HUTU CHAPTER 11HUT

HUTU





CHAPTER 11







Yau sati daya kenan da yin bikin Zeena da Khalil, soyayya sabowa suka shimfidawa rayuwar aurensu, Jamil da MK sun koma school banda Anwar da har yanzu bayajin dadin jikinshi, Khalil yazo ya dubashi ya mishi allurai da bashi magunguna, en biki duk sun watse saboda haka ya bar bq ya koma main house inda yake samun kulawa sosai daga wurin Mom harma da Dad. Binta kuwa tana nan kullum zuciyarta na azalzallarta akan ta kira Anwar amma kuma wata zuciyar na hanata wanda ga dukkan alamu tafi abin zuciyar da ke hanata kiran Anwar dukda ba karamin azabtuwa takeyi da kin kiran nashi da batayi ba. Kausar ta gane da abinda ke damun Binta ta tambayeta amma Binta tace ba komai kawai tana miss din Zeena ne dukda kowa a kullum se sunyi video call, yanzu sosai Kausar ke kokari wurin ganin tana girki wanda Miemie ta sata a grps biyu duka na girki ne kuma tana zuwa tana kowa mata wanda baza’a rasa ba sannan ita kanta Kausar din tana duba internet tayi wasu girke girken, Miemie da Ya Ahmad wan Kausar soyayya sosai suke a tsakaninsu wanda a halin yanzu ma an sa rana nan da wata biyar, Salma da saurayinta engineer Hafiz ma an sa musu rana Seema ce dai har yanzu shiru.


Kwance take kan gado, yau ita kadai ce a gida dan Kausar da Hydar sun fita, rike take da wayanta tana tunanin ta kira ko karta kira, harga Allah tanaso ta kirashi taji muryarshi ko hankalinta ze kwanta, contacts dinta ta shiga ga MY SOULMATE 💕💘💋 nan baro baro amma ta kasa dail dinshi, “ahhhh”, wani ihun takaici tayi tareda wurgi da wayar ta rufe fuskarta cikin pillow tana takaicin wannan hali data tsinci kanta a ciki, ganin idan bata kira ba kanta zata cuta se kawai ta mike zaune ta dau wayan tayi dail din number dinshi gabanta na mugun bugawa, har wayan ya karaci ringing dinshi ba’a dauka ba haushi yasa taki sake kira amma ganin bazata iya hakura ba seta sake kira wanda luckily ya dauka tareda cewa “hello”, lumshe ido tayi tareda dafe kirjinta saboda bugawar da yakeyi sannan tace “Assalamu alaikum”, shiru taji ba’a amsa mata sallama ba not knowing shima yana chan dafe da kirji kaman yadda ta dafe, kara sallama tayi Anwar da lumshe ido ya bude tareda gyara zaman sannan yace “amin wa alaiki salam”, “Ya Anwar”, ta kirashi a hankali yayi murmushi dan he was dying to hear her call his name again se gashi ta kira dat too perfectly, gabadaya se yaji ba wanda ya iya kiran sunanshi kaman ita dan kuwa sunan yafi dadi a bakinta.


“Binta kin wahalar da zuciyata, se yau kikaga daman kira”, samun kanta tayi da murguda baki kaman yana gabanta a ranta tace “ai ba kai kadai ka wahala ba malam”, a fili kuwa cewa tayi”ban gane ba, me kake nufi”, jingina yayi jikin kujeran da yake zaune kai yace “ki bani dama in ganki dan in fahimtar dake”, shiru tayi na dan wani lokaci kafin daga baya tace “gidan da nake akwai security sosai baza’a bari ka shigo ba haka zalika nima baza’a bari na fita ba”, sosai yasha mamaki wai har Binta tayi wayewar sanin security, lallai kuwa in yayi wasa yanaji yana gani zata mishi nisa, “a wani gida kike”, ba tareda wani tunani ba tace “gidan Ya Hydar”, “Hydar” ya maimaita a ranshi “Hydar soja?”, ya tambayeta tace “eh shi”, take yaji wani mugun kishi ya kamashi wanda ya rasa dalilin wannan kishin da idan Hydar da Binta sukazo wuri daya yakeji, cike da command yace “meke tsakaninku?”, tasha mamaki jin yadda yayi maganan amma seta share tace “cousin brother dina ne, I was able to find my family”, wani ajiyar zuciya ya sauke wanda ita da kanta tajishi sannan yace “na tayaki murnan ganin family dinki, yanzu ya zamuyi mu hadu”, shiru tayi na dan wani lokaci sannan tace “bani five minutes will call u back”, bata jira response dinshi ba ta kashe wayan, ta barshi da dunbin mamakinta, wai itace take turanci, dat too fluently.



Binta tana kashe wayan ta shiga duba MY SPECIAL 😘 a contact dinta ta kira, ringing biyu Kausar ta dauka tace “Hello Binta”, “na’am anty”, ta amsa Kausar tace “ya akayi”, shiru tayi dan bata saba yiwa Kausar karya ba, amma a yau dai idan dai zataga Anwar toh a shirye take da ta shirgawa Antynta karya saboda haka se tace “Anty yanzu Afeefah (frnd dinta ta school idan baku manta ba), ta kirani wai yau birthday din brother dinta, dan Allah Anty inaso inje”, shiru Kausar tayi na dan wani lokaci dan bata taba barin Binta ta fita ita kadai ba amma tinda Binta nason zuwa bazata hanata ba saboda haka tace “shirya bari na David magana ya kaiki”, da murna Binta tace “nagode anty”, sannan ta kashe wayan, Anwar ta sake kira wanda ke zaune yana jiran kiranta ya dauka tareda cewa “zaki samu fitowa”, tace “mu hadu a asokoro nan da 30mins”, da murna yace “toh”, sannan ya tashi ya fita dan yaje ya canza kaya saboda kar yaje mata bayan kayanshi ya kwashi warin bar din. Itama tana kashe wayan ta fada bathroom da murna ta fara wanka, wanke jikinta takeyi kaman zata canza fatar jikinta, tana fitowa ta shafa mai tasa wani gown peach color, batayi wani kwaliya ba banda powder da lipstick se brushing din gashinta da tayi tasa white veil da white heel dan yanzu ta kware a tafiya da heels, wanka tayi da perfs ta dau purse dinta white ta fito, koda ya fito David na jiranta da wani mota fara kirar 4matic, saboda kar a samu matsala ta kalleshi tace “oga david”, yace “yes madam”, tace “to tell u the truth I’m not attending any birthday party but I’m going out to meet a friend”, da mamaki yake kallon ta tace “yes, my aunt won’t allow me if I told her I’m to meet a frnd dats y I lied, I hope you will not reveal dis little secret of mine”, da sauri ya kad’a mata kai tareda bude mata mota ta shige baya ya shiga gaba yaja yana tsoron kar maigidanshi Hydar ya gano wannan lamarin da Binta ta janyoshi ciki karfi da yaji.

(A/N:- idan zaku lura a last page nayi amfani da Mahmoud instead of Mubarak, well na canza sunan ne saboda Mubarak sunan boyfriend din kawata ne and tace in canza saboda batason tana karantawa tana jin sunan saurayinta as a bad guy,😂 kumin afuwa🙏).


A daidai gaban gidansu Afeefah dake asokoro Binta ta bari yayi parking, tin daga nisa ta hango Anwar tsaye jikin motarshi yana baza idanu yaga ta ina zata bullo, da murmushi ta fito daga motan sannan taje ta wurin drivers seat ta kalli David tace “wait for me oga David, this won’t take long”, kai ya kada mata yana mamakin wannan sabon salon na Binta. Tsallakawa tayi ta sameshi se kallonta yakeyi yana tuna months ago fah shi yake kula da wannan yarinyar dake gabanshi he’s the only one she depends on amma cikin ikon Allah gashi yanzu a karkashin ikon wani take. Hannu tasa tana yawo dashi gaban idonshi ganin se magana takeyi amma ya tsaya yana kallonta, murmushi yayi yasa hannu yana sosa dan guntun sumanshi sannan yace “I missed you”, murmushi tayi ta sunkuyar da kai kasa ya sake cewa “I can’t believe this”, dagowa tayi tana kallonshi tace ” can’t believe what?”, be amsa ta ba yace “baby girl I feel like hugging you right now but I don’t have that right”, murmushi tayi a zuciyarta tace “he looks dashing”, “kalli ni baby girl and tell me do you miss me”, dagowa tayi tace “yes I missed you”, murmushi yayi tareda sauke ajiyar zuciya yace “toh meyasa baki kirani ba?”, “I promised my aunt I won’t call u”, ta fada mishi sincerely ya kada kai tareda cewa “so u broke the promise?”, tace “I have no choice”, shikam mamaki yakeyi ya akayi in a short period of time Binta ta goge tayi blend haka, ga iya dressing, ga fluent English, ga uwa uba kyau da hankali da nutsuwa data kara.

Kallonta yayi yace “if you don’t mind, bani lbr yanda akayi kika hadu da family dinki”, take yaga annurin fuskarta ta canza sakamakon tunowa da Mahmoud da tayi, cikin taushin murya yace “karki damu if that will remind you of your bitter memories”, girgiza kai tayi tace “don’t worry zan fada maka, sannan ta fara bashi lbrn abinda ya faru tsakaninta da Mahmoud a ranan da suka dawo daga hospital bayan ya koma gida tareda fada mishi yadda akayi ta hadu da Kausar har ta dauke ta tasata makaranta da kuma yadda akayi aka gane cewar Hydar cousin dinta ne which means they are related by blood ta fannin Abba mahaifin Hydar da kuma Ummi mahaifiyarta sannan ta bashi lbrn kamasu Zinaru da akayi wanda a halin yanzu ma they are under police custody, numfasawa yayi bayan ta gama bashi lbrn amma har yanzu be sani ba koh Mahmoud yaci nasara koh beci ba saboda taki fitowa karara ta fada mishi abinda ya faru saboda kunya wanda kin fada mishin da batayi ba yasa ta tabbatar da maganan Mahmoud, sosai zuciyarshi ke soyuwa amma ya dake ya kalleta yace “I’m happy for you baby girl, finally kinga family dinki amma I want to tell you something”, kallonshi tayi tana jira taji me zaice, kallonta yakeyi ido cikin ido yana tsoron fada mata abinda ke ranshi dan be sani ba koh zata yarda koh bazata yarda ba, murya na cracking alaman nervousness yace “baby girl basan ta inda zan fara fada miki abinda ke zuciyata ba, ina tsoron amsan da zan samu daga wurinki”, ita dai kallonshi kawai takeyi, yana sosa keya yace “baby girl idan na fada miki seda nayi jinyar zuciyata saboda sonki da rashinki zaki yarda”, gwalo ido tayi waje dan duk a tunaninta jinyar gaske yake nufi nan kuwa batasan yana nufin ya azabtu da rashinta bane, murmushi yayi ganin yadda ta gwalo ido yace “ina nufin sonki ya wahalar dani sosai fiye da tunanin me tunani”, murmushi tayi ta sunkuyar da kai yace “I hope u also feel the same love that I felt for you”, kada mishi kai tayi yayi murmushi tareda riko hannunta yace “baby girl gobe zan koma India, shekara daya da six months ya ragemin na kammala karatuna, promise me u will wait for me”, dagowa tayi ta kalleshi sannan a hankali murya na cracking saboda yace mata gobe ze koma tace “I promise I will wait for you till eternity”, murmushi yayi yayi pecking din goshinta tareda cewa “thanks baby girl, I love you so very much”, kanta a kasa tace I love you too”.

Sosai yamma tayi dan har an fara kiran magrib yace “kije gida kar a ga kin dade, ki bar wayanki a kunne zan kirani komin dare”, kai ta kada mishi tareda cewa “bye”, sannan ta juya zuwa inda sukayi parking David har ya gaji da jira ta shiga ta zauna tana dagawa Anwar hannu shima yana daga mata, yana ganin wucewar motarsu shima ya shiga tashi motar ya tadata cike murnan sake samun Binta a karo na biyu wanda yama kanshi alkawarin wannan karon baze bari ta kubce mishi ba. Koda ta koma gida Kausar da Hydar basu dawo ba saboda haka ta rage kayan jikinta tayi alwallah tayi magrib sannan ta shiga kitchen dan nemawa kanta abinda zataci, tana cikin juye indomie a plate taji sallaman Kausar ta sauri ta karasa abinda zatayi ta fito taga Kausar zaune tana shafa cikinta da yake nunawa sosai yanzu, karasawa tayi ta zauna kusa da Kausar tace “anty sanda zuwa”, Kausar tace “yauwa kedai Binta ya birthday din”, “it was boring”, Binta ta fada tana turo baki gaba kaman da gaske Kausar tayi dariya tace “don’t worry, naga kaman kinason party sosai, gobe zan bari Uncle dinki ya kaiki dinner party dinda friends din Khaleel suka hada mishi”, da murna Binta tace “da gaske”, Kausar tace “da gaske nake”, haka sukata hira har aka kira isha Binta tama manta ta dafa wani abu waishi indomie.

Story continues below

Washegari

Hydar ne kwance Kausar na kwance jikinshi tace “my hubby”, yace “humm”, tace “pls idan zaka dinner din Khaleel kaje da Binta”, kallonta yayi yace “ke kuma fah?”, ta girgiza kai tace “I don’t think I can make it, banjin dadi sosai nafison na kwanta a gida na huta”, kallonta yayi sosai sannan yace “amma kuma ai ba yara kamanta wurin, duka abokanshi da matansu zasuje”, dagowa tayi daga jikinshi tace “shiyasa nace kaje da Binta seta wakilceni kaji, pls”, shiru yayi na dan wani lokaci sannan yace “shikenan, amma make her look decent, banason idon mutane a kanta”, murmushi tayi tace “don’t be over protective, the girl won’t like it, zaka takura mata”, murmushi yayi yana shafa suman kanta yace “ya na iya, she’s my little sister”, da haka sukaci gaba da hira har dai daga karshe suka tashi dan suyi wanka. Da yamma bayan sunyi magrib Kausar tasa Binta yin wanka sannan ta zauna da kanta ta tsantsara mata kwaliyya na gani na fada, gown tasa black me kyau tareda rolling kanta da nude veil.

Hydar dai yana zaune parlour cikin shirinshi na bakin suit da white inner yana jiran fitowansu, yanajin karan murda kofa ya kalli direction dinsu baki sake ya tsaya yana kallon Binta, ya manta kaman basu kadai bane a wurin harseda conscience dinsh…
Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.
Hydar dai yana zaune parlour cikin shirinshi na bakin suit da white inner yana jiran fitowansu, yanajin karan murda kofa ya kalli direction dinsu baki sake ya tsaya yana kallon Binta, ya manta kaman basu kadai bane a wurin harseda conscience dinshi yace mishi “dude control urself your wife is here”, sannan yayi gyaran murya ya mike da murmushi kwance a fuskarshi yace “u look beautiful”, “thanks”, tace kanta kasa Kausar tace “toh se kuzo ku tafi kar lokaci ya kure muku, seda ya gyara zaman suit dinshi sannan yayi gaba suka bishi a baya, zama Binta tayi gaban mota Hydar kuwa seda yayi pecking din matarshi sannan ya shiga ya tada motan saboda bada masu tsaronsa zashi ba, seda taga fitarsu sannan ta koma cikin gida hankalinta kwance (ni kuwa nace Kausar hala bakisan mijinki ya fada soyyayar Binta bane kike kara bashi dama).


Shiru sukayi a mota bame cewa kala har suka kai wani rantsatssen hall wanda aka hadawa Khaleel da Zeena dinner a ciki, suna fitowa ya riko hannunta wanda seda ta dago ta kalleshi ya mata murmushi tareda basarwa suka shiga hall din, kowa ido ya dawo kansu masu gulma har an fara dan Hydar ba boyayyen mutum bane haka zalika matarshi, amma Binta babu wanda ya santa, harda masu kiran Kausar suna kai mata rahoton ga mijinta nan da wata, Zeena sosai taji dadin ganin Binta a wurin da murnar ta ta rungumeta sannan suka samu wuri suka zauna anata gudanar da taro amma yawancin mutanen wurin idonsu na kan Binta musamman ma mazan, ita kowa ko a jikinta dan she’s enjoying the moment alot. Se wuraren 2am suka bar wurin, a kasalance suka koma gida Binta dakinta ta fada tareda kwanciya saboda wani irin bacci da takeji.

5month later

Hydar ya dade da komawa bakin aikinshi yayinda cikin Kausar ya kara girma sosai haihuwa yau koh gobe at the same time kuma son Binta na kara ruruwa a kokon zuciyarshi a yayinda Binta da Anwar kuma soyayya ce mai karfi a tsakaninsu a koda yaushe cikin waya suke koh chatting amma dukda haka wannan be hanata karatu ba, Kausar ta lura da ita amma ta share dan ta yarda da tarbiyyan Binta kuma tasan watarana Binta zata fada mata, anyi bakin wan Kausar Ahmad da kawarta Miemie haka zalika ma anyi bikin Salma da saurayinta engineer Hafiz yayinda Seema kuma tayi kamu a cikin abokan Salma wani kyakyawan saurayi me suna Salahuddeen wanda har manya ma sun shiga maganan, Zeena da Khaleel soyayya se abinda ya karu dan a halin yanzu ma tana dauke da cikin wata uku wanda koh kadan baya bata wahala sabanin sanda cikin Kausar ke sabo, Zeena ta samu admission a Base university tana karatunta na civil law cikin kwanciyar hankali. Yau Kausar tin cikin dare takejin ciwon baya da ciwon mara se safa da marwa takeyi a daki saboda batason ta tashi Binta dan tun tafiyan Hydar Binta ta dawo kwana tareda Kausar saboda cikin jikinta, ganin ciwon be mai dainawa bane seta sauka kasa zuwa kitchen ta dora ruwan tea din breakfast tareda fare dankali dukda azaban da takeji (ni kuwa nace kodai zafin ciwon ne), a haka ta gama hada breakfast batamasan ta gama ba, kwanciya tayi a parlor tana duk addu’an da yazo mata, kiran sallahn farko a kunnenta ya fada ta tashi ta haura sama tayi alwallah tayi raka’atainul fajr sannan ta zauna har aka fara sallah tabi liman, kaman kar ace tayi sallah ciwon ya tsananta sosai bayan ta idar, haka ta daure ta tashi Binta bayan Binta ta idar da sallah tace “anty lfy”, girgiza kai tayi tace “Binta dauko kit din baby, asibiti zamu”, a wahalce take magana ai da sauri Binta ta dauko kit da taimakon ta suka sauko kasa David na ganinsu ya taso ya bude musu motar suka shiga ya fita se asibiti, kafin sukai ciwon ya mugun tsananta, haka aka karbeta da sauri Binta duk ta gama rudewa, Ummi ta kira ta fada mata yayinda Ummi ta fadawa kowa harda Hydar da Zeena, sosai hankalin Hydar ya tashi gashi baya gari yana Lagos, kafin gari ya gama wayewa an gama cika a asibintin amma har yanzu Kausar shiru ba lbr.

Sunfi awa uku suna zaune gaban labor room, daga masu safa da marwa se masu tagumi, se masu addu’oi, haka zalika masu kuka nayi irin Binta da hankalinta ya gama tashi ya gama fita daga jikinta, she can’t imagine losing her anty Kausar, matar da ta dauke ta ta jawota jiki dukda batasan ko ita wacece ba amma ta rike ta tsakani da Allah kaman ciki daya suka fito. Hydar roko yake a bashi leave koda na sati dukda ya fada masu halinda matarshi ke ciki amma sunce ya bari ya gama aikinshi na ranan sobada akwai cases dayawa da akace yayi reporting amma be samu yayi ba shikuma a yanzu bashi da nutsuwar da ze iya yin wannan aikin, El Ameen ne ya taimaka mishi suka samu suka gama yayi signing papers din sannan yaje yayi submitting wanda a lokacin karfe hudu da rabi na yamma amma kuma har yanzu babu wanda ya kirashi ya shaida mishi koh ta haihu kuma koh ya kira amsa daya ake bashi “har yanzu bata sauka ba”, sosai wannan kalaman ke hargitsa kwanyan kanshi, shi tunani ma yakeyi kodai wani abu ya sameta ko kuma ya samu babyn amma aka ki fada mishi, cikin sa’a da yaje airport ya samu jirgin da zeje Abuja straight wanda ba bata lokaci ya yanki ticket dukda da kyar suka bashi saboda mutane dayawa sun rigashi booking.

Doctors ganin Kausar bazata iya haihuwa da kanta ba kuma ta galabaita suka yanke hukuncin mata operation bayan ta tashi dan sun mata alluran bacci saboda ta huta, koda suka fadawa su Abba Dad dinta cewa yayi a jira mijinta yazo shi ze yanke hukuncin abinda ya dace a mata. Hydar se bayan isha ya samu kanshi a asibitin, amma bega kowa ba dan duk sun koma gida saboda su dan samu hutu tinda Kausar din ta samu bacci amma banda Binta dataki binsu ko nan da chan, wayan Khaleel ya kira wanda shine ya fito yazo ya shigarshi dashi dakin da Kausar ke bacci, Binta na zaune kan sallaya tana rokawa ‘yar uwarta sassauci a wurin Allah. Gadon Kausar ya nufa ya zauna tareda kare mata kallo, kowa ya ganta yasan baccin ma a wahale takeyinshi, hannunshi yakai kanta yana shafawa a hankali yana tunanin irin rayuwar da sukayi da Kausar a baya da yadda take kokarin canzawa a yanzu dan ganin ta faranta mai, besan yana hawaye ba seda yaji dumi a fuskarshi ya taba yaji ruwa, rungumeta yayi tsam a jikinshi yana kuka itama Binta dake kan sallayar kuka takeyi ganin uncle dinta na kuka.

Kausar da bata dade da tashi ba tace “I can’t breathe”, cikin kasalalliyar murya, sakinta yayi ganin ta tashi Binta ma da sauri ta karaso wurinta tana cewa “anty kin tashi, kin tashi”, Hydar kuwa murmushi ne ya subce mai yace “how do u feel”, murmushin ta mayar mishi itama sannan ta koma hannun Hydar cikin wahalalliyar murya tace “mijina dan Allah kar ka bari doctors dinnan su yankani, kome ze faru karka bari sumin operation”, cike da damuwa yace “even if it means losing you”, ta kada kai tace “even if it means losing me”, sannan ta juya wurin Binta ta kamo hannunta ta hada dana Hydar sannan ta kallesu tace “ga Binta nan dan Allah inaso ka aureta, ka riketa amana, ka bata kulawar uwa da uba sannan kuma ka bata kulawar miji”, kallonta yayi cikin rashin fahimta yace “me kike nufi, kodai zafin ciwo ne”, murmushi tayi me ciwon gaske sannan ta kalli Binta tace “Binta tindaga ranan da na ganinki kika shiga raina na, inaso ki kularmin da abinda zan haifa kaman ke kika haifeshi, abinda na miki a duniyar nan nasan bazaki taba iya biyata ba amma Binta abu daya kacal nakeso kimin wanda idan kika min wannan kin biyani”, cikin kuka Binta tace “anty”, Kausar taci gaba da cewa “inaso ki aure mijina, ki bashi kulawa fiye da wanda na bashi, ki soshi fiye da yanda nake sonshi, ki zamo macce wacce ta iya girki ta kuma iya gyara turakar mijinta, ko kadan karki dauko halayena na rashin iya girki da rashin yin aiki”, Binta kuka Hydar kuka gashi Kausar ta kama hannunsu ta damke wuri daya tana bar musu wasiha wanda Hydar a ganinshi ba komai bane ya sata wannan maganar se zafin ciwo.

Ciwon nakuda sabowa fal ta dawowa Kausar akayi sauri aka maida ita labor room, tin wajejen goma na dare Kausar ba lbr har asuba dan kuwa Hydar yayi yadda yace ko kadan be bari an mata CS ba, da asuba kiran sallahn farko Kausar ta haifi santalelen danta namiji amma iya galabaita sun galabaita daga ita har yaron, da kyar numfashinta ke fita wanda wannan yasa suka bata taimakon gaggawa saboda daidaita numfashinta. Khaleel ne ya fito da ka kalli fuskarshi zakasan an samu nasara, da sauri Hydar ya karasa wurinshi yace “Khaleel meke faruwa har yanzu shuru”, da murmushi keta Khaleel yace “dude calm down mana, se kace ba soja ba”, Hydar ganin fuskar Khaleel yasan an samu nasara saboda haka shima seya kwantar da hankalinshi yace “yimin albishir din, nikuma na baka tukwuici”, dariya Khaleel yayi yace “shege soja mazan fama dazu ba marairaice min murya kayi ba?”, shidai Hydar burinshi kawai yasan wani hali matarshi take, Khaleel ganin Hydar be tanka mishi ba seyace “alhmdllh, Kausar ta sauka lfy, ta samu wani sojan amma ita saboda wahalar da tasha numfashinta be daidaitu ba amma mun bata taimakon gaggawa, kayan baby na hannuna wanda Binta ta bani da sukazo saboda haka nan da 30mins zakaga matarka da danka idan an gama gyarasu”, Hydar beyi wata wata ba wurin kai gwiwarshi kasa yayi wa Allah ma daukakin sarki sujjada tareda gode mishi akan kyautar da ya mishi, kyautar da kudi koh mulki basa iya siyanshi, sannan ya kara mishi godiya akan barin Kausar da yayi ba tareda ya dauke ta ba dukda duk sun sadakar bazata tashi ba, Binta kuwa dan murna seda tayi hawaye ta kira gida ta fada musu halin da ake ciki wanda suma duk suna hanyar zuwa.

Story continues below

Kaman yadda Khaleel ya fada bayan 30mins aka kawowa Hydar danshi me kama dashi sak kamar yayi kaki ya ajiye, rungume danshi yayi ajikinshi yanajin wani sanyi na ratsa duka ilahirin jikinshi, dakin da Kausar ke kwance aka nuna mai Binta ta karbi yaron suka shiga dakin tare, Kausar na kwance ga oxygen nan da aka samata saboda numfashi, Hydar ne ya karasa bakin gadon ya sunkuyar yayi pecking din goshinta yana hawaye yace “thanks for giving me this lovely son, thanks for not giving up, thank you so much my baby mama”, Binta dake bayansu murmushi tayi tana hawaye at the same time ta rungume yaron tsam a jikinta kaman ance za’a kwace matashi. Ba dadewa su Ummi sukazo cikin lokaci kankani dakin ya cika da en uwanta, ita kuwa Kausar baccinta take, Binta ta hana kowa jariri data miko maka ka ganshi kasa albarka zata karbeshi, da akace ta ajiyeshi dan ya huta sosai seta kwantar dashi a dan karamin gadon dake dakin amma se taki barin wurin, cikin zolaya Ummi tace “toh kodai aure zamu miki saboda ki haifo me kama dashi”, dariya Binta tayi tace “ai ni ga dana nan, sedai anty ta haifo wani”, dariya akayi gabadaya ta kalli Hydar tace “Uncle ko bazaka bani baby ba”, yayi murmushi yace “ai kece uwarshi kece ubanshi na baki shi”, dadi sosai Binta taji dan ita duk a tunaninta da gaske yake saboda wauta irin nata, nan kuwa shi wasa yake mata. Khaleel ne ya shigo yace “Hydar da Binta ya kamata kuje gida ku huta koh”, Hydar yace “no she might wake up anytime soon”, Khaleel yayi murmushi yace “ba yanzu zata tashi ba, se nan da 2hrs”, jin haka Ummi tace su tashi suje su kimtsa su dawo, badan sunso ba suka tashi Zeena ma tace zata bisu, Binta ta kalli Hydar tace “Uncle nan zamu bar baby”, kaman zatayi kuka tayi maganar Hydar yace “karki damu ai yanzu zamu dawo”, narai narai tayi da ido yace “kinga idan antynki ta tashi bata ganshi ba bazataji dadi ba, muje mu dawo kinji”, badan taso ba ta bishi suka fita kowa se mamakin yadda akayi takeson yaron lokaci daya.

A gida suna zuwa ta shiga wanka hakama Hydar, Zeena kuwa kitchen ta wuce dan tasan sunajin yinwa, rabon Binta da Hydar da abinci tin daren shekaranjiya, a dinning taga abincin da Kausar tayi jiya da safe duk ya gama lalacewa ma saboda haka ta zubar tayi wanke wanke sannan ta dora musu breakfast, Binta ta riga kowa gamawa abincin ma sauri sauri ta cishi dan burinta be wuce ta koma hospital wurin babynta ba, sun koma hospital ba dadewa Kausar ta tashi, an cire mata oxygen din saboda sun samu numfashinta ya dawo, kallonsu takeyi daya bayan daya suna mata sannu, Hydar zama yayi kusa da ita yace “baby mama ya jikin”, cikin sanyin murya tace “da sauki”, dan she couldn’t believe she made it alive, bata taba tunanin zata haifa kuma ta tashi da rai ba dan iya wahala ta wahala ita kanta tasan tayi gagarumin kokari harda ta kokarta ta haifo da kanta, “where is my baby”, ta tambayi Hydar ya kalli Binta dake rungume da jariri ta karaso gaban gadon ta mikawa Kausar ” seda Kausar ta tashi zaune sannan ta karba jaririnta tana kallonshi cike da tsantsar so, “my baby, my beautiful baby”, ta fada tana kissing din goshinshi, kowa wurin kallonsu yakeyi, Zeena ta dora hannunta kan cikinta wishing she’s the one, amma ganin yadda Kausar ta wahala wurin haihuwa sosai ya tsorata ta amma Khaleel yace ta kwantar da hankalinta ba abinda ze sameta idan lokacinta yazo. Kallon Hydar Kausar tayi tace “an mishi huduba”, yace “a’a inaso ki fada sunan da kikeso da kanki se a mishi huduba dashi”, zataso asa sunan mahaifinta amma tana gani kaman za’ace tayi sonkai, haka zalika tanaso tace asa sunan mahaifin Hydar amma mahaifinta na tsaye wurin zega kaman bata mishi adalci ba, saboda haka seta kalli Binta tace “asa sunan mahaifin Binta Tanim”, Binta bata taba expecting Kausar zatace asa sunan mahaifinta ba, ita da mahaifinta ba kowansu bane tinda ko saninshi basuyi ba, hawaye ne ya zubowa Binta tace “anty na gode”, Kausar tayi murmushi tareda cewa “u deserve it”, nan take Hydar yama yaro huduba da Tanim amma za’a dinga kiranshi da Nawaf meaning (high, lofty).

Kwanansu uku a hospital aka sallamesu gida inda Kausar ta koma gida mahaifiyarta saboda ta dinga samun kulawa sosai, Binta ta bita dan bata ganin akwai abinda ze rabata da Nawaf wanda take kira da Abbana, ta sanar da Anwar komai akan haihuwar Kausar da sunan da aka sawa baby din, basuyi wani shagalin suna sosai ba illa family da abokan arziki da aka hadu sukayi walima. Bayan sati biyu da haihuwar Nawaf Hydar ya koma bakin aikinshi amma ya nemi alfarmar a sake maidashi headquarter dinsu dake Abuja dan yama kanshi alkawarin baze sake yin nisa da iyalinshi ba, alhmdllh ya samu sun yarda wanda a halin yanzu suna processing komawarshi, Binta na nan tana zuwa school koda yaushe kuma tana karatu sosai both Arabi da Boko, kowa yasanta da Nawaf danshi yaron kanshi yafi gane Binta kan Kausar, Anwar yana chan yana karatu kuma ya ba bada himma sosai saboda yanaso ya fita da flying colors kodan yayi saurin securing din aiki kodan ya auri Binta ba tareda bata wani lokaci ba dukda yasan shi samun aiki a wurinshi ba matsala bane, kilama aiki na nan yana jiranshi, har yanzu Anwar da Binta ba wanda yasan tsakaninsu, a fagen soyayya kuwa se abinda yaci gaba a yayinda Kausar ta sawa Hydar da Binta ido dan ganin suna nema su watsar da maganan da ta musu a asibiti na cewar Hydar ya auri Binta, tana cikin hayyacinta sanda ta fada hakan bawai zafin ciwo bane amma ta musu shiru, sedai ta kudurta a ranta cewar Binta batada wani mijin da ya wuce Hydar dan ta dade da sanin cewar Hydar na son Binta amma ya kasa fada mata, saboda haka itakuma ta kudurta zata tayashi wurin samun cikowan farin cikinshi dukda karfin hali zatayi amma a yadda takeson Binta toh ba Hydar ba kowaye ma zata bata.

Not edited

A kwana a tashi ba wuya wurin Allah har Kausar tayi arba’in, seda ta, zagaya dangi da abokan arziki sannan ta koma gidanta, Hydar ma ya dawo Abuja da zama yanzu dan ya samu ya dinga bawa iyalanshi kulawar da ta dace dasu ba tareda yayi nisa dasu ba, sosai Binta ke bawa Nawaf kulawa kaman ita ta tsugunna ta haifeshi yayin da Nawaf ke kara girma sosai kaman ba dan wata biyu ba, kowa sonshi yakeyi tareda son daukanshi saboda yanada shiga rai kaman Mahaifinshi, Kausar ta koma bakin aikinta tareda amincewar Hydar yayinda bata bari aikinta na shiga hakkin rayuwar aurenta, sosai take bawa mijinta da danta kulawa tareda kokarin sauke duk wani hakkokin aure da ya hau kanta. 

BAYAN WATA SHIDA

Yau Anwar ya dawo Nigeria sakamakon gama karatunshi da yayi a kasar India, da murna Mom da Meena suka tarbeshi, “I miss u Mom”, ya fada in a more masculine voice bayan ya gama hugging dinta, sosai ya kara girma har wani gemu ya tara wanda ya hade da sajen shi ya kara kawata fuskarshi, murmushi Mom tayi tace “I miss you more my son”, kallon Meena yayi ta rungumeshi tareda cewa “thank God my Ya Anwar is back”, murmushi yayi yace “do you miss me that much”, ta kada kai tana kallonshi, kallonta yayi ta kara girma da wayo compared to Binta da bata wani kara girma sosai ba se tsayi kaman yadda yake gani a pics dinda take turo mai. Koda suka mota Meena nata mishi surutu amma tunaninshi yafi tafiya akan yadda zega sanyin idaniyarshi, har suka kai gida be bar tunanin Binta ba.

Wanka yayi yayi sallah sannan yaci abinci ya kwanta tareda daukan wayanshi yayi dailing numbern Binta, ringing biyu ta dauka saboda tasan numbernshi na naija, murmushi yayi yace “did u miss my voice da kikayi saurin daga wayan”, murmushi tayi tace “hmm, tin jiya fah naketa kiranka amma not reachable, meyasa baka fada min zakazo naija ba”, “just want to surprise you”, ya bata amsa, ta bata fuska sannan tace “not much of a surprise tinda ka kirani”, gyara zama yayi sannan yace “I’m missing you so badly that why I called if not sedai kawai ki ganni a gidanku”, zaro ido tayi tace “rufamin asiri karkazo gidanmu dan wlh idan aka tambayeni waye kai bansan me zance ba”, ba tareda wani tunani ba yace “u can tell them I’m ur boyfriend”, da sauri Binta tace “no anty Kausar bazataji dadi ba dan I promised her I won’t date u”, sosai ranshi ya sosu amma se yayi shiru dan yasan yarinta na damun Binta sosai, share maganan yayi yace dauko wani hiran, sosai suka bata lokaci suna hira sannan sukayi sallama saboda jin kiran sallahn asr.


Kausar ce zaune a daki Hydar da zaune kan couch yana wasa da Nawaf  dake dariya abinshi, “Abban Nawaf”, ta kirashi da sabon sunan da ta saka mishi ya dago ya kalleta tareda cewa “ya akayi Mommyn Nawaf?”, murmushi tayi tace “ya maganar mu”, cike da rashin sani Hydar yace “wace magana kenan?”, tace “maganan kai da Binta”, kallonta yayi yace “nida Binta kuma?”, ta kada kai tace “maganan da na muku a hospital”, dariya yayi yace “ai lokacin kina maganan ne saboda zafin ciwo, karki damu ni ba auren Binta zanyi ba”, ya fada tareda maida hankalinshi kan Nawaf yaci gaba da mishi wasa, “amma ai kana sonta?”, yaji ta tambaya wanda yasashi saurin dagowa ya kalleta yace “ban gane ba”, murmushi tayi tace “nace amma ai kanason Binta”, zeyi magana tayi saurin cewa “karka karyata dan na dade da sanin kana sonta tin kafin a maka transfer zuwa Lagos, sannan na dade da gane cewar Binta ce cikowan farin cikin ka, nasha kamaka kana kallonta koh kuma naga kana daukanta hoto bada saninta ba, ina ganin irin kallon da take maka”, shiru Hydar yayi kaman ruwa ta cinyeshi, all this while yana tunanin dagashi se Khaleel ne kawai suka san abinda yake feel akan Binta ashe ba haka bane, kunya ce take kamashi yaji kaman yadda nutse a nan wurin, he couldn’t believe that his one & only wife ta gano abinda yake kokarin boyewa kar kowa ya gano.



Tashi yayi ya kwantar da Nawaf sannan ya koma inda take zaune ya zauna tareda riko hannunta yace “Kausar I’m sorry, nasan ban miki adalci ba na fadawa tarkon soyayyan Binta amma inaso ki sani bazan taba auren Binta ba kodan saboda hallacin da kika mata, ni ba butulu bane, saboda haka bazan taba saka miki ta wannan hanyar ba”, girgiza kai tayi tace “no Abban Nawaf zaka auri Binta wannan ba komai bane a wurina ba, ni na baka go ahead”, zeyi magana tayi saurin katseshi da cewa “pls Abban Nawaf, kaga Binta marainiya ce, bazanso na aurar da ita a gidan da banda tabbacin samun walwala da kwanciyar hankalinta ba, amma kaga idan ka aureta zaka kula da ita kuma nima zan kula da ita, bazamu taba samun sabani a tsakaninmu ba, Nawaf ze girma a kusa da ita kaman yadda take muradi, zata dawwama cikin farin cikin da nake mata fatan samu”, girgiza kai Hydar yayi yace “no Kausar wannan ba hujja bace, naji inason Binta amma banga zan iya aurenta ba, babu abinda na nema a gunki na narasa”, da sauri Kausar tace “akwai abubuwa da dama da bandashi wanda yake tattare da Binta, ban iya girki ba amma Binta koda bata iya yanzu ba nan gaba zata iya, bazan aurar maka da ita ba harse ta kware, bana iya daukan nauyinka kullum”, da sauri yace “se akace miki Binta ce zatayi ita da ba kwari ke gareta ba ga rashin lfy wanda badan mun tsaya tsayin daka ba da kullum tana fama da ciwo”, shiru Kausar tayi yace “look Kausar dan Allah ki ajiye wannan maganan kuma karki kara min irinta”, da fadan haka yayi pecking din goshinta ya fita, sosai taga alaman ranshi ya baci amma kuma she’s not ready to give up.


Daukan Nawaf tayi ta sauka kasa zuwa dakin Binta dake karatun exam, Binta na ganin Nawaf ta tashi ta karbeshi shima kaman ya ganeta ya shiga wangale baki, dariya tayi ta fara mishi wasa Kausar ta zauna kan gadon Binta tana kallon yadda takewa Nawaf wasa, murmushi tayi tace “Binta wata alfarma nazo nema wurinki da fatan zan samu?”, hankalin Binta na kan Nawaf tace “Anty fadi duk abinda kikeso indai befi karfina ba zan miki”, “befi karfin ki ba Binta”, Kausar ta fada tana kallonta, har yanzu Binta bata juyo ba tace “inaji anty”, daga sama taji Kausar tace “Binta inaso ki auri mijina”, kiris ya rage Binta bata yarda Nawaf kasa ba har ya fara kuka saboda zamewa da yayi daga hannunta tayi saurin taroshi sannan ta kalli Kausar tana jijjiga Nawaf tace “anty bazan iyaba”, Kausar tace “Binta ki taimaka”, Binta na hawaye ta girgiza kai tace “wlh bazan iya ba”, “zaki iya”, cewar Kausar dake kokarin tasowa, Binta tayi saurin ja da baya ganin Kausar na neman riko hannunta, kallon mamaki Kausar tawa Binta ganin yadda taja baya kaman taga abin tsoro Kausar tayi murmushin takaici tace “Binta ki taimakamin kar mijina ya karo min wata bare wacce bansanta ba dan wlh Binta ban iya girki ba ban iya komai ba watarana idan Hydar ya gaji dani karo mata zeyi”, sosai Binta ke kuka tana girgiza kai at the same time tana jijjiga Nawaf tace “anty Allah kin iya girki tinda gashi kinayi kuma munaci”, “amma ai bakwa jin dadinshi”, cewar Kausar da itama idonta ya cika da kwalla, “wlh anty da dadi”, shiru Kausar tayi dan batada abin cewa saboda ta lura Binta a tsorace take, karban Nawaf tayi saboda ta bashi nono sannan ta fita ta bar dakin, tana barin dakin Binta ta durkushe nan wurin tareda sakin marayan kuka, a yanzu babu abinda take muradi kaman taga mahaifiyarta tazo tana lallashin ta tana ce mata “all is well”. Bayan Isha Anwar ya kira Binta ta dauka amma jin muryarta kaman tayi kuka se yace “My forever meya faru kuka kikayi?”, aikuwa seta sa mishi wani kukan, sosai hankalinshi ya tashi yace “dan Allah my forever tell me what is wrong kina tayar min da hankali”, cikin kuka ta kawo mishi sharhin abinda ya faru tsakaninta da antynta, sosai hankali Anwar ya tashi, he can’t believe they are trying to separate him from the love of his life, sosai Binta ke mishi kuka a waya amma to be strong for both of them se yayi calming kanshi sannan ya shiga lallashin ta yana bata baki hardai tayi shiru, seda yaga tayi shiru sannan yace “Binta I want you to do a favor for me”, “inajinka”, tace mishi ya sauke ajiyar zuciya sannan yace “inaso ki hada kayanki gobe da sassafe ki shirya ki koma gidan Ummi Hydar ko anty Maryam koh Zeena amma idan kina gidan nan hankali na baze kwanta ba, zan dinga gani kaman zanyi losing dinki at any given moment”, shiru tayi tana tunanin Kausar da Nawaf amma ita kanta tin dazu tayi wannan tunanin saboda haka ta mishi “anything for you” sauke ajiyar zuciya yayi sannan sukaci gaba da hira, bashi ya kyaleta ba seda ya tabbata hankalinta a kwance yake sannan ya mata sallama, yana mata sallama ta tashi ta dauki akwati daya acikin akwatinan da Kausar ta bata sannan ta shiga hada kayanta, seda ta gama tsaf sannan ta kwanta tana jira garin Allah ya waye ya bar gidan saboda kar Kausar ta kara mata wannan maganan, a daren ranan ran zukata hudu sun kwana ne cike da kunci da tunani tunani. 
Kiran sallah farko Binta ta farka daga bacci, seda tayi wanka sannan tayi alwallah ta fito, hijab tasa har kasa tayi raka’atainul fajr sannan tayi sallah asuba bayan taji kira, kafin wayewan gari ta riga ta gama shiryawa cikin jallabiya tana zaune tana tunanin hanya batama Kausar rashin adalci ba idan ta tafi, tasan matukar Kausar ta gane Binta bata gidan baza taji dadi ba, amma kuma she has no other choice than to leave dan gani take kaman idan ta zauna gidan Kausar zatace dole se ta auri Hydar, wanda ita ko digon sonshi bata taba ji a zuciyarta ba illah soyayyan en uwan taka.

Seven on dot ta dauki jakanta da duk wani abu da tasan zata bukata ta fito, a compound taga David yana ganin ta ya karaso wurinta yace “Hajiya where u wan go”, “oga’s house”, ta fada gabanta na faduwa, David na jin tace oga’s house yasan gidan iyayen Hydar take nufi amma se yace “but oga never tell me say u go commot”, kallonshi tayi tana tunanin wani irin karya zata mai ta samu ta kubuta, murmushi tayi tana kallonshi tace “I’m going there to spend my weekend”, David tantama yakeyi ya kaita ko kar ya kaita dan bayason abinda ze janyo mishi magana wurin oganshi, kallon Binta dake tsaye yayi kawai seya dau trolley dinta yasa a bayan mota sannan ta shiga ya zauna ya jasu.

Tinda David ya fara tafiya Binta tayi shiru tana tunanin maganan Kausar da kuma Anwar dinta, a yanda takeson Anwar bata tunanin zata iya barinshi, koda yaushe tana bin maganar Kausar dan ta dauketa ne kaman uwa amma unfortunately not this time around dan abinda Kausar ke nema a wurinta yafi karfinta. Batasan sun kai gidan ba seda David ya juyo yace mata sun iso sannan ta fito, shiya ja mata trolley dinta har bakin kofa ya kwankwansa sannan ya juya ya wuce, me aikin da aka samowa Ummi tana bude kofa taga Binta tsaye seta matsa mata ta shiga da kayanta ciki sannan ta  kulle kofan tana kallon Binta, juyowa Binta tayi tace “Ummi ta tashi?”, “a’a bata tashi ba”, ta bata amsa, kada kai kawai Binta tayi sannan taja jakarta zuwa sama dakin da Zeena ta bari, ta ajiye jakarta itama ta kwanta saboda baccin dake idonta, ba dadewa kuwa baccin ya dauketa. 


Ummi bata tashi ba se wuraren karfe goma, tana saukowa ‘yar aikinta ta fada mata Binta tazo tana sama, sosai Ummi tayi mamakin zuwan Binta kuma da sassafe, zuwa tayi ta leka dakin Zeena ta kuwa ganta tana bacci saboda haka seta kyaleta dan ta huta, se wuraren sha daya Binta ta tashi ta sauko Ummi dake kallon news ta kalli Binta tace “en matan gidan Kausar”, murmushi Binta tayi ta zauna kusa da Ummi tace “ina kwana Ummi”, “Lfy lau, ykk”, “Lfy lau “, Binta ta amsa mata dashi tana jira Ummi ta fara mata tambayoyi kan meyasa tazo da sassafe amma se Ummi ta basar tace “tashi kije kici abinci, gashi chan kan dinning”, tashi tayi taje ta cika cikinta sannan ta dawo ta zauna kusa da Ummi, Ummi ta kalleta tace “kin koshi”, ta kada kai Ummi tace “toh yanzu fadamin meya baro dake gidanku da sassafe”, shiru Binta tayi dan batasan me zatace ba, tace saboda Kausar tace ta Hydar ita kuma bata sonshi, ai Ummi baza taji dadi ba tinda Hydar din ai danta ne, “Binta”, Ummi ta sake kiranta ta dago ta kalli Ummi tace “na’am”, Ummi tace “hala suna miki abinda bakyaso ne”, shiru Binta tayi ta girgiza kai Ummi tace “to menene”, cikin sanyin murya tace “anty Kausar ce tace wai in auri ya Hydar, nikuma bazan iya ba shine na bar gidan”, shiru Ummi tayi tana tauna maganan da Binta ta fada mata kafin daga baya ta dago ta kalli Binta tace “ita Kausar din da kanta”, kada kai Binta tayi Ummi tace “shikenan yi zamanki anan zan musu magana”, da haka Ummi ta samu Binta ta warware sukaci gaba da kallon tare. 


Kausar ta tashi ta shiga kitchen ta kokarta ta hada breakfast tareda jerawa a dinning sannan ta koma dakinta, koda ta shiga Hydar ya tashi ta karasa ta gaisheshi ya amsa mata yana rungumota jikinshi yace “Mommyn Nawaf kin tashi lfy”, tace “lfy lau, kimtsa muje muyi breakfast”, murmushi yayi dan sosai yakejin dadin yadda Kausar ke kokarin bashi kulawa yanzu, tashi yayi ya shiga bathroom ita kuma ta dauki Nawaf zuwa dakin da suka ware mishi ta mishi wanka ta shirya shi sannan ta bashi nono, sosai tayi mamakin abinda ya hana Binta zuwa dan kusan kullum tare sukewa Nawaf wanka indai weekend ne haka ma tana zuwa kitchen ta tayata aiki amma yau setaga tsabanin hakan, Nawaf na gama shan nono ta sauka kasa zuwa dakin Binta rike da danta a hannu, kwankwasawa tayi taji shiru saboda haka ta shiga da sallama dan duk a tunaninta bacci Binta keyi, amma koda ta shiga bataga Binta ba, tayi tunanin ko tana bathroom ne saboda haka ta zauna tana jiranta amma tayi ten minutes bataji karan ruwa ba seta tashi taje tana kwankwasa kofan bathroom din amma shiru, bude kofan tayi amma babu kowa a ciki da sauri ta fito ai kuwa sukayi karo da Hydar ya kalleta yace “lfy, meyafaru”, ya hargitse tace “Binta bata gidan nan”, kallonta yayi yace “ban gane ba”, tace “nace maka Binta bata gidan nan”, kallon mamaki yawa Kausar yace “toh ina zata?”, shiru Kausar tayi tana tunanin Hydar ya kama hanyar waje, yana fita ya fara kwalawa David kira dan shi ke kai Binta duk inda zata, da sauri David ya karaso gabanshi na fadawa saboda irin kiran da Hydar ke mishi, yana zuwa ko amsa gaisuwan da David ke mishi beyi ba yace “ina Binta?”, cikin David ne ya duri ruwa baki na rawa yace “oga she dey ur mama house”, Hydar ya kalleshi yace “with whose permission”, shiru David yayi Hydar yace “you’ve been suspended from work for a month since u don’t know ur job”, shiru David yayi dan yasan ran oga ya baci, Hydar cikin gida ya koma sannan ya kalli Kausar dake zaune idonta cike da kwalla ya zauna kusa da ita yace “ki kwantar da hankalinki tana gidan Ummi”.

Girgiza kai Kausar tayi hawaye na tsiyaya kan kuncinta tace “ashe yanzu har akwai abinda zesa Binta barina, akwai abinda zesa Binta ta bar gidan nan”, lallashin ta Hydar ya shigayi tareda cewa “bari mu gama breakfast se muje mu dawo da ita”, girgiza kai Kausar tayi tace “bazani ba, tinda ta zabi ta bar gidan nan shikenan taje, amma koda wasa ni bazanje da sunan naje daukota ba”, tana fadin haka ta tashi ta wuce sama ta bar Hydar wurin yana tunanin zuciya irin na Kausar. 



Anwar ne zaune kan dinning suna breakfast ya kalli Dad yace “dad akwai abinda nakeso na gayama when u ar free”, kallonshi Dad yayi yace “yanzu ma I’m free ina jinka”, susa keya yayi yace “Dad dama akwai wata yarinya da nakeso kuje kuma iyayenta magana”, kallonshi Dad yayi da kyau sannan yace “ka shirya aure ne?”, gyara zama Anwar yayi yace “Dad indai zaka nemamin aurenta a shirye nake”, jinjina kai Dad yayi yace “bataka stable job, at the same time zakayi masters, tell me ta yaya zaka rike matar”, sosa keya ya sakeyi yace “u don’t have to worry about that Dad, zan samu stable job kuma zanyi masters dina dan Allah Dad karkace no”, kallonshi Dad yayi da murmushi yace “ai bazance maka no ba tinda sunna zaka raya, ‘yar wace gidace?”, ” ‘Yar Alhaji Mahmoud ce, cousin sister din Hydar abokin Khaleel”, murmushi Dad yayi yace “kace en gida daya kuka kwaso mana da kai da yayanka”, Mom da tin dazun tayi shiru tace “nima shi na gani, ya sunanta?”, “Binta”, ya bada amsa, Mom tace “Allah ya sanya alkahiri”, duk suka amsa da “ameen”, sannan Dad yace “gobe Sunday zanje naga mahaifin nata”, dadi a wurin Anwar bata misaltuwa, a yanzu burinshi be wuce Abba ya amince ya bashi Binta a matsayin mata ba dan baya ganin ze iya rayuwa idan waninshi ya auri Binta wanda bashi ba. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *