INAAYA CHAPTER 2
Da gudu suka shiga gidansu sultana suna kiran “sulty! Sulty!! A tare suna shiga suka tarar da wata mata middle aged fara ce sosai ga dogon hanci da lashes sosai murmushi tayi tace “iyyeh yau su wa ne a gidan namu yaran mamiii ne kenan” smiling sukayi suna gaisheta umma barka da wuni “yawwa yarana ya mamiinku da ummi? “Lafiyan su kalau suna ma gaishe ke” murmushi tayi tace to ina amsawa bata ida rufe baki ba sai ga sultana ta sauko da gudu tana kiran “babesss” tashi sukayi suka rungume juna su duka ukun “i missed you guys so much wollah” cewa sultana awwwn! We also missed you too sweetheart “Ikr guys lets go to my room” inji sultana “yess lets go” cewar mimi suka tashi su duka suka nufa dakin sultana itakam sultana harda cewa umma bye umma mun tafi muyi having fun a daki tana dariya itama umma dariyan tayi tace kyaji dashi. Da karfi inaaya da mimi sukayi bouncing kan bed in sultana suna cire veil in su “heyy guys don’t break mu bed please oo” dariya suka sa suna fadin “what is we do anyways yanzu me zamuyi for fun ni kam na gaji da
boredom “I think we should go out for ice cream and some pizza” mimi ta fada “yeeepi nice idea muje cold stone but sultana ki tambayan mana umma” inaaya tafada “yess right away”sultana ta fada tana fita da sauri.
Dawowa tayi tana tsalle guys lets get going umma ta bari but tace dole driver ne zaya kaimu “no pee get ready so that we can go” da sauri sultana ta sa black abaya a saman jeans and T-shirt in dake jikinta ta sa lipgloss and kohl ta dauki wayanta da jika ta sa slippers inta na gucci suka tafi.
Driver in su sultana malam shehu ke driving sultana na agaba sai inaaya da mimi abaya motan shiru sai wakan I don’t care na ed sheeran da justin bieber dake tashi har suka isa cold stone sauka sukayi malam shehu yace zai jirasu suka shiga ciki suka zauna kowa yayi placing order inshi suna labarin school “OMG” fadar mimi kenan kallonta sukayi su duka suna fadin “ke lafiyan ki” dawo da hankalinta tayi gurinsu tana fadin wallahi I AM IN LOVE this is more than crush dan allah ku kalla guy din can wurin kofan fita da sauri a tare inaaya da sultana suka juya suga waye wannan daya kama zuciyar mimi at first sight saboda sunsan she don’t easily get a crush on a guy talk more of love, saurayi ne ya kai kimanin shekara 28 fari ne sosai kuma dogo MashaaAllah da pointed nose with full curved brows ga gashin kanshi kaman na larabawa yana sanye da sweat pant baki da black riga yasa wasu shades sun mishi kyau matuqa ga agogon shi na hublot a left hand yana tafiyan shi na kasaita yasa hannu cikin aljihun wando. juyowa sukayi suna kallonta mouth agape sai kuma sultaana ta fashe da dariya ya Allah! Tafada tana dariya itama inaaya dariya take kasa kasa frowning face mimi tayi wai what is this guys kuna ta mun dariya this is not a joke fa in between dariyan sultaana tace mimi bakisan waye ba ya habeeb ne fa my bro for life zaro idanu mimi tayi tana rufe fuska da sauri taji kaman kasa ya bude ta shiga don kunya dariya suka ci gaba da yi mata sai sultaana ta tashi ta nufa gurinshi tayi hugging inshi yaya habeebi ai dama kai ka kawo mu remember you even promised me we’ll have a dinner date murmushi saurayin yayi yace oh god! What have i done i am so unlucky for meeting this stubborn and crazy sister here pouting tayi tace shikenan let me be going ni mai bro nazo ina ya habeebi seems like you’re not happy seeing me dariya yasa yace ohh my dearest sissy of course am happy infact get what ever you want will you like to go for shopping ma tsalle ta danyi kadan tace yeey thats why i love you bro of course we’ll like to go for shopping i am together with my friends umma tace malam shehu ya kawo mu but let me tell him to go we’ll come back with ya habeebi “the greatest talkative najii go and tell him” da sauri tayi waje don fada ma malam shehu tana fita ya karasa wurin table in da suke zaune har lokacin mimi kunya ta rufe ta smiling yayi yace yau su sister ba ko hi dariya inaaya tayi tace habaa ya habeebi ni na isa ina wuni ya aiki “fine sister” ya fada hankalinshi ya koma kan wayan dayake latsawa dkyar mimi ta ita dago fuska hade da fadin ina wuni da siririyar muryanta tana samun kallonshi saboda wayan dayake latsawa.kaman daga sama yana latsa waya yaji wata siririyar murya nacewa ina wuni ko baa fada ba yasan me ita saboda yaga mutun a zaune daya zo wurin,daga mata kai kawai yayi ko dagowa baiyi ba haka sultaana tashigo tasamesu zaune su duka winking tayi ma mimi da suka hada ido tace what have I missed inaaya tayi dariya tace nothing sai tace to ya habeebi muje ko “eh yace hade da tashi ya nufa waje su kam kwashe orders insu sukayi suka bi bayanshi bakin wata Range Rover sport suka ganshi tsaye ash color da tinted glass super dark motan suka nufa suna zuwa kaman hadin baki inaaya da sultana suka bude sit in baya suka shiga tsayawa mimi tayi tana kallonsu tazo zata bude back seat itama ta shiga taji wata deep husky voice nace mata get in the front tana shivering saboda tsoro da yanda zuciyanta ke pounding ta bude gaba ta shiga shima shiga yayi ya tada motan suka nufa hanyar jabi lake mall.+
Shopping sosai sultaana tayi da taga abu tanaso sai ta dauka inaaya kam chocolates kawai ta dauka dan a nan tafi kwari mimi kam shiru kake jin ta komi bata dauka ba sunata cewa ta dauka saidai tai ta bin su da smile wurin bracelets da wristwatches suka shiga inaaya da sultana suka dauka wani wristwatch kusan kala daya suka ce ma mimi ta dauka tace no saidai haka nan suka daukan mata irin nasu,wani silver bracelet ne yayi caughting idanun mimi taje wurin ta tsaya tana kallo yayi kyau sosai tana tsaye batasan lokacin da sultana da inaaya suka barta ba murya taji bayanta wanda yanzu ko a bacci taji saita gane na waye yana fadan are you guys done? Juyowa tayi duk ta daburce tana fadan no yess banga su sultaana ba daidai lokacin sai gasu sun shigo dama wurin shades suka nufa kuma card nashi yaba sultaana suka biya suka wuce gidansu sultaana. Da gudu sultaana ta karasa parlour da shopping bags hannunta umma na zaune ta fada kanta tana umma we went shopping with ya habeebi it was fun kinga abunda muka siya “dagani babban kawai dake naji Allah yasaka da alkhairi to lokacin su inaaya suma sun shigo suna parlour in to atashi aje ayi sallah ko umma tafada duka tashi sukayi suka nufa dakin sultana suna ta shewa banda mimi da jikinta duk yayi sanyi suna shiga dakin sultana da inaaya suka kalla mimi suka fashe da dariya sai ga kwalla a idon mimi ya sauka shiru sukayi sai sukayi hugging inta su duka a tare come on mimz sorry meya faru nothing tace masu ta cire veil inta ta nufa toilet ta dauro alwala tafito sai da suka gama sallah su duka suna zaune suna duba stuffs in dasuka siya sai kira ya shigo wayan inaaya “maaama❤️🔐” ne fa fito jikin screen in ta dauka tana fadin mamii na dayan bangaren mamii cewa tayi inaaya driver bayanan kuma dare yayi daddy ya aikeshi ko driver in su sultaana zaya dawo daku ta mamii bari mu gaya ma umma cewar inaaya “to yawwa ” mami tafada.sultana ce taje ta sanar da umma sakon mamii sai tace to shikenan malam shehu bayanan saidai habeeb ya maidasu amsa mata tayi da to ta koma ta gaya ma kawayen nata itakam mimi taji dadi cux she’ll
get to see him again haka suka fara firan ankon dazasuyi bikin ya sarah “ehen sulty yaushe ma ya sarahn zata dawo?” Inaaya tafada “I don’t know for her oo ni bansan miyasa takeson lagos ba gidan anty khadija(kanwar umma dake aure lagos) but nasan very soon cux the wedding is around the corner.haka sukayita fira suna duba ankon daza yayi masu kyau color in har sukayi sorting har dai inteesar suka kira suka yi sorting tare da kuma labarin mimi da suka bata itama ta fashe da dariya tana girl he’s too old for you fa haka sukayita jan mimi suna dariya sun bata haushi sosai har umma ta aiko a kirasu suzo su tafi kaman sultaana ta yi kuka da zasu tafi suna gaya mata ai gobe InshaaAllah kano zasuje.suna waje bakin mota sultaana tasake hugging insu tana thanks guys sai nazo nima my regards to mamii aneesah and twins da to suka amsa mata suka shiga motan wannan karin ma inaaya tashiga baya tabar mimi da gaba the drive back home was a silent one har ya kaisu gida suka sauka hade da mishi godiya ,yana tsaye da mota har suka shiga cikin gate idonshi na kan mimi wat a silent girl yafada a hankali sannan ya juya kan mota ya bar anguwan su.gaishe da mamii sukayi dake parlour suka bata labarin shopping da abubuwan dasuka shiga smiling mamii tayi tace Allah ya saka da Alkhairi sukace amin daki suka je mimi ta rage kayan jikinta ta fada toilet tasamu warm bath ta dauro alwala tafito tayi sallah.inaaya ma wanka tayi ta dauro alwala ta gabatar da sallah isha da pj’s suka sauka kasa suka zauna suna kallon indian series a zeeworld “young dreams ” har 9 tayi sannan mamii tace suje suyi bacci gobe 10 zasu tafi kano InshaaAllah. saida safe sukayima mamii suka tafi daki.
Mimi yau batayi labari sosai ba tayi bacci inaaya kam na zaune tana scrolling a instagram ta kara ganin post in guy in da wata ke neman numbern shi comments ta shiga tana karanta wa taga wasu mata na fada wadda take neman numbern shi da wata sunata exchanging harsh words on each other saboda dayar tace itama she loves him and will try and get him at any cost hissing inaaya tayi her heart boiling with anger batasan miyasa ba takoma kan picture in nashi tana kare mishi kallo a zuciyanta tana fadin”damn it! The guy is not that handsome ma fa ladies are trash wlh” ta kashe
wayanta gaba daga ta ajiye ta kwanta taja duvet addu’a tagama yi bacci.1 week later*
+
Yau ta kama Friday ranan da abba zayazo da iyalanshi daga switzerland inaaya dadi ta kasa rufe baki saboda jindadin ganin Besty inta da zatayi domin bacci ma kasayi tayi da wuri ta tashi a ranan,
Inaaya ce tsaye a kitchen tana ta taya su mamii aiki tana murmushi abunta sai aneesah dake zaune kan freezer tana shan fruit salad hankalinta kwance, ita kam inaaya tana ta faman sauri tana hada hibiscus drink(zobo) mamii ta kalleta tace “ke inaaya bazaki je kiyi wanka ba kin tsaya bata lokaci har time in saukan jirginsu ya kusa haka mutane zasuzo su iske ki?” Murmushi tayi tace “habaa mamii zanyi mana inaso na gama hada special zobo ina mana sai na tafi kuma i have an hour before suyi landing kinga yanzu 2:30 sai 4:00 ne flight nasu” kallonta mamii tayi tace”to kiyi sauri ai nasan halinki da nawa” aneesah dake gefe ta sa dariya tana kallon inaaya “habaa yaya inee yanzu ke in banda abunki waya ke shan wani zobo that too made by you” bata fuska inaaya tayi hade da zuba mata harara “see you! Me kika sani please get out of this kitchen self” sauka daga freezer in aneesah tayi ta fita tana dariya.
Inaaya ce ta fito daga closet tana sauri saboda kiran da mamii keyi mata tayi kyau sosai ba kadan ba wani straight gown ne tasaka maroon colour sai black turban da wasu black dangling earrings da suke ta shining a kunnenta sai wani dan karamin necklace a neck inta wanda ba sosai ake noticing inshi ba na cartier, dress in yayi fitting inta sosai dan karamin black veil inta da ta saka a shoulder da takalmi low heel black color da black watch fuskanta babu wani makeup just simple tasaka powder da kohl sai lip gloss amma tayi kyau sosai saboda natural beauty ne da ita, tafiya take da sauri cikin natsuwa tana kamshin perfume nata na cartier har Ta isa parlour tana “mamii gani nagama muje ko” mamii kallon diyan tata tayi gwanin burgewa tayi murmushi ta gyade kai “eh muje ina aneesah take ta fito muje su ayman na mota tun dazu” tana rufe baki sai ga aneesah itama ta sauko tayi kyau abunta MashaaAllah! Gown ne tasa irin na inaaya amma nata royal blue ne color ne tayi dan nude makeup dama aneesah akwai son make up kuma gashi ta iya “ganiii mamii let’s get going 3:40 yanzu ” inaaya ta kalleta tace “eh after wasting our time ba” she smiled “habaa yayaas are you jealous don naga nafiki yin kyau” hararanta inaaya tayi cikin wasa”you wish sissy but shaa you look beautiful cux I know my sister is sooo beautiful” hugging in inaaya tayi tace”and my sorella is more beautiful and amazing” hanyan fita sukayi da sauri dan kar mamii ta tafi ta barsu karasa wa sukayi inda akayi parking motan dazasu shiga kirar pilot ce mami na zaune a baya already sai a can back seat in aymaan ne da ammar sun saka kaya iri daya komai iri daya gasu kyawawa MashaaAllah identical twins ne suna kama da daddy sosai, aneesah ta shiga gaba sai inaaya kuma ta shiga tazauna kusa da mamii tana cewa”babies in mamii sunyi kyau” frowning sukayi a tare suna cewa “mamii kin ganta ko mu fa mun girma ba babies ne ba” dariya kawai mamii tayi driver ya tada motan suka kama hanyan airport suna tafiya ne mamii tace “daddynku na airport da motanshi daga office ya wuce can yace flight in yayi delaying sai 4:30-5:00 haka zasuyi landing InshaaAllah” dagowa inaaya dake kan wayanta tayi tace ” ok mamii ai kafin mu isa 4:20 yayi maybe mimi ma tace manii suna a hanya yanzu suma wow! I really can’t wait wlh mamii” haka suka cii gaba da fira kadan kadan har suka isa Nnamdi Azikiwe airport.
Abba da Ammah ne zaune a cikin jirgi a first class a bayan seat nasu kuma ahmad ne da inteesar sai nasir da aliyu. Inteesar ce take ta faman smiling”wlh am so happy twiny I just can’t wait to see my loves I missed those girls so much wlh” kallonta yayi yace ohh please mun kusa landing dai a huta da wannan I can’t wait in” hitting nashi tayi tana “kill joy kawai”. Naseer ne yasa earpods a kunnenshi ya lumshe ido fari ne kyakyawa MashaaAllah da dogon hanci with amber eyes da thick brows da dimple nashi beside him kuma aliyu ne rike da wayanshi yana ta danne danne sai can kuma ya aje ya fara magana” it feels so good to be in nigeria it’s been long maybe non of the uncles will recognize me” smiling nasir yayi yace” no they sure will you haven’t changed a bit I’m telling you” murmushi kawai aliyu yayi sai aka fara announcing jirgi zaiyi landing yanzu, rufe idanunshi aliyu yayi ya lumshe su he doesn’t know what he’s feeling but the feeling is good.
STORY CONTINUES BELOW
Mimi ce tsaye tare da inaaya wurin arrivals sunata jira suji anyi announcing they were eager to meet inteesar nan kawai sukaji anyi announcing flight from switzerland zaiyi landing, kaman suyi rawa dan murna they were just smiling sun kasa su rufe baki a nan har jirgin yayi landing aka fara saukowa komawa sukayi sunyi tsaye suga inteesar.
Phew! Finally inteesar ta fada bayan sunyi landing sun fara saukowa tana taka stair case a hankali sanye take da wani red long floral dress da matching veil da handbag nata na bottega veneta da takalminta hermes black tana tafiya tana kallon taga ina zataga favorites in nata ai kam can tayi spotting nasu tsaye suna ta kallo su gan ta, ai da sauri ta karasa saukowa nan su mimi da inaaya suka ganta da gudu aka karasa sukayi hugging juna harda tears of joy “inteeeeee we’ve missed you wallah kaman dreaming mukeyi” inaaya da mimi suka fada a tare, dariya ta fashe da shi tana “girls don’t kill me mana i also missed you that I can’t tell how much” sakin juna sukayi sai ga sauran family kowa ya karaso a gurin anata murna ana hugging juna, da shagwaba inaaya ta fada ta rungume abba tana abbana I missed you so much mumushi mutumin yayi suna kama da d
addy sosai yana “to nifa mamana bata girma ” nan duk aka gaisa suna ganin Ahmad ya karaso wurinsu suka fara tsokananshi “amadu anzo nigeria” sunata jin dadin ganin junansu, har da naseer suka gaisa dayake ba mai yawan surutu bane shi but he’s friendly haka suna ta labari about everything and nothing har aka gama loading kayansu suka nufi gurin motocin su dukansu. Aliyu na saukowa daga jirgin yaji heart inshi yayi twisting he excused himself yace yana zuwa he will meet them zaiyi using rest room koda ya dawo inda ya ke tunanin suke yaga basa nan sai ya dan fara dubawa ko zaya gansu har ya hangi wani kaman naseer a tsaye ya nufa wurin. Duk suna tsaye bakin mota baffa yace wa abba “wai ina dan nawa yake ba kace hardashi zaku zo ba” smiling abba yayi “eh hardashi yanzu zaku ganshi yaje zaiyi using rest room yace” dariya daddy yayi yace “aliyu manya”. A haka ya iso wurin motan yaga mahaifinshi da uncles nashi nan ya shiga gaishesu ana gaisawa da dan fira kadan na yaushe gamo almost 17years smiling kawai yake nan suka gaisa da su abubakar(abby) and his other cousins harda wan inda bai taba gani ba su aneesah da ayman and ammar nan take kam yaran suka shiga ranshi sunata mishi labarin su. Su inaaya kuma da mimi da intee na can sun shiga motan ya abby suna jira yazo su tafi sunata fira da shewa cikin motan inaaya ce zaune a front seat sai inteesar da mimi A baya.
Bayan sun gama gaisawa kowa ya shiga mota dan duk gidan baffah zasuje can zaa ci abinci a ida labari har zuwa dare kafin kowa ya tafi. Kowa ya shiga mota sai Aliyu dake tsaye nan abby yace mashi yazo suje motanshi a baya ya bishi suka tafi suna zuwa abby ya shiga drivers seat shikuma Aliyu zai shiga front seat bai zata akwai mutun ba saboda tinted glass ne yana bude kofa ita kuma inaaya ta dago taga waye kawai idanunta ya sauka kanshi suka fara staring at each other gabansu na faduwa su duka, saurin dauke kai inaaya tayi cux she can’t keep eye contact da mutane shi kuma haushin kanshi yaji daya tsaya kallan ta ma tsaki yayi kawai ya saki kofan motan yayi baya bai ce komai ba nan abby yace mata” sis koma baya kinji” slowly ta fita ta koma back seat har lokacin chest nata bai bar bugawa ba tana fita ya shiga ya rufe kofan da karfi tabe baki inteesar tayi sai ya abby yace mimi baku iya gaisuwa ba ne nan mimi ta gaidashi ya amsa ahankali sai a lokacin inaaya da samu muryanta ya fito ta furta “ina wuni” a hankali kaman ba zai amsa ba sai kuma yace “lafiya”. The drive to Baffah’s house was silent babu wanda yace komai cikinsu ita dai inaaya ta kwantar da kanta jikin seat ta lumshe ido ita kadai ta san yanda heart inta ke beating da sauri sauri. It wasn’t a long drive but a silent one kusan duk a tare motocin suka shigo compound in gidan Baffah duk suka fito akayi cikin gida. Sama zuwa dakin mimi su inaaya suka nufa mimi nata ba inteesar labarin graduation nasu ita kuma inaaya shiru kake jin ta suna shiga ta kwanta kan gado ta rufe ido inteesar ce tayi mata magana “inee what’s wrong with you seems like someone is not happy to see me” ta fada tana murmushi smile inaaya ta kirkiro tace “habaa intee wlh kaina yake mun ciwo ne fa i woke up early today” “eyya sorry babes kisha magani and rest we’ll gist later sosai i have lots of stories” mimi ce tace “ok a barta ta huta let me get diclofenac for you” haka mimi ta kawo mata maganin tasha ta koma ta kwanta. Parlour kowa yake an jera tons of kulolin abinci a kan carpet su mimi da aleesha da khady da aneesah suka fara serving kowa abunda yakeso “ina inaaya” mamii ta fada “bata jin dadi tasha magani ta kwanta” inteesar ta gaya wa mamii nodding kai kawai mamii tayi nan saiga yan mazan sun fito bayan sun gama sallah suma zama sukayi a parlour in akayi serving insu dayake parlour in nada girma haka they ate in silence suna gamawa masu aiki suka zo sukayi clearing wurin nan suka fara fira. Baffah ya kalla aliyu yace “da na ai nasan yanzu kanen nan naka ba duka ka sani ba ko?” Duke kai yayi yace eh ah hankali murmushi Baffah yayi yace “to duk gasunan nasan dai kasan fareeha wannan abokiyar fadan ka ce ma ta yarinta, kasan abby kuma sai aleesha itama kasanta ko?” Eh yace sai Baffah yaci gaba ” ga khadija ita kuma tana karama last zuwanka, sai mimi ita kuma tana few months lokacin, sai inaaya sunce tana daki bata jin dadi lokacin ita kuma ranan da aka haifeta kukazo ranan sunan ka tafi” inaaya yaita maimaitawa a ranshi ko itace ta dazu motan abby yake fada a ranshi maganan Baffa ya katseshi ” sai neeshasha inmu ita baka nan sanda aka haifeta da twins ammar da ayman” MashaaAllah yace bayan baffa ya gama sai ya juya ga yaran yace “to kunga babban yayanku ko ya aliyy sunanshi” eh sukace a tare nan aka cigaba da fira suna tambayan aliyu ya aiki da naseer suna ya karatu yana dai maida hankali ko? Su mamii kuwa dama sun tafi falon ummi itada Ammah suna firansu aleesha da khadija sun nufa daki mimi da intee kuma na zaune mini parlour kusa da dining don basu san ta da inaaya daga bacci, ayman da ammar sun bi ya aliyy da ya abby sunata masu labari, Aneesah kuwa tana can sun nufa garden in gidan da ahmad don mutunen ta ne suna shiri sosai jan shi tayi tana ” ya ahmad please kazo muje garden in gidan baffah ya hadu you’ll love it” they’ve so much in common suna san zaman garden haka ya bi ta yana “haba nee da kin bari sai wani lokaci I’m tired yanzu” bata ce komai ba taja shi har suka je garden in nan suka zauna kan swing in tana ta bashi labarin abunda ya faru a school for the past one year he has been away. Mimi da inteesar kam sunata fira mimi nacewa “wai finally yau munga ya Aliyy he’s cute and hot wollah” dariya inteesar tayi tace “hmmmm! Mimz kodai kodai” dariya itama tayi” habaa wa intee no fa he’s cute and hot but not more than my guy of course” duka suka sa dariya sai kuma inteesar tace “whaaat!!!! Guy? Which guy? Ahh you guys are so bad shine ko ku bani labari ugh!! I hate you” tafada feigning hurt dariya mimi tayi tace “heyy chill it’s recently fa kuma it’s nothing serious it’s just me that kinda erm! Erm! Like him” dariya inteesar tayi sosai tana OMG!! Mimz you like a guy ahh gaskiya to kowa ma yayi BTW who’s the guy?” Inteesar na fadan haka har mimi ta fara blushing tace ” sultaana’s brother” tafada tana rufe fuskanta nan inteesar tayi ta teasing nata sai tace suje su ga idan inaaya ta tashi.suna shiga suka isketa ta zauna kan gado with a sick face nan sai suka fara “sorry dear let’s go and tell mamii a kaiki asibiti” tana ganin faces insu ta fashe da dariya harda clutching onto her stomach tana nuna su da hannu hade da fadin “gotcha! Dama just wanted to see ya zakuyi it’s just headache kuma ya tafi” gadon suka fada su duka suna dariya har saida sukayi mai isansu sannan intee tace ” so inee baki gaya mun sistern ki ta kamu ba” ta fashe da wanii dariya nan inaaya tayi joining nata don tagane inda ta nufa tsaki mimi tayi ta kyalesu sukayita tsokananta har suka gaji suka cigaba da labari har kiran sultaana sukayi ta face time she was so happy tace gobe she’ll pack her clothes and join them. Har time in sallah magrib yayi suna nan zaune tashi sukayi kowa yayi sallah suka sauka falo inaaya zataci abinci, kadan taci suka sa kallo har 7 yayi sannan daddy yace suzo su tafi gida nan mimi ta shirya kaya don tare zasu tafi sleepover a gidansu inteesar. Sallama sukayi kowa ya fito suka tafi nan abba ma da iyalanshi suka fito tafiya dan suma gidan nasu a gwarimpa yake close to na daddy.Motan daddy ne su inaaya ke ciki driver na tuka su har suka isa Efab estate gwarimpa, gidansu inaaya suka fara sauka dan inaaya zata dauka kayanta. Ko da suka shiga su mamii da aneesah da twins har sun iso suna zaune palo tare da daddy,Abba,Ammah hankalin su kwance MashaaAllah! Parlourn suka nufa suka zauna tare da iyayansu dan sai after dinner zasu tafi gidan Abba which is a walking distance from gidan su inaaya. Bbc news ne su daddy ke kallo suna labarin yanda kasa take ciki nan Abba ya kalla inaaya yana fadin”maama na an gama karatu ko keda mimi” smiling sukayi sukace “eh abba” MashaaAllah ya fada sai kuma yace to yanzu addmission ake jira kuma duk baze in zakuje irin na yayyenku mata” harda sauri inaa
ya ta ce”abba wlh ni banason baze amma daddy yace bazanje wani kasa ba” dariya yayi “to mamana ko dai switzerland zan tafi daku sai kuyi karatunku a can da ke da mimi da zainaba” inteesar dake gefe tana pressing phone jin abunda abba yace ta dago “kai abba wa ce wani zainaba a nan” duk dariya suka fashe dashi a parlourn sai daddy ne ya goya mata baya “habaa inteesar sunan diyata, kuma ina kake ganin zaiyi a hada yaran nan makaranta daya ai sai an korosu makarantan kasan yanda suke idan sun hadu” yar dariya abba yayi “eh kuma fa hakane” daga kan kujera inaaya ta zamo kasa tana cewa “wallahi daddy Aa ba abunda zamuyi we’ll be good girls its a promise right girls?” With pleading eyes dukansu sukace “eh daddy it’s a promise” murmushi daddy sukayi da su ammah dake parlour sai daddy yace”To sai nagani dai”. Zaune suke dining karan spoons da forks kawai kakeji suna cin abinci kowa yayi shiru, steamed basmati rice suke ci with shredded beef sai chapman harda zobon inaaya a kan table in ammah babu wanda ya sha aneesah ce take ta kallon inaaya tana stucking out tongue tana nuna mata babu wanda yasha special zobon ta ai kam nan ta hade rai tana hararan aneesah daketa murmushi ko a jikin ta. Bayan sun gama cin abinci suka nufa dakin inaaya ta shirya kayanta suka fito da dan akwatinta karami tana ja sai da safe tayi ma mamii da daddy tana ta eyeing aneesah ita kuwa she’s finding it funny ma, har sun kai kofa sai ammah tace “kai nikam naga wani zobo a dining daxu ko zan tafi dashi in kai ma aliyu yanason zobo” da jin dadi inaaya taje ta dauko shi suka tafi.
Bayan sun isa gidan abba wanda basu fi 5minutes ba gidane babba duplex sai kuma two other chalets suna facing juna, kana shiga gidan parlour ne babba yasha royal chairs da carpet babba mai kyau very neat parlour in sai ka ce akwai mutane a gidan sai kamshi ke tashi , sai da safe sukayi ma ammah da abba upstairs suka nufa direct dakin dake na inteesar suka shiga daki ne babba da closet and toilet a ciki sai two beds suna facing each other komai na dakin pink ne different shades of pink. Hissing inaaya tayi hade da fadawa kan gado tana “i so hate this room imagine upon all colors wai pink” “hehhe naji thats how i wanted it to be” inji intee mimi dai kan couch in dake dakin ta fada ta kwanta sai kuma ta tashi tana “guys bamuyi sallah ba fa” nan suka tashi kowa ya gabatar da sallah isha suka dawo sai mimi ta ci gaba da cewa ” you know wlh i love the idea of going to switzerland for school Allah yasa daddy ya yadda nasan daya yadda ya gaya wa baffah babu wani problem” sai inaaya itama ta tashi zaune “eh wlh and I’m thinking kaman daddy zaya yadda wlh it’s going to be damn cool!” “Like really cool” cewar intee, so “what are we going to do girls?How about a game?” “Yess a game it is” mimi tace “ohhk how about twenty questions?” Inaaya tayi suggesting “so who’ll go first?” Intee ta fada sai mimi tace ” I’ll my first question is for you both and promise you’ll tell nothing but the truth” gyade kai sukayi sai tace “who are your crushes” “Aha ni dai it’s mr no one obviously” inaaya ta fada its kuma intee shiru tayi kaman tana day dreaming sai da suka tabota sai tace “oww sorry girls it’s no one actually” tana fada tana avoiding hada ido dasu “LIE Big fat lie” inaaya ta fada “oww come on sis your secret is safe with us” mimi ta fada in a teasing tone, rufe idanu tayi tace “ok ok I’ll tell you guys but promise you won’t tease me and no one will hear about it” a tare sukace “yess your majesty” rufe idanu tayi sosai tasa palm inta ta rufe fuska sannan ta furta “ya sa’id” a hankali “WHAAAAAAAAAAAAT!! Ya sai’doo” inaaya ta fadi da ihu “OMG!! So now I’ll not be teased alone yanzu nasamu partner” mimi ta fada tana dariya itama inaaya tayi joining inta sunata dariya suna teasing nata ita kuwa ta rufe fuska inaaya na fadin”sultaana needs to hear this but sai gobe idan tazo” inteesar tayi gathering courage tana enough guys lets continue, I’m next and my first question goes to mimz here it is, so if Erm! What’s his name again tafada in a teasing tone ehen! Ya habeeb asked you out what will you reply with” kafin ta gama question in nata ma mimi tayi turning red saboda blushing “come on intee why will you have to include HIM! In this convo?” Nan suka saka dariya intee da inaaya aka koma teasing mimi, a haka sukayita questionnaires insu suna teasing juna har 1 yayi sannan suka tashi sukayi changing into pj’s insu suka kwanta nan bacci yayi gaba da su.