JALILA
CHAPTER 12
Hankalinsa ya kasa kwanciya, fitowa yai daga motar tare da dan matsowa kadan da kofar shiga yadan leka ciki kadan.+
Security din dake gun ne ya kalleshi yace “Yallabai shiga zakai?”
Hade rai yai ya juya jikin motarsa, hannayensa ya hada yana dan hadasu da waresu, kafin ya koma cikin mota ya dauko wayarsa.
Mintinsu sha biyar kenan da shiga, me sukeyi haryanzu? Ko alert bai gani ba bare yasa ran sun biya.2
Wayarsa ya dauko ya danna number Ameera.
Sukuwa suna ciki Jalila kome Ameera ta dauko indai taga kudi sai ta maidashi, Ameera ta tsaya tace “to nidai bansan me kikeso mu siya ba, duk abinda na dauko sai ki maida.” Ta karasa maganar tana kallan kwandon nasu da bakomai a ciki sai atamfa kwaya daya.
Kiran Hassan ne yasa ta kalli Jalila tace “Yaya!”
Jalila ta kalleta bayan ta amsa kiran, Ameera tace “Yaya….”
Yace “me kukeyi haryanzu? Badai shirme kuka tsaya yi ba?”
Tace “a”a Yaya, ni narasa me zamu siya ne, duk abinda na dauko sai Yaya Jalila tace wai yayi tsada sai ta maida.”
Hassan ya kashe wayarsa baijira ya gama jin abinda zatace ba.
Tahowa yai ya shiga ciki, security din ya bishi da kallo yana yan kunkuni, inkasan shigowa zakai gulmar ta menene? Tun dazu ka tsaya kamar mai jira.2
Hassan na shiga ya sake kiran Ameera ya tambayeta inda suke, ta sanar dashi.
Yana isowa ya bugama Jalila kallan harara sannan ya kalli Ameera yace “ina kayan da kika zaba?” Nan ta shiga daukowa tana sawa a cart din, mamaki na kara ratsata, bata dade a gidansu Aina”u ba yaushe har yayanta ya koma haka?
Jalila na tsaye tana kallansu sai zuba kaya sukeyi a cart din har sai da ya cika sannan suka nufi gun biyan kudi.
Tana can gefe suka biya kudin sannan ya kalleta ya nuna mata ledoji, matsowa tai ta dau leda biyu manya itama Ameera tadau biyu suka nufi kofar fita.
Yana kallanta da yanda ledojin suka mata nauyi dan kamar ma janta sukeyi, kallanta ya sakeyi sannan ya kalli ledar ji yake kamar yaje ya amsa sai dai inaaa bayaji zai iya yin hakan, balle agaban Ameera.
Taje kusa da motar bata kula da saman interlocks din daya dago ba, jitai tayi tintibe da sauri yasa hannu ya riko cikinta.
Ajiyar zuciya tai dan ta tsorata ga kayan da suka kara rinjayarta.
Juyowa tai ta kalleshi kawai sai tai dariya tace “yaya wlh na tsorata, har na hango kaina ya bugu da jikin motar.”
Jawota yai ta mike daidai sannan ya kalli gun datai tuntube, lalai mutanen nan basuda hankali tayaya bazasu gyara gun ba? Fuska a daure ya kalleta yace “meyasa bakya kallan kasa in kina tafiya? Da bana kusa ko da banyi hanzarin kamoki ba me kike tunanin zai faru?”
Ta kalleshi jikinta yai sanyi tace “wlh ban……”
Gani tai ya wuceta rai a bace, ledar hannunta ya amsa ya sa a boot din motar sannan ya bude ciki ya shiga.
Ameera ta ajiye nata itama ta shiga baya sum sum.
Jalila ma jiki a sanyaye ta shiga, to laifinta ne? Itama ai da saninta bazata bari ta fadi haka ba.
Harya tada motar ya fito daga ciki ya nufi gun secuydin.
Kallansa yai fuskar nan a daure, security din ya kalleshi yace “Yallabai da wani abun ne?”
Shiru yai yana tunani, menene damuwarka da har kazo nan zakai fada akan su gyara gun da yarinyarcan zata fadi? Menene damuwarka Hassan.
Bai tanka mai ba ya juya, security din ya bishi da kallo yace “yau ni kuma ina na samo wannan?”8
Hassan ya bude motar ya shiga dya rufota da karfi yaja motar da gudu suka bar gun.
Shiru motar tai ba wanda yake magana, sai sanyin Ac dake ratsa cikin motar.
Jalila ta kalleshi taga ba alamar wargi, tai gum.
Can ta sake kallansa nan ma taga ba alama tai gum.
Sunyi nisa sosai sai tace “Yaya kashanye yoghurt dinka?”
Bai tanka mata ba sai dai yasa hannu ya miko mata ledar, ba haka taso ba, ta daure ta sake cewa “kasan yaya sai da muka shiga cikin store din nan naji cikina yana wani kara?”
Nan ma baiko tanka mata ba, ta amshi ledar ta ajiye a kusa da ita sannan ta kalli Ameera datai shiru tana danna wayarta.
Itama jan bakinta tai bata sake cewa komai ba.
Suna isa gida Ameera ta fito da sauri saboda tsoron kar reshe ya juye da ita.
Jalila ta zauna ba alamar fita, kallanta yai yace “me kikeyi?”
Tace “Yaya kaima kasan ba kaifina bane, tuntube nai sannan wlh bawai kula bane banayi”
Yace “kinji nace wani abun?”
Tace “bakace ba amma……”
Ya katseta “sauka inkuma bazaki shiga ciki ba sai ki kulle motar inkin gama zaman.”2
Kallansa tai ranta yadan sosu ta fito daga ciki ta duba boot ta dauko ragowar ledojin sannan tai ciki.
Kallanta yai harta shiga ciki sannan ya dan saki huci yace ” ba saboda ke raina ya baci ba saboda kaina ne.”
Idanunsa yadan rufe da hannunsa kafin ya fito daga motar.
Ummy najin motsin shigowarsu ta fito daga dakinta tana cewa “Jalila kun dawo?”
Ameera ce ta taho da gudu ta rungumeta, Ummy tai dariya tace “Auta saukar yaushe?”
Ameera ta kalli Jalila tace “tare muke dasu Yaya Jalilah.”
Ummy ta kalli Jalila wacce ta karaso tana cewa “da ita muka je ai Ummy.”
Ameera ta kalli Ummy cikin zumudi tace “Ummy kinsan waye ya kaimu?”
Ummy ta kalleta, Ameera ta kara matsowa tace “Ummy karkiyi mamaki………”
“Hassan kun dawo?” Abinda Ummy tace ne yasa Ameera saurin boyewa abayanta, Hassan yace “eh Ummy.”
sannan yace “Abba fa?”
Ta nunamai falo tana kallan Jalila wacce tana tsaye yazo ya wuce kamar baiganta ba.
Hassan ya wuce falo, Ameera ta kalli Ummy da sauri tace “Ummy kingani? Ummy yaya ne yake magana haka.”
Ummy ta kalleta tace “naji hajiyar magana, akwai baki a dakinki kije ku gaisa.”
Ameera tace “baki? Su waye?”
Ummy bata tanka mata ba ta matso kusa da Jalila tace “Jalila wani abun ya faru ne?”
Jalila tai yake tace “bakomai Ummy, Kinga kayan da Yaya ya sai mata.”
Ummy ta kalli ledar tace “basai kin ciro ba, angode Allah ya saka masa da alkairi.”
Jalila tace “Ameen.”
Muryar Abba sukaji yana kiran Ummy.
Ummy ta falo, Jalila kuma ta dau leda tai dakin Ameera.
Hassan na zaune kusa da Abba ta shigo, ta zauna sannan ta kallesu tace “d”a da uba ne suke hirar yaushe gamo?”
Abba yai murmushi yace “nikaina ina jiran wannan lokaci, lokacin da Hassan zai zauna dani muyi hirar duniya.”
Hassan bai tanka musu ba, Ummy tace “wani abun ya faru ne?”
Yace “a”a kawai dai sirikarsa ce ta nemi mu barta ta tafi tana kunyar zama gida daya da sirikinta da mu.”
Ummy tace “hakane munyi laifi da bamuyi wannan tunanin ba, sannan bamu tambayeta ra”ayinta ba.”
Hassan ya kalli Ummy yace “Ummy ita so take takoma kauye nikuma ina ganin hakan ba solution bane.”
Tace “mekake tunani?”
Yace “gwara a nemarmata gida anan ta zauna karami, can yayi nisa.”
Murmushi tai ta kalli Abba tace “gaskiya kam yama Jalila nisa wanda zai sata damuwa.”
Kare tsuke fuska yai yace “Ummy me kike…..”
Katseshi tai tace ” ni ba da komai nake nufi ba.”
Abba ya kalleta yace “wani abun kike tunani?”1
Tace “a”a shawararce naga tayi, me zai hana a gidan da ka siya kwananan wanda ke tarauni a maidata can? Naga gidan karami ne sannan ga yarinya ma mai kula da ita.”
Abba ya jinjina kai yace “hakan ma shawara ce, kinga Allah ne yasa bamu sa haya ba dan har an fara tambaya, Hassan sai ka dau Jalila kunduba gidan sai a sai abunda ya kamata.”
Yace “to.”
Bai jira wani abu ba ya mike, yanasan yama Abba godiya sai dai bakinsa bazai iya furatawa ba, harya kai kofa ya juyo yace “Ummy na hau sama.”
Tace “to Hassan.”
Ya juya ya fita, Ummy ta kalli Abba tace ” Ya kagani?”
Murmushi yai yace ” tunda na dawo kullum Hassan sai ya bani mamaki, lalai dolene muje muyina doctor godiya ba shakka shawararsa itace babban magani a tattare dashi.”
Ummy ta sake yin murmushi…..
Jalila kuwa tana shiga daki inda Goggo take ta hau nuna mata kaya, Ameera kam tana gefe tana mamaki, kenan mahaifiyarta ce ta asibitin nan? Me yasa a lokacin bata nuna mata itace mahaifiyarta ba? Goggo ta kalli Jalila tace “Jalila garin yaya kika barshi ya kwaso kaya haka? Kudi fa aka sa aka siya.”
Ameera tai dariya tace “Goggo ashe ke tayo, shiyasa takasa bari na dau kaya ko daya wai tsada, sai da yaya yazo.”
Goggo ta kalli Ameera tace “ke kuwa yar nan ina zan kai kayan nan?”
Jalila ta kalli Goggo wani abu ya tsirga mata na tausayi, tunda Goggo take bata saka kaya masu tsada haka ba, ba ta tana samun kaya kwatan yawan wannan ba, gaba daya kayanta…….”
Idanunta ne suka ciciko ta kalli Goggo tace “yaya ya fadamin abinda kikace.”
Tace “ya sanar dake?”
Jalila ta daga kai, Goggo ta riko hannunta, Ameera tai saurin fitowa daga dakin.
Goggo ta kalli Jalila tace “Jalila kiyi hakuri, nasan burinki ma shirme nasan ganin mun zauna tare bayan kinyi aure sai dai ko a da can jinki nakeyi dan bazan iya zama da sirikina ba.”
Jalila ta daga kai alamar ta fahimta dan batasan tai kuka.
Goggo ta kalleta tace “shiyasa a koda yaushe ake cewa Allah ba azallumin bawansa bane, Jalila ban taba tunanin zakiyi aure cikin gata irin wannan ba, gaba daya mutanen gidan nan zuri”ace ta albarka, dolene mu gode ma Allah akan baiwar daya miki ta samun dangin miji irin wannan.”
Jalila ta kalleta idanunta suka zubo da kwalla, Goggo tai murmushi tace “nikam wannan yaran kanin mijinki…..”
Da sauri Jalila tace “oh Ya Sageer? Oh Goggo kinsanshi ne?”
Kallanta tai taga ba wani alama ta wani abun tace “a”a na dai ganshi a asibiti.”
Jalila tace “oh haka ne.”
Sundanyi hira kafin ta mike ta fito.
Tunda ta shiga daki taganshi a kwance ta fito ya dawo falo ta zauna, yunwa ce ta sata shiga dakin a hankali ta dauko tiren abinci ta fito falo taci ta zauna tana danne danne a waya, daga baya ma ta sauko kasa sukai girki ta koma gun Goggo sukai hira da Ameera.
Abincin ranarsu ma data kai taga yana kwance ta diba ta fito falo taci ta koma kasa sai da suka gama abincin dare ita da Ameera sannan ta dauko nasu ta hawo sama.
Yanzu kam a kasa ta ganshi kan sallaya yana karatu, gefe ta koma ta zauna tana sauraran kartun nashi, tana lumshe ido saboda dadi, tana bala”in sha”awar taga tana rera karatunn qur”ani haka.
Hassan na nan zaune har aka kira isha”i sannan yai sallah, itama tai.
Sai binshi take da kallo tanasan tamai magana amma ba fuska.
Mikewa tai ta zubo mai abinci tace “Yaya ka sauko kaci abinci.”
Kallanta yai yace “ban dade dacin na rana ba.”
Ta mike daga zaman datai a kasa ta matso kusa dashi jikin gado tace “Yaya dan Allah menene? In laifi na maka dan Allah kayi hakuri.”
Idanunya kura mata, a ransa yace “me kika min? Haushin kaina nakeji da duk abinda zanyi tun dazu sai naji kina raina, haushin kaina nakeji nasan na ganki kusa dani, haushin kaina nakeji na rashin sanin abinda ke damuna a kanki.”
Jalila ta kalli yanda ya kafe ta da ido kana gani kasan tunani yakeyi, tace “Yaya?”
Littafinsa ya dauka baice mata komai ba.1
Tsayawa tai shiru kafin ta zauna taci abincin nasa data zuba, kadan ta iyaci dan ya mata yawa.
Har dare Hassan bai kula ta ba, itama haushi yasa ta dauke kai daga kansa tai kwanciyarta, kankace me bacci yayi gaba da ita.
Kwanciya yai ta saitinta yanda yana hangota daga kan gado, ya kura mata ido, what are u to me?
Gani yai tayi juyi ta juya mai baya.
Mikewa na ga yayi ya dau pillow dinsa ya kwanta akan kujera yanda zai ganta dan kusa da kujerar take shimfida.
Ajiyar zuciya yai ya kalli bargon data shimfida yace “wannan bazai sata ciwon baya ba? Kullum kwana a kasa? Gata ba jiki ba?”6
(Nikuwa nace waye ya sata🤨)2
Ya dade a haka yana kallanta har bacci ya daukeshi.
Yauma Alhamdulila bai farka da ciwo ba, wajen asuba ya farka, da sauri ya mike yana mamakin kansa anan ya kwana? Ahh wai Hassan hankalinka daya kuwa?
Alwala yai sannan yazo kusa da ita, ya saba sa kafa ya tasheta yau sai gani nai ya sunkuyo yasa hannu yadan bugi kafadarta tare da cewa “Jalila?”3
Idanu ta bude cikin bacci ta kalleshi, mikewa yai.
Ta mike itama tai alwala………..
Tunda ta tashi take jinta ba dadi, ba sabon abu bane tasan period dinta ne ya kusa, ita kuma gashi duk sanda zatai al”ada sai tasha azaba na ciwon mara, a gida Goggo sai ta sata tasha dauri, ko ta siyo panadol……
***********
Inna ce tasa aka kira mata dady, yana zama mumy ta shigo taja ta zauna.
Inna tace “Fatima meye hakan? Magana zamuyi.”5
Mumy tace “kome zakuyi kuyi agabana, sannan nima magana nazo fadamiki.”
Inna ta kalleta tace “maganar me?”
Tace “kiba Abubakar mukamin Chairman na company ke kiyi resigning, dama ai kin dade kina cewa zaki bani ke kuma ki sauka.”
Inna ta kalleta cikin tashin hankali sannan ta kalli Dady wanda shima yai alamar wai mamaki, tace “Abakar kai ka zigata?”
Da sauri Dady ya kalleta yace “Menene hakan? Ce miki nai inasan shugabanci na company din? Meyasa kike neman sa Inna taga kamar nine nake saki abu? Banasan irin wannan abun.”
Mumy ta kalleshi tace “Dadyn Yasmeen.”
Ya hade rai yace “Taya zaki yanke hukunci ba tare da kin sanar dani ba?”
Tace “gani nai….”
Inna ta kalleshi lalai yaran nan me? Ce miki akai inasan shugabanci?????
Tai wani murmushin takaici…….
Ummy ce ta kalli Jalila tace “Jalila lafiya? Naga tau kamar bakyajin dadi?”
Tace “lafiya ta kalau Ummy.”
Ummu tace “da ina tunanin ko in dau Goggo da Ameera muje dakanmu mu siyo kayan gidan muje a saka, kamar zaifi dan nasan halin Hassan bazai shiga gun kayan ba, kinga kuma ke kadai abin bazai yiwu ba, sai da babba.”+
Jalila tace “to Ummy.”
Ummy tace “ko kinfiso kije da kanki? Ko mu tafi tare?”
Da sauri tace “a”a wlh Ummy hakan yafi, ni me na sani a wannan harkar?”
Ummy tai murmushi ita kuma bataso subar Hassan shikadai dan Abba ya fita duba wani aiki.
Jalila tace “me za”a dafa da rana?”
Ummy tace “komai ma duk abinda miki.”
Jalila tai murmushi sannan tace “to Ummy nagode Allah ya saka da alkairi.”
Ummy ta kalleta cikin kulawa tace “Hassan fa?”
Jalila tace “yana daki.”
Ummy tace “nasan yana daki ai haryanzu bai sauko ba?”
Jalila tace “Ummy kema harkin gane? Ni na rasa me namai.”
Ummy ta guntse dariyar dake neman zuwa mata tace ” da alama dai kin mai babban laifi tunda har nima na gane.”
Jalila tai ajiyar zuciya tace “na kasa gane me namai, kuma shima ya ki fadamin.”3
Ameera da ta fito tasa dariya tace ” ba kunya?”
Jalila ta kalleta sannan tai saurin mikewa, sai yanzu ta fahimci bai dace ba.
Ummy tasa hannu ta rikota ta makama Ameera harara tace “to uwar sa ido, menene damuwarki? Ni bana sirikanta da ita “ya ta ce.”
Ameera ta kara yin dariya tace “hmm nayi shiru ai.”
Ummy ta kalleta tace “kicema Goggo ta shirya zamuje wani guri.”
Ameera tace “ina zaku bani?”
“Ko shirya dake zamuje kema, in muka sai kayan farko sai ke da Lantana da Goggo akaiku gidan ni da Sageer sai mu karasa siyan abinda ya kamata.”5
Ameera tace to, tai ciki da sauri.
Haka suka shirya Jalila na kusa da Goggonta, Goggo sai tambayarta take wai ina zasu? Itakam Jalila cewa kawai take nima ban sani ba Goggo.
Haka suka fito Sageer ya daukesu a mota, Jalila ta baishi da kallo duk ya canza da dai ba haka tasan Uncle ba, mutum ne faran faran dasan tsokana, yanzu kuwa ya rage sannan duk yadan rame.
Tana tsaye har motar tasu ta bar gidan sannan ta dawo ciki.
A falon kasa tadan kwanta dan mararta ciwo take mata daurewa kawai takeyi, mikewa tai can ta hau sama dan tana san shiga toilet.1
Hannu tasa ta bude kofar dakin dakin ta shiga, yana zaune a kasa yana cin abinci da alama baima dade da tashi ba.
Tana shigowa ya kalleta, itama kallansa tai ta tsaya sannan tace “Yaya ka tashi?”
“Umm, dazu.” Ya fada idansa na kanta, ta dan tsaya kafin tace “hmm su Ummy sun fita tare da su Goggo.”
Yace “okay.”
Tadanyi shiru kadan sannan tace ” duk tare suka fita.”
Yace “nagane, kina nufin daga ni sai ke kenan ko?”
Tace “hmm can gidan zasu.”
Yace “duk na fahimta.”4
Juyawa tai ta nufi toilet kafin ta kara juyowa tace “Yaya!”
Ya kalleta tace “abincin bai huce ba?”
Yace “me kikesan ji? Da alama wadannan maganganun naki akwai abinda kike san ji.”
Tace “bakomai.” Ta shige toilet.
Da kallo ya bita ya dade kafin yacigaba da cin abincin.
Tana fitowa yana gama cin abincinsa, tadan tsaya a jikin kofar saboda ciwon da mararta yakeyi gashi daga bayanta yake tahowa.
Da kyar ta taka ta zauna akan kujera tadan tukunkune.
Mikewa yai daga kasa ya juyo ya kalleta, bai kawo komai a ransa ba ya dauka dai kwanciyar tai ko toilet din data shiga ne ya sa ta.
Komawa yai ya zauna ya dau littafi, dan nishin datai kadan ne yasa ya juyo da sauri ya kalleta.
Yace “Jalila!”
Dagowa tai ta kalleshi a hankali tace “naam.”
Ganin haka yasa ya sauko da sauri yazo kusa da ita inda take a kwance, kusa da inda kanta yake ya zauna sannan yasa hannu ya dagota.
Kallanta yai itama ta kalleshi yace “menene?”
Tace “bakomai yaya…”
Yace “menene kikeyi to hakan?”
Tace “me nayi?”
Idanu ya kara kura mata sannan yace “menene? Karkisa na sake tambayarki.”
Ta kalleshi tace “marata”
Yace “ciwo?”
Ta daga kai alamar eh.
Yace “kinayi ne ko yau ne kika fara?”
Tace “inayi dama.”
Shiru yai yana kallanta yace ” menstrual pain?”
Kallansa tai sannan ta saukar da idanta kasa.
Yace “ko muje asibiti?”
Tace “a”a yaya zai daina zuwa dare.”
Idanunta tadan runtse dan abin karuwa yake yi.
Sa hannu yai ya dagota ya kawota jikin gado yace “kwanta.”
Kallansa tai sannan ta kwanta.
Zama yai kusa da ita yana kallanta, ita kuma idanuwanta a runtse suke tasa hannunta kan kasan cikinta.
Wayarsa ya dauko ya shiga google ya rubuta how to relieve menstrual pain.
Nan ya shiga dubawa, kallanta yai sa hannu ya gyara mata kwanciyarta zuwa rubda ciki.
Juyowa tai ta kalleshi yace “menene?”
Kai ya girgiza alamar ba komai sannan ta gyara kwanciyarta.
Shiru yai yana tunani, massage lower back and abdomen? Ta ina zai iya?
Mikewa yai tsaye da sauri ya koma kan kujera ya zauna dan jin yanda zuciyarsa ke bugawa da sauri.
Jalila kam abin ne ya kara motsawa juyawa tai ta kara dukunkunewa tana dan nishi kadan.
Kallanta yakeyi sai dai hankalinsa duk ya tashi.
Ya mike ya taso kusa da ita ya gyara mata kwanciyarta zuwa na dazu, idanunta ne suka ciciko ta kalleshi tace “yaya hakan bayamin dadi.”
Yace “na sani daurewa zakiyi.”
Tace to sannan ta gyara kanta tana runtse ido.
Jitai hannunsa akan kasan bayanta inda yake mata ciwo, kallansa tai, ya kalleta shima fuska a hade yace ” ki kwanta ba wani abin zan miki ba.”
Shiru tai ta kwanta, janye rigarta yai yana neman kaita wajen kirjinta, da sauri tasa hannu ta rike sannan ta kalleshi.1
Kallanta yai idanunsa na kanta ya sa hannu ya zare mata hannunta, shiru tai tana kallansa.
Sai dayakai rigar saman cikinta sannan ya tattareta a gun.
Hannu ya saka a bayanta yana mata tausa da hannayensa suka biyun.
Idanunta ta rufe gaba daya jikinta yai sanye, Hassan kam tausa yake mata sai dai daurewa kawai yakeyi.
Kallanta yai yace ” kinajin sauki? Naga haka suka rubuta haka akeyi.”
Ta daga kai idanunta a rufe dan bazata iya kallansa ba.
Hassan ya cigaba da yi mata, tun tanajin abin har bacci yai gaba da ita.
Ganin alamar bacci takeyi yasa ya kalleta, kusa da ita ya matso ya sa hannu akan gefen fuskarta yadan shafa kadan, meyasa kike sani yin abubuwan da ban taba tunani ba?
Ganin motsin idanunta sun canza da alama nauyin baccin nata ya fara raguwa, komawa yai ya sa hannu ya cigaba da yimata.
Sai can ya tsaya ya kalleta tana bacci hankalinta a kwance, murmushi yai wanda shikansa bai sani ba.
Sannan ya mike ya cire kayansa ya daura towel ya shiga wanka.
Bai dade ba dan yana tunanin karta tashi, a hankali ya bude kofar ya fito ya zo zaisa kaya.
Wayarta ce tai kara da sauri ya matso ya dauka, number Ummy ce ya daga a hankali yace “Ummy.”
Cikin mamaki tace “Hassan?”
Sageer dake kusa da ita ya kalleta, Ummy tace “Hassan kaine? Ina Jalilan?”1
Yace “bacci takeyi bata danjin dadi ne.”
Da sauri tace “lafiya? Me ya sameta?”
Yace “ba wani abun bane Ummy sako ne?”
Samun kanta tai da wani murmushi tace “a”a bakomai kace kartai abinci ta kwanta ta huta.”
Yace to ya kashe wayar.
Da kallo yabi wayar sannan ya kalleta, me nakeyi hakan?2
Ajiye wayar yai ya zo ya saka doguwar riga ta jallabiya sannan ya zauna akan kujera ga dau littafi wanda ya kasa karanta ko layi daya.
Sai kallanta da yakeyi, duk motsin datai a kansa.
Can ya daure ya koma ya maida kansa kan littafin, motsinta yaji, ya mike ya zauna a bayanta ya dan fara yi mata tausa a gun.
A hankali ta bude idanunta kallansa tai, yace “kin tashi?”
Da sauri ta kalleshi tace “yaya, bansan nayi bacci ba wlh yahkuri.”
Mikewa yai tsaye yace “ya jikin?”
Tace da sauki sosai, yace “ki tashi ki sake wanka amma yanzu kiyi da ruwa mai zafi, sannan kisha ruwan tea black ne.”
Tace “to.”
Juyawa yai da sauri ta riko rigar jallabiyarsa.
Juyowa yai ya kalleta, yace “menene?”
Tace “yaya nagode, sannan kayi hakuri.”
Shiru yai yana kallanta, yace “kin gode dame?”
Tace “taimakon dakamin.”
Yace “karkiyi tunanin wani dalili ne yasa na taimakeki, I really hate naga wani bashida lafiya, ko wanene na gani cikin wani hali ko ba ke bace zan taimaka mai.”
Kallansa tai jiki a sayaye sannan ta sakar mai rigarsa, ai dama batace dan ita special bace, me yasa wai yaya baya magana da sanyi?
Ta dan saukar da idanunta tace “nasani, duk da hakan nagode, sannan kayi hakuri da laifin da bansani ba.”
Ya sake kallanta yace “nagane tashi kiyi abinda nace, kina mace amma bakisan menene zai taimaki lafiyarki ba, na rasa me yasa gaba daya baki damu da kanki ba.”
Jalila ta kalleshi tadan canza fuska zuwa shagwaba tace “to ni ya zanyi?”
Yace “ba ni zaki tambaya ba.”
Ya juya ya zauna.
Mikewa tai tana mamakin yanda taji sauki, dan ta saba in har ta fara da safe to fa sai dare, in kuma da daddare ta fara sai safiya.
Dan ma tayi sa”a tanajin yanayin nan ta sanar ma Ameera ita kuma ta bata pads, ta boye a cikin basket na laundry din dake cikin toilet din.
Ruwa mai zafi tasa ta gasa jikinta ji tai jikinta ya sake warewa ta tsaya a toilet din, sanye da toilet, taya zata fita? Shiyasa fa daga ta tashi takeyin wanka in kuma batai da wuri ba sai ta bari ya fita takeyi, tunowa tai jiya daya ganta tana sa bra.
Shiru tai tana tunani, ta kalli kayan data cire wanda tasa a ciki basket din laundry.
Ganin ba yanda zatai ne yasa tadan bude kofar kadan ta leko kanta.
Shikuma yana jin alamun bude kofarta ya kalli gun.
Suna hada ido ta komar da kanta.
Mikewa yai dan ya fahimceta.
Agoggo ya kalla, yaga azahar tayi ya mike ya tada sallah.
Ita kuma tana komawa ciki ta jingina da kofar toilet din, massage din daya mata dazu ta tuno, da sauri ta girgiza kai.
Sake lekowa tai taga yana sallah, a hankali ta fito tazo jikin wardrobe ta bude ta zura hijab.
A cikin hijab din tasa bra sannan ta zura skirt ta sa riga sannan ta cire hijab din ta matso jikin madubi ta shafa mai sannan ta fesa body spray da turare.
Kallansa tai yana zaune akan sallaya ta lalaba tai waje.
Tana sauka ta hada tea kamar yanda ya sata tasha, sannan ta koma kitchen ta bude fridge ta dauko nama zata sa tafashe.
Bayan ta fita ne yai tunanin yanzufa sai ta tafi sa abinci ko?
Mikewa yai ya sauko kasa, kitchen ya nufa, ya taka ciki ya shiga.
Raban da Hassan ya shiga cikin kitchen shikansa ya manta, ko magana zaiyi sai dai ya tsaya daga falo, ko kofa.
Juyowa tai jin motsin shigowa, kallansa tai cikin mamaki tace “yaya!”
Me zance? Abinda zuciyarsa ta tambayeshi kenan.
Hade rai yai yace “ruwa zaki bani.”
Tace “ruwan sama har ya kare?”
Yace “a”a ba sanyi ne.”
Cikin mamaki ta mikomai robar ruwa tana cewa ko na kashe fridge din?
Mikamai ruwan tai yasa hannu zai amsa, kan hannunta hannayensa suka taba, kallansa tai shima ya kalleta.1
A hankali ta zare hannunta ta dan juya.
Ya amshi ruwan kafin yace “me kike? Ke da ba lafiya ba?”
Tace “abinci zanyi kaga ba kowa a gidan.”
Yace “dan ba kowa sai akace mara lafiya yai abinci?”
Ta juyo tace “ba haka nake nufi ba, kaga sanda zasu dawo ne a gajiye zasu dawo.”
Yace “in ance bakya kula da lafiyar ki kice ba haka ba, to Ummy ce tace karkiyi.”
Ya juya ya bar kitchen din.
Da kallo ta bishi, tadan yi ajiyar zuciya tace “oh ni, yanzu ma laifi na sakeyi?”
Maida namantai cikin fridge din sannan ta fito.
A falo ta sameshi tace “Yaya!”
Ya kalleta yace ” kin warke ko na kaiki asibiti?”
Tace “Allah na warke har mamaki nakeyi.”
Ya juya ya hau sama.
Shiru tai tare da binsa da kallo.
1
*******
Ummy kuwa tana kashe waya ta saki wani murmushi, Sageer ya kalleta yace “Ummy wani abun ne?”
Tace “a”a bakomai, kawai dai abin ne kemin dadi, dan na tabbatar yanzu Hassan ya fara san matarsa.”
Sageer ya kalleta wani abu ya ratsomai, ya daure yai murmushi yace “ai Ummy ki daina damuwa na tabbatar Yaya zaiso Jalila yanda bakya zato, tanada halayen da zaija ra”ayinsa.”2
Ummy ta jinjina kai cikin jin dadi tace “sosai ma, na yarda dakai Sageer.”
A tare sukai murmushi Ummy tace “ya kukai da Goggo dazu?”
Sageer yace “ai bakiga kukan datake ba nidai har na taho tana kuka akan itakam da munbarta ta koma kauye ina ita ina wannan gida haka?”
Ummy tai murmushi tace “Sageer in na tuno abinda mutanen nan sukayima Jalila da mahaifiyarta sai naji kamar bai kamata mu kyalesu ba.”
Yace “hakane Ummy koni abin na damuwa, bansan haka tai rayuwa ba.”
Ummy tace “nikaina, sai dai mu barma Allah komai.”
A ransa yace “bansani ba Jalila, bansan haka kikasha wahala a rayuwa ba, i am really sorry…….”
*******
Suna saukowa Dady ha kalli Mumy yace “mumyn Yasmeen me kikeyi hakan?”
Rungumeshi tai tace “ba sai ka shiga maganar nan ba, wannan shikadai ne hanyar da zaisa Inna tadinga ganin girmanka.”
Dady ya dago ya kalli sama, inna ya gani a tsaye tana kallansu, murmushi ya mata sannan ya kankame Mumy tare da sa kansa a wuyanta.
Inna ta dunkule hannunta sannan ta juya, snake yanzu kake nunamin abinda ke boye a kasan zuciyarka, u really try na yanda ka boye fuskarka a cikin mask ba wanda ya fahimci abinda ke tattare da ita.1
Tace sai dai ka makaro dan kana tafin hannuna wlh.
Goggo tana zaune tana kara bin gidan da kallo, hawayenta yaki tsayawa, ashe alheri ne a dukulle a tattare da sharrin da aka jefesu dashi.
Ba wani katon gida bane, falo daya ne babba sai 2bedrooms a cikin falon da toilet daya.+
Sai tsakar gida kato wanda za”a iya ajiye motoci kananan guda biyu.
Ameera da Lantana dake sa labule ta kalla tama rasa ta ina zata fara, ashe a rayuwa akwai rana irin wannan? Shiyasa mutane ke cewa Allah yasa muci darajar “ya”yan mu, a da bata fahimtar abinda ake nufi da hakan amma yanzu ta gane dalilin fadan hakan, in kai a rayuwa bakai sa”ar abokin zama ko iyaye ba sai ka nemi sa”a akan “ya”yanka.1
Hawayenta ta share, ko mahaifiyarta da mahaifinta nada rai?
Haka su kai ta aiki, itama tana tayasu, sai yamma su Ummy suka dawo, sun siyo abin kitchen, tv set, toilet, abinci da sauransu, dama zuwan farko aka siyo kujeru, gado da labulaye.
Haka suka taho musu da gashashiyar hanta da juice suka ci suka sha, Ummy ta nunama Goggo kawai komai ta samu tayi. Hamdalla bawai taita kuka ba, hakan yasa ta saki jiki sukaci abinci tanata godiya.
Sai wajen Magrib suka kammala komai, Ummy tace su tafi, sai asa ranar tarewarta.
Goggo tai shiru tana tunani, Ummy ta matso tace “lafiya? Ko kina tunanin zama ne gaba daya?”
Goggo tace ” indai hakan zai samu nafisan hakan, dan maganar gaskiya kunyar gidan nakeyi.
Ummy tace “shikenan ai ba wani abu bane, in har hakan yafi kwanta miki a rai, sai dai kamar ba”a gama jan wutar gidan ba, sannan bamu siyo generator ba.”1
Goggo da sauri tace “hakan ma ya isa, ba sai anja wutar ba dan acan gidan ma bamu samu wannan darajar ba ni har na rasa ta inda zan soma yi muku godiya.”3
Ummy tace “dan Allah ki bari, yanzu bari mu barku anan, sai nasa yanzu Sageer ya samo katuwar fitila kafin a gyara wutar gidan, kayanki kuma gobe in Jalila zata zo sai na bada a kawo miki.”
Goggo ta kamo hannun Ummy cikin wani irin yanayi na farinciki tace ” nagode nagode, sai dai dan Allah ina da alfarma daya dazan nema.”
Ummu tace “menene?”
Goggo tace “Jalila tana bala”in san makarantar addini ta islamiyya, bansani ba ko da yanda zakuyi ku taimaka mata.”3
Ummy tace “basu sata a makaranta ba?”
Tace “basu sata ba, karatun da nake dashi kadan shi na koya mata.”
Ummy tai shiru tana tunanin wannan muguntar kafin tace “shikenan zan sanar ma mijinta, hafizi ne na karatu dan da wuri ya sauke alqur”ani zan ji shawarar da zai yanke.”3
Goggo tace “nagode sosai.”
Haka suka fito sukabar Goggo da Lantana a gidan, sai da suka sai katuwar fitila suka kai musu sannan suka fito.
Ummy a hanya ta kalli Sageer tace “Sageer akwai iyayenda in basuyi wasa ba alhakin “ya”yansu shine dalilin da zaisa su shiga wuta.”2
Sageer yace “Ummy nikam haryanzu kwakwalwata na mamakin irin wannan mahaifin, wanda san kansa yamai yawa da har baya damuwa da halin da “ya”yansa suke ciki.”
Ameera ta kalli Ummy tace “Ummy nikam dan Allah kumin bayani, wai ya akai Goggo ta zama mahaifiyar Jalila, Mumy fa? Nifa gaba daya na rasa meke faruwa tun jiya nakesan yin tambaya.”1
Ummy tasa yatsa ta ta tura goshita tace “gulmar me kike sanji? Magana daya dai wannan ce mahaifiyarta me kike nemanji bayan wannan?”
Sageer ya sa dariya yace “Ummy in Ameera batai gulma ba ai ba Ameeran bace.”
Cikin shagwaba tace “Yaya Sageer haka zakace? Harda wani in banyi gulma ba?”
Ya kara sa dariya yace “To yahkuri ba gulma ba.”
Ummy ta kalleta tace “ba wani tayi hakuri, ai dama uwar gulma ce da san jin komai.”
Ameera ta kara shagwabewa tace “Ummy Allah ni abubuwan da nakeso in tambaya dayawa fa amma tun yanzu kunsa na kasa.”
Ummy tace “sai ki hadiye gulmarki inkin samu Abbanki sai ki tambayeshi.”
Tace “shikenan ai nasan Abbana bazai min haka ba…”
Haka sukai ta zolayarta suna dariya cikin farinciki har suka isa gida.
********
A can gida kuwa Hassan tunda ya shiga daki ya zauna a bakin gado yai shiru yana tunani, tabbas gaba daya rayuwarsa ta canza a “yan kwanakin nan, gaba daya yarinyar nan taki barin zuciyarsa.
Abu daya ne ya fara zuwa mai badai santa kake ba?
Da sauri ya girgiza kai yace “so? Ni? Yarinyar nan?”
Kai ya sake girgizawa alamar ba haka ba yace “tausayine.”
Tausayi akan me? Ka tabbatar shi kadai ne? Damuwar da kakeyi fa in abu ya sameta?
Tambayar dake tamai yawo a zuciya kenan, shiyasa ma gaba daya daga ta shigo sai yai gamar yana bacci, ko ya dau littafi wai a dole karatu hakeyi ko ya dau wayarsa….
Ita kuwa daga baya ta sauka falon kasa ta zauna.
Bayan tayi sallar isha”i ne Abba ya dawo, ta gaisheshi ya amsa fuska a sake bai dade da dawowa ba su Ummy suka dawo.1
Tanajin dawowarsu ta tashi da sauri tazo taryarsu.
Ummy ta kalleta cikin kulawa tace “Jalila jikin ne?”
Tace “na warke Ummy gashi banyi abinci ba.”
Tace “nina hana kiyi, bakida lafiya wake ta abinci?”
Sunkuyar da kanta tai, Ummy ta amshi ledar hannun Sageer tace “ga shi kije kuci da Hassan muma munyo namu tsarabar.”
Jalila ta amsa tace “angode.”
Ta fada sannan ta leka bayan Ummy, Ummy tace “tana can.”
Jalila ta sunkuyar da kai tace “tam.”
Ameera ta matso tace “ya jikin?”
Jalila tace da sauki.
Ummu tai gaba Ameera ma tabita, ta kalli Sageer tace “Sannu da zuwa.”
Kallanta yai yace “ya jiki?”
Tace “na ware ba wani serious bane dama.”
Ya kalleta cikin kulawa yace “Sannu Allah ya kara sauki.”
Tace Ameen ta juya, da kallo ya bita.
Kowa daki ya shiga da ledarsa dan duk sun gaji.
Jalila ta wuce sama.
Tana shiga ta sameshi a zaune, yana ganinta ya dau littafi wai karatu yake.
A ranta tace ko gajiya bayayi.
Ta matso dan dama ta dauko plate daga kasa, ta bude tace “yaya sauko Ummy ta kawo mana abin dadi.”
Kallanta yai yace “menene abin dadin?”
Ta bude kedar ta ciro ledar juice sannan ta ciro foil paper ta bude, kaza ce da kuma daurin kundu wanda yasha hadi na musamman.
Juyowa tai ta kalleshi, kallanta yai sannan ya sauko fuska ya zauna, dandai yunwa yakeji amma da cewa zaiyi bazaici ba.
Kallansa tai batasan yanda zata raba musu ba gashi plate daya ta dauko, kallansa tai shima kallanta yai tace bari na dauko wani plate din.
Ta fada tana kokarin mikewa, hannu yasa akan hannunta data dafa kasa zata tashi, kallansa tai, yace “muci tare.”
Tace “naam?”
Yace “me? Dama ba haka kikeso ba?”
Tace “nakeso kamar ya kenan?”
Yace “duba ki gani, kinsan mu biyu ne a dakin nan kika dauko plate daya, yimin bayani meyasa kikai hakan to?”2
Jalila ta kalleshi kamar zatai magana kawai sai tasa dariya tace “lalai Yaya, yanzu nace zan dauko plate ka hanani sannan kace nice nakeso.”
Yace “to ba hakan bane?”
Tace “wlh ba haka bane, ni na…..”
Yanda ya mata da fuskarsa ne yasata ta kasa magana alamar bayarda zaiyi da duk abinda ta ce ba.
Bismilla tai tasa hannu tana cewa “shikenan tunda an dakeni an hanani kuka.”
Bai tanka mata ba yasa hannunsa, a tare suka fara ci, itadai kunya take, shikam wani irin sanyi yakeji a ransa, yana kallanta yasa hannu cikin plate din, a kann hannunta yasa hannunsa.7
Dagowa tai ta kalleshi, kallanta yai sannan ya kalli hannunsa, yace “yanzu nine nasa hannuna ko kece?”
Tai dariya sannan ta kalli hannun nashi tace “to hannun waye a sama?”
Ya kalla yace “nawa ne sai dai me yasa nakeji a jikina kamar dauramin akai?”1
Tace “me? Daurama?”
Dariya ta fara yi tana kallansa, samun kansa yak da shagala gun kallanta, wanda har bai san ganin yanda take dariya yasashi sakar murmushi ba.
Tsayawa tai da dariya tace “Yaya! Kasan kayi murmushi yanzu?”3
Fuska ya hade tare da zare hannunsa da sauri yace ” a ina nai murmushin?”
Tace “wallahi kayi yanzu, baka san kayi ba?”
Juya kansa gefe yai yace “u are mistaken.”
Tai shiru tana kallansa kafin tace ” mistake nai? Amma na tabbatar naga kayi murmushi.”
Yace “are u sure ba hakan kike san gani ba?”
Tace”wannan karan bazan musa ba, dan ina san inga ka yi murmushi kullum fuskarka a daure take.”
Ya kalleta tare da daukan cup din juice yasha.
Haka sukaci abinci tare sannan ta mike ta wanke hannu ta sauka kasa dan kai plate.
Tana fita ya saki ajiyar zuciya yace “Hassan?”
Gaban madubi ya koma ya kalli kansa, a hankali naga yanayin fuskarsa ya canza zuwa tashin hankali, yasa hannu ya bude drawer karshe ta jikin madubi.
Wani littafi ya dauko ya bude tsakiyar hoto be ya bayyana, kallan hoton yai cikin wani yanayi sannan yamaida hoton ya rufe ya runtse idanunsa, bancancanci farinciki ba, ban kuma cancanci inso ko a so ni ba.4
Mikewa yai ya dafa kansa dake sarawa……..
Gaba daya ranar bai sake magana ba har ta gaji ta kwanta dan ba alamar fuska.
Washegari ma da Ummy tace ya kaita gidan Goggo bai musa ba ya jira ta suka fita tare, yana kaita kofar gidan baijira me zatace ba yai gaba.
Da kallo tabi motar tana mamakin abinda ya faru, ko a mota duk yanda taso suyi magana kin yarda yai.
Shikuwa yana ajiyeta yaja mota yana tunani.
Jalila kam tana shiga gidan Goggo ta saki baki tana kallan iko Allah, ta shigar da kayan data taho dashi, nan suka zauna suka hau hira cikin farin ciki.
Lantana ma ta zauna sukaita hira.
Goggo cikin hira ne take tambayarta wanda ya kawota.
Jalila tace driver dinsu ne ya kawoni, Yaya ya fita ne.
Goggo tace “Allah sarki, na dauka shine ince bai shigo mun gaisa ba na mai godiya.”
Jalila tace “zaizo shima.”
Haka sukai ta hira suna tuno rayuwar baya da yanda sukasha wahala, Goggo tanata kara nuna mata ta kula da mutanen nan dan tabbas sun musu hallacin da basu taba tunani ba.
Jalila jefi jefi tana tuno abinda yaya ya mata yanzu da zata sauko, ta fito ta kalleshi tace “Yaya baza……”
Gano tai ya dauke kai yana neman wucewa.
Tsayawa tai dagalo tana kallan ikon Allah kafin ta shigo.
Meya sameshi?
Sai bayan magrib yaro ya turo ta fito, tana fitowa taga Mamman, jikinta ne yai sanyi ta bude bayan mota ta shiga tayima Lantana da Goggo sallama akan sai ta dawo.
Haka suka hau hanya, ta kasa daurewa tace “Mamman ina Yayan?”
Yace “wlh Hajiya bansani ba, waya yamin yace in daukoki.”
Tace “okay.”
Haka suka isa gida taitama Ummy godiya da Abba.
Kafin ta hau sama.
A daki ta sameshi yana karatu, sallamarta kawai ya amsa shima baiko kalleta ba, Jalila ta daure tace “Yaya na dawo.”
Yace “naganki.”
Shiru tai a tsaye kafin ta nufi toilet, tai wanka ta sa kayan bacci sannan ta fito ta dau bargo ta shimfida tana cewa “Yaya bacci nakeji, yau da alama na zama kasa, ko dan banyi baccin safe bane? Ina ta zumudi?”
Bai tanka mata ba, tai dariya tace “hmm basa banba, ni fa da agida bansan ma wani baccin safe ba amma yanzu jin dadi yasa har in banyi ba sai naji wani iri.”
Bai tanka mata ba hakan yasata yin shiru, ta sa bargo ta kwanta, bata dade ba bacci ya dauketa.
Juyowa yai ya ajiye littafin ya kura mata ido, idanunsa ne suka canza kala a fili yace ” Jalilah! Jalilah!”
Sannan yai shiru, mikewa yai ya shiga toilet ya watsa ruwan zafi sannan ya zura riga, harzai wuceta ya tsaya, sai kuma ya koma ya zauna kusa da ita.
Hannu yasa a gefen fuskarta yana kallanta cikin wani yanayi.
Cikin wata raunaniyar murya yace ” nasan i am hurting u, sai dai kafin kiji zafin abinda nake miki ni na ji zafi, duk sanda na wulakantaki inaji a jikina sai dai bansan ya zanyi ba, Jalilah bansan ya zanyi ba banasan naga na dawwama a koda yaushe a cikin kuntata miki.”
Shiru yai yanajin wani abu a kirjinsa kafin yace “Jalila Husain…….”
Ya runtse ido a hankali wasu hawaye naga sun zubomai masu zafi, hannunsa yakai kan labanta.
Idanunsa ya sake rufewa a hankali ya shiga matso da kansa ya sumbashi bakinta, bakinsa ya bari a kan labanta.3
Idanunta ta bude, me zata gani?
Shima idanu ya bude suka kalli juna, da sauri tasa hannu ta tureshi, ya mike tsaye da sauri.
Tace “Yaya!”
Yace “bargona nakesan dauka sanyi nakeji.”
Tace “bargo?”
Bargo a…….
Ta kasa karasawa, yace “bargo a me?”
Tace “bakomai, nagane tun jiya kaki kulani, yanzu kuma gashi kanamin magana.”
Yace “yanzun ma bakiji me nace miki ba? Bargona zaki bani.”4
Tace “to in na baka in shimfida me?”
Ya kalleta taya zaiyi yace mata shi kwanan kasan ne bayaso?
Ya hade fuska yace “sai ki kwanta akan gado ni sam laushin katifa samin ciwon baya take.”1
Da sauri tace “haba? Da gaske na kwanta?”
Ya kalleta sannan ya dau bargonsa ya kwanta akasa.
Murmushi tai sannan ta hau kan gado tana dariya jin dadi.
Can kuma tace “yaya badai barmin kai ba?”
Yace “barmiki? Bakiji me nace ba?”
Tace “oh naji.”
Ta kwanta tare da juya baya.
Shiru tai kamar mai bacci tana tunanin abinda ya faru yanzu, hannunta takai kan labanta ta shafasu, shima kwanciya yai yana tuno abinda ya faru, me yakai shi? Baisan ya akai yaji a lokacin sumbatarta yakesan yi ba.
Ahhh kansa ya shafa yace “Hassan!”
Yana cikin barci wajen karfe uku taji ana wani irin numfashi sama sama, yanzu kam ta riga tasan shine da sauri ta sa hannu ta danna waayarta sannan ta kunna fitilar dakin, yau a rufda ciki ta gashi ya tukunkune daga can gefe hannunsa nakan wuyansa gaba daya zufa ce take keto masa, mikewa tai da sauri tazo kusa dashi.
Hannuntasa ta janye hannunsa daga kan wuyansa, idanunta sun ciciko tana kiran sunansa.+
Amma ina, hannunsa ya fizge daga gunta ya rike kansa dake wani irin sarawa, Jalila ta ga yau abin nasa dayawa dan har pillow ya dauka ya danne kansa dashi.
Cikin tsoro da tausayinsa yasa ta janyowshi ta rungumeshi ta baya tare da sa kuka tana cewa “Yaya! Yaya dan Allah kandaina…….”
Jitai jikinshi duk yanata ketowa da zufa, sakeshi tai da sauri ta kure karfin AC din dakin sannan ta dawo a rikice ta kara janyoshi tana kuka.
Yau abin ya dade dan ita kawai data rungumeshi ta kifa kanta a jikinsa bata sake dagowa ba.
A hankali numfashinsa ya dawo, ya bude idanunsa, ganinshi yai a jikin Jalila tanata kuka.
Shiru yai cikin takaici abinda ke faruwa wanda gashi duk sanda abin ya tashi sai yasa Jalila kuka haka.
Mikewa ya fara kukarinyi, idanunta ta bude ta daukeshi a kansa, da sauri tace Yaya?
Zama yai sannan ya jawota kusa dashi, jiki a sanyaye take kallanshi.
Bata an kara ba taji ya rungumeta tsam, ya kwantar da kansa kan kafadarta.
Bakinta na rawa tace “Yaya!”
“Let”s stay like this for a moment……” cikin wata murya mai sanyi ya fadi hakan, shiru tai ta kasa motsi.
Can yasa hannu a bayanta kamar me lallashi yace ” sai yaushene zaki canza hobby dinki?”
A hankali tace ” to ya zanyi duk ka canza lokaci daya, ga…..”
Yace “are u worried about me or are u scared?”
Tace “zaka fara ko Yaya?”
Shiru yai kafin ya saketa ya kalleta yace “irin wannan kure mana AC haka fa?”
Ta tashi ta dau remote tana cewa, zufa kaketayi shiyasa na kunna.
Ya kafeta da ido yace “kin tabbatar dan ni kika kunna?”
Tace ” ban gane ba???”
Yace “a”a to haka kawai dan ina zufa sai a kure AC haka?”
Ta kalleshi tace “nikam ko dan ka kwanta a kasa ne? Naga ka dade lafiya.”
Kallanta yai sannan ya girgiza mata kai yace “ko daya.”
Ta kalleshi bayan ya mike daga gun tace “Yaya nikam dan Allah meke damunka? Mafarki kakeyi? Ko…….?”
Sai kuma tai shiru, yace “ko aljanu gareni?”1
Da sauri tace “ba haka nake nufi na….”
Ruwa ya dauko yasa sannan ya dawo ya kwanta, kallanta yai da take dukushe a gun yace “Hajiya zan kwanta.”
Tace “Hajiya? Lalai Yaya matar da bata taba zuwa hajj ba, batama iya karatu sosai ba itace Hajiya.”
Juyowa yai ya kalleta sosai yace “daki shiga islamiyya ku dinga zuwa da Ameera da kuma ki zauna a gida wanne yafi?”
Tace “in zauna a gida kamar ya?”
Tai tambayar tana kallansa, juyawa yai baice komai ba.
Da sauri ta kalleshi tace “da ka koyamin a gida?”
Idanunsa ya rufe da sauri tare da harde hannayensa, ta sako kanta tace “Yaya dagaske?”
Bude idanunsa yai, sam baiyi tunanin ganinta daf dashi haka ba, idanunsa ne ya sauka a nata, da sauri ta mike tsaye ta hau kan gado ta kwanta tare da saurin kashe fitilar dake jikin gadon.
Kwanciya tai tana dan ajiyar zuciya a hankali.
Dakin ne ya baibaye da duhu.
Tana kwance sai dan juye takeyi, can tace “yaya kayi bacci?”
Shiru yai baice komai ba sai dai yana jinta, tadan sake ajiyar zuciya kadan.
Muryarsa taji yace “baki taba tambayata dan uwana ba, bayan duk wanda yaji sunana Hassan ya tabbatar inada Husain.”
Juyowa tai ta kwanta akan tafukan hannayenta ta jiyo ta saitinshi, duk da duhu ya sa bata ganinshi tace “taya zan tambayeka abinda ka kasa fadama kowa?”
Shiru yai dan harta dauka bazaice komai ba sai taji yace ” shekararsa sama da 10 kenan da rasuwa.”
Zatai magana taji yace “tare suka rasu da dan kanin Abba, Sudais wanda yazo gidannan karatu.”
Jalila yanzuma hartace “sh……..”
Ya kara katseta yace “karkice komai kijini kawai.”
Shiru tai tana kallangun da yake.
Yace ” karki kunna fitila.”
Tai shiru, tare da kallansa, Hassan yana kwance yace “they died because of me……”2
Ya fada tare da runtse idanunsa da karfi yana jin wani abu na tokare mai zuciya.
Wasu zafaffan hawaye ne suka zubomai, yace “He is a bright person, mutum ne mai tsananin hakuri, a koda yaushe cikin fara”a yake Jalila………..”
Nauyin da zuciyarsa taci gaba dayi, ga numfashinsa na seizing ne yasa yai shiru, saukowa tai da sauri har tana buge kafa ta matso kusa dashi.
Tace “yaya!”
Ta dauka abin ne ya tashi.
Jinta a kusa dashi ne yasa yasa hannunsa dan jin a inda take, a durkushe a kusa dashi ya jita.
Hannunta ya riko sannan ya kwantar da kansa akan kafafunta dake a durkushe.
Da sauri ta kalleshi.
Hannunta ya riko.
Kallansa tai zuciyarta na bugawa da sauri, a hankali tace “karka cigaba yaya inhar zuciyarka bazata iya dauka ba, sannan bansan menene yafaru tsakaninku ba amma na tabbatar ba…………”
Yanzu ma katseta ya sakeyi, yace “don”t comfort me.”
Shiru tai, yace ” nikaina bansan meyasa nakesan fadamiki abinda ban fadama kowa a duniya ba, sai dai ina alakanta hakan da zaman da nai dake sannan da yanda nasan komai naki.”3
A hankali ya lumshe ido zuciyarsa na kunna, yace “later…..”
Kai ta daga tace ” later Yaya…. sanda kaji zaka iya.”33
Kansa ya kara gyarawa, shiru tai sai jikinta dayai sanyi, zuciyarta na bugawa da sauri.
Ya dade a haka kusan minti ashirin kafin yaji an fara kiraye kirayen sallah, ita ta dauka ma bacci ne ya daukeshi, ga kafarta ta fara zafi.
A hankali ya dagata sannan ya mike ya kunna wutar dakin.
Haske ne ya baibaiye dakin, kallan juna sukai, ya dauke kai ya shiga toilet.
Yana shiga ya kalli kansa a madubi, yanzu kam ya tabbatar ya fara san yarinyar nan, garin yaya? How can i??? Ya furzar da wata iska.
A inda ya barta anan ya ganta, ya kalleta yace “me kike anan?”
Da sauri ta mike ta fara ninke bargo tace “bakomai.”
Kallan fuskarsa tai, tanaso taga canji a tattare dashi, kallanta yai yace “kallan fa namenene?”
Ta mike rike da bargo tace “bakomai, ba kai na kalla ba.”
Yace “then?”
“Uhmm yauwa toilet na kalla.”
Sallaya ya shimfida batare da ya kalleta ba, ta mike da sauri ta shiga toilet.7
Tana rufe kofar tai ajiyar zuciya tace “meke damun yaya? Ya tone din maganarsa ta koma ta da?”
Shima tana shiga toilet ya kalli kofar toilet din sannan yai ajiyar zuciya shima, ya tadda sallah.
Pad ta canza ta fito, yana sallah ta fito, zama tai a bakin gado tana dan lekashi.
Yana idar da sallah ya bude qur”ani, jitai yace “taso.”
Da sauri ta taso tace “gani.”
Ya kalleta sannan ya kalli kasa, da sauri ta zauna a kasan carpet, tana kallansa.
Ya kalleta fuska a hade yace a ina kika tsaya?
Tace can karshe, ta fada tana neman taba qur”anin, da sauri ya rike hannunta sannan ya kalleta, itama kallansa tai dan batasan me tai ba.
Yanda yaga tana kallansa ya fahimci batasan ma metai ba, yace “ba asan taba qur”ani izu sittin in mutum na fashin sallah.”
Kunya ce ta kamata, ta kalleshi.1
Sake mata hannnu yai sannan yace can kasa ina?
Tace “a ikira.”
Kallan mamaki ya mata kamar zaiyi magana sai ya fasa.
Nan ya bude ya yafa biyawa, tana zaune a gefe tana biyawa.
Sura daya sukai yace “sai gobe kuma.”
Kallansa tai tace “nagode Yaya.”
Bai amsa mata ba ya fara karatunsa, mikewa tai ta zauna akan gado, can dai ta fito falo ta kwanta sai bacci.
Hassan kam ya dade yana karatu kafin ya kwanta akan sallayar, bacci yai gaba dashi.
1
************
Inna ta kalli Mumy wacce ta kirata tace ” Abakar ya tafi gun aiki?”3
Tace “eh.”
Inna ta kalleta tace “haryanzu fishin kikeyi dan nace mijinki yace shine yai komai?”
Ta kalleta tace “Inna dan Allah Abakar yaci darajar jikokinki.”
Tace “kamar ya?”
Mumy ta kalleta tace ” ki barmai company din nan dan Allah, karfa ki manta yanda yake kokari ganin komai ya tafi daidai, sannan mijinki yarka ne fa? Sai yaushe ne zaki maidashi d”a?”
Inna ta kalleta tai murmushi tace “a koda yaushe in kina abu mamaki yake bani, ke wai sai yaushene zaki fahimci wanene Abakar? Sai yaushe ne zaki gane ba saboda ke yake zaune agidan nan ba, ba saboda ke yakemin ladabi ba?”
Cikin takaici tace “ko ma saboda me yake tare da ni bai dameni ba, tunda ni haryanzu ina sanshi kuma banasan “ya”yana su rabu da mahaifinsu.”
Inna tai shiru tana kallanta, wannan fa bazata fahimci komai ba, tace ” to naji, sai ki shirya muje gidan mu basu hakuri, in kuma ni kadai zanje ba laifi bane.”
Da sauri ta kalleta tace “da gaske?”
Tace “eh, sannan ki bar maganar bashi company din zuwa wani lokacin, in komai ya daidaita zan nadashi a matsayin shugaba ni kuma nai resigning.”1
Da sauri mumy ta taso tazo ta rungume inna tace “godiya nake Inna ta.”1
Inna ta kalleta kawai, cikin murna ta fita.
Inna ta bita da kallo tace “i know she is naive but I don”t expect her to be foolish, ta bari yaranan duk ya gama lalatata da dadin baki.”
Tai kwafa sannan tace “bari na gama tallafo company din, in na ma da Taura zan dawo kanshi.
*********
Ummy ce ta kalli wayar hannunta wacce aketa kira tana rejecting, Sageer wanda kecin abinci yace “Ummy wai waye yaketa kira haka?”
Ta kalleshi kawai tai murmushi dan batasan me zata ce ba, Zaliha ce, sam bama ta gajiya da kiran wayar.1
Ummy ta kalleshi tace “ya maganar takardun naka?”
Yace ” gamunan dai muna jira basu bamu ba.”
Haka suka gama yin break, ta kalli hanyar sama tacema Sageer yau da alama bacci mai nauyi sukeyi naga shiru.
Sageer ya kalli saman shima sannan yai yake yace “da alama kam, sai dai Allah yasa ba ciwon yaya bane ya tashi.”
Da sauri ta kalli Sageer tace “kasan Sageer tsabar naga Hassan yanata canzawa sam ina mantawa?”
Da sauri ta nufi hanyar sama.
Jalila bata dade da tashi ba ta kalli agoggo da sauri ta mike cikin mamakin baccin da tai, a hankali ta tura kofar dakin, Hassan na kwance akan sallaya yanata bacci ta wuce toilet.
Wanka tai ta fito a hankalita zura riga da skirt ma atamfa,tana shafa hoda taji knocking.
Da sauri ta kalli Hassan sannan ta taho gun kofar.
A hankali ta bude, Ummy ta gani, Ummy ta kalleta tace “Hassan fa?”
Tace bacci yakeyi.
Ummy tai ajiyar zuciya sannan tadan ja baya, Jalila ta fito ta kalli Ummy sannan ta gaisheta.
Ummy ta kalleta tana murmushi tace “sry Jalila wlh na dauka ko matsalar Hassan ne ya tashi.”
Jalila tace “a”a Ummy bacci ne ya daukeni wlh banmasan lokaci yayi haka ba.”
Ummy tai murmushi sannan tace “hakan yayi ai ki fito ki dauko muku breakfast.”
Tace to, Ummy ta juya, komawa cikintai ta fesa turare dannan ta yafa dankwalinta ta sauko.2
Tana fita daga dakin ya bude idanunsa sannan ya maidasu.
Sai dayai sama da minti biyar sannan ya mike ya shiga toilet.
Meyasa batacema Ummy komai ba?2
Har ya zauna sai kuma ya fito dan yanasan jin ya ake ciki akan maganar yar iskar yarinyar nan.
Bakowa a falon sanda ta sauko, Ummy ta jiyo a kitchen da sauri ta karasa ciki.
Ba ita ta gani ba, ashe Sageer ne yake dauraye kwanukan da yaci abinci.
Ta gaisheshi sannan ta karasa kusa dagun kadan tace “da ka barshi zan wanke.”
Ya kalleta ba tare da ya sake aikin ba yace “yaya fa? Jikin nashi ne?”
Kai ta girgiza mai tace “ba shibane bacci ne kawai ya daukeni.”
Yai ajiyar zuciya sannan ya cigaba da wankewa, ta sake cewa “dan Allah ka barshi nayi.”
Muryar Umny taji tace “barshi Jalila indai Sageer ne.”
Jalila ta fito Ummy na cewa “matar Sageer ta huta dan akwaishi dasan yin aikin girki da wanke wanke, kinsan da har shara yake tayani.”3
Jalila ta kalli inda yake tai yake tace “lalai akwai kokari.”
Ummy ta kalleta tace “Jalila bakida wata kawa ne ki hadasu?”2
Da sauri ta kalleta, Sageer ne ya fito hannunsa rike da plate yace “Ummy!”
Kallansa tai tace “menene? Da kacemin da wacce kakeso yanzu kuma naji shiru, kaga kwara ni na mike tsaye.”
Tai maganar cikin zolaya, Jalila ta kalleshi.
Ummy tasa dariya tace “meye hakan?”
Hannunsa ya kalla ya ganshi rike da plate, dariya shima yasa yace “Ummy ai duk kece.”
Jalila ce ta kalleshi itama tai dariya, Hassan wanda yake saukowa daga kan steps ya tsaya yana kallansu cikin jin dadi, Ummy ce ta fara hangoshi.
Tace “malam Hassan ina zaka bakai breakfast ba?”
Ya karaso kusa da ita yace “ba fita zanyi ba.”
Sageer ne ya kalleshi yace “Yaya.”
Kallansa yai yace ” mikakeyi da plate?”
Yai dariya yace “Ummy ce take neman tadamin hankali.”
Ya kalli Ummy, dariya tai sannan tace Wani abun kake so?”
Jalila ta kalleshi, gani tai ko kallanta baiyi ba, a hankali ta mike ta shiga kitchen.
Sageer ya biyota, wanke wanken ya karasa ya dauraye hannayensa ya fito, har yaje kusa da kofa sai ya juyo kamar zaiyi magana sai kuma ya fita.
Da kallo ta bishi sannan ta fara hada kayan abincinsu.
A falo kuwa Hassan ne ya kalli Ummy yace “ya maganar yarinyar nan?”
Tace “dazuma tayita kira ina rejecting.”
Yace “sim dinshi na gunki ne?”
Tace “eh.”
Yace “in har bata daina kira ba zuwa dare kimin magana, ni zan mata magana, in ta kama ma sai inje har gidansu naci mutuncinta.”
Ummy tai dariya tace “Ba sai ankai ga haka bama, insha Alla, Allah na tare damu.”
Jalila ce ta fito rike da tire.
Ummy ta kalleta tace “Jalila! Goggo tace ya kamata a saki a islamiya, shine nace zan fadama.” Takarass maganar tana kallan Hassan.
Itama Jalila shi ta kalla, hartace “Ummy ai……”
Hassan ne yai saurin cewa “karki damu da wannan Ummy, zansan yanda za”ai.”
Jalila ta kalleshi jiki a sanyaye tai sama.
Ummy ta kalleshi tace “kai Hassan! Wannan magana kamar ranka na bace?”
Ya kalleta yace ” haka kika gani?”
Tace “bani kadai ba har ita Jalilan, kalleta ka gani mana.
Juyawa yai ya kalleta, jiki a sanyaye take taka matattakalar.
Shiru yai tare da kura mata ido.
Ummy ta kalleshi sannan tace ” kaje kuyi breakfast.”
Ta fada tare da mikewa.
A hankali ya mike shima ya nufi saman, taje bude kofar, ya sa hannu ya bude mata.
Juyowa tai ta zuba mai ido…..
Shima kallanta yake…….