INAAYA CHAPTER 1
Yarinya ce yar kimanin shekara sha shidda tana tafiya kaman tana tausayin kasa sanye take da abaya baka tasha stones ajiki ta yafa gyalen abayan ta, kafarta sanye take da slippers inta na hermès brown color ga jikarta rataye a kafadar ta kirar channel black color hanunta na dama kuma sanye yake iwatch ce series 3. Fara ce batada tsayi sosai kuma ba guntuwa bace, sannan siririya ce tanada shape daidai mai kyau, fuskarta doguwa ce da dan karamin bakinta ga lips in ta pink shade da dogon hancin ta ga idanunta farare tas tanada hazel brown eyes. Kyakyawa yarinya ce dan saboda kyawunta baya misaltuwa she’s an epitome of beauty itace yarinyar da ake kira da INAAYA.1
Tafiya take cike da natsuwa kaman batasan taka kasa hannunta rike da wayarta iphone 8 da wata leda da aka rubuta shoprite a jiki, hannunta na dama rike da makulin mota tana tafiya harta isa wurin wata mota hyundai elantra 2018 ta bude ta shiga ta tada motar ta fara tuki a hankali. Cike da natsuwa take driving har ta isa bakin wani babban gate tayi horn sai wani dattijo ya fito da murmushi a fuskarsa ya bude mata tazo shiga ta sauke glass tace malan aminu an wuni lafiya da murmushinsa ya ce lafiya kalau mamana me sunan yan gayu da murmushi ta ida karasawa wurin parking ta ajiye motar ta fito ta karasa zuwa wurin wata kofa babba ta bude ta shiga falo ne mai girma sosai amma ba mai tarkace ba kujeru ne ash color sai curtains navy blue da katuwar tv a jikin bango sai a tsakiyar falon centre table ne na glass mai kyau. Da sauri tana murmushi ta karasa cikin falon inda wata mata ke zaune tana kallo fadawa tayi jikinta tana dariya ta kama kunnenta tana cewa “sorry
mamii’am wallahi traffic ya tsaida ni” murmushi matar tayi mai kama sosai da inaaya dan dai ita tanada dimple tace naji tou ki je ki ga abinci a dining ki ci tace ok my mamii i will freshen up first. Upstairs ta hau ta bude wani daki wanda yake mallakinta ta shiga daki ne mai girma hade da walk in closet da bathroom a ciki dakin dauke yake da Queen sized bed navy blue color da ash curtains sai wani standing mirror daga gefe da dan karamin fridge sai a dayan bangaren kuma study table ne da chair ajiye jikarta tayi da ledan datazo dashi a kan gado ta isa wurin fridge ta bude ta fiddo ruwa ta sha sannan ta tube kayan jikinta ta daura towel ta shiga bathroom wanka tayo tare da dauro alwala ta fito closet inta ta shiga ta ja stool ta zauna gaban dressing mirror ta fara shafa man ta ah hankali ta gama ta fesa turarukanta masu dadin kamshi ta shirya cikin doguwar riga me laushi ta dauko doguwar hijab ta saka tayi sallah ta zauna nan ta gama addu’a sannan ta dawo daki ta dauke ledanta da chocolates ne a ciki tasaka a fridge da daura dankwali a kanta ta fita parlour wurin mamii.
Tana zuwa tazauna kusa da mamii tana cewa “mamii kizo muci abinci tare ” kallonta mami tayi tace A’a ci ke kadai ni sai daddynku ya dawo turo baki tayi kaman zatayi kuka ta nufa dining inda aka jera abinci taja kujera ta zauna ta bude kula taga fried rice ta tabe baki ta rufe da bude dayan kulan da masa ne a ciki sai ta saki murmushi ta zuba guda uku a kan plate tasa miyanshi dayaji kayan hadi a hankali ta fara ci ta gama ta dauka plate in ta taje kitchen ta wanke shi saboda inaaya ba me son ba masu aiki wahala bace dawowa tayi parlour ta zauna tace mamii wai yaushe su aneesah zasu dawo nayi missing nasu gidan is so boring without them yar dariya mami tayi tace ai hutu ya kusa karewa sun kusa su dawo tsalle tayi tace yaaay! Dan harararta mamii tayi tace kefa bakisan kin girma ba kike tsalle haka turo baki tayi tace sorry mamii’am ta tashi tace bara naje na duba wayana sama ta hau ta shiga dakinta ta hau kan gado ta dauka wayarta taga 20missed calls from besty murmushi tayi ah hankali tace this girl is crazy sannan ta danna mata kira ringing uku tayi ta dauka tace inteeeee you crazy girl naga kin kirani har so 20 meya faru ne? ah dayan bangaren kuma cewa tayii you useless girl i have good news for you shiyasa guess what? Are you getting married cewar inaaya mtsww mumuu not that i am coming to Nigeria next week ihu inaaya tayi ta tashi tana rawa tana tsalle tace are you for real dariya inteesar tayi tace for real amma there’s a bad news two weeks kawai zamuyi saboda abba nada aikin yi to ai sai abba ya barki nigeria tunda yanzu hutu mukeyi cewar inaaya ko baya barinki murmushi inteesar tayi tace bansaniba sai munzo dai I’ll ask him then shiru inaaya tayi sai tace tou shikenan can’t wait sukayiyy dan fira tasu ta kawaye kafin tace ki gaida su ammah bye ta kashe wayar tana sauri ta fita da gudu ta sauka kasa tana ta ihu mamii! Mamii!! Da sauri mami ta fito kitchen tana lafiya inaaya me ya faruu mamii next week su inteesar zasuzo nigeria murmushi mamii tayi tace ai kece baki sani ba dama tace mamiii dama kin sani baki gaya mani ba tace eh dama inteesar tace a bari ta gaya maki dan turo baki inaaya tayi sai kuma tayi murmushi.
aneesah tanada shekaru 13 wadda take js3 yanzu a great heights academy a abuja sai yan biyu maza ammar da ayman shekarunsu 10 yanzu suna js1 suma a great heights academy. Sai haj. Fai’za wacce suke kira da AMMI tana zaune a bauchi wanda mijinta dan gamawa ne a garin bauchi alhaji isah sani gamawa suna zaune cikin kwanciya hankali da yaransu biyu adnan me shekaru 30 wanda yake a gombe yana aiki da matarsa fareeda yar gombe ce ita suna da yara biyu yen mata hayfaah da hayraah shekarunsu 4 yanzu sai kanwar adnan me shekaru 23 fatima(aleena) wadda take serving yanzu ta gama karatu. Haj. Rabi itace karama a gidan alh. Abubakar geidam ana kiranta da MOMMY tana aure a garin kano yaranta hudu duk yan mata Allah bai bata da namiji ba nafeesah(feenah)ce babba shekarunta 25 wata biyu da suka wuce akayi aurenta sai aisha(ummi) me shekaru 23 tagama karatu tana serving a garin kano sai farhana shekarunta 19 tana karatu a BUK kano tana karantar bsc nursing sai autarta saleema tanada shekaru 13 tana js3 a crescent international school kano wannan kenan.
am tana scrolling tana liking pictures kadan kadan sai taga hoton wani saurayi mai kyau anyi posting a wani page northern blog wai wata ta tura picture nashi a taimaka ko handle nashi a sama mata she’s in love with him tabe baki inaaya tayi bata ko yi liking ba ta kashe data ta aje wayan side drawer ta kashe wutan dakin tayi addua cikin few minutes bacci ya dauketa.
w da zobo mai sanyi dama kuwa inaaya nasan zobon ummi its the best in town sun fara cin abinci sai ga aleesha da khady sun zo sun zauna suma suka gaishe da mamii suka gaisa sanna suka fara cin abincin shiru kakeji sai karan spoons har suka gama kowa ya koma abunda yake. Haka har dare yayi bayan magrib su inaaya zasu tafi basu ga baffah ba don ya tafi kaduna wani aiki mimi ta sauko stairs da gudu da dan karamin trolley inta tana cewa ummi danAllah ummi ni su inaaya zani bi nagaji da zama shiruu dariya ummi tayi tace to shikenan ai yanzu dakun shirya da su khadijan na ganki kin dawo smiling kawai mimi tayi tana ma su khady da aleesha stucking tongue haka tabi su inaaya suka tafi.