INAAYA CHAPTER 11

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Bayan sun tafi inaaya na kwance idanunta sun kumbura ga wani ciwon kai sai taji ana knocking dakinta aneesah ce ta turo kofan a hankali kallonta tayi tace “ya inaaya meya sameki naji mamii nata miki fada me kikayi” kallonta inaaya tayi ta kirkiro murmushi tace “babu komai nee” kallonta tayi da rashin yarda tace “kaii ya inaaya see your eyes fa sunyi ja sun kumbura something is wrong” Murmushi kawai tayi mata sai aneesah tace “since you’re not telling me mamii na kiranki a dakinta” jiki a sanyaye inaaya ta tashi ta nufa dakin mamii tana zuwa ta iske mamii dakin ta shiga ta samu wuri ta zauna mamii nan ta fara mata magana a hankali tana mata nasiha kaman ba ita tayi fada dazu ba tana cewa “inaaya I’m only doing this not because i hate you, i am your mother dole na saka ki a hanya daidai ko da ba love marriage bane mutun yayi the name is marriage and it comprises of the same thing dole kiyi wa mijin ki biyayya hakkinshi ne yasan idan matanshi zata fita bawai hakanan ba in bar ki kiyita yawo babu izinin shi na shiga abunda bai kamata nashiga ba idan nayi haka, komi kike ganin inayi ba takura miki nake ba gaskiya ce nake gaya miki dole kisan duk wa innan kuma su daddy sunyi fixing lokacin bikin nan da 3months da kin gama exams din semestern nan zaki tare dakin ki you will have to take

responsibility ba nan zaki dawwama da zama damu ba, yanzu kawai idan da kin tare sai kawai su biyo miki ku fita yawo ba da sanin shi ba dole ki gyara ki dinga hakuri da kuma biyayya” gyade ma mamii kai tayi ta bata hakuri sannan ta tashi ta nufa dakinta. Bayan inteesar ta koma gida duk bata jin dadi nan ta fara ba ammah labarin abunda ya faru harda hawayen ta “Ammah this is seriously not fair on inaaya wlh ammah bakiga yanda mamii take mata fada ba kuma ba laifinta bane she’s hurting wallahi and ya aliyu shi kuma i called him” ta dunga ba Ammah labari harda shessheka kuka dafa ta Ammah tayi tace “to yi hakuri miye na kuka shi kuma aliyu bai kyauta ba” tana cikin magana saiga aliyu ya shigo sanye da jallabiya harara ya watso ma inteesar dan yaji me take gayawa Ammah yana shigowa Ammah tace “inteesar bamu wuri zamuyi magana” tana tafiya ammah ta juya kan aliyu tace “i never expect this from you aliyu itama fa yarinya nan  dole akayi mata she’s hurting and har yanzu she’s young sun saba su dan fita tare su hudu but tun tana gidansu ka fara takura mata kana making din ta miserable haba Aliyu marriage aside she’s a younger sister ko wani kaga yana mata haka ka hanashi balle kai da kanka” sai da Ammah tayi mashi fada sannan shima yaga rashin kyautuwar abunda yayi yace ma ammah ayi hakurii sai ammah tace “ba hakuri zaka bani ba gyarawa zakayi she’s your wife komi responsibility dinta na kanka aliyu tun da nace kaje bayan biki ka kara zuwa ka duba ta?” Gyade kai yayi alamun aa tace “kai kaga hakan ya dace in three days zamu koma zaka bar kasar kaida zuwa sai lokacin bikin amma baka tunanin ka dubata kuyi magana akan biki build a relationship try to understand each other ko numbern ta ka karba ka dinga kira kaji lafiyarta ko bayan ka tafi saboda responsibility dinka ce ba wai dan iyaye sun hada ku ba ka yi taking advantage of that ka wulakanta masu diya kaji tsoron Allah” jiki a sanyaye ya amsa ma ammah yace gobe zayaje ya dubo ta in Allah ya yarda.

+

        Wurin amare kam duk sun wani kara kyau sai cin amarci akeyi dan har zuwa yanzu babu wacce ta fara girki cikinsu sai bayan one week, aleesha ce kwance a kan sofa a parlour gidanta wanda yayi kyau komi na ciki sabo parlour dinta shades of pink ne yayi kyau da pink curtains kallo take a jikin makekiyar Tv dinta tana kallon zee World Series ne love happens take kallo kawai sai inaaya ta fado mata rai tana cewa ko ya take tun bayan biki basuyi magana ba wayanta ta jawo tayi dialing numbern inaaya har ta katse bata dauka ba

Parlour din aleesha👆👆

      Sai bayan kusan 30minutes sannan aleesha taji wayanta na ringing tana dubawa taga inaaya ce ta dauka da sauri inaaya tace “hello ya leesha amarya” dariya aleesha tayi tace “uhmm kema ai naga amaryan ce ko” inaaya dai kawai uhmm tace sai tace “Shikenan an kaiki gidan ya mubarak duk kin manta da mu yar dariya tayi tace “habaa ni na isa na manta da ku kundai manta ni ko irin kuzo ganina tunda aka gama walima” murmushi inaaya tayi tace “to idan munzo me zaki ajiye mana zaki mana girki me dadi” aleesha tace “ko ba girki ba ni babu wani girkin dana fara kuzo dai a siyo mana” inaaya tayi dariya tace “kai ya leesha to zamuzo InshaaAllahu” da jin dadi aleesha tace “yauwa Allah yasa da gaske kike bari ma nasa mimi ta tattaro mani ku day after tomorrow kuzo” murmushi inaaya tayi tace “to shikenan Allah ya kaimu” sukayi sallama aleesha ta kashe wayan sai taji karan bude kofa ta tashi ta nufa kofan mubarak ne ya shigo tayi hugging dinshi as if her life depends on him tana cewa “babe i missed you ka bar ni ni kadai tun dazu” yayi murmushin sa mai kyau yace “oww i also missed you so much sweetheart but I’m here now and for the whole day just for my baby” Murmushi tayi tana tura kanta a chest dinshi yayi dariya ya ja ta suka nufa parlour.

         

            Washegari tunda inaaya ta tashi ta sake ba laifi har parlour ta sauko sukayi fira da daddy da aneesah har kitchen ta shiga tare da ita akayi making lunch tuna spaghetti da salad sai ta hada fruit parfait da mocktails tasaka a fridge ta nufa daki tayi wanka tayi sallah ta shirya cikin wani jeans da red shirt haka kawai taji tana son dressing yau din har zata fita daki taji wayan ta na kara ta duba taga inteesar ce tayi picking they talked for like 10minutes inteesar taji dadin jin muryan nata normal sai tace mata “mimi called me tace zata kiraki kema we’re going to ya aleesha’s house tomorrow and no going back InshaaAllah murmushi kawai inaaya tayi mata tace ok sannan ta kashe wayan ta sauka parlour kasa babu kowa mamii na sama a parlour din daddy ita da daddy aneesah kuma da twins suna karamin parlour suna game ita kuwa tayi kwanciyar ta kan kujeran parlour tana dan kallon wani movie sama sama kafin kace me bacci yayi awon gaba da ita.

           Aliyu tunda ya tashi yau jiki ba kwari yake ta abubuwan shi don yasan yau dole yaje ya ganota idan ba haka ba ammah saita mishi fada shi kuwa har ga Allah baisan me zaya ce mata ba idan yaje shiyasa duk yayi wani iri kaman wanda bayajin dadi a haka har yayi sallah zuhr ya shirya cikin wani yadi fari kal ya gama shirin ya fito ya nufa cikin gida ya tarar da ammah a parlour ya gaya mata sannan ya fito ya fada mota ya nufa gidan daddy, saboda yanda yake tafiya a hankali saida yayi 10minutes kafin ya isa yana zuwa dayake mai gadin yasanshi ya bude masa gate ya shiga da motan yayi kusan 5minutes sannan ya fito ya nufa cikin gidan yana takawa a hankali har ya isa parlourn gidan shiru yaji kaman ba kowa sai ya hangi mutun kwance a bisa kujera da alamu bacci akeyi yana kara sawa inaaya ya gani kwance ta dan takure tana bacci peacefully gashin kanta duk ya zubo saboda
babu dankwali a kanta gashin nan baki wuluk sai shining yakeyi ga shi yaji kitso sai kamshi ke fita daga gashin da ido yabi gashin nata yana kallo dan kuwa gashi na daya daga cikin abubuwan dayake burgeshi a mace matsowa yayi yai squatting kusa da kujeran da take bacci fuskan ta ya kallo fayau babu komai sai long lashes dinta da full brows dinta da pink cute lips dinta tsura mata idanu yayi yana kallo a hankali ya kai hannu yana dan shafa gashin kanta abunka da light sleeper nan da nan ta bude ido ganin mutum kusa da ita yasa tayi tunanin ko aljani ne ba shiri ta fara kwalla ihu ta tashi tsaye shima aliyu tashi tsaye yayi hade da jawo ta ta fada jikansa kamshinsa yayi hitting hancin ta sai ta kasa ci gaba da ihun ta natsu tayi shiru zuciyanta sai bugawa ya keyi tana jin wani shock na bin spine dinta shima aliyu wani shock yabi jikinsa sanadiyyar hade jikin nasu da yayi da sauri ya sake ta ita kuwa da gudu ta nufa sama zuwa dakinta zuciyarta nata bugawa dum! Dum!

Mamii ce ta sauko da sauri su ma su aneesah da twins sun fito daga karamin parlour jin ihun yayar tasu aliyu suka tarar dashi a parlourn tsaye kaman an dasashi mamii tace “ahh ahh son yaushe ka shigo” dakyar ya dan natsu yace “mamii yanzun nan na shigo” mamii tayi murmushi tace “to sannu da zuwa” Murmushi ya kakalo sannan ya zauna mamii ma zama tayi ya gaisheta suka gaisa ta tambaye shi ya Ammah yace lafiya qalau sai ga su aneesah sun karaso parlour ta gaishe shi ya amsa mata twins kuwa inda yake suka nufa suka zauna dayake sun saba dashi suna shiri sosai ayman yace “uncle aliyyy yau kam sai munyi game da kai munyi winning” murmushi yayi ma yaron yace “can you beat me” ammar yace “yesss just try playing with us yanzu we just finished winning and ya neesah lost” Murmushi yayi masu kawai yace ok then, mamii ce ta kalla aneesah tace “aneesah je ki kira inaaya” amsa wa tayi da to sannan ta nufa sama zuwa dakin inaaya. Tana shiga taganta a tsaye tana kai koma cikin dakin kallon aneesah tayi sai aneesah tace “ya inee mamii na kiranki” inaaya tace “meya faru” tace “nothing ya aliyu ne yazo” the mere mention of his name saida gabanta ya buga katon hijab dinta na sallah ta jawo ta saka sannan ta nufa kasa tana zuwa ta tarar ba kowa parlourn sai aliyu kasa tayi da kai sum sum ta shigo parlourn da nesa ta zauna dashi tace “ina wuni” kanta a kasa ya amsa mata da “lafiya qalau, miye na yi wa mutane ihu cikin gida da wani gudu kaman wata yarinya taga dodo” shiru tayi har saida ya kara tambayanta tace “I’m sorry i was frightened that was why” shiru yayi baice komai ba sai kuma bayan minutes yace “uhmm how’re you” da mamaki ta dago tana kallonshi sai kuma ta maida kanta a kasa a hankali tace “fine” shiru ya ratsa kusan 10minutes sannan ta tashi tana tafiya a hankali ta nufa kitchen ya bi ta da kallo yanda take tafiya kaman tana tausayin tiles din har ta shige kitchen ruwa da drinks da snacks harda fruit parfait ta hado kan tray ta kai ta ajiye kusa da shi ta koma ta zauna inda take ruwa kawai yasha kusan 30minutes babu wanda yace wani abu can sai yace “we have nothing much to say to each other, I’ll be going back day after tomorrow I’ve given you my card you can use it for everything, your needs and for the wedding preparations and I’ll leave my house keys with you in case you need to go and see the house for somethings, and feel free to use the card for school needs and everything cux its my responsibility” sauraronshi kawai takeyi ita dai ya gama tace “ok a hankali” sannan yace mata “if you need anything you can call me” nan ma dai ok kawai tace a haka wani shiru ya ratsa har mamii ta sauko still yana nan tace “son ta kawo maka abinci ko” Murmushi yayi yace “Aa mamii Alhamdulillah na koshi da dai akwai zobon nan ne” yafada yana shafa kai mamii yace “ahh ku da abunku a ga mai zobon nan a gaban ka ta tashi tayi maka” kallon inaaya yayi surprised dan bai san itace keyi ba tsaye ya tashi yana cewa “aa mamii babu komai ni wucewa zanyi yanzu” mamii tace “to ai sai ka dawo anjima ka karba ai ba wani abu” sake ce wa aa yayi saida mamii tayi insisting sannan yace zaya dawo after isha sannan ta amince ya tafi har bakin kofan parlour inaaya ta tashi sum sum ta rakashi saboda kallonda taga mamii nayi mata daidai bakin kofa ta tsaya tace “Allah ya tsare” yace amin ya wuce a ranshi yana tunanin not bad tana da hankali ya kula ya tada mota ya kama hanya zuwa gidansu fareed.tana shigowa ciki mamii tace taje tayi mishi zobo asa fridge yayi sanyi kafin ya dawo ta amsa da to ta nufa kitchen ta shiga aikinta a natse.

+

A daki ya tarar da fareed kwance yana what he knows best waya da khady zuwa yanzu they’re inseparable lovers shigan aliyu yaji fareed yana cewa “come on baby k, you know how much i love you no one can separate us please stop saying that” tsaki fareed yaji a bayanshi sai lokacin ya dago yaga aliyu ya dan wara ido he wasn’t expecting him sai yace ma khady yana zuwa ya kashe wayan ya kalla aliyu yace “malan lafiya daga zuwa sai tsoki” aliyu yace “kaine da ban haushi mana kullum bakada aiki sai waya da diyar mutane” murmushi fareed yayi yace “uhmm in mutum yaji zafi ya yi da matarsa mugani, kai ni wlh yaushe zaka rakani zuwa gaida baffah irin na formal introduction din nan nace mun daidaita azo ayi kawai” duka aliyu ya kai mishi yace you’re jobless sukayita firansu na abokai sai da magrib tayi sannan aliyu yace “shit banso magrib ya sameni a nan ba wanted going home gashi kaja mun” kallonshi fareed yayi yace “kanada appointment ne” aliyu yace “no naso nakoma nayi sallahn magrib acan nayi isha sai naje gidan daddy idan ban je ba na bani da mamii nace mata …..” bai karasa ba fareed ya fashe da dariya yace “kai guy ba sai kayimun corner ba kace zakaje kaga matarka kawai” harara aliyu yayi masa yace “idan ganinta zanije yi tsoranka nakeji da zan boye maka” dariya fareed ta dinga yi sai aliyu ya mashi dukan wasa sannan ya bashi labarin yanda akayi yace ya gane. A tare suka je masallaci sukayi sallah sannan fareed yace suje tare shima yanason fita duk yau bai fita ba a haka ya shirya a tare suka tafi saidai mota daban ko dasuka isa gidansu aliyu an fara kiran sallah masallaci suka nufa sukayi sallah sannan suka wuce gidan su inaaya, suna zuwa a parlour suka tarar da daddy da mamii suka gaishesu har daddy yake cewa “yau su fareed ne gidan namu” murmushi kawai fareed yayi daddy yake ce masu to dama dinner zasuyi dan haka duk sai sunyi joining a haka babu yanda suka iya sukayi joining table din mamii tasa aka kira inaaya da take daki tun bayan ta gama hada zobon saida taji zuciyanta ya buga data sauko ta tarar da aliyu bata ma kula da fareed ba sai da ta ida karasowa da Murmushi ta gaisheshi ya amsa mata, mamii tace ta fiddo zobo ta kawo kan dining din, taje ta dauko kujeran dake opposite aliyu kadai ya rage haka ta zauna ba yanda ta iya but duk uncomfortable takejin kanta haka sukaci abinci in silence sai karan spoons kawai kakeji suka gama daddy da mamii sukayi parlourn sama ita kuwa inaaya kiran fauziyya tayi ta tayata clearing table saida suka gama sum sum ta shigo parlour din fareed ne yace “amaryan mu wannan shiru shiru haka ban sanki da shi ba fa” kakalo Murmushi kawai tayi tace “kai ya fareed ina yayarmu” dariya yayi nan ya dunga bata labarin khadija this and that da irin yanda yake son ta sukayita fira inaaya harda dariya wanda ya ba aliyu mamaki ashe ta iya magana har haka shi dai nashi ido har wurin 9 sannan aliyu yace ma fareed su je ko tashi inaaya tayi taje ta sanar ma mamii suka sauko sukayi bankwana sannan inaaya taje ta dauko jug din zobon ta bi su a baya dashi sun kai bakin kofan parlour fareed ya karba jug din yace “to amaryan mu kawo na rike kar ki fito dare yayi” Murmushi tayi ya miko hannu ta bashi sai yayi gaba ya basu wuri, Aliyu ne ya juyo yana facing dinta tana tsaye a bakin kofa yace “thanks for the drink” a hankali tace “never mind” yace “alright bye” har ya juya ya tafi itama zata shiga ciki kaman wacce ta tuna wani abu da sauri ta juyo tace “ya Aliyu!” Da dan karfi dan yaji shi kuwa har tsakiyar kanshi yaji yanda ta kira sunan nashi juyowa yayi yana kallonta sai tace “uhmm dama inaso ne zamuje gidan ya aleesh
a gobe please” kallonta yayi for a minute duk a tsorace take muryanta har wani shaking yake yace “yes it’s ok you can go” sannan ya juya ya tafi ita kuwa tayi cikin gida tana sakin ajiyar zuciya ta wuce zuwa dakinta.

Washegari cikin jindadi inaaya tayi shirinta wani doguwan riga na atamfa light purple da olive green cinderella style yayi kyau sosai style din ga hannun long pencil hand ne tayi daurin zahra buhari style sai ta ciro wani veil olive dan babba haka sai tasaka shi a kan kai kawai taji tana son sakawa ya mata kyau sosai handbag na lv da takalmi na lv tasaka da Apple Watch a hannunta tagama shirinta tsab gwanin burgewa tayi kyau ta sauka kasa mamii na parlour kallon diyar tata tayi gwanin ban sha’awa tayi murmushi tace “yau dai ina fatan ba ni kikazo ki gaya ma zaki fita ba kin tambayi wanda ya kamata” dan murmushi tayi sai tayi kasa da kanta tana gyade kai mamii taji dadi ta dafa kanta tace “Allah ya miki albarka” a zuciyarta tace amiin sai sukaji karan bude kofa da sallama mimi ce da inteesar suka shigo gaida mamii sukayi suna zama wani kallo sukeyiwa inaaya datasha gyale a saman kai, mamii tace “to ko kun fasa tafiyar” dariya sukayi suka tashi suna aa zasu tafi mamii tace to su gaishe mata amaryan sukace to! Suka nufa waje kaman suna jira ana shiga mota inteesar tace “inee lafiya dai wannan sabon salo gyale saman kai” murmushi kawai inaaya tayi mata mimi kuwa dariya tayi tace “ke kuwa intee aure ba wasa ba” suka saki dariya nan haka sukayita tsokanan ta ita dai bata ce komai ba har suka isa gidan su sultaana suka dauketa itama saida tayi maganan gyalen inaaya. Wuni sukayi ma aleesha taji dadi sosai sai bayan magrib suka baro gidan kamar kar su tafi har take cewa ai bayan isha zasu je gidan abbah ma yi musu bankwana kudi ya mubarak ya basu kowa 10thousand suka mishi godiya suka tafi, a ranar mimi da inteesar gidan su inaaya suka kwana sukayi having fun sosai yanda suka saba daren da su inteesar zasu koma sunyi kallo da games mostly inteesar da inaaya ne suke yi mimi sai waya take da love din nata ko gajiya basa yi har inaaya tayi mata magana tace “wai ke mimi ki isa mutane kaman zaku cinye juna haba” Murmushi kawai tayi tace “ba laifin ki bane fa wait till you fall in love with ya Aliyu I’ll ask you ya kikeji” dariya inteesar tayi ita kuwa inaaya shiru tayi gabanta na duka sosai jin abunda mimi ta fada just the mere thought of being in love with him makes her heart beats at a faster rate, haka daren nasu ya kare sai 2 sukayi bacci. Da safe karfe 10 suka tashi duk suka shirya sukayi breakfast flight din su inteesar 2:00pm ne don haka sun dan kara spending time together dayake nan su abbah zasu biyo su dauketa duk ta gama shirya kayanta and all 12:30 su abbah sukazo gidan har lunch sukaci ammah har wani kara ji tayi da inaaya ita kuwa kunyanta ma takeji ahmad kuwa sai tsokanan inaaya yake yana cewa “anty inaaya gashi har zamu tafi bamu ci girkin amarya ba” duk sauran dariya sukayi banda inaaya da ke feeling uncomfortable saboda aliyu dake wurin. Karfe 1 suka kama hanyan airport wurin 1:40 suka isa su mimi da inaaya kaman suyi kuka dan rabuwar da zasu yi kuma inteesar ce tace “come on don’t cry if not nima I’ll just 3months fa and I’ll be back for the biki wow mimi we gotta start preparing call me everyday on facetime bamuda time sosai dole mu shirya sosai Fa wedding of our one and only inee” Murmushi kawai sukayi a haka suka rabu an fara boarding plane suka yi ma su Abbah Allah ya kiyaye sai abbah ya kalla aliyu yaga idan zasuyi magana da inaaya ganin haka aliyu ya matsa kusa da ita yace “I’m leaving call if you need anything” a hankali tace “Allah ya kiyaye” yace amiin ya kakalo Murmushi abbah da daddy sunji dadin hakan wucewa sukayi sunata daga masu hannun suna waving har suka bacce masu gani kafin duk suka juya sukayi wurin motocinsu don komawa gida.
+
*five days later
Inaaya ce zaune tare da mamii a parlour ta sa ta a gaba tana ce mata sai ta zaba furnitures ita kuwa inaaya ko maganan ma bataso tace ma mamii kawai ta zaba kowane tayi order she’s Ohhk with it amma ina mamii bata rai tayi shiyasa babu yanda ta iya ta karba wayan mamii tana kallon furnitures din different kinds of furnitures ne irin na turkey wasu complete set ne na bed,wardrobe,dining table,tv stand, sofas,da centre table wasu kuma bed ne kawai wasu sofas kawai haka tayita kallo tagama sannan ta ce ma mamii “mamii kawai a dauka me complete set din yafi” itama mamii shi yayi mata kyau don haka ta amince, shirin biki mamii tafara sosai tun bayan tafiyan su abbah har waya tayi da yar uwarta dake a maiduguri anty Baraka wadda duk yaran ke kira anty Bee sunyi magana har tace ma mamii zata turo wata mai gyaran jiki yar chad ta iya sosai tazo ta zauna a nan gidan ta dinga mata gyaran jikin tunda 3months ne kawai bikin mamii ta amince shirye shiryen su sukayi sosai wanda inaaya tanaji tace ma mamii ita wallahi bata wani gyaran jiki sai da anty bee ta ce mamii ta ba inaayan waya ta ce mata bata isa ba sai anyi shi kar ma ta bata mata rai babu yanda ta iya dasu haka ta amince akan saura two months bikin matan zatazo. Suna gama selecting kayan da mamii ta nufa sama ta shiga dakinta cikin sauri tayi shiri tayi sallah saboda lectures din da take dashi by 2:00pm ko da ta sauko kasa mamii na kitchen ta sanar mata ta tafi school mamii tace to ta bi a hankali kuma sai yaushe zata dawo, tace zatayi 2pm-4pm sai kuma 4-6pm mamii tace mata kar tayi dare ta amsa sannan ta fita ta nufa wurin mota elantra hyundai 2018 ta shiga ta tada nan da nan mai gadi ya fito ya bude mata gate yana daga mata hannu ta fita daga gida ta kama hanyan baze university.
STORY CONTINUES BELOW
Ko da inaaya ta isa school tayi late don haka parking tayi da sauri ta fito sanye da abaya ash mai kyau da wani backpack dinta navy blue tayi kyau babu makeup a fuskanta tana sauri ta nufa class tana zuwa taga mutun biyu yan ajin nasu tsaye a bakin kofa tana zuwa suka sanar mata ai mutumin ya hana shiga sai ta tambaye su “amma ai baya hana wa why now” wani dan saurayi fari da bazaya wuce 18years ba yayi Murmushi yace “wallahi kuwa ba wancan lecturer din ne ba ya gama part din shi yanzu wani ne zayayi part dinshi kinsan dama ko da Dr aminu yazo yace mana introduction to computer science part biyu ne zaya gama nashi sai Dr anwar yayi nashi to yanzu Dr anwar ne yake ciki” kallonshi inaaya ta tsaya yi ita har ta gaji da bayanin da yake mata akwai shi da surutu murmushi kawai tayi tace ok suna nan tsaye har kusan mutun 5 suka karu sun kusan su 10 sai inaaya tace “ni fa na gaji let me try entering idan zaya bar ni” saurayin mai suna saifullahi yace “hmm! Lallai kinsan ko waye Dr anwaar ai kome zamuyi bazaya bari mu shiga ba haka yake daya shiga babu mai shiga kuma kila yayi test ma” inaaya dai cewa tayi “let me try” wurin kofan ta nufa a hankali ta shiga tura kofan har ta bude shi gaba daya, Dr anwaar ne dayake gabatar da lecture din nashi maganan shi ko fitowa bayayi sosai dama haka yake fari ne sol kaman balarabe dogo dan chubby da dogon hancinsa yasa glass da ya kara ma fuskan nashi kyau ga full beard dinshi turo kofan da akayi ya bashi haushi who dare open the door while he’s in juyowa yayi cikin jin haushi da niyyan wulakanci fuskan da yaci karo dashi yasa yayi freezing yaji heart dinshi yayi twisting kasa dauke idonshi yayi daga kanta ita kuwa inaaya tana bude wa tayi narai narai da ido tace “we’re sorry sir, please can we come in this will be the first and last we’ll be late by Allah’s grace” Dr anwaar bai ma ji abunda take fada ba kawai kallonta yake a cikin zuciyar shi yana fadin MashaaAllah! Yana yaba kyawunta da kwarjinin da Allah yayi mata, kusan five minutes da tayi magana shiru kasa tayi da kanta ganin yanda yake kallonta kaman wanda ya tuna wani abu yayi sauri yayi kasa da kanshi ya masu alama da su shigo da hannu sauran students da sukejin labarin halinsa sunsha mamaki ba kadan ba suka shiga suka zauna duk jikinsa a sanyaye haka ya karasa masu lectures din yana dan satan kallon inaaya every now and then karfe 3:30pm ya kammala lecture din nashi ya fita har ya
fara tafiya sai ya dawo nuna inaaya yayi da hannu yace “meet me in my office” ya fice ita kuwa hankalinta ya tashi tana cewa ihsan “ohh god! Ihsan I’m doomed what have i done” ihsan ta dan yi squeezing hannunta tace “come on its nothing yanzu dai muje kar kuma ya zama wani laifi na raka ki” haka da tashin hankali inaaya tace to suka nufa zuwa office din nasa dayake ihsan tasan wurin, suna isa sunanshi ne jikin kofan Dr anwaar abdullah sunfi 5 minutes a wurin ihsan tace tayi knocking jiki a sanyaye tayi knocking kofan taji an amsa a hankali ta tura kofan suka shiga ita da ihsan yana zaune a kan wani kujera ya jingina kansa ya rufe ido tsaye sukayi sun rasa me zasu ce sun dan dade kafin ya bude ido ya gansu su biyu a tsaye yace “I only remembered calling one person” sum sum ihsan ta fita ta bar inaaya a tsaye nuni yayi mata da kujera ta zauna yace “what is your name” a hankali tace “fatima umar geidam” ya kada kai yace “do you know that no body enters my class as soon as i step in” kada kai tayi alamun aa abun yabashi haushi yace “don’t you talk” a hankali tace “I’m sorry sir, I don’t know” kallonta yayi na wasu seconds ta burgeshi yanda tayi kasa da kai tana wasa da yan yatsu sannan yace mata “this should be the last time don’t come to my class late again” tace “ohhk sir InshaaAllah” baisan sanda wani murmushi yayi escaping lips dinshi ba abunda ya dade baiyi ba sai yace “good you can go now i gave an assignment when I entered the class make sure you get it done before submission date” amsa mashi inaaya tayi ta hankali ta tashi ta nufa kofa zata tafi sai taji muryanshi yace “you can come if you need any help” ta amsa mishi da “ok thank you sir” sannan ta fice daga office din tana fita ta tarar da ihsan tsaye Murmushi tayi mata sannan suka tafi tare zuwa masallaci yin sallar la’asar a kan hanya ihsan ta tambaye ta yanda akayi ai kuwa ta gaya mata sosai ihsan tayi mamaki tace “inee I’m surprised wlh thought wani rashin mutuncin zaya maki but this never saw it coming hmmm gaskiya Dr anwaar kodai kodai” hitting shoulder dinta inaaya tayi tace “please kawai dai dama maybe baayi understanding nashi bane shiyasa babu wani kodai kodai Allah ya sawake ni I’m unloveable to any other guy”  dariya ihsan tayi tace “ahh lallai ko ba baayi understanding nashi ba uhmmm yayi hard girl unloveable abii” Murmushi inaaya tayi sai tayi sad face tace “you won’t understand ihsan” ita kuwa ihsan bata kawo komai a ranta ba sai maganan da taci gaba dayi tace “uhmm ni dama ni wlh I’m really crushing on him yana shigowa har wani dis! Gabana ya bada” dariya inaaya tayi ma ihsan yanda tayi maganan, a haka suka ci gaba da firansu har suka isa masallaci sukayi sallah sannan suka nufa next lecture nasu one hour yayi kadai 5pm ya fita daga ajin duk kowa ya fita ya kama gaban sa, koda suka fito saida inaaya ta dan zauna itada ihsan for 20minutes driver din dazaya dauketa ya iso sannan sukayi sallama kowa ya shiga mota inaaya ta tada mota sai gida.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *