IN AN KI JI (BA A KI GANI BA) BOOK 2 CHAPTER 4 BY ZAINAB LAWAN BIRGET

IN AN KI JI (BA A KI GANI BA) BOOK 2 CHAPTER 4 BY ZAINAB LAWAN BIRGET

Www.bankinhausanovels.com.ng 


Mun tsaya 

Yayi dariyar nishadi “Dadin dake akwai dadin baki”. “Baka yarda ba kenan?” Ta tambaya.
“Ni na isa nace ban yarda ba?kin san
nima tawa zuciyar tana gareki sai yanda kika yi
da ita, dan haka nake son ki nadani sarautar
zuciyarki na zama sarki mai jan ragamarta ba waziri ba”.
Tayi wata dariyar mamaki da kissa “Au a cikin zuciyar harda wani sarki da waziri”. Alhaji Nura ya amshe da sauri “Eh mana a cikin zuciyar ko wace mace akwai sarki da waziri, cikin samarinta wanda tafi so shi ne sarki me biye masa kuma waziri”.
Dariya ta yi tace “Ba kowacce macen ba, domin ni sarkin kawai nake da shi bani da waziri kuma kai ne sarkin”

Wani dadi ya ji a ranshi saboda yanda ta wasa shi, kawar da wannan hirar yace “To yanzu ya aka yi? Me kike yi a daidai wannan lokacin?”. Nan da nan dabara ta fado mata tace
“Ina shirin fita ne”.
“Please kada ki fita ki jira ni yanzu ina zuwa ina kan hanyar zuwa, yanzu ma ina mota na kira ki”.
Cikin tsokana tace “To naji amma karka wuce 20 minutes, idan ka wuce haka ba zaka same niba domin ina da uzuri”.
Jikinsa na rawa yace “Please a dubi darajar soyayya ayi min afuwa kar a tafi a barni ina so nayi rakiya ne”.
Tayi dariya tare da kashe wayar.
Bai ma kai minti ashirin din baya iso, tayi
kwalliya sosai kamar fitar zata yi tace “Barkanka
da zuwa”. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Yauwa na zaci har kin fita ina ta Allah Allah na zo na kaiki, domin bana son a rinka kalle min ke, wai ina ma za ki je ne?”.
Ta dan jujuya kai “Just daman shopping zan je domin mayukana da turaruka sun kusa karewa” Ya bude mata motar yace “Shigo muje in tayaki zabe”. Ta shiga tare da rufe kofar, shi kuma yaja


motar suka tafi.Wani katafaren shopping mall ya kaita tare da bata damar ta zabi duk abinda take so, mayuka da sabulai da turarrukan da take amfani das u kawai ta dauka sai mayukan gyaran kai da shampoo da hand cream, ganin ta dakata da dibar kayan sai Alhaji Nura ya dauki Kwando yana zuba duk abinda yaga ya yi masa, ita kuma tana biye da shi.
Cikin rashin sa’a kawai sai Kamal ya isa harabar mall din kofar shiga mall din Kamal din da ba ya kasar dawowawarsa kasar kenan ko hutawa bai tsaya ya yi baya dauki mota domin ya yo mata siyayya kasancewar bai samu ya yi mata tsarabar ba.
Shigarsa mall din keda wuya ya sanya kansa a layi na farko kawai ya yi arba da ita, tare da Alhaji Nura rike da wani kwali suna dubawa, purple din shaddar nan da mominsu ta batace a jikinta, amma duk da haka bai gama yardawa kansa ba, so yake ta jiyo yaga fuskarta domin ya kara tabbatarwa ai kuwa kamar wacce aka cewa ta juta tana juyawa sai taga Kamal a tsaye kikam yana kallonta kamar an dasa shi tsoro ne ya cikata ta saki kwallin dake hannunta faduwar kwalince ta saka Alhaji Nura ya juya inda ya sunkuya ya dauko kwalin, sai dai bai ga abinda ya faru ba saboda Kamal din tuni ya fita, suna  Www.bankinhausanovels.com.ng
Hada ido ya tabbatar itace sai ya fita a fusace ya fada mota. Da gida zai koma amma säi ya zarce gidansu  Safina sbd bazai taba yiwuwa ba kenan, akan me za,a hada soyayyarshi data wani,
Ko fitowa baiyi ba ya zauna jiranta  Ba,a dadeba sai gashi Alhaji maitama ya ajiyeta ya baiwa yara kayan suka kai mata gida, suka yi sallama ya tafi ta juya zata shiga gida sai taga Kamal jingine a jikin motarsa, turus tayi domin bata zaci  ganinsa ba, abinka da wacce tasan hannunta nan da nan ta gyara fuskarta ta nufeshi da fara’a “Barka dan dawowa mutanen Singapore dazu shi ne na hange ka amman ko Magana baka yimin ba na nemeka na rasa. Kallon da yakeyi mata mai cike da tsarguwa ne ya sanya ta dakatar da maganar ba tare data shirya hakan ba, hakan ya bashi damar cewa “Da ma abinda kike yi kenan idan bana kasar? Wanene wannan dana ganku tare da shi?”.Dariya tayi a kokarinta na son kwantar masa da hankali “Ayya yanzu Alhaji Nura ne gayen? Wanan ai sai dai kace dashi magidanci, idan ma aka yi la’akari da shekarunsa da yaransa ace masa Baba”.ya  katse ta “Niba wannan na tambaya ba, meye alakarki da shi?””Laah abokin yaya Isma’il ne fa, tare sukayi school”.
“Shi ne ya dauke ki haka siddan ya yi miki shopping?”. Cikin gatse ya yi tambayar da sauri ta maida numfashi. Ta fahimci inda tambayar tashi ta dosa dan haka tayi dariya tace “Haba Kamal fince dînsa fa zai yiwa siyayya ya nemeni don na yi masa rakiya na ta yashi zaben kayan kwalliya”. Jin haka ya sanya jikin Kamal yin sanyi,
ya dubeta yaga kwayar idonta domin ya tabbatar da abinda ta fada masa yace “Kin tabbatar abinda kika fada min haka yake?”. Tace “Haba Kamal, tunda muke-da kai ka taɓa kamani da laifi yin maka karya?”. Shiru ya yi baice komai ba, hakan ya bata damar ci gaba
da cewa “Ka kwantar da hankalinka Kamal, ni
Safina takace bazan taba canza ra’ayina akan ka ba”.
Kamal yace “Ai dole ne hankalina ya tashi saboda ina da matukar kishin abinda nake so, dan haka yana da kyau ki kiyaye domin ban taba yin soyayya ba sai akan ki, bana fatan na kara son wata mace bayan ke”. Www.bankinhausanovels.com.ng
“In dai ni ce kada ka ji komai, domin babu wanda yake burge ni da har zan saurara a duniyar nan bayan kai”.
Kamal ya yi murmushi, ganin murmushin ne ya bata damar ci gaba da kalallame shi da dadadan kalamanta, abinda ya tabbatar mata ya sauka shi ne maganar daya yi wacce yace “Amma ni dai babu ruwana idan uwar gidan tashi ta ganoki”.
Kamar gaske sai Safina tace “Sai dai tayi duk abinda zata yi amma mu muna bayan amarya ita ce sabuwar ya yi”.
Ya dauko wani littafi guda biyu ya mika mata daya an rubuta ‘An introduction technology must know’ ya hada da kudi ya bata tunda bai samu damar yi mata tsaraba ba.
Tayi masa godiya ganin yana shirin tafiya sai ta daure fuskarta, cikin damuwa tace “Ina fatan ba wannan abin ne yasa zaka tafi da wuri ba ko?”.
Da sauri yace “No, zanje gidane na huta ban dade da sauka banace gara na zo naganki, kar ki damu ai gobe zan dawo kuma ma ai za muyi waya da daddare”. Ya shiga mota ya zauna inda ta rufe masa kofar ta lekashi tace “Don Allah kayi tuki a hankali ka kularmun da kanka”.
Yace “I will, kada ki samu damuwa”. Yana tafiya ta daga kafada tare da fadin “Wahalallu sai kuyi ta yi”. Ta kada kai ta shige gida dama ta tsaya ta kalallame shi da dadin baki ne sabida
tana saka ran samun wani abu daga hannunsa.
Ta shirya zata je gidan Rahama don ta kwana biyu bata je ba, sakamakon karatu daya sha kanta, shi yasa yanzu ta daure ta yakice tun kafin su soma jarrabawa.
Tana shiga ta iske su a kitchen, Rahama tana zaune tana hada fruit salad, Idris kuma yana zaune dirshan yana aikin spring roll yanata jefa wa a mai cikin gwaninta tamkar mace.
Tintsurewa tayi da dariya “Rahama yau haka kika maida maigidan naki kamar kuku?”. Idris ya yi caraf “Karki dauki alhakinta na maida kaina dai, kin san sha’anin masu juna biyu ba a son aga suna shan wahala, kin dai sanni
da tausayi”.
Cikin shagwaba Rahama tace “Ka ga abinda nake fada maka ko? Zaka saka ni a bakin duniya ace na mayar dakai mijin tace”. Ta juya ga Safina “Haka ma fa da sallah dan bana son warin nama kanen shi suka zo suka tarar da shi yana şoyar nama baki ji kunyar daya bani ba”,
Safina tace “Ai kuwa nima zan so na ganshi a gaban kasko”. Suka kyalkyale da dariya su duka sannan ya dubi matar tashi yace “Karki damu da maganar mutane, ba dama suga miji yana taimakon matarshi sai su ce ta shanye shi, zaman aure ai taimakon juna ne rayuwa sai da taimakekiniya”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Tom Safina ta rike baki kafin tace “Ni na rasa ta cewa ai na zaci da zarar an fara haihuwa duk soyayyar nan dainata ake yi”.
Idris ya yi murmushi “Banda abinki ai haihuwa ita take kara dankon soyayya, soyayya sai dai abinda ya karu”. kan
Safina ta karbe aikin da yake yi shi kuma ya shirya ya fita dan dama yana da uzuri, bayan. fitarsa ne ta dubi Rahama “Wai dama ciki ne dake? Ke kuwa me kike son maida kanki? Sai kace wata Akuya duk shekara sai kin – haihu yanzu shekarar Shahid nawa? Ai kamata ya yi ki bari sai ya shekara biyar kafin ki kara samun wani cikin, shi yasa fa ni bana son yin aure yanzu, haka kawai kana haskawa a fara saka ka a layin iyaye duk kabi ka tsofe”.
Wani irin kallo Rahama ta jefi Safina dashi wanda ke nuna baki san me kike yi ba, Safina bata kula da kallon da take yi mata ba tace “Koda yake baku da aikin yi ne shi yasa”.
“Mu kuwa muke da aikin yi tunda zaman aure muke yi, haihuwa kuwa ita ce ribar auren”. Tayi shiru tana jiran jin abinda Safina zata. ce, bata ce komai ba sai juya akalar hirar tasu da ta, yi tace “Bara na zubo miki abinci sabida naganki zuru-zuru kamar mai yin azumi”.
Ta dube ta tace “Ke dai bari wallahi nasha wahala wajen samun motar haya, yanzu kamar ni ace na tsaya a bakin titi ina neman tasi mutuncina duka ai ya zube wallahi”.
Rahama tace “To ke wace ce dahar za kice kinfi karfin shiga motar haya alhalin baki da taki? Idan kika yi hakuri ai komai lokaci ne, nan gaba sai kiyi kamar ba a ba, a hankali nan gaba idan kika fara aiki sai kiga kin sayi taki motar”.
“Yaya Usman ne ya dauki motar ya fita da ita balle in rokeshi ya kawo ni, da ma ace motar kwaya daya a gida kamar rai gashi kuma muna da yawa kuma kowa na da nashi uzurin”.
Mamakin Rahama ya karu matuka dan taga da gaske Safina take maganar ba da wasa ba tace “To ki godewa Allah domin wasu ko babur babu a gidansu kuma babu abinda ya rage a jikinsu”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Wuni tayi a gidan suna ta hirar zumunci ita da ‘yar uwarta, cike da sha’awar yanda wannan iyalin suke gudanar da rayuwarsu ta baro gidan, duk da cewar Idris din ba mai kudi bane amma suna gudanar da rayuwarsu cikin kwanciyar hankali da rufin asiri, babu damuwaa tare da su, abinda yafi daukar hankalinta shi ne
yanda Idris din ke ririta matarshi tamkar kwai yana matukar ji da ita.

**

Misalin karfe takwas na dare Alhaji Maitama ya zo, bata zaci shi ne ba domin yaro aka aiko, saida ta fito ta ganshi jingine a jikin motarshi, kafin tace komai yace “Kinyi mamakin ganina da daddare ko? Ai tun yamma na zo aka ce min kinje gidan yar uwarki gashi kuma kin rufe wayarki aida na san gidan sai dai kawai ki ganni domin hankalina ba zai taba kwanciya ba matukar ban sanya ki a idanu ba ko kuma ban ji zazzakar muryarki ba mai kama da sarewa”.
Kallonshi kawai take yi tana murmushi, Alhaji Nura mutum mai cike da kuzari da baya sanya a al’amuranshi a koda yaushe yana cikin nishadi da annashuwa kamar bai taba ɓacin rai ba, irin mutanen nan ne masu barkwanci da ba wuya sun sa ka manta da duk damuwar da kake ciki, abinda yake kara burgeta das hi kenan. Duk zuwan da zai yi wurinta da yamma yake yi, ba ya zuwa da daddare, hatta waya ma da rana zuwa yamma yake kiranta, amma da zarar ya koma gidansa baya yi mata waya, yakance lokacin uwargida ne yana matukar kiyaye wadannan lokutan domin yana ji da Uwargidan tashi saboda
halaccinta gare shi,ko Safina ma ta san da hakan
domin duk inda ya zauna bashi da hirar data wuce iyalinsa. Ta nade hannaye tace “Ashe dana biye ta Rahama na yardazan kwana acan da tsakar
dare zaka dameni da kiran waya kenan”.
Murmushi ya yi yace “Ai yan kwanakin nan sam na kasa samun sukuni, kin hanani sakat, ko me nake yi kina raina, gani nake yi sam lokacin karatun nan naki ba ya sauri nifa duk na kagu”.
“Kai dai ka fiye wutar ciki”. Inji Safina. Alhaji Maitama yace “Ba haka bane na matsu ne naga na mallake ki, ina ganin lokaci ya yi da Baba zai san da maganata”. Ta hangame baki.Ni dai Alhaji kar kasa a dauramin aure ban sani ba”. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Wato na fiye azarbabi ko?” Ya duba agogon hannunsa “Na shagala da yawa kuma lokacin kadan uwargida ta aramin gashi kuma akwai maganganu da yawa a bakina, sai dai gobe kenan ma karasa”.
Ko dar Safina bata ji sabida bata saka shi aka ba balle taji kishinsa “Karfe nawa zaka zo goben?” Ta tambaye shi.

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *