IN SO YAKI NE CHAPTER 3
Gyara zama Suraj yayi ya d’aura k’afa d’aya kan d’aya kafin yace “Yes…..? How may i help you?” Kai Sufyan ya girgiza kafin yace “Suraj…..Na tabbata Habeeb ya sanar da kai cewa akwai wata muhimmiyar magana da zamu yi na jira ka amma baka zo ba”.+ Ajiye wayar shi Suraj yayi a gefe ya koma ya jingina da kujerar sannan ya nad’e hannuwan shi a k’irjin shi ya zuba musu ido na wasu dak’ik’ai kafin yayi murmushi yace “Sufyan kana magana kamar wani k’aramin yaro……. Kai ne kake da matsala kai ya kamata ka zo inda nake ba ni zan same ka ba, kai kanka kasan that is not my way Sufyan, amma tunda yanzu ka zo, ga waje be seated se muyi maganar ai”.1 Wani Murmushin yak’e Sufyan ya saki kafin ya nemi waje ya zauna, Muhseen kuwa hannun shi har rawa yake yi tsabar takaici ya ma kasa zama a garin haka ya kwara wa Suraj champagne d’in da yake sha a jikin shi… “DAMN! Me haka ka aikata kenan? Kayi hauka ne? Are you out of your senses! Did you know how expensive this jacket is?” Suraj ya fad’a a fusace bayan ya mik’e suna fuskantar juna da Muhseen. Sufyan da sauri ya shige tsakanin su yana bawa Suraj hak’uri shi kuwa Suraj ya kasa kawar da kallon shi daga fuskar Muhseen yayi ballantana ya ja da baya. Da gudu Habeeb ya taho ya janye Suraj domin in ba Habeeb ba babu wanda zai iya controlling Suraj in ba Habeeb ba a wannan lokacin. “Suraj control yourself! We are at a party! Kazo muje bathroom kayi cleaning mess d’in nan….. Please calm down Suraj” Suraj bai sake cewa komai ba ya wafce jikin shi daga na Habeeb ya d’auki wayar sa ya fice daga gurin rai a dak’ile. Habeeb ya dubi mutanen dake tsaye kowa yayi charko charko yace “I am truly sorry about what happened, Suraj baya cikin yanayi mai dad’i amma ba haka yake ba ” Nan da nan kowa ya cigaba da harkar sa Sufyan ya dafa kafad’ar Muhseen yace “Am Sorry about that Muhseen… Suraj kenan, haka yake hot tempered, arrogant and rude, amma kasan muna buk’atar shi a wannan tafiyar saboda haka abunda ya faru yanzu kada ka kai shi ga zuci”. Kai Muhseen ya girgiza yace “No way man! Ga dukkan alamu baka san hali na ba! Ni ba mutumin da za’a wulak’anta bane a zauna lafiya, Suraj Abdoul-Maleek ya d’ebo ruwan dafa kansa, sannan wannan partnership d’in bazan yi shi ba am out! Sufyan.” Da kyar Sufyan ya shawo kan Muhseen ya amince zai tsaya suyi magana da Suraj a karo na k’arshe. “Amma kar kayi tunanin cewa zan manta abin da ya yi min a gaban wad’annan mutanen, kuma believe me se na nuna mishi matsayi na i will teach him a lesson that he will never forget!” “Look at this mess Habeeb! Dubi yanda ya min wanka da drink! Wannan ai wawanci ne! Ban san me yasa ka d’auke ni daga wajen sa ba ai da na koya mishi hankali coz ga dukkanin alamu bai da hankali!” Habeeb de bai ce qala ba har suka isa washroom a nan Suraj ya sa towel da ruwa yana goge jacket d’in nashi. “Suraj what was the need to fight over such a small matter? Please kayi hak’uri ka rabu da shi, ni kai na bana k’aunar sa infact kamar yanda ka tsane shi nima haka na tsane shi, ka ma san miye? Naji suna magana d’azu da Sufyan ga dukkan alamu wannan partnership da suke son yi da mu kawai cuta ce amma basu san naji maganar su ba, kawai kai ma kayi pretendinng komai ya wuce muga irin kwallon da zasu buga, na tabbata akwai abu a k’asa amma Suraj try and control yourself. Mu koma ciki sannan please act normal Suraj”. Kai kawai Suraj ya jinjina Habeeb ya fice ya bar shi a ciki yana kimtsa wa. A kan kujera ta Hango Tasleem zaune se zuba surutu take yi ita da waitress d’in nan, da gudu Layla ta k’arisa ta rugume ta kafin tace “Me yasa bakya jin magana Tasleem? Na fad’a miki kar ki fita daga mota infact duk abunda kike buk’ata akwai a ciki me yasa kika fita?”. “Mommy Me yasa kike kuka? Wani Uncle ne ya siya min abinci a nan, ya kula da ni sosai, mommy yunwa nake ji shiyasa na fito. Am very sorry Mommy bazan sake ba i promise”. Murmushi Layla tayi sannan tace “ya wuce, amma kar ki sake yin irin wannan, kuma ai na sha fad’a miki never to talk to a stranger! Sannan dubi rigan ki duk kin b’ata zo muje in gyara miki kafin stain d’in ya kama jiki” Layla na gama magana ta kama hannun Tasleem suka wuce……. ******* ***** ******* A tsanake Habeeb yake tafiya yana gyara rigar shi bai aune ba yaci karo da Tasleem. “Ouch! Ouch!…..” Suka furta a tare kafin ya dube ta ya durk’usa gaban ta yace “Am sooo Sorry princess,ina fatan baki ji ciwo ba?”. Kai ta girgiza tana murmushi, shima Habeeb murmushi yayi mata kafin ya bud’e baki ya sake magana yaji wata murya ta doki kunnen sa, “TASLEEM! TASLEEM” muryar da bai manta da irin sautin ta ba, haka ma taste of fulfulde bai bar kan harshen ta ba. Habeeb bai yarda da abunda kunnuwan shi ke jiye mishi ba don haka ya mik’e ya dubi inda yake jin k’iran ai kuwa abunda ya ke tunani shine yake a zahiri “LA…..Y..LL…A…H???” Habeeb ya furta tamkar mai k’ink’ina, jikin sa har b’ari yake tsabar rud’e wa. Juya wa yayi ya kalli k’ofar washroom d’in da Suraj ke ciki kafin ya sake juyo wa ya dubi Laylah wanda tuni idanuwan ta sun fara kwaranyo ruwan hawaye marasa adadi. Dukkanin su suka tuna abubuwan da suka faru shekaru bakwai da suka wuce “Habeeeb! Habeeb kai nake gani ko de mafarki nake yi?”. Kasa magana Habeeb yayi se ma had’e rai da yayi ya bi gefen ta ya wuce rai a dak’ile Da gudu Layla take bin shi “Habeeb! Habeeb…. Don Allah ka tsaya lets talk, listen to me, please ka saurare ni Habeeb……Habee….Habb…….” Durk’ushe wa tayi a k’asa tana kuka shi kuwa Habeeb ya bar ta a wajen tun tuni “Me yasa bazaka saurare ni ba? Na san ban yi daidai ba but atleast give me a chance to explain everything!”.. Da gudu Tasleem ta rungume ta, daidai lokacin Suraj ya fito daga Washroom yana waya bai ma gan su ba ya wuce cikin sauri. Muryar Suraj ne ya doki kunnen ta, babu shiri ta yi zumbur ta mik’e tamkar zautacciya, wulgawar shi kawai ta gani ai kuwa ba shiri ta saki hannun Tasleem ta ruga ta bi bayan shi. Amma kafin ta k’arisa Suraj ya b’ace a cikin taron partyn, kamar Mahaukaciya se dube dube take yi har gumi take yi tana magangan “I know it’s Him! Na san kai ne Suraj muryar ka bazata tab’a b’uya ba a gare ni ina kake? Ina ka shiga? Ya Allah ka nuna min Suraj”.. Bata ankara ba taji an dafa kafad’ar ta, da fara’arta ta juya tace “Surr…” bata k’arisa ba ganin Muhseen ne tsaye ya tamke fuska ya rik’o hannun Tasleem. “Meye haka kike yi? Kin yi hauka ne? God! Na san bazaki tab’a chanja wa ba, ki d’auki y’ar ki ku b’ace min daga nan! Before i loose my temper!!” nan Layla ta kama hannun Tasleem suka fice shi kuwa Muhseen ya bi ta da kallo kafin yayi rolling idanuwan shi ya cigaba da harkokin shi….. Meenah ce zaune a bar tana kallon fitowar Suraj tayi odan glass d’in juice ta faki idon mutanen wajen ta d’auko kwayar dake purse d’inta ta jefa guda d’aya a cikin juice d’in ta girgiza sannan ta k’ira wani waiter ta bashi tayi masa nuni da Suraj. Ko da waiter ya kai wa Suraj juice Suraj bai b’ata lokaci ba ya kafa a baki dama chan k’ishirwa yake ji. Meenah kuwa dariya tayi sannan ta mik’e ta d’auki purse d’in ta ta na kallon shi da alama jira take kwayar ta fara aiki Suraj! Good thing you are here, daman d’azu naso muyi magana ne a game da partnership da…….”+ Kafin Sufyan ya k’arisa Magana Suraj ya d’aga masa hannu, alamar ya dakata kafin ya ce “Sufyan just in case baka sani ba barin sanar da kai cewa i don’t talk business at parties, we are here for your anniversary saboda haka lets enjoy, in yaso ko ku same ni a office ko a gida but not here”… Yana kai nan ya wuce ya bar Sufyan tsaye a wajen Da kyar yake iya d’aga k’afafu, nan take ya fara gani bibbiyu, ganin haka Meenah ta saki murmushi ta nufo inda yake “Suraj what’s wrong? Me ya faru haka? Naga kamar jiri kake ji…are….you alright??” Tana maganar ne idanuwan ta kan fuskar shi, Suraj kuwa she faman lumshe idanuwa yake da alama pills d’in da ta saka masa ne ke aiki. Ba tare da kowa yayi noticing ba Meenah ta ja Suraj har zuwa inda motan su yake , saboda bai san me yake yi ba se abunda tayi da shi, direct gida ta nufa…… A chan wajen party kuwa duk k’ok’arin Laylah na ganin tayi magana da Habeeb ya ci tura saboda daga ta dumfaro inda yake, Habeeb sai ya bar wajen sam yak’i sauraron ta. Wajen su Ameer ya nufa rai a dak’ile yace “Ya kamata mu tafi it’s already late dare yayi sosai kuma gaskiya na gaji” Ameer ya mik’e yana gyara rigar shi yace “Wlhy nima haka, duk na gaji, at first kamar partin zai yi dad’i amma yanzu sam babu wani nishad’i i’m bored already. Ku tashi mu tafi don ni barci ma nike ji” Habeeb yayi murmushi ya mik’a wa Khadijah makullin mota yace mata “You drive, bazan iya tuk’i ba saboda na gaji” Ba musu ta amshi makullin daga hannun sa suka wuce gaba. Ameer ya lura akwai damuwa tattare da Habeeb don haka ya dafa kafad’ar sa yace “What now? Naga ranka a b’ace, you look quiet upset, akwai wata matsala ne? Ka fad’a min se mu shawo kan matsalar tare”. Hannun Ameer Habeeb ya rik’e kafin yace “Matsala kam akwai shi, babbar matsala ma kuwa, amma kafin na fad’a maka matsalar don Allah mu bar nan wajen, zamu yi magana a gida domin duk dak’ik’a d’aya da na k’ara yana tuna min da wasu alamura da suka faru a baya wad’anda bana so in tuna su”. Habeeb yana maganar ne idanuwan shi cikin na Laylah dake tsaye daga bayan Ameer tana hawaye musamman ma da taji kalaman da ya furta. Habeeb kuwa jan hannun Ameer yayi suka fice ba tare da ya juya ba ko da sau d’aya. Yayinda Ameer ke mamakin yanayin Habeeb a wannan lokacin. * ******* ******* ******* Tuk’i take amma idanuwan ta kan fuskar Suraj shi ma kallon nata yake yi yana lumshe idanu daga gani ka san ba a hayyacin sa yake ba. Mayar da hankalin ta tayi kan tuk’in da take yi tana maganganu ita kad’ai “Afuwan Suraj!….. Ban sani ba in daidai na yi Amma ko kad’an bazan yi nadama ba, three years! For three fucking years i was shunned by you, farin ciki kawai nake buk’ata da soyayyar ka but you are not ready to give them to me! I gradually started to become weak and now i am helpless, you left me with no option than this, Suraj ban damu ba abunda zai faru gobe but a daren yau you will surely be mine, ban damu ba da irin kallon da zaka min after tonight, na gaji da jira Suraj please forgive me!”.. Isowar ta gida bayan tayi parking mota ta fito gami da bud’e wa Suraj k’ofa, jan jiki yayi ya fito se rirrik’e ta yake yi bata ankare ba suka zube a k’asa idanuwan su cikin na juna “Laylaaah” Suraj ya furta yana murmushi ya sa hannu yana shafa fuskar ta yana Maimaita sunan Laylah, ita kuwa Meenah ba ta sunan take ba hasali ma cewa tayi “In de har zan samu kusanci da kai irin haka toh Suraj i am ready call me any name! Ka k’ira ni da sunan ko ma wacece ban damu ba all i want is your love”. Tana gama rufe baki ya fara smooching d’in ta, sun dad’e a haka kafin ya janye jikin sa daga nata ya mik’e tsaye, da kyar Meenah ta mik’e ita ma k’afafun ta duk sun mutu tamkar an buge su da katako. Dauk’ar ta yayi chak tamkar y’ar tsana ya raba ta da k’asa ba shiri ta sa hannuwan ta a wuyan shi ta rungume ya nufi cikin gida …….. Khadija tana parking suka yi gaba ita da mubeenah yayinda Habeeb ya jingina da motar Ameer kuwa ya sa shi a gaba ya nad’e hannuwa a k’irji yace “Go on! Ina sauraron ka, me yake damun ka haka naga ka sauya all of a sudden?” Ajiyar zuci Habeeb yayi yace “zan fad’a maka amma se in har kayi min alk’awari bazaka sanar da kowa ba, and i am serious Ameer real promise nake so kamin”. Ameer yayi murmushi yace “don’t worry bro, your secret is safe with me, i promise i won’t tell anyone anything”. Habeeb ya sake tambayar sa yace “Not even Suraj or my wife Khadijah nor Mubeenah”. A wannan karon Ameer ya d’an girgiza amma ya dake yace “yes! Ba zan sanar da kowa ba amma ni ka sanar da ni mana duk ka saka ni a duhu” “Ameer Yau naga LAYLAH” Ameer da bai tabbatar da sak’on da suka shigo kunnuwan sa ba , sake tambaya yayi yace “MENE? Habeeb ya sake maimaita abunda ya fad’a da farko “Naga LAYLAH yau a wajen party” Wani murmushi ne da farinciki mara misaltuwa shimfid’e a fuskar Ameer yayinda Habeeb ya dake yana kallon sa “Amma Habeeb, me yasa ranka a b’ace bayan ka gano sanadiyyar da zai dawo da farin cikin d’an uwan mu Suraj? Kamata yayi ace kana farin ciki! Isn’t that what you wanted?” ya kamata mu sanar da Suraj! He deserve to know” “NO! bazaka fad’a wa Suraj komai ba game da wannan maganar, kar ka manta kayi alk’awari,ya kamata ka rik’e alk’awarin ka, ina take lokacin da yafi kowa buk’atar ta? Ina take lokacin da yake muradin ganin ta , lokacin da yake durk’ushe a kan gwiwowin sa yana rok’on ta dama d’aya kachal k’i tayi, where was she when he tried to commit suicide not once, not twice but times without numbers, A dalilin Laylah na kusa na rasa Suraj! Ka kuwa san muhimmancin Suraj a gare ni? Sannan se yanzu da ya fara saita rayuwar shi , komai ya fara saituwa sannan kwatsam zata fad’o, me zata gaya min? Bazan bata damar ganin Suraj ba ko da sau d’aya trust me if i tell you Ameer ba cikin sauqi zan yafe wa Laylah wulak’ancin da tayi wa Suraj ba, lokacin da ya nemi yayi magana da ita ko da sau d’aya ta k’i bashi dama, in fact ita ce ta nemi saki daga wajen shi, there is no greater pain for Suraj than rabuwa da Laylah but anyways ya sadaukar da soyayyar shi domin ta. Suraj yayi mata alfarma ne ma.”…. Cikin rawar murya Ameer yace “I understand you completely Habeeb, but har na tsawon wane lokaci zamu cigaba da b’oye wa Suraj wannan lamarin? For how long will it last, whether you admit it or not Suraj was, and is still in love with Laylah! ita tamkar rayuwar shi ce, she is in his dreams, his thoughts, in his heart, infact Habeeb Laylah exit in Suraj’s heart, bugun zuciyar sa ce ita me kake tunani idan ya gano cewa mun zama tamkar gini na k’arfe tsakanin shi da Laylah ?” Habeeb ya jijjiga Ameer yace “ka farka Ameer! Wake up and face reality! Laylah barin Suraj tayi when they needed each others support! Kayi tunani me zai faru da Meenah?……..Ok! Na sani cewa Suraj bashi da wani feelings towards Meenah but what about Her? Meenah ta zauna da Suraj for three damn years! She dealt with his cruel nature, na tsawon shekara uku, ya nuna mata k’iyayya, Meenah ta ga b’acin rai iri daban daban, but ko da na dak’ik’a d’aya bata nuna gaza wa ba, bata fasa k’aunar sa ba, ta shanye hantarar sa da bak’ak’en maganganun sa, she never even complained not once! Shekaru uku ta shanye a wad’annan halayen nashi. Did you know why? Because she loves him, that is what i call true love! Duk musguna mata da Suraj yake yi Meenah bata bar side d’in shi ba, duk takura da yake mata , bata daina murmushi ba, she never complained! Kasan me yasa? Because her feelings for Suraj are real, because he is her number one priority! Because she truly loves him! And Layla?….. What did she gave Suraj in return? NOTHING! NOTHING but a total destruction , ta d’auke farincikin shi, duniyar shi a cikin shekara guda ta sauya masa rayuwa, bazan bari ta dawo ta dagula mishi alamura ba, Meenah ita ce tayi deserving soyayyar Suraj ba Laylah ba!” Habeeb yana kai nan ya fice Ameer de kawai bin shi yayi da Kallo domin duk wata kalma ta riga ta sark’e ya kasa furta wa…………… Da kyar yake taku har tuntub’e yake shi kad’ai, ganin haka yasa Meenah ta ce “Suraj ka sauk’e ni akwai duhu , wutan a kashe ne, barin kunna wuta” Matse ta yayi a jikin sa yace “Stay! I like the room this way just don’t leave me sweetie, na rasa ki na tsawon lokaci amma banda yanzu , kada ki matsa ko da taku d’aya i won’t like it” Dim light dake d’akin shi ya bawa Suraj daman ganin inda gado yake don haka ya k’arisa ya dire Meenah a kan gadon sannan yayi mata rumfa da faffad’an k’irjin shi. Rumtse idanuwan ta tayi yayinda bugun k’irjin ta ya k’ara increasing a hankali ya matso daf da ita yana smooching tuni ita ma Meenah ta fara maida martani. Before you know it course ya chanja they were enticed to the core……..+ ****** ******* ****** SHERATON ULTIMATE HOTELS Abj. Ta dad’e zaune a gefen bathtube d’aure da towel daga gani ka san ta zurfafa a tunanin da take yi “Tabbas ina ji a jiki na Suraj yana wajen wannan partin, amma me yasa Habeeb zai k’i kula ni? Ya nuna kamar bai san ni ba, i really want to meet you Suraj, akwai abubuwa da dama da nake son sanar da kai , i have a lot of questions to ask you Suraj. Ina da tambayoyin da basu da amsa se kai kanka.” Cikin zuciyar ta take wannan sak’e sak’e bata ankare ba taji ta cikin ruwa da kyar ta daidaita numfashin ta duk ta gama rud’ewa. D’ago kai tayi ta k’ura mishi na mujiya cikin ranta tace “yau kuma me nayi cikin wannan tsohon daren? In dai yana kusa toh ko gashin kaina ma a tsorace yake tsabar tsangwamar sa “. Muhseen ya nad’e hannu a k’irji yace “Me kike nufi da kika zo kika zauna a nan d’in? Ni zan yi pampering yarinyar ki tayi bacci? Am i a baby sitter or what?” Jiki na b’ari tayi yunk’urin tashi daga cikin bath d’in amma duk k’ok’arin tashin da tayi se ta zame. Tsaki Muhseen ya ja kafin ya nad’e hannun rigar sa ya d’ago ta chak ya fitar sannan ya direta yanda da kyar ta iya daidaita tsayuwar ta duk se tsiyayar ruwa towel d’in ta yake, shi kuwa ko ta kanta bai bi ba ya nufi inda shower yake ya cire kayan sa sannan ya sakar wa kansa ruwa ita ma chanja wani towel d’in tayi sannan ta fice tana goge hawaye…. ****** ****** ******* K’arfe Shida ne na safe amma zaka ce time d’in bai kai haka ba, Ruwa ake tafka wa kamar da bakin kwarya, k’aran thunder ne yayi sanadiyyar farkawan shi daga nannauyan barcin da yake yi, wayar sa ya d’auka ya duba time sannan ya mayar ya ajiye a kasalance yace “Oh God! Na makara ban ma yi sallah ba” K’ok’arin tashi yayi se da kanshi ya sara ba shiri ya dafe kan, se lokacin ne ya lura cewa ba shi kad’ai ne ba a kan gadon hakan ba k’aramin d’aga hankalin Suraj yayi ba, babu shiri ya mik’e daidai lokacin Meenah ta bud’e ido ita ma a firgice ta mik’e, yanda ta kalle shi ne yasa Suraj ya fahimci baya sanye da komai a jikin sa, zanin gado ya fisgo ya rufa jikin sa da shi har numfashin sa ya fara sauya wa tuni ya ji kamar ya had’iye rai, doguwar rigarta ta d’auka ta zira kafin ta nufo inda yake tsaye ya bata baya “Sura……Suraaj…pl….ea.se let mme explain, i didn’t mean to do this, i am sorry Sur….” Wani juyowa da yayi had’i da tsawa ya damk’e wuyan ta ya had’e da bango idanuwan sa sun isa su nuna wa Meenah b’acin ran da yake ciki a wannan lokacin “Sorry? ME KIKE NUFI DA SORRY? HUH? Tambayar ki nake yi!!!” Ita de Meenah iskar shak’a ma kusan rasa wa tayi bata da wani bakin magana se girgiza kai take hannuwanta na k’ok’arin janye hannun shi daga wuyan ta. Da hawaye a fuskar sa Suraj ya sake ta, tuni ta zube k’asa tana tari tana neman daidaita numfashin ta yayinda shi kuwa ya juya ya fice gami da banko k’ofar numfashin shi sama sama ya nufi wani d’aki dake k’arshen wani corridor, wasu numbobi ya danna k’ofar ta bud’e ciki baka iya ganin komai se duhu amma ko a jikin sa ya mik’e straight ya bud’e wata k’ofar sannan ya shiga ya rufe bai jima ba ya fito se lokacin ya kunna wutan bedroom d’in, d’aki ne mafi k’ayatuwa a cikin wannan gidan, cike da memories , ko wanne b’angare na bango yana d’auke ne da potraits na Layla, wannan d’akin shi ke d’auke da long lost memories na Suraj, d’akin ya kasance amsa ne ga duk me son sanin rayuwar Suraj a baya. Sallaya ya shimfid’a ya gabatar da sallar Asubah ya ida adduo’in sa sannan ya zauna ya zuba wa d’akin ido yana tuna past events da suka shud’e shekaru bakwai a baya, had’uwar sa da Laylah, Soyayyar su, unpleasant events da suka faru da kuma rabuwar su, mik’e wa yayi ya d’auki kwalban turare dake gaban madubi yana kallo, kasancewar Suraj namiji hakan bai hana kwalla kwaranya daga idanuwan sa ba “for seven years! Seven years, i filled this room with memories of you, i kept every single favourite things of yours with love and hope that you will one day knock at my door, Amma ko wacce rana in na farka se inga kawai mafarki nake yi, maybe lokaci yayi da zan manta da ke, it’s time i move on for good Laylah. Menene ban miki ba? Wanne hali ne ban shiga ba dalilin ki? But kamar kyafta ido kika datse soyayyar mu karaf d’aya ba tare da kin bani one chance to make things right ba. Laylah………..Laylah banbsan dalilin da yasa kika barni ba in wannan ita ce k’addarar mu then so be it! Habeeb yayi gaskiya! Kullum yakan ce min “Duk mutumin da yake k’aunar ka da gaskiya ba zai t’aba barin ka ba no matter how hard the situation is”. Tsaya wa yayi yana k’okarin tuna abun da ya faru tsakanin shi da Meenah tun daga auren su har abunda ya faru a daren jiya, karkarwa hannuwan shi ya fara kafin kace me , ya yi wurgi da kwalban turaren ya had’e da glass d’in hoton Laylah suka tarwatse haka ya dinga raruman kwalaben turarrukan dake gaban mirror yana harin hotunan Layla da su, kafin wani lokaci d’akin ya koma total mess. Ja yayi da baya ba tare da ya damu da glasses d’in da yake taka wa ba murya na rawa yace “I gave you everything! And what did i get in return? You took my heart and left me lonely! Sosai na karaya da soyayya irin naki! ” Kusa da hoton ta ya matsa Ya k’ura mata ido yace “Amma yau zan miki wannan alk’awarin Laylah! Today i close the door to the past,and open the door to the future! I will open a new chapter in my life, a gareni yanzu ke ba komai bace illa tarihi” Yana gama fad’in haka ya juya ya fice daga d’akin ya nufi hanyar living room “Ina kuke!! Zainab! Sarah! Ali! Salihu! Come here at once!! Kafin kyafta ido duk masu aikin da ya k’ira sunan su har sun jeru kowa kai a k’asa jiki na rawa “FOLLOW ME!!” Ya umarce su, babu shiri suka bi bayan shi har zuwa d’akin, snapping fingers yayi yace “Kafin na shirya na fita ina so in ga d’akin nan empty! In na ce Empty ina nufin empty, ku kwashe hotunan na kakaf ku k’ona su a backyard ko gadon dake d’akin ku karairaya ku kai main store sannan in kun gama zaku iya tafiya ku cigaba da ayyukan ku but for now! Umarni nake muku kuma bana son mistake! A slight mistake might cost you your job” Ai kafin Suraj ya gama rufe baki tuni sun hau aiki yayinda shi kuwa Suraj ya fice yana sak’e sak’e a ransa “I’ts over Laylah! It’s over!” D’akin sa ya nufa sedai a wannan lokacin Meenah bata cikin d’akin, tuna abunda yayi mata ya fara tuni ya rumtse idanuwan shi ya cije leb’e kafin ya dunk’ule hannu ya doki mirror dake d’akin ba tare da ya damu da jinin dake zuba ba “Ya ilahy……. I am sooo stupid all this while! Dubi kuskuren da na tafka! Na wahalar da baiwar Allah, na cutar da Meenah, how am i going to look into her eye’s? Na yanke shawara i will apologise to Meenah for shekarun da na b’ata na rayuwar ta ina kyarar ta, i will make things right, na fahimci cewa abunda ya faru jiya sam babu laifin Meenah! I am the one at fault! Nine mai laifin it’s because of my rude, and arrogant behaviour towards Meenah. Now i will give her all the happiness she deserves!”………….