ITACE QADDARATA CHAPTER 10
A ranar Hajiya ta tafi Zaria,Sosai Maman khairat taji dad’in zancen da tazo mata dashi,”Amma sai naga kamar Imran yayi yaro da aure gwara khairat” “Ba wani yarinta,Imran na da hankali nasan zai iya rik’e khairat,fatan mu kawai Allah ya basu zaman lafiya” “Ameen Ya Allah” Sun tattauna sosai akai ,kuma sun yanke shawarar sa rana nan bada dad’ewa ba,A ranar ta koma,ba yadda Maman khairat batayi da ita ba ta kwana,Tak’i tace a ranar take son komawa. Naseer na tafiya,Shima Imran ya tashi ya nufi gida dan ji yayi bazai iya cigaba da zaman office d’in ba. Noor da ta bar d’aki,Kitchen ta nufa,ta tarar an tara kayan wanke-wanke ta hau wankewa,Bayan ta gama tasa hannu suna aikace-aikacen kitchen,a ranta tana tunanin maita irin ta Yazeed,a ranta tace “ko kafi k’oda naci In shaa Allahu ba zaka samu abunda kake so ba” Sai da suka gama aikin kitchen tas,ta koma d’akinta,ta share inda kwalba ta fashe, Ta kwanta kan katifarta,ita kanta yau bata ci lunch ba,ta riga ta saba tare da Imran suke ci,Cewa kanta tayi “Noor ki ma kanki fad’a,kima dawo da cin abinchi ke kad’ai kamar yadda kika saba, dan Imran ya kusa zama mijin wata daga ya aureta kuma shikenan,ganinshi ma wuya zai rik’a miki” Wasu zazzafan hawaye taji sun zubo mata “Ya Allah! Ka cire mun abunda nake ji a raina game da Imran”. Tsakanin Imran da Yazeed yanzu sai sama sama,basa zama suyi hira kamar da,Yazeed shakkar Imran yake,Imran kuma najin haushin shi Yazeed na zaune falo yana kallo,Imran ya shigo tare da yin sallama, Yazeed ya juyo ya kalleshi tare da amsawa yace “Yaya sannu da zuwa” “Yawwa sannu,me ya samu goshinka ko wata kaje dannewa ta bugeka?” Yazeed sai da hanjin cikinshi suka bada k’olulolo ya d’an yi dariyar yak’e,Yace “No wlhy,bugewa nayi da bango” “Hmmm toh Allah ya sawwak’e” “Ameen” Ya wuce d’aki ya barshi nan,Yazeed sai hamdala yake da Imran bai gano shi ba. Ruwa ya watsa,ya chanza kaya,ya fito ya nufi garden,ya aika a kira masa Noor Da d’an aike yazo,Noor har tayi niyyar tace aje ace mishi bacci take,sai kuma taji tana son ganinshi Hijabi ta zura,ta nufi garden Tun da ta shigo garden d’in yake kallonta har ta samu wuri ta zauna,Idonta ya kumbura yayi jajir tsabar kuka ganin haka ba k’aramin d’aga mishi hankali yayi ba Yace “Noor me ya sameki? Me aka miki? Wa ya tab’aki?” “Kaina ke ciwo” ta bashi amsa a tak’aice “Banda abunki Noor kanki na ciwo,ai sai ki gaya mun baki ta kuka ba,baki san kuka na k’ara sa ciwon kai ba,tashi muje a siyo miki magani,daga nan mu zagaya gari” “A’ah Imran barshi nasha panadol,yawo kuma ba sai munje ba” “A’ah ki bari muje dai kiga likita,sai muje kisha ice cream” “Imran kenan ya kamata tun yanzu mu rage sabawa da juna,mu d’an rik’a nisa da juna” A kid’ime ya kallo ta yace “Akan me?” “Ka kusa zama mijin wata,kuma da kayi aure shikenana fah ,dole ka zauna gida tare da matarka” “OMG! me yasa kika tuna mun da zance nan,ni fah bazan auri khairat ba,kuma ko na aureta ba abunda zai canza daga alak’armu” Da mamaki take kallonshi “ba zaka aureta ba?” “Ni dai plxx ki bar zancen nan tashi muje” “Ni fah ba inda zani” “Haba Noor me yasa kike haka,yanzu so kike na nisanta kaina dake?” Ta gyad’a kanta sama “Wlh bazan iya ba Noor,ko nayi aure bazan iya ba,ballatana a yanzu da banyi ba,plxx Noor kar kice haka” Ya fad’i maganar cike da damuwa Kawai taji ya bata tausayi,itama tana tausayin kanta dan rashin Imran a kusa da ita babban cuta ne,Tace “Muje” tana d’an murmushin dole Sosai farin ciki ya bayyaa a fuskar Imran Yace “Yawwa ko ke fah” Ya kaita chemist ya siya mata maganin ciwon kai,sannan suka je wuraren shak’awata da NEXT ya mata siyayya tare da siyan mata kayan k’walama Sun dawo gida cike da nishad’i,damuwar da Noor ke ciki ta rage sosai. Khairat ce zaune gaban madubi,tana ta tsara kwalliya,Ihsan tace “Wai ina zaki kike ta kwalliyar nan?” “Ina zani da ya wuce wajen Yayana” “Lallai fah masu Yaya,Allah dai ya nuna mana aurenku mu sha biki” “Ameen yar’uwa” ta mik’e tsaye “Ya kika ganni nayi?” Tana jujjuya wata doguwar riga ce a jikinta material,ta mata kyau charas charas, “Wow kin had’u sis,wannan ai sai kisa Ya Imran ya rikice” Khairat ta k’yalk’yace da dariya,kanta ya k’ara girma Turare ta sake fesawa,ta gyara d’aurinta tace “sai na dawo” “A dawo lafiya”. Bayan sun dawo d’aki yaje ya kwanta yana huce gajiya,Da sallama khairat ta shiga d’akin Ba tare da ya d’ago ba ko ya kalleta,Ya amsa sallamar,ya gane muryarta “Yayana sannu da hutawa” ta fad’a tare da zama kan kujerar kusa da gadon “Yawwa sannu k’anwata” ya fad’a tare da kallo ta,Sosai yaga ta mishi kyau Ya mik’e zaune yace “k’anwata wannan kwalliyar sai ina?” Ba kunya tana murmushi tace “kai nama Yayana” “Ni! Lallai k’anwata toh nagode kuma kinyi kyau” (tausayinta yake ji,yana ganinta marainiya shiyasa yake k’ok’arin yin duk abunda zai faranta mata rai) Sosai taji dad’in yadda ya yaba mata,tayi murmushi tace “nagode Yayana” Haka suka cigaba da hira mai dad’i,Khairat nayi na sako kalaman soyayya a ciki,hakanan Imran ke daurewa yana mayar mata kalaman,Dad’i duk ya gama lullub’eta. Noor tana bubbud’e kayan,taga ledar kayanshi an had’u da ita,Tace “wannan kayan Imran ne bari na kai mishi” ta mik’e. “Yayana kana sona kuwa kamar yadda nake sonka?” Noor tasa kai kenan cikin d’akin, taji Imran na cewa “Ina sonki sosai k’anwata fiye da yadda kike sona ma” (ya kawai fad’a ne amma ba har zuci ba) Da sauri ta juya ta koma,sai hawaye shaaa Kan katifar ta,ta fad’a tana kuka sosai,tana tuna kalaman Imran kukanta na k’aruwa sai da tayi mai isarta sannan ta dawo hayyacinta take tambayar kanta “To ke Noor meye na kuka? Me ye naki a ciki dan Imran na son Khairat? D’an mijinki ne fah” Tai saurin goge hawaye taja siririn tsaki “me zai sa na b’ata lokaci har ina kuka”. Kwana biyu Yazeed bai waiwayi Noor ba duk yana cikin plan d’inshi, Da yamma lokacin Imran ya dawo daga office Yazeed ya siyo kaza,da youghurt mai sanyi,ya zuba maganin bacci mai nauyi a ciki Ya ba Abu yace ta kaiwa Noor tace inji Imran “Gashi inji Imran” ta ajiye mata,bata jira me zata ce ba,tasa kai ta fita Ta bud’e ledar,a ranta tace Allah sarki Imran Dama yunwa take ji,ta hau ci,ta kura da youghurt Hamma ta fara,wani irin bacci ta fara ji,tashi tayi ta rufe d’akin tasa key,tabar key a jiki bata cire ba In less than 1min bacci ya d’auketa Bayan kamar minti sha biyar,Yazeed ya shiryu yana lasar baki “Yana yau zan fad’a kogin dad’i,damo zai kai ga harawa,yau zanyi yadda nake so dake” Yana ta waige-waige yaga ba kowa,ya murd’a k’ofar a rufe,ya fiddo spare key yasa yak’i shi(kunsan tabar key a jiki)yai ta sawa yak’i shiga,Ya lek’a yar kusurwar,yaga a rufe Tsaki yaja tare da buga k’afa yace oh shit! Damn it! Yace “idan yau kin kub’uta next time bazaki kub’uta ba wlhy” Ya tafi yana cizon yatsa,plan d’inshi yayi ruining. Khairat na nunawa Imran so har na fitar hankali,ganin irin son da take mishi yasa take bashi tausayi shima yana kulata,Sukan zauna suyi hira,su fita yawo Tana k’ok’arin ganin ta rabashi da Noor,buh still Imran na nan manne da Noor,sai dai sun rage zama tare,saboda khairat tayi kane-kane,Abun na damun Noor,idan ta gansu tare sai dai tayi ta kuka tana cewa tun yanzu sun fara rage zama toh ina ga idan yayi aure. Yau weekend Imran na gida,Suna zaune garden da Noor suna hira cikin nishad’i da kwanciyar hankali,Yace “In shaa Allahu ranar monday zanje makarantar da nake so na nemar miki,kiyi JSCE,idan yaso sai ki fara daga SS1,Zaki iya yi dai ko?” Wani dad’i ya lullub’eta ta gyad’a kai sama “Eh zan iya” “Toh Mashaa Allah,In shaa Allahu zan siyo miki text books da zasu yi helping d’inki,kuma zan rik’a miki lesson” “Nagode so….” “Shhhh” ya katseta “Anything for you” Tayi murmushi tare da jin son Imran na ratsa dukkan sassan jikinta,ba tare da tasan SON SHI bane Khairat ce ta shigo garden d’in tana yatsina fuska dama tasan a tare zata gansu Kamar an soketa da kibiya haka taji da taga yadda suke hira cikin nishad’i,tana rangwad’a ta k’arasa wajen su “Yayanah kazo muje ka kaini saloon” “Haba k’anwata kije driver ya kai ki mana” Wani k’ulloton bak’in ciki taji yazo ya tokare mata wuya,ta juya ta tafi, a ranta tana cewa “Saboda banzar nan zaka ce naje driver ya kaini” D’aki ta koma tana hawaye “Lafiya sis cewa yayi ba zai kai ki ba?”Ihsan ta tambaya “Ni wlhy Noor na shiga gona ta da yawa,na tsaneta na gaji da ganinta cikin gidan nan,wai Alhaji ba zai saketa ba kowa ya huta” “Hmm ai da zai iya sakinta da tuni Hajiya tasa ya saketa amma tunda kika ga Hajiya ta sa ido,toh kowa ma ya zuba ido” “Toh ni kuwa ko Alhaji bai saketa ba da k’afarta zata bar gidan nan,zo kiji” Ta rad’a ma Ihsan magana a kunne suka yi shewa,suka tab’a. Daddyn Noor,da mummy da k’annenta sun manta da wata wai ita Noor,harkokinsu kawai suke suna cin duniyarsu da tsinke,Sana’ar caca nata habbak’a ,yana ganin ya rabu da tsiya(Noor),Baba mai gadi kuwa kullum cikin kewar Noor yake yana addu’a “Allah yasa can tana samun kula bata wahala”. Hajiya ce ta fito daga d’akinta tana masifa, “Uban wa ya shiga d’akina ya d’aukar mun sarkar gwal da yan kunne” Ihsan,Khairat da Iman ne suka fito a tare Ihsan tace “Sark’a kuma mummy kin duba ko’ina?” “Sosai ma kuwa na duba,ko kira mun masu aikin gidan nan” Iman ce ta tafi kiransu, Noor na kwance a d’aki coz Imran ya fita,ya tafi gidansu Naseer “Ki taso Mum na kiranki” Jiki na rawa ta mik’e dan tasan kiran Hajiya ba alkhairi bane Duka masu aikin gidan sun hallara,suna duk’e gaban Hajiya hadda Noor Hajiya ta nuna su da yatsa “Cikin ku waya shiga d’akina ya daukar mun sark’a da yan kunne” Nan fa kowacce ta hau rantse-rantse ba ita bace “Sark’a zata d’auki kanta ne,wacce ta d’auka tun wuri ta kawota,idan ba haka ba,idan nasa aka binciki kayanku aka gani,ko wacece zata fuskanci hukunci mai tsanani” Dukkansu ba wacce ta motsa,rantsuwa suka cigaba da yi Noor ita dai jikinta ne yayi sanyi duk da tasan ba ita bace Hajiya tace “Ihsan kuje ku bincika mun kayansu,ku kuma ku tsaya nan har su dawo”Ta koma kan kujera ta zauna tana karkad’a k’afa. Suna fita suka tab’a suka kashe,Khairat tace “Yau zata ci ubanta” Ihsan tace “ke dai bari yar’uwa” Bayan mintuna kad’an suka dawo da sark’a suna salati Hajiya ta mik’e tsaye tace “A ina kuka gani?” Iman tace “hmm mum abun mamaki ko da yake ba abun mamaki bane,a kayan Noor” Hajiya ta rafsa salati tana tafa hannu”La haila ha ilallahu Noor sata kika koma” tayi kanta ta wanketa da lafiyayyan mari sai da ta fad’i Ta rik’e kumatunta,tana hawaye ba marin ya mata zafi ba, sharrin satar da aka mata,Ita da ko tsinke bata d’auko ba amma yau ance ta saci sark’ar gwal,Tace “Wallahi tallahi ba ni ba….” kafin ta k’arasa hajiya ta kai mata wani wawan naushi a baki “Yi ma mutane shiru munafukar Allah,Yau Allah ya toni asirinki ,kud’ina ma da ake sacewa nasan ba kowa bane face ke,kin zamar mana annoba cikin gida” Noor kukan bak’in ciki take,Zuciyarta na k’una kamar zata fito, Masu aiki kowa na tofah albarkacin bakinsa,Su khairat na zaginta da fad’a mata bak’ak’en maganganu Hajiya tace “Yau zan hora ki dan ya zama darasi ga yan baya” Yazeed ne ya shigo yana tambaya “me ya faru?” Iman ce ta fad’a mishi abunda ya faru Yayi murmushi a ranshi yace “ga wata dama na samu da zan cimma k’udirina” Ya kawar da tunanin yace “Tunda tace ba ita bace,ku bani 1min na keb’e da ita xanji gaskiyar al’amarin” Khairat tai saurin cewa “wane gaskiya,abunda k’iri k’iri a kayanta muka gani” “Me kike ce na baka na zuba,Noor biyoni” Addu’a su khairat keyi “Allah yasa kar plan d’insu yayi ruining”. “Noor nasan bake kika yi satar nan ba,sharri aka miki dan haka ki bani had’in kai,idan har kika bani had’in kai na miki alk’awarin wanke ki daga sharrin da aka miki,idan kuma kika k’i zance tabbas ke kika yi satar nan har in bada gudunmuwa a hukuntaki” Murmushin takaici tayi tace “kayi asara Yazeed,to bari kaji ko za’a yanka naman jikina gunduwa-gunduwa wlh tlh bazan baka had’in kai,Allah na nan shi zai wanke ni,bana neman kariyar kowa sai ta Allah” “Haka kika ce zaki ci k’wal ubanki kuwa” Ya zare belt zai zuba mata,tai saurin rik’ewa ta nuna shi da d’an yatsa “Ahir! d’inka da akayi wannan lokacin da nake ganin mutuncinka amma yanzu bana ganin mutuncinka ko na sisin kobo,mutunci madara ne idan ya zube bai kwasowa,kana dukana zaka ga abunda zan aikata ma” Gaba d’aya jikinshi yayi sanyi,ya tsaya yana kallonta da mamaki,ya fisge belt d’in a hannunta ya koma cikin falo,ta biyo bayanshi “Mum ita tayi satar nan,wlh ki hukuntata yadda gobe ko sweet ta gani ba zata d’auka ba” Yazeed ya fad’a Noor a ranta tace “Allah na nan shi zai mun sakayya” Hajiya ta fisgo Noor,ta jata xuwa kitchen,Duk suka biyo bayan Hajiya,Serving spoon ta d’auko irin flat one d’in nan,ta kunna electric cooker Ta d’aura a kai sai da ya d’au zafi rau,yayi jajir Ta jawo hannu Noor,ta manna mata a tafin hannunta,Tana ihu tana kuka,tana k’ok’arin k’wace hannunta,ba tausayi Hajiya ta cigaba da manna mata Ba mai ba Hajiya hak’uri sai ma k’ara zugata da suke Tana sawa a wuta,tana manna mata a hannu,sai da hannu Noor ya sale duk ya k’one,yana ta jini sannan Hajiya ta sake ta Tace “wannan shine hukuncinki yan baya sai ku koyi darasi” Noor ta duk’e nan k’asa rik’e da hannunta tana kukan azaba,ba wanda ya kulata,Kowa ya fice sai Yazeed Yace “kinfi son haka akan ki bani had’in kai?” Tai banza dashi ,Ya juya ya fice. Ta mik’e ta koma d’akinta,tana kallon hannun yadda yayi,sai rad’ad’i yake mata tana kuka Ta hau magana ita kad’ai “bazan iya da azabar nan ba da cin mutunchi,tafiya zanyi na bar gidan nan,nafi son nabi duniya da na cigaba da zama gidan nan” Duk wani mai imani yaga Noor a yanayin nan dole ta bashi tausayi”. Imran suna zaune,suna hira da Naseer,kawai yaji gabanshi na fad’uwa “Naseer gabana ke fad’i,ina ji kamar ba lafiya ba” “Kar ka damu ba wani abu bane abokina” “No naseer,bari na tafi gida,ina ji a jikina ba lafiya ba” “In shaa Allahu lafiya zaka tarar da kowa,ba wata matsala” “Allah yasa friend” “Ameen sai munyi waya” Su khairat,a d’aki sai dariya suke suna murna,Plan d’insu yayi,Khairat tace “kunga Yayana na dawo aka ce mishi sata tayi,mutunchinta zai zube a idonshi k’ila har tsanarta sai yayi,shikenan ba zance wata alak’a tsakaninsu,mu kuma kinga sai mu samu damar azabtar da ita da kyau tunda ba mai tareta ,har sai ta bar gidan nan dan kanta” Ihsan tace “Very gud idea,kanki na kawo wuta fah” Sukayi shewa. Imran hankalinshi duk ba’a kwance ba ya shigo gida Sashen Hajiya ya nufa,Ya sameta a falo zaune tana shan kayan marmari,tana kallo hankali kwance,Ajiyar zuciya yayi(hakan da ya gani ya tabbatar mishi lafiya) “Mum sannu da hutawa” “Son Ya kake? Ina ka shiga ne tun d’azu ban ganka ba” “Lafiya lau,ina gidansu Naseer” “Kai mai kare Noor baka had’ata da kowa ba,toh ka sani b’arauniya ce,har d’akina ta shiga ta saci sark’ar gold” Kamar an watsa mai ruwan zafi haka yaji zancen Hajiya “Wallahi mum Noor ba b’arauniya bace sharri aka mata” ya k’arasa maganar kamar yayi kuka “Dama haka zaka ce” Da sauri ya mik’e Yace “ina zuwa” D’akin Noor ya nufa da saurinshi har yana tuntub’e Noor har a lokacin kuka take tana kallon hannunta, inda take ya durk’usa idon shi ya sauka kan hannunta,a firgice ya kamo hannunta yana cewa “Wa ya miki wannan Noor? Waye ya k’ona miki hannu? Wane azzalumin ne?” Kukanta ne ya tsananta ta kasa cewa komai Shima tuni ya fara hawaye,yana kallon hannunta zuciyarshi na k’una da tafarfasa,ga mugun tausayinta da ya kama shi Yana kuka,a fusace yace “ki gaya mun Wa ya miki wannan abun? I swear i won’t spare that person” Ya k’arasa maganar yana huci,hawaye na zaba daga idonshi. …….. Bata bashi amsa ba, hawaye ne kawai ke kwaranya daga idonta “Please ki gaya mun wane ne?” “Hajiya” ta fad’a da shesshek’ar kuka Ya saki hannun ta da k’arfi ya mik’e, ya nufi hanyar fita “Ina zaka Imran? Don’t do something stupid mahaifiyarka ce” bai tanka ta ba, ya fice Ta durk’ushe nan tana kuka tana fad’in “Oh Allah! Gani gareka ka samar mun mafita”.+ Da k’arfin tsiya ya turo k’ofar falon Hajiya,sai da taji tsoro Gaba d’aya fuskarshi ta chanza tayi jajir,sai huci yake, yana maida numfashi da k’yar, jikinshi na rawa Yace “Mum why are you so heartless?, mum ina tausayinki da imaninki suke? Wlhy mum ban tab’a tunanin rashin tausayinki ya kai haka ba, ban tab’a jin na tsani kasancewa ta d’anki ba sai yau, Mum why? Why? Mum me yasa kike haka? Ba zaki ji tausayin marainiyar Allah ba, wuta fah kika sa kika k’onata, zaki yi iyawa Iman ko Ihsan haka? na tabbata idan sune sukayi satar nan wlhy bazaki k’ona su ba, ballatana ita da ba ita tayi ba, sharri aka mata, ko ita tayi wannan hukunci ya mata tsauri, wlh tlh idan na gane wanda ya mata sharrin nan dat person must pay for it” ya k’arasa maganar yana dafe zuciyarshi da yaji tana mishi zafi, jiri na neman d’ibarshi Hajiya tunda ya fara magana jikinta yayi sanyi (bata tab’a ganin Imran yanayi irin na yau ba, gaba d’aya ta tsorata da ganinshi, tana masifar son Imran bata son abunda zai tab’a shi) Da sauri ta k’arasa inda yake ta rik’o shi tana cewa “Kayi a hankali imran” Ya cire hannunta a jikinshi yace “its okay, Am fine” Ya juya ya fita Hajiya tabi bayanshi da kallo,Yau ce rana ta farko da ta fara nadama akan abunda tama Noor ba don komai ba, sai yanda taga Imran, Addu’a take Allah yasa kar wani abu ya sameshi, tana kuma mamakin yadda yake masifar son Noor Duk abunda ake su Khairat naji daga d’aki coz da k’arfi yake magana, Haushi duk yabi ya cikasu, kuma sun tsorata da jin yadda Imran ke magana, abunda yafi tsorata su shine da yace idan ya gano wanda ya mata sharri………… D’akin Noor ya koma, Ya k’arasa inda take “Sannu Noor tashi muje asibiti” Da hannu d’aya tasa hijabi Ya bud’e mata k’ofa ta shiga, ya mayar ya rufe ya koma driver’s seat Yana ta lallashinta, yana bata hak’uri *Manan Specialist hostipal* Asibitin Dr.Aysher Basma(DANGIN MAHAIFINA) suka nufa Basu samu ganinta ba lokacin ta tafi kaduna(d’ayan asibitinta) D’aya daga cikin k’wararrun likitan asibitin d’an india Dr.Aditya yayi treating d’inta, shi kanshi ta masifar bashi tausayi, yana cewa waya mata haka? Da a k’asar sune takai k’ara, Sai an d’aure mutum Ya gama treating d’inta, wurin aka sa bandage aka rufe, ya rubuta mata drugs Imran da Noor suka mishi godiya sosai, suka tafi A mota Imran ke k’ara bata hak’uri “Noor ki k’ara hak’uri komai kika gani muk’addari ne daga Allah, duk wahalar nan da kike shiga watarana sai labari, nasan baki yi sata ba sharri aka miki, wlh idan na gano wanda ya miki sharrin nan ba zai ji da dad’i ba” Noor murmushi kawai tayi, matsayin Imran na k’aruwa a zuciyarta, tabbas babu mai sonta a duniya kamar Imran, wa’inda aka k’onata a gabansu basu ji tausayinta ba, shi da ba’a gabanshi akayi ba hadda kuka, ji yadda ya tada hankalinshi, Duniya bani da masoyi kamar Imran, ta sake yin wani murmushi, Zuciyarta ta wani harbu akan Imran(SO) Imran a ranshi masifar tausayin Noor yake ji, da sonta da ya dabaibayeshi, tunaninshi hanyar da zai bi ya taimaketa ta fita daga wahalar nan yake. Da suka koma gida, zama yayi a d’akinta, yana ta jan ta hira, yana bata labarai masu sanyaya zuciya da kwantar da hankali, Kiran sallar magrib da yaji yasa shi tashi ya fita Sashen su ya nufa, Ya rage rad’ad’in da yake ji sosai sbd Noor ta daina kuka har tana dariya, Ya fad’a kan gado tare da yin ajiyar zuciya, “WAYE YAMA NOOR SHARRIN NAN? WHO COULD DAT PERSON BE? WHO? WHO?” Ya kasa kawo kowa a ranshi Ya kawar da tunanin yace “yanzu ya zanyi, na taimaki Noor, ta fita halin k’uncin nan da azabtarwa?, its pain me alots naga ana azabtar da ita, Wlhy ko shara na tsani naga tana yi, Zuciyata zafi take” Ya d’an yi shiru yana nazari tare da buga kanshi,sai can Yace “Yes i have an idea” Yayi murmushi Alwala ya tashi yayi, ya gabatar da sallar magrib tare da yin nafila, ya zauna yana karatun Qur’ani har aka kira isha’i, Yana idar da sallar Isha’i Ya d’auko wayarshi ya kira Dr.Moha (suka gama magana ya ajiye wayar tare da mishi godiya) Gado ya hau,yaja bargo ya rufe kanshi. Bayan mintuna kad’an, sai ga Khairat ta shigo rik’e da tray na abincin shi, ta ajiye kan centre table “Yayana tashi ga abincinka” Wani irin numfashi ya rik’a yi, Da sauri ta k’arasa inda yake tace “Yayana me ya sameka? Wani irin numfashi yaja, sai kuma d’ib ya d’auke Ihu khairat ta fasa da taga baya numfashi, da gudu ta fita sashen taje ta gayawa Hajiya Hajiya a rud’e da gudunta, ta nufi sashen su Jijjiga Imran ta hau yi tana fad’in “Dan Allah Imran ka tashi,nasan ni na saka halin nan wallahi na tuba,Dan Allah ka tashi, kayi hak’uri” ta fad’a kanshi tana kuka Khairat ce ta kira Dr. Moha, Cikin minti uku sai gashi Khairat tace “Dr har kazo” “Eh dama ina nan area nazo duba wani patient” “Ok” Dr.Moha yayi gwaje-gwajen da zanyi sannan ya juyo kansu Yace “A gaskiya damuwa tama Imran, yanzu haka ya kamu da ciwon zuciya” Hajiya a firgice tace “Ciwon Zuciya Dr” ta fashe da kuka Khairat ma ta tsorata da jin furucin Dr “Eh ciwon zuciya,dan haka sai a rik’a kiyaye duk abunda zai sa shi damuwa ko ya b’ata mishi rai, idan ba haka ba Zuciyarshi zata iya bugawa ya rasa ranshi” Hajiya na sharar k’walla tace “ba kowa ya haddasa masa ciwon zuciyar nan sai ni, In shaa Allah Dr za’a kiyaye” “Yawwa Dan Allah Hajiya a kiyaye ni zan koma,Nan da 1hour zai farfad’o In shaa Allah” “Toh Dr. Mun gode” “Ba damuwa” Hajiya zaune tayi gaban Imran, tana kallonshi tana kuka, cike da nadamar abunda ta rik’a ma Noor dan shi ya jawo halin nan da yake ciki Khairat ma sai hawaye take, Su Ihsan suma duk sun hallara a d’akin, Yazeed baya nan yana can wajen sharholiyarshi Noor na d’akinta bata san abunda ke faruwa ba. Bayan awa d’aya, Imran ya farfad’o, yana ganin Hajiya akanshi yai saurin juyar da kanshi, Yace “me kuke yi anan?” Kunzo nan ne ku k’arasa ni, in mutu ku huta” Hajiya tai saurin katse shi “A’ah Imran kar kace haka, muna sonka, ba zamu so wani abu ya sameka ba” Wayarshi da keyn motarshi ya d’auka ya bar d’akin, Hajiya ta bishi da kallo tana hawaye, Su khairat ma mamaki ne ya cika su. D’akin Noor ya fara zuwa, ya murd’a yaji a rufe, yayi knocking shiru, haka ya tabbatar mishi barci take Yana shiga motarshi, Yayi dialing numbern Dr.Moha “Dr. Na kira ne na k’ara maka godiya, nagode sosai fah, Allah ya biyaka” “Haba! Imran Anything for you, kafi k’arfin haka a wurina” Yayi dariya yace “ai godiya dole ne” Dr.Moha yayi dariya Imran yayi hanging-up Ya tada motarshi zuwa gidansu Naseer Zuciyarshi cike da farin ciki, Finally Noor zata huta. *BAYA* Imran a lokacin da yana tunani, idea da tazo mishi ita ce “Yasan Hajiya na masifar son shi ba zata so abunda zai cutar dashi ba, shiyasa ya yanke shawarar had’a baki da Dr.Moha ace yana da ciwon zuciya yasan itace kad’ai hanyar da zai kub’utar da Noor, Dai-dai lokacin da yasan Khairat na kawo mishi abinchi, Dr.Moha yazo ya mishi allurar da zata sa shi unconcious for some hours Yana mishi allura ya tafi, shiyasa ana kiranshi yazo ba b’ata lokaci.