INAAYA CHAPTER 12

INAAYA CHAPTER 12

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Da safe karfe 9 inaaya ta tashi duk idanunta sunyi ja ta tuna abunda ya faru gashi tun jiya wayanta switched off yake haka ta tashi ta nufa kasa domin zuwa gyaran jikin nata da suka tsara lokacin shi, ba ita tayi wanka ba saida sukayi morning session dinsu da yagana sannan tayi wanka ta shirya cikin wani atamfa skirt da riga sai kamshi takeyi kamar an yi sati biyu ana mata gyaran tayi breakfast ta zauna tana jiran zuwan su mimi shiru har ta gaji sai ta jawo wayanta ta kunna data ta shiga whatsapp kawai sai taga sabuwan number na kiranta kaman bazata dauka ba har ta kusa katsewa sannan ta dauka muryan aleena taji tana cewa “hello sis habaa kiranma sai ya kusa ya katse zaki dauka” nan take tayi murmushin jin dadi tace “ya leeeeee so it’s you wlh bansan ke ce ba ina wuni,ya gida,how’s ya hilal” dariya aleena tayi tace “kai inee all this questions ni kadai take it easy and besides komai lafiya qlw i am perfectly fine and hilal is fine too” Murmushi inaaya ta sake yi tace “MashaaAllah gaskiya I missed you so much wlh ya lee” dariya aleena tayi tace “habaa baby sis don’t worry ai ina nan zuwa ai a week to the wedding zanzo ma saboda shiri zamuyi na musamman wedding din favorite lil sis ba na wasa ba and yawwa how’s ya aliyu” tana mentioning wedding dariyan fuskan inaaya ta dauke tace “haba ya leena what’s left of it after sunyi nikkah already  ni banason komai fa banayin komai and how will i know how he is suna Switzerland” baki bude aleena take sauraronta tace “ke lafiyan ki kuwa inaaya kinsan baki isa ki ki yin komai ba ko

wannan ma abar maganan and what! Bakisan ya yake ba miye matsalan ki kuwa it’s your husband we’re talking about here zakice mun baki sani ba inaaya don’t tell me you guys don’t talk” shiru inaaya tayi sai kuma tace “ya leena what do you expect me to do my life is messed up already this marriage is not like other people’s marriage it’s different and weird he doesn’t talk to me we don’t talk I don’t even know what to say to him we are just not compatible” aleena tace “habaa mana inaaya banyi expecting kina fadan haka ba you can make it work he’s already your husband it can’t be changed you can’t sit and lose hope have some hope and make it work teach yourself how to love him and also teach him how to love you care for him if he doesn’t call you even once in a while call and greet him try and build a relationship don’t just sit and be crying everyday do something ya aliyu is one of the softhearted people I’ve ever known he has a soft heart just understand him i know you might think he’s way too older than you or you’re too young and all but it doesn’t work like that when it comes to marriage talk with him make him your bestfriend so that he’ll be free with you and share his problems with you” kwalla sun fara zirarowa a fuskan inaaya murya na rawa tace “ya leena I don’t know how to do it I don’t know what to do I don’t know how to make it work I don’t know how to build a relationship with him I don’t know how to talk to him I just don’t know anything” ta fada tana fashewa da kuka sosai aleena taji tausayin yar kanwar tasu tace “shh don’t cry please take it easy don’t be hard on your self just start with trying to know how to talk to him you can just start with messaging him after few days asking of work and how he is with that he’ll feel loved and will even start caring for you too you know trust me he’s a caring type now just take your phone and message him” inaaya tace “I don’t even have his number” aleena tace “i am sure intee does ki ce ta turamiki” da sauri inaaya tace “no no! I can’t” dariya aleena tayi tace “oh god don’t tell me inlaw kikeyi da ita” inaaya tace “no kawai yanzu they’ll all start teasing me” aleena tace “yeah so what ai ba wrong abu kikayi ba he’s yours *wink” saboda kunya har rufe fuska inaaya tayi kaman tana ganinta tace “kai ya lee” dariya aleena tayi tace “ohh ni fatima unbelievable wai inaaya da aure shaa let me save you from the teasing zan tura miki numbern shi and make sure kinyi abunda na gaya miki” amsawa inaaya tayi da toh tayi mata godiya sannan sukayi sallama ta ajiye wayan tana ajiyewa taji an turo kofar dakin nata mimi ce da sultaana a bayan ta suka shigo sultaana na cewa “Amaryaaaaaaa how far” nan take inaaya ta daure fuska tana cewa “habaa mana sultaana miye haka” mimi kuwa dariya tayi masu sannan suka karaso ciki suka zauna inaaya tace “shine kuka bar ni nayi ta jiranku komai ku you’re not punctual” dariya mimi tayi tace “sannu Anty punctuality ke ai gashi kin shirya da wuri” sultaana tace “inee share wannan fa ita ta tsaidamu wai naje kofan gidansu yarinyan nan ko wanka batayi ba sai da nayi mata jiran kusan 1hour 30minutes sannan kuma har wani bata lokaci take dan tasan bazan iya tafiya na barta ba saurayinta ne ya kawo mu” dariya inaaya tayi Ba kadan ba tace “kai! Sultaana ba dama” hararan wasa mimi tayi mata tana cewa “zan hadaki ma dashi ne in baki bi a sannu ba” dariya sultaana tayi kawai sai tace “ohh by the way inee kin ganki kuwa duk wanda zaya ganki sai drooling yanzu MashaaAllah you too fine babe” Murmushi kawai tayi sai wayan mimi tayi ringing duk suka kalleta picking tayi tasa a speaker muryan Ihsan ce sukaji tace “hello mimzz” inaaya naji tasan me zata tambayeta, mimi kuwa cewa tayi “ihsanuuu how far, ya kike, mike faruwa?” Ihsan tace “fine wallahi ya gida da school two days mun bar haduwa ko a school” dariya mimi tayi tace “kedai bari ihsan abubuwa sai a hankula ga exams dinnan da ya kusa” Ihsan tace “ai kam dai may Allah see us through. Uhmm mimz dama wani magana nakeson muyi ne fa” kallon juna sukayi mimi da sultaana da inaaya sai mimi tace “tooh! Fa wane magana ne ihsan meya faru” tace “it’s about inaaya” mimi da sultaana duk suka kalli inaaya da ta jingina kanta da bango ta lumshe idanu, mimi tace “inaaya kuma me ya faru” Ihsan ta saki ajiyar zuciya sannan tace “I don’t know what is wrong with her we even had an argument last night mimi kinsan inaaya dai is not getting any younger like she will just be acting as thou she’s small like as her friend na gaya mata not once not twice that ta daina abunda take yi she’s beautiful well mannered  cool nice religious and all so duk namijin da ya ganta will definitely fall for her kullum idan muna tafiya tare a school, guys din da suke approaching dinta ba kadan ba and ba wai zakice irin guys din nan ne da na bata lokaci ba no manya matured wasu siblings nasu suke kawowa a school su ganta suyita bi amma ko ci kanku inaaya bata ce masu abun babu dadi na mata magana sai kawai tace mun I won’t understand narasa gane kanta kuma a iya sanina da ita bata da wani boyfriend amma bata tsayawa ta saurari kowa na gaya mata wulakanci da take ba dadi ta daina but bata ji na and all that aside mimz the thing is about our lecturer wallahi he really likes her jiya da ta yi blocking nashi cikin dare ya nemo numberna ya kirani bakiji shi ba kaman yayi kuka a matsayin shi na malamin mu amma yama rasa ya zayayi sai gayamun yake kaman wata kawarsa like abun ba dadi i called inaaya shine nagaya miki we had an argument wai she’s telling me na kyaleta that she is married habaa! Ko yaro zaka gaya ma wannan he won’t buy it inaaya na zaune a gidansu ta
ce mun she’s married habaa I’m not a fool I’m just trying to show her the right thing as a friend that love her” mimi da sultaana duk sauraro sukeyi har ta gama jikinsu duk yayi sanyi inaaya kuwa har lokacin bata bude ido ba kallon juna sukayi sultaana kawai ta gyade ma mimi kai sai mimi tayi ajiyar zuciya tace “Ihsan I know bakiji dadin argument din naku ba I’m sorry about that and ni yanzu bansan ma me zan ce miki ba ko ya zan fara” ihsan tace “just talk to her the lecturer is hurt wallahi har yau da safe saida ya sake kirana nace mishi I’ll call you and talk to you and ni bansan me zan ce mata ba idan na kirata wlh she have changed ba kaman inaaya da na sani at first ba tun bayan mid semester break ta canza gaba daya na kasa gane kanta ma” kallon inaaya su mimi da sultaana sukayi a lokacin sukaga hawaye ya fara silalowa daga idanunta duk sai jikinsu ya kara yin sanyi sosai sunajin tausayin yar uwar tasu mimi tayi gyaran murya tace “ihsan kinsan dai we will not lie to you cux ba abunda karyan zatayi let me be clear to you and tell you the truth dan Allah ki bawa lecturer din hakurii and just know how to console him cux that’s the only thing possible cux by Allah inaaya is married” Ihsan duk ta zama confused tace “habaa mimz kema story din zaki bani” mimi tace “wallahi ihsan it’s the truth kaman yanda kikace inaaya changed tun bayan mid semester break yeah nima na sani she has changed even to us she is not the inaaya we all know and i am sure it’s all because of the marriage it’s affecting her she only have time for thinking and crying now but we can only be there for her and praying for her she doesn’t know about the marriage ita kanta sai bayan an daura auren ta sani our parents fixed everything and got her hitched with our cousin yayan inteesar and it happened lokacin auren su ya aleesha su baffah suka daura auren without her knowing sai bayan an daura auren suka sanar mana duka” dan pausing mimi tayi har ta fara kwalla sai taci gaba “i…naa..ya she was helpless babu abunda zatayi than to embrace the truth that is the reason she changed she’s still trying to accept the truth and live with it and she didn’t tell you cux probably tanada reasons dinta so please ihsan be gentle on her she’s going through alot” Ihsan da ke sauraron mimi batasan sanda jikinta yayi mugun sanyi ba har hawaye sun taru a idon ta tace “mimi wh…at h..o..w ohh god! Inaaya i was being harsh on her and accusing her of wulakanta mutane kai! I don’t even know what to say ya Allah! Mimi I’ll call you later let me digest this first” tana gama fadin haka ta kashe wayan mimi ce ta kalli inaaya da alokacin hawaye sun wanke mata fuskan ta mimi da sultaana duk sukayi engulfing inta into a warm hug sannan ta saki kukan nata a hankali lallashin ta suka shiga yi suna bata hakuri har tayi shiru sannan ta dan natsar da kanta tace “uhmm let’s get going munyi wasting too much time already girls” ta dan kakalo Murmushi sannan duk suka tashi tsaye toilet ta je ta wanke fuskan ta sannan ta dan gyara fuskan suka sauko kasa suka tarar da mamii da aneesah a parlour suka ce ma mamii sun tafi tace sai sun dawo suka yi waje suka shiga mota suka nufa bridal fabric shop din dazasu je.

STORY CONTINUES BELOW

Aliyu ne zaune da MacBook gabansa yana karatu wayanshi ne yayi kara yana duba wa yaga fareed ne ringing biyu tayi ya amsa hade da yi ma fareed sallama cikin tsokana da dariya fareed yace “wa alaika salaam aliyu mijin inaaya ko fatima zance” tsaki aliyu yayi yace “kaifa kanada matsala idan abunda zakace kenan sai anjima” dariya fareed yayi sosai sannan yace “habaa mana aliyu ya zani kira ka kashe ai dai kasan ba hakanan zan kiraka ba” aliyu yace “to ai shine naga baka da niyyan maganan dayasa ka kira ka fara wata daban shiyasa” murmusa wa fareed yayi yace “aboki na kenan so how far ya kake ya gida dasu ammah” aliyu ya amsa masa da duk suna lafiya shima ya tambaya fareed ya mutanen gidan ya amsa masa da duk lafiya sai fareed yace “ehen dama fa inaso naji ya shirye shiryen bikin how is it going” aliyu yace “shirye shiryen miye after an yi daurin aure ai ni banga wani abun shiri ba” hade rai fareed yayi yace “bangane ba me kake nufi aliyy habaa ko dai dinner ace bazakayi organizing ba abu dan once dai habaa dai aliyu” aliyu yace “haba fareed kaman bakasan situation dina ba dinner din me zanayi it’s not like everything is happening as per my wish so don’t expect me nayi wani dinner” fareed yace “habaa mana aliyu be considerate idan kai bakayi saboda bakason auren itafa yarinya so daya fa a rayuwanta zatayi shine zaka ki ka tauye mata hakki haba this is not fair on her nasan bazata gaya maka ba amma dole tanason tayi wani event dai haka and atleast it’ll be a memorable one idan anyi” ajiyar zuciya aliyu yasaki yace “fiiiine naji kar ka cinye ni you can go ahead with the preparations for that na wakilta ka and also clothes din da zana saka take care of everything” Murmushin jindadin nasara fareed yayi yace “yauwa abokina akwai ka da saukin kai ko kai fa and naji zanyi taking care of komai InshaaAllah, amma dai kaman ana saura 2weeks zakazo ko” forming smile kawai aliyu yayi yace “I am not sure sai yadda hali yayi” amsa mishi fareed yayi da ok sannan sukayi sallama suka kashe wayan, fareed har sauri yake ya kira khady ya sanar mata mission accomplished ringing uku ta dauka har sauri yake ya bata labarii da dan kara khady tace “yeeey! In such a small time kayi fixing komai wow! Wow! Ya fareed you’re the best i am soooo happy what can i do without you ” Murmushi yayi sannan ya daure yace “Amore who is ya fareed please thought we’ve talked about that” dariya khady tayi tace “ohhhhh not agaiiin, sorry habibty na manta ne i am just so happy” dariya mai sauti fareed yayi yace “ehen ko ke fa amore and yeah you deserve all the happiness in this world babe i will do anything for you so long as it’s permissible in Islam this is how much I love you the love is so deep babe I can’t even think of living without youuuu, you’re my completion please give me the chance to talk to baffah so that i can make you mine forever real soon” kunya ta kama khady sai faman blushing take tana feeling butterflies in her stomach she is so happy kullum fareed always makes her smile duk yanda mood dinta ya zama bad sai ya samu yanda zaya sata dariya ta manta she’s feeling him har cikin ranta dan ita kanta she can’t describe how deeply he made her fall for him tana shiru tayi yace “love are you there” gyaran murya tayi “uhmm uhmm habibty i am perfectly fine thank you so much for always making me happy I love you so much and as for baffah you’ll definitely come to meet him let ya Aliyu’s wedding be over” yayi farin ciki sosai da jin maganan nata suka ci gaba da fira sai yace mata “babe kinsan aliyu said I should take care of everything na dinner din har clothes dinshi so kinga you’ll help me we have to get matching color clothes for then you know” khady tace “yeah definitely I’ll help you we’ll organize the best wedding dinner for them InshaaAllah” fareed ma yace eh InshaaAllah sai kuma khady tace “habibty i am just worried for inaaya I know ya aliyu is not bad but he doesn’t even talk yanzu a hada su gida daya she’ll always be sad ko komi bazaya ce mata ba harkan shi kawai zaya na yi” fareed jikinshi yayi dan sanyi yace “yess i am also worried but har yanzu dai ina ta tunanin abunda zanyi inaaya is the perfect match for him i will try as much as i can to create a relationship between the two but i know it won’t be easy” khady ta murmusa tace “it won’t be easy but we are in this together we can do it we’ll help them” murmushi shima fareed yayi sukaci gaba fa firarrakinsu.

Suna fita shop din bridal fabrics suka nufa aso_ebi couture ah area 11 garki abuja, sun dade suna duba fabrics iri iri inaaya ta kasa deciding wanda zata dauka har aka kira sallah zuhr suna dubawa can inaaya ta ga wani maroon ombre beaded design yayi mata kyau sosai suma su sultaana duk suna ta yaba shi sai ta daukeshi ta hada da wani mint green shima shiny fa
bric ne sannan su mimi da sultaana suka fitarda wani fabric nude color sai atamfa full package na asoebe sukayi da head da komai a ciki mutun zaya biya ne kawai a bashi da atamfa da fabric da head din sai da suka gama sannan suka bar shop din suka kama hanyan limpopo street maitama shop din style temple inda inaaya zata bata dinkin nata shima a can sunyi kusan 2 hours saida aka dauka measurements da komai inaaya har tace “ni fa bansan me zanyi da fabrics biyu ba da daya na bari cux kamu ne kawai kunshi is traditional something” sai mimi tace yeah chill ai kamun zaki canza kaya ne after kin saka iro and buba na mint green fabric sai ki canza into maroon gown for pictures daga kai kawai tayi ba yanda ta iya ta yarda sannan tace tanason simple styles suka gama suka baro wurin suka nufa kampala street wuse shop din hudayya su mimi da sultaana suka bayar da dinkin nasu har da na inteesar ita ma inaaya tace dasu zata koma ta kai sauran dinkunan nata na laces sai a sannan suka nufa gidan su inaaya sai 2:50 suka isa gidan mamii da yagana suka tarar a parlour suka dan zauna suna ba mamii labarin fabrics din da suka siya harda hoto suka nuna mata, sallah suka farayi sannan suka ci abinci suka nufa dakin inaaya a sama.

Suna zaune a daki suna ta fira kadan kadan wanda duk yawancin fira sultaana da mimi ne keyi sai wayan mimi yayi kara taga inteesar ke kiranta nan ta dauka inteesar ta tambayeta ya sun gama komai mimi ta shaida mata eh har dinki sun bada zata tura mata pictures din fabrics din sai inteesar tace “guess what” mimi tace “ohh you know i am terrible at guessing” inteesar tace kedai guess” sai mimi tayi rolling idanu tace “fiiine ya sa’id asked you out?” Tsaki inteesar tayi su inaaya da sultaana suka fashe da dariya “mtsww ke mimz kinada matsala noo ba haka ba ya khady ta kirani tace komai is going as planned” ihu mimi tasa “woooooooooooo are you for real wow this is like the best thing I’ve heard today wow gaskiya kin iya shawara” sultaana da inaaya da suka matsu ta gama wayan suji me ke faruwa suka gama maganan su mimi ta kashe waya inaaya tace “meya faru” mimi tace “uhhmm no babu komai fa chill wani turban ne da muke ta nema inteesar tace ta samo mana dama ita ta bada shawaran mu musaka turban din ba head din anko ba” inaaya tace “turban kike ma jin dadin nan you’re sick wlh” ita kuwa sultaana dariya tayi saboda ta dago da abunda ke faruwa. Sai bayan la’asar sunyi sallah sannan suka bar gidansu inaaya ya habeeb ne ya dauke su suka nufa gida, inaaya ta dawo parlour tare da mamii da yagana suna dan fira kadan kadan har yamma yayi lokacin evening session dinsu na gyaran jiki hakanan dai inaaya take yi ba dan taso ba tana ta dan bata rai har aka gama.

+

Can da dare wurin karfe 9 inaaya har ta kwanta amma ba bacci takeba tanata tunane tunane taji ringing din wayan ta ihsan ke kira da bazata dauka ba har ya kusa katsewa ta dauka cikin sanyayar muryanta tace “hello” Ihsan ma a hankali tace “hello inaaya ya kk ya gida da su mami” inaaya tace “lafiya qalau Alhamdulillah kefa?” Itama ta amsa da lafiya sai shiru ya biyo baya na yan wasu seconds sai kuma ihsan tace “look inee I’m sorry I misunderstood you abun ne is confusing ko wa kika cewa you’re married bazaya yarda ba and sorry for that please forgive your dumb friend” dan Murmushi inaaya tayi “come on Ihsan you’re not dumb kawai kina komai ne for me and I appreciate you i am not angry i totally understand you” ihsan tayi chuckling tace “yauwa ko kefa we are cool yeah?” Inaaya tayi dariya tace “we are always cool ai uhmm by the way how is Dr anwaar i feel terrible for hurting him so bad” Ihsan ta saki ajiyar zuciya tace “uhmm he’s not so good but Alhamdulillah na gaya masa and he understood so it’s ok” inaaya tace “ohhk then that’s good” sai ihsan tace “no mrs aliyu geidam nothing is good so at first ma meyasa ki kikayi tunanin kin gaya mun you’re married when were you planning on telling me ko kuwa baki gaya mun and second your wedding is taking place in two months shima baki gaya mun ba gaskiya i feel hurt ko inviting dina bikin ba ayi” inaaya tace “habaa Ihsan kinsan bazanki inviting dinki ba ko sorry kawai the thing is too much please accept my apology” Murmushi Ihsan tayi tace “don’t worry I understand you Allah ya kaimu biki can’t wait woooow!” Smiling kawai inaaya tayi mata tace sai sun hadu school Monday sukayi sallama da juna ta kashe wayan ta saki wani sigh of relief sai ta kunna data dinta ta shiga whatsapp taga inteesar tayi adding dinta a wani group mai suna FA20..LOVE STORY shiga group din tayi taga wa inda suke ciki taga mimi,sultaana,ihsan,inteesar sai ita inaaya sai lateefa(secondary school mate din su inaaya),yumnerh(inaaya’s maternal cousin),rufaidah(mimi’s maternal cousin and inaaya’s friend), khaleesat(secondary school mate), sadiya and sabeeha(twins and inteesar’s maternal cousins also inaaya’s friends) su 11 a group din iya kan su kenan bridesmaid saboda inaaya bata san tar kacen kawaye messages ta fara gani suna shigowa group din

Inteesar~hello babes what’s going on

Mimi~ intee what is the group name again babu ruwaana idan inaaya ta gani

Inteesar~ hahhahhhhh you want me to write hate story abii

Mimi~LOL noo fa

Sultaana~ hello intee and inlaw *wink

Mimi~mtsww abeg hold it😂

Inteesar~sultaanassssss how far

Sultaana ~fine inteee

Mimi I’ll report you now and you know where

Lateefa~assalamu alaikum group members hope you’re all good I only know 4 people in this group mimi,sultaana,khaleesat and inaaya please who is getting married this seems like a bridesmaids group

Sultaana~wa alaika salaam lateee it’s been lonnng and it’s inaaya that’s going to get married

Lateefa~whaaaaat😳 inaaaya ewooo🙆‍♀️ wait sultaana is it the inaaya I know as in fatima inaaya the no nonsense inaaya the hard girl the no love in my dictionary inaaya

Mimi~ LMAO😂😂😂😂 ohh lateee must you mention everything😅 she’s the one the fatima inaaya you know

Inteesar~ohhk this is funny😂😂😂

Khaleesat~ hello everyone please am I dreaming naga kaman ana cewa inaaya and marriage

Mimi~ khaleesat please better wake up oo it’s no dream😂

Khaleesat~ ahhh🙆‍♀️ please let me go and tell my daddy to get me married too tunda har inaaya zatayi the team no love inaaya

Sultaana~ haaa’an latee and khaleesat don’t finish inaaya oo things do change mana😅

Lateefa~gaskiya na yarda things change wow MashaaAllah inaaya i am so happy for Allah yasa Alkhairi

Khaleesat~yesso things do change sosai ma i’m also so happy for you inee Allah ya tabbatar da Alkhairi

Sultaana~Amiiiin

Mimi~Amiiin

Inteesar~Ameen

Mimi~so guys ga picture din asoebe nan na tura muku you’ll just pay and collect your thing it’s fabric and atamfa da head a ciki

Lateefa~wow yayi kyau sosai when is the wedding date exactly

Mimi~ 27th July

Khaleesat~wow wow wow this thing too fine let grab mine da wuri

Yumnerh~heyy babes hope you’re all good kaii gaskiya yayi kyau wa za ayi wa sending kudin

Mimi~you can send me sai na ba wa matan and collect it for you guys

Rufaidah~ Salam kaiii! Gaskiya kun iya fitar da anko yayi kyau sosai

Sultaana~yesso and ni na fitar😅😅

Mimi~lieeee

Sabeeha~ Assalamu alaikum beautiful people kuna lafiya! Iyyeh this anko fine oo har na ga style din da zana yi

Mimi~😂😂kaii beeha

Sadiya~ knock knock! Kaii naga wani fiiiine fabric a nan omg! Ya hadu

Inteesar~kaii sai hyping ankon kuke ni baimun kyau ba tunda ba ni na zaba ba😂😂😂

Mimi~jealousy

Inaaya~yeen yeen yeen yeen yeen kowace🙄

Lateefa~amaryaaaaaaaaaaa

Inaaya~ehh naam ango

Lateefa~you’ll never change😂😂😂💔💔💔💔💔

Khaleesat~Amarya ta ango😂😂

Inaaya~khaleesat🙄…..Inteesar ke kuma it’s me and you
today wuce private muje

Inteesar~habaa mana tawa😂😂😂😂😂😂😂😂😃

Inaaya~ki bar yaudaran nan ma fa

Inteesar~naji😂😂😂😂😂 nasan maganinki ai call me on video call muyi maganan😅

Inaaya~wicked soul👊🏻👊🏻

Inteesar~😂😂💔💔

Inaaya~goodnight ladies mu kwana lafiya

Mimi~niiight

Khaleesat~bye amaryaaaa

Lateefah~aurevoir

Haka ta karanta messages din ta kashe data din zata kwanta taji karan text message daga aleena taga numbern Aliyu ta tura mata sai tayi mata typing thanks tazo zatayi saving numbern ta rasa me zata saka kawai tasa ya aliyu tayi saving ta ajiye wayan ta kwanta bata jima sosai ba bacci ya dauketa

STORY CONTINUES BELOW

*one month two weeks later

Inaaya ce ta fito daga toilet ta gama wanka da towel daure a jikinta iyakanshi knee dinta ya tsaya ta wani canza ta kara haske jikin sai sheki yakeyi fatanta tayi wani laushi da ka ganta kaga amarya taka kasa take kaman tana tausayinta gaban mirror ta ja ta zauna a hankali a natse ta gama shafa mai ta shirya cikin wani jallabiya grey tayi mata kyau sosai kamar wata balarabiya, a watan da ya wuce abubuwa da dama sun faru ciki harda exams dinsu na first semester da suka kammala da shirin biki da ya kan kama sosai duk dinkunan ta zuwa yanzu duk sun zama ready har da wanda ta bada na laces daga baya da kuma dawowan ya sa’id ya kammala karatunsa na masters inda yanzu ake ta neman masa aiki, kwanciya inaaya tayi bayan ta gama shirin nata saboda gajiya tunda safe mamii ta sata a gaba sukayi da aikin abinci saboda zuwan su Abbah bayan sun gama hada masu abincin aka kai a can gidansu da mamii ta tura masu aiki suka gyara aka jera masu a dinning table sai karfe 1 suka iso gidan su saboda jirgin nasu 12 yayi landing, bayan sun gama abincin still mamii tace karfe hudu zasu fara hada dinner saboda a nan gidan nasu zasu zo cin dinner sun sha aiki a kitchen sai 6:30 suka gama saida inaaya tayi sallah magrib sannan tayi wanka shine ta fito ta shirya ta kwanta a kan gado.

Karfe 12 daidai jirginsu aliyu ya sauka a Nigeria sai karfe 1 suka isa gida inda suka tarar da abincin da aka jera masu daga gidan daddy saida sukayi freshening up sannan sukaci abincin kowa ya nufa dakinsa domin ya huta zuwa dare abbah yace zasuje gidan daddy dinner wanda aliyu baiso ba dan yasan za a saka shi a awkward situation ne babu yanda ya iya haka ya nufa daki ya kwanta amma bacci ya kasa daukansa wayansa ya daga ya dubo nigerian sim dinsa a wallet ya zare na Switzerland ya saka na Nigerian ya fara kiran layin fareed tana fara ringing fareed ya dauka “iyyeeh ango saukan yaushe” tsaki aliyu yayi “mtsww miye haka wai daga na kiraka… yau bamu jima da zuwa gida ba ma ya mutanen gida” fareed yace “to duk lafiya ai tunda kazo sai mu fara shiri ko *wink” aliyu yace “wlh you’re not serious ma dai” fareed yayi dariya sukayi firansu na dan lokaci kadan sannan suka kashe wayan bayan aliyu ya kashe wayan baa jima ba bacci ya daukesa sai wurin 4 yatashi yayi sallah bai fito ba yana zaune a daki har magrib yayi bayan yayi sallah ne sai ga ahmad ya shigo dakin yace “ya aliyu Ammah ce tace nace maka ka shirya yanzu zamu je gidan daddy da to kawai ya amsa masa saida yayi 10minutes zaune kafin ya tashi ya shiryan cikin irin moroccan jallabiya na maza mai long sleeves navy blue color sai yasa hula da takalman sa yayi spraying perfume dinsa mai kanshi kaman ba dan nigeria ba idan ka gansa fitowa dakin yayi ya nufa cikin gidan ya tarar da su duka a parlour sai abbah yace to suje amma shi da ammah zasu tafi da motanshi su kuma su dauka dayan motan, haka suka yi abbah da ammah cikin mota daya sai daya motan Aliyu ne ke driving sai ahmad gaba sai Inteesar a baya banda naseer da ya dade a kano inda yake serving ma yanzu baa jima ba suka isa gidan daddy tun kafin su shiga ciki twins suka fito da gudunsu suna kiran “uncle aliyy uncle aliyy” murmushi yayi shima ya danyi hugging dinsu sannan suka kama hannunsa kowa daya suka nufa cikin gidan mamii da daddy na zaune a parlour da aneesah ta gaishe ta kasa rufe baki ganin favorite brother din nata ahmad suna zaune a parlour Inteesar ta tashi ta ja dan trolley dinta ta nufa sama da saurinta ta shiga dakin inaaya, kwance inaaya take tana jin bude kofa ta tashi taga inteesar da jin dadinta tace “inteeeeee” baki bude Inteesar ta tsaya kallonta tace “ohh sorry please ya akayi kika sanni sorry ko na shigo wrong room ne dakin inaaya zani je ina take” dariya inaaya tayi tace “wlh you’re unbelievable intee” dariya ta fashe dashi tayi hugging din inaaya tana cewa “wow wow worlds best kin ganki kuwa OMG! Ba a ganeki fa MashaaAllah i can be bragging about having the world’s most beautiful sister and inlaw” dan dukan wasa inaaya tayi mata tace “useless who is your inlaw uhmm abeg ya hanya ina su ammah da abbahna” dariya tayi tace “uhmm sirikan ki na palo” rolling idanu inaaya tayi tace “ke kika sani dai” sai tayi hanya fita dakin zuwa downstairs a hankali take taka stair case din duk da yanda takeji kaman ta juya ta fasa saukowa dan heart dinta sai bugawa yake tana addua a zuciyan ta Allah yasa ban da aliyu aka zo haka a hankali har ta sauka kasa muryoyin abbah da daddy taji a parlour tayi kewan abbah sosai da saurinta ta karasa parlour ta ma manta da wani zancen aliyu, tana shiga ammah da abbah ne zaune a kam two seater batayi wani tunani ba ta rugo da gudu tana hugging abbah ta baya tana cewa “Abbahna I missed you soooooo much” murmushi abbah yayi sanin wacece yace “mamaaaana ta kaina nayi kewan ki sosai diyata” ammah tace “yau kuma dai Abbahn naki kawai kika gani” Murmushi inaaya tayi tana rufe fuska da hannu tace “kaii Ammah ya zaayi na manta my only Ammah” tafada tana karasawa tayi hugging ammah sai ammah tace “kaii MashaaAllah Allah abun godiya diyata kin ganki kuwa kinga yanda kika koma MashaaAllah Allah yayi maki albarka” dan Murmushi tayi sai tayi kasa da kanta saboda kunyan da taji kawai sai taji muryan ahmad yana cewa “anty inaaya ina wuni” dagowa tayi ta kalleshi ta maka mashi harara tana cewa “Ahmad wallahi ka bari if not this house will not enter all of us” kowa na parlour yayi dariya banda aliyu dake zaune can gefe inaaya bata lura dashi ba ma tunda ta sauko yake kallonta bata ma sani ba kallonta yake duk maganan da takeyi ba karamin kyau tayi masa ba a zuciya yake ta yaba kyawun da Allah yayi mata yana cewa she’s beautiful MashaaAllah ta canza ta kara haske da kyau, kawai inaaya da ta hada ido da mamii ta zabga mata harara sai tazama confused ta rasa me ya faru dagowa tayi ta kara kallon parlourn sai sannan tayi spotting aliyu zaune idonshi a kanta gabanta ne ya fara duka ba kadan ba duk ta rasa natsuwanta kallonshi tayi a hankali sai idanunsu suka hadu taganshi ya kara kiba da kyau kasa dauke idanunta tayi sunkai 5minutes suna kallon juna kaman wacce ta tuna wani abu tayi kasa da kai da sauri ta ma rasa ya zatayi kallon mamii ta karayi taga yanda take mata wani kallo tayi kasa da kanta a hankali ta fara takawa wurin kujeran da yake zaune kaman wacce kwai ya fashewa a ciki tana isa wurin kujeran ta dan dafa kujeran kanta a kasa tace “ina wuni ya hanya” duk idon iyayen nasu a kansu shima ciki ciki ya amsa “lafiya Alhamdulillah mun sameku lafiya” ta amsa ta lafiya lau sai shiru ya biyo baya kanta a kasa ta rasa me zatayi sai daddy da ya lura da tension din yace to yanzu muyi sallah mana sai ayi dinner abbah ma ya ce gaskiya haka ya kamata inaaya da ta kasa motsi daga wurin saida Inteesar tazo ta ja ta sannan tabi bayanta sum sum suka yi sama zuwa daki domin gabatar da sallah.

A can daki inaaya ko magana bata yi duk a hankali take ta abubuwa ta dauro alwala tazo tayi sallah ita kadai tasan yanda zuciyanta ke mata ji takeyi kaman ta rufe kanta tayi bacci kar ta kara haduwa da Aliyu inteesar da ta kula da yanda takeyi ta dan bata space bata ce mata komai ba suna zaune shiru sai ga
aneesah ta shigo dakin tace mamii tace su sauko ayi dinner haka inaaya ta tashi jiki ba kwari suka sauka kasa a tare duk suka tarar kowa zaune a table din aneesah ta karasa ta zauna kujera gefen Ahmad, da kyar inaaya take takawa a hankali inteesar tayi gaba ta barta ta ja kujera gefen mamii ta zauna inaaya na karasowa mamii tace ita zatayi serving kowa abun bai mata dadi ba amma babu yanda ta iya ta fara da su Abbah da daddy tayi serving dinsu creamy shrimp pasta sai chicken soup as a starter tazo tayi serving ammah da mamii sai inteesar dake kusa da mamii tace “I’ll serve my self nayi saving dinki wahalan” murmushi kawai ta dan kakalo tayi mata aneesah da ahmad ma duk sunyi serving kansu sai inaaya tayi serving twins da ya sa’id wanda yake zaune close to empty seat daga empty seat din sai Aliyu inaaya dai kaman ta zuba ihu saboda dole a seat din zata zauna dan shi kadai ya rage haka ta daure ta taka zuwa wurin Aliyu ta fara zuba mishi a kan plate kanta a kasa tana cikin zubawa taji muryanshi a hankali yace “it’s ok” sai ta tsaya har zata zauna kaman wacce ta tuna wani abu sai ta nufa fridge ta bude ta jug ta ciro na zobo ta taho dashi a hankali tazo ta dauka cup din dake gaban aliyu ta juya shi ta aje ta zuba masa a cup din sannan ta zauna tana zama ya sa’id yace “uhmm mu ba a bamu zobon ko kuwa ba namu bane” saida yaba kowa dariya a wurin ita dai inaaya shiru tayi ta dauka jug din ta mika mashi duk ya sakata jin kunya abinci da diba dan kadan tasa kan plate dinta mamii ta kalleta tace “ke inaaya mi ke damunki tun breakfast bakici komai ba zaki saka dan abincin nan kan plate kin kara ko sai raina ya bace” ta gefen ido aliyu ya kalla plate din nata yaga dan abincin da saka haushi abun ya bashi kawai ya ja serving spoon ya diba abincin dayawa ya kara kan plate din ta sam hankalin shi baya kan kallon da kowa keyi masu ya saka sannan ya ajiye ya dauka fork ya fara cin abincinsa.Bayan sun gama dinner anyi clearing table Abbah da daddy suka nufa parlourn daddy na sama domin tattaunawa twins da sun sa ahmad gaba dole yayi game dasu haka suka nufa part din ya sa’id yin game din harda aneesah sai ya sa’id da ya aliyu suna zaune nan parlour suna kallo suna fira inaaya kuma da inteesar daki suka nufa, mamii ce ta leka ta ga sa’id da aliyu kawai a parlour sai ta nufa dakin inaaya tana shiga ta gansu kwance suna kallo mamii ta hade rai tace “ke inaaya so nawa zan miki fada sai kawai ki tafi daki ki bar mutum kina abu kaman bakida wayau” shiiru tayi batace komai ba har mamii ta gama a hankali tace “kiyi hakuri mamii” bata ce komai ba ta fita a dakin dan kwalla ya sako a idon inaaya tasa hannu ta goge inteesar tayi dan patting bayan ta tana lallashin ta tace su je tare, a tare suka sauka kasa sukaje parlourn suka tarar da ya sa’id da ya aliyu zaune sai suma suka sama wurin suka zauna shiru ba wanda yayi magana sai ya sa’id yace “haj. Intee big girls shikenan dama da kin tafi Switzerland sai ki manta da mutane sai kinzo kasan namu ko” dariya inteesar tayi tace “habaa ya sa’id bahaka bane ba fa kasan school sai a hankula fa” sa’id yace “uhmm yen university kenan to ya school” a haka sukayita fira tsakanin sa’id da inteesar ita kuwa inaaya tana zaune shiru batace komai ba tana zaune a one seater dake gefen inda aliyu yake zaune shima shiru yake rike da wayanshi bayan few minutes sai ya dan ajiye wayan shiru shiru sai can muryan shi a hankali ko fita sosai batayi a hankali kaman yana rada yace “uhmm so, ya school” bata yi zaton zaya yi mata magana ba shiyasa maganan tazo mata a ba zata itama a hankali ta amsa masa “lafiya Alhamdulillah ya aiki?” Shima ya amsa da “lafiya qlau” sai shiru ya biyo baya sai kuma yace “i see so haven’t used the card i gave you and i am sure kina zuwa school why” shiru shiru ta rasa me zatace ma muryanta na kyarma tace “ermm uhmm daa…ma da..ma ai nayi using na account di…na ne” aliyu yace “eh ai nasan da na account din naki na baki card dina” shiru tayi ta kara kasa da kanta shi kam aliyu tabe baki yayi yace “anyway you can tell me if you need anything for the hidima and i hope you know there’s going to be a dinner” tanajin zancen dinner batasan sanda ta dago ta kalleshi ba kallon rashin fahimta irin dinner kuma yaushe tana stammering tace “ahh ahh a’a ban sani ba” aliyu shikuma bai damu ba yace “well then i am telling you now kin sani” batada objection babu yanda ta iya haka tayi shiru tana ta tunani iri iri a ranta. Sai 10:30 su abbah suka bar gidan bayan sun sha firan su.

STORY CONTINUES BELOW

Hidiman biki ya kan kama sosai ba kadan ba dan duk yan uwan mamii sun fara zuwa daga maiduguri da yawansu ya rage saura sati daya hidiman bikin yau ta kama sunday ranar da zaa kawo kayan lefe dan haka suketa shirye shirye duk da dai abu na family daya ne tunda safe mamii ta ce inaaya ta shirya su tafi gidan baffah da ita da inteesar da mimi da sultaana da yumnerh sai sabeeha da sadiya dan saboda haka al’ada ta tanada amarya bata zama a gida ranan da zaa kawo lefe tsab suka gama shirinsu suka bar gidan amma maimakon su je gidan baffah sai suka nufa gidan ya aleesha inda itama su aleena da ummi suka sauka dan suma duk sunzo bikin suna shiga gidan suka tarar da aleena da ummi a parlour da jindadi suka karasa suka rungume juna aleena tace “MashaaAllah waii Allah inee kin ganki kuwa ya Allah! Narasa me zance ma MashaaAllah wannan idan ya aliyu ya ganki ai sai ya saki baki yana kallonki” dariya su inteesar sukayi mata ita kuwa kaman zatayi kuka tace “kaii ya leena haba mana” dariya tayi tace “to sorry wasa nake amma dai gaskiya mamii ta hada ki dayawa” nan ma duk sukayi dariya sai ga aleesha ta fito daga kitchen tace “naji kaman nayi baki su waye” tana karasa wa tace “wow manya manyan baki nayi kennan sannu da zuwa matan yayanmu” inaaya ta hade rai ta juya tace “it was a bad idea coming hear ni natafi ma” dariya suka saka mata su duka ummi tace “kai habaa kun sa mana ita gaba ku barta ta huta mana” Murmushi sukayi aleesha tace su zauna bari ta kawo masu something to drink suka zauna nan ana ta dan taba fira inteesar tace “ohh wai ni ya ummi ina anty farhana *lol” dariya ummi tayi tace “babu ruwana idan ta ji ki kinsan hali” inteesar tayi dariya tace “kaii ni gaskiya nidai duk inlaws din nawa cikin family suke dai” nan ma duk sukayi dariya sai ga aleesha ta dawo dauke da katon tray da kayan sha dana motsa baki ta ajiye masu. Sai yamma karfe 4:30 sannan suka bar gidan suka nufa gidan baffah suna zuwa a can ma ummi bata nan sai khady da farhana da haneefa suna shiga farhana suka tarar parlour da ya naseer anata zancen da aka saba inteesar ta karasa tana dariya tace “kaii ai kuwa dazu nake tambayan ya ummi wai ina anty farhana” hararanta farhana tayi tace “to zaki fara ko” dariya ta karayi tace “habaa anty na…. uhmm su ya naseer an tashi daga dan gidanmu an koma dan gidan mommy ko” hararanta yayi yace “ke wai miyasa kin cika sa ido a koda yaushe” tabe baki inteesar tayi tace “to natafi” duk sauran suka gaishe da ya naseer ya amsa sai yace ma inaaya “our wife our wife how far” kaman zatayi kuka tace “kaii ya naseer harda kai kaima” dariya yayi mata yace “to ya zaayi” sama suka wuce dakinsu mimi nan ma suka tarar da haneefa tana waya sai basuyi ta mata surutu ba. Sai da sukayi sallah magrib sannan suka bar gidan suka koma gidan su inaaya suna shiga sukaji sound din magana anatayi ana shewa suna shigowa anty bee ta taso tace “kaii wayyo Allah ai diyata ba a baya ba dole takeyin goshi haka inaaya kinga kayan lefen naki abun baa magana akwatuna 18 MashaaAllah gaskiya kinyi sa’a Allah ya tabbatar da Alkhairi a auren naku ya kara so da kauna” duk sauran yan uwan mamii dake parlour sukayi dariya ita kuwa inaaya kaman kasa ta bude ta shige saboda kunya haka dai anty bee ta jata zuwa parlour wurin akwatuna tace “zauna in bude maku ku gani yan mata” ai ko duk suka zauna ita inaaya akwatunan ma suka burgeta set daya na louis vuitton sai set na biyu na gucci sai set na uku na channel duk set guda 6 ne sun mata kyau sosai aka fara bude kayan ita kanta saida ta dunga yabawa a ranta duk designers ne komi mai kyau ba tarkace ba saida suka gama sannan su
ka tafi daki baa jima ba mamii ta shigo ta kira inaaya zuwa dakinta sum sum ta bita a baya suna shiga babu kowa mamii tace ta zauna ita kuma ta zauna sai mamii tace “to fateema ina fatan dai kinga kayan lefen ko” daga kai tayi sai mamii tace “to madallah meya kamata kiyi yanzu” shiru tayi batasan me zata ce ba sai mamii tace “to idan ma baki sani ba yanzu gashi zan gaya maki waya zaki dauka ki kira shi aliyun ki yi masa godiya saboda kowa na san appreciation a kawo maki kayan nan dayawa kiyi shiru sam bai dace ba sannan kuma idan kinasan ganin bacin raina kar kiyi” inaaya tace “aa mamii InshaaAllah zanyi” mamii tace “to madallah Allah yayi maki albarka” ta amsa da amiin sukayi shiru sai mamii kuma tace “inaaya nasiha nakeson nayi miki shi aure da kike gani ba abun wasa bane ibada ne sannan yana da sharudda ba hakanan ake yin shi ba, ni na yarda da ke da tarbiyyan dana yi miki amma ina kara gargadin ki da ki zama mace ta gari a mijinki kiyi masa biyayya ki girmama shi ko ba aure tsakaninku yayanki ne nasan rashin kunya ba halinki bane amma dai fada nake miki kawai sannan idan ma wata matsala kuka samu da mijinki bance ki zo ki gaya mani ba ko daddynki ko abbahnki ko ammah ku daidaita komai tsakanin ku ko su inteesar bance ki gaya wa ba saboda babu mai shiga tsakanin miji da mata sannan na karshe hakuri dole ne kisa hakurin a zaman aure saboda ba komi zaya tafi yanda kikeso ba idan kikayi hakuri zakiga ribar abun ku gina understanding da juna komai sai yazo da sauki kinji ya ta” inaaya da hawaye sun gama wanke mata fuska ta tashi ta rungume mamii tana sakin kuka haka tayi ta lallashin diyar tata itama kaman tasa kukan har anty bee ta shigo itama ta lallashe inaaya sannan mamii tace ta tashi ta tafi daki sai ta tashi ta tafi tana zuwa ta iske yan matan suna game din truth and dare Tayi murmushi sultaana tace yawwa inee ke muke jira tun daxu come lets play tace “ok carry on yanzu zanzo” sai ta kalla inteesar tace “intee please can i see your phone” tace “mi zakiyi da shi” tace please mana sai inteesar ta bata kan gado ta zauna ta shiga contacts ta rasa ta ina zata fara neman numbern ya aliyu na nigeria searching ya aliyu tayi taga babu ji tayi an karba wayan ta juya ta ga inteesar ce zaune gefenta bata san sanda ta zauna ba ma sai ta kasa ce mata komai bayan minti daya sai ta miko mata wayan a hankali ta karba sai taga ” yaya A❤️🔐” a jiki da number tayi shiru ta ma kasa dagowa ta kalla inteesar ta rasa ma me zatayi a hankali ta dago kai ta kalla inteesar ita kuwa dan Murmushi tayi mata assuringly ta gyada mata kai sannan ta tashi ta koma cikin su sultaana ta bar inaaya nan zaune kaman wacce aka dasa kusan 5minutes tana zaune sai ta jawo wayanta ta rubuta numbern ta ajiye wayan inteesar ta nufa closet ta shiga ta zauna kusan 10minutes tana tunanin me zata ce kafin tayi gathering courage tayi dialing kaman baza ya dauka ba har ta kusa katsewa sannan ya dauka cikin sasanyar muryanshi yace “Asslamu alaikum” jin muryan nashi zuciyanta saida ya buga ta lumshe ido ta bude sai ta ce “uhmm uhmm wa alaika salam ina wuni” yana jin muryan ta ya gane amma sai yayi kaman bai gane ba yace. “Lafiya qlw dan Allah waye” tace “fa..fa..fatima ce” ta samu kanta da cewa fatima ba inaaya ba shi kuwa aliyu kaman dadin cewa bai gane yake ba yace “fatima? Wace fatima?” Ta rasa ya zata ce masa sai tace “inaaya” yace “ohh ohh ok me ya faru” tace “Aa babu komai dama dama ankawo kaya ne naga kaya na gode jazakallahu khairan” ya amsa mata da “Amin thanks” shiru ya biyu baya sai yace “to sai anjima” ya kashe wayan ajiyar zuciya ta saki ta zauna kusan five minutes kafin ta tashi ta fito ta tarar sunata game din ta zauna tayi joining dinsu suna game din sunata teasing juna har 12 tayi inaaya tace kai lets sleep 12 yayi sai sultaana tace “habaa mana one more spin” tace ” fiiine spin” sultaana tayi spinning bottle din cover ya tsaya a kan yumnerh button kan inaaya dariya yumnerh tayi tace “yessssss get ready cousin idan bakiyi ba you’ll have to do what i say for next one week kin yarda” inaaya tayi rolling eyes tace “yessss naji” tace “yauwa so truth or dare” inaaya tace “dare” dariyan mugunta yumnerh tayi tace “hmm hmm hmm! You’re in hot soup” duk sukayi dariya yumnerh tace “i dare you to hug ya aliyu when next you see him” dariya sukayi kowa ya juya inteesar nacewa “lallai babban magana kenan” sultaana tace “yumnerh kin balle ruwa wlh” mimi ma tace “waii Allah ni kam saida safe” sadiya tace “gaskiya yumnerh baki duba ma poor inee ba” dariya sabeeha tayi tace “hahhah miye kuke ta wani zamewa its not a big deal kuma dai ba haramun bane ai ni naga yumnerh ma tayi mata sauki idan da nice cewa zanyi kiss him when next you see him” inaaya tunda yumnerh tayi magana kaman an dasa ta ta kasa komai, dariya suk suka saki mimi tace “uhmm sabeeha ke babba ce fa ni nayi bacci” yumnerh tace “ohh kinga ni nawa da sauki ma ineee ina jinki are you in or not” inaaya tace “habaa mana yumnerh you know this is not nice” dariya tayi tace “sorry but you’ll have to if not for a week za ki na yin abunda nace” rolling eyes inaaya tayi ta tabe baki ta nufa gado ta kwanta baa jima ba duk bacci ya daukesu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *