IN AN KI JI. (BA A KI GANI BA) BOOK1 CHAPTER 1 BY ZAINAB LAWAN BIRGET

IN AN KI JI. (BA A KI GANI BA) BOOK1 CHAPTER 1 BY ZAINAB LAWAN BIRGET

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Adaidaita sahu ne ya yi parking a
A daura da harabar bankin u.b.a
dake kan titin unity, bankin dake
kasuwar Suture ta
fuskantar katafariyar
yammacin Africa wato kasuwar kantin kwari dake
tsakiyar birnin mai dadadden tarihi, birnin kanon
dabo. Yan mata biyune suka fito daga cikin
adaidaita sahun, daya daga cikinsu ta sallami
direban ta hanyar biyansa hakkinsa, sai da suka
duba kowane bangare na titin sannan suka
tsallaka cikin nutsuwa da takun kasaita.
Tsantsar kyawun yan matan ya dauki
hankalin mutanen dake kusa da wurin matuka,
wani armashin ma shi ne irin kwalliyar da suka
cacada da kuma takun kasaitarsu. Tafiyarsu
kawai suke yi ba tare da sun kula da kiraye-
kirayen kasuwar da yan kasuwar suke yi musu
ba, kowa na burin su shiga shagonsa domin
sayayya,ko da yake wasu daga cikin masu kiran
nasu ba, dan sayayya suke kiransu ba
Suna kiran nasu da biyu, kodai a yi ciniki ko kuma
ayi daidaito da fahimtar juna, babu shakka


adonsu ya dauki hankalin yan kasuwar shiga
suka yi ta kece raini, kayan su iri daya ne, kyansu
daya haka kamaninsu ma kusan daya sai dai
dayar farace tas wacce fatarta ta surka da launin
ja-ja, zaka rantse da Allah jinsu labaraba ce ko
kuma abzinawa domin ko a farcenta bata yi kama
da jinsin Hausawa ba ita kuma dayar kalar fatarta
wankan tarwaca ce mai dogon hanci wanda ya
kusa danganawa da bakinta. Www.bankinhausanovels.com.ng
Adon leshi suka yi ruwan madara da
aka yi masa ado da zare launin coffe, leshin yana
da manyan duwatsu tsalli-tsalli kayan sunyi
masifar yi musu kyau. Dinkine na kwararrun
madinka da ya kara fito da kyawun yan matan,
musamman ma daya zamo kusan tsawonsu daya
fararce take rike da kyallen atamfar anko wacce
ga dukkan alamu ita suka zo siye, basu saurari
ga
kiraye-kirayen da ake yi musu ba har suka hau
saman bene gidan da aka kwatanto
musu yake wanda suke da tabbacin samun
atamfar anan
Katafaren kantine da aka cikashi makil
da atamfofi zalla; atamfofine daban-daban
iyakar ganinka, jibge suke tun daga kasa har
sama iyakar ganinka shagon babbane amman
makare yake babu masaka tsinke, babu nauin
atamfar da babu a wannan kantin kama daga
atamfofi na gida Nigerian da Ghana da cote de
Voire da kuma atamfofin English, Holland, classis
da Diamond da ma sauran nau ikan atamfofi na
gida dana kasashen waje masu kyau da tsada
Da shigar su suka fara cin karo da wani
babban mutum dake zaune akan wata kujera a
inda ake biyan kudi, ko ba a fada maka ba kasan
shi ne mamallakin shagon, tare suke da wani
matashin gaye da suke kyautata zaton shi ne
babban yaron dake kula da shagon da alama ma
lissafi suke yi, sauran yaran shagon ne suka yi
musu sanna da zuwa, ba tare da bata lokaci ba
suka gabatar da kyallen atamfar da suka zo nema Www.bankinhausanovels.com.ng
cikin sa’a kuwa aka dauko musu ita kasancewar
bata shiga rububi sosai ba, ciniki suka farada
daya daga cikin yaran shagon inda ya fada musu
farashinta su kuma suka taya, saida suka dan
fafata kafin daga bisani cinikin ya fada duk abinda
suke yi basu lura da idanun. matashin nan dake
tare da Alhaji yana
maganganun da suke yi a cikin cinikin yana
sauraronsu, zazzakar siririyar muryar Safiną ce ta
yi matukar dauke masa hankali, zakin muryar
Zakin muryar tata ya dace da ita wanda yasa yaji
har baya son ta daina Magana.
Sai da suka zo za su biya kudin sannan
Sulaiman ya yi dabarar fara jansu da hira
Amman gaskiya kun iya fitar da anko, a cikin
ankon da yan mata suka rika saya a kantin nan
cikin wannan shekarar ban ga atamfar data
burgeni irin taku ba”.
Rahama ta daga atamfar tana kara
dubawa, cike da yabawa tace Kwarai kuwa
domin kowa yabon atamfar yake yi”. Suleman ya
dubi Safina ko zata ce wani abu amma taki
Magana dan haka ya kalleta yace “Hala wannan
ce amaryar?” Itama Rahama sai ta dubi yar
uwarta cike da mamaki tace wa Sulaiman.
“Me ka gani?”
“Gani na yi ta yi kama da amarya”. Inji
Sulaiman. Www.bankinhausanovels.com.ng
Rahama ta danyi dariya “Au, su amaren
har wata kama garesu? To baka canka daidai ba
domin ita wannan da kake gani ko shekarar
aurenta ma bata kama ba, karatu take son yi mai
zurfi…” Sulaiman ya katse Rahamna ganin ya ji
abinda yake bukatar ji Wato dai allurer ruwa ce
mai rabo ka dauka?”

HMMM WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *