JALILA
CHAPTER 13
Kallanta yai yace “bazaki shiga ba?”
Juyawa tai ta shiga dakin, ta ajiye tiren sannan ta kalleshi tace “Yaya abinci.”+
Bai kalleta ba yace “sai nayi wanka.”
Ya fada tare da nufa ciki,, da kallo ta bishi tana mamakin halayensa.
Harta bude zata zuba sai kuma ta maida murfin kular ta rufe.
Hannu tasa ta janyo littafin da yake karantawa ta dauko, ta bude cikin littafin.
Ajiye littafintai sannan ta kalli hanyar toilet, ta mike ta fito falo.
Tv ta kunna tai shiru tana tunanin abinda ya faru tsakaninsu a daren jiya.
Kalamansa na kara dawo mata, meya faru a can baya? Wanda yake hanashi bacci? Yake hanashi shiga mutane? Yake hanashi murmushi? Yake hanashi zama cikin yan uwansa?
Shiru tai tana tunani, da alama shima yanada painful past wanda yafi nata.
Yana fitowa daga wanka ya shirya, ganin bata dakin ga motsin karar TV a falon yasa yasan tana can, sai dai bazai iya kiranta ba.
Zama yai akan kujera yana kallan kofa yana jiran shigowarta, dan yunwa yakeji.
Jalila kuwa ta shiga tunani sai can ta dawo daga tunanin nata, ta mike ta bude kofar, a zaune taganshi tana shiga suna hada ido, yana kallanta yai saurin dauke kai.
Ta shigo ciki tace “Yaya ka fito shine ba magana?”
Bai kalleta ba yace “inyi magana ince me?”2
Ta kalleshi tace “kacemin ka fito in taso.”
Ya kalleta yace “gashinan ai ban kiraki ba kin taso.”
Tace “lalai yaya, to bari nakoma sai ka kirani.” Tai maganar cikin zolaya.
Yace “nidai kafin ki koma bani abinci naci inyaso sai ki koma.”
Ta kalleshi tadan canza fuska tace “ba kara ma kenan? Bari na fadama Ummy to nace kace ba sai naci abinci ba.”
Baisan sanda ya dan murmusa ba yace “yaushe kika koma haka?”
Matsowa tai tace “yaya wlh yanzu bakinka ya motsa, wallahi yau na gani sosai.”
Tsuke fuska yai yace “yau menene ruwanku da dariyata?”
Tace “ni kuwa nake da ruwa yaya, bakasan yanda abin ke damuna ba, kome fa zakace fuskarnan a tsuke kake fada.”5
Kallanta yai yace “bakyaso?”
Ta daga kai da sauri tace “sosai ma, wani sa”in in tone din maganarka ya koma cold sai jikina yai sanyi.”
Kalaman Ummy ya tuno data fadamai dazu, kallanta yai yace “magana zaki tsaya yi bazakiban abinci ba?”
Ta dan turo baki ta nufi inda ta ajiye abincin, a ranta tana cewa what am I expecting?
Zubamai tai tace “ka sauko.”
Yace “yanzun ma kin manta da plate din ne? Dan muci tare?”
Cikin shagwaba tace “yaya Allah fa ba haka bane.”
Yace “shagwaba kika koma?”
Ta kalleshi tace “yaya wai meyasa kakemin haka?”
“Menai?”
Ta kalleshi kamar zatai magana sai kuma tai shiru, a ranta tace “rannan kamin kiss bance komai ba, jiya ka kwanta a cinyata bance komai ba amma kai komai nai sai ka fassara.”
Mikewa taga yayi ya wuceta ya zauna a inda ta zubamai abincin.
Kallanta yai tana tsaye hannu yasa ya jawota, ta zauna a kusa dashi.
Kallansa tai tana mamaki tace “Yaya!”
Yace “wai ni yaushe nake yayanki ne? Kin kama suna kin rike kamar ke kika samin?”
Baki tadan turo sannan ta zuba abinci a nata plate din, gani tai yasa spoon dinshi cikin plate dinta.
Da sauri ta kalleshi yace “ba haka kikeso ba?”
Tace ” bangane ba….?
Bai kara mata magana ba yacigaba da ci, kallansa ta tsaya yi tama kasa ci, sai can ya kalleta yace “kin koshi ne?”
Spoon din ta maida ciki ta cigaba daci ta mamakin wannan abu.
Yana gamawa ya dau key ya bar dakin baice mata komai ba, baki ta saki tana kallan ikon Allah.
Saukowa yai kasa ba kowa a falon, yai hanyar waje.
Mota ya shiga kawai ya fita, Jalila ta dade a zaune kafin ta kwaso kwanuka ta fito.
Ganin bakowa a falon ta wuce kitchen ta wanke kwanukan, tasan Ameera na skul, da alama Ummy na daki.
Sageer fa? Bude kofar daki taji da sauri ta kalli gun.
Sageer ne ya fito sanye da kaya da hula da alama fita zaiyi.
Kallanshi tai shima ya kalleta, da sauri ta dauke kai ta juya zata koma kitchen.
Yace “Jalila?”
Tsayawa tai a inda take sannan ta juyo ta kalleshi.
Ya matso inda take kadan ya kalleta yace “ina making dinki uncomfortable ko?”
Kallansa tai ta girgiza kai alamar a”a sannan tace “a”a
Yai murmushi yace “kiyi hakuri Jalila.”
Tace “Uncle sai yaushe ne zaka daina bani hakuri? Bazance ban taba jin zafin abinda ya faru ba, dan da naji zafinka sosai sai dai a yanzu ko kadan banajin zafin ka, na fahimceka, nasan dalilinka.”1
Kallanta yai yace “nagode Jalila, nagode da fahimtar da kikamin.”
Ta kalleshi tace “Ummy tace duk ka canza, ni kaina nasan ba haka kake ba, Allah yasa banice sillar canzawarka ba.”
Ido ya kura mata kafin yace “ko kadan Jalila, inma akwai dalili to bazai wuce zuciyata ba wanda kuma basai kin damu da ita ba, zata daina da kanta.”
Kallansa tai tace “Uncle!”
Yace “kidinga cemin Sageer kawai, hakan shine daidai a matsayinki na matar yayana.”
Shiru tai kafin tace “saidai na kiraka da Yaya sageer yanda Ameera ke cewa.”
Yace “hakan yayi, nagode Jalila sannan Please let us take it to our grave, kar kowa yasan abinda ya faru.”5
Zatai magana sukaji muryar Ummy tana cewa “Sageer fita zakai?”
Da sauri ya juya dan baiji karar kofa ba, Jalila ma ta kalleta.
Ummy ta kalleshi tace “menene?”
Yace ba komai, na fito ne banganki ba nake tambayar matar Yaya.
Tace “ina ciki ina addu”oi.
Yace “Ummy zanje gun Abban.”
Tace “to Allah ya bada sa”a.”
Yace “Ameen ya fita.”
Ummy ta kalli Jalila tace “Jalila!”
Jalila ta matso tana cewa ” Ummy nikam banga Ameera ba.”
Ummy tace “sun koma skul yau dama hutu ya kare.”
Tace “oh shiyasa, naji gidan shiru.”
Ummy tai dariya tace “wlh kuwa, Jalila gidan namu is so boring.”
Jalila tai dariya itama tace “muma haka gidan yake, Sultan kullum yana daki yana game ko jin kida, Safeena kuma tana gun Mumy ko suna kallo ita da Yasmeen, Inna na sama, Mumy kuma itama ko tana falo ko daki, dama gun Goggo nane muke zama muyi ta hirarmu.”
Ummy tace “sanda kowa yake zama, bacci da kallo ke me kikeyi?”
Tace “aiki, girki, ko wanki.”
Ummy tace “hmm da alama ya kamata ki kara samun hutu a gidan nan, yanda kikai aiki acan ba hutu yanzu duk sai ki fanshe hutunki gun mijinki.”
Jalila tai dariya tace “ai nan gidan ba aiki Ummy.”
Tace “ba wani nan, ina mijin naki?”
Cikin kunya ta girgiza kai.
Ummy tai ajiyar zuciya tace “Haryanzu baice miki zai fita?”
Tace “eh, yanzu ma fa…..”
Sai kuma tai shiru tare da sa dariya.
Ummy ma tai dariya tace “Jalila bansan ke ba amma i am sure Hassan na sanki, idanunsa kadai sun tabbatar da hakan.”
Jalila ta kalleta sai dai batace komai ba.
Ummy ta dafata tace “Jalila godiya, kina sani farincikin dana dade bansamu ba, ganin Hassan na samun sauki yasa kullum zuciyata nakejinta tass, shikansa mahaifinshi yanzu hankalinsa yafi kwanciya har yake fita aiki ya dade haka.”
Jalila ta sunkuyar da kai a ranta tace me nayi? Ummy tace “mungode Jalila, sai dai ki kara hakuri sannan ki kara kula dashi, insha Allahu bazaki tabba dana sanin auran Hassan ba.”
Dagowa tai ta kalli Ummy sannan ta daga kai alamar to.
Hassan na fita yaje bakin wani shago yai parkin, fita yai ya shiga ciki.
Mai shagon ya tambayeshi abinda yakeso, Hassan yai shiru kafin yace “kawai abashi abunda ya dace.”
Cikin mamaki mai shagon yace “abinda ya dace kamar me kenan?”
Gidan mamar matata zankai, ya fada tare da dauke kai.7
Mai shagon ya guntse dariyarsa sannan yace “katan din juice fa?”
Hassan yace dame?
Yace sai ka hada ko da kayan tea ne.
Hassan yace “samin to.”
Nan mai shagon ya laftamai kayan tea dan kana kallan motarsa kasan da akwai kudi, ya sa mai juice kala uku a bayan boot ya cafki kudinsa.
Hassan na fita yace “Alhamdulila Allah ya kara kawoka.”3
Hassan ya shiga mota yai gidan Goggo.
Ya dade a waje yana tunanin abinda zaice kafin ya shiga.
Almajirai yasa suka shiga da kayan.
Goggo na zaune tana jin radio ana hada musu wuta a waje ya shiga ciki.
Tanaganinsa ta mike fuska dauke da fara”a tana lale lale.
Ya zauna ya gaisheta ta amsa cikin farinciki, shidai yai shiru.
Kowa ta tambayeshi sai dai yace “lafiya.”
Data gama tambayar tai shiru shima yai shiru.
Can yace “ba wuta ne? Naga kamar da wuta a layin?”
Tace “gyarawa sukeyi yanzu, Hassan mungode sosai sosai, Allah yayi albarka ya inganta rayuwa.”
Yace Ameen
Shiru suka karayi kafin ya mike yace zai tafi.
Tace “da wuri haka?”
Yace “eh.”
Tace “to mungode.”
Tana fitowa waje tai karo da kayayaki, nan ta kara mai godiya har ya fita.
Mota ya shiga yai ajiyar zuciya, sannan ya tada kota ya juyo gida.
Jalila kuwa bayan ta gama komai a kasa, ta daura abincin ran.
Yana shiga yaji motsi a kitchen, lekawa kitchen din yai, hangota yai tana aiki, yanka vegetables takeyi, tsayawa yai daga inda yake ya kura mata ido, gaba daya yanayin fuskarsa ya canza.
Ya dade yana kallanta har itama jikinta ya bata ta juyo.
Ganinsa tai a tsaye da alama ya tafi tunani, ta matso tace “Yayah!”
Kallanta yai yaganta a gabansa, tace “yaya naga kana……”
Da sauri ya wayance yace “kallan yanda kike aiki nakeyi, kin tabbatar kin wankesu kafin ki fara yankawa dai ko? Dan naga kamar baki wanke ba.”8
Cikin mamaki ta kalleshi, juyawa yai ya fita, da kallonta bishi,, yanzu kam ranta ya sosu, me yake nufi?
Haka ta cigaba da aikin ta ranta a bace, dan bakin cikin har kwalla ce tadan zubo mata.
Shikuwa yana hawa sama ya bude drawer ya dauko hoton Husain yana kallo, a fili cikin wata murya yace “Husain ya zanyi? Nasan bai kamata ba, bai kamata nai sha”awar rayuwa ta jin dadi da wata ba, ban cancanci yin farinciki ba, ban cancanci a soni ko inso wani ba sai dai bansan meke damuna ba, Husain i am really hurting her, wanda nakeji kamar na fita jin zafin abinda nake aikata mata.”
“Zuciyata na kwadaitamin yin rayuwa da ita, zuciyata na san ta kyautata mata, inasan ingana cikin farinciki, Husain inajina kamar bani ba.”
Yai shiru tare da rutse idanunsa, ya koma ya jingina da jikin drawer din, a ransa yace “Husain zan sanar da ita komai, dan abinda zuciyata ke rayamin kenan, in har na sanar da ita zan barta tai deciding abinda taga ya dace, inhar tana tunanin rabuwa dani shine mafita shikenan, in kuma…..”
Sai yai shiru, tare da kara runtse idanunsa,shiru yai ya dora hannunsa akan goshinsa yana tunanin abinda ya faru a baya.
Baisan hawaye sun zubo mai ba.
**********
Mumy ce ta kalli Dady bayan ta amshi hular dake kansa tace “Dadyn Yasmeen! Inna ta yarda.”
Yace “dame?”
Tace “bazata daurama laifin abinda ya faru ba.”
Yace ” meyasa kike takurama kanki? Nacemiki bakomai, zan iya yin komai indai a kanku ne.”
Ta ajiye hular ta rungumeshi tace ” karka damu, na fadama it”s my turn to protect you”
Kallanta ya shafa sannan yace ” nine ya kamata nai protecting dinki ke da yarana.”
A tare sukai murmushi……
Yanajin motsin shigowarta ya mike ya maida hoton sannan ya fito daga dakin, da kallo ta bishi tace “yaya!”
Ko kallanta baiyi ba bare tasa ran zai amsa mata, saukowa kasa yai ya zauna a garden.
Ita kuwa ganin yanda ya giftata ko kallanta baiyi ba tace “me kuma nai? Ni Habiba?”+
Abba ne ya dawo, yana sauka daga cikin mota ya hango kan Hassan, gunsa ya nufa.
Jin motsin tahowar mutum yasa Hassan juyowa.
Ganin Abba ne yasa ya juya yana kara tunani, Abba ya karaso ya zauna daf dashi.
A hankali yace “sannu da zuwa.”
Abba yai murmushi yace “Eldest me kake tunani? Naga ka dade banganka anan ba.”
Hassan yai shiru sai dai ya kalli Abba.
Abba ya sa hannu a kafadarsa kamar abokinsa yace “Mata ne?”
Da sauri ya kalleshi.
Abba yai murmushi yace ” na canka kenan.”3
Yai saurin cewa “a”a ko kadan.”
Abba yai dariya sannan ya sauke hannunsa daga kafadar Hassan, yadan yi shiru.
Hassan bai kalleshi ba yace “ina yarinyar? Ka daina tunaninta?”
Abba shima yana kallan kasa yadan hade hannayensa gu daya yadan matsa, yace ” ba kamar da ba.”
Hassan ya dan kalleshi yace “kana tunanin santa kake?”
Abba yace “yanzu gaskiya kakeso na fadama ko kuma abinda nasan zai kwanta maka?”
Hassan yace “gaskiya!”
Abba yadanyi murmushi kadan yace ” inayi sosai, sai dai kamar yanda mahaifiyarka tace zanyi kokari ganin na cireta a raina, dan ina ji a jikina ni kaina ba san daya kamata nake mata ba.”
Hassan yai shiru kafin ya jinjina kai yace ” nagode Abba da kake kokarin cire ta aranta dukda abin ba mai sauki bane.”
Abba ya riko hannunsa yace “kasan yanda hankalina ya tashi? Lokacin da naga kana fada akan abin? Nayi tir da zuciyata nayi dana sani wanda bazan iya misaltamaka ba.”
Hassan ya kalleshi sannan yace “bansan nima sanda na hau haka bane…..”
Abba ya kalleshi yace “naji dadi a kasan raina, at least inada wanda nasan zai hanani, kaga kamar Sageer na tabbatar bazai dage akan abinda nakeso ba, balle Amira, kai kuma ba lafiya ce dakai ba, balle ka hanani abinda zuciyata ke neman jefani, sai dai bansan har jikinka yayi sauki haka ba ina can ina shirme.”
Ya karasa maganar jiki a sanyaye.
Hassan yai shiru kafin yace “Abba a koda yaushe ka dinga tuna wacece Ummy a garemu, in har wannan tunanin na zuwa maka na tabbatar ba abinda zai gifta zuciyarka.”1
Kai ya jinjina yace “ni kaina bansan ya akai zuciyata ta nemi kawomin shirme haka ba, bayan nasan irin kaunar da kakema Mahaifiyarka, bayan kai din kaine rayuwata.”
Hassan ya kalleshi cikin wani yanayi na tausayawa.
Can ya dauke kansa da sauri saboda kwallar dake neman taruwarmai a ido, ya juya kansa da sauri.
Abba ya sake dafa kafadarsa yace “ya ya? Fada kukai da matar taka shine kai yaji?”1
Hassan ya kalleshi sannan ya dan murmusa kadan.
Cikin tsananin mamaki Abba yace “Hassan murmushi kai?”
Yace “wa? Ni?”
Abba yace “sosai ma kuwa, na tabbatar kayi murmushi yanzun nan.
Hassan ya mike da sauri, Abba ya jawoshi ya zauna ya riko hannunsa yace “nagode Hassan.”
Hassan ya kalleshi yace “name?”
Yace “na komai ma, kai d”a na ne wanda na haifa sai dai ban taba alfahari da komai a rayuwa ba kamar ka.”
Jiki a sanyaye yake kallansa kafin yace “bancancanci samun wannan matsayin ba.”
Abba ya dan harareshi yace ” in tuno ma?”
Da sauri Hassan ya mike dan ya fahimci abinda yake nufi yai hanyar ciki, Abba na cewa “in ban tuno ma ba na tunawa matarka.”
Da sauri ya shiga ciki, Abba ya bishi da kallo cikin tausayawa, har idanunsa suka dan canza, ya juyo tare da dan runtse ido yace “Alhamdulila!”
Tana kasa taga hawansa sama, da kallo ta bishi, shigewa yai.
Bata hau sama ba sai bayan magrib, dan sunatare da Ameera da Ummy bayan ta dawo daga makaranta, bayan magrib din ma Ummy ce tacemata dare yayi.
Ameera tai dariya tace “kai Ummy ba kara?”
Ummy tasa hannu tadan kwadeta tace “zaki fara ko?”
Mikewa tai ta hau sama, Ummy ma ta mike tace “ke kuma sai kiyi ta zaman gulma.
Ameera tace “bari na jira Ya Sageer ya dawo muyi hira, tunda dai ni kowa ya watse ya barni.”
Ummy tai tafiyarta tana cewa “bari ma na kirashi naji naga ya dade bai dawo ba.”
Jalila tana hawa sama ta ganshi a kwance, yau ba karatu yake ba sai dai a kwance kawai yake shiru, ta shiga da salama.
A hankali ya amsa wanda ita kanta bataji ba, shiga ciki tai tana kallansa.
Yaci abinci, a ranta tace yau ba jira?amma rannan harda jin haushinsa.
Hartana neman zama a kan kujera sai ta juyo ta fito falo ta zauna, ta kunna Tv.
Shiru tai tana tunani, meke damunshi? Ko bashida lafiya ne?
Da sauri ta mike ta shiga dakin, tazo jikin gado tace ” Yaya? Bakajin dadi ne?”
Kai kawai ya girgiza mata alamar a”a idanunsa a rufe.
Tai shiru kafin ta juya, har zata fita sai kuka ta shiga toilet.
Tana rufo kofar ya mike, ya kalli kofar toilet din.
Mikewa tsaye yai ya dau makullin mota ya dau wayarsa.
Tana fitowa ya kalleta ya mika mata hijab dinta, kallansa tai tace “me?”
Gani tai yayi gaba, da kallo ta bishi tace “yau maganar ma wahala take?”
Fitowa tai dan ta fahimci ta biyoshi yake nufi.
Haka ya fita, tana kokarin fita Ameera ta fito jitai tace “Amarya sai ina?”
Harararta tai tace “inda kika aikeni, kicema Ummy zamu fita.”
Da gudu Ameera ta taho tace “ina zaku? A daren nan?”
Jalila ta in fada miki?
Tace eh ina? Ta fada tana matso da kunne Jalila tai dariya tace “inda Ameera ta aikemu.”
Tai saurin yin waje tana dariya, dan tana tsoron karta dade a tsaye tai laifi.
Yana cikin mota harya tada ta bude gefensa zata shiga yace ” shiga baya.”
Komawa tai baya ta shiga tana yan kunkune, tana rufe mota yaja suka fita.
Suna fita motar Sageer na shiga gidan.
Tafiya yake, ba mai magana a cikin motar, ita kuma haushin ce mata dayai ta shiga baya yasa batai magana ba.
Kanta ta sunkuyar, jin alamun an tsaya yasa ta dago.
Gidan Goggo? Kallan gidan tai sannan ta kalleshi cikin mamaki.
Kashe motar yai sannan ya kwantar da kansa jikin kujera.
Jalila cikin mamaki tace “gidan Goggo?”
Shiru yai har tana tunanin bazaiyi magana ba, cikin wata murya taji yace.
” Jalila?”
A tsorace tace “naam.”
Shiru ya sakeyi na wasu lokuta kafin yace ” Zan fadamiki abinda ke damuna, abinda na aikata wanda a koda yaushe dana saninsa shike hanani sukuni, a duk sanda na tuno da abin ko cikin bacci ne nakan ji kamar nima na mutu, nakanji gaba daya duniyar ta zamarmin bakinkirin, nakanji komai na cikin duniyarnan ba abinda yake birgeni, zan sanar dake a gaban gidan mahaifiyarki idan harkinga bazaki iya zama dani ba, sai ki bude kofar ki shiga gida gun mahaifiyarki, in kuma har………”
Sai yai shiru, dan bayasan yasa ransa akan abinda bazai samu ba.
Shiru ne ya kara ratsa cikin motar, ita kam Jalila tayi tsuru tsuru.
” Abdullah Taura shine mahaifina, tunda ya tafi karatu kasar Egypt suka rikeshi ya fara musu aiki a can, gaba daya mutum ne mai tsananin san aiki, hakan yasa ba ruwansa da mace balle aure.
Ganin yanda bashida niyyar yin aure yasa mahaifinsa ya masa kamun mata, wacce take “yace ta abokinsa.
Amininsa ne tare suka taso, yanada “ya”ya dayawa sai dai duk maza ne su uku ne mata.
Babbar yarinyar Uwargidan ce, su kuma biyun matarsa ta tsakiya ce ta haifesu, dan matansa uku.
Babbar tanada mijinta sai aka bashi ta tsakinyar mai suna Hauwa”u suna kiranta da Jidda.
Daga can aka sashi ya dawo, yana zuwa ya ganta ya aminta da ita akai aure a sati biyu da zuwansa dan dama sun shirya komai, anayi ya dau matarsa suka koma garin Egypt.
Bazaka taba tunanin auran hadi ne tsakaninsu ba dan suna kula da kaunar juna.
Basu dade da aureba Allah ya bata ciki.
Irin girman cikin yasa hankalin Taura ya tashi, ba shiri ya ajiye takarda akan yana bukatar hutu mai yawa suka taho.
Gidansu ya kaita dan hankalinsa da nata sai yafi kwanciya.
A lokacin da suka iso dama ana ta fama da bikin kanwarta, ganin yanda Yayarta ke shan wahala yasa sam hankalinta ya tashi, tana kuka muraran aka kaita gidan miji, haka aka gama biki lafiya ta tare, aka dukufa da mata rubutu da kula da ita, saboda cikin yasata ta kumbura sosai.
Taura a koda yaushe yana gidan, kai abin makulashe, magani da duba jikinta, har Allah ya kawo lokaci.
Satinta daya tana nakuda wanda ya kara wahalar da ita, aka dauketa aka kaita asibiti aka bata gado.
A wata ranar asabar aka yanke hukunci yi mata tiyata dan abin yaki karewa.
Kanwarta a rikice tazo asibitin dan labari ya kai mata, kuka kamar ranta zai fita, haka aka shiga da ita tiyata tana rike da hannun kanwarta.
A dakin tiyata ana zaro “ya”yan nan biyu ana kokarin yi mata dinki tace ga garinku nan.1
Tashin hankalin da suka fuskanta a asibitin nan ba”a magana.
Kowa ka gani hankalinsa a tashe yake, haka duk sanda aka kalli jariran nan biyu sai an zubar musu da hawaye.
Haka aka kaita gidanta, Taura kamar zaiyi hauka, dauriya kawai yakeyi ba magana, dan inya tuno da jariran yaran nan wadanda ko ganinta basuyi ba sai aji hankalinsa ya tashi.
Kanwarta ita ke kula dasu dan ko gidanta bata koma ba, dayake mijinta shima na gida ne, a karshen layin ma ya kama gida.
Jin ance ta koma gidanta yasa tace itakam dasu zata tafi, duk yanda akaso ta hakura amma taki, kuka ma tasa tace itakam abarta dan bazata iya barinsu ba.
Haka aka hakura ta tafi dasu, sai Taura ya hadata da kanwarsa wacce take shekara 14 suka tafi tana taimaka mata.
Gaba daya Taura ya canza, kullum sai yaje ganin yaran nan hankalinsa ke kwanciya, kowa ya gansu bazai taba cewa basuda uwa ba dan sosai take kula dasu, kowa jinjina mata yakeyi dan yarinyace sannan ko haihuwar fari batai ba.
Duk wani bukatunsu Taura ya dauke musu, sannan ya kasa komawa ma gun aikinsa.
Har yaran nan suka shiga shekara guda, suka fara tafiya, kowa ya gansu abin sha”awa.”
Hassan yai ajiyar zuciya yace “A wata rana mahaifinta da mijinta sunyi tafiya sukai hatsari wanda ya dauki rayuwarsu.1
Taga tashin hankali ga mutuwar miji ga kula da yara biyu, sannan gashi batasan tanada karamin ciki ba.
Gashi duk yanda akai yaran nan su barta taji da abinda ke damunta sunki dan su itace mahaifiyarsu ita kadai suka sani.
Ita ma ta nemi a barsu, haka ta sha wahalar wannan lokaci duk ta rame ta fige.
Taura tsananin tausayinta yasa ya umarci dauke yaran sai dai kuka tasa ta nemi a barmata wai mijinta ya tafi kar a rabata da “ya”yanta.
Haka ya bar mata su, har Allah ya kawo mata nata haihuwar ta haifi danta namiji aka sa mai Sageer.”1
Ajiyar zuciya yai yace “Kin fahimci labari na kashe na farko?”
Jalila wacce idanunta ke zubar da hawaye tace “Kune yaran kanana, sannan wacce ta rikeku wato kanwar mahaifiyarku Ummy ce???”1
Hassan yace “eh, Ummy ce.”1
Haka muka taso mu uku, sai dai nu biyu mun girmi Sageer da shekara biyu, dangin mahaifinsa suka daukeshi saboda takaicin yanda take kula damu.
Haka muna kuka aka tafi dashi, bayan mun dawo gidan mahaifanta ne aka yanke shawarar hada auransu.
Da harta ki amincewa sai dai ganin za”a kwacemu yasa ta amince.
Tunda take bata taba nuna tanasan akawo mata danta ba, duk kuwa da kowa yasan zuciyar uwa.
Haka Abba ya daukemu muka koma Egypt, zamansu zama ne na kara bawai na aurataya ba, har a hankali suka fahimci mahimmancin junansu.
Shekararmu takwas a garin muka dawo nigera, na taso da tsananin kaunar Ummy wanda ko hawaye ko damuwa naga tanayi sai na yi tayin kuka, ganin yanda take zama tai shiru wani sa”in tana kallan hoton Sageer yasa nai ta kuka nace a dawo Nigeria adauko mana shi.
Tundaga lokacin Ummy ta ajiye hoton ta daina daukowa, shima Abba ganin haka yasa ya ajiye aikinsa muka dawo.
Husain nada magana sannan akwai saukin kai, muna tsananin san Ummy sai dai shakuwar dake tsakanina da ita daban ce.
Muna dawowa nace Abba na yaje ya dauko Sageer.
Haka mukaje suka hanamu, gashi a kauye suke sun tubure akan dansu bazaiyi agola ba.
Sai da Abba ya daukeni mukai zuwa kauyen nan sau kusan goma kafin su amince.5
Haka suka bamu shi muka kawoma Ummy shi, tayi kuka sosai dan bata taba tunanin za”a bata shi ba.
A kuma lokacin ta dauki alkawarin bazata taba banbantamu da Sageer ba.”
Cikin tsananin mamaki Jalila ke jin wannan labarin, to meyasa Uncle yace bazai ko dan abinda su Hassan suka mai bazai iya musu butulci ba? Saboda daukoshi da sukai?
Hassan yai shiru kafin ya dan runtse idanunsa, wani abu na ratsashi………
Wata irin muguwar shakuwa ce tsakanina da Ummy wanda ko mahaifina banajin kaunarsa haka a raina, ita kanta ko yaya naji ciwo kafin nace da zafi fuskarta ce zata nuna tanajin zafin abin, hakan yasa ko banida lafiya banfiya nuna mata ba, Husain nada kawaici sannan baifiya makon uwa kamar ni ba, da farko bamu taba sanin ba Ummy bace ta haifemu saboda yanda muke, har saida muka dawo daga Cairo, mu kawai mun dauka kanin mu Sageer ne kawai babansa daban.
Sageer shikansa baisani ba shi sai da yaje ziyara gun dangin mahaifinsa, sai dai koda wasa bai taba nuna mata ma ya sani ba, duk wani tunani da zakiyi akan yanda Uwa zataso danta Ummy na mana wannan san, Aunty Nana itace yayarsu Ummy amma mahaifiyarta daban, halayenta ba irin na Ummy bane sai dai itama ko da wasa bata nuna mudin ba “ya”yan Ummy bane, har yau babu wanda na taba ji yace mu ba “ya”yanta bane sai wanda ya sani tun fil”azal.
Yai shiru sautin numfashinsa ya canza kafin yace “haka rayuwarmu ta taso cikin farinciki da kaunar juna har zuwa shekara 13, a lokacin mu muna shekara sha uku shi kuma Sageer na shekara 11, wannan lokacin ma aka kara samun matsala dan “yan Uwan mahaifinsa daga zuwansa hutu suka rikeshi wai sun kula Ummy ba ta kawoshi duk hutu da alama so take ta daukeshi.
Hankalinmu ya tashi dan ni da Husain har zazzabi mukai, sai dai ganin Ummy ta watsar da komai yasa muka ware muma.
A wata rana wacce ta zamarmin ranar bakinciki a tarihin rayuwata, a lokacin kanin Abba yazo shida matarsa da “ya”yansa sunzo gida tayamu murna na suna dan Allah ya albarkaci Ummy da samun “ya mace ya wato Ameera.1
Dukansu mata ne sai Sudais kadai wanda yake namiji sannan shine karami dan shekararshi shida a lokacin, yan uwa da dama sunzo tayamu murna.
Da yake ni duk inda taro yai yawa ba sanshi nake ba hakan yasa na fito daga cikin gida.
Har nayi waje Husain ya kwallamin kira na juyo, yace “ina zaka?”
Dayake akwai shaguna a karshen layin mu nace shago zani, yace “bari inzo muje.”
Nan ya taho da sauri, muna fita kofar gida mukaga Sudais, nace “Sudais daga ina?”
Yace “alawa na siyo.”
Ya nuna mana alawar hannunsa, Husain ya amshi daya ya bude muka taho mu uku, muna tafe munata hira wanda ni kaina a yanzu na manta hira me mukeyi.
Har mukaje karshen layin, hango wasu maza mukai a kan titi suna kan doki gashi mutane sai kallansu akeyi, abinka da yarinta kawai sai muka kutsa ciki kuna kallo.
Daga tsallaken titi na hango wata mota kamar ta Abba, nace “Husain kaga motar Abba.” Ni a guna nasan ba motar bace zolayarsa nakeyi, shikuma yana gani ya yarda yace “ai kuwa muje.”
Nace ka bari su gama wucewa.
Nan muka tsaya har suka wuce nace to mu tsallaka, Sudais sai tsalle yake wai ya hango Abba, wanda ni a guna mugunta na shirya inata dariyar yarinta.
Kamar zamu tsallaka titin, harna fara tafiya dasu na dawo baya ina dariya, ina cewa ba Abba bane ziraku nayi.
Husain na rike da hannun Sudais ya juyo shima yana dariya yace “amma lalai Hassan, wallahi ni harna yarda
Shikuma Sudais, duk ya damu a karasa karshen titi, Husain ya kamo hannunsa suka juyo da shirin dawowa.
Gaba daya bamuyi auni ba ina kallansa shima yana kallona muna dariya sai gani nai anyi gaba da……….3
Numfashinsa ne ya sarke, wasu zafaffan hawaye ne suke zubomai, karar faduwarsu kawai mukaji.
Sam bamu kula da tahowar mota ba, mutanene suka taho gun a rikice, jini……. jini…….
Numfashinsa ne ya shiga fita da sauri da sauri. Kansa na wani irin sarawa, yace ” Tsoro da fargabar abinda na gani na fara ja da baya da baya, ina kallan jinin da ke zuba daga kansu.
Inaji mai motar na tambayar waye ya sansu amma bakina ya kasa magana saboda numfashina da yake hawa da sauka, kaina na wani irin juyawa saboda jinin dake kwaranya…….
Kansa ya matse da karfi wanda ke mai wani irin azaba, Jalila kam hawaye duk ya gama jika mata fuska.
Matsowa tai tasa hannunta akan kafadarsa tace “Yaya?”2
Hannunta ya dan ture tunda ya fara labarin sai yanzu ya juyo ya kalleta fuskarsa gaba daya ta canza, bata taba ganin Hassan haka ba, yace “Nine sanadiyar rasa rayukansu, wanda haryau kanin Abba Allah bai kara bashi haihuwa ba, wanda ranar sunan Ameera ya zama ranar rasuwar yayana, wanda nai sanadiyar mutuwar daya daga cikin farin ciki Ummy, farincikin mahaifina sannan farinciki na, bancigaba da makaranta ba saboda na dade a asibiti a kwance, sai dana samu sauki ne Abba ya kawo wani gida yana koyamin, a haka da kyar Ummy ta sani nai exam din waec daga nan ban cigaba da komai ba.
Nine sanadi, Taya zan samu farinciki a rayuwata? Taya zanyi murmushi a rayuwata, tunda abin nan ya faru har yau basusan nine sanadi ba, sai dai kowa tausayamun yake akan rashin dan uwa nane yasa ni canzawa haka? Na lalata farincikin kowa na lalata…….:”
Kansa ya kifa akan sityarin mota yanajin wani abu na ratsashi.
Ya dade a haka kafin yace ” ki shiga gun mahaifiyarki, bancancanci samunki ba, bancancanci samun farinciki ba.”
Shiru tai tana kallansa sai hawaye dake zubo mata wanda kamar korosu akeyi, hannu tasa ta bude kofar motar ta fita.
Idanunsa ya runtse da karfi yasan za”ai hakab sai dai zuciyarshi ce ta sake zafi dayaji ta fita, hakan shine daidai shikuma yanzu rayuwarsa sai tafi tada dan ta riga ta shiga rayuwarsa wanda yanzu ya tabbatar cireta babbar gibe ne a gareshi.
Jiyai ta sake bude motar, dagowa yai ya hade rai sannan ya kalleta.
Yanzu kam gaban mota ta bude gefensa ta bude, kallanta yai sai dai baice komai ba, Jalila ta shiga ta zauna sannan ta rufe motar, kallansa itama tai sannan tace ” Inyi magana?”
Kallansa yai kallan mamaki, tace “ka fadi duk abinda ke ranka ni baka barni na fadi nawa ba.”
Yace “kamar ya kenan?”
Shiru tai kafin tace ” yaya kana tunanin dan Uwanka abinda yakeso kenan?”
Kallan tambaya ya mata, tace “yanzu in yasan saboda shi ka maida rayuwarka haka kana tunani zaiyi alfahari da hakan?”
Idanu ya kura mata, tace “yaya kana yaro lokacin sannan ba da saninka bane…….”
Da sauri ya juya kai ya bude kofa yana neman fita, da sauri tasa hannu ta riko hannunsa.
Juyowa yai ya kalleta tace “inhar kanasan in tafi zan tafi, sai dai inhar akan dalilan nan ne hujjajun basu karbu ba.”
Kallanta yakeyi, murmushi tamai tace “wace irinn rayuwa kai zuciyarka na dauke da abubuwan nan?…..”
Batai auni ba ya jawo hannunta ta fada jikinsa, kankameta yai tsam, yanajin wani abu na ratsashi, duk da gabanta dake faduwa a hankali tace ” meyasa kake tunanin su Ummy zasu ga laifinka akan abinda ya faru?”
Idanunsa ya lumshe kawai, bayansa tadan shafa alamar lalashi tace “Yaya kaine abin tausayi ba su Husain ba, su kansu na tabbatar da zasusan abinda ka aikatawa kanka bazasuji dadi ba.”
A hankali ya dagota daga jikinsa kallanta yai, ita kanta kallansa takeyi, sai dai ganin kallan da yake mata yasa ta saukar da idanunta kasa, ya rike fuskarta da hannayensa yace “Jalila kinfi kowa sanin halina, inada dizgi? Shariya? Rashin san magana? Rashin iya magana? Rashin iya hulda da mutane? Kin tabbatar zaki iya zama zama dani?”
Shiru tai tana kallansa, sai dai a wannan lokacin ta tabbatar bazata iya bijire masa ba, batada tabbas akan ko tana sanshi sai dai bazata iya musa mai ba, kai ta daga a hankali.
Kansa ya sunkuyo a hankali saitin bakinta, yakai labbansa kan nata.
Labanta ya tsotsa kadan sannan ya dago ya kalleta yace ” banasan na zama nine sanadiyar ruguzamiki rayuwa.”
Idanunta ta lumshe dan wani abu taji yana ratsata, a hankali ya kara kai bakinsa cikin nata, wani salo yake mata wanda yasa taji gaba daya kanta na juyawa, wani abu na ratsata har cikin kanta.
Trauma is defined by the American Psychological Association (APA) as the emotional response someone has to an extremely negative event. While trauma is a normal reaction to a horrible event, the effects can be so severe that they interfere with an individual”s ability to live a normal life. In a case such as this, help may be needed to treat the stress and dysfunction caused by the traumatic event and to restore the individual to a state of emotional well-being.+
Some common sources of trauma include:
Rape
Domestic violence
Natural disasters
Severe illness or injury
The death of a loved one
Witnessing an act of violence e.t.c.
Idan muka duba abinda ke rubuce a sama, zai bamu damar cikaken fahimtar matsalar Hassan, Trauma na ganin mutuwar kaninsa da yake tsananin so sannan da Guilty na laifin da yake tunanin shine sanadiyar yin hakan, kafin na fara rubuta matsalolin Hassan sai danai bincike akan matsalar cutar Trauma wanda ke damunsa, na dauko bayanin sama ne saboda mu fahimci matsalarsa musan me ake nufi da wannan kalma ta Trauma, akwai mutane dayawa dake dauke da wannan matsalar sai dai bama damuwa da abinda ke damunsh saboda rashin sanin matsalarsu, wasu cikin bacci zakaga suna razana, wasu kansu ke daukar zafi, wasu duk sanda sukaga jini, duk wadannan na faruwa ne a yayin da sukai karo da wani mumunan abu wanda ya taba ayuwarsu yakan hanasu yin rayuwa yanda ya kamata.
Allah ya mana mai kyau ameen…..15
*54*
A hankali ya dago ya kalleta, itama ta bude idanunta.
Kallansa tai sannan tai saurin saukar da idanunta kasa, ta zame daga jikinsa ta koma ta zauna akan kujera, karamin gyaran murya yai na burin kunya yace ” zaki shiga ku gaisa da Goggo?”3
Bata kalleshi ba tace “a”a.”
Tada mota yai sukai gaba, shiru ne ya ratsa motar ba wanda ya sake magana.2
Sunyi tafiya sosai, kafin ta daure tace ” Yaushe kuma Ya Sageer din ya dawo?”
Yace “Sageer? Bayan abin ya faru ne hankalin su Abba ya tashi shine suka nemi alfarma akan a dawo dashi, ko hankalina dana Ummy zai kwanta, dakyar dai suka amince.”
Ta dan kalleshi tace ” Yaya na kasa fahimtar abu daya, me yasa kafi damuwa da Ummy kadai? Dan na kula yanda ka damu da Ummy baka damu da Abba ba.”
Kallanta yai sannan yace “haka kike gani?”
Tace “bani kadai ba hakan ne ma.”
Shiru yai har kamar bazaiyi magana ba sai yace ” Abba a koda yaushe in na ganshi nakanji tsananin tausayinsa, nine sillar rasa dansa da kuma dan kaninsa sai dai yanda yake nunamin so shine ke damuna, i have to be cold to him saboda ya rage damuwa dani, dan ban cancanci kaunar da yakemin ba, inasan ya rage san da yakemin ne saboda ko daga baya inyasan abinda ya faru bazai dameshi ba.”
Jalila ta kalleshi kawai sai jitai tayi dariya, kallan mamaki ya mata yace “dariyar menene?”
Tace “yaya, wallahi rashin sakarma mutane fuska da zama cikin mutane yasa gaba daya tunaninka daban ne, kana tunanin wai abinda kakemai na zafi zafi shine sai sa ya rage sanka? Ko ya rage damuwa dakai?”-
Hassan ya kalleta cikin mamaki, tace “ashe ma gwara ni.”
Fuska ya hade yace “gwara ke me?”
Tace shikenan.
Shiru yai baice komai ba ta kara cewa “tab lalai yau naji abinda ban taba ji ba.”
Harararta ta yai yace “zaki cigaba ko?”
Ta rufe bakinta tace “bance komai ba.”
Haka suka isa gida, suna isa suka shiga ciki, Abba na kallansu ta glass din falonsa, murmushi yai na jin dadi tare da godiya ga Allah.
Suna shiga daki ta shiga toilet tai wanka saboda fashin sallah da takeyi, sannan ta fito ta dau bargo zata shimfida, kallanta yai yana zaune akan gadon yace “ki dawo nan ki kwanta yau ma a kasa zan kwana.”
Tace ” a”a ka kwanta.”
Kallanta yai tace “in na kwana yau gobe ma anan zan kwana.”
Yace “sanda na matsu da gadon sai na tureki na kwanta.”
Tadan hade rai kadan tace “bari na dau hijabina na tafi gidan Goggo kafin ma a tureni inji ciwo.”
Murmushi yai yace ” wannan dai neman magana kike, matar dana kaiki har kofar gidan kikace bazaki iya rabuwa dani ba?”1
Baki ta bude cikin mamaki tace “a yaushe akai hakan?”
Yace “musawa zakiyi kenan?”1
Ta matso kan gadon wai ita a dole an ba ta mata rai ta kwanta tare da juya baya tace ” wallahi na kula duk abinda banceba sai acemin nace.”
Kallan bayanta yai ya tuno abinda ya faru a mota, kallanta yai yace “to ko mu sanar da Goggo laifin da mukai?”
Juyowa tai ta kalleshi tace “laifin me?”
Yace “na fitsarar da mukai……”2
Da sauri ta mike tasa hannu ta toshemai baki tace “yayah.”
Kallanta yai sannan ya zare mata hannun data rufemai baki yace “yanzu yanda kika hau kaina me kike nufi?”
Da sauri taja baya tace “wai ni yaya…..”
Yace “wai a yaushe na zama yayanki ne?”
Baki ta turo tace “to ni me kakeso nacema?”
Yace “oho amma ni bansan yayan nan.”
Tace ” to naji ka daina tsokanata.”6
Fuska ya hade yace “a yaushe na tsokaneki? Bakiyi rashin kunyar bane? Ko yanzu baki hau kaina ba?”
Tace “kaine fa ka jawoni kamin kiss sannan yanzu bafa kanka na hau ba.”
Kansa ya juyar gefe yace “ni? Kin tabbatar bake kika fara ba?”
Ta saki baki tace “yaya tanan ka bulo? Su biyu fa kenan kana min haka.”
Murmushi ya sake yi.
Da sauri tace “yaya kayi murmushi wlh.”
Shiru yai yana kallanta sai dai yanayin fuskarsa ya canza yace “Jalila!”
Gyara zama tai a hankali tace “naam.”
Yace “nagode.”
Kallansa tai cikin mamaki, yace “zan sanar ma Abba komai, ko tsanata zaiyi ko hukuntani zaiyi zan dau komai, nagode da kika budemin zuciyata kika nunamin rayuwar daya kamata nai.”
Kallan rashin fahimta tamai tace “ni?”
Yace “kin tabbatar zaki jure ganina a kasa?”
Tace “kamar ya?”
Yace “duk girman gadon nan sai na sauka?”
Tace “tare zamu kwana?”
Yace “ba haka kikeso ba dama?”
Tace “yaushe nace?”
Yai ajiyar zuciya yace “yanzu abinda na gani kenan kin fada a fuskarku.”3
Tai tagumi tace “oh ni.”
Kwanciya yai ya dau littafinsa yace “ba abinda zan miki in ma shi kike tunani, tunda dai har kikai fitsara a gidan goggo ai kwana tare ba zai zama issue ba.”5
Jalila tai dariya tace “wallahi yaya na fahimci kawai so kake kai ta zolaya ta.”
Bai amsa mata ba ya fara karatu, kwanciya tai daga can karshe tace “wai yaya mai kake karantawa haka kullum?”
Yace “kawai karantawa nake nai ta tisawa ina san dauke tunani daga raina.”
Shiru tai tana kallansa, yace “inkingama kallan nawa sai kiyi bacci.”
Da sauri ta rufe idanunta a haka har bacci ya dauketa.1
Bargo ya ware ya luluba mata sannan ya kura mata ido yana kallo, Jalila! Jalila! Nagode da amincewa da kikai dani.
Murmushi ne ya sake bayyana a fuskarsa, sannan yai shiru yana tunanin Abba da Ummy dasu Sageer, gobe zai sanar dasu komai ya kuma nemi yafiyarsu, kome zasumai gani yake zai dauka tunda tana tare dashi.
Sai can ya kwanta yai bacci, bacci mai dadi yai wanda shikansa bai sani ba,bai farka ba sai biyar saura, wanda raban dayai irin baccin nan ya dade, addu”oi yai tayi da neman yafiya har gari yai haske kafin ya dawo ya kwanta, yaso tashinta tayi karatu amma yabarya saboda ganin yanda take bacci.
*********
Wajen karfe 9 suna aiki da Ummy a kitchen akai sallama, Sageer dake kallo a falo ya bude kofar, mamaki ne ya kamashi ganin Inna da Mumy.
Inna tace “Taura harya fita?”
Ya daure ya gaisheta kafin yace “yana nan.”
Tace “ko zaka sanar dashi?”
Muryar Ummy yaji tace “Sageer wanene?”
Sageer yace ” Matar gidansu baban Jalila ce.”
Ummy tace “matar me?”
Yana kallansu yace “kishiyar Goggo.”4
Ummy tace oh Sageer akwai tsiya, kallan Jalila tai wacce tai tsuru tsuru, Ummy ta dafata tace “kin manta a inda kike ne?”
Kallan Ummy tai sannan tai murmushi tare da girgiza kai.
Ummy tace “shigo dasu mana.” Sannan ta wanke hannu ta fito, a falo suka zauna.
Ummy ta karaso suka gaisa duk jikinsu a sanyaye.
Inna ta daure tace “Hajiya dan Allah a mana magana da Taura.”
Ummy ta kalli Sageer tace “Sageer kira Abbanka.”
Mikewa yai ya nufi falonsa.
Aiki yakeyi sanda ya shiga nan ya sanar dashi, Abba yace yana zuwa.
Jalila kam aikinta ta cigaba, tanaji harsanda Abba ya shigo.
Inna ta gaidashi kamar irin itace karama, Mumy ma ta gaisheshi.
Zama yai yace “lafiya? Da safen nan?”
Inna ta murmusa tace “dama munzo ne muyi bayani.”
Yace “bayani?”
Tace “munsan kunsan komai akan abinda muka aikata.”
Yace “sai akai yaya?”
Tace “laifinane, sai dai ina baka hakuri, muci darajar marigayi karka kwace kudinka.”
Abba ya kalleta kamar zaiyi magana sai yace “Sageer yima yayanka magana.”
Inna najin haka gabanta ya fadi, ita kanta Mumy hankalinta ya tashi tace “ai ba sai yazo ba, hakuri mukazo badawa.”8
Abba yace “na sani kuma na fahimta, matarsa ce wacce kuka wahalar kuka nemi tozartawa, hakkinsane ya yafe muku ko yaki, sannan ita yarinyar ita zaku ba hakuri ba ni ba, idan har yarinyar da mijinta sun yafe muku banaji ni inada matsala.”
A ran Inna tace nasan Jalila batada matsala, babbar matsalar yaran nan……
***********
Kallansa tai tace “me kake nufi RAM?
Yace “haba Safeena ke sai yaushe ne zaki bar gidadanci? Baki kula duk mutane ba wanda yakesan harka dake ba saboda kauyancin da kike nunawa?”4
Shiru tai tana kallansa kafin tace “To ya kakeso nayi wai?”
Yace “ki tashi dalla ki canza wannan shirmen na jikinki kisa wando da riga ki bar ragowar a hannuna, ni zan maidake fitaciya a skul din nan.”9
Kallansa tai cikin gamsuwa sannan ta kike……..