IN SO YAKI NE CHAPTER 6
Tana jin takun shi tayi maza ta nufi wash basin, famfo ta kunna ta wanke fuskar ta tas sannan ta fito tana goge fuskar da towel, tamkar wata mara gaskiya haka take takun. Gaban mirror ta nufa ta d’auki powder ta shafa sannan ta sa kwalli hakan yasa fuskar ta d’an yi kyau kuma ta b’oye alamar kukan da ta dinga zabga wa. Se lokacin ta juyo suka had’a ido da Muhseen dake mik’e kan gado yana wani shu’umin murmushi, da sauri ta jefar da towel d’in hannun ta tana kallon shi se damk’e rigar jikin ta take kamar zata yayyaga shi, tana rau-rau da ido, tsalle yayi ya mik’e daga gadon yana takowa inda take, ganin haka yasa ta fara ja da baya har ta ci karo da dressing mirror, a d’an tsorace ta ja gefe tana baya baya aka yi sa’a ta damk’o handle d’in k’ofa sedai kafin ta yunk’ura ta bud’e k’ofar Muhseen ya chafko ta da hannuwan sa biyu ya warb’ar da ita a k’asa. Tsabar zafi saida ta saki k’ara “Wasshh Allah” kanta ya fad’a yana k’ok’arin raba ta da rigar jikin ta, tun k’arfin ta take kwace wa hakan yasa Muhseen yasa hannuwan shi ya shak’e wuyan ta “Womman! Shut the fuck up! So kike ki tara min jama’a ne? What are you thinking? Iye? Na kawo ki nan ne domin ki ci ki sha sannan ki kwanta? Is that what you think. Wannan kyaun naki yana d’aya daga cikin dalilin da yasa na auro ki, ki sani cewa you are not my type of girl, i prefer spicy hot girls, kina tare dani ne don in biya buk’atar kaina a duk lokacin da naga dama, kud’ina nake ci! Sa’ar ki d’aya ina benefiting daga kasuwancin mahaifin ki if not me zan yi da RAGOWAR WANI? Saboda haka zai fi miki ki kwanta da kai let me have what i want in ba haka ba kuma you will get hurt as usual, because kin san halina duk gardaman ki baya hana ni yin abunda naga dama a kanki so just cooperate LAYLAAAH!” Ya k’arashe maganar da k’arfi gami da fisge rigar jikin ta ya rage daga ita se bra. Ihu ta saki tana kare k’irjin ta shi kuwa ko a kwalar shi iya k’arfin shi ya danne hannuwan nata a k’asa yana sniffing k’amshin turaren dake k’irjin ta tamkar mahaukaci. “Leave me alone! You bastard!!” Kalman bastard da ta furta ne yasa Muhseen ya fusata, d’aga ta yayi ta hanyar rik’o gashin kanta sannan yasa hannu ya kaura mata marika har uku har saida bakin ta ya fashe. Hankad’a ta yayi kan gado saboda wayar sa da yaji tayi ringing sannab ya d’auki wayar ya kara a kunne “Yeah babe ki shigo ina ciki, ki k’araso ina d’aki, daman it’s already boring in here, come and cheer me up bebs. Yana k’arashe maganar ya katse wayar yana murmushi idanuwan shi kan Laylah dake kwance lamo kan gado duk jiki a sanyaye sai maida numfarfashi take duk ta jik’e da uban gumi. Cikin salo ta banko k’ofar sannan ta jingina da k’ofar tana taunar chewing gum, idanuwan ta ta sauk’e kan Laylah sannan ta saki wani shu’umin murmushi ta dubi Muhseen tace “Gaskiya baka da kyau Baby! This is too much? In kana hannu me zai hana ka k’ira ni? Am just one call away. Me zaisa ka k’are k’arfin ka a kan wannan abar… Such a pity” Da murmushin sa ya nufi k’ofar, daf da ita ya tsaya ya d’an juya ya kalli Laylah dake k’ok’arin tashi sannan yace “Come in Bebs, besides this is also your room” Rigar shi ta chafko hakan ya sa k’irjin shi da nata suka had’e har numfashin su na gauraye wa, kafin ya ankara ta shiga kissing nashi shima tuni ya fara maida martani. Kukan ma Laylah nema tayi ta rasa tsabar takaici. Cije baki tayi chan k’asan mak’oshin ta tace “ina cikin d’akin zaku aikata wannan bad’alar? I will show you! Bata k’arashe maganar ba Se ji tayi sun afka kan gado nan da nan wani abu ya tokare mata mak’ogoro ganin duk sun ma mance tana cikin d’akin. Sauk’a tayi daga gadon ta nufi wardrobe, doguwar rigar ta na material ta zira gashin kanta duk sun barbaje amma bata tsaya neman mayafi ba se huci take tamkar macijiya, glass tumbler ta hango kan nightstand ai kuwa wani shu’umin murmushi ta saki da saurin ta tad’auko tumbler d’in, daidai gadon ta tsaya. Sama ta d’aga ai kuwa tana sauk’e wa se kan matar “KWALL” kake ji tuni Muhseen ya tarkato hankalin shi waje d’aya ba shiri ya mik’e saboda ihun da matar ta saki “BEBs! Bebs! Feenah! What happened? Are you ok? Ita kuwa Feenah ko magana ta kasa se uban ihu da take shilla wa ta rik’e k’eya musamman ma da ta d’ago hannu taga jini a hannun. “Ta kashe ni Muhseen! Oohh! My head, look it’s bleeding ka fitar dani daga nan tun kafin ta k’arisa ni, ban tab’a sanin mahaukaciya ka aura ba se yau!” Tunkaro Laylah yayi a fusace ya had’a ta da wardrobe yace “Kin yi hauka ne? Dubi abunda kika aikata fa! In ta mutu fa? Ita de Laylah bata ce komai ba se murmushin k’eta da take masa, har zai kai mata duka Feenah ta sake sa ihu “Aaah! Baby ka kaini asibiti i don’t want to die like this, ai kuwa kamar zararre ya ruga ya koma wajen Feenah, rigar shi ya maida sannan ya rik’e ta da jakar ta ya jata suka fice daga flat d’in se uban rarrashi da yake mata . Laylah kuwa har k’asa ta bi su rik’e da tumblern tana fad’in “Take her anywhere you want but a gabana bazan d’auka ba, zan iya jure duk rashin imanin ka domin komai ya faru da ni nice sila amma bazan yarda kuyi fasiqanci a gaba na ba, ko yanzu ta dawo a shirye nake in tarwatsa mata kai tsinanniya kawai….. Fitan su Feenah ke da wuya suka bi stairs shi kuma Suraj ya fito daga lift, don haka suka yi sab’ani. Direct hanyar flat d’in su Muhseen d’in ya nufa a cike yake da wannan matar don haka tamkar mahaukaci haka ya dinga danna doorbell. D’ago kai tayi ta kalli hanyar k’ofan kafin tayi kwafa tace “Au! Ashe bai ishe ki ba kenan let me show you! A fusace ta nufo k’ofar rik’e da tumbler da ta rafka wa Feenah domin a tunanin ta Feenah ce ta dawo saboda yanayin bugun k’ofar ba na mai hankali bane. Tana bud’e k’ofar kuwa ido rufe cikin masifa ta d’aga tumbler ta rafka ma Suraj a kai “I told you… I do not want to see you here ever again! Who do you think you a….ar……… K’ak’are wa maganar tayi ganin cewa ba Feenah ce a k’ofar ba, tamkar mai k’ink’ina ta fara furta sunan shi Ba shiri ta saki glass tumblan ya fad’i k’asa ya tarwatse. Sannan ta sa hannuwan ta biyu ta toshe bakinta a tsorace. Da kyar ya iya d’ago wa saboda tsananin zafin da yake ji a wannan lokacin. Idanuwan sa ma a hankali ya ke bud’e su, hannun sa kuwa ya dafe goshin sa da shi sannan ya sauk’e idanuwan shi a kan fuskar ta, suna ido hud’u ya yi wani Murmushi na takaici sannan ya kauda kai gefe yace “Hmmmph!!…… She gave me pain seven years back and now after seven long years she is still giving me pain! When will you change?” Ya k’are maganar yana kallon cikin idon sa. Taji abunda yace sarai amma se ta basar tamkar bata ji shi ba saboda ko ba komai ta san gaskiya ya fad’a ta sani cewa she hurts him a lot Hannun sa ya sauk’e daga goshin ya k’ura mata ido tamkar zai had’iye. D’ago wa tayi ta ga goshin sa yayi ja a tsorace ta matso daf dashi kamar zata rik’e shi sai kuma ta tuna bata da wannan hurumin nan da nan ta ja da baya Murmushin takaici ya sake yi yace “Dubi abunda muka zama, look at what we’ve become, abunda ya kasance naki ne mallakin ki yafi k’arfin ki tab’a shi and this is all your fault, we can’t even hug after so many years! Coz now i have nothing to do with you and you have none to do with me” Hawayen da ke k’ok’arin gangaro mata ta share sannan cikin rawar murya tace “Suraj goshin ka ya kumbura, you will have to apply some ice in ba haka ba zai maka ciwo “please ka shigo zan kawo maka ice se ka saka” Dariya ce ta kufce masa yace “Nice try! Kin bada ciwon kuma zaki bada bagani, i like this treat of yours”.. K’ala bata ce masa ba se juya wa tayi ta nufi fridge, k’ank’ara ta d’ebo daga ice bucket ta saka a bowl sannan ta dawo falon ta tsaya. Se lokacin ya sa k’afa ya shigo falon ita kawai yake kallo ya kasa tsayar da hawayen idanuwan sa. Waje ta nuna masa ya zauna, ba b’ata lokaci ya zauna ta sa hannu cikin bowl d’in ta d’auko cube d’aya na k’ank’ara ta kai goshin sa, karaf idanuwan sa ya sauk’a kan hannunta inda Muhseen ya damk’e ta, bai jira ma ta sa mishi k’ank’aran ba ya chafke hannun nata “Miye wannan? What’s this? Yaya aka yi kika ji ciwo?” Yayi tambayar ne idanuwan sa kan l’abb’an ta wad’anda suke ta karkarwa tsabar ta rasa amsar bashi. yana jira ne kawai yaji amsar da zata bashi amma se tayi sauri ta fisge hannun ta tace “Suraj wannan ba komai bane just a minor injury, ruwan zafi ne ya zuba min d’azu da zan had’a tea”… Ta ka’re maganar da kawar da kanta gefe Bowl d’in k’ank’aran dake hannun ta ya doke a fusace cike da tsawa yace “LIAR! Mak’aryaciya kawai!” tsabar ta razana zube wa tayi bisa kujera tana kuka ta toshe bakinta da hannuwanta biyu. Suraj yacigaba da cewa ” Idan da gaske kike ruwan zafi ne ya k’ona ki shi kuma d’ayan hannun fa, look at your cheeks duk sun yi ja bakin ki a fashe dubi wuyanki tamkar wanda aka shak’e za’a kashe, su d’in ma kina nufin duk ruwan zafin ne? Ko kina so ki maida ni mahaukaci ne?” Da sauri ta kad’a kai tace “Allergy ne ke damu na ba komai ba, kuma ni babu wanda yayi min wani abu, Suraj please leave kafin Miji na ya dawo”+ Wani bugu k’irjin sa yayi jin kalaman ta na k’arshe har saida ya ja da baya yace “wow! Miji? Mijin ki…… ” shiru yayi ya kasa magana tsabar takaicin kalaman da tayi jin haka yasa ta ruga zuwa d’aki da gudu tana kuka se lokacin ya lura cewa duk takun da tayi tafin k’afarta se ta bar shatin k’afar don jini da take yi saboda haka ne ya bi bayan ta “Laylah! Stop ki tsaya please” ko a jikin ta bata bi ta kansa ba ta shige d’akin ta zaune kan gado tana kuka mai tsuma rai. Ya dad’e a k’ofar yana kallon ta cike da tausayawa a hankali yake k’ariso wa cikin d’akin yana k’are ma d’akin kallo, karo yaci da kwalban turare don haka ya sunkuya ya d’auka sannan ya ajiye kan dressing mirror. K’aran ajiye wa taji hakan yasa ta d’ago, da sauri ta mik’e ganin da tayi cewa Suraj ne a d’akin “Suraaaj??…….mm…me kake yi a nan? Ya kamata ka tafi, you really should leave kafin Muhseen ya shigo ,me yasa ka shigo nan? Me kake tunani hakan this is my husbands bedroom please ka fita…”. Dariya yayi na takaici tsabar yaji d’acin maganar ta bai san lokacin da ya dunk’ule hannu ya kai duka a mirror ba, kafin ta ankara se gani tayi glasses sun tarwatse. Wani ihu Laylah tayi a tsorace ganin yanda Suraj ya birkice karaf d’aya jikin ta ya d’au rawa “Suraj please ka daina, you are hurting yourself, don Allah ka saurare ni, ka sake glass d’in da ka damk’e baka ganin jini yanda yake zuba? Please Suraj!! Da sauri ta chafko hannun shi da kyar tayi k’ok’arin ware yatsun shi sannan ta wafce glass d’in a birkice take surutai. Hannun sa ya wafce ya dakatar da ita da hannu mai jinin ta hanyar ware yatsun tamkar zai damk’i fuskar ta Chak ta tsaya tsabar tsoron yanayin sa Rai a b’ace yace “D’akin miji ki….. D’akin mijin ki My foot!! Laylah zan gaya miki gaskiya! The truth is you are the reason i don’t believe in love anymore, i can’t even look at you anymore!! Babu abunda nake gani se stranger a tattare da ke you mean nothing to me saboda haka kada ciwo na ya dame ki! You are too weak to hold my heart but too strong to break it! Why Laylah? Me yasa? Ko sau d’aya bakiyi tunanin halin da zan shiga ba not even once so bana son jin kalma d’aya daga gare ki, baki da abunda zaki ce min..” Juya wa yayi zai fice bai ankare ba yaji an chafko jacket nashi hakan yasa ya tsaya chak……….Trust me Suraj bani da laifi, ni ban buk’aci in rabu da kai ba, kai ka yanke mana wannan decision d’in, kai ka yi silar rabuwar mu tunda ka rubuta min saki duk da cewa ka san na tafi da tsohon cikin ka, ni sam ban buk’aci mu rabu ba saboda ina matuk’ar k’aunar ka Suraj” Fisge rigar shi yayi sannan ya juyo yana kallon ta, duk da cewa ta bashi tausayi se cewa yayi “So yanzu nine da laifi kenan? Barin fad’a miki wani abun da baki sani ba, tun da kika shigo rayuwa ta ban tab’a tunanin rabuwa da ke ba ko da na dak’ik’a d’aya, amma ke fa? What about you Laylah? You are the one who chose to leave without giving me a single chance! Dama d’aya tak na nema daga gare ki domin mu warware matsalar mu amma se kika rufe idanuwan ki tamkar baki san ni ba, i cried and begged, a kan gwiwowi na nake ina rok’on ki kada ki barni but what did you do? Tafiyar ki kika yi ba tare da tunanin wanne hali zan shiga ba. Bayan kin san ina mutuwar son ki!… Mahaifiya ta!…….. Mahaifiyata….. Matar da ta d’auke ki tamkar y’arta, ta zab’e ki sau dubu a kai na, ta fifita ki fiye da komai, ta kuma nuna miki soyayya mara misaltuwa, ita ta sabar da ke yanda dad’in mahaifiya take amma ki duba yanda kika saka mata! Har ta bar duniya burin ta taga kin dawo garemu, she died hoping that one day you will come back se kuma gashi. You broke her heart and i will never forgive you for that!” Zaro ido tayi waje tsabar shock da ta ji lokacin da Suraj yace Mom ta rasu, mik’e wa tayi ta kaura masa mari tana maida numfashi “Kayi hauka ne? Saboda kana son in koma gareka shine kake d’aura wa Mom mutuwa? Yaushe ka zama mak’aryaci Suraj? Get out of here! Bana so in sake ganin ka! You are so disgusting! Sosai yaga razana da firgici a fuskar ta don haka ya fice daga d’akin bayan ya janyo wani pink mayafin ta daga bakin gado ya nannad’e hannun shi mai ciwon. Zubewa tayi k’asa tana kuka tana tuna irin tarayrayar da Mom ke mata. Wani haushin kanta take ji don ji take tamkar ta kashe kanta ta huta.. A hankali taji an kama k’afar ta don haka ta zauna a tsorace. “Suraj?…baka tafi ba daman?..” Ko kallon fuskar ta bai yi ba yace “I am not that heartless, bazan iya jure wa ba when someone is in pain, kin fasa tumbler sannan kin taka glasses d’in k’afan ki na bleeding , let me treat your wounds in ya so se in tafi” Janye k’afan tayi tace “Ka bar shi zan yi da kai na” Bai ko saurare ta ba ya Kamo k’afar ya ajiye kan cinyar shi duk saida ya zare k’ananun glass dake ciki ya wanke da disinfectant ya shafa ointment sannan yasa bandage ya rufe, haka yayi wa d’ayan k’afan ma ita kuwa hakan ya bata free chance na k’are masa kallo har wani murmushi ta saki. D’ago wa yayi karaf ya kalli fuskar ta domin a jikin shi yake ji kallon sa take. Bata ma san ya gama ba kawai murmushin take yi don ta riga ta fad’a wata duniyar ta daban. Tsayawa yayi yana kallon ta shima se ya saki murmushi kawai ya juya ya fita, se lokacin ne taji k’aran k’ofa, da sauri ta mik’e ta bi bayan shi, yana jin steps d’in ta amma ya k’i juya wa, se ma murmushi da yayi. Laylah ta kasance wanda duk tarin laifi da zata aikata Suraj a makance yake a kanta, haka kawai yaji ya mance b’acin ran shi ya tsinci kanshi cikin tsananin jin dad’i. Saida ya isa k’ofa sannan ya juyo da sauri ta b’oye a corner tana lek’a shi, Murmushi yayi sannan ya fice.. Da gudu ta nufi wani tafkeken french window ta tsaya, daga windon kana iya ganin harabar Hotel d’in, har cije baki take tana Allah Allah taga b’ullowan shi. Ya d’an d’auki lokaci kafin ya fito hannun shi nad’e da pink mayafin nata, wani ajiyar numfashi ta sauk’e sannan ta juya zata koma ciki daidai lokacin Suraj ya bud’e motar sa zai shiga yana d’aga kai ya hango shigar ta d’akin. Motar shi ya tada ya bar harabar Hotel d’in babu abunda ke masa flash a fuska se murmushin ta………+ Doorbell taji yana ringing don haka ta rufa kanta ta daddafa ta bud’e k’ofan, waitress ta gani tsaye d’auke da abinci mai rai da lafiya, a tare da ita kuma wata likita ce rik’e da box d’in kayan aikin ta. Hanya ta basu suka shigo sannan ta maida k’ofan ta rufe, ajiye abincin tayi sannan ta dubi Laylah tace “Mrs Muhseen Sunana Habiba, this is doctor Fidelia, Mr Suraj Maleek ne ya turo ta zata duba lafiyan ki, sannan yayi umarnin a kawo miki abinci, please eat well, ga number na yace if you personally need something ki min magana, yanzu zan turo cleaners su gyara flat d’in”. Gyad’a kai Laylah tayi har idanuwan ta sun cicciko da hawaye ta gimtse kukan nata sannan ta amshi numban. Waitress d’in ta juya ta fice. Da murmushi doctor Fidelia ta dube ta sannan ta janyo stool ta zauna kusa da ita ta fara y’an dube duben ta, saida ta kammala ta dubi Laylah tace “Kina zazzab’i sannan baki sa komai ba a cikin ki dubi yanda kika zama pale. Did you know you are pregnant?” Zaro ido Laylah tayi ta kad’a kai se lokacin ta saki hawayen dake reto a idanuwan ta suka kwararo Kai da girgiza alamar “A’a”. Murmushi Doctor tayi sannan tace “It’s ok, kar kiyi stressing kanki, you will be fine” zan rubuta miki wasu magunguna, ko kuma bari na je na siyo magungunan, kafin nan ki samu ki sa abinci a cikin ki coz in baki cin healthy meals zai iya tab’a lafiyar baby d’in da ke kanki, already daman kin jigata, jira ni zan je in dawo.” Kai kawai Laylah ta jinjina mata, ai kuwa doctor na fita ta saki wani uban kuka mai tsuma rai ta damk’e cikin nata. Abincin ta kalla ta kawar da kai tacigaba da kukan ta…. A hankali Tasleem ke bud’e idanuwan ta, domin tun lokacin da tayi d’akin ta barci yayi awon gaba da ita bata ma san wainar da ake toyawa ba Fitowa tayi tana mutsika idanuwa, jin kukan Laylah yasa ta rugo da gudu ta rungume ta “Mommy me ya same ki? Mesa kike kuka?? Mommy what happened?” Kai Laylah ta girgiza tace “Shush! I’m alright baby… Am ok, babu abunda ya same ni, i am just happy, kwanan nan zaki zama big sister, so these are tears of joy” Tsalle Tasleem ta fara tace “I want a little brother! Just like Sadiyas brother. (Sadiya wata School mate d’in ta ce lokacin suna Newyork) Dariya Laylah tayi ta janyo trolley d’in abincin ta bud’e musu plate d’in. Sosai suka ci abincin don dama da guntun yunwan su, musamman ma Laylah da tun safe banda ruwa babu abunda ta saka a cikin ta. Suna gama wa Tasleem ta kwantar da kanta kan cinyar ta se tambayoyi take mata game da new baby tun Laylah na amsawa har ta gaji wasu tambayoyin ma abun dariya. Basu dad’e ba Doctor Fidelia ta dawo, magungunan ta bata sannan ta yi warning d’in ta da kada tayi wani abu na k’arfi don chance na survival d’in baby d’in kad’an ne” daga nan ta musu sallama bayan ta shaida musu kullum zata dinga zuwa don duba lafiyar Laylah…… Tun da likita ta shaida mata cewa juna biyu gareta Laylah ta shiga damuwa da farko de ita uwa ce ta kuma san dad’in d’a bazata so wani abu ya tab’a lafiyar abunda ke cikin ta ba, na biyu kuma bata san yanda zata tunkaro Muhseen da maganar ba domin babu abunda ya k’i jini irin ciki, domin sau uku yana zubar mata da ciki kuma ba k’aramin wahala take sha ba, infact a na ukun ma ba’a yi zaton zata rayu ba. Don haka ta yanke shawaran bazata fad’a wa Muhseen ba har se cikin ya bayyana don kanshi sannan wannan karon bazata bari ya illatar mata da d’an cikin ta ba. Ta d’an nisa sannan ta dubi Tasleem tace “Baby i want you to promise me that you will never tell Mr Grumpy about our little secret” kai Tasleem ta jinjina tana dariya “I promise mommy barin fad’a mishi ba”. Murmuahi Laylah tayi ta Sumbaci goshin ta…………..