IN SO YAKI NE CHAPTER 18

IN SO YAKI NE CHAPTER 18

 

  Gari bai gama wayewa ba ya kai Dad airport don dama chan ya shirya zai wuce Adamawa (Belel). Bai tafi ba har saida plane d’in yayi take-off. Tuki yake amma hankalin sa duk ya tattara ya koma ga tunanin kalaman Dad “My son…… Whatever decision you make, what ever the outcome might be i will always be there for you! Na yi missing opportunities da dama na nuna maka soyayya irin na uba. I want to make it up to you so badly, your life has been miserable over the past seven and half years saboda haka ina son komai ya koma tamkar yanda yake a shekarun baya….. I am talking about Laylah!! She owes me alot, i somehow feel like saboda ni ne kuka shiga k’uncin rayuwa kai da ita. But deep down na san bazan taɓa samun d’iya kamar ta ba, she is extraordinary, soyayyar da ta nuna wa mahaifiyar ka Razia lokacin tana raye…….that bond between them made me love her even more, ina so ku manta da abubuwan da suka faru a baya , settle down and talk, you love her and I’m sure she loves you more than anyone can imagine. She has gone through so many hardships, take her back as your Wife! Ko babu komai do it to secure Tasleem’s future, I Know it’s not easy with Meenah around……but na tabbata idan har Meenah tana da hankali she will understand you and your love….. And if she fails to do so, then she doesn’t deserve an explanation. Ka wahala sosai a kan Laylah! Enough now! Kada ka bari wannan damar ta kufce maka.” Tamkar zararre haka yake ta washe hak’ora har ya kusa loosing control d’in motar. Lokacin da ya isa gida har Habeeb yayi shirin fita yana tsaye jikin motar sa yana magana da Khadijah, driver na tsaye yana jiran su Tasleem su fito domin an yi resuming school, tare da Mubeenah suka fito tsaf cikin complete uniform, daga ganin Suraj kuwa suka dinga rigima wai shi zai kai su school, ranar he’s in a good mood da murmushi ya buɗe musu k’ofar mota suka shiga shima ya koma ciki har ya kunna motar Habeeb ya lek’o kanshi ta window kasancewar glass d’in sauk’e yake, da sauri Suraj ya d’ago kanshi still smiling bai ce komai ba. Kai Habeeb ya girgiza yace “Ka san de akwai ayyuka da yawa ko? Kuma shine zaka tsaya kai yara school??” Tab’e baki Suraj yayi yace “Relaaax Bro. ….. Take a chill pill! Jiya da na fita ai office naje, I’ve completed all the important paper works,abunda ya rage qalilan ne cikin awa ɗaya ma za’a iya k’arasa wa so take your time in ma baka gama sallamar Sister in-law ba go back and don’t be a dull husband… Romance! Habeeb Romance!!! Dariya ce ta kufce wa Habeeb ya kai ma Suraj punch a kafad’a yace “Have you gone mad? Kids are here what are you talking about?? Infact what sort of a Dad are you??” Dariya Suraj yayi bai ce komai ba ya sake tada motar sannan yace “matsa min a jikin mota kar ka sa yarana su yi latti or else in fisge ka da motar yanzun nan”. D’aga wa Habeeb yayi yace “Allah ya kiyaye hanya.” “Ameen” Suraj ya amsa a tak’aice ya ja motar suka tafi….. Ajiyar zuci Habeeb yayi kafin ya juya ya dubi Khadijah dake kusa da motar sa, suna haɗa ido yayi winking idon shi yana k’arasa wa daf da ita “Hey beautiful…………. I was thinking maybe we should spend some quality time together.. just the two of us aloooone and……..” Murmushi Khadija tayi sannan tayi wrapping hannuwan ta around his neck tace “Someone sounds so romantic all of a sudden as if ba kaine kake rushing d’azu ba infact saboda kar kayi latti You even forget to give me a kiss remember??? Why change your mind all of a sudden? ” Bai jira ta shak’i numfashi ba ya haɗe ta da motar ta ya fara sumbata tuni ta fara maida masa feedback. Hannu yasa ya buɗe k’ofar motar Ya ɗan janye jikin sa yace “Get in the car…” “Ina kuma zamu je?” Ta tambaya tana sauk’e numfashi Idanuwan sa cikin nata da murmushi yace “Somewhere quiet and romantic, somewhere i will devour you entirely my baby”. Shiga tayi tana murmushi ta bishi da kallo har ya zagayo ya shiga motar shima sannan ta duk’ad da kai dana dariya gogan ya ja motar suka bar harabar gidan……. __________1 Ko da Suraj ya kyale Laylah ma bata fito daga d’akin ta ba yau, breakfast ma bata yi ba haka ta kwanta tana sauraron ƙaran ruwa daga bathroom ji tayi an turo k’ofa da sauri ta juya da dubi k’ofar ita kanta bata san lokacin da tayi wuf ta mik’e ba ganin Meenah tsaye riƙe da baby Razia a hannu, for full minute babu wanda ya yi magana wa ɗan uwanda sai Meenah ce tayi breaking silence d’in “Assalamu~alaikum” Da mamaki Laylah ta amsa domin kuwa abunda ya faru jiya bata manta shi ba “What is she up to this time?” Ta tambayi kanta lokacin Meenah ta k’araso ciki. STORY CONTINUES BELOW “Laylah……..na zo in baki hakuri kan abunda nayi miki jiya. I was wrong and i have hurt you alot, duk da na tabbata kin fi kowa sanin dalilin da yasa na aikata hakan, i was jealous and envious, zaman da kika yi da Suraj bai kai zaman da muka yi tare da shi ba yet you still understand him, his likes and dislikes, his hubbies, everything about him! As of me i only knew about his temper, i recently started gaining his love after 3 years and then you showed up, i was scared he will forget about me again, that’s why i did what i did, it’s not like i hate you please forgive me” ta k’arashe maganar tana kwalla. Sosai Laylah ta tausaya mata, ita kanta ta san bazata iya sharing soyayyar ta da kowa ba, it will be tough for her domin ko ba komai idan ta tuna Suraj is no longer her’s zuciyar ta kuna take mata, da sauri ta kamo hannun Meenah ta zaunar bisa gado ta durkusa a gaban ta tace *Na fahimce ki Meenah i know exactly how you feel, ni sam ban rik’e ki a zuciya ba. So let’s just bury the hatchet and move on komai ya wuce.” Miƙa mata Baby Razia tayi, Laylah ta amsa cike da murna ji take tamkar ita ta haifa it reminds her of the time Tasleem was born, da sauri ta koma bakin gado tace “She’s just like a little version of you Meenah, so cute and beautiful” Murmushi Meenah tayi bata ce komai ba coz she still feels guilty. Haka Laylah tayi ta janta da hira har ta saki jikin ta tamkar wanda suka saba dama chan. A nan Meenah ta fahimci simplicity na Laylah” “Bari na je nay wanka ina da follow-up likita ya bani appointment by ten it’s almost time” kai Laylah ta jinjina yayinda Meenah ta fice ta bar ma Laylah Baby Razia. Tests results d’in cancer nata da hand card ta fitar ta ajiye su bisa gado sannan ta shiga wanka. Har zai shiga Company ya tuna ya bar wasu papers a gida don haka ya juya akalar motar sa ya koma gida. Ko da ya shigo gidan shiru kamar babu kowa se sapna da ke barci ta nutse cikin kujera kamar bata wajen. Staircase ya nufa zuwa d’aki da sauri… Takardun da ya gani bisa gado ya fara dubawa to his surprise se yaga duk tests ne ɗauke da sunan Meenah, kusan guda huɗu kuma duk a kan abu ɗaya (Cancer) har ma da wasu suggestions daga different neurosurgeons ya dai duba yaga sunan ta ne ya kuma sake karanta wa a karo na biyu he couldn’t believe his eyes! Ya san how dangerous brain cancer is bai gaskata abunda ya gani ba ya yi deciding se ya tambayi likitan tukunna bazai nuna wa Laylah cewa ya san komai ba. Motsin ta da yaji tana ƙoƙarin fito wa yasa yayi saurin maida papers d’in inda ta ajiye kamar bai gani ba ya buɗe drawer yana duba takardun da ya zo nema. A jikin ta taji something is not right amma tayi shiru da sauri ta kwashe tests d’in ta saka a handbag d’in ta sannan ta nufi wardrobe ta ciro kayan da zata saka “Are you going somewhere??” Ya tambaye ta bayan ya ɗauko documents ɗin. Kai ta jinjina masa domin bata yi tsammanin zai kula ta bama sannan tace “follow-up zan je” Ya ɗan yi jinkiri sannan yace ina Baby”. “Tana wajen Laylah” ta amsa shi a takaice. Ji yayi kamar ba daidai yaji maganar ba musanman da ya tuna abunda ya faru jiya amma sai ya tab’e baki ya juya zai fita. Da sauri ta kamo hannun shi ya juyo yana kallon ta bai ce komai ba. “I’m sorry Suraj, jiya ban san me ya shiga kaina ba na aikata ma Laylah…….. Anyways! We have sorted everything out with Laylah, we are now on good terms. I know i have also hurt you so please forgive me Suraj”. Bai san me yasa ba haka kawai yaji daɗin kalaman da tayi, janyo ta yayi jikinsa yayi hugging yana shafa bayan ta a hankali “I’m glad to hear that………..and thank you” A ranta tace “wow……by apologizing to Meenah i got a warm hug, how about being kind to her?? In shaa Allah i will love Laylah even More Suraj if that’s all i have to do to gain your love and trust”. Shi kuma cikin ranshi waɗannan tests da ya karanta ne ke damun shi, idan Meenah tana da brain cancer why didn’t she bother to tell me? Me yasa ban tab’a ganin ta so weak ba? Ko de mistake ne? Or is it because i didn’t give her full attention? Is it because she feels insecure around me? Ya ilahyy…….. I need answers.. STORY CONTINUES BELOW Janye jikin ta tayi a hankali tace “tunanin me kake yi? Zan yi lattin zuwa asibiti bari in shirya…….. Laylah zata raka ni.” Ta juya ta cigaba da sa kayan ta. Da kyar Muryar sa ke fita yace “Ina jiran ku a mota zan kai ku, besides nima ina da abunda zan yi a chan asibitin” kai ta jinjina shi kuma ya fice da sauri ya koma cikin motar ya zauna zaman jira, basufi Seven minutes ba suka fito Laylah na biye da Meenah ɗauke da Baby Razia, ganin fuskar ta kaɗai ma yasa yaji sanyi a ransa nan take ya saki murmushi da bai yi shiri ba ya tada motar, suna shiga ya dau hanyar asibitin, sau goma in Laylah zata d’ago kai sai sun haɗa ido da Suraj, tana mamakin yanda yake kasa controlling emotions d’in sa when it comes to her. Ita de Meenah ta kwanta kwanta jikin kujerar ta lumshe ido tana sauraron ƙaran iskar dake shigo wa motar kasancewar gilashin wajen ta a ɗan buɗe yake…… Suna wucewa wajen likitan da ya bata appointment Suraj ya fita direct ya nufi office d’in Aunty fatima, da sallamar sa ya shiga ta amsa da mamakin ganin sa sedai idin yanayin kallon da yake mata yasa ta shakku don haka ta bashi wajen zama “lafiya kuwa na ganka haka? Is Meenah alright?” What happened to Meenah??” Tun daga nan Suraj ya tabbatar abunda ya gani ba k’arya bane tsabar b’acin rai bai san lokacin da ya doki table ɗin Aunty Fatima ba yace “kina tsoro ne ko ciwon ta ya tashi? Are you scared?? For how long have you two been hiding such important issue from me! For God’s sake i am her husband! Does this Meenah I don’t deserve to share in Meenah s pain??? She has been suffering from cancer and you taught it’s best to hide it from her own husband! What kind of an Aunt are you! You are so heartless! ” Da kwalla ta ce “No Suraj it’s not my fault…… I ……i really wanted to tell you about this tun farko but Meenah made me promised her that i will never tell you, she said she doesn’t want your pity she only wants you to love her sincerely not out of pity. Trust me Suraj i know you are hurt but please calm down idan Meenah ta ganka haka she will never forgive me”. Bai kula ta ba tsabar takaici ya juya ya fice daga office din duk komai ya chakud’e masa. Zaune ya iske Laylah inda ya barsu yace “ina Meenah?” Da yatsa tayi nuni da wani consulting room bai ma jira ba ya nufi inda k’ofar take ya buɗe a hankali “Doctor tell me………. How much time do i have?? I’m dying right?? It’s worst isn’t it?” Likitan ya fara mata kame kame ta haɗe hannuwan ta biyu tace “Doctor please……just tell me i will be fine” Doctor ya ɗan gyara zama yace because of the medications we put you on you have been alright for years and also because of the pain killers, but now you are experiencing hair lost, kin ce sometimes bakya gani sosai at this stage i can only say kina da not more than five months, akwai maganin da zan baki make sure not to skip a day, sannan please ki sake duba maganar surgery d’in nan its too risky chances na success are very low ” Kai ta jinjina ta mik’e “thank you doctor” sannan ta juya zata fita da sauri Suraj ya maida k’ofa ya rufe jikin sa har karkarwa yake yi ya kasa tsayar da hawayen shi ya yi saurin fice wa ya bar wajen Laylah sosai ta tsorita da yanayin shi don haka ta bi bayan shi da sauri. “Suraj are you alright? What happened? Me yasa kake kuka??” Kafad’un ta ya riƙe yace “How can life be so strange? Laylah I’ve hurt Meenah alot not knowing that she’s already in pain! I can’t forgive myself for what i did Laylah” Ita de bata fahimta ba sai ta sake tambaya”what is it Suraj why do you look so broken? “Meenah is suffering from Cancer!…. she’s got brain cancer and she doesn’t even have much to live Laylah and there is no other alternative doctor said there’s a lot of risk if they were to conduct the surgery! For years now she has been enduring such grave pain alone and i couldnt even see it through her……i was such a failure and i still am! I can’t forgive myself Laylah I can’t!!! But please do me this favor ….. Meenah bata san na sani ba bazata ji daɗi ba idan ta fahimci hakan so please let’s act normal please Laylah” Kasa maganar ma Laylah tayi da sauri ta rufe bakin ta da hannu don hana fito da kukan dake shirin fita musamman da ta hango Meenah tana tahowa. Murmushin ta take tamkar babu abunda ke damun ta shi kanshi Suraj ya rasa wani irin karfin hali ne Meenah ke displaying don ya tabbata idan da shine a gurbin ta bazai iya ba…… STORY CONTINUES BELOW __________ Tunda ya shigo ya nufi d’aki babu wanda ya sake jin motsin shi, haka ya wuni ƙwaƙwalwar sa na tariyo mishi rayuwar sa da Meenah he still can’t believe tana ɗauke da cutar cancer all this while, he still can’t believe she hid this serious issue from him for so long, “How can someone endure such pain all alone?” Ya tambayi kanshi duk da yasan bashi da wata amsa da zai bawa kansa koma wa yayi ya jingina da gado yana kunna wutar d’akin yana kashe wa sam bai yarda cewa Meenah bazata rayu ba, “There must be some other way She might live maybe i should take her abroad” Ya yi maganar a fili wannan karon Bai ankara ba yaji Muryar Meenah “Don’t waste your time Suraj….. It’s not like i haven’t been outside the country for treatment, please don’t stress yourself. Ganin cewa ka damu da ni ma is ok for me, I don’t want anything else, idan kaga na mutu lokaci na ne yayi besides ko da yau zan rasa raina i will be glad i will have no fear because my daughter has another loving mother, she has Laylah with her! Na san na yi wa Laylah Laifuka da dama but I’m sure bazata taɓa banbanta Tasleem da Baby Razia ba Suraj na zo in rok’e ka alfarma Please….” Mik’e wa yayi da sauri ya riƙe kafad’un ta yana ƙoƙarin hana hawayen sa zuba yace “Anything for you Meenah”. Ajiyar zuciya tayi sannan tace “Please Suraj before i die…..i would like to see my family completed. Ina so ka mayar da Laylah gurbin ta besides she is yours to begin with i will only be at peace when i leave my daughter in her care she is the only woman who can love Baby Razia endlessly Suraj please marry her, she is your happiness your i know you love her so don’t keep her waiting”. Kai ya girgiza yace ” Meenah…… I know i love her but right now your health is more important the marriage can wait na tabbata of all women Laylah will understand my decision.” Fisge jikin ta Meenah tayi ta haɗe rai “Me yasa bazaka fahimta ba?! There’s nothing you can do about my sickness…… it’s terminal ko da an yi successful surgery babu tabbacin zan dawo normal, besides chances of success are very low! No matter how no matter what i am going to die! I only ask you a favor for the first time in three and half years and you are not giving it to me kar ka sake min magana in de har ba…….” Bakin ta ya rufe da hannun shi yace “fine! I’ll do it….. Please don’t stress yourself i will marry Laylah zan yi duk abinda kika ce” Rungume shi tayi tana dariya kafin ta janye tace “it’s a promise! Now let’s go talk to Laylah na san cewa she won’t deny it” ta ja hannun shi suka fita daga d’akin bashi da zaɓi illa ya bi yanda tace coz baya son ranta ya ɓaci duk da cewa a yanzu duk wani so da zai nuna wa wani bai kai kwatankwacin son da yake ma Laylah ba kuma bai yi tsammanin akwai wanda zai so kamar ta ba………. __________ Kwance suka iske ta idanuwa a lumshe, sanyin Aircon da k’amshi daddad’an turare kawai ke tashi ko mayafi babu a kanta gashin ta ya rufe fukar ta daga gefe ɗaya daga gani kasan ba barci take ba domin rabin ta a ƙasa yake saman jikin ta ne bisa gadon tayi rigingine. A hankali ta k’araso inda Laylah ke kwance tayi nisa cikin tunanin lamarin Meenah ita kanta she couldn’t believe abuda Suraj ya fad’a da murmushin ta tace “Assalamu-alayki…….Barka da hutawa” Kamar wanda aka watsa wa ruwa haka ta yi firgigit ta tashi zaune tana gyara gashin dake rufe mata fuska bata ma lura da Suraj dake tsaye ba yana kallon yanda ta rikice “she looks cute acting this way” ya fad’a a ranshi kafin yayi saurin kawar da murmushin dake bisa labb’an sa ya gyara tsayuwar sa yana kallon su “Sorry Laylah……nayi zaton ba barci kike yi ba coz babu wanda zai iya yin barci yanda kike kwancen nan, hope am not disturbing you?” Murmushi Laylah tayi tana girgiza kai “Not at all ba barci nake ba.” Zama tayi gefen Laylah ta riƙe hannun ta tace “Na zo in rok’e ki alfarma Laylah but first promise me you will do what ever i ask you to do no matter how hard…..” Saida Laylah ta d’an jinkirta tayi tunanin kar tace A’a kuma ciwon Meenah ya tashi don haka ta girgiza kai alamar ta yarda. Gyara zama Meenah tayi sannan tace “Ina so ki auri Suraj…..” Wani blast Laylah ta ji a K’irjin ta da sauri ta wafce hannun ta sannan ta mik’e “What??? Ban fahimta ba!…” Mik’e wa Meenah ma tayi ta ɗan saki murmushi tace “Na san kin fahimci me na faɗa i want you two to settle down, Suraj loves you and i know how much he loves you! Saboda ni kada ki tauye hakkin zuciyar ki, ni da kaina nake rokon ki babu wanda ya sa ni dole i’m just doing what you couldn’t do Laylah a duk duniyan nan ke ce kaɗai macen da zan iya damka wa tarbiyyar Baby Razia ke kad’ai ce zaki riƙe ta tamkar uwa infact ke ce zaki maye mata gurbi na ko da bana raye.” Laylah ta ja da baya tana girgiza kai tace “No Meenah! I……i just can’t!!. Maganar Baby Razia Kuma in Allah ya yarda you will be with her…..” Bata gama maganar ba Laylah ta katse ta “You promised me Laylah that idan na roke ki koma miye baza ki k’i ba so don’t go back on your words please” Laylah ta girgiza kai tace “I know nayi miki alkawari but this is too much ki rok’e ni koma miye amma banda wannan Please Meenah Please” A fusace Meenah ta juya ta dubi Suraj sannan tace “What’s wrong with the two of you!!!! If I don’t have a problem with the two of you getting married then why do you have problem??! Kar ku ƙara min magana a gidan nan unless you have come to your senses!” Bata jira me zasu ce ba ta nufi k’ofa zata fita nan take ta ji kanta ya sara, ta fara gani dishi dishi bata ma san ina take ba ita de ta ji an rik’e ta kafin ta kai k’asa amma daga nan bata san me ke faruwa ba………… Meenah!! Meenah!!……. Please open your eyes! Suraj what is happening to her? Do something!!” A rikice Laylah ke maganar Suraj bai bi ta kanta ba ya d’ago Meenah ya aza bisa gado sannan ya dubi Laylah yace “Relaaax she’ll be fine quickly go get my phone i think na barshi a d’aki na hurry!” Bata jima ba ta dawo riƙe da wayar Suraj ta miƙa masa har zai k’ira likita yaji an rik’e hannun sa da sauri ya juya ya kalli Meenah dake murmushi tana ƙoƙarin zama “Sooo much care… So much concern! I do not want all of it idan har baza ku cika min alkawari ba”+ “Meenah what are you saying?? Baki da lafiya ki bari na k’ira doctor please” Suraj ya fad’a yana haɗe hannuwan shi waje ɗaya” Kai ta girgiza tace “NO Suraj …. In da zan mutu sedai na mutu in har bazaku amince da magana ta ba I don’t need your concern and i won’t let any doctor attend to me” Tana gama rufe baki taji kanta ya sara bata san lokacin da ta saki ƙara ba cikin firgici both Laylah da Suraj suka haɗe baki wajen faɗin “Fine! We will get married!” Da sauri Suraj ya kalli Laylah sannan ya jinjina kai ya maida duban shi ga Meenah yace “I will marry her, i will do whatever you want i promise”. Hugging d’in shi tayi tace “thanks a lot Suraj” ta sake shi sannan ta dubi Laylah tace “Yanzu zaka iya k’iran doctor ko ma a ina yake besides we have a wedding to prepare and i have to be healthy right?” Murmushi suka yi kawai Suraj ya k’ira doctor thankfully babu matsala stress ne kawai she needs a lot of rest, saboda haka ta sha magunguna ta kwanta…… Dad da yaji daɗin labarin da ya samu game da Suraj da Laylah ya kuma jinjina wa Meenah saidai lamarin rashin lafiyar ta babu wanda ya sani se Suraj da Laylah se daga bisani Aunty Fatima ta k’ira Meenah ta sanar da ita yanda suka yi da Suraj a asibiti “I’m sorry Meenah but Suraj ya riga ya gama kure ni at that time to the extent that i had no choice but to tell him the truth please forgive me my dear”. Kashe wayar Meenah tayi jiki a sanyaye ta nufi d’akin Suraj baya nan don haka ta sauk’o zuwa living room, ko ina duhu ne don wutan a kashe yake gashi ko ina yayi shiru I can feel your presence Suraj….. I know you are here kuma na tabbata kana ji na. Tun da safe i wondered why behavior naka ya sauya, you were quite and looked disturbed nayi zaton maybe saboda maganar aurenka da Laylah ne, ban yi zaton cewa akwai wani abu daban a ranka ba wanda ya hana ka sukuni…. Suraj i know it’s hard and i know exactly how you feel Aunty fatima just called me, ta sanar da ni duk yanda kuka yi Suraj i.,……..” Bata k’arashe maganar ba Suraj ya katse ta “Me yasa??.” Tambayar da yayi ne yasa ta gano inda yake da sauri ta juya gefen ta, daidai lokacin ya kunna switch ɗin wuta duhun ya washe. A fusace ya taso ya kama kafad’un ta yana jijjiga ta “Me kika ɗauke ni? Heartless? How could you not tell me? I know we had our ups and downs but that doesn’t mean you should hide such thing from me! Tsawon lokacin nan you are sick, and you knew about it but you choose to hide the truth from me! How could you endure this pain alone? “Suraj I’m sorry ban b’oye maka don don baka isa ka sani ba, nayi haka ne kawai don ba tausayin ka nake buƙata ba, i need your love and I’m pretty sure idan har ka san abunda ke damu na you will only pitty me I don’t want that at all Suraj ban damu ba ko da yau zan mutu because i now know that i have a special place in your heart…… That’s enough for me” Suraj bai san lokacin da ya janyo ta jikinsa ba ya rungume tamkar wanda zai murkushe ta ko kuma wanda za’a kwace ta tana jin dumin hawayen sa na d’iga a bayan ta, she knows exactly how he’s feeling, she knows it’s unexpected for him but one truth is he has to embrace the truth soonest. “Wannan shine dalilin da yasa na kasa sanar da kai tun farko, bana son ganin ka karaya, idan har ka kasance a haka ni kuma yaya zan yi?”. Janye ta yayi daga jikin sa yace “There must be a solution Meenah! Watakila likitocin ba kwararru bane! I’ll speak with one friend friend of mine……. He …. He is now in Germany we can go there he’s a very professional doctor and cancer specialist who knows maybe a miracle will happen, I’ll do one thing gobe in_shaa_Allah zan yi booking mana flight okay??” Murmushi kawai Meenah tayi ta sauk’e hannuwan shi daga jikin ta sannan ta fuskance shi tace “Suraj I don’t want to hurt you in anyway but I’m afraid babu abunda zamu iya akai, don’t work yourself out besides wannan ciwon shi yayi sanadiyar da na rasa Mahaifiya ta i know exactly how it is so please I don’t need any of this buƙata kawai shine ina so ka kasance kusa da ni a koda yaushe, give me happy memories make me the happiest woman that’s all i want Suraj, don’t feel bad about it this is my destiny, and i am ready to accept it……” Hankad’a ta yayi gefe a fusace yace “you are very strong headed! I’m not asking for much just come with me to Germany…… That’s all i ask for why are you making things difficult for me? Ko kin k’i ko kin so zan yi abunda naga dama ne kawai I can’t afford to lose you Meenah!!” Ya janyo ta jikin shi yace “Idan har baki taho da ni ba bana jin zan iya yafe wa kaina because somehow i feel this is all my fault, i have hurt you alot……” Fuskar shi ta riƙe cikin tafukan hannayen ta tana cewa “Suraj look at me! Suraj……. I said look at me, ka d’ago ka dube ni!” A hankali ya d’ago idanuwan sa ya haɗa da nata wanda ko seconds hud’u bai yi ba ya sake kawar da kansa gefe yana matso hawayen da suka cika masa idanuwa “This has nothing to do with you! It’s not your fault that I am sick….. It’s my fate, there’s nothing you can do to change that! Na yarda zan bika muje Germany but only on one condition! Har sai an d’aura auren ka da Laylah” Kai Suraj ya girgiza yace “ni da nake so mu tafi gobe? Meenah aure na da Laylah se nan da one month we all agreed to it! we still have time before the wedding!” “Na sani Suraj idan haka ne why not a d’aura auren nan da sati ɗaya? In yaso se mu tafi bayan nan i just want to make sure you belong to each other pls Suraj kar kace A’a this week’s Friday will be your wedding day! Afterall kai kanka kace baka son biki mai hayaniya it will be simple and perfect only family and friends, kuma idan kace A’a then consider our trip to Germany cancelled”. Babu yanda Suraj ya iya don Meenah ta fishi sweet talks tuni ya amince in a week a d’aura auren shi da Laylah duk da cewa ita Laylah ta yi iya kokarinta na ganin ta sauya tunanin Meenah abun yaci tura don haka ta zuba mata ido kawai. By now duk cikin su babu wanda bai san rashin lafiyar Meenah ba, suna supporting d’in ta a duk inda take da buƙatar hakan kuma duk wani abu da zai tayar mata hankali suna taka tsantsan da shi, Suraj’s attitude towards Meenah have improved, he spent much time with her, he does anything she wants, kafin sati d’ayan nan ya k’are Suraj yaga yanda Meenah ke struggling da ciwon ta kuma yaga changes da yawa a attitude nata, wasu lokutan bata yarda da kowa, ji take kamar wani zai cutar da ita, wasu lokutan kuma mantuwa, wani lokacin tace bata gani sosai. As of Laylah bata iya riƙe kukan ta saboda haka take wuni a d’aki musamman ma da yanzu kulawar Baby Razia ke hannun ta idan bata d’aki toh tana garden ko kuma saman terrace…… Bayan Sallar jumma’ah aka d’aura auren Suraj da Laylah kamar yadda addini ya tsara, su Dad har ma da mai martaba were present, Dad bai iya b’oye farin cikin shi kuma Suraj ya lura da hakan “I wish your Mom is here today Suraj, she’ll be the happiest mother ever!” Murmushi kawai Suraj yayi domin shi kaɗai yasan nauyin da yake ji a zuciyar shi, bai san me ya kamata yayi ba whether to express his happiness or sadness on one side his dreams have finally come true! Rabin ranshi ta dawo gareshi, and on the other side his wife Meenah is struggling for her life every single day!!…. Shi ko reception ba’a gama ba ya fice ya bar wajen direct gida ya koma, tamkar ba kowa a gidan saida ya buɗe parlour tukunna ya ga mata wadanda kakaf cikin su babu wanda bai sani ba , bayan sun gama gasa wa ne Ya dubi Sapna yace “ina Meenah?” “Tana tare da Laylah” Ta bashi amsa a takaice, bai b’ata lokaci ba ya mik’e zuwa upstairs…… Laylah miye haka kike yi? Come on! It’s your wedding today you have to apply some make-up” Meenah ce ke maganar tana ƙoƙarin saka wa Laylah makeup yayinda Laylah ke b’oye fuskar ta daidai lokacin Suraj ya bud’e k’ofa duk suka maida hankalinsu ga k’ofar, k’araso wa yayi cikin d’akin ya tsaya ya ce “Meenah……. We need to talk Ba musu ta ajiye powder dake hannunta sannan ta bi bayan shi, suna fita d’akin shi ya nufa tana biye da shi+ “I have fulfilled my promise Meenah, now is your turn…… Nayi mana booking flight we will be leaving tomorrow morning, wannan karon bazan karb’a excuse dinki ba ko ɗaya”. “But Suraj you just got married…… atleast spend the weekend with Laylah, it’s not fair ace yau an d’aura auren ka washegari ka bar gari not fair!!….” Hararar ta yayi ba tare da yace komai ba ya juya yana cire agogon hannun shi ya haɗe fuska. Murmushi tayi ta kwantar da kanta a bayan shi tace “Sorry Mr Maleek! I’m just kidding but still you have to go and talk to Laylah about it nasan baka sanar da ita ba remember now she has equal rights as me…… So you go now and talk to her, while i star packing”. Murmushi yayi ya juyo ya ce “that’s mah gal!!” Ya fice da sauri zuwa d’akin Laylah. Duk iya kokarinta na ganin ta gimtse kukan ta abun yaci tura she didn’t know when she bursted into tears, it’s hard….. Very hard for her to believe that she will be leaving all this new love behind, her new world cikin sati ɗaya kawai Suraj turned her into the happiest woman. “I don’t want this feeling to end, with you by my side i don’t want anything else, with you by my side i forget even my pains….” Da sallamar sa ya shiga d’akin yanda ya bar ta zaune haka ya iske ta. Ta amsa sallamar ba tare da d’ago wa ba har ya k’arasa inda take zaunen. Durk’usa wa yayi gaban ta ya d’aura hannuwan shi bisa cinyoyin ta “Hey…… Are you okay?” Ya tambaye ta ganin yanda kwalla ke tsere bisa kumatun ta. Kai ta jinjina tana ƙoƙarin haɗiye kukan amma ta kasa ganin haka yasa Suraj ya koma gefen ta ya zauna sannan ya janyo ta jikinsa “Shhhhhushh……. It’s okay Laylah please stop crying i know why you are crying, haka Allah yake al’amuran shi kuma sai da ikon shi komai ke faruwa, rabuwar mu tamkar jarrabawa ce daga Ubangiji, kuma komai da ke faruwa a rayuwar mu it’s our own fate, our own destiny only Allah can decide what’s best for us, today we are united as one, after so many years i have my wife back my family! What else could i have asked for? Laylah we both have been through a lot it’s enough now!… Let’s put everything aside and be happy. Mu gode ma Allah domin non of this is possible if it is up to us….” Murmushi Laylah tayi ta jinjjiga kai tace “Alhamdulillah”. Shima murmushi yayi ya maimaita “Alhamdulillah” da ta faɗa in almost a whisper. Daga nan ne ya sanar da ita yanda suka yi da Meenah ya kuma tabbatar mata gobe zasu tafi, Laylah taji daɗin hakan domin ko ba komai the trip will bring them more closer kuma tayi fatan za’a yi nasara, “Amma what about Baby?” Laylah ta tambaya sedai kafin Suraj ya amsa mata Meenah ta shigo riƙe da Baby Razia a hannu “Baby will be staying with her Mom, Laylah” Maganar Meenah yasa Laylah ta d’ago da sauri cike da mamaki tace “Meenah…,.. yaya za’a yi ki tafi ki barta? She’s so young and…” Meenah ta katse mata maganar tace “Seriously Laylah!???… Ni da zan tafi ganin likita, da wanne zan ji? You are her Mom she’ll stay with you, besides bana son in shak’u da …….” Da sauri ta gimtse maganar ganin yanda both Suraj and Laylah suka watso mata harara tayi saurin miƙa wa Laylah Baby tace Infact daga yanzu ta dawo wajen ki, i know my princess is in good hands so i have no regrets whatsoever, na tabbata bazaki banbanta ta da Tasleem ko kuma Boboh ba, i trust you on this one so barin je in kai kayan ta zuwa d’akin ki….” Da sauri Meenah ta fita Laylah ta dubi Suraj tace “Daki na kuma? Ba nan ne d’aki na ba?” Kada kai yayi yace “Meenah has prepared another room for you, but it’s okay if you love this one you can still use it” Kai ta girgiza tace “no Suraj, Meenah da kanta ta gyara min d’akin how can i not like it? It’s okay with me…” Murmushi yayi sannan ya mik’e tsaye yana kallon ta Yanda hankalin ta ya koma ga Baby Razia, they look cute together saida ta d’ago suka haɗa ido se yai dariya ya juya ya bar d’akin itama dariyar tayi tacigaba da wasa da Baby……. Washegari……. Shida ta wuce…….. Six thirty…. Seven…… Suraj is still sleeping! wai wanda zai tafi seven ne ko farkawa bai yi ba ballantana shiryawa, a hankali Meenah ta Turo k’ofar d’akin shi, sosai yayi nisa cikin barcin sa bai ma san me duniya ke ciki ba, haɗe gira ta ɗan yi sannan ta girgiza kai tace ” He never listens…… First he left his new bride alone, gashi ya gaji sosai but yana so yayi tafiya yau, its good thing that we’ve missed the flight. Na san abunda zan yi! Just wait and see Suraj dear” Juya wa tayi ta janyo masa k’ofar ta rufe sannan ta nufi hanyar d’akin Laylah, tun kafin ta buɗe k’ofar su Tasleem suka fito da gudu suna dariya da alama wata rigimar suka shirya. Da sauri Meenah ta tare su tana dariya “Little one’s!! Me kuka yi haka kuke gudu? Are you troubling your mommy da sassafe haka? Ya naga bakwa shirin school? ” Bata gama rufe baki ba Laylah ta fito riƙe da uniform nasu a hannu tace “Good thing you caught them in ba haka ba da ban san ya zanyi ba, tun d’azu muke tsere da su a d’akin wai basa son zuwa school, da sassafen nan sun gajiyar da ni!…. Wait!! Meenah! Ya na ganki a nan? What about your flight? It’s already 7:20” Guntun dariya Meenah tayi tace “what can i say?…… Mr President har yanzu barci yake infact a very deep sleep, we’ve missed the flight but hakan ma yayi coz ina so in kai Baby hospital for her vaccination daga nan kuma akwai Magana da zamu yi da Aunty Fatima, kinga ma it’s almost 8am bari in shirya na fita, see u later amarya” Smirking Laylah tayi tana bin Meenah da kallo har ta daina kallon ta se ta girgiza kai ta janyo yaran zuwa d’aki don kammala shirya su, ta ɗauko rigar Boboh wayar ta yayi ƙara bata ma tsaya duba waye ke k’ira ba ta kara a kunne “Hello…….Salamu-alaikum…… Hello da wa nake magana? Who’s on the phone pls?” Shiru babu amsa don haka ta cire wayar daga kunnen ta tana kallon screen ɗin kafin ta mak’e kafad’a ta yi wurgi da wayar bisa gado, sai lokacin ta lura yaran sun fice da sauri ta kwashe uniform d’in ta bi bayan su da sauri don taga wulgawar su, dariyar su taji a d’akin Suraj sai ta nufi k’ofar a hankali ta lek’a taga baya kan gadon se su Boboh ne suke faman b’oyewa cikin blanket, wani sight of relief ta sauk’e sannan ta shiga d’akin tana ƙoƙarin yaye musu blanket d’in, tana yayewa kuwa to her surprise sai taga ashe yana kwance kawai ya takure ne waje ɗaya saboda shure shuren da su Tasleem suke yi. Ba shiri ta saki bargon bakin ta na k’ok’arin furta kalmar da babu sauti “Yaaa ilahyy……” A hankali ta fara ƙoƙarin ma maida masa blanket d’in, firgigit yayi ya bud’e ido ya aza kallonsa bisa fuskar ta kafin ya saki wani exquisite smile ya riƙe waist d’in ta da hannun shi ɗaya yace “Good morning baby….. I didn’t know u are so naughty. What are you trying to do? Early morning in my bedroom on my bed bayan haka kuma on top of meeee and you are lifting my blanket!” Cike da zolaya yayi maganar yana ƙoƙarin janyo blanket d’in da d’ayan hannun shi covering his broad chest” Kwace jikinta tayi daga rik’on da yayi mata tana ƙoƙarin sauk’a daga jikin shi ba tare da furta kalma ba shima bai hana ta ba yayi murmushi ya zauna yana k’are wa screen ɗin wayar sa kallo da alama time yake gani kai ya girgiza kafin ya shiga contacts yakira wata number inda yasa ayi musu booking night flight tunda sin riga sunyi missing flights ɗin. Kafin ya juya ma Laylah ta bar d’akin se su Tasleem dake ta giggling, shi har a ranshi bai san cewa yaran suna wajen ba, da kanshi ya yi dabarar shirya su, ko wanka bai yi ba ya saka su a gaba ya kaisu har school….. Ko da ta koma d’aki wannan numbar ta d’azu ta gani an yi ta k’ira har 12 missed calls kuma ko ta k’ira ba’a amsawa daga bisani ma kashe wayar tayi ta ajiye kafin ta shiga wanka………

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *