai sake dulmiyar da shi cikin qara sonta ta katse shi daga tunanin wucin gadin da ya tafi da shi,har yanzu bai dena kallon ta ba,wannan karon baya yayi ya jingina da hannun  kujerar wacce ta kasance 3 sitter yana murmushin nan nashi dake qara mashi kyau,yayin da yake sake kwantar da Fawad bisa qirjin shi.

Kunya ce ta dan kamata,duk da dai dama can din tun bai isoba ya soka mata wata sabuwar kunyarshi a ranta sakamakon abinda yafada mata a waya lokacin yana gaf da isowa.

“Ki tabbatar kin bani kyakkyawan hug yau inna iso,wata qila ya taimaka wajen sassauto abinda nakeji game dake,dagaske nake hakuri na yaqare,yau dinnan ba sai gobe ba zan kawo qarshen lamarin nan,i can’t take it anymore.”

Kamar yasan me take tunani,murya qasa qasa yace mata,

“You look breathtaking,i can’t breathe!”

Dariya ta riqa yi qasa qasa tana cuno dan qaramin bakin ta,lokaci guda tana mai sanye tafin hannunta ta na rufe fuskanta tana dariya,kana ta riqa qunqunin kai Daddy.kamar daga sama suka jiyo muryar fawad yana cewa,

“Ann kema kizo ki hau nan saman cikin Daddy na,bari in matsa maki.”

Ya idasa maganar yana bubbuga qirjin Kabeer din alamun nan yake nufi,lokaci guda kuma yai sama wajen wuyan Kabeer din da zummar matsawa Ann din tashi guri itama ta hau,kunya da haushin Fawad din ne suka taru sukai mata rubdugu,hakan yasa ta dan dago qasa qasa tana dalla wa Fawad din harara,sai dai kalamen da suka fito daga bakin Kabeer din ne sukai nasarar sa ta ta fashe da kukan shagwaba.

“Oyaa come over here,ga kayakkyawan masauki yarona ya samar maki,banson gulma nasan dama tuntuni abinda kike jira kenan.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *