IN AN KI JI (BA A KI GANI BA) BOOK 2 CHAPTER 2 BY ZAINAB LAWAN BIRGET

IN AN KI JI (BA A KI GANI BA) BOOK 2 CHAPTER 2 BY ZAINAB LAWAN BIRGET

Www.bankinhausanovels.com.ng 


Mun tsaya 

Jin haka sai Safina ta dada rushewa da kuka tana fadin “Dan Allah Baba kayi hakuri kar ka neme shi, wallahi yanzu Sulaiman ya daina sona, idan aka neme shi zai ga kamar neman kai ake yi dani”.
Inna tace “Au, tanan kuma kika bollo? Ai
indai akan mubi son ranki ne sai dai ace ba ma
sonki, idan har kina da gaskiya ki bari a nemoshi

shi mana”. Tace “Baba ni a yanzu bana son Sulaiman, ina da wanda nake so daban”.
Mallam Yusuf yace “Wannan kuma abinda ya shafeki ne amma har yanzu mu Sulaiman muka sani, da na san haka za ki yiwa yaron nan da karatun ma ba zan barki ki yi ba”.
Ismail yace “Babu ruwan karatunta da
gurbacewa tarbiyyarta, sai dai ita ta hada kai da
mugayen kawaye”.
Abbas yace “Ai babu ma batun wasu kawaye tunda dai ita ba yarinya bace da har wasu za su sauya mata tunani”.
Sun rabu akan yaya Ismail zai je ya nemi’
“Sulaiman domin ya ji daga gare shi kamar
yanda Mallam Yusuf mahaifinsa ya yi masa umarni”.
Yaya Ismail ya yi sa’ar samun Sulaiman a inda aka kwatanta masa da zuwansa wajen ya gane Sulaiman din sallama ya yi masa sannan ya nemi ganinsa.Bayan sun ware suka sake gaisawa kafin Www.bankinhausanovels.com.ng
ya soma yi masa bayyanin abinda yake tafe dashi “Mallam Sulaiman ina fatan ka gane ni?” “Kwarai kuwa” Inji Sulaiman. Yaya Ismail ya gyara’ tsayuwarsa yace


“Na zo wajenka ne a madadin iyayen mu da
kuma ‘yan uwana, mun gano akwai wani abu mara dadin ji da muke zaton Safina ta yi maka kamar yanda ‘yar uwarta Rahama ta sanar da mahaifiyar mu bayan da muka titsiye Safina da tuhuma sai muka gano akwai alamun rashin gaskiya a cikin lamarinta, domin ta kasa yi mana gamsashen bayani game da rashin ganinku tare a ‘yan satittikan da suka shude, bisa wannan daliline mahaifinmu ya wakiltani domin na zo gareka inji daga bangarenka, domin ba zai yiwu mu dogara da abinda ta fada mana ba, dan haka nake so ka daure ka sanar da ni komai domin muna kyautata zaton matsalar daga bangarenta take”.
Sulaiman ya girgiza kai cike da gamsuwa sannan ya nisa tare da fara Magana cikin nutsuwa da kuma girmamawa ga Isma’il din “Alhamdulillah gaskiya na ji dadi da yanda Allah ya sa kuka kyautata min zato, hakika akwai abubuwa da dama da suka faru a tsakanina da Safina, sai dai ina ganin bai kamata mu tsaya waiwayen baya ba, na dauka duk abinda ya faru a matsayin kaddara na rufe wannan babin kuma na tunkari rayuwata ta gaba. Amma ko kadan ban kulaci Safina ba saboda ina sonta, na yafe mata duniya da lahira, amman banga wani amfani ba mu tsaya muna tuna abinda ya riga ya wuce…” Yaya Isma’il ya ce “Ai ba haka bane Sulaiman yana da kyau ka tsaya ka yi min bayanin abinda ya wakana a tsakaninku domin asan yanda za a kamo bakin zaren al’amarin ta yanda za a gyara kuskuren da aka yi a baya a tunkari gaba”. Sulaiman ya ce “Ai ni tuni na hakura da batun Safina, sabo da haka ma yanzu na jingine batun soyayya ko aure daga shafin rayuwata, amman hakan ba yana nufin na rike Safina da wani abu ba a cikin zuciyata, na yafe mata kuma ina yi mata addu’ar Allah ya sada kowa da alheri, wannan shi ne abinda zan iya Www.bankinhausanovels.com.ng
fada maka babu dadi babu kari”. Jin haka sai Isma’il ya hakura bai sake matsawa Sulaiman din ba akan abinda ya zo ji daga gareshi ba suka yi sallama Ismail ya koma gida gwiwarsa babu kwari.
Isma’il ya kwashe duk yanda suka
kasance tsakaninsa da Sulaiman ya shaidawa
iyayensa wadanda sune suka aike shi, jinjina
lamarin sukayi hakan ne ya tabbatar musu cewar
ba karamin abu Safina ta yiwa Sulaiman ba.
Haka rayuwar Safina ta ci gaba da gudana tun bayan rabuwar su da Sulaiman,rabuwar tasu ta bata damar maida hankali dari bisa dari akan soyayyarta da Kamal.
Kamar yanda ya faro haka ya ci gaba da kashe mata kudi babu kakkautawa, basa rabuwa da junan su kullum suna tare, idan har kaga bai je wajen Safina ba sai dai idan baya gari, tafiye-tafiyen ma yanzu ba a son ranshi yake yinsu ba, domin baya son duk wani abu da zai nisanta shi da ita komai muhimmancinsa, shi kanshi yana mamaki ta yanda aka yi ya kamu da son Safina haka, idan yana gida tunaninta yake yi, haka ma idan ya fita tunaninta ne yake kasancewar tare da shi a zaune ko a tafiye. Www.bankinhausanovels.com.ng
Bashi da abin Ambato sai Safina ko a cikin barcinsa ya daina mafarkin kowa sai ita da soyayyarta. Amma hakan ba abin mamaki bane idan ya tuna da kyakkyawar kulawar da take nuna masa, Allah ya yi mata tarin baiwa, Safina ta iya soyayya ga dadadan kalamai ga ladabi kamar ‘yar syruf, kissa da kinibibi irin na mata ba a Magana, da ire-iren wadannan abubuwan ta sace zuciyar Kamal ta yi masa daurin huhun goro.
Inna kuwa tuna bin bai damunta harta fara tsinkewwa da lamarin Kamal din saboda yanda taga yana kashewa diyar tatta kudi tamkar a kasa yake kwaso su, ranan dai Safina ta shiga gida da ledoji makare da kayayyaki iri daban-daban kama daga na kwalliya zuwa na ciye-ciye masu kyau da tsada hakan ne yasa Inna ta kasa daurewa tace wa Safina “Nifa na gaji idan har yaron nan da gaske yake kice masa ya fito, amma wadannan kyaututtukan sun yi yawa, sai kace ke kadaice mace budurwa a duniya nan? Duk wanda yake sonki sai ya yi ta kashe miki kudi ba jiba gani, to tunda Sulaima din ya janye sai ki baiwa shi wanda kike so din damar ya fito tunda dai karatun ma har kin kusa gamawa, ina gudun kara samun wata matsala kada sa samu wani ya kuma hure miki kunne”.
“Haba Inna ki daina zargin wai hure min
kunne aka yi”. Inji Safina. Inna tace “Ai dole in zargi haka tunda kika bijiro da sabon al’amarin daba a sanki da shi ba a baya, ni dai ina shawartarki da ki daina
biyewa zugar kawaye”. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Haba Inna ni wa zai iya zugani, ai na kai muzalin da zan iya zabawa kaina abinda ya dace da ni”. Inna tace “To kowa dai rai ya yiwa dadi barin mai shi ne”.
Ziyara ta musamman Safina ta kaiwa Hajiyar Kamal, tare suka je da kawarta Nafisa.Tun daga harabar gidan suka ga bambanci da ziyarar da suka kai gidan su Sulaiman, kai bama’ gidan ba unguwar kanta da bambanci data su Sulaiman, a unguwar Bompai su Kamal suke zaune gidansu katafaren gida ne na zamani, gidan kewaye yake da wata kayatacciyar Katanga wacce furanni suka rufeta lub-lub, gidan katafare ne mai dauke da makeken get.
Tun daga harabar gidan Nafisa ta fara santin gidan tare da yiwa Safina barka da arzikin samun kamal da kuma rabuwa da Sulaiman, basu karasa tsinkewa da al’amarin gidan ba said a suka shiga cikin falon gidan, kujerun falon kadai abin kallo ne banda kayan kallo na zamani dake falon.
A falon suka samu Hajiyar kamal din zaune tana jiran zuwansa, farar mace ce ‘yar hutu da suke yin matukar kama kamar an tsaga kara, Hajiyar mace ce mai fara’a da son jama’a gaisawa suka yi cikin walwala inda take tanan nan da su tamkar zata hadiye su, take ta sanya ‘yan
aiki suka cika musu gabansu da abinci kala kala hadi da lemuka masu tsadar gaske, kafin daga bisani ta bar musu falon domin ta basu damar sakewa, suma su Laila barin falon suka yi domin su basu damar cin abubuwan da aka tara musu. Abinka da ‘yan mata ‘yan kwalisa su Safina basu ci abubuwan da aka tara musu sosai badan gudun kar a raina su, daga nan kuma su Lalla suka yi musu rakiya zuwa gidan Aunty Basma domin su gaisa. Gidan bashi da nisa daga gidansu Kamal din, Kamal din ne ya kai su a mota kafin daga bisani su dawo yiwa Hajiya sallama. Www.bankinhausanovels.com.ng
A falo suka tarar da Hajiyar tana duba wasu kayayyaki, dinkakkun shaddojin ready made ghaliloli masu sheki da kyau a jibge a gabanta.
Bayan sun samu wuri sun zauna ne Kamal
yace “Hajiya wadannan kayan fa?”. Hajiya tace “Yanzu nan na tura direba ya karbosu a wurin kawata Hajiya Kubura, ita ce take sayar da su shi ne na sa a karbo min domin na dubawa bakin nawa”.
Safina da Nafisa dake zaune suka yi
murmushi tare da sunkuyar da kansu kasa. Wasu hadaddun riga da zani ta zabar musu, shaddar deep brown ce data sha aikin sama wanda aka cike gaban riga da zanin da shi. Hajiya da Kanta ta karawa Safina tana fadin “Ai kuwa kaga za su yiwa surukar tawa kyau”.
Kamal ya girgiza kai domin shima ya ga hakan, da ma jiki Safina ba daga nan ba in dai wajen daukar kaya ne, duk abinda tasa kyau yake yi mata.
Daga bisani Hajiya ta karawa Safina wata purple din doguwar riga itama tasha aiki na gani na fada an hada musu sha tara ta arziki inda sukaita godiya, wannan ziyarar ta yiwa Safina da Nafisa dadi sosai, sun samu komai yanda suke so ba kamar lokacin da suka je gidan su Sulaiman ba, daga nan Kamal ya dauke su ya mayar da su gida.
Karatun su Safina ya yi nisa, yanzu haka suna second semester a aji 3, daga sun kammala za su shiga final year jinta take tamkar wata sarauniya domin kuwa tana ganin ta riga ta hada duk wasu abubuwan da mazan wannan zamanin suke so, gata da kyau ga ilimi ga tsantsar wayewa da iya kwalliya sannan kuma ga kayan kwalliyar sun wadataceta, dadin dadawa fa alfaharin ta samu hadadden miji wanda za su tsara rayuwar su mai ban sha’awa abar kwatance, kai gaskiya ta zo duniyar nan a sa’a domin komai na tafiya cikin nasara, rayuwar tana gara mata yanda take so. Yanzu babu abinda take so irin ta mallaki Kamal Allah-Allah take ayi bikinsu ko itama ta fara rayuwa cikin daula, zuwa yanzu hangenta na rayuwar da zata shimfida a gidan Kamal ne, Www.bankinhausanovels.com.ng rayuwar cikin A.C. A sati na biyu da tafiyar Kamal na Singapore aka kwantar da maman Nafisa a wani asibitin kudi, sam Safina ba ta samu zama ba, kullum daga makaranta take zarcewa tana taya Nafisa zaman jinyar mahaifiyarta, su Inna ma sun je sun duba maman Nafisa domin kowa ya san yanda suke da Safina duk yawon su tare suke zuwa, rawar kansu iri daya hakan ran yanga da karyar duk iri dayace.
Ranar Lahadi kasancewar babu makaranta a can asibitin Safina ta wuni a nan ne ma Nafisa ke shaida mata cewar washegari suke sa ran za a sallamesu domin tuni Nafisar ta gaji da zama a asibitin, sam babu sakewa gashi kuma babu wasu ‘yan kudaden da suke shigo mata.
Zaman dakin ne ya ishi Nafisa da Safina saboda ‘yan dubiyar da suka cika shi, harabar asibitin suka fita suka samu gindin wata bishiya mai sanyi suka shimfida rug suka zauna, dama. ita Nafisa ko a danginsu ba kowa ne ya yi mata ba sai wanda yake da shi take hulda sabanin Safina dake matukar kaunar daginta, tana alfahari da danginta baki dayansu da mai kudi da mara kudi.
suna hirarrakinsu wanda yawancin hira tasu ta samarin su ce, samarin kuma na Nafisa domin ita Safina tunda ta samu
Kamal duk ta raina ajin kowanne saurayi, sam ba sa birgeta a banza take ganinsu, ita yanzu bata da zance idan bana Kamal ba, wayar da aka bugowa Nafisa ta zama karshen hirar su, hakan kuma shi ne ya baiwa Safina damar nazarin wata mujalla mai lura da matsalolin mata masu mai suna Hantsi.
Aka yi parking din wata galleliyar mota a gefensu, sam Safina bata kula ba domin hankalinta ya yi nisa a cikin karatun, Nafisa ceta zubawa motar ido har ta manta da cewar waya take amsawa da mamallakin motar ya fito sai ya yi musu sallama ya wuce, suka amsa sallamar da kunuwansu suka jiye musu, Nafisa tadago tana kallon mai sallamar, Nafisa kuwa bata iya amsa sallamar ba sai kallo data bi mai sallamar da shi. Har ya wuce yana ta waiwayen Safina saboda muryarta data dauke masa hankali, ga kuma fuskarta daya gani ta kara rikita masa tunani. Www.bankinhausanovels.com.ng
Bayan kamar mintina biyar ya dawo hannunsa rike da wasu takardu daga hanyar labority ya fito koda ya zo daidai inda suke sai ya sake yi musu sallama, ganin Nafisa ta gama wayar da take yi sai ya matso kusa da fadin “Sannunku da hutawa”.
Safina na ta karatunta ko dago kanta bata yi ta kalle shi ba, ita kuwa Nafisa tayi caraf ta

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *