HUTU CHAPTER 6

HUTU






CHAPTER 6




Kallon Anwar Mom tayi tace “Son kana bata min lokaci kana batawa kanka lokaci, kaji dani mana” numfashi yaja ya fitar sannan yace “Mom kinsan su Mubarak friends dina dinnan?” Tace “wa’anda na rabaka dasu kakiji ba” ya sunkuyar da kai sannan yace “toh sunan yawan raina min hankali wai ni har yanzu yaro tinda basan ‘ya mace ba”, “Ina lillahi wa inna ilaihi rajiun”, Mom ta doka salati tareda cewa “Son?” Ya sunkuyar da kanshi yace “Mom kwantar da hankali in karashe miki bayanin, i swear babu abinda na aikata” girgiza kafa ta soma yi alaman ranta ya fara baci shikuma yaci gaba da bata lbrn hadashi da Hajiya da Mubarak yayi har zuwa dauko Binta da yakeyi, yanda yake kula da ita da rashin lfyrta, kwanciyar da tayi a hospital har zuwa shekaranjiya da aka sallamosu sannan ya kara da cewa “Mom wlh na barta ita kadai a gidan nan ba abincin se ruwan sha, dan Allah ki bari naje na dubata, i promise zan mayar da ita inda na dauko ta kuma bazan sake zuwa dauko taba, I will be serious with my studies” Mom da ranta ya gama baci ya galla mishi harara me kyau da lfy sannan tace “son ngd da abubuwan da kakeyi a gari kana jamana zagi, yanzu kai har nawa kake da kake nema ka fara kula mata, kalli yayanka Hydar shekara talatin da wani abu amma har yanzu mata basa gabanshi se kai, Allah ya shiryeka” sosai yayi regret din abinda yayi, yama kasa dagowa ya kalli idanunta, seji yayi tace “ita yarinyar da ka dauko gidan ubanwa ka kaita” yanda tayi maganan yasan ranta a bace yake a hankali yace “Mom gidana ne” kallonshi tayi da mamaki tana tunanin a ina ya samu kudin siyan gida shida ko fili bashi dashi se wanda Dad dinsu ke siya musu, cike da mamaki tace “gidanka fa kace” yace “eh mom”.

Sosa keyanshi yayi yace “mom sanda kukaje India da Abba duba lafiyarshi kukace in muna bukatar kudi mu duba safe dinshi, a lokacin ne na cire 1.5mil na siya gidan” gyara zama tayi ranta a bace tace “sata kenan kayi” da sauri yace “No Mom, ba sata nayi ba, dauka nayi” ranta ya kara baci ta kankance ido tace “da izinin wa ka dauka?” yayi shiru “nace da izininwa ka dauka? Nan ma shiru tace “yanzu ka yarda sata kayi” shiru ya kumayi tace “banda lokacinka yanzu, jirani ina zuwa dan tare zamuje naga shegiyar karuwar taka” da sauri yace “Mom pls, she’s innocent” harara ta galla mishi sannan ta mike ta haura sama shikuma ya fara tunanin idan Mom taga Binta ya zata react, ba dadewa ta dawo rike da jaka da mayafi ran nan nata a hade ba tareda ta kalleshi ba tace “muje”. Mikewa yayi suka fita compound zuwa inda motoci yake ta mika mishi key din BMW dinta suka fice suka bar gidan, a gaban gidan yayi parking suka fito Mom se kallon gidan takeyi “gida me kyau” ta fada a zuciyarta, knock yayi gateman ya bude mishi gate suka shiga yana gaba Mom na baya.

Tinda yaga kofan parlor a bude hankalinshi ya fara tashi, shiga sukayi Mom na biye dashi, a parlor yaga wayan Binta dauka yayi yasa a aljihu duk Mom na kallonshi ya shiga dakin da yake zaton Binta na cike amma ga mamakinshi yaga wayam, se veil dinta da takalma dake yashe a kasa se broken glass, gabanshi ne ya fara faduwa da sauri ya duba bathroom bata ciki ya duba dayan dakin duk bata ciki, hankali tashe ya dawo wurin mom yace “Mom bata nan” Mom tace “ahap, ta gaji tayi tafiyarta ne mana” da sauri yace “No Mom, Binta is not dat kind of a person, infact batasan ko ina a garin nan ba”, tabe baki Mom tayi tace “toh me kakeso nayi?” Shiru yayi tareda sa hannunshi a kai duk tunanin shi sun birkice, kallon Mom yayi sannan ya fita zuwa wurin gateman yace “kai useless fool, where is the girl that I left behind” cike da tsoro yace “oga she don run, na d boy wey u come with dat day come her place, I no knw wetin happen as she waka run outside, i dey call her she no even answer me”, “Mubarak” Anwar ya furta a hankali idonshi na cikowa da kwalla, daga sama yaji murya mom nacewa “mu tafi dan Allah idiot”, jiki ba kwari yabi bayan mom ta karba key din taja mota suka wuce dukda yaso yaje yaga Mubarak amma yasan Mom bazata yarda ba.

Yau kwana uku kenan da Anwar ya shiga tashin hankali saboda rashin sanin inda Binta take, wani hali takeyi ciki, was she raped, me Mubarak ya mata duk ya rasa amsa, gashi ya nemi Mubarak sama da kasa ya rasa numbernshi ma baya shiga, ya daina cin abinci, ba yadda Mom batayi dashi ba amma ina gabadaya ya koma wani iri saboda rashin sanin halin da Binta ke ciki, Mom kanta hankalinta a tashe yake saboda sanyin idaniyarta baya cikin kwanciyar hankali saboda haka tayi shawara da Dad akan ya tura Anwar India ya karasa karatunshi a can, at first Dad yaki yarda amma daga baya ya amince dan Mom ta tabbatar mai da cewar muddin Anwar na garin nan baze bar halayenshi na banza ba dan kuwa baze bar abokan shi ba, da wannan tunanin Dad ya amince ba tareda sun sanar da Anwar ba.

Story continues below


✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴ 

Su Zinaru tsab suka shirya suka dau mota se Abuja inda suna kaiwa suka dau taxi se gidan Hajiya mai gidan dadi, Hajiya tayi mamakin ganinsu amma ta tarbesu da fara’a dukda hankalinta a tashe yake, bayan sun gama gaisawa sunci naci sunsha nasha sunyi nak Zinaru ta goge bakinta da gefen mayafinta sannan tace “toh Hajiya munzo ganin Bintoto ne dama a kira mana ita” Hajiya gabanta ya fadi amma se tayi murmushi tace “ayyah gashi kuwa ta fita tareda en uwanta bata nan” Antyn birni tace “Hajiya ba matsala bari mu jira ta” shiru Hajiya tayi dan batasan me zatayi ba, kwana biyu kenan tana kiran Anwar da Mubarak amma baya shiga, zama tayi tayi tagumi tana jiran ikon Allah dan yau dai tasan gayenta ya kade saboda Antyn birni ba mutunci ne da ita ba. 

Suna nan zaune  awa daya, awa biyu, awa uku amma shiru ba Binta ba lbrn ta gashi dare ya kunnu kai, Zinaru ce ta mike tace “Hajiya fito mana ‘yarmu kafin ranki ya baci a nan, wani irin wulakanci ne wannan kin shanya mu kaman wasu kayan wanken ina taje da har yanzu bata dawo ba, na tabbata in ita batada waya ai en uwantan dan kikace suna dashi” shiru Hajiya tayi dan yanzu kai kam batada ta cewa Antyn birni tace “Hajiya ke muke saurara fa” Hajiya ta nisa sannan tace “kinga Antyn birni wlh nida kaina yau satin daya da en kwanaki kenan bansan inda Binta take ba, yaron da ke zuwa daukan ta kuma wayanshi bata shiga haka na abokinshi ma” Zinaru ta zaro ido kaman da gaske tace “Inna lillahi ina kika kaimun ‘yar tawa,  na shiga uku ni Zinaru daga kawo ‘ya aikatau” da sauri Hajiya tace “dakata malama aikatau kika kawo ‘yarki ko karuwanci?” Zinaru ta kankance ido alaman masifa tace “duk uwasu daya dan dama daga aikatau ake fadawa karuwanci se an ma yaranmu ciki a turosu gida bayan ‘ya’yan masu kudi sun gama lalatasu, kinga kuwa dana turata aikatau in tashi a tutar babu gara na turata karuwanci inji dam a hannuna, yauwa” Hajiya ta girgiza kai sannan “nidai ba hayaniya nake nema ba, kuje zan kawo muku ‘yarku har gida da kaina”. 

Zinaru ta watsa mata wani kallo tareda cewa “ina bansan zancen ba” shiru Hajiya tayi dan batasan ta cewa ba Antyn birni ta kyaftawa Zinaru ido Zinaru ta zauna tareda yin kasa kasa da murya tace “kinga hajiya bari muyi maganan ta fahimta a wuce wurin, kinga zan baki zabi ko ki fitomin da ‘yata koki bani miliyan biyar ko nasa en sanda su kamaki” cike da mamaki Hajiya ke kallonta kafin tace “aiko karene ya cijeni bazan bada wannan kudin ba” murmushi Zinaru tayi tace “toh shikenan karki bayar, amma duk abinda ya sameki ke kikaja, dan daga nan ofishin en sanda nayi, in kin gudu kafin suzo kema kinsan zasu kulle gidan nan ya koma na gwamnati” shiru Hajiya tayi kaman me tunani kafin tace “toh ina laifin in baku miliyan uku, kun rage zafi”,  kallon Antyn birni tayi ta girgiza mata kai sannan ta juya tace “bazamu amsa ba, kefa muke nema mu rufawa asiri saboda haka kawai ki bamu abinda mukace ki bamu” shiru Hajiya tayi tana tunanin “yanzu idan suka fadawa en sanda ai nima zan iya sawa a kullesu tinda da hannunsu suka kawo ‘yarsu karuwanci kuma ma karamar yarinya, na tabbata suma za’a kamasu” saboda haka tayi murmushi tace “na tabbata idan aka kamani kuma se nasa an kamaku da laifin muzgunawa Binta da kikeyi kafin ki turota karuwanci dukda karancin shekarunta” gaban Zinaru ya fadi amma ita Antyn birni dayake kanta a dan waye yake se tayi murmushi tace “ba damuwa, idan munje ai zamu iya fadawa en sanda cewar sace mana yarinya kikayi dan dama duk yarinyar da kika gani kan titi seki saceta da wayo ki kawo ta karuwanci” shiru Hajiya tayi a zuciyarta tace “lallai mutanen nan ba kanwan lasa bane,  tsaf zasu iya kulleni da karyarsu dukda basu da shaida amma ai inada karuwai a gidana, kuma ina dauko na titi amma seda izinin su dan ban sace su nakeyi ba” kallon Zinaru tayi sannan tace “shikenan naji zan baku abinda kuka tambaya amma inaso ku sani, idan bayan nan baku Binta ta dawo gidan nan bazan maido ta ba” dariya Zinaru tayi tace “tafi nono fari nidai naji dumus a hannuna” girgiza kai Hajiya tayi kafin tace “shikenan ku dawo gobe ku karba”, mikewa Antyn birni tayi tace “karfe nawa zamu dawo” Hajiya batare da ta kallesu ba tace “da yamma” kada  kai sukayi ba tareda sun mata sallama ba suka fice suka barta da danasanin karban Binta. 


Story continues below


✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴

Wasa wasa yau sati daya kenan Binta na kwance bata tashi ba, in wani ya ganta se yayi tunanin kota mutu ne badan machine dinda ke kusa da ita dake beeping yana nuna numfashinta na aiki ba,  sosai Kausar ta damu da rashin tashin Binta dan tasan ba mamaki en uwanta na chan suna neman ta, yau ya kama Monday Hydar yasu dawowa weekend amma besamu dama ba, bayan Kausar taje office ta gama ganawa da clients dinta ta dawo hospital ta zauna tana addu’an Allah yasa Binta ta tashi, kiran sallahn la’asar akayi Kausar tayi alwallah tazo ta tada sallah, tana cikin sallah Binta ta tashi tana bude ido ta rufe saboda haske kafin a hankali ta sake budewa, kallon dakin ta shiga yi ta tabbatar wa da kanta cewar lallai a hospital take danta tana kwanciya a ciki kuma ba yanda za’ayi ta manta warin hospital toh amma meya kawo ta nan? Nan ta fara tuna abubuwan da suka faru tindaga lokacin da Mubarak yazo gidan har zuwa sanda mota ya buge ta, hankalinta ne ya tashi ta fara numfashi da kyar dan gani take kaman Mubarak ze dawo at anytime, machine dinne ya fara deeping da sauri da sauri Kausar dake addu’a ta kalle machine din ta kalli Binta hankali tashe tace “Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun” da sauri ta mike ta fita tana kiran doctor ai kuwa taci karo da Khalil da sauri yace “Kausar lfy” bata iya tayi magana ba se nuna mishi dakin tayi tareda juyawa ta koma inda taga har yanzu Binta na kokawa da numfashinta. 


Da sauri Khalil ya karasa tareda sa mata oxygen sannan ya kira nurse aka mata allura nan da nan ta rufe ido ta koma bacci Kausar kam se kuka takeyi dan idan yarinyar nan ta mutu batasan ina zatasa kanta ba, kallonta Khalil yayi yace “calm down Kausar she’s safe now, ta farka ne se kuma fear toke over her, ta tsorata da wani abu ne amma yanzu anjima kadan zata tashi, don’t worry” kada mishi kai tayi tana goge hawayenta sannan ta zauna kan kujera tana shafa kan Binta, murmushi Khalil yayi dan a zamanin nan mutane kalilan ne masu hali irin na Kausar dan wasu idan sun buge mutum ko tsayawa basayi balle ma su kaisu hospital har suyi dawainiya dasu. 

Baccin awa uku Binta tayi ta farka, Kausar dake zaune tana danna waya ta dago ta kalleta sannan ta karasa wurinta tace “baiwar Allah kin tashi” kallon Kausar tayi tanaso tayi magana  amma makoshinta  ya bushe, ganin haka yasa Kausar fita dan kiran Khalil, tare suka dawo da wata nurse, dubata Khalil yayi yaga she’s stable ya juya ya kalli Kausar yace “alhmdllh she’s stable now, ki bata ruwa tasha sannan ki hada mata tea me kauri zan dawo anjima da mugungunanta”,  kai Kausar ta kada tareda cewa “nagode” yayi murmushi ya fita, Kausar ta kalli nurse  din tace “pls we need brush” murmushi nurse din tayi tace “dats wat I’m here for” sannan ta nuna mata tray dinda ke hannun wanda ke dauke da brush da towel da ruwa a boil da kuma empty boil, tashi Kausar tayi tace “ok I’m coming” sannan ta fita ta kira gateman dinsu a waya ta fada mishi ya dauko mata kayan tea a kitchen da ruwan zafi akwai a flask da cup nd spoon sannan ta fada mishi hospital dinda ke  ya kawo nan, komawa tayi ciki bayan ta siya ruwa taga nurse din har tagama wankema Binta baki tana goge mata jiki, fita nurse din tayi Kausar ta bude ruwan ta mikawa Binta tace “sha ruwa” karba Binta tayi tana bin Kausar da kallo bayan ta gama sha ta mikawa Kausar bottle din ta ajiye sannan a hankali  tace “anty dan Allah ki kaini gida banason warin hospital” kallonta Kausar tayi sosai taji dadin girmamata da Binta tayi, shafa fuskarta tayi sannan tace “karki damu zan kaiki idan an sallame mu, ya sunanki?”, “Binta” ta bata amsa a hankali,  murmushi Kausar tayi tace “wat nice name”. 


Kiran gateman dinta ne ya shigo wayanta da dauka tareda fita zuwa compound din hospital din ta karba basket din hannunshi sannan ta koma ciki, tea me uban kauri ta hadawa Binta ta mika mata tareda cewa “karbi kisha bari da duba doctor naji yaushe za’a sallamemu” kada mata kai Binta tayi Kausar ta fita zuwa office din Khalil, da sallama ta shiga ya dago ya amsa tareda cewa “matar soja” murmushi tayi ta zauna tace “doctor yarinyar na complain wai batason warin hospital ka taimaka ka sallamemu yau inyaso seka hadamu da nurse dinda zata dinga dubata” kada kai yayi yace “ba matsala zan baku sallama amma remember what I told u about she needs to take her medication on time” murmushi Kausar tayi tace “Insha Allah”. 


Cikin kankanin lokaci aka basu sallama Kausar tayi settling bills dinsu sannan suka wuce parking lot tareda nurse dinda aka hadasu da ita, sosai Binta taji dadi dan dama bason hospital din takeyi ba, suna zuwa gida Kausar ta kai Binta da nurse din wani daki dake kasa sannan ta kalli Binta tace “ki huta sosai kinji, gobe zamuyi magana” murmushi Binta tayi Kausar ta mayar mata sannan ta wuce zuwa dakinta inda tana shiga habibinta ya fara kiranta, murmushi tayi ta daga wayan tasa a speaker ta ajiye kan dressing mirror sannan ta fara rage kayan jikinta, tanayi tana waya, zama tayi kan kujeran dressing mirror tace “Mine akwai abinda nakeso na fada maka amma se gobe”, “why not now?” Ya tambayeta wondering what it is she wants to tell him, murmushi tayi tace “yanzu na gaji bacci nakeji, i promise I will tell u tomorrow”, “ok no issues, ai da yau da gobe duk dayane Allah ya kaimu”, “Ameen” ta amsa tareda cewa “mine I have to go, yau nagaji sosai”, “ok baby take care love you”, “love u more, bye” da haka ta kashe wayan ta tashi ta shiga bathroom. 

Washegari Kausar na tashi tayi abinda zatayi bayan gari ya waye ta dau waya ta kira Mom, ringing biyu Mom ta dauka tareda yiwa Kausar sallama kafin tace “Kausar ykk, ya mai jiki?”, “jiki da sauki amma sallame mu”, “alhmdllh da fatan dai ba wata matsala?”, “babu, Mom ki turomin Laure tazo ta ragemin kuran gidan nan”, maimakon ta tambayeta meyasa ita bazatayi da kanta ba se cewa “toh yanzu zansa driver ya kawota” da haka sukayi sallama sannan ta kira secretary dinta itama dauka tayi bayan sun gaisa Kausar tace “maybe nayi late yau ko kuma ba zanzo ba, so take care of everything in my absence”, “okay ma’am” kawai secretary din tace dan basu da schedule ta kowa a kasa, sallama sukayi ta ajiye wayan ta sauka kasa inda taga Binta bata tashi ba nurse din kuma na hada kayanta, “tafiya zakiyi?”, juyowa nurse din tayi dan bataji shigowan ta ba sannan ta gaisheta ta amsa kafin taci gabada cewa “tafiya zanyi, night duty ne dani dama, amma zan dawo anjima da rana” sannan ta nunawa Kausar maganin Binta da yadda zatasha ta mata sallama ta wuce bayan Kausar ta bata kudin mota dan basu da driver a gidan. 




Karan gate taji, nan ta leka taga Laure aka kawo, driver din na ajiyeta ya juya Laure kuma ta karasa cikin gidan tana mamakin Kausar wai aikin gidanta ne bazata iya ba se anzo an mata, da sallama ta shiga parlorn Kausar ta amsa mata tana mata sannu da zuwa, gaisawa sukayi kafin Laure tace “bari na tashi dan Mom tace karna dade”, Kausar ba tareda ta damu ba tace “ba matsala fara daga dakinshi sama by the left”, ajiye hijab dinta tayi tinda tasan mai gidan  baya nan sannan ta haura sama, dakin da take zaton na Hydar ne ta bude ta shiga inda taga kura ya cike dakin dan tinda Hydar ya tafi Kausar batabi takan dakin ba, ba bata lokaci Laure ta fara gyarawa ta share ta goge ta canza bedsheet tasa air freshener ta kunne AC sannan ta shiga bathroom nanma ta wanke towels da undies dinda ya bari unwashed kafin ya tafi,  se Allah ya wadar sa halin Kausar takeyi ace mace har mace amma bata iya kula da miji ba wannan ma a matan ai suna kawai taci, fitowa tayi bayan ta gama inda wani kamshi ya bugi hancinta a hankali ta furta “tsafta ma ni’ima ce”, fita tayi taja kofan haka ta dinga bin dukanan tana gyarawa har dakin Kausar inda itama undies dinta ne jibge cikin basket da kayan wanki duk  seda Laure tasasu a washing machine ta wanke ta shanya ta gyara parlor tayi mopping tasa turare sannan ta shiga kitchen, ba karamin mamaki tayi ba dataga dattin da kitchen din yayi, kwanuka ne jibge ba’a wanke ba dan tinda Hydar ya kori last ‘yar aikinta inaga batayi wanke wanke ba sedai aci a ajiye plate, fita da kwanikan waje Laure ta fara yi dan bazata iya wankesu a kitchen ba, jikasu tayi cikin ruwa sannan ta koma ta share kitchen din tayi mopping tayi dusting sannan ta fito ta fara wanke wanke with a mental note na cewar in taje gida dole ta fadawa Mom halin da Kausar ke ciki na rashin kula da abinda ya kamata ace tanayi dan wannan ai kazanta ce, sedai in za’a fita a dau wanka ayi kwalliya amma ba’asan a gyara gida ba. 



Binta ba ita ta tashi ba se karfe goma da en mintuna, Kausar ta gani kan gadon ta jingina da dashboard tana chatting da friends dinta a FOREVER FRIENDS GRP tashi tayi zaune tareda cewa “aunty ina kwana” dagowa tayi ta ajiye wayan sannan tace “Binta kin tashi, ya jikin”, “da sauki” ta bata amsa tana sauke kafanta daga kan gadon, kallon Kausar Binta tayi tace “aunty fitsari nakeji” murmushi Kausar tayi tace “ga bathroom chan shiga kiyi daganan kiyi wanka kiyi brush kiyi alwallah ina zuwa” kada kai Binta tayi ta tashi ta shiga Kausar kuma ta tashi ta fita zuwa dakinta, sosai taga gidanta na kyalli yana sheki ga wani ni’imtaccen kamshin dake fita, har kitchen ta leka taga nan ma fes ta window ta hango Laure a baya tana wanke wanke, batasan sanda murmushi ya kubce mata gabadaya setaji ta sakayau, “inama kullum zan dinga ganin gidana haka” ta fada a ranta sannan ta juya ta haura sama, dakinta ta shiga ta dauko lotion da turare da powder sedai tasan kayanta baza suma Binta ba saboda haka ta dauko mata top da zani ta koma dakin Binta ta zauna tana jiranta. 

Ba jimawa Binta ta fito tayi wanka amma seta maimaita kayan jikinta, kallonta Kausar tayi ta dauko zani da top tace “ungo wannan, cire na jikinki kisa” haka ta koma bathroom ta canza sannan ta fito, sallaya Kausar ta mika mata da hijab tana kallon yadda Kausar ke sallah zuciyarta ya raya mata sallan ba daidai takeyinshi ba, tanadai dungurawa ne. Bayan ta idar Kausar ta bata mai ta shafa tasa turare da powder ita kanta seda taji dadin jikinta se murmushi takeyi, “muje” Kausar tace, parlor suka fito suka zauna Kausar ta kunna TV tana jiran order dinda ta musu ya karaso suyi breakfast Binta ta samu tasha magani, ba dadewa order din ya karaso chips ne kawai se peppered chicken ba laifi Kausar ta iya boiling ruwan zafi, cikin lokaci kankani ta hada musu tea ta juye abincin a plate ta ajiye na Laure gefe sannan ta kira Binta, sosai Binta taci abincin dan yunwan da takeji ta gama ta kora da tea tayi hamdala Kausar ta bata maganinta tasha, se a lokacin Laure ta shigo da anganta ansan ta gaji, zama tayi kan kujera tana “wash” Kausar dake dinning tace “sannu Laure”, “yauwa Kausar” ta amsa mata ba tareda ta juya ta kalleta ba, “ga abincin ki” ta fada tana kallon Laure, tashi tayi itama ta dauka tana cikin ci Kausar tace “Laure in bazan takuraki ba ki dafa mana lunch kafin ki wuce” kai kawai Laure ta daga dan bazata iya cewa Kausar a’a ba, kallon Binta Laure tayi tace “wannan ce yarinyar da kika bige”, “eh itace”, “ina kwana” Binta ta gaishe da Laure ta amsa mata da “lfy lau en mata”, “ya baki maida ita gidansu ba?” Laure ta sake tambaya Kausar tace “ba’a gama treating nata ba, kuma ban ma tambayeta ba tukun” kai kawai Laure ta kada taci gaba dacin abincinta Kausar ta tashi ta rike hannun Binta suka haura sama zuwa dakinta Binta se kallon dakin takeyi dan ya hadu iya haduwa. 


Zaunar da ita tayi kan gado itama ta zauna sannan tace “Binta bani lbrnki, meya sameki ranan kike gudu da daddare kan titi?” Sauke kai Binta tayi kafin ta fara cewa “ni asalina ‘yar kauyen cakawa ne a karamar hukumar madagali dake adamawa, mahaifina mata biyu gareshi,innata da kishiyarta Zinaru wacce nake kira da goggo”…….nan ta shiga bata lbr tindaga mutuwar mahaifiyarta har zuwa azaban da takesha a hannun Zinaru da mutuwar mahaifinta, aurenta  da kallamu da fasa auren saboda bala’in Zinaru zuwa kawota birni da sunan aikatau, zaman gidan Hajiya har zuwa haduwanta da Anwar da yadda yake kula da ita zuwa rashin lfyn da tayi dawowansu gida da zuwan Mubarak wanda yayi sanadin bigetan da Kausar tayi. Kausar batasan hawaye takeyi ba seda taji suna sauka kan fuskarta, tabbas Binta taga rayuwa dukda karancin shekarunta amma not anymore dan ta dau alwashin bazata mayar da Binta gidan Hajiya ko kauyensu ba, zata riketa ta bata kulawar da batasamu ba a baya, “Allah ya rabamu da MATAR UBA (littafin Aisha Muazzam) irin Zinaru” Kausar ta fada a zuciyarta sannan ta goge hawayenta ta kalli Binta tace “zaki zauna dani?” Ai da sauri Binta ta kada kai Kausar tayi murmushi, wayanta ne ya shiga ringing ta duba taga Hydar ke kara saboda haka ta juya tace “Binta je parlorn kasa gani zuwa” tashi Binta tayi ta fita sannan ta dauka wayan tareda sallama. 



✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴

Hydar zaune a rantsatsen office dinshi se juyi yakeyi da kujera dukda aikin dake gabanshi amma he’s curious about what Kausar wants to tell him, tin jiya da tace akwai abinda zata fada mishi ya kasa samun sukuni se addu’a yake Allah yasa alkhairi zaiji daga bakinta, ganin inba ta fada mishi ba baze iya aikin gabanshi yasa ya dau waya ya kira  ta wanda seda ya kusa tsinkewa ta dauka tareda mishi sallama, murmushi yayi dan muryanta kadai yana sashi nishadi, amsa mata sallaman yayi tareda cewa “wifey ykk, hope everything is fine”, “yes everything’s fine amma da abinda nakeso na fada maka I hope u will forgive me after listening to me” dama abinda yakeso yaji kenan amma meya kawo maganan forgiveness, “inajinki” kawai yace mata nan kuwa ta fara bashi lbrn ta buge yarinya da mota ranan da ya tafi Lagos amma bata fada mishi ba saboda kar hankali ya tashi, sosai ranshi ya baci cikin daga murya yace “Kausar wat I’m I to u?” A hankali tace “My husband” yace “shine zaki shiga matsala amma ace bansani ba yarse da aka sallameku daga hospital sannan kike fadamin saboda baki daukeni a bakin komai ba koh?”, da sauri tace “no dats not it, baka dade da fara aikinka a Lagos ba and idan na fada maka u will want to come kuma zuwanka babu abinda ze amfanemu dashi” zama yayi yayi reason da ita sannan a hankali yace “ina yarinyar take yanzu?” Nan tace mishi tana nan gida tareda bashi lbrn Binta da kuma intention dinta nason ajiye Binta, bece a’a ba sema addu’a daya mata tareda sa mata albarka akan rike marainiyar Allah datakeson yi, nan sukayi sallama bayan ya shaida mata cewar Insha Allah yana nan dawowa Friday. 

A ranan Kausar bataje aiki ba kaman yadda ta fadawa secretary dinta, suna gama cin lunch dinda Laure ta dafa musu bayan sunyi sallahn azahar Kausar ta canza kaya ta dauko key din mota da ATM dinta se purse ta fito, a parlor taga Binta da Laure se janta da hira Laure keyi, murmushi Kausar tayi tace ” Binta ina hijabin da kikayi sallah?”, “yana daki” ta bata amsa, “dauko kisa muje”, ba musu ta dauko duk suka mike harda Laure wacce zasu sauke a gida. Gateman ne yaja musu gate Kausar taja motanta sukabar harabar gidan. Gidansu Kausar suka fara zuwa inda har ciki suka karasa, a parlor suka ga Mom da sauri Kausar ta fada jikinta tareda cewa “My Mom I miss u” murmushi  Mom tayi tace “ni dagani dan Allah, an girma ba’asan an girma ba”, Laure ma dariya tayi sannan ta gaishe da Mom kafin ta wuce kitchen, kallon Binta dake tsaye bakin kofa Kausar tayi tace “Binta  karaso ki zauna kin tsaya”, karasawa  Binta tayi ta zauna kujeran dake facing dinsu tace “Ina wuni” murmushi Mom tayi tace “lfy lau”. 



Kallon Kausar Mom tayi tana neman karin bayani, murmushi Kausar din tayi tace “Mom itace wacce na buge” se a lokacin Mom ta sake kallon Binta tace “baiwar Allah ya jikin?”, “da sauki” ta bata amsa a takaice, “Mom zamu wuce saboda akwai inda zamu kar muyi dare, zan kiraki a waya anjima”, “toh sena jiki”, mikewa Kausar tayi Binta ganin haka itama ta mike Kausar tace “a gaishemin da Dad da Ya Ahmad in sun dawo” da haka ta fita Binta na biye da ita a baya.



Mota suka shiga basu tsaya ko ina ba se Seema’s closet, boutique ne babba wanda iyayen Seema kawar Kausar suka bude mata, tanada en aiki amma itama tana zuwa ta zauna, yawancin kayansu Kausar da Miemie da Salma duk a nan suke siya, parking tayi gaban wurin sannan ta fito suka shiga Seema na ganin tasa ihu tareda rungumeta duka ma’aikatan wurin kallonsu akeyi Seema tace “shegiya matar soja idonki kenan, ko kira sedai a ganki online” murmushi Kausar tayi tace “kedai Seema har yanzu ba’a rabaki da shirme naga kema ba zuwa gidana kikeyi ba”, bata fuska Seema tayi tace “inzo wa’annan banzayen masu kakin su tsayar dani”, dariya Kausar tayi a yayinda suke zama tace “na bari fa an sallamesu da dadewa saboda ni kaina basonsu nake a gidan ba, yanzu guda daya kawai aka bari shima kuma bakin gate ne post dinshi”, “da dai yafi” cewar Seema kafin ta juya tana kallon Binta dake bin shagon da kallo tace “ina kika samo bafullatana”, murmusawa Kausar tayi tace “ina girl dinda nake ce muku na bige”, “eh na gane”cewar Seema “toh itace and she went tru a horrible past infact zan iya ce miki she’s homeless”, “and don’t tell me u are planning on letting her stay with you”, “yes dats wat I’m even doing dan har na fadawa Hydar kuma ya yarda”, kallonta kawai Seema keyi da mamaki kafin tace “Kausar are being serious, kin kuwa san me kikeyi?”, kallon Binta Kausar tayi taga hankalinta bayama kansu sannan tace “I knw wat I’m doing, u don’t knw d slightest hint of wat dis girl went, da zakaji kila kema u will do wat I just did”, shiru Seema tayi kafin tace “hint me toh”, ba tareda tunanin komai ba Kausar tace “can u believe as small as dis girl is her stepmom send her out for prostitution”, “What!!!” Seema da bata tabajin al’amari irin wannan ba tayi exclaim tareda juyawa tana kallon Binta da itama ta juyo jin ihun Seema, Seema dan guntun hawayenta ta share ta kalli Kausar tace “babe da gaske kike”, mikewa Kausar tayi tace “nazo mata siyayya ne, gatanan let her gist u about her life bari na zaga naga wani collections kike dashi”, da fadan haka Kausar ta kusa kai cikin shagon ta bar Seema  da Binta, Seema ta kalli Binta tace “en mata ya sunanki “Binta”, ta bata amsa murmushi Seema tayi tace “ashe kakata ce, tsohuwa ban lbrn ki a takaice”, ba tareda wani tunani ba Binta ta bata lbrn sosai Seema ta girgiza dajin cewar mutane irinsu Zinaru still exist, amma Zinaru batada mutunci.  Murmushi Seema tayi tace “karki damu Kausar nada kirki nasan zata kula dake. 



Kausar kaya take kwasarwa Binta long gowns, skirt, tops, atampha, lace kai babu abinda bata dauka ba, komai da tasan zata bukata seda ta daukar mata ta harda undies ta biya bills din sannan suka fito tareda Seema seda tasa kayan a mota sannan suka shiga next shop wanda aka rubuta ‘Seema’s cosmetics’ kayan mai da makeup ta siyawa Binta wanda tasan zebi da kalan skin dinta sannan suka koma section din kayan accessories ta siya mata bag da shoes of different type da kayan jewelries sannan Seema ta dauko wani agogo me shegen kyau da perf na smart collection taba Binta kyauta Binta tayi godiya suka fito daga shagon lokacin har yamma tayi, sallama sukayi da Seema bayan Seema ta kalli Binta tace “zanzo na dauke ki weekend in kaiki gidanmu wurin sister dina, innaje zan fada mata ba mata kawa”, murmushi Kausar da Binta sukayi Binta tace “toh anty” sannan sukayi sallama sukaja mota se KFC inda suka siya abinci sannan suka koma gida. 


Story continues below


Kausar kanta a daure ta shiga gida ganin tun daga waje ta fara ganin ma’aikatan da tacewa Hydar ya sallamesu bata sonsu, amma wai se gashi an dawo dasu, ko amsa musu gaisuwar da suke mata batayi ba ta fito daga mota Binta na biye da ita ba tareda da sun kwaso kayan da suka siyo ba suka shiga ciki, a parlor ta zauna ta dau wayanta ta shiga kiran Hydar amma yana ringing baya dauka, tsaki taja ta ajiye wayan tareda kallon Binta tace “na manta ban dauko abincin da muka siyo ba, dauko mun ban rufe motan ba”, amma Binta ko  gezau, ganin taki tashi yasa Kausar cewa “Binta bakiji bane”, kallon Kausar tayi idonta cike da kwalla tace “ni tsoron masu bindigan nan nakeyi” ko a kauyensu idan taga mafarauta guduwa takeyi bare yanzu data gansu dayawa ko wanna a murde ga bindiga a hannu, dariya Kausar tayi sannan ta tashi dan taje ta dauko. 


✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴


Hydar tinda sukayi waya da Kausar hankalinshi ya kasa kwanciya dan gani yake kaman rashin security ne yasa ta yin reckless driving harta bige ‘yar mutane, shiyasa tin farko yasa mata securities saboda tsaron lfyrta amma tace ita bataso kuma ya sallamesu saboda farin cikin ta amma not anymore, tinda bawai yana zaune a garin bane dole yasa mata securities dan in yau ta bige mutum gobe Allah kadai yasan abinda ze faru dukda bawai fata yakeyi ba, saboda haka ba bata lokaci ya dau wayanshi ya kira branch dinsu na chan Abuja tareda fada musu abinda yakeso wanda cikin lokaci kankani aka aiwatar dashi, kiranshi sukayi suka fada mishi sun aika yara gidanshi kaman yadda ya bukata ya musu godiya tareda  ajiye wayan. 


Yana dawowa gida ya shiga bathroom wanda seda ya dade a ciki kafin ya fito, fitowa yayi daure da towel a kugunshi da kuma wani yana goge jikinshi dashi bayan ya gama ya shirya cikin jeans da top ya gyara suman kanshi da gemunshi ya feshe jikinshi da turare kumawa yayi kan gado inda ya ajiye wayan ya dauka yana dubawa yaga miss call din Kausar, murmushi yayi dan yasan za’a rina ya sake danna mata kira a daidai lokacin da take dawowa daga dauko abincin dake cikin mota, daukan wayan tayi yayi murmushi kaman tana gabanshi yace “wifey hope all is well”, bata rai tayi tace “bana ce maka banason wa’annan masu kakin ba, koda  yaushe fuskarsu a murtuke ni wlh ka fada musu su bar gidan nan”, ta karashe magananta a shagwabe, dariya yayi Allah ya gani yana kewar matarshi fiye da tunanin me karatu, yana kewarta sosai da sosai dukda rigimammiya ce wannan be hanashi kewarta ba. 


Kasa yayi da murya yadda yasan dole ta amince da magananshi yace “look wifey I’m doing this for your own safety, hankali na ba’a kwance yake ba yadda ina nan kena chan ke kadai, kinsan I’m a well known man, kowa yasanni haka zalika a halin yanzu kowa yasan bana garin, basan ta ina kuma a ina nakeda haters ba, and nasan dole akwai mutanen da zasuyi using wannan opportunity din na ganin sunga bayana and I can’t sit here doing nothing for my only family, yanzu da ace da zaki fita ranan akwai security a gabanki da bayanki I’m sure da baki kade kowa ba amma rashin su yasa kinyi abinda ya tasar miki da hankali, so babe just this once ki bari nayi abinda naga shi yafi dacewa da rayuwar mu”, shiru tayi na en wasu dakiku kafin a hankali tace “shikenan”, daga haka kuma aka fada hiran soyayya. 


✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴

Zinaru da Antyn birni sunyi nasarar karban kudin da suka yankewa Hajiya me gidan dadi wacce banda nadamar karban Binta ba abunda takeyi, koda ta fadawa Asabsy itama bataji dadi ba, Zinaru gida lafiyayye suka kama me 2bedroom da bathroom parlor se kitchen inda suka hada hannun jari suka fara business din kayan atampha da shaddodi wanda a kano suke sarowa, Antyn birni duk ta riga ta fadawa kawayenta ta kusa fara business sukace Allah kawo kusawa tareda cewa in kayan sun iso ta kawo musu su gani, Zinaru duniya sabuwa ta samu tana holewarta ba maganan komawa kauye.   

✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴

Anwar ne zaune a beer parlor da kwalban vodka a gabanshi amma hankalinshi na wani wuri daban, Binta ce kawai a wannan kwakwalwar nashi, banda tunaninta ba abunda yakeyi, a ina ze ganta, ta ina ze fara nemanta a gari irin Abuja dinnan, me Mubarak ya mata ranan da yaje gidan, wani hali take ciki, me zaije ya cewa Hajiya me gidan dadi, tunani babu irin wanda beyi ba cursing his Dad under his breath dan a ganinshi duk shi ya ja mishi, da be dakeshi yaji mishi ciwo ba kila da yau Binta is safe with him, amma duk saboda over protective Dad dinshi gashi ya rasa yarinyar da yakejin ta har cikin jikinshi, he’s freaking 22 for goodness sake amma still his Dad treats him like he’s 2years, ya rasa meyasa Dad dinshi yasa mishi ido haka, good nd fine yasan his Dad is a well known politician wanda wannan dalilin yasa suma ko ina suka shiga an sansu amma dat does not give him the right to stop him from doing what he deprives pleasure from, shi ina ruwanshi da wani society, society din sun dade basuyi pointing finger akanshi ba tinda it won’t show on his body, he’s no longer a teenager yet his Dad treats him like one. 



Kallon kwalban dake gabanshi yayi without thinking twice ya daga ya kai baki be sauke ba seda ya kai rabi, ajiyewa yayi ya dau car key da phone dinshi ya mike ze tafi, dago kan da zeyi ya hango Mubarak rungume da wata yana mata dariya, ai tuni ran Anwar yayi mugun baci ganin wanda yayi sanadiyar salwantar Binta, beyi wata wata ba ya karasa tareda kaiwa Mubarak wani wawan punch a fuska wanda seda ya sadashi da kasa, mikewa yayi yana kallon Anwar da mamaki danshi yama manta da wata Binta yaci gaba holewarshi, “Anwa.. ” ya kirashi amma kafin ya karasa Anwar ya riko colar din raganshi ya shakeshi tareda cewa “ina ka kai mun Binta”, wani harara Mubarak ya watsa wa Anwar sannan da karfin gaske ya zame hannun Anwar daga riganshi yace “wani irin tambaya ne wannan, ka bani ajiyarta ne zaka wani zo kana tambaya na ina na kaita, ko da yake da alama ba cikin right sense dinka kake ba, it’s the alcohol in you”, sosai ran Anwar ya baci cikin daga murya yace “Mubarak don’t try me in ba haka bazakaji da dadi ba, what where u freaking doing with her the day she disappeared?”, ya tambaya jijiyoyin kanshi na tashi. 



Murmushi Mubarak yayi yace “oho, kace u are here to confirm ne, don’t worry I will tell u everything, the day ur beloved Binta disappeared I did want u weren’t able to do”, “meaning?”, Anwar ya tambaya confused, wani wawan smirk Mubarak yayi yace “meaning I f*cked her”, runtse ido Anwar yayi mentally playing the scene in his head, take ya fara jin ihun Binta asking for help from this monster, wasu hawaye masu zafi ne suka soma zubowa Anwar beyi wata wata ba ya fara kaiwa Mubarak punches ta ko ina musamman ma wurin manhood dinshi yanda next time ko tunanin sake lalata yarn mutane bazeyi ba, Mubarak kuwa ihu yakeyi tsabar azaba da kyar aka raba Anwar daga jikin Mubarak, rai a bace ya bar wurin tareda barin Mubarak yashe a kasa ya rike joystick dinshi yana kukan azaba. 

Anwar motanshi ya shiga ya tadashi da gudu yabar harabar wurin, jijiyoyin kanshi duk sun fiffito waje, idonshi yayi ja saboda bacin rai, babu abinda ke mishi yawo a kai se hango Mubarak da Binta da yakeyi, sosai yake kara gudu duk inda yabi se an kalleshi inda shikuwa beda wani buri daya wuce ya ganshi a dakinshi a wannan lokacin. Horn yakeyi ba kakkautawa da sauri gateman din ya bude kofa dan ba yau Anwar ya saba mishi irin wannan horn din ba. Fitowa yayi bayan ya gama parking ya shiga ciki direct se dakinshi, ba kowa gidan daga Meenah se masu aikin gidan saboda haka ba wanda yaga shigowanshi. 




Yana shiga daki ya kulle da key tareda yin wurgi sa key din sannan ya karasa gaban dressing mirror ta tarwatsa komai dake wurin se jin karan fashewan kwalaben turare, maida numfashi yakeyi hanunshi dafe da dressing mirror din, kallon kanshi yakeyi a cikin madubin, kuka yakeso yayi ko yaji saukin radadin da zuciyarshi ke mishi amma kukan yaki fitowa fili sena zuci da yakeyi wanda akace yafi na fili ciwo, maganan Mubarak kawai ke mishi yawo akai, “Noooooo” yayi wani ihu tareda kaiwa mirror wani wawan duka da hanunshi take mirror din ya tarwatse hannunshi kuma jini ne ya fara tsiyaya amma radadin da yakeji a hannushi bekai kwatan kwatan wanda yakeji a zuciyarshi ba. 



Meenah dake kitchen tana zubawa masu aikinsu surutu taji karan fashewan glass ita da masu aikin, da sauri suka fito ya isa dakin Anwar suka shiga bubbuga kofan amma ko kallon kofan beyi ba, zama yayi a kasa tareda rike kanshi dake wani tsara mishi gashi bubbuga kofan sukeyi which is not helping his situation, cike da bacin rai ya tashi yayi wurin kofan cikin daga murya yace “will u guys stop that and get ur f*cking legs out of here”, gabadayansu juyawa sukayi dan sunsan waye Anwar banda Meenah da taci gaba da cewa “Ya Anwar ka budemin nice Meenah, kaji ka bude min pls”, jin muryanta ba karamin tsinka mishi zuciya tayi ba saboda tunowa da muryan Binta, murya me sanyi da dadin sauraro, zama yayi dabas a kasa ya rike kanshi wanda se a lokacin yaji wasu hawaye masu zafin gaske a fuskarshi, shi ba abinda Mubarak ya mata ke daga mai hankali ba, knowing the fact that batada kowa a garin yafi komai daga mishi hankali dan besan ina take ba, a ina ze ganta ya gasgata maganan Mubarak, meyasa Mubarak ya mishi haka “why?”. 





Meenah data gaji da buga kofan komawa parlor tayi ta dau waya ta kira Mom tareda shaida mata abinda ke faruwa, sosai hankalin Mom ya tashi bata wani bata lokaci ba ta shigo gidan dan dama makota ta shiga, tana shigowa parlor taga Meenah na hawaye, batabi ta kanta ba tayi hanyar dakin Anwar Meenah na biye da ita a baya, knocking ta farayi tana kiran sunanshi a hankali, “Anwar, Anwar, Son bude Mommyn ka ce, pls son open the door”, Anwar na jin muryan Mom ya tashi ze bude dan ita kadaice wacce ze rungumewa a wannan halin ya fadawa damuwarshi, bashida sama da ita amma yana kaiwa bakin kofa ya nemi makulli ya rasa, besan inda ya jefa ba, kuka ya saki me cin rai da ban tausayi ya  kafanshi ya shiga dukan kofan kafin ya koma ya zauna kasa yaci gaba da kuka, “na shiga uku” cewar Mom dake jin duk abinda yakeyi itama Meenah kukan takeyi jin yayanta na kuka. Da sauri Mom ta wuce dakin Dad ta dauko spare key ta dawo ta bude kofan tareda kutsa kai ciki, “inna lillahi wa inna ilaihi rajiun”, abinda ya fito daga bakin Mom kenan ganin ta’addin da Anwar yama dakin, kallonshi tayi taga shima ita yake kallo da sauri ya tashi ya karasa wurinta tareda rungume ta ya saka mata wani marayan kuka wanda seda ya tsorata ta dan bata gaba ganin Anwar a wannan yanayin ba, dagoshi tayi tareda jan hannunshi suka fita zuwa dakinta ta zaunar dashi tayi tareda cewa “auta dauko min ruwa a fridge”, daukowa tayi tana goge kwallan ta Mom ta mika mishi ruwan se a lokacin taga raunin dake hannunshi, kallon Meenah ta sakeyi tace “auta dauko min first aid box a dakin Khalil”, fita tayi ba bata lokaci ta dawo da box din Mom din ta karba tareda treating din wurin sannan ta kalleshi tace “son”, dago da rinannun idanunshi yayi ya kalleta ta shafa kanshi tace “son me aka maka haka harda zaka jiwa kanka ciwo, meya faru, i thought mun gama akan wannan yarinyar kacemin zaka manta da komai toh yanzu me kuma ya faru?”. 




Story continues below


Kallonta yayi wasu hawayen na sake zubowa ba tareda yace komai ba ya dora kanshi kan cinyarta tareda lumshe ido, tinda taga haka tasan ba magana zeyi ba saboda haka itama tayi shiru tareda sa hannunta a sumar kanshi tana wasa dashi har bacci ya daukeshi, Meenah dake rakube jikin Mom itama tuni tayi bacci saboda  yadda shirun dakin yayi yawa, gyara musu kwanciya tayi tareda mikewa ta fita zuwa kasa inda ta samu en aikinta suka gyara  dakin Anwar. Anwar bashi ya tashi ba se gab magrib, koda ya tashi Meenah ya gani kwance tana bacci kusa dashi, murmushi yayi tareda shafa kanta sannan ya tashi ya fita  zuwa dakinshi beyi mamakin ganin dakin a gyare ba, wanka yayi yasa jallabiya ya wuce masallaci.  Bayan isha sauna dinner dukkansu banda Khalil Dad ya kalli Anwar yace “ka hada kayanka gobe jirgin tara zakabi zuwa India, na riga na gama maka komai akan transfer dinka, kaje chan ka karasa karatunka cikin kwanciyar hankali da mutunci, banaso naji ko naga ancemin kayi ba daidai ba da fatan ka gamsu”, da mamaki yake kallon Dad dinshi kafin ya maida kallon wurin Mom, kallon Dad dinshi ya sake yi yace “amma Dad…. “, hannu Dad ya daga mishi yace “na gama magana”, sannan ya mike ya haura sama, “Mom” ya kira ta itama kallonshi tayi tace “I’m sorry son, this time around dole kayi abinda mahaifinka keso”, girgiza kai yayi yana kallon Mom dinshi disappointedly, ko a mafarki akace mishi watarana his Mom is going to send him to an exile baze yarda ba dan a ganinshi ba karatu sukeson turashi ba koranshi suke sonyi  saboda sun gaji dashi, a hankali ya furta “fine” tareda mikewa Mom tabi bayanshi tana kiranshi amma ko juyowa beyi ba dan ranshi ya gama baci,  yana shiga daki ya bugo kofa tareda dauko trolley dinshi ya fara zuba kaya kota kan Mom bebi ba. 



✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴


Momin Kausar ce zaune a parlor da Ya Ahmad dake bata lbrn Miemie kawar Kausar sun hadu a mall yake cewa Mom shikam yana ganin yasamu matar aure, murmushi Mom tayi tace “ai Miemie mutuniyar kirki ce, se kama Kausar magana ta sanar da ita”, da sauri yace “ai na karba numbernta manta da Kausar yanzu seta sani gaba da tsokana”,  dariya Mom tayi a daidai  lokacin da Laure ta fito daga kitchen ta karaso parlor Mom tace “Laure da magana ne”,  kada kai tayi tace “eh Hajiya dama maganan Kausar ne”, “Kausar kuma?”, Mom ta tambaya Laure tace “ita fa hajiya” Mom da kanta ya daure tace “inajinki wani abu ne ya faru”, Laure ta gyara tsayuwarta tace “Hajiya ba komai bane dama so nake kiwa Kausar fada akan gyara gidanta, sam sam bata gyarawa, jiya da naje bakiga yadda gidan tayi datti ba, hatta wanke wanke Kausar batayi sedai taci abinci ta ajiye plate”, Ya Ahmad dake jinsu yace “wannan ai kazanta ce, ita haka taga anayi a nan”, Mom ta kankance ido ta kalli Ya Ahmad tace “ba haka taga anayi ba amma kuma ai kasan da cewar ko a nan bata aiki, ban aurar da ‘yata da ta zamemasa ‘yar aiki ba, auren HUTU na mata, saboda haka in har baze bari ta samo en aiki ba sedai acigaba da zama hakan nan duk randa ya gaji ya samu en aiki da kanshi”, Laure kam ta cika da mamaki inda Ya Ahmad ya kada kafada ya mike tareda cewa “in kikace zakici gaba da daure mata gindi wata rana dake zatayi kuka ba wani ba”, “fadamin magana marar kunya kawai”, fita yayi zuwa part din hajja ba tareda ya kula Mom ba, Mom kuwa juyowa tayi ta kalli Laure tace “ke kuma idan na aike ki gidanki Kausar kije kiyi abinda ya kaiki bana cikin sa ido da kinibibi”, “yi hakuri hajiya”, abinda Laure tace kenan kanta kasa Mom kuma ta tashi ta wuce daki. 



Kausar fa yau ba kanta dan gobe Hydar ze dawo, daukan wayanta tayi ta shiga Forever friends tareda musu sallama ai kaman jira sukeyi duk suka fito tareda amsa mata sallama Seema tace “matar soja ya kike ya Binta?” 

Kausar:- duk muna lfy.  

Salma:- Wacece kuma Binta🤔?” 

Seema:- long story, I will gist u later?” 

Salma:- no issues, 
ina Miemie naji ta shiru?” 

Miemie:- I’m right here, so wats popping Matar soja me lbr?” 

Kausar:- guys I need ya help, gobe sojana ze dawo 💃kuma inaso in burgeshi kaman ba gobe” 

Seema:- da gaske?” 

Kausar:- A’a da wasa, pls guys I’m damn serious😞” 

Miemie:- so me kika shirya mishi?” 

Kausar:- nothing” 

Salma:- Kausarrrrr, wai yaushe zaki girma kiyi wayo ne for heavens sake, mijinki ze dawo amma kuma baki mishi komai ba, ke kanki nasan baki gyara kanki ba🤦🏻‍” 

Kausar:- @salma shiyasa nace I need ya help, abeg u guys should come over pls”. 

Seema:- nikam gani zuwa kodan naga Binta dan wlh girl din ta tsaya min a rai”. 

Miemie:- @Seema nikam wacce yarinya ce wannan?” 

Seema:- @miemie @salma let’s me up at kausar’s seku ganema idonku, bye need to get ready. 

Salma:- ok” 

Miemie:- Kausar ki ajiye mana abin dadi. 

Kausar:- se kunzo. 

Da haka ta ajiye wayan sannan ta mike ta sauko kasa inda taga Binta zaune da gown a jikinta tana kallo a zahirance amma a badinance hankali ta ya tafi wani wurin. Zama Kausar tayi tareda cewa “Binta” juyowa tayi tace “aunty kin fito”, “na fito Binta kinci abinci”, “eh naci” haka Kausar ta dinga janta da hira har su Seema suka karaso Seema ce farkon zuwa, da sallama ta shigo parlorn ran nan nata a hade Kausar tace “Seema yadai”, harara ta wurgawa Kausar sannan tace “dama samudawanki na nan kikace an sallamesu”,  murmushi Kausar tayi tace “wlh jiya aka dawo dasu kaman kar muyi hiransu dawowa na gida na gansu nima”, gyara zama Seema tayi tana kallon Binta kafin tace “tsohuwa ba gaisuwa”, murmushi Binta tayi tace “ina wuni”, “lfy lau, ykk”, “lfy lau” Binta ta bata amsa, ledan dake kusa da ita ta dauko ta mikawa Binta tace “gashi tsaraba na kawo miki”, karba tayi tareda cewa “ngd”, ta leka taga chocolate ne aciki da kayan zaki,  Kausar ta kalli Seema tace “wato abin ‘yar wariya ce koh”, Seema batakai ga magana ba su Miemie suka shigo se kallon Binta sukeyi Kausar tace “Binta shiga daki kinji”, tashi Binta tayi bayan ta gaishe dasu Miemie sun amsa mata sannan ta wuce daki rike da ledan da Seema ta bata. 

Kallon Kausar sukayi alaman neman karin bayani tayi murmushi tace “ga Seema nan uwar surutu ta sharhanta muku”, dariya Seema tayi ta fara basu lbrn Binta sosai suma suka tausaya mata Kausar tace “daga ina zamu fara, kunga  yamma nayi”, miemie ce ta dauko kayan tsimin data kawowa Kausar tace “gashi nan kitasha har kin shanye daga yanzu zuwa gobe, in yaso daga baya kinmin gdy”, duk sukayi dariya da yake miemie ‘yar maiguduri ce shiyasa duk tasan sirrin irin wannan kayan dan su tun suna yara ake tsumasu. Salma kuwa mikewa tayi ta dawo kusa da Kausar tace “yanzu tashi in rakaki salon a wanke miki kai, ki gyara nails dinki inta kamama har lalle kiyi”, ya mutse fuska Kausar tayi tace “nifa ba wannan ba, maganan what I have to serve my husband nakeyi”, dariya sukayi Miemie tace “muna sane, kuje keda Salma, nida Seema zamu miki snacks da drinks kafin ku dawo”, marairaicewa tayi tace “toh gobe fah, zakuzo da safe kumin girki”, harara suka fara aika mata dashi Seema tace “ai ga irinta nan, ya hanaki dauko ‘yar aiki”, da sauri Miemie tace “wani irin magana ne wannan Seema,  ai ko tanada ‘yar aiki ba ‘yar aiki bace ya kamata tayi girki ba, itada take matarshi ita yaci tayi”, “hakane” cewar Salma, tabe baki Seema tayi Kausar tace “nidai ba wannan ba pls ku bari mu tsara abin mana”, Miemie ce tace “zanzo gobe amma ki sani tare zamuyi aikin dake”, amsawa tayi da toh badan zatayi ba sedan kar aja magana  da tsayi. Tashi tayi ta dauko mayafinta da abinda zata bukata sannan ta fito, dakin Binta ta shiga ta shaida mata zata fita sannan tace ta fito ta zauna dasu Miemie, fita Kausar da Salma sukayi inda seda sojoji suka bisu dukda bataso ba amma order ne daga wurin me gidansu wato Hydar, su Seema kuwa aiki suka fara tareda Binta dake kama musu tana tayasu. 

Se yamma lis sannan Kausar da Salma suka dawo gida, ta wanke kai tayi pedicure da manicure sannan taje spa tayi gyaran  jiki sannan suka dawo a lokacin su Miemie har sun gama abinda abinda sukeyi suna jiran dawowarsu, da sallama ta shiga parlor ai kuwa gabadaya taji gidan ya bade da kamshin snacks murmushi tayi tace “har kun gama”, kallonta kawai sukayi ba tareda sunce komai ba, Seema  dake kwance kan kujera tace “kunga yamma tayi tinda ta dawo ku tashi mutafi”, “haba haba ina zakuje? Karfe nawa ne yanzu?”, cewar Kausar dake neman shiga kitchen dan taga abinda sukayi, Seema tace “ke wlh Popsie na gari, kuma kinsan bayaso muna dare a waje, dan Allah Miemie ku tashi”, ba musu suka mike Salma tace “nima gara na tafi dan yau zanyi bako, gashi ba abinda na shirya”, dariya Kausar tayi tace “Salma ta engineer Hafiz, Allah ya barku tare musha biki”, murmushi kawai Salma tayi ta mike tareda cewa “ki gaishe mana da Binta kice mata mun wuce”,  se a lokacin Kausar ta tuna ashe yanzu fa ba ita kadai bace a gidan ba, ” ina take?”, ta tambaya tana kallonsu Seema, Miemie da tun dazun batayi magana hankalinta na kan chatting dinda sukeyi da Ya Ahmad tace “tana daki, tinda ta shiga sallah bata fito ba, kila bacci takeyi”. 


Har waje inda sukayi parking ta rakasu sannan ta dawo cikin gidan, dakin Binta ta shiga taga tayi tagumi gaban dressing mirror tana tunani, mamaki ne ya kamata “me take tunani?” ta tambayi kanta sannan ta karasa cikin tace “Binta”, da sauri ta juyo dan bataji shigowanta tace “Binta tunanin me kikeyi haka”, shiru tayi tana wasa da yatsun hannunta Kausar ta sake cewa “tambaya nake miki, koh bazaki fadamun ba?”, dagowa Binta tayi ta kalli Kausar sannan a hankali tace “kawai ina tunanin Ya Anwar ne, nasan kila yana chan yana nemana”, murmushi Kausar tayi tace “karki damu, everything will be back to normal, with time zaki manta dashi”, ita dai Binta kallonta kawai take dan ba duka abinda ta fada ta dauka ba tinda bajin turancin take ba. “Kinga an kira sallah, tashi kiyi kizo muci abinci”, kada kai Binta tayi sannan ta tashi ta shiga toilet dan ta dauro alwallah yayin da Kausar kuma ta tashi ta fita zuwa dakinta dan tayi wanka  tayi alwallah. Seda sukayi isha sannan Kausar ta sauko kitchen ta shiga ta debo meat pie da doughnut se drink ta dawo ta ajiye kan dinning sannan taje ta kira Binta, suna cikin cin abinci ta lura da kayan dake jikin Binta tin wanda tasa da safe shine har yanzu a jikinta, “Binta kina wankan yamma?”, tambayar da ta fara mata kenan, Binta ta girgiza kai alaman a’a, Kausar tace “daga yau ki dinga wanka so biyu a rana, safe da yamma, sannan in kinyi wanka da yamma kayan bacci zaki dinga sawa kinji”, “toh aunty”, tace sannan taji gaba dacin abincinta, suna gamawa Kausar taja hannun Binta zuwa dakin Binta sannan ta dauko kayan da ta siyo mata, cikin kayan baccin ta dauko mata wani pj’s pink da takalminshi tace “gashi nan, in kin fito wanka kisa, sannan ki cire hijabin nan kanki yasha iska zuwa Sunday zan kaiki saloon”, murmushi Binta tace “toh”, sannan Kausar ta dauko mata mai da turaruka tace “in kinyi wanka ga mai nan da turare ki shafa sannan ki kwanta”, nan ma da “toh” Binta tabi ta sannan Kausar tace “ni zanje na kwanta, seda safe kinji”, daga kai Binta tayi sannan Kausar ta fita dan tasan Hydar ya kusa kira. 

✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴

Hydar yana dawowa daga office yayi wanka ya canza kaya zuwa 3quarter da loose shirt sannan ya dawo parlor ya zauna tareda daukan wayanshi ya kira Ummi, ringing biyu Ummi ta dauko tareda yin sallama ya amsa, nan suka gaisa take tambayarshi ya aiki yace “aiki alhmdllh, gobe ma Insha Allah zan taho”, “daga zuwa kuma se dawowa dan nan ko wata daya bakayi ba”, murmushi yayi a ranshi yace “Ummi bakison abinda ze dawo dani bane”, amma a fili kuwa cewa yayi “Kausar ce ba lfy, zanzo na dan dubata, sannan kuma akwai meeting dinda zamuyi a nan Abujan”, “toh shikenan, Allah ya kawoka lfy”, murmushi yayi yace “ameen, Zeena fah tana ina?”, “Zeena ta gudu gidan Maryam ta barni daga ni se masu aiki”, dariya yayi yace “haka anyi hutun sch ne?”, “eh sunyi hutu, shine ta gudu ta barni”, dariya yayi yace “ai zata dawo, bari na kira anty Maryam semu gaisa da ita”, “ai kuwa daka kyauta”, sallama sukayi sannan ya kira Anty Maryam suka gaisa da yaranta da Zeena sannan ya kira Kausar suka sha soyayyar su tareda kara jaddada mata gobe yana kan hanya. 

Story continues below


Washegari tinda asuba da Kausar ta tashi kasa komawa bacci tayi saboda zumudi, wanka tayi yasa gown bayan tayi sallah ta sauka kasa zuwa dakin da Binta take, tayi mamakin ganinta tana sallah dan duk a tunaninta bata tashi ba, nan kuwa Binta tin a kauye ta saba da tashi da asuba koma bata komawa bacci, tana idarwa ta gaishe da Kausar ta amsa mata tareda cewa “ashe kin tashi”, murmushi tayi ta daga kai sannan tace “koma ki kwanta kafin gari ya waye”, Binta kwanciya tayi badan baccin zatayi sedan batada abinyi a wannan lokacin. Kausar kuwa fita tayi ta koma daki ta dau waya ta kira Miemie, dauka tayi tareda cewa “matar soja lfy kira da asuban fari”, murmushi Kausar tayi sannan tace “karfe nawa zakizo?”, “se goma”, da sauri Kausar tace “haba haba wani irin goma shida jirginsu ze tashi karfe daya”, cike da mamaki Miemie tace “da karfe nawa kikeso nazo”, “dan Allah kizo 8, kinga semu gama komai da wuri koh?”, dariya Miemie tayi tace “kai Kausar har wani abin zaki dafa da zan dauko kafa inzo 8, ki dai bari nazo 9 tinda so kike a gama komai da wuri”, Kausar badan taso ba tace “shikenan, se kinzo”, murmushi Miemie tayi sannan tace “kuma ki koma bacci, dan nasanki da shegen zumudi”, dariya kawai sukayi suka  kashe wayan, kaman yadda Miemie ta fada kuwa Kausar kasa komawa bacci tayi tana dai kwance ne tana murnar yau zataga sanyin idaniyarta, masoyinta abin kaunarta. 


9:30 Miemie ta iso gidan alokacin Kausar tayi jira har ta gaji dan gani take ko wani lokaci Hydar na iya zuwa dan tasanshi da son surprising din mutane, tana zuwa basu bata lokaci ba suka shiga kitchen, sosai Kausar tayi mamakin ganin kitchen a gyare kuma ko ba’a fada mata ba tasan Binta ce tayi wannan aikin, Kausar da tace zata taya Miemie suyi aikin tare zama tayi kan stool tana danne danne a waya se Binta ce ta shigo ta taya Miemie duk abinda takeyi tana kallo, fried couscous tayi da stew da yaji kayan nama da veggies a ciki sannan tayi pepper soup din catfish, kamshi ne bade kitchen din Kausar tasowa tayi tana cewa “hmm amma fah girkin nan yayi”, harara Miemie ta watsa mata sannan ta karasa aikinta, karfe sha biyu sun gama komai Miemie tasa turaren wuta a gidan sannan ta koma dinning dinda ke cikin kitchen ta zauna se a lokacin su Binta sukayi breakfast, suna gamawa Miemie ta musu sallama ta wuce dan tasan by now kila Hydar yana hanya, kallon Binta Kausar tayi tace “je kiyi wanka, in kin fito ki jirani na zo na zaba miki kayan da zakisa”,”toh” kawai Binta tace dan ita batasan ma me ake ciki ba. 

Kausar wanka ta tsala ba kwa ce ita bace, zama tayi ta bata lokacinta wurin kwalliya sannan ta sa wata less wine and cream color sannan tayi daurin ture kaga tsiya, ta feshe jikinta da turare se zuba kamshi takeyi. 

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.

Kausar👆 

Saukowa tayi ta nufi dakin Binta inda ta ganta zaune da towel a jikinta ta shafa mai Kausar take jira “anty kinyi kyau”, cewar Binta dake kallon yadda Kausar ta dau wanka, murmushi Kausar tayi tace “ngd sis ai kema yanzu zansa kiyi kyau”, wurin kayan Binta ta nufa wanda har yanzu ba’a shiryashi acikin closet ba ta dauko mata gown me budadden shoulder wine da nude din dankwali, zama tayi ta mata simple makeup sannan ta taimaka tasa kayan sega en nonuwan Binta da suka fara fitowa nan sun tsastsaya, murmushi Kausar tayi tana daurawa Binta dankwalin tace “ya kamata in siyo miki topbra tinda kin fara girma”, binta da ido kawai Binta tayi dan batasan me take nufi ba, fesa mata turare tayi tana murmushi tace “My baby girl is looking so beautiful”, murmushi Binta tayi dukda batasan me Kausar tace ba amma tasan compliment ne, daukanta hoto Kausar tayi suna cikin dauka sukaji doorbell, da sauri Kausar tace “Binta my husband is back”, sannan ta fita leaving the puzzled Binta behind. 

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.

Binta👆

✴✴✴✴✴✴✴✴✴

Anwar kwanan bakin ciki yayi, shida yake son ya nemi Binta yanzu Dad dinshi ya bata mishi plan da cewar ze turashi  India karatu, kuma ba’a fada mishi ba se a kurarren lokacin “why?”, tambayan da yakewa kanshi kenan, “toh kodai Mom ta fada mishi maganan Binta ne?”,  ya tambayi kanshi amma ba amsa, se kuma maganan Mubarak ya fado mishi, yasan yanzu ko yaga Binta baze sake da ita kaman da ba saboda shi kadai yasan da irin idon da ze kalleta dukda yasan ba laifin ta bane, to him she’s not pure, his best friend ya riga yayi lalata da ita so baya ganin ze iya cimma burinshi akan Binta koda kuwa ya ganta saboda haka to him tafiyanshi India wani advantage ne da zesa yayi saurin mantawa da ita , amma kuma what of the feelings he has for her, shi kanshi he’s not sure whether it’s love or pity, amma yet again yasan zuwanshi India will help him find out, in sonta yakeyi yasan baze taba manta taba whereas in tausayinta yakeyi yasan with time ze manta da ita, saboda haka yayi make up mind dinshi na zashi Indian kodan ya samu answers to his questions. 



Tinda asuba daya tashi be koma bacci ba knowing dat jirgin 9am zebi, kayan da ya hada ya sake dubawa sannan yayi parking din komai wuri daya, 7:30 ya fito a kitchen yaga Mom tana hada breakfast yace “good morning Mom”, kallonshi tayi da murmushi a zuciyarta tace “har ya gama fushin”, a fili kuwa cewa tayi “morning Son, ka tashi lfy”, “lfy lau”, kallonshi tayi tace “ka hada kayanka?”, kai ya kada mata, rage gas din tayi sannan ta karasa wurinshi tareda rike hannunshi tace “look son, nasan bakaji dadin wannan sudden transfer din naka ba amma inaso ka sani ur Dad is not fault infact nice ma na bashi shawaran turaka India”, kallonta yayi da mamaki yace “Y Mom?”, ba tareda ta boye mishi komai ba tace “saboda banason ganinka cikin damuwa all because of that girl, ko mema sunanta, ni na manta”, ba tareda ya kalli cikin idonta ba yace “Mom Binta is a nice girl”, kai tsaye tace “I don’t like her, dukda ban taba ganinta ba amma banason ta tinda itace silar shiganka damuwa”, yake yayi yace “Mom look, fries dinki na konewa bari naje nayi wanka”, murmushi tayi dan tasan yana gudarwa zancen Binta ne kawai amma babu abinda ke konewa. 

Zaune suka gabadayansu zasu fara breakfast Khalil ya shigo da sallama da anganshi ansa a gajiye yake, Mom ce tace “gaskiya Khalil ya kamata ka dauki hutu a wurin aikinka ka huta”, murmushi yayi kawai shima ya zauna Dad yace “dan beyi aure bane, in yayi aure dole yaba matarshi lokaci ai”, sunkuyar da kai kawai yayi ba tareda yace komai ba Mom tace “manta dashi yaki yayi aure ga Hydar nan ya zama magidanci ya barka”, nan ma murmushi yayi Meenah tace “Ya Khalil yaushe zakayi aure”, Zeena ce ta fado mishi a rai yayi murmushi ya kalli Meenah yace “wacce zan aura batama gama secondary school ba, saboda haka da saura”, Anwar besan sanda yayi dariya ba yace “Yaya kace baby ce ma”, duk suka dara shikuwa abincin shi yaci gabadaci har suka gama, Mom tace “Son ya kamata na shirya karka makara kasan flight dinka 9 ze tashi”, Khalil ne ya kalli Mom yace “tafiya zeyi?”, Mom tace “India zashi ya karasa karatunshin a chan”, ko kadan Khalil be goyi bayan tafiyan nan ba, yana nan da idon mutane a kanshi ya aka kare balle kuma yaje chan wata duniyar da ba dagin iya bare na uba, bame tsawata mishi, yaso yayi magana amma kuma se yayi shiru dan yasan yanzu  nan sesu bata da Mom dan ita akan Khalil batajin komai. Su Mom ne suka saukeshi a airport basu koma gida ba harse da sukaga tashin jirginsu sedai muce Anwar Allah ya  kiyaye hanya. 



.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *