ITA CE QADDARATA CHAPTER 4

ITA CE QADDARATA CHAPTER 4

  Har 15mints ya cika,Yazeed bai ga Noor ba,Yace me yarinyar nan take nufi,bari in k’ara mata 5mints in gani Yana yi yana duba Wall clock d’in falon,har 5mints ya cika A fusace ya tashi yace lallai yarinyar nan ta raina mun hankali,amma zanyi maganinta Ya tashi ya fita, yana huci “”Noor sharar barcinta kawai take, tayi nisa a barci “”K’ofar d’akin ya tura da k’arfi,kwance ya ganta tana barci “”Ya cije yatsa yace kutt! Wato ma yarinyar nan barci take,ni zata maida d’an iska Ya fita d’akin,kitchen ya nufa ,ya bud’e fridge,ya d’auko ice block(k’ank’ara),ya farfasa ta yasa jug,Sannan ya samu ruwa masu bala’in sanyi,ya zuba a k’ank’anrar “”Ya koma d’akin, Ya shek’a mata ruwan,ice block na dukan jikinta Firgigit ta tashi,kafin ta k’arasa bud’e ido,ya fara zabga mata belt(ku hango an zuba maka ruwa,an dake ka,k’arshen zafi kenan) “”K’ara ta saki saboda zafin bulalar,Tace Dan Allah kayi hak’uri,kayi mani rai “”Yace hak’uri,hak’uri fah kika ce,ni zaki maida d’an iska ,daga baki 15mints kizo nan kina barci,ko kina d’aukar kanki har yanxu a matsayin matar Daddy,in ma kina tunanin haka,u bttr remove it frm dat ur corrupt head,coz yanzu ke Baiwa ce a gidan nan “”Tana hawaye tace wlh nima ban san lokacin da barcin ya kwasheni ba “”Zama ki sani ne,ya cigaba da zabga mata belt “”Tun tana kuka,tana rok’onshi, har ta gaji da rok’onshi,sai da ya mata lilis “”Ya dakata,yana hak’i Wayarshi ta hau ringing Yayi receiving “”Hello Baaba kana ina? Abokinshi ya fad’a “”Ina gida wlhy “”Toh kai sauri kazo yau akwai test “”Ok toh,Gani nan Yayi hanging-up Ya juya kanta yace ki jira dawowata,i will mercilessly deal with you today,coz kashe ki ne kawai bazan yi ba “”Yana fad’ar haka ya fice,a harabar gidan,Yaga Imran “”Imran yace daga ina haka,kana ta hak’i “”Ni da waccen yar’iskan,wlh yau sai ta gane kurenta,bata san waye Yazeed ba,ni zata raina ma hankali “”Imran yayi murmushi,ya k’ark’ada kai ,kawai ya wuce A ranshi yana jin dad’i,gwara da Allah ya hada ta da Yazeed,shi zai koya mata hankali,inda ace da ne kafin ya gano matar Daddy ce,zai iya yiwa Yazeed magana,ya k’yaleta(coz yana da tausayi) but tunda ya gano matar Daddy ce,baya tausayinta ko kad’an,dan shi kawai baya son hayaniya ne but da shima sai ta gane kurenta a hannunshi “”Noor ta kifa kanta tana kuka mai tsuma rai,tana magana a fili “”Wannan wacce irin rayuwa ce,ni bani nace ina son Daddynsu ba,nima ba da son raina na aure shi ba,amma sunzo suna ta huce haushi a kaina,da sun san ta hanyar da Daddynsu ya aureni,da shi zasu tsana bani ba “”Tana ta kuka,tama manta da zancen gyaran d’akin Iman “”Lami ta shigo d’akin rik’e da plate na abinchi Da saurin ta ajiye plate d’in,ganin Noor na kuka Tace Subhanallah! Ya kike kuka?me Yazeed d’in ya miki “”Ta fad’a ma Lami komai “”Tace kaii wlh mugu ne,su kwata kwata basa tausayinki,kamar ba matar ubansu ba,ko da yake laifin Alhaji,shi da ya auro ki,ya banzatar dake,kamar baki da hak’k’i a kanshi,ya bari matarshi da ya’yenshi na gallaza miki “”Noor tana sharar k’walla tace haka Allah ya k’addaro mun rayuwata,ba yadda na iya,kar ki d’aura laifin kan Alhaji, “”Lami tace eh da wannan kuma,ga abincinki nan, “”Tace toh,nagode Tana kai loma d’aya bakinta,Taji muryar Iman na k’wala mata kira,sai a lokacin ta tuna da aikin da tasa “”Yan hancinta suka kad’a,ta mik’e zumbur tace Lami ina zuwa “”Lami tace ki dawo,ki gama cin abincinki,sannan kije “”A’ah bari kawai inje Lami “”Jiki na rawa ta tafi,a falo ta sameta ita da Ihsan “”Ta d’an tsaya nesa da ita,dan kar taji, ta kai mata masga “”Iman ta fisgota ta shek’e mata wuya tace ina gyaran d’akin da na saki “”Da k’yar take magana saboda yadda ta shek’eta ,tace mantawa nayi “”Iman ta saketa da k’arfi tare da hankad’ata,ta fad’i Tace kin manta koh, ta juya kan Ihsan tace Sis,wane punishment xan ba yar’iskan nan “”Ihsan tace ki bata punishment irin na yan boarding,ki sata zama kan takalmi “”Yawwa sis,very gud idea “”Ta d’auko takalmi,ta mik’ar dashi tsaye,tace oya tashi ki zauna a kai “”Noor ta zaro ido,tana mamakin taya za’a ce,ta zauna kan takalmi “”Iman tace ke nake jira,kin tsaya kina b’ata mun lokaci “”Noor ta tashi da k’yar,ta zauna kan takalmin Sai ta tafi tangal-tangal kamar zata fad’i,Iman ta masgota, dole ta gyara zamanta kan takalmin “”Tsawon minti biyar 20 tana haka,duk ta gama gajiya “”Sai ga Imran ya fito daga d’akin Hajiya “”Wani irin tsaki yaja ganinta yace Why wai nake had’uwa da yarinyar nan,i hate seeing her in my life,Sai kuma yayi murmushi ganin punishment d’in da take(a ranshi yace ko dan ina son ganinta a wahala,shiyasa duk lokacin da take cikin wahala, nake xuwa wurin) Ya sake yin wani murmushin,ya wuce batare da yace ma su Ihsan komai ba “”Sai da ta k’ara 10mints sannan Iman tace oya foolish tashi kije ki gyara mun d’aki “”Noor jiki ba k’wari ta tashi ta nufi d’akin Iman,ta hau gyarawa………………………………………….. *Note: masu cewa wahalar da ake ba Noor tayi yawa,Hak’uri zaku yi,haka tsarin labarin yake,kuma ba haka zata yi ta zama cikin wahala ba,kunsan dukkan tsanani yana tare da sauk’i, So ku cigaba da biyo mu dai,Sannu a hankali komai zai warware,Wahalar da take ciki zai k’are Hausawa sunce komai nisan jifa k’asa zai dawo* Tana gamawa,ta koma d’akin ta k’arasa cin abincinta Ta fito zata kai plate kitchen,taga Yazeed ya dawo kenan za shi sashen Hajiya Tai saurin komawa d’aki,Yace fito yar’iska,na ganki “”Ta fito jiki na b’ari, “”Yace wato wasan hide-and-seek zamu fara dake shaa,tunda ni sa’anki ne “”Ta girgiza kanta tace a’ah “”Useless ki ma fara,Oya wuce kije sashenmu ki jira ni,dama na gaya miki yau haaaaa…….ba sai na k’arasa ba “”Tace toh+ Kitchen ta fara xuwa ta ajiye plate d’in Ta wuce sashen su,a ranta tana cewa ko wacce muguntar zai mun kuma,ni dai Allah kai mun tsari dashi,Monster kawai “”Ta murd’a k’ofar falon a hankali ta shiga, Imran dake falon,ya d’auka Yazeed ne ya shigo,dan haka ya juya yace Yazeed ya test d’in ? “”Kawai ya ganta,tsaki yaja ,ya kawar da kanshi a ranshi yace why ??why?? Oh shit,wallahi na tsani ganin yarinyar nan,tana sa naji b’acin rai ,buh sai ganinta nake all time,how can i get rid of her,ya kawai wuce d’akinshi “”Noor da mamaki ta tsaya tana kallonshi,ita dai yana burgeta,dan ba ruwanshi bai tab’a mata wani abu,amma ta rasa gane,me yasa duk lokacin da ya ganta,sai ya b’ata rai ya bar wurin, Tana cikin tunanin,Yazeed ya shigo, Kallon uku saura kwata ya mata,ya wuce d’akinshi Jeans trousers ta gani ya kwaso da yawa, sun kai guda ashirin Ya jibge su gabanta “”Yace ina so ki wanke su tas,sannan kar ki kuskura,ki sa su a washing machine ko ki wankesu da brush,da hannunki nake so ki wankesu “”Tuni idonta ya kawo k’walla,ita dai taga ta kanta,taya zata iya wanke jeans din nan “”Ya daka mata tsawa kinji ni ko baki ji ba “”Ta d’aga kanta sama alamun taji “”Oya dismiss “”Ta mik’e,da k’yar ta iya kwashe su,saboda nauyinsu “”Ta fita tana hawaye Can wajen d’akinsu,akwai famfo nan taje,ta ajiye Ta fara wankewa,tana kuka Da k’yar take wankewa,gashi yau ta wahala da yawa,duk ta galabaita, Wasu ma duk a wanke ne,tsabar mugunta ce kawai,ya had’a mata dasu “”Bayan wasu mintuna Imran na kwance a d’akinshi,yana latsa waya “”Can kuma yace wa kanshi i have to warn Yazeed,idan zai sa yarinyar nan aiki,ya daina kawota sashenmu,yaje can ya gaya mata aikin da zata mishi,kuma daga yau bazan sake zuwa sashen Mum ba,sai na tabbata yarinyar nan bata nan,Daddy baka kyauta mana ba wlhy, Mtcheewww yaja tsaki ya mik’e,ya fito “”Yazeed ya kira sunan shi fuska babu annuri “”Na’am Bro, “”Ina so daga yau kar ka k’ara kawo yarinyar nan sashen nan,idan zaka sa ta aiki,kaje can ka gaya mata “”But me yasa ? “”Saboda bana son ganinta,tana sani b’acin rai,idan na tuna matar Daddy ce,da kuma yadda ta banzatar da rayuwarta akan kud’i “”Yazeed yace ok bro,am sorry bazan k’ara kawota ba “”Bai sake cewa komai ba,ya juya ya koma d’akinshi Lami rik’e da baki tace Noor waya saki wannan aikin ? “”Noor ta d’an yi murmushi tace wa kuwa banda wancan mugun “”Ohh ni Lami,na rasa me yasa yafi kuwa tsanarki a gidan nan “”Noor tace tun k’uje masa mota da nayi,sai kuma ya bani 15mints nazo ina bacci,da kuma haushin na auri Babansu “”Ai wannan duk ba k’akk’aura hujja ce da zai sa ya tsaneki haka ba,gwara na auren Babansu but duk da haka tsanar tayi yawa,ya dai bi a hankali wlh,dan idan k’iyayya tayi yawa tana iya komawa so,duk da kina matar babanshi kuwa,bari na taya ki, “”Kamar daga sama suka ji ana tafi “”Lokaci d’aya suka kai dubansu ga mai tafin “”Yazeed ne “”Gaba d’ayansu sai da gabansu ya fad’i,Noor duk tafi tsorata “”Yace weldone👍🏻,Allah ya tona asirinki dama kece mai zuga ta ko “”Jiki na rawa,Lami ta girgiza kai tace a’ah “”Lafiyayyan mari ya mata,Yace a’ahn Ubanki,naji komai ai,Yau zaki bar gidan nan,kije ki fara had’a kayanki “”Ba Lami kad’ai ba,har Noor ta girgiza da jin furucin shi “”Lami tai saurin kai gwiwoyinta k’asa tace kayi wa Allah da Annabi ,ka rufe min asiri kayi hak’uri,iyayena da wannan aikin nawa suka dogara “”I don’t care,b’ace mun da gani ko in tattaka ki “”Jiki na rawa ta wuce tana kuka “”Ya juya kan Noor,yace da take ce miki k’iyayya zata iya komawa So,let me make it clear to you,nan ba film bane ko littafin hausa,da saurayi zai gama gasa yarinya,ya dawo yana sonta,nan ana maganar reality ne,so listen to me carefully,na tsaneki na tsaneki,bazan tab’a sonki ba,ko da ace ba igiyar auren Babana a kanki ballatana akwai,I hate you more dan u could ever imagine,sannan kika ce ni mugu ne koh “”Baki yi k’arya ba ni mugu ne,amma har yanzu baki shaida mugunta ta ba,but daga yau zaki tabbata cewa lallai Yazeed mugu ne,……… “”Sashen Hajiya,ya nufa Tana zaune falo Yace mum,wacce yar’iskan Lami ta bar gidan nan yau,munafuka ce ita ke zuga Noor “”Hajiya tace yau d’in nan kuwa,dan ina adawa da duk wanda zai nuna soyayya ko tausayi ga yarinyar nan,a cikin gidan nan,toh wlh sai ya bar gidan nan,dan haka barinta gidan nan ya zama dole, “”Noor d’aki tabi Lami,tana bata hak’uri “”Kiyi hak’uri Lami,In shaa Allahu bazai kore ki “”Muryar Hajiya suka ji tace kamar kin bar gidan nan kin gama,ko awa biyu,bana so ki k’ara a cikin gidan nan,hakan ya zama gargad’i ga yan baya,duk wanda ya nuna so ko tausayi ga Noor kora ce “”Na baki minti talatin ki had’a kayanki kibar gidan nan,ko ki fuskanci mummunan wulak’anci,ta watsa mata kud’inta,ga kud’inki nan Ta fice fuuuu “”Kukan Lami ya tsananta,Noor ma kuka take sun k’ank’ame juna A ranta tana cewa me yasa ake son raba ta da masoyanta,haka zata yi ta zama da wa’inda basa sonta,ita dai wannan *itace kaddarata* “”Lami ta raba jikinta,dana Noor,tace bari in tashi in tafi Noor,kar ta dawo ta wulaknta ni “”Noor na kuka tace yanzu tafiya zaki yi,ki barni ,ke kad’ai ke sona gidan nan Lami,gashi kema zaki tafi “”Kiyi hak’uri Noor,ki ta hak’uri watarana sai labari “”Har bakin gate tama Lami rakiya ,Suna ta kuka Ta dawo cikin gida,rai a jagule,ji take kamar Allah ya d’au ranta ta huta Har wani dishi-dishi take gani,Zuciyarta na mata zafi Jiri ta fara gani,anan tsakar gidan ta fad’i sumammiyya “”Imran ya fito ,xai fita yana cikin mota,kawai yaga mota kwance gabanshi “”A tsorace ya fito daga motar “”Noor ya gani kwance bata numfashi,a rud’e yayi kanta har zai tab’ata,sai ya tuna matar babanshi ce, kuma ko ba matar babanshi bace ita ba muharramarshi bace “”Yayi cikin gida a rud’e yana kiran Lami! Lami! Lami! Shiru “”Abu(dayar mai’aikin) ta fito tace Lami bata nan “”Toh ke zo,tabi bayanshi “”D’auketa da sauri ki sata mota,mu kaita asibiti “”Da yake Abu k’atowa ce,kuma Noor bata da nauyi Nan da nan ta d’auketa,ta sata mota “”Imran yaja motar sai asibiti “”Ta samu taimako na gaggawa,Imran duk ya rud’e saboda yana da masifar tausayi Sai zirga zirga yake a passage d’in asibitin “”Bayan wasu mintuna,Likita yace yana son magana dashi “”A bisa binciken da muka yi,mun gano yarinyar nan damuwa ta mata yawa da tashin hankali,bai kamata ace at her age,tana da wannan damuwar ba Dan haka tana buk’atar kula sosai,idan ba haka ba,komai zai iya faruwa,Zuciyarta zata iya bugawa ta mutu “”Imran a kid’ime yake kallon likita “”Likita yace Yes,so dan haka a kiyaye,yanzu zan rubuta muku,magunguna,ta rik’a sha In shaa Allahu zata samu sauk’i,amma fa sai ta rage damuwa,da shiga tashin hankali “”Ok Doctor,In shaa Allahu za’a kiyaye “”Ya rubuta mai drugs,ya fito kanshi na masifar sarawa,Yanzu ya zai yi,yasa ta samu kyakkyawar kulawa,yasan Hajiya ba zata tab’a barinta ta huta ba,ko su Yazeed,Shima kanshi bai so haka ta faru ba,Yaso ta cigaba da gasuwa tunda ita ta jefa kanta a halin,but yana da tausayi,Ba zai iya bari ta cigaba da shiga halin k’uncin nan ba,daga k’arshe ta mutu,iyayenta da danginta wane irin mutane ne,da zasu aurar da yarinya ba zasu rik’a zuwa suna duba lafiyarta ba,ko mahaifiyarta ce ya kamata ace tazo,tunda aka kawota ko mage bai tab’a ganin tazo dubata ba,gashi ko kayan arzik’i bata dashi kullum cikin yagaggun kaya,Daddy bai mata lefe bane da zai aureta,duk talaucin iyayenta ba’a ce an kawo ta gidan miji,da yagaggun kaya ba??? Me yasa ???? Shi ya kasan gane wannan al’amari ???? Pharmacy d’in asibitin yaje ya siyo drugs da likita ya rubuta,ya koma wajensu “” “”Noor na zaune kan kujera duk ta galabaita,tana maida numfashi da k’yar,Kallo d’aya Imran ya mata yaji ta masifar bashi tausayi,Ya kawar da kansa gefe Yace Abu kamata mu tafi gida Abu ta amsa da toh””+ “”Dukkansu bayan mota suka shiga,ko kad’an Imran bai damu ba,dan sun zauna bayan mota,ba kamar yadda samari ke yi ba suce an maida su driver,Tuk’inshi kawai yake,da tunani kala-kala a ranshi da kuma tausayin Noor”” “”Noor tayi shiru tana tunani,garin yaya haka ta faru ? Ita dai tasan ta raka lami,ta dawo cikin gida,daga nan bata k’ara sanin me ya faru ba Ta juya ta kalli Abu, murya can k’asan mak’oshi tace Dan Allah Abu me ya faru dani ? Duk da a hankali tayi maganar amma hakan bai hana Imran ji ba,Ya rasa gane me yasa duk lokacin da yaji muryarta sai gabanshi ya fad’i kamar yadda in ya kalli fuskarta Kafin Abu ta bata amsa, yace ki bari idan kun sauka kya tambayeta,bana son sake jin muryarki a motar nan Tsit Noor tayi bata k’ara cewa komai ba,a ranta tace Ikon Allah,to meye da muryarta da ba’a son ji”” “”Har suka kawo gida ba wanda ya sake magana Da suka fito daga motar ya ba Abu magangunan Yace gashi ki rik’a bata,ki tabbatar da tana sha akan lokaci Ta amsa da toh Noor suna fitowa dama gaba tayi abunta,kafin yace baya son ganinta”” “”A d’aki ta sami Noor,ta jefa mata maganin Tace gashi nan ba dani ba,ba zaki ja a koreni aikina ba,ni yanzu ko hanya ma bana son mu had’a dake,tasa kai ta fice Noor tayi murmushin tak’aici tace ni dai Noor ,na zama mujiya a cikin mutane kuwa baya sona,gashi ni ba mummuna ba balle ace muni na ya jawo aka tsaneta,ina ga bak’in jini ne dai dani Ya Allah! Ina rok’on ka ka yaye mun bak’in jinin nan nawa,kasa soyayyata a zuciyar bayinka(Ameen)”” “”Ta jawo ledar magungunan tana dubawa Tacewa kanta tabbas ko shakka babu,bayan na raka lami fad’uwa nayi,shine Imran ya kaini asibiti,a gaskiya Imran nada zuciyar imani,duk da cewa baya sona, ko ganina baya son yi amma yana tausayina,Allah ya saka mai da mafificin Alkhairi Ta tashi tayo alwala,ta kabbara sallah”” “”Imran d’akinshi ya wuce straight,ya kwanta kan gado,tunanin d’azu akan Noor ya sake dawo mai Ina dangin yarinyar nan ? Me yasa Daddy zai aurota yasan bazai kula da ita ba ? Ko mummy ce ta hana shi kula ta ? Wata zuciyar tace mai itace ma,Daddy me yasa kake haka ka bari mummy na mulka ka,dole in maka magana akan Noor,ka gyara, ka bata cikakkiyar kulawa,in kuma baza ka iya ba,ka sallameta ta koma gidan iyayenta bazan zuba ido inga yarinyar mutane ta mutu ba”” “”Ya mik’e da zafin nama,ya nufi sashen Alhaji Alhaji na zaune shi kad’ai a falon shi yana kallon news Bayan yayi sallama,sun gaisa Cikin girmamawa Imran yace Daddy ina so muyi magana da kai Alhaji ya d’an yi murumshi yace ina saurarenka d’a na”” “”Amma Daddy Dan Allah ka tsaya ka saurareni,ka fahimce abunda zance”” “”Imran kenan,ina saurarenka”” “”Daddy akan maganar Noor ne Wacce Noor Matarka Alhaji da mamaki yake kallon Imran yace Matata kuma ina da wata mata ne bayan hajiya Imran ya d’an yi yar dariya yace Amaryarka toh “”Take Alhaji ya murtuke fuska yace dama maganar yarinyar nan zaka mun,toh ahir d’inka”” “”Daddy matarka ce fah,kuma tana da hak’k’ina a kan ka”” “”Nafi ka sanin matata ce,amma yanzu bani da iko da ita,sai abunda hajiya tace Imran wani bak’in ciki yaji ya turnuk’eshi,shi bai tab’a ganin miji irin babansu ba,mai tsoron matarshi yace Daddy kai fah ne mai gidan nan,kai da iko ka fad’i abu,ayi ko kar ayi A fusace Alhaji ya mik’e yace baka tab’a ganin b’acin raina ba koh,toh wallahi idan ka k’ara mun maganar nan zaka ga mummunan b’acin raina “”A hasale Imran,ya tashi ya bar falon Zuciyarshi na mai masifar k’ona,wani irin uba ne dasu Yanzu shi ya zai yi ya ceto Noor daga wannan hali Tunda Daddy baya sonta,why not bazai sake ta ba Bari yaje ya samu Noor d’in yaji ina danginta suke? Duk inda suke zai je ya nemo su,a raba auren nan kowa ya huta “”Noor kwata-kwata ta manta da zancen wanke jeans d’in Yazeed Kamar an tsunkile shi(Yazeed) yace bari in tashi inje in gani,yar iskar yarinyar nan ta wanke su,ko kuwa”” “”Jibge ya gansu,ita kuma bata wurin A fusace yace what!! Diz girl is trying me,wato i should do my worst,i swear to God i won’t spare her today,sai na mata abunda har ta manta bazata tab’a mantawa dani a rayuwarta ba,ni zata ma iskanci,ta nuna mun ita mai taurin kai ce Noor ! Noor ! Ya k’wala mata kira kai kace tashin duniya ne yadda yake k’wala kiranta A gigice ta fito ,jiki na rawa tace Gani Bai tsaya wata-wata ba,ya d’aga hannu zai falla mata mari ,Yaji an rik’e hannunshi ta baya,an murd’e hannun Noor har ta damtse ido tana jiran saukar mari Shikuwa da mamaki ya juya yaga waye ya rik’e mai hannu,to his suprise yaga Imran Noor kuwa jin bata ji saukar mari ba,yasa ta bud’e ido,ta tsaya tana kallonsu Da mamaki yace Yaya,Noor ce fah zan mara,ba Ihsan ko Iman ba “”Imran ya d’an yi murmushi irin na manya,Yace kana tunanin bansan wacece ba,ina sane da ita ce”‘ “”Yaya kasan itace ka hana ni, Ofcourse Yes,bari kaji daga yau kada ka k’ara d’aga hannunka,kace zaka mareta ko daketa,infact duk wani aiki kar k’ara sata,ka fita harkar ka,Matarka ubanka ce ,ba Baiwa ba ,kamar yadda kuka dauketa”” “”Baki sake yake kallon Imran,Yace Yaya kasan me kake fad’a,yarinyar da ka tsani ganinta itace kake protecting yau,anya kasan me kake kuwa,ya fara tattab’a shi yana dudduba shi,yaji lafiyarshi kuwa”” “”Imran ya fashe da dariya,Yace kana tunanin bansan me nake fad’a ba,lafiyata lau, “”Yazeed yace idan kuwa kace zaka goyi bayan yarinyar nan,zaka fuskanci mummunan b’aci rai daga wajen mummy Imran yace na dai gaya maka,ka kiyaye yarinyar nan,b’ace mun da gani Ya wuce ya gunguni,yana huci,a ranshi yana sak’a irin muguntar da zai mata idan Imran baya nan”” “”Cike da mamaki Noor ke kallon Imran,tana mamaki ya aka yi yau yayi protecting d’inta,tana jin d’ad’i a ranta,yanzu ta samu mai kareta Yana kallon gefe yace kada ki d’auki kare ki da nayi a matsayin wani abu,ko tausayinki yasa haka,bana tausayin masu irin halinki(ya fad’a ne kawai but yana masifar tausayinta) nayi hakane saboda abunda likita yace “zaki iya rasa ranki,idan kika cigaba da shiga halin k’unci, ni kuma bana so ki mutu ,a zarge iyayena so yanzu nazo ki gaya mun ina iyayenki suke ? Kuma taya akai kika auri Daddy ? Gabanta ne ya fad’i ba zata iya gaya mai tarihinta,saboda mummunan halin Babanta ,ba zata so yasan waye ubanta ba Haka bazata iya gaya mai ya akayi ta auri Babansu ba,saboda tasan basu san sana’ar ubansu caca ba,kuma ba zata so su sani ba,ta dalilinta Ba zata so familyn su shiga wani hali ba ta dalilinta Duk wanda yaji sana’ar ubanshi caca dole ya girgiza *Toh masu karatu,ku ba Noor shawara,me zata cewa Imran,ta fada mai gaskiya ko tayi shiru* *Idan ta fada mai gaskiya tabbas zai daina ganin laifinta ,kuma zai taimaki rayuwarta* *Amma kuma idan ta fada zata sa shi cikin tashin hankali,shi da k’annenshi zata ruguza musu farin ciki,Zasu daina ganin girman Ubansu,Toh yanzu ya zata yi*

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *