INAAYA CHAPTER 8

INAAYA CHAPTER 8

                 Www.bankinhausanovels.com.ng 

Karfe tara suka tashi washegari duk a gajiye dai suke sukayi breakfast sai mai gyaran jikin amaren tazo aka fara gyaran jiki saura kuma duk sukayi wanka suka shirya cikin kayansu sabodaa babu wani event a ranan, saida suka shirya su duka da inaaya da aminnan nata sannan suka ce zasuje su dawo gidan abbah zasuje a parlour suka tarar da mamii da yen mutane kada suka gaisheta suka sanar mata inda zasuje tace to kar su dade tana so ta aike su suka amsa mata da toh sannan suka fita suka nufa gidansu inteesar inda mutanen are less dakin inteesar suka nufa bayan sun gaida Ammah ta amsa masu da fara’a ba jima wa duk suka kwanta dama bacci ya kaisu gidan dan sun san idan har suna can babu bacci, sai da sukayi baccin kusan 3hours karfe daya na rana suka tashi sukayi sallah sai a lokacin inaaya ta tuna da wani abu ta jawo wayanta tayi dialing numbern ihsan ringing hudu ta dauka tana cewa “hello yan hidiman biki ya dai” forming vex inaaya tayi tana cewa “ihsan wlh kin kyauta like sosai shine jiya na ji ki shiru ko” Murmushi tayi tace “habaa sorry sweetheart wlh maama ce ta hanani zuwa wai yayi dare sai dai yau, kinsan yanzu ma na gama shiryawa ina tunanin na kiraki nazo sai after kamu din maama tace sai na kira malam ya’u yazo daukana” smiling inaaya tayi tace “to! Kiyi sauri please mu ma yanzu zamu koma gida daga gidansu inteesar but please kiyi sauri” ihsan tace “ahh babbar bakuwa tazo kenan finally! I’ll get to see her not in labari”

sallama sukayi suka kashe wayan sai a sannan mimi tace “ni wlh inee sai yanzu ma na tuna da school mun dai samu an yi mid semester, let me call that useless girl ma, na ta binta tazo amma kinga bata zo ba yanzu zatace bata samu wanda zaya kawota ba from hostel” tana kiran firdausi kuwa hakan tace mata babu wanda zaya kawota sai anjima amma zata zo sallama sukayi su ma suka kashe wayan. inaaya ta sauka kasa zuwa kitchen saboda yunwan da taji bata kai da ida saukowa ba kaman ance ta daga kai ta hango aliyu zaune yana magana da Ammah har ramewa yayi nan da nan gabanta ya shiga duka da sauri sauri kaman zuciyanta zaya fado dan tunda suka zo yau ne farkon data ganshi, ba shiri ta juya zata koma da gudu taji Ammah ta kira sunanta babu yanda ta iya haka ta juyo ta karasa parlourn kanta a kasa tana wasa fa yan yatsunta ita kadai tasan halin da ta shiga Ammah tace “daughter ya kin sauko zaki koma kuma meya faru” muryanta na rawa tace “Amm…Amm..ahh da…maaa yun..wa yasa na sauko amma yanzu na daina ji” Murmushi kawai Ammah tayi tace “ba ayi haka ba an taba jin yunwa aka daina maza je kitchen ke nema abinci” da rawar murya ta amsa ta to tayi hanyan kitchen din sau Ammah tace “daughter kaman dai baki ga yayanku ba” a lokacin inaaya ji tayi dama kasa ta bude ta shiga saboda duk basu gane halin da take shiga idan ta ganshi da kyar ta juyo ta kakalo Murmushi ta kalla aliyu da yake zaune yana danna waya ko kallonsu bayayi tace “in…in…ina wuni ya aliyu” bai dago ba kawai yace “lafiya” ta juya da saurinta kaman gudu gudu ta nufa kitchen Ammah dai kallonsu tayi duka ta kada kai, tana shiga kitchen din ta nufa wurin sink ta tsaya hannu ta kai a chest dinta tana taba saitin heart dinta tana jin yanda yake bugawa gashi she hates the feeling with passion bata ankara ba taji hawaye ya silalo mata ta bude tap ta wanke fuskan ta tana dan siririn tsaki ta yi abunda zatayi ta fito kitchen din taji dadin ganin ba kowa parlour da gudunta ta koma sama.

Tun bayan zuwansu nigeria aliyu ya kara wani shiru maganan da kyar ake samu yayi har dan ramewa yayi daka ganshi kaga mai damuwa kwance yake a kan wani makeken gado bayan ya baro wurin Ammah ya nufa gidansu fareed ne, yana kallon ceiling yayi shiru sai aka bude kofa ko kallon kofan baiyi ba saboda yasan mai dakin ne ya shigo har wurin gadon fareed ya iso sannan yace “wai kai aliyu na kasa gane kan ka miye haka kakeyi ma rayuwan naka wallahi sometimes in kana wani abun sai ace bakayi ilimin addini ba” juyowa kawai aliyu yayi ya kalleshi baice komai ba haka fareed yayi ta mishi fadan shi har ya gaji ya kyaleshi ya zauna ya bude wayanshi ya kira khady suka cigaba da wayan su ya yi kaman ba aliyu a cikin dakin.

Wurin 2pm suka koma gidansu inaaya suka tarar da amare da kawaye yanda suka saba zama a dakin inaaya sukayi joining suna fira bayan sunyi lunch can sai ga ihsan ta kira inaaya tace mata tana kofan gidansu da jin dadi inaaya ta fita tarbo ta dasuka shigo saida ta kai ta parlour ta gaida mamii sannan suka nufa sama dakin inaaya suna shiga ta ajiye kan kujeran dakin tace ta zauna saida ta zauna da fara’anta ta gaishe dasu aleesha smiling ya ummi tayi tace “kaga mai hankali harda gaishe mu” dariya sukayi mimi tace “mu kuma mahaukata ko” aleena tace “eh something like that” sukayi dariya ihsan da kawai smiling tayi sai tace “ahh su mimi manya kwana dayawa ba a jin ki” smiling mimi tayi tace “kedai bari ihsan hidiman dayawa” da dariya tace “ke da inaaya yanda kuke fadin hidiman nan kaman ku zaayi wa auren ko kuma kune iyayen bikin” dariya kowa na dakin yayi sultaana kuwa forming anger tayi tace “sannu ihsan su kadai kika gani” dariya Ihsan tayi tace “habaa my sulty sorry wlh gaisuwan naki daban ne shiyasa nafara gaisawa dasu, ya kike and everything” sai a lokacin sultaana tayi smiling ta amsa mata da lafiya qlw sai ga inaaya data fita daga dakin ta shigo tace “Ihsan meet the greatest zainabuu that you’ve been hearing of” ta dan matsa gefe tana nuna wa ihsan inteesar dake Bayan ta ita kuwa inteesar ta harare inaaya ta wuce ta nufa wurin ihsan tayi hugging dinta tana cewa “finally got to meet you dear! It’s so nice” smiling ihsan tayi tace “ayy thanks babe nice meeting you too” suka gama gaisawa kaman sun saba suka dan fara surutu ba sosai ba duk da harda sauran yan dakin akeyi. Karfe 3 amare duk sunyi wanka za a fara masu makeup yau kam kowada mai makeup dinta photographer ma da me videography sunzo sun fara aikin nasu making video of how the event preparation is going on da kuma speech from friends da sisters sai kuma snapping din kayan amare daga clothes, shoes, jewelries komai dai da amare ke saka wa duk yana ta video yana dauka, Nate genius ne mai video din sai photographer kuma artilary photography ne shima ya fara aikin nashi, a daki daya ake masu makeup din kowa da side din da suke aleena lbvmakeover keyi mata sai aleesha kuma dazeita ita dai tanason makeup din dazeita simple sai ummi kuma genovera makeover duk sun fara magic din su a face din amaren su kam photographer da videographer sunata aikinsu na capturing. A can dakin inaaya kuwa masu makeup uku ne suna ma friends da sisters casual da rjtmakeup pro da bookie lavida sai ronaldthe7th, inaaya bataso yin makeup ba kawayen nata suka ce sai tayi da kyar ta yarda tace masu amma babu brows just lips sai little foundation and powder and little eyeshadow and eyeliner haka kuwa akayi mata amma sai kace tayi full make up sosai tayi kyau suka yita MashaaAllah suna yaba kyawu irin nata asoebe dinsu suka saka na sisters atamfa ne irin exclusive embellished super wax din
nan sai shining takeyi sun saka shi ne saboda kamu traditional event ne dinki sukayi duk iri daya wani simple fitted gown me dan tail kadan a baya da dogon hannu ba dogo sosai ba ya wuce quater dai dukkan an daura masu dankwali an hada shi da wani raw silk coffee haka an daura irin na zamani yayi kyau sosai

1

Khady👆👆 with her anko.

Duk sunyi kyau gwanin burgewa suka fara snapping pictures da wayoyin su, abokanan amare ma sunyi kyau anko din wani atamfa sukayi mai round shape light pink and light purple sai white ne color din atamfan tayi kyau sosai suma they all looked peng. A bangaren amare kuma wani iro and buba suka yi su duka na ya ummi coral sai ya aleesha red sai ya aleena coffee sunyi kyau sosai makeup dinsu yayi kyau sun gama shiryawa tsab! Photo session ya shiga don duk sauran yan matan sun zo dakin ganin amare tun anayi a daki har aka koma parlour ana photo session sannan aka kawo motocin tafiya mutane suka fara tafiya suma grooms din saida suka zo akayi photo session dasu suma sunyi kyau sosi ya mubarak yasa wani white shadda mai kyau ka kamshin cool turaruka yanayi da tsadaddar hula mai kyau, haka ya hilal shi kuwa irin yadin maza me kyau da tsada brown ya saka shima yayi kyau ba kadan ba, sai ya nazeer kuma yasha white shadda da aikin wani color kaman golden kaman ba golden ba duk sunyi kyau sosai tubarakallah sai wurin 5:30pm sannan suka nufa zuwa inda za ayi event din blue velvet marquee ne ga decoration din yayi kyau sosai, su inaaya already sunje wurin amare kawai suke jira ayi entrance din sai wurin 6:30 sannan amare suka shigo anyi grand entrance sosai yayi kyau friends ne farko sai some of the brides sisters sai brides sai sauran sisters duk kowa ya nema sit number dinshi ya zauna event ya cigaba and just like yanda akeyin kowane kamu haka akayi abun nasu yayi kyau da tsari kowa da souvenir nashi under seats aka ajiye su saidai mutun ya duba ya dauko nashi, ansha pictures dan iyayen amare ma baa barsu a baya ba duk sunyi attending ankon wani switzerland lace sukayi mai kyau iri daya kowa da color din nashi.Aliyu ne zaune gefe tunda yaje event din yake zaune shiru da phone sai faman pressing yakeyi sai daya gaji ya ajiye wayan can karshe ya hango fareed zaune da khadija sai faman gaya mata wani abu yakeyi tana blushing shi kuwa tabe baki kawai yayi, sai 10 sannan duk an watse mutane sai dai yasu yasu yan uwa suka dinga rawa har suka gaji inaaya dai dama wuri ta samu ta zauna dan tasan jiya da tasha rawa ciwon kafan da tasha. Zuwa 10:30 duk suka bar hall din suka nufa gida a gajiye suna zuwa sallolin su kawai sukayi suka saka nighties sunyi shirin kwanciya saboda gobe will be a long day tunda safe su abbah and others zaa tafi kano daurin auren ya sameer duk su ammah da mamii zasuje suma kanon da sauran yanuwan su daddy da maama saboda dauko amarya dayake shi babu wani event sai an kawo amarya Saturday za ayi budan kai sai dinner da dare, kafin kace me wasu sun fara bacci cikin su wasu kuwa da waya anata posting ana update duk suka gama around 12 duk sunyi bacci.

Washegari karfe 7 inaaya ta tashi duk yawanci su basu tashi ba fitowa tayi daga dakin ta ta nufa dakin mamii ta tarar ba kowa dakin har an gyara shi Ac kawai ke tashi da kamshin turaren wuta zama tayi a kan  bed din for kusan 10minutes dan tasan mamii na closet definitely har ta tashi zata tafi sai taji an tura kofar closet din mamii ta fito sanye da wani voile blue da golden tasa sarkanta  da dan kunne da bangles na gold sunyi mata kyau ta fito da laffaya golden a hannunta tana ganin diyar ta ta tasakin mata murmushi inaaya tace “mamiii ina kwana, kinganki kuwa yanda kikayi kyau kaman ba ke kika haifa tsohon ya sa’id dinnan” dariya mamii abun ya bata sai tace “lafiya lau inaaya, har kin tashi, yo ai ba sa’id kadai ba sai ace yarana daga aneesah sai twins” pouting inaaya tayi tace “kaii mamii yanzu ni ya zaayi ace ba ki haifeni ba yar karama da ni” murmushi kawai mamii tayi mata sai tace “ke kin girma baki barin shagwaba dama tun jiya ina son nayi maki wani fada amma naga kun shiga busy ko” yar dariya tayi tace “wlh kuwa mamii” sai mamii tace “fatima” tana jin ta kirata da sunan ta ta san serious abu ne ta sha jinin jikinta mamii ta cigaba “kinsan ita a rayuwa kowa da yanda Allah ya tsaro mishi kuma duk abunda kaga Allah yayi maka ko miye ka gode mishi kila shine mafi Alkhairi a rayuwan mutun, ana so a kullum mutun ya zama mai tawakkali da abunda allah yayi ka rungumi kaddara hannu bibbiyu da mai kyau da mara kyau” tunda ta fara kan inaaya na kasa tana sauraronta sai mamii ta cigaba “kuma kinsan cewa mu iyayenki a kullum masu son ki ne kuma baxa mu taba abunda zaya cutar dake ba hope kinsani” kai inaaya ta gyada tace “eh mamii ai nima banida kamar ku amma mamii miye ya faru kike cewa haka” smiling mamii tayi tace “yayi kyau, to saida wani abu zan yi wa diyata fada? Hakanan fada ne from mother to daughter, Allah yayi miki albarka” murmushi inaaya tayi tace “to amin mamii yaushe ne flight din ku” mamii tace “karfe 10 ne shiyasa na shirya da wuri yanzu zamu wuce airport anjima kuma jirgin 4 ne InshaaAllah zuwa 5 dai muna abuja” inaaya tace “toh! Mamii’am Allah ya kiyaye hanya” ta amsa mata da amin sannan inaaya ta tashi ta nufa dakin ta tana zuwa taga duk sun tashi yawancin su har wasu sun fara wanka mimi tace “malama ya dai ina kikaje tunda safe” kallonta inaaya tayi tace “ikon Allah yanzu dan na bar daki sai anyi questioning dina to zance na fita” dariya ta basu kowa na dakin ya fashe da dariya inteesar tace “wayyo Allah cikina! Har naga inaaya na zance” sultaana ma dariya tayi tana cewa “hmm! Big show kenan” aleena dake kwance kan bed tace “lallai yara zakusha mamaki yo bata isa ba ko bata iyawa kuke nufi” haneefa tayi dariya tace “aa wai dai kawai dai” sukayi dariya ita kuwa inaaya daurewa tayi bata sake ce musu komai ba.karfe 1:00pm aka daura auren sameer sulaiman abubakar geidam da nabilah mujahid sidi akan sadaki dubu dari sosai sameer yake murna yana farin ciki bayan an gama suka je gidan su amaryan da abokanshi da cousins dinshi maza akayi hotuna karfe 3 bayan reception aka fara shirin tafiya airport saboda 4 ne jirgin, amarya tasha kuka sosai da za a tafi da ita tasaka wani alkyabba peach kawayenta su 10 da iyaye 10 da sisters dinta sukayi mata rakiya.

+

           Duk a gidan baffah suka wuni yau saboda wani dan kaman mothers day amaren sun sha lace kowa da irin nata da irin bridal veils dinnan masu kyau ga kida na tashi dj ya saki sauti gidan ya cika ya cika sosai daga waje har ciki saboda duk harda su mommy da Ammi da dangin iyayen su aleena da ummi suka zo anci ansha sosai anyi hotuna zuwa yamma duk mutane sun rage sosai. Karfe 5:40 su mamii suka sauka garin abuja daga kano da amaryar sameer nabila da kawayenta da iyaye da yan uwa gidan abbah aka nufa da ita inda mahaifiyar ango take da yan tarban amarya saida aka kaita wurin mama sannan sai gab da magrib aka kaita part din su naseer da aka gyare don ajiye amarya saboda anan zata zauna for the time being bayan biki zasu koma kano inda yake aiki da gidanshi a can.

               “Intee! Please kuyi sauri time is going ya khady just called” inaaya ta fada da karfi dan intee ta ji sun gama shirin su na dinner tsab! Anko ne wani fabric navy blue yayi kyau sosai brides world ta fidda masu anko din na sisters ne kawai fitted gown ne dinkin sai wani chiffon da aka sa ta gefe an sake shi yana jan kasa gown din tazauna mata sosai a jiki shape dinta ya fito sosai an daura mata head tie din nata very simple but elegant dan touch up ne a fuskanta amma tayi kyau ba kadan ba da dan clutch a hannunta silver da takalmi dan low heel su ma silver komai nata simple but classy she’s the real definition of beauty komai nata MashaaAllah. Su inteesar da mimi da sultaana suka sauko suma duk da anko dinsu sunyi matukar kyau ba kadan  ba a tare sukayi waje suka tarar da ahmad yana jiransu dama sun ta rokinshi akan ya dawo ya kaisu bayan ya kai su aneesah
motan suka shiga suka kama hanyan zuwa hall din suna isa suka fito ya khady suka gani wurin kofan hall din inda ake arranging for entrance din aneesah da saleema ne a gaba suma sun sha anko dinsu sunyi kyau sai ya aleena da ya hilal wani bustle gown tasaka grey yayi kyau sosai da silver jewelries angon yasa shadda ash da black hula da takalma sai bayansu friends dinta da abokan ya hilal sun jero sai su inaaya suka jero sai ya ummi itama bustle gown me fabric din milk da maroon  da head dinta maroon angon yasa brown shadda sai kawayenta da abokanan ango a bayansu sai su khady sai ya aleesha itama bustle gown ne fabric din nata cream da purple sai purple head ango yasaka white yadi na maza mai kyau sai baya kawayenta da abokan ango, haka sukayi entrance din nasu yayi kyau har amare suka iso inda aka tanadar masu su zauna friends ma kowa ya zauna kan table din friends aka fara event ansha rawa har couple dance aka kira amare aka saka masu say you won’t let go by  james arthur sukayi wani slow dance anci ansha sosai ba kadan ba wurin grand dinner dinnan komi kakeso zaka samu foods,snacks,desserts komai dai da pictures sosai sun gayyaci big h studio yayi covering event din the dinner was grand, fun and enjoyable sunsha rawa sosai. Aliyu tunda yaje wurin dinner din zaune yake wuri daya yasa wani shadda sky blue mai kyau kaman shima angon ne tare da fareed da sauran cousins dinsu suka zo bayan sun dawo daga daurin auren sameer, shiru yake yana ta kallan yanda suke ta rawa cikin rawan ya hango su inaaya inteesar nasaka ta dole tayi rawa idonshi was fixed on her ya kalleta sama har kasa ya dan tabe baki baice komai ba, Sai 12 aka tashi daga wurin event din suka koma gida a gajiye sosai suka gama sallah suka yi shirin bacci sannan suka zauna suna ta fira ana maida yanda akayi sai wurin 2 sukayi niyyan bacci kowa yayi bacci banda amaren da duk sun kasa bacci kwance kawai suke amma ba bacci aleena ta tashi ta shiga toilet ta dauro alwala ta fito ta kabbara sallah tayi nafila 2 raka’ats ta gama tana ta adduan zaman lafiya da kwanciya hankali ummi da aleesha ma suka tashi duk suka dauro alwalan sukayi nafilan nasu sannan suka samu bacci ya dauke su, karfe 3:30am inaaya ta farka saboda duk a takure take baccin duk bata jin dadi ta rasa me yake mata dadi ta tashi zaune ta kwanta har kusan awa daya sannan ta shiga tayo alwala tazo ta kabbara ta dinga salloli har kusan asuba sannan ta bude drawer ta dauko qur’ani ta fara karantawa a hankali har aka yi kiran sallah sai ta rufe ta tashi ta gabatar da sallahn ta sannan ta fara tada yan uwan nata duk sunyi mamakin yanda batayi bacci ba tace masu kanta ke ciwo kawai sannan ta koma ta kwanta bacci ya dauketa wurin 8:00am ta tashi saboda haya niya duk kowa ya tashi taga anty fareeha a dakin tana saka su aleena su tashi suyi wanka su gama shiri ayi masu makeup yanzu lokaci ya kusa 12:00pm ne daurin auren a an noor mosque, jiki a sanyaye duk suka tashi kowacce daka ganta kasan jikinta yayi sanyi don sunsan yau duk za a kai kowacce dakinta haka suka tashi jiki ba kwari mai gyaran jiki tazo tayi masu na karshe sannan duk suka shiga wanka a different bathrooms din gidan.²⁰

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *