IN SO YAKI NE CHAPTER 12
Suraj stop the car! Please pull over! We need to talk! Na fahimci irin wutar dake ruruwa a zuciyar ka but i think we need a plan in ba haka ba zamu fad’a tarkon Sa’eed! Kuma it will be an advantage to him….”+ “Keeeeech! Suraj ya ja burki ya tsaya yana sauk’e numfashi da jajayen idon shi ya dubi Habeeb yace “I just feel like strangling that bloody bastard da hannuwa na! I have had enough already Habeeb! I want them to understand that i am not weak anymore i wont spare both of them!” Kai Habeeb ya girgiza yace “Kamar yanda kake ji haka nake ji, they have crossed all limits musamman ma Sa’eed……….but akwai hanyoyi da dama na fito da maciji daga ramin shi, haka zalika you can never go fishing without a bait! I mean we need a perfect plan, please just calm down for the time beign Suraj.” Kai Suraj ya kad’a yace “You are absolutely right Habeeb! Na san abunda zan yi ….” Wayar sa ya d’auka ya k’ira Inspector Victor ya sanar da shi yana son su had’u “But kazo gida na dake Maitama a chan zai fi, ok i’ll see you there at 7:00 pm sharp in shaa Allah.”……….. Falo ne madaidaici kuma ya kasance babu haske cikin sa se d’an hasken da Television ke bayar wa, hayak’i ne kawai ke tashi se k’aran glasses na giya, duk su biyar d’in a buge suke babu mai laka a jikin shi don da kyar suke bud’e ido. Wutar da aka kunna ne yasa duk suka ankare. Dariyar sa ya sa duk suka mik’e kamar ba bugaggu ba. Cike da isa Sa’eed ya k’araso cikin falon yana tafa hannu yana kad’a kai “What a party! What a party! You guys are really enjoying!” Yana rufe baki duk suka zube k’asa suna magiya “Boss! Mercy Boss….please spare us..” Hannu Sa’eed ya d’aura kan leb’en sa yace “Shush…..quiet down, dole zaku samu hukuncin abunda kuka aikata amma kafin nan ina so in san dalilin yi min k’arya..” Babban cikin su ya jijjiga kai yace “Boss! Tabbas mun yi kuskure, bamu san cewa ba Suraj ne a motar ba kuma mun maka k’arya amma zamu gyara kuskuren mu… Umarni kawai zaka yi mana yanzun nan duk inda Suraj yake se mun gurfanar maka da shi kafin wayewar gari!” Wani mugun dariya Sa’eed yayi yace “Idan kuna tunanin zan baku second chance then you are mistaken! S’aeed never gives anyone a second chance ko da kuwa shi uban waye!” Ajiye musu kwalbar expensive Hennessy wine yayi ya juya saida ya isa k’ofa yace “Here’s a small token for your loyalty” Yana ficewa suka mik’e suna goge zufa babban ya bud’e giyar yana dariya yace “Gayu!…. Gaskiya mun tsallake rijiya da baya ai ni a zato na zai fasa mana kwanya da alburushi sai kuma gashi a madadin hakan mun samu shegiyar mai tsada!” duk suka bushe da dariya kowa ya kawo glass aka zuba masa wine duk a tare suka shanye ko mintina biyu masu kyau basu kai ba suka zube k’asa suna shure shuren mutuwa. Shi kuwa hannuwa a aljihu ya koma motar shi ya tada ya bar unguwar, direct hotel ya koma sannan ya k’ira Muhseen “Zan bar gari for two weeks! Ina da wasu ayyuka da zan kammala, kafin nan keep Laylah Safe for me, make sure bata had’u da Suraj ba a cikin wad’annan satikan biyu sannan i want you to stay away from Suraj for the time being akwai yaran da na sa su kula da komai kafin na dawo just let them do their job”. Kai Muhseen ya kad’a yace “What about my sister? Kayi alk’awari idan na yi abunda kake so zaka yi releasing k’anwa ta, please keep your promise” Dariya Sa’eed yayi yace “Muhseen….Muhseen…. Muhseen!! You are right i promised zan kyale maka k’anwar ka but the plans have changed…..you have to wait for another two weeks and remember! Idan har wani abu ya tafi ba daidai ba consider your beloved sister dead!” Har zufa Muhseen yake ya had’iye miyau yace “I won’t let you down but you must keep you promise, Laylah will be safe sannan bazan bari ko da sau d’aya ta had’u da Suraj ba cikin wad’annan two weeks d’in” Kai Sa’eed ya jinjina yana tab’e baki yace “Then consider your lovely sister safe!” ya katse wayar yana dariya har d’akin na d’aukar sautin….. ***** ***** ****** Idan na fahimce ka Suraj kana nufin accident d’in da Ameer yayi ba Naturally bane it was a well planned accident kuma ma kai akayi niyyan kashe wa…….well! Suraj looking at halin da Ameer yake ciki da kuma yanda motar ka tayi condemn i am sure ba don Ikon Allah ba Ameer could’nt have make it out of that car alive….. Kuma na tabbata koma waye ya ke da hannu a laifin by now baya nan a cikin garin nan” Da mamaki Suraj ya dubi inspector Victor yace “How sure are you Victor?” Murmushi Victor yayi yace “Asali kai ne target d’in shi, sannan plans d’in sa were chopped off, tabbas ya san dole kana da wani clue a kan shi saboda haka zai sauya shek’a domin ya sake sabon shiri, na tabbata don bai yi nasara a karon farko ba hakan ba yana nufin he will back off bane! No he is planning something big! Let’s say for now ba zai kawo maka hari ba no matter what but he will keep a close eye on you, shige da ficen ka, schedules d’in ka and so on! Saboda haka we have to be extra careful Suraj saboda in dai har abunda na fad’a gaskiya ne toh na tabbata zai iya cutar da duk wani na kusa da kai don ya samu ka fad’a tarkon shi, zan yi increasing securities ta ko ina a gidan ka sannan zamu k’ara yawan Surveillance cameras a duk lungu da sak’o na gidan zamu yi monitoring duk wani shige da fice a gidan na tabbata Sa’eed will surely make a wrong move!” Kai Suraj ya jinjina ya mik’e tsaye yana gyara rigar shi, Habeeb ma ya mik’e suka yi sallama da Victor ya fita. Waya Suraj ya fitar ya k’ira masu aikin shi na gida ya ce “Kuzo gidana dake Maitama district, ina son ko ina a gyara a share infact make it lively!” katse wayar yayi ya dubi Habeeb yace “Habeeb ban sani ba ko decision d’ina babu matsala, wannan gidan sashe d’aya ne, we will live under one roof, i’m sure akwai enough flats but still…….” Habeeb ne ya kats’e shi “Suraj….. Whats the big deal? Wannan gidan has about five different flats sannan ko wanne flat akwai d’akuna biyu da living room! It’s more than enough Suraj, besides sai sun fi kowa understanding dalilin dawowar mu nan saboda it’s for their own safety. So forget about that muje kawai Asibitin mu sanar da su abunda ake ciki” murmushi Suraj yayi ya jinjina kai yace “Fine then. Lets go……” K’arfe tara na dare Suka iso harabar gidan, kusan a tare Suraj da Habeeb suka iso, suna parking Meenah ta fito tana kallon Khadija cike da mamaki Meenah tace “Suraj where is this place? Ba gida zamu je ba?” kai Suraj ya kad’a yace “We are home baby, we will be staying here for the time being, for your security please ku shigo ciki.” Ba musu suka sa kai zuwa cikin entrance d’in mai cike da k’awa, Meenah tana sa k’afa karaf idanuwan ta suka sauk’a kan tafkeken portrait d’in Suraj da Laylah, Saida ta had’iye miyau tsabar yanda taji wani shock ya bi jikin ta, da sauri ta kawar da kanta tana k’are wa gidan kallo, duk inda ta juya se hoton yana mata gezo a ido don haka ta k’ank’ame ido ta tsaya ta kasa d’aga ko da k’afa d’aya. Suraj ya fahimci hakan se ya rik’e hannun ta “Sorry about that, kin san wannan gidan shine wajen da duk happy memories d’ina suke, i spend my life here with Laylah, this house is the very first place where i learned to love even more! Na san zakiga abubuwa da dama wad’anda basu miki dad’i ba, but please understand that ba da gangan nayi hakan ba, if you don’t like it right this moment i will get rid of all this photos, zan sa a kai su flat d’in Laylah saboda bazan iya setting foot a wannan wajen ba sorry to say it still brings more pain to me.” Murmushi Meenah tayi se ta bud’e idanuwan ta da suka cicciko tace “Na fahimce ka Suraj, and i’m sure ka fahimci situation d’in da nake ciki, so kayi duk abunda ya dace i promise i won’t complain.” Kai Suraj ya gyad’a sannan ya dubi d’aya daga cikin masu aikin yayi masa alama da ido, da sauri mutumin ya d’auke hoton daga bangon ya haura da shi stairs bai dire ko ina ba se side na Laylah, yana gama wa ya ja k’ofar ya dawo, Suraj ya dubi Meenah da Murmushi yace “Happy??” Murmushi kawai tayi sannan suka k’arasa ciki. Kowa ya gaji don haka Habeeb ya ja khadija da Boboh ya nuna musu nasu flat d’in haka ma Suraj ko hanyar d’akin Laylah bai bi ba ya kai Meenah wani sashen daban duk da bai kai wancan girma ba, daga bisani su Abbah da Ummi suka iso Sapna kuwa ta zab’i ta zauna tare da Mubeenah ko don Iman ma…….. ****** ****** ****** Satikai biyun nan sun yi wa Laylah tsauri saboda tamkar matar kulle haka Muhseen ke gark’ame ta a gida Ko Tasleem driver ke kaita in ta fita securities su rufe k’ofa, har sai in ta dawo, sosai ta shiga damuwa saboda bata san dalilin da yasa Muhseen ke hakan ba se tayi zaton ma kawai wani sabon salon cin zarafin ta ya d’auko domin shi idan ya fice sai ya wuni bai dawo ba kuma naturally idan ya shigo gidan toh tabbas da mace yake shigo wa sannan da safe su fice tare kuma kullum tamkar riga haka yake chanja sabuwa…… B’angaren Ameer kuwa Sati biyun nan da yayi a asibitin jin su yake tamkar shekaru biyu, luckily he is healing fast sedai kullum orthopedics suna kan shi kullum yana magiya a bar shi ya koma gida, Suraj kuwa saida ya tabbata gidan shi na zagaye da full security ta ko wanne b’angare infact shige da ficen kowa na gidan is monitored a koda yaushe…… Sa’eed kuwa yau sati biyun nashi ya cika don haka ya d’au haramar dawowa k’asar, kuma a shirye yake bai damu da me zai je ya komo ba domin har yanzu a kan bakan shi yake na ganin ya wulak’anta Suraj!. Yayinda Suraj ko wacce wayewar gari burin shi ya ga Sa’eed ko Muhseen ayita ta k’are………. MALEEK HOLDING’s 9:00am+ Tiriri ke tashi daga coffee mug dake kan table nashi, yayinda Suraj ke tsaye ya baiwa table d’in baya ya hard’e hannun shi a baya yana kallon harabar company d’in. Maganar Inspector Victor ne ya sa shi juyo wa yana kallon shi “Suraj i think sun fahimci cewa mun yi deploying tight securities a gidan ka that’s why har yanzu basu yi wani slight move ba, sati biyu kenan fa.” Kai Suraj ya jinjina ya dafa kujerar shi ya d’an yi bending a kai sannan yace “Right! Nima na fahimci hakan! Amma na tabbata iya sanin da nayi wa Sa’eed he will not back off easily…. Yanzu me ya kamata mu yi?” Gyara zama Victor yayi yace “Mun yi renting gidan dake opposite naka zamu d’ebe securities d’in zuwa gidan, they will manage all the Cctv from there zamu sa abun ya zama tamkar babu security ko d’aya on guard, ganin hakan zai sa ya yi tunanin taking step.” Kai Suraj ya jinjina yace “What about Muhseen?” “Muhseen……… Muhseen……! You know Suraj! Cikin satikai biyun nan daily activities na Muhseen ya sauya, mutane na suna updating d’ina a kan duk wani move nashi ba inda yake zuwa daga Bar sai gida daga gida sai Bar kuma macen da ya fita da ita ba da ita yake koma wa ba, as for Laylah kwata kwata ma babu wanda yake spotting d’in ta outdoors sedai d’iyar ta Tasleem driver ke kaita school kuma ya dawo da ita, i am sure duk wannan is part of S’aeeds plan! Let’s just wait and see their next move”. Dafe kai Suraj yayi yana cije leb’e sannan ya ce “You have to understand victor…Laylah and my daughter are still in the tigers Den and you are telling me to calm down? Tsawon sati biyu kenan babu wanda yayi spotting Laylah a waje what if Sa’eed ya tafi da ita already?” Kai Victor ya girgiza yace “Suraj. I understand your plight kuma i can assure you Laylah tana nan cikin gidan Sa’eed bai tafi da ita ba just relax, ni yanzu zan tafi idan na kammala shirya komai zan maka magana”. Ba tare da jiran amsar Suraj ba Victor ya fice daga office d’in Suraj kuwa kasa zama yayi se safa da marwa yake, ranar de babu abunda ya yi a office haka har lokaci ya k’ure ya d’auki wayar sa da key d’in motar shi ya fice, tun kafin ya isa ga motar Habeeb ya k’ira shi a waya “Suraj……. Please kazo hospital ni na fita zan d’auko Boboh a school, Talk some sense into Ameer wai so yake a dinga bashi home treatment, to cut it short so yake ya koma gida can you imagine?” Murmushi Suraj yayi yace “Ok toh barin je in same shi, i’ll talk to him”. Yana kashe wayar ya shiga motar bai tsaya ko ina ba sai asibiti………… A kasalance take tafiya duk jikin ta babu dad’i, abinci ta d’auko a warmers ta ajiye kan table ta gama setting table kenan Tasleem ta shigo da gudun ta “Mommy i’m home!” Da murmushin ta tace “Welcome home baby”. Ji tayi hannun ta na hagu ya rik’e da har wani jerking yake, zafin da taji a k’irjin ta yasa tayi saurin dafe k’irjin tana fitar da wahalallen numfashi tana ta tari, har k’asa ta kai tana tari da gudu Tasleem ta rik’e ta, haka ma mai aikin gidan “Ranki shi dad’e sau da dama ciwon nan naki yakan tashi amma kin k’i zuwa asibiti yanzu gashi yana so ya fi na kullum ya kamata kiga likita ai”. Ture ta Laylah tayi gefe sannan ta k’ok’arta ta mik’e tace “Ki ba wa Tasleem abinci ta ci ni zan je in d’an kwanta idan na tashi anjima zan ji normal kar ki damu, da kyar ta haura stairs ta rik’e k’irji gam, tana shiga d’aki ta rufe k’ofar ta nufi bathroom, haka ta dinga coughing har tana fitar da jini, da kyar ta iya wanke fuskar ta tana sauk’e numfashi sannan ta dawo d’aki ta kwanta kan gado ga zazzab’i da take ji…. Tun kafin Habeeb ya k’arisa shiga school d’in Boboh ya hango shi da gudu ya nufo inda motar take yana tsalle “Daddy! Daddy! Daddy! Habeeb na parking ya fito yana dariya “Daddys boy!” yana fad’in haka ya d’aga Boboh sama yana dariya “Shauk’e ni Daddy shauk’e ni!” Bud’e mota Habeeb yayi ya saka Boboh a ciki ya d’aura mishi belt sannan ya zaga ya shiga ya ja motar, tun da ya d’au hanyar gida suke bin shi, sedai bai ankare ba ya ji tamkar a mafarki motar tayi juyin k’osai, ihu Boboh ya sa yana kuka da kyar Habeeb ya iya bud’e ido yana kallon yanda d’an nashi ke struggling kafin kace me mutane sun taru a wajen wuta ya kama motar, wayar Shi ya hango da kyar ya janyo ta da yatsun sa biyu yayi dialling numbar Suraj, ringing biyu kawai Suraj ya d’aga wayar, jin yanayin muryar Habeeb ma kawai ya bawa Suraj alama cewa d’an uwan shi ya shiga matsala, da Sauri ya mik’e daga gefen gadon Ameer yace “HABEEB!!” “Suraj! Please save Boboh we had an accident! Muna kusa da gida just hurry!!” Da gudu Suraj ya fice ba tare da ya saurari tambayar da Ameer ke masa ba, jikin shi har rawa yake don motar ma gani yake tamkar ba gudu take ba, yana hawaye ya ma kasa tsaida natsuwar shi waje guda. Tari Boboh yake saboda hayak’in da ya turnuk’e Habeeb kam ko motsi ma baya yi kawai ya zuba wa d’an nashi ido Ko gama kashe motar Suraj bai yi ba da ya hango taron jama’a da gudu ya kutsa ta cikin su ya dubi yanda motar ke ci da wuta, kafin kace me suma jama’a sun ja da baya, police, ambulace fire sevice duk sun hallara anyi anyi Suraj ya matsa baya ya k’i se ma fisge jikin shi yayi ya nufi jikin motar, durk’usa wa yayi yana kallon cikin motar glass d’in a d’an sauk’e don haka ya zira hannun shi cikin motar yayi ta kokawan bud’e wa, police na jan shi yana fisge wa at last yayi nasarar bud’e k’ofar saboda force da ya bata har hannun shi yana jini, belt d’in jikin Boboh ya bud’e ya janyo shi waje, ganin haka ya sa rescue team suka nufo shi suka amshe Boboh sannan Suraj ya kutsa kai cikin motar yana k’ok’arin janyo Habeeb shi kanshi smoke d’in saida ya shak’e shi ya dinga tari, saida mutane suka sa hannu tukunna ya iya janyo Habeeb, da gudu aka saka su a ambulance suka kama hanyar asibiti, sauran kuma ya rage wa fire service su kashe wutan dake ci a motar. A gigice Suraj ya shiga motar sa ya bi bayan ambulance d’in zuwa asibitin kawai kuka yake tabbas ya san Sa’eed ne yayi hakan, inspector Victor was right! Sa’eed yayi shiru ne don ya ga yawan securities around us, yanzu da aka janye su he attacked Habeeb! Damn it! This is all my fault! How am i going to face khadijah in wani abu ya faru da d’aya daga cikin su? SA’EED! fad’an ka da ni ne! Why are you hurting others? Why?” Luckily Boboh babu abunda ya same shi sedai hayak’in da ya shak’a ya so ya illata shi, amma ko kwarzane babu a jikin shi, Habeeb kuwa ya d’an samu sprain a k’afa se yankan da glass ya mishi a hannu, sedai likita ya buk’aci su k’ara atleast two hours ko za’a gano wani abun. Ko da lokaci yayi Doctor ya sallame su sannan yayi recommending maganin da Boboh zai sha saboda yanda yake numfashi har lokacin ba daidai bane due to the smoke. “Suraj………what do you think will happen da ace baka iso ba on time? Would my Son still be alright? Suraj ban san yanda zan fara gode maka ba… Ka sa rayuwar ka a hatsari to save both of us, i can’t thank you enough, i will always remember this day……” Bai k’arasa maganar ba Suraj ya dafa kafad’ar shi yace “miye kake fad’a haka Habeeb? Kana sani naji tamkar we are not brothers, abunda na yi ban yi don kayi min godiya ba i did it for my brother, i will still do it ko da sau d’ari ne ko dubu ko ma fiye da hakan” Murmush Habeeb yayi yace “Suraj kana tunanin Inspector Victors idea na janye securities zai yi aiki kuwa?” Shiru Suraj yayi bai ce komai ba har suka isa gida saida yayi parking yace “Victor bai janye securities ba, suna wancan gidan, kuma suna monitoring komai just relax mu shiga ciki you need some rest.” Boboh ya d’auka suka shiga cikin gida Habeeb na biye da su yana d’ingisa wa da kyar…… Da gudu khadijah ta nufo su tamkar wanda ta haukace, bata tsaya ta saurara musu ba wuf ta amshe Boboh daga hannun Suraj shima se lokacin ya fashe da kuka “Mommy……Daddy ya ji ciwo” Se lokacin ta dubi Habeeb daga sama har k’asa tace “Habeeb……you!….” kasa k’arasa maganar tayi tana kuka Suraj yace “Khadija calm down please, just pull yourself together i can understand how you feel and……”+ “And what? Huh? And what Suraj? I don’t believe you can feel the pain inside me, you understand nothing! And you will never understand because you have nothing to loose!” D’if kake ji wajen yayi shiru kowa na mamakin kalaman da suka fito daga bakin Khadija musamman ma Habeeb da ya kasa furta ko da kalma guda ya saki baki Share hawayen ta tayi ta cigaba da cewa “Duk wannan saboda mutum d’aya tak? And that too a woman! I understand you have a past with her and but that was seven years back! Why do we have to pay for her mistakes?……. For years muna zaune cikin farinciki babu fargaba amma tunda ta dawo rayuwar ka abubuwa suke faruwa, first it was Ameer and now Habeeb! Harta innocent child ma basu ragar wa ba! Duk kuma because of that good for nothing woman Laylah! A fusace Habeeb ya daka mata tsawa “KHADEEJAH!!!….” Kallon sa tayi ido cikin ido tace “What?? Did i say something wrong? Habeeb ka kuwa san yanda naji a lokacin da na fuskanci Tv knowing that it might be the end for My beloved Son and Husband? I was freaking shocked to the extend that…….. Ka san me Habeeb? I don’t care how anybody feels but when it comes to you and my son bazan ragar wa kowa ba!.. Idan nace kowa kuma ina nufin ko da Suraj ne”. Tana kai nan ta rungume Boboh ta nufi hanyar d’akin su , Kasa tsayuwa Habeeb yayi tsabar yanda jikin shi yayi sanyi ya d’ago yana kallon Suraj da jajayen idanuwan shi yace “I’m Sorry Suraj.” “No Habeeb it’s ok, wollah ba komai na fahimci halin da take ciki, i’m sure ba da niyya tayi hakan ba, ko da nine in her place zanyi hakan koma fiye da hakan so let it go, and please kar ka mata magana she was just shocked, ka kula da kan ka…. Ni zan shiga ciki” Suraj ya shiga Meenah de ta tsaya tayi jugum da ita Allah ma yasa su Ummi suna wajen Ameer da abun bazai k’are da dad’in rai ba mik’e wa Habeeb yayi rai a b’ace ya fice daga falon ya nufi garden nan ya zauna yayi shiru. Ko da su Ummi suka shigo ma sosai sun yi noticing something different sedai babu wanda ya yi yunk’urin sanar da su abunda ke faruwa. Haka kuma babu wani wanda ya nemi abun ci don ko dinner ba’a yi ba, ummi tayi zaton saboda shock d’in accident d’in ne don haka bata k’ara tambayar su ba itama……….. Har kusan eleven Habeeb bai shigo ba tun tana zaune har ta gaji ta mik’e tsaye tana lek’a window, daidai lokacin ya bud’e k’ofa a zaton shi ta yi barci ma sai yaga akasin hakan. Da sauri ta tare shi tana fad’in “I’m Sorry…. Please forgive me Habeeby, ban san dalilin da ya sa na tafka kuskuren nan ba, i’m sure i have hurt you alot , but at that time i could’nt think straight i was worried about you and Boboh” ta k’arashe maganar da kuka. Sosai ta bashi tausayi sai ya kasa jure wa kukan nata, hannu ya sa ya fisgo ta jikin shi ya rungume “Shush….. Ya isa haka, let it go. Naji dad’i cewa kin gane kuskuren ki wannan ma kad’ai ya ishe ni, Na tabbata Suraj bai kwanta ba so let’s go to him, you have to apologise about what you did saboda ni bani kika yi wa laifi ba na tabbata Suraj was more hurt than i am”. Dim light ne a falon Suraj na zaune bisa kujera ya kifa fuska a tafin hannuwan shi yana tunano maganganun Khadeejah. Ajiyar zuciya Habeeb yayi sannan ya k’arisa gaban shi ya tsaya, hannu ya sa ya dafa shi yana mai k’iran sunan sa “Suraj”.. Da sauri ya d’ago ya aza idanuwan shi kan fuskar Habeeb yace “Hey bro! Na zaci har ka kwanta ai”. Kai Habeeb ya girgiza da murmushi yace “Oh oh.. Ban kwanta ba tukunna, we have come to talk to you” ya k’arashe maganar yana kallon Khadijah da ta sunnar da kai tana kwalla “WE??”. Suraj ya tambaya don shi bai ma lura tana wajen ba. Kai Habeeb ya kad’a yace ni da Khadijah ne”. Da sauri Suraj ya mik’e yana maida buttons d’in rigar shi yace “What’s the matter bro? Me zai hana muyi maganar gobe in Allah ya yarda? Kai kanka ba isasshen lafiya gareka ba and……” Kukan Khadijah yasa Suraj ya dubi Habeeb da suspicion yace “What now? Habeeb me kayi mata? Me ya saka ki kuka, tell me idan yayi miki wani abun!” Kai ta girgiza tsabar kuka da kyar ta ce “I am SORRY, i know i have hurt you a lot d’azun i was shocked and scared please forgive me Ya Suraj”. Lumshe idanun sa yayi tsabar yanda yaji baya son kukan nata. Ruwa ya d’auko mai sanyi a fridge ya zuba a cup ya mik’a mata yace “karb’a ki sha and please stop crying, baki min laifi ba ko kad’an i understand yanda kike ji a lokacin because na san yanda zafin rabuwa da masoyi yake duk abunda kika yi babu d’aya da yayi tasiri a raina because i believe ba haka kike ba so just relax and forget it. Sannan it’s already past eleven, ya kamata ki kwanta especially kai Habeeb you are stressing yourself” Kai Habeeb ya jinjina yace “Gud night bro ” “Gud nyt” Suraj ya maida masa da Murmushi, khadijah ta kasa motsa wa Suraj ya dubeta yace “Anything else?” kai ta girgiza masa sannan ta bi bayan Habeeb suka shige ciki. Ajiyar zuci Suraj yayi sannan ya d’auki wayar sa ya nufi d’aki already Meenah tayi barci don haka ya nemi waje ya kwanta shima yana ta sak’e sak’e har yayi barci…….. ***** ****** ****** Washegari Da Safe……. A fusace ya fito rik’e da wani farin envelope ya nufi d’akin Laylah, bai wani tsaya b’ata lokaci ba ya kutsa kai ciki yana ta huci, daidai lokacin ta fito daga wanka kenan, sosai gaban ta ya fad’i don tasan a yanayin da ta ganshi kam tabbas kashin ta ya bushe jikin ta ya fara b’ari har tana had’iye miyau tsabagen tsoro. “What’s this?” ya wurga envelope d’in a fuskar ta, a hankali ta sunkuya ta d’auka jiki na rawa ta bud’e, result na pregnancy test ne a ciki nan da nan ta zaro ido tace “Muhseen please don’t hurt this baby! I promise duk abunda kace zan yi amma ka barni in haife wannan, baka tsoron Allah ne? Please Muhseen don’t …..” Har kamar zai masge ta sai kuma ya fasa ya tsaya yana kallon ta , ita kuwa don tsabar tsorita har ta kai k’asa ta dunk’ule a bango tana kuka se da taji takun k’afar sa ta d’ago taga har ma ya fice daga d’akin. Wani dunk’ulallen kuka ne ya zo mata nan kuwa ta kwanta tana rerawa har ta gaji ta tashi jiki babu kwari ta janyo wata yar riga ta saka T-shirt ce har ta wuce cinya haka ta kwanta bisa gado tana kuka ko tunanin breakfast bata yi ba. Gaban mirror yake tsaye yana saka buttons na shirt nashi amma daga gani ka san ba a hayyacin sa yake ba, wayar shi ya d’auka ya nufi d’akin Laylah, tun daga k’ofa yake k’are mata kallo har ya iso bakin gadon. Zama yayi gefen ta ya sa hannu yana gyara mata gashin ta da ya sauk’o zuwa fuska. Daman tun da taji shigowar sa ta rufe idanuwan ta tamkar mai barci amma tana jin duk abunda yake yi. Da sauri ya mik’e ya fita ita kuma sai lokacin ta bud’e ido tana kallon k’ofar tana mamakin abunda ya aikata yanzun nan, “wanne sabon game d’in kuma yake playing this time around? Tana juya wa gefen ta sai taga babban box ajiye da note a saman “Ki shirya anjima zamu fita”. Bud’e Box d’in tayi taga kaya ne ciki, designer doguwar riga royal blue ya sha stone work ga accessories masu ubansun tsada, tab’e baki tayi ta ture gefe ta ma fice daga d’akin……. Yana fita k’iran S’aeed ya shigo “Kar ka damu leave everything to me, in dai zaka yi keeping promise ka kyale min K’anwa ta i promise to bring Laylah to you! Its a deal!” Yana kai nan ya kashe wayar ya shiga motar sa ya ja yana murmushi………..