JALILA CHAPTER 2
Da kyar ya tura abincin sannan ya mike ya shiga bandaki, wanka yai tare da dauro alwala. Jalabiya ya zura ya tada sallah, ya dade sosai akan sallayar yana mika rokonsa gurin Allah sannan ya kwanta a kasa, a takure ya kwanta , sam baisan sanda bacci yai gaba dashi ba. Ummy ce ta leko ta ganshi yana bacci, kusa dashi taje ta zauna tana kallansa cikin tsantsar so da kulawa da kuma tausayi, jan numfashi tai sannan ta mike ta dau tiren abincin da yaci tai waje. Gab da magrib yana bacci yaji kamar ana shakemai wuya, wani irin mumunan mafarki yakeyi wanda ya shiga sandarewa yana kankake jikinsa, idanunsa a runtse sai wani irin zufa da yake kwaranya daga jikinsa, numfashinsa ne ya shiga hawa da sauka, shure shure ya shiga yi saboda tsananin azabar da yake fuskanta. Har zai shiga dakinsa yaji alamar motsin Hassan, da sauri Sagir ya tura kofar, ganin Hassan a kankame yasa yai saurin shiga dakin, tabashi yai yana cewa Hassan! Yaya! A firgice ya bude idanunsa tare da jan wani irin numfashi, Sagir ya dagashi zaune yace “in kawo ma ruwa?” Hassan ya daga kai, da sauri ya mike ya dauko mai ruwa, amsa yai ya lafa bakinsa, sai dayasha sosai sannan ya kalli Sagir ya mikamai jarkar. Sagir ya amsa sannan yace “akwai abinda kake bukata?” Kai ya girgiza alamar a’a. Cikin tausayawa Sagir ya kalleshi sannan ya mike yace “Yaya kazo dan Allah ko waje ka fita kaji iskar duniya.” Bai kalleshi ba haka kuma bashi da niyyar amsamai, Sagir ganin haka yasa ya fita tare da ja mai kofar. Sagir yabi bayan kofar da kallo sannan yace “Allah ya yaye maka ya baka lafiya.” Dakinsa Sagir ya shiga kallan kayan da ya cire dazu yai sannan yai murmushi ko a ya ta koma gida? Cikin nuna halin damuwa yace ” ba ta dai jike ba ko?” Kai ya girgiza yace ” ya za’ai ta jike ga lemar da ya bata sannan ya tabbatar tace ai zuwa za’ai a daukesu.” Murmushi yai sannan ya dau wayarsa dayazo dayka ya sauka kasa. ************** Jalila ce zaune tanacin abincin dare ita da Goggo, tunanin abinda ya faru dazu takeyi. Jitai Goggo ta tabata tace ” Jalila wani abun ya faru ne dazu?” Jalila ta kalleta tace “Bakomai kawai dai ni akwai abinda na dade ina san tambayarki ne Goggo.” Goggo ta kalleta tana neman karin bayani, Jalila tace ” Bawai da wani abin bafa nake san ji Goggo, kawai dai tambaya ce.” Goggo tace “Ina jinki.” Jalila tace ” Ni Goggo baki da kowa ne sai Dady?” Murmushi tai tace”Ban gane banida kowa ba sai shi? Kin tabaganin wanda bashida kowa a duniya?” Jalila tace ” To ni Goggo na kasa fahimtarki ne sam, na rasa takamaimai ke mukeyi a cikin gidan nan.” Goggo ta tsame hannunta sannan tace ” Lalai Jalila, muhallin Mahaifin naki kike fadama haka?” “Muhalli? Ai kowa yasan gidan Mumy ne ba nashi ba, sannan ni waye ma yasan ni ‘yarsa ce, ko suna a makaranta ni ansa nayi amfani da Auwal wato kakan Dady, dan kawai karma asan ni yar sace.” Goggo tace” ya isa to, ke dai ba ruwanki da wannan, mahaifinki da mahaifinki ne, sannan banaji yana da laifi a harkar nan, laifin na iyayenmu ne.” Jalila tace “Goggo dama tun can baya sanki” Harararta tai tace”Wai yau me kikesan ji ne haka?” Tace”ni dan Allah ki fadamin tarihinki Goggo.”1 Hannunta ta wanke a robar ruwan da Jalila ta kawo ta dan matsa kadan tace ” sai randa hankali yazo miki.” Jalila ta dan turo baki tace “ni yau meyasa ake tacemin banda hankali?” Goggo tace ” Ce miki akai mara hankali a cikin gida?” Tace “Safeena ce.” Goggo tace “Fada kukai kenan?” Jalila ta hade rai tace ” ni ai…..” Goggo tace “sai yaushe ne zaki dinga hakuri Jalila? Na dauka na rokeki akan kai zuciya nesa?” Jalila ta kalleta tace “Yanzu duk hakurin da nakeyi bakya gani? Wlh a yanda nake ji da wata rana sai na fasama ‘yar nan baki, kawai hakuri nake sawa a zuciyata.” Goggo tausayinta ya kamata tace”kiyi hakuri, duk tsanani yana tare da sauki, shiyasa a koda yaushe nake miki fatan miji na gari, wanda ke sanki ina tunanin hakan ne kadai zai kawo salama a zuciyata da taki.” Jalila tace “ni duk wanda zan aura sai dai in zai iya rikemin ke, dan bazan iya aure na barki ba.” Dariya Goggo tai tace “Lalai yarinta na damunki Jalila.” Haka sukai ta hira har suka kwanta…………. ********* Washegari……… Yau tana gama aiki ta shirya ta fito dan jiransu, dadi takeji yau ta rigasu shiryawa, yanda taga Dady ya fito da sauri ko gaisuwarta bai tsaya amsawa ba tasan lalai da matsala, mota taga ya shiga da sauri, sai ga Mumy ta taho da gudu tare da shiga gefensa itama, nan taga sun fita a guje. Baki ta tabe tace “ko ina zasu haka oho” Su Safeena ne suka fito,Yasmeen na ganinta ta isa gunta da gudu tana nuna mata sabon school bag din da Dadynta ya siyo mata. Jalila tace “inyee lalai tayi kyau.” Tafada tana kallan wata yagwalgwalaliyar jakar dake bayanta. Mota suka shiga, Safeena ta kalli Sultan tace “Sultan kamar akwai matsala a company dinsu Dady ko?” Sultan ya kalleta yace” ina na sani, in so kike kiji me yasa baki tambayeshi ba da zai fita?” Haushi ne ya kamata tace ” Wai kai meyasa mutum bai isa yai maganar mutunci dakai ba?” Tsaki tai sannan ta maida kanta kan Jalila cikin masifa tace “ke kuma uban me kike kallo?” Jalila tace “Ba ni na kar zomon ba Hajiya.” Safeena ta kara kuluwa, da saninta tasa kafa ta tako kafar Jalila, Jalila ta kalleta. Safeena tace ” sry fa ban kula ba.” Jalila ta kalli safarta wacce ta baci sannan ta kalli Safeena tace ” mantawa nai ashe idanunki basa aiki.” Ran Safeena ne ya baci tace “mene?” Jalila ta kalli window ganin sun kusa isa, me zata gani? Uncle Sagir ta gani yana parking din mashin dinsa, ga mamakinta murmushi ne ya bayyana a fuskarta, Safeena ce ta kalli inda take kallo nan idanunta suka sauka kan Sagir. Idanu ta kuramai, waye wannan? Batasan a fili ta fada ba, Jalila ta kalleta tace “Uncle dinmu ne na Math.” Safeena ta kara kallanshi sannan tace “Driver tsaya anan mana ta sauka.” Jalila ta kalleta ta tabe baki sannan ta sauka. Muryarta yaji tace “Good Morning Uncle.” Juyowa yai ya kalleta, yanayin fuskarsa kadai zaka kalla kasan ganinta ya sashi farinciki. Jalila ta dan matsa gunsa kadan tace “Sir nayi laifi.” Bai ce komai ba sai wani kallo da yake mata, gana kokarin b’oye abinda ke ransa, dan bai manta ita din dalibarsa bace. Ta fara wasa da hannunta sannan tace “Lemarka jiya ta samu matsala.” Yace “ta samu matsala ko dai ba’a damu da ita ba an lalatata?” Da sauri tace ” ba haka bane, Allah iska ce ta dinga bankareta…..” Yanayin fuskarsa ne ya canza zuwa kulawa, yace “ba dai abinda ya sameki ko? Are u okay?” Ganin yanda ya damu da ita yasa taji ta kasa cewa komai, yanda take kallansa ne yai saurin juyawa ya kalli daliban dake ta shiga makarantar yace ” Ki wuce cikin makaranta.”maganar ya karasa tare da juyawa yana kallan mashin din. Jalila ta fara tafiya a hankali tana mamakin kulawar da yake nuna mata wanda ke kokarin sa zargin so a zuciyarta, anya kuwa? Karfa zuciyarta ta raya mata abinda ba haka ba, Uncle Sagir yafi karfinta, dan mata dayawa na sanshi, sannan da alama dan gidan wani ne duba da yanayin yanda yake zuwa wani sa’in a mota. Wata zuciyarce ta ce mata ina ruwan so da wannan? Juyowa tai bayan tayi tafiya mai nisa, ga mamakinta gani tai idanunsa na kanta, suna hada ido yai saurin juyawa, Jalila ta juya cikin yanayin jin kunya. 1 ********** A company dinsu Dady kuwa suna isa sukaga mutane ancika a waje. Da sauri sukai parking Dady ya fito cikin tashin hankali, suna ganinshi sukayo kanshi. Mumy na gefensa, cikin tsantsar tashin hankali yace ” gaba daya kayanda muka adana sun lalace?” Cikin damuwa yace ” Muje ka gani.” Store din da suke adana dukan kayan aikin da sukeyi ya bude. Store din acike yake da kayan ma’a dana na abinci. Gaba daya hankalin Dady ya tashi dan kana gani kasan lalai lalata musu akai. Juyowa yai yace ” How can this happen? How…….” Mumy ma hankalinta ya tashi ta kalli Dady tace “Yanzu ya zamuyi? Gashi zuwanka Abuja munyi signing da Al-Company zamu aika musu da kayan cikin satin nan.” Wata zuface ta karyomai yace “Muje gida mu sanar ma Inna, sai muyi tunanin mafita, dolene mu san yanda zamuyi kafin nexweek.”1 Hankali a tashe suka juya gida. Inna macece wacce tasan kan kasuwanci, dan company dinsu ya bunkasa ne harda tsananin iya kasuwancin ta, shiyasa mijinta yake girmama kalamanta sannan takeji da kanta itama. Har Allah ya mai rasuwa, ta dade tana juya company din da kanta duk kuwa da ganin Dadyna iya nasa kokarin a karkashinta,har sai dataga girma ya kamata tana bukatar Hutu sannan tabar Dady yakejan ragama. Inna wacce yanzu ne ta maida sunanta haka, dan da kowa Hajiya yake kiranta, yanzun ma Sultan ne ya sa mata hakan har kowa ya koma kiranta haka a gidan, amma daga ta fita sai dai kaji ana Hajiya. Tai shiru kafin tace “nawa ne a account dinmu?” Yace “Hajiya mun kwashe rabin kudin mun sai kayan aiki, ba nakawo miki budget din ba?” Hannu tasa ta shafi fuskarta tace “Kudin bazasu kai musai wasu kayan ba kenan?” Kasa yai dakai yace “Gaba dayan mun gama shirya plan dinmu banaji ko kwata zai kai.” Ta dade batace komai ba da alama nazari take kafin tace “Sai dai kenan mubi last option din da banaso.” Yace “Loan?” Tace ” dole zan duba a cikin mutanen Alhaji da nawa wanene na amana sai musan yanda zamuyi, either mu samu loan ko kuma yayi investing.” Kai ya jinjina sannan yace “bari a kira board meeting sai a tattauna.” Tace “No ka bari sai zuwa gobe in na samu wanda zai tallafa mana.” Yace ” To Hajiya.” Nan ya mike ya fita, wani karamin diary ta d’auko ta shiga duba sunaye tana auna mutane……. Yau a staff room yai shiru yana tunanin yanda zaiyi, ya dade yana tunani dan baisan ma sanda wani staff yazo kusa dashi ba yace “Sagir mu mun wuce sai gobe in Allah ya kaimu.” Kallanshi yai cikin mamaki sannan ya kalli agoggon dake jikin bango, lalai har an tashi da kusan minti goma ma. Yace “To Sai goben.” Nan ya shiga hada kayansa shima, a tsaye ya ganta a inda ta saba tsayuwa, ya dade yana kallanta sannan ya karasa kusa da ita yace “Malamar jira.” Kallansa tai sannan ta sunkuyar da kanta tana murmushi dama yanzu take tunanin bata ga fitarsa ba. Jitai yace mata “D’an zo.”ya fada tare da fara tafiya, cikin mamaki take binsa har suka shiga wani class. Zama yai a saman desk sannan ya mata alama data zauna daga kujerar dake gefensa kadan. Bata musa ba ta zauna, sai daya d’an yi shiru na wasu dakiku kafin taji yace ” Jalila!”+ Yanda ya kira sunanta ne yasa taji wani abu yar wanda ya hanata amsawa sai kallansa datai, yana kallanta yace ” labari zan baki.” Nan ma batace komai ba sai kallansa data sake yi, murmushi yai sannan yace “akwai wani sokon abokina da ya taba ganin wata yarinya tun last year, ya taho shida kanwarsa zasuje gidan yayar mahaifiyarsu, sun tafe sai kanwar tasa tace “Yaya dan Allah mu tsaya musai maganin ciwon kai, tun dazu nake kai na kemin ciwo. Parking yai da saurin ganin chemist a tsallaken titi sannan ya fita. An miko mishi magani kenan zai amsa ta shigo da sauri, kallo d’aya zaka mata kasan hankalinta a tashe yake, tana zuwa tace ” Dan Allah maganin ciwon kafa.” Nurse din ne ya kalleta yace ” Ciwon kafa wani iri?” Tace ” ban sani ba kawai kafar Goggo ce ta kumbura.” Tana hawaye take mai bayani. Wanda yazo siyar maganin ciwon kai sai duk tausayin yarinyar nan ya kamashi, zuciyarshi yaji ta shiga cikin matsananciyar damuwa na ganin yanda yarinyar nan take hawaye. Yace “Ku kaita asibiti mana.” Bata ko kalleshi ba tace ” Dan Allah nikam ka bani maganin da zai taimaka mata, banida kudi yanzu sai dari biyu, inya fi haka zan kawoma ko gobe ne.” Tsananin tausayinta ya kara shigarsa kallan Nurse din yai sannan yamai alama daya hada mata maganin nan masu kyau, bayan ya bata ta mai godiya ta fita. Kallan Uncle take idanunta sun ciciko da hawaye, ba shakka daga baya tayi ta mamakin arhar maganin kenan Uncle siya mata yai? Dan ko bai fada ba tasan da kanshi yake, tunda dai na farko itace yarinyar, to in har abokinsa ne yaza’ai yabashi labari haka dala dala? Sagir yace ” tundaga wannan rana Abokin nan nawa ya shiga wani yanayi akan yarinyar nan, jefi jefi yanabi ta layin nan ko zai ganta, sai dai cikin rashin sa’a bai sake ganinta ba har sai da akai assigning dinsa zuwa inda zaiyi bautar kasar sa, duk yanda yaso ya daure akan san yarinyar nan da damuwa da ita ya kasa, shine nake so ki ban shawara me abokin nan nawa ya kamata yai? Yana tsoron kar ya bari ya huce…..” Wata irin kunyarsa ce ta kamata, kanta na kasa tana wasa da hannunta tana murmushi. Yace “Jalila, bakice komai ba? Ko ba kya ganin yarinyar nan zata soshi?” D’agowa tai cikin jin kunya tace ” Ta ya zatai ta…….” Yanda yake kallanta ne yasa tai saurin sa tafukan hannayenta ta rufe fuskarta cikin jin kunya.” Yace idanunsa na kanta “Ya zatai ta soshi?” Kallansa tai da sauri tare da cewa ba haka zance ba….” Murmushi yai sannan yace”Ya za’ai ta kasa sanshi?” Da sauri ta mike cikin tsananin jin kunya tai hanyar waje, har taje kofa zata fita taji yace ” ba kya tunanin abokin nawa yayi rashin kunya? Duba da yanayinta na dalibarsa?” Bata juyo ba tace ” Ai ba malami ne na dindindin ba sannan ko malamin ne banaji…….” Sai kuma ta kasa karasawa tana murmushi, yace “wasa wasa al’adarki ce tsayawa a tsakiyar magana, gashi nikuma zuciyata so take taji me zakice.” Cikin jin kunya ta juyo ta kalleshi sannan taj waje da sauri. Idanunsa ya lumshe cikin wani irin jin dadi sannan yabi bayan kofar data fita da kallo. Jalila kam tana tsaye ita kadai tana murmushi, lalai yau tana cikin jin dadi. Ganin motarsu tayi parking ne yasa tai saurin shiga dan ta hango Uncle na tahowa, ita kuma yanzu kunyarsa takeji. Tana shiga motar Safeena tace ” Jalila ya sunan wannan malamin?” Jalila ta hade rai tace “Wanne?” “Wanda muka gani dazu da safe, yauwa wanda ya ajiye motar can.” Ta fada tana nuna motar uncle Sagir. Jalila ta kara hade rai tace “menene?” Safeena tace “Meye kuwa, kawai dai burgeni yai nake tambaya.” Jalila tace “Sai ki tambayi matarsa dan ni bansani ba.” Safeena tace “Yana da mata?” Jalila ta guntse dariyarta a ranta tace “yayarki ba insha Allah.”3 ************* Hassan shi kadai a zaune a garden din gidansu, dan da kyar Ummy ta lalabashi ya fito, idanunsa a rufe sai dai ni kaina bansan tunanin me yake yi ba, ko kuna idanun kadai ya rufe. Daga bayansa yaji an rufe masa idanu, mikewa yai a zabure, Aina ta turo baki tace “Yaya!” Kallanta yai sannan yace “Meye hakan?” Tace “Yaya wai ni sai yaushene inka ganni zaka nuna farinciki kamar da?” Bai tanka mata ba sai kokarin barin gun da yai,idanunta ne suka canza, tsananin tausayinsa ya kara ratsata, sai yaushene Yaya zai dawo kamar da? Tana tsaye har sai da taga ya kulle. Tahowa tai daga gun jiki a sayaye, tana tura kofa taji ance “WAH!” Idanu ta runtse dan ta tsorata, dariya taji an kwashe mata dashi, ta bude idanunta cikin shagwaba tace “Ya Sagir!” Yace “Matsoraciya!” Tace “Naji din na tabbatar ko kaine sai ka tsorata.” A tare suka nufi cikin falon suna tafe suna hira, Ummy tace “Haba Aina, an shigo da trolly banga mai trolly din ba.” Tace “Ummy Yaya na hango shine naje mu gaisa.” Ummy tace “kece ashe kika koroshi daga inda yake” Kusa da Ummyn taje tare da zama a kasa tace “Ummy ina wuni?” Ummy ta amsa sannan Aina tace “Ya jikin Yayan?” “Jiki Alhamdulila zance kenan? Sai fatan Allah ya yayemai larurar nan.” Tausayin Ummy ne ya kama Sagir, kusa da ita ya zauna yace “Ummy d’anki yayi girlfriend” Kallansa tai tace “Haba?” Aina ta tabe baki tace ” da alama yarinyar bata da taste.” Harararta yai tare da maka mata pillow yace ” uwar sanjin gulma sai kije can ki shiga da kayanki kafin Ameera ta dawo.” Ta tabe baki sannan ta mike tare da jan Trolly dinta. Ummy cikin zumudi tace “a ina take Sagir?” Yace “Makarantarmu.” Tace “students ce?” Kai ya daga yana murmushi. Ummy tace “bani labari.” Dariya yai sannan ya mike yace “Ummy ba yanzu ba.” Tace “bama nasan ji.” Nan yai sama yana cewa “zama na musamman zamuyi ai Ummy na.” Da kallo ta bishi tana murmushi azuciyarta tace”Allah ya kawo randa zanga Hassan na walwala kamar haka, Allah ya kawo sanda zaimin zancen mace.”2 *********** Inna ta dade tana nazari kafin ta zagaye sunan mutane hudu a cikin dan littafin nata. Nan ta kira Sani wanda ya kasance Secretary dinta ne a lokacin da take ganiyarta, bayan sun gaisa tace “Nikam ya labarin Alh Ayuba?” Yace “Alh Ayuba ai yana England tun shekaru hudu da suka wuce shi da iyalansa.” Tai shiru sannan tai cancel din sunan sa tace ” Alh Muhammad fa?” Yace “Hajiya kin manta shine na baki labari an rufe company dinsu?” Tace “Oh na manta.” Nan tai canceling din sunansa tace “Alh Abdullahi Taura fa?” Sai daya danyi nazari yace ” eh shi yana nan garin Kano, sai dai yayi retire daga managern banki ya fada kasuwanci.” Tace “kasuwancin kamar ya yake?” Dariya yai yace “Kasuwanci mai karfi, dan yanada company na motoci, yanada gidan mai sannan yanada store a nan garin.” Murmushi tai tace “bashida wani issue na matsala ko personal life dinsa?” Sani yadan yi shiru yace “Ba komai a iya sanina na dai san akwai yaransa uku, sai dai akwai kananan maganganu akan babban dansa wanda inaji kamar akwai wata matsala da yake fama dashi, sai dai su suna kokarin boyewa.” Ba tare da wani dogon nazari ba tace “yauwa na gode, yanzu ka bincika ka samomin number dinsa, cikin gaggawa.” Yace “To Hajiya!” Harzata tambayeshi mutum na karshe da take tunani sai ta fasa dan dama tafisa ran mutane ukun. Mikewa tai ta shiga dan xagaye d’akin nata tana tuanani, tabbas tanajin ba matsala dan kuwa tasan Taura akwai mutunci sai dai tasan harka ta business bani in baka ne.” Ta tabbatar in ta nemi taimako dole sai ya nemi wani abu itama daga bangarensu, waya ta daga ta kira Dady tace “Abakar ya situation din directors dinmu?” Yace “Hajiya abin dai ba dadi, duk an rasa mafita” Batace komai ba ta katse wayar, hoton mijinta wanda sukai ita da Mumy da mijinta ta kalla, sannan ta zauna tare da bude littafin da take karantawa, wanda jin matsalar nan ya sa ta ajiye. Su Jalila an shiga tarkon kauna tunda Sagir ya bayyana mata zuciyarsa, yau komai take in ta tuna kalamansa sai dai kaga tana murmushi ita kadai, yau aikin gidan ko wahala bai bata ba dan yau zuciyarta a cikin shauki take. Nace Hmmmmm Kamar hadin baki yau Sagir da Jalila wani irin bacci sukai mai cike da mafarkin junansu, Jalila bayan tayi sallar asuba ta kalli Goggo dake jan carbi sannan ta gaisheta. Goggo ta amsa sannan tace “Jiya na kula a farinciki kike Allah ya kara kawo farinciki mai d’orewa a rayuwarki.” Jalila tace “Ameen Goggo.” Sannan ta d’ora da cewa “Goggo kidinga min addu’a inkin yi sallah Allah yasa na auri wanda yake sona nima nake sanshi wanda zai kularmin da ke.” Goggo ta daga carbi alamar zata zula mata,da sauri ta matsa tana dariya. Goggo tace “wato gaba d’aya yanzu kinci idon akuya ko? Na kula kwanan nan fitsara kike ji sannan aure kikeso.” Tace “Goggo daga cewa amin addu’ar miji sai kice aure nake so?” Goggo tace “bazakuwa ki daina cewa Miji ba kuwa ko?” Jalila tace “Goggo kice komai na a rayuwa, ni ba kawa ba in ba a boko ba, ni ba kowa ba, kedin dai kece komai na, kinga kuwa dole komai na nasanar dake.” Goggo tadan murmusa sannan tace ” kashe fitilar nan ga haske nan ya fara shigowa, kinga kar battery dinmu yai sanyi.” Jalila ta kashe sannan ta mike tace “Na tafi bauta.” “Bauta? Kai Jalila bakida dama.” Har takai kofa ta juyo tace ” Allah ya taimakemu an daina bauta amma wasu karfi da yaji nema suke su mai dani baiwa.” Ta fada tare da bude kofa, Goggo tai murmushi tare da bin bayanta da kallo, tace “a koda yaushe addu’ar miji na gari zan miki Habiba.”+ Jalila na fita ta zagaya ta baya inda kofar kitchen take dan tanan take shiga wai dan kar ta tashesu daga bacci, kwanukan da akaci abincin dare ta hade guri d’aya sannan ta zauna ta soma fere dankali, tana d’aura mai ta shiga yin wanke wanke, tana zubawa tana gyaran kitchen, tana gamawa tasa tafashen naman kaza sannan ta fito falo ta fara shara, haka ta gama shara tai goge goge, tana gama abinci lokacin suke fitowa daga daki alamar tashi daga bacci, nan ta shiga dakuna ta gyara ta wanke toilet sannan ta fito ta dafa ruwan tea, ta dau bread din da aka ajiye domin su, nan ta fita. Tana zuwa ta fada wanka tana fitowa ta zura kaya sannan ta shafa mai, duk abinda takeyi tanayi tana duba agoggo, tana fitowa falo Goggo ta miko mata tea a kofi tace “zauna.” Jalila ta kalli agoggo taga bakwai da ashirin, da sauri tadan kurbi shayin tadan gutsiri bread kadan tadan ci, tana jin alamar tada mota ta suri jakarta da hijab dinta. Goggo tace ” kidan kara ci mana ai naga motar sai tayi zafi” Jalila tace “Goggo ai yanzu ba late a rayuwata.” Tai waje da gudu a ranta tana cewa “ina san bari Uncle Ya ganni a cikin late comers?” Ta riga su Safeena ma fitowa, a cikin mota ta sa safa sannan tadan karkade sandal dinta. Safeena ta tabe baki tace “Jalila nikam dan Allah ki daina karkadomin disease.” Jalila ko kallanta batai ba ta kalli madubin gaban mota ta shiga dan duba fuskarta, Safeena ta kara jan tsaki tace “Mutum sai kace wanda zaije tallar kai, sai wani iyayi akemana, ni wlh na tsani iskancin banza.” Jalila ta kalleta tace “ke da wa?” Tace ” tambaya kike?” Jalila ta tabe baki tace ” ba tambaya nake ba dan na kula ke kullum cikin neman masifa kike.” Safeena ta bita da harara. Fuskarta ta maida jikin window tana kallan titi tare da tunanin yau da wani ido zata kalli Sagir? Ita duk kunya takeji. Yana tsayawa ta sako daga motar sannan tama Yasmeen bye bye. Tana kokarin shiga makaranta taga mota tayi parking a gaban makarantar. Jalila ta juya tare da kallan motar, kamar tasan motar nan, kara kallan motar tai sannan ta juya tare da cewa “in ma na san motar meye nawa a ciki?” Jitai ance Jalila! Tsayawa tai dan ta gane muryar mai maganna. Sagir yasa kanshi a cikin motar bayan ya fito, yace “Yaya godiya, zakaxo d’aukana?” Kallansa Hassan yai sannan yamai alama da hannu akan ya cira kansa daga cikin motar. Sagir ya fita tare da daga mai hannu, juyawa yai ya kalli kofar, gani yai bata gun. Murmushi yai a ransa yace ” naji dadin ganinki.” Shiga cikin makarantar yai fuskarsa dauke da fara’a. Kasancewar yau friday karamar rana ce sannan Sagir shine last period dinsu. Kafin ya shigo Jalila ta kalli Zarah tace “Zarah yau bakizo da sosan hoda bane?” Zarah ta mata kallan mamaki sannan tai dariya tace “yau kece da kanki?” Jalila ta dan canza fuska tace ” in an tashi ba gida zani bane, ba kuma nasan inje fuskata na maiko.” Zarah tace “sai ki bari sai an tashi sai ki nema bawai tun yanzu ba.” Jalila tace “ana tashi nake san tafiya b……..” Gaisuwar dataji anayi ne yasa tasan Uncle ya shigo. Harara ta makama Zarah sannan ta sunkuyar da kanta kasa. Uncle kuwa ko kallan ida take baiyi ba har ya fara lesson dinshi. Ganin baya kallanta ne yasa tadanji ba dadi a ranta sannan ta dago tare da kallan abinda yake koya musu.1 Har ya gama sannan ta fita, yana fita Zarah fa miko mata sosan powder da madubi. Jalila ta ture hannunta tace “banaso.” Sannan ta maida kanta kan desk ta kwanta, Zarah tace “tashi mu tafi.” Jalila tace ” jeki ni sai anjima zan fita.” Zarah ta fita tai gaba, tana kwance har aka wa watse, idanu ma ta rufe kamar mai yin bacci, batasan sanda ya shigo class din ba. Ya nemeta a waje bai ganta ba shiyasa yai tunanin ajin, kallanta ya tsaya yi yana murmushi, a hankali ta bude idanunta dan jin kamar ana kallanta. Idanunta ne suka sauka akan fuskarsa shagwabe fuska tai dan ta tabbatar kila tunaninsa da takeyi ne yasa take ganin kamar shine. Maida idanun tai zata rufe yace ” fushi ake da ni ne?” Da sauri ta bude idanunta tana kiftasu, sannan tai saurin komawa ta zauna, Sagir yace ” me kike a class ke kadai?” Batasan me ya sameta ba kawai ganintai ta wani hade rai wai ita a dole an mata laifi. Sagir yace “Da alama wannan Malamin yayi laifi kenan?” Kallansa tai fuska a hade tace ” ba kai bane dazu ko kallan inda nake bakai ba?” Tayi mamakin canzawar ta da kuma yanda take magana, a ranta tace “Lalai Jalila wato kin zama kwarariya.”1 Sagir samun kansa yai da darawa sannan yace ” Nayi laifi, sai dai kin manta dazu Uncle Sagir ne malamin student a ajin?” Tace “Yanzu fa?” Yace “Yanzu kuwa Urs Sagir ne.” Da sauri ta sa hannu ta rufe fuskarta. Kallanta ya sakeyi yace ” ba haka bane?” A hankali tace “Hakane.” Murmushin jin dadi yai sannan yace ” tunda na ganki hankalina ya kwanta dan dama Abbana zan raka wani guri, nace bari nazo na ganki.” Kallansa tai tace “Okay, sai Monday kenan.” Yace “Kai! Har sai monday fa ko?” Tace “ka manta yau friday?” Fuska taga ya canza yace “gashi naga alama ke ko yar wayarnan baki dashi, anya zan iya jure missing dinki har sai monday?” Kanta ta sunkuyar kasa tana murmushi, ajiyar zuciya yai sannan ya matso daf da ita yace “bari nai full charge yanda zan cancana battery dinA.” Kallansa tai sannan ta maida idanunta kasa tana murmushi. Ido ya kura mata sosai sannan ya ce “Na tafi.” Sai dayaje kusa da kofa sannan tace “sai anjima.” Juyowa yai sannan ya juya ya tafi. Ta window ta bishi da kallo, wani zazzafan so na ratsata. Sam ta shagala da tunani kafin ta farga ta fito da sauri, Tafi minti goma a tsaye taga dai ba alamar su Safeena, sannan ba alamar ma d’alibai suna wucewa, lalai ta tsaya soyayya antafi an barta, yau tana cikin wani hali dan tasan masifa kam ba’a magana. Tana tafe tana dan mitocinta ita kadai………. ************ Inna ce ta kalli Sani sannan ta kalli takardar daya kawo mata dauke da sunan Taura da number sa. Tace ” da ka sake bincike ba wani abu game da rayuwarsa da ta kyalansa bayan matsalar yaran?” Sani yace “eh gaskiya ba wani abu special, sai….” sai kuma ye ” ba ma dai komai.” Tace “da ke zaka fada?” Yace dama kamar yaransa maza biyu ne, ‘yan biyu babban Hassan sai kaninsa Husaini, sai dai jiya sai aka cemin wai Hassan ne da Sagir sai macen. Inna tace ” ko dai kaine ka manta ba?” Yace “zai ita yiwuwa inaji Husainin tun yana karami ya rasu.” Tace ” Dama ai maza biyu mace d’aya kacemin.” Yace “hakan na sani amma nadauka ‘yan biyun ne ashe wa da kani ne.” Inna ta jinjina kai cikin rashin damuwa tace ” ba wani abu bayan nan?” Yace “babu.” Nan ta saka number a wayarta sannan ta anna dialing. Sai atai ringing hudu sannan ya d’aga. A banngarensa yana zaune a bayan mota shi da Ummy, sai Sagir dake zaune a mazaunin driver shi kuma hassan na gefe, suna hanyar zuwa asibiti. Yana daga wa Inna tai sallama,Abba ya amsa sannan yace “ban gane ba.” Inna tace ” Taura nice Hajiyar grain.” Sai daya danyi nazari na wasu dakiku kadan sannan yace “Hajiya ina wuni?” Yai magana tare da canza yanayin maganarsa zuwa girmamawa.” Inna ta amsa sannan tace ” Taura ganinka nake san yi ina fatan zaka bani lokaci.” Yace ” Haba Hajiya, kina wani gari ne?” Tace ina kano, ina neman alfarma ganinka sanda kake da lokaci. Yace ” yau dai inada abinyi, sai dai banaji gobe akwai abinda zanyi, a ina zamu hadu?” Ya fada yana kallan Ummy, tace ” gida na zakazo ko nice zanzo ko kuwa a wani gurin zamu hadu?” Yace ” a’a ba matsala ni zan zo.” Tace “Nagode Taura zan turoma da address din gidan.” Ya amsa da to sannan ya kashe wayar, Hassan ya kalla wanda idanunsa ke rufe kamar me bacci sai dai kowa na cikin motar yasan ba bacci yake ba, Ummy ya kalla ya shiga fada mata wacce ta kira. Gate din wani katon asibiti naga an bude musu, Sagir ya shiga da motar. 1 ************* Jalila kam taci uwar tafiya kafin ta isa gida, duk ta gaji tayi ligib. Tana shiga ta tadda Mumy a bangarensu, gabanta ne ya fadi sannan ta kalli Goggo wanda kuka ne kawai batai ba amma da alama daurewa kawai takeyi. Mumy na ganinta tace “kin dawo daga yawon iskancin?” Jalila fuska ta canza sannan ta kalli Goggo wacce ta tabbatar an kare mata cin mutunci ne, tace ” Mumy ban gane b…..” Marin data kifa mata ne yasa ta kasa karasawa sannan ta rike kuncinta, Mumy tace ” ce miki akai nan gidan karuwai ne? Ko me?” Mamaki ya kama Jalila tace ” Mumy ban ga………” Wani marin ta kara kifa mata tace “a gidan ubanwa kika tsaya? Kungurmar munafuka? Dama kwanakin nan na kula bakyasan dawowa tare dasu Safeena saboda kina yawon bin maza.” Cikin wata irin kakkausar murya Goggo tace ” RAMLATU!” Kallan Goggo sukai a tare ita da Mumy, dan Jalila bata taba ganin ran Goggo ya baci ba haka. Goggo cikin jin zafin kalaman Mumy tace “Ta ya zaki kira yarinya ta da haka? Kina tunanin ‘ya’yanki sunfi na wa ne? A koda yaushe ina jure komai ne badan banajin zafin abinda akema Jalila ba sai dan ina tunanin kila hakan shine zai kawo salama a zuciyarta, komai da kika gani inayi inayinsa ne domin ta, taya ma zaki kalli ‘ya a gaban uwarta ki kirata da wadan nan munanan kalaman?”+ Mumy ba shakka ta dan tsorata, ta daure tace ” ni kike yima fada? Kijira ni.” Tafada tare dayin waje da sauri, tana fita Goggo ta rike kirjinta wanda ya mata wani irin nauyi, ga wani irin dum na tsananin ciwon kai daya fara sara mata, Jalila ta karasa kusa da ita tare da rungumeta tace “Goggo na.” Cikin shagwaba tai maganar, Goggo ta daure dan batasan Jalila ta gane batada lafiya tace ” Karki damu, ko me za’amin indai har akanki ne zan ita jure komai.”7 Jalila ta kwantar da kanta akan kafad’ar Goggo cikin tausayama kansu. Banko kofar da akai ne yasa ta d’ago da sauri cikin tsoro, Dady ta gani bayansa Mumy ce. Jalila da sauri ta mike ta tsaya a gaban mahaifiyarta alamar kareta tace “Dady kome ya faru laifi…….” Wani wawan mari daya kifa mata sai data fadi kasa, Goggo ta d’agota da sauri tana tambayarta. Dady cikin tsananin bacin rai ya kalli Goggo yace “uban wa ya baki dama ki cima matata mutumci?” Goggo ta kalleshi tace ” ni duk mutuncin data cimin bai zama laifi ba kenan?” Yace ” Me yasa bakya abu da tunani? Ko kuwa kwakwalwarki ce bata aiki? Gidan da kike zaune,abincin da kike ci, kayan da kike sakawa, karatun ‘yarki duk a cikin arzikin wa kike ci?” Goggo tai shiru tare da maida kanta kasa, sannan tace ” duk da haka banaji tanada damar cima ‘yata mutunci….” “Yanzu yarinya tayi laifi kina nufin tafi karfin a hukuntata ne ko me?” Jalila ta mike da sauri ta rike kafafun Dady tace “Dady na tuba, dan Allah kayi hakuri laifinane.” Kafa yasa ya hankadata yace ” gayyar tsiya.” Sannan ya juya ya kalli Mumy ya dafa kafadarta yace “muje ciki ko?” Yi tai kamar me share kuka tace “Ba sai danace kayi hakuri ba?” Juyowa yai ya bugama Jalila wani kallo na takaici daga ita har Goggon sannan ya juya shida Mumy, har sun kai kofa Jalila tace ” Dady me kake nufi da gayyar tsiya?” Wani banzan kallo ya buga mata sannan yace ” idan kika sake min magana da wannan vibe din wlh sai jikinki ya gaya miki, sannan kiyi gagawar tasowa kiyi aikin daya kamata kiyi.” Ya juya shida Mumy sukai gaba, Jalila da kallo kawai ta bisu idanunta na zubar da hawaye, kallan Goggo tai kamar zatai magana sai ta fasa, hawayenta ta share sannan ta mike ta daukoma Goggo maganinta ta mika mata tace “Goggo share kinsan halin Dady akwai saurin hawa kamar farashi, amma na tabbatar ba duk abinda ya fada yake nufi na, ai uba ubane ko?”3 Goggo ta tabbatar tannayi dan hankalinta ya kwanta ne shiyasa itama ta daure ta daga kai tace “haka ne.” Jalila ta cire kayan makarantarta sannan ta fita. Yau kam tana aiki tana zubar da kwalla, itakam dole me gaskiya tana gama makaranta tace Sagir ya fito suyi aure ta d’auke Goggonfa subar wannan dan iskan gidan.6 ************ A asibiti kuwa bayan sun shiga cikin office din wanda a saman kofar naga an rubuta Neurologist, suna shiga ya mike daga zaman da yake sannan ya saki fuskarsa yana cewa Welcome Taura.2 Abba ya karasa kusa dashi ya mika mai hannu suka gaisa, sannan suka gaisa da Sagir, Ummy tace “Dr Ahmad mun sameka lafiya.” Yace “Lafiya kalau Hajiya ya mai jikin?” Kallan Hassan tai sannan tai murmushi kawai. Guri suka samu suka zauna ita da Sagir, shi kuma ya shiga wani dan d’aki shida Hassan da Abba. Hassan ne ya kwanta akan wani abu, sai naga an tura abun cikin wani inji, da alama dai scanning din brain dinsa ake san yi, mutumin yana daga zaune yana duduba yanayin kwakwalwar Hassan. Bayan ya gama d’aukan hoto sai ya dana wani abu sai Hassan ya fito, Nan Abba yaje ya taimakamai ya sauko. Guri ya bashi ya zauna sannan shima ya zauna kusa da Dr Ahmad ya kalli Hassan yace ” Hassan!” D’agowa yai ya kalleshi baice komai ba, Dr yace ” kana experiencing din wasu sababbin symptoms ne?” Hassan ya girgizakai alamar a’a sannan ya dan hadiyi miyau yace ” Sai dai kwanan nan bana baccin awa d’aya nake farkawa.” Dr yace “da mafarkin kake farkawa?” Yace eh Bayan su fa? Yace ” bakomai sai yanda dama na saba.” Yace “Haryanzu kanajin numfashinka na rikewa?” Kai ya daga, alamar eh, yace ” kirjinka fa? Kai ya sake d’agawa, yace rashin san hayaniya fa? Nan ma ya daga kai, Dr yace “duk ba abinda ya ragu daga abinda kake ji da?” Hassan ya d’aga kai. Dr yace ” tashi kaje.” Hassan ya mike ya fito daga d’akin, Dr Ahmad yai gyaran murya sannan yace “Taura abin ne sai mun dage da addu’a sannan mun bulo mai ta yanda ya kamata, da farko dai kamar yanda ka sani har yanzu ba matsala dan gane da kwakwalwarsa, matsalar tana tare ne da zuciyarsa dolene sai mun dage inhar munasan ganin ci gaba.” Abba yace “Ni Ahmad na rasa yanda zanyi, abin nan ko ina muka je za’ace matsalar bata kwakwalwa bace, kuma nima na yarda da hakan, tunda yana tuka mota da kansa ba tare da matsala ba sannan bai taba yimana abu na mahaukata ba, sai dai na rasa yan…….” “Abinda ya faru dashi a baya, na tabbatar shine ya rike mai zuciya, yana zargin kansa ne akan duk abinda ya faru a wannan lokacin laifinsa ne.” Abba ya kalleshi cikin nazari kafin yace “amma bayan abin nan ya faru yafi shekara d’aya a asibiti ba’a hayyacinsa ba, sannan bayan ya farka akace mana ya manta da abinda ya faru dashi a wannan lokacin.” Ahmad yace “That’s what we think, sai dai ina tsoron kar dai abin na nan a ransa, kawai dai yana nuna ya manta ne dan neman kwanciyar hankali.” Jikin Abba ne yai wani irin sanyi tsananin tsoro ya kamashi yace “Ahmad ya zamuyi?” Dr yadan yi shiru sannan yace “akwai solution, na farko ku yarda da abinda ya tsara na mantawa dayai, karka fadawa kowa tunda nima ban tabbatar da hakan ba, sai abu na biyu ina ganin ku nemomai mace wacce zata dinga kwana dashi tana yini dashi, in kuka samarmai mace mai hankali wacce zatasoshi a hankali mekin dake zuciyarsa zai warke, ko akwai wacce yake so?” Abba yace ” ina ma yake kallan macen bare?” Ahmad yace “to in wannan bazai yiwu ba sai dai in sake research in dubo wata hanya, dole dai a cikin gida maganinsa yake, sannan yana bukatar kukawar dukaninku, ta hakan ne guiltiness din dake makale a zuciyarsa sai kankare.” Abba yai shiru kafin can yace “na fahimta sannan duk wani abu indai har bai sabama shari’a ba zan iya aikatashi indai har Hassan zai samu sauki, domin ni da matata Allah ne kadai yasan halin da muke ciki.” Ahmad yace “Karka damu Allah na tare da mu insha Allah.” Nan sukai sallama suka fito, Ummy ce kawai a d’akin, Abba yace “Hassan fa?” Tace yana fitowa waje yai, sai naga Sagir ya bishi. Ya karayina Ahmad godiya sannan suka fita. Hassan na zaune a can gefen asibitin ya kurama kasa ido yana karzar hannunsa na dama da farcen babban yatsarsa na hago, Sadiq na gefensa kadan a tsaye. “Inama Allah ya d’auki ransa a wannan lokacin? Babban bakin cikinsa bai wuce yanda iyayensa ke fama a kansa ba, gaba d’aya bayasan ya zama haka, sai dai ya zaiyi?” Sagir ne ya matso da sauri ya sa hannunsa ya tare hannun damarsa yace “Yaya!” Kallansa yai sannan ya kalli hannunsa wanda sam bai kula ba ashe ya karje hannunsa har ya fara jini. Hannun Sagir ya matsar sannan yace “I’m okay.” Sagir cikin tausayawa yace “muje mota gasu Ummy sun fito. Mikewa yai suka shiga mota. Duk yanda Abba yai akan yai bacci ya kasa, Aina? Kai ya girgiza da sauri dan yasan halin Aunty Nana, duk da yaya take agun Mumy ya tabbatar bazata yarda a aura mata Hassan ba, balle dama ta taba cewa Ummy ya kamata akai Hassan psychiatrist. Ummy ce tace ” abinda Dr Ahmad ya fadama ne yake damunka?” Yace “ba abinda yacemin, baccin ne dai na kasa yi.” Bata sake cewa komai ba dan ta riga taji komai, Hassan da Sagir na fita ta je jikin kofar dan dama ta damu tasan cikaken halin da d’anta yake ciki, sai dai koda yaushe Abba bai fada mata. Ba shakka itakam gobe zatama Aunty Nana magana akan Aina taji. Taura yayi shiru a d’aki yana nazari, Ummy ce ta turo kofar tare da sallama. Bai jita ba dan ya nustu sosai, kusa dashi ta tsaya tace “Lafiya?” Kallanta yai sannan yadan murmusa yace ” tsi wlh hankalina ya tafi tunani ne.” Tace “abinda kajeyi bai yiwu bane?” Yace “Hafsa dan zauna.” Zama tai kusa dashi tana kallansa, yace ” yau naga wata yarinya a gidan danaje, ban san meyasa ba naji yarinyar ta kwantamin sosai wanda nakema Hassan sha’awarta, tarbiyarta yasa nake tunanin zata kula da shi fiye da tunanin mu.” Ummy tace ” yarinyar gidan dakaje ne?” Yace “eh.” Zata sake magana Ameera ta bude kofar da gudu tace “Ummy yaya ne…….” Da gudu suka mike suka hau sama, yana kwance a kasa da alama fadowa ma yai ya kankame jikinsa yasa hannunsa a yuwansa wanda ya kasa jan numfashi. Sagir sai kokari yake gun taimaka mai, Ummy kasa karasawa tai sai kuka da take yi, Abba ya karasa da sauki yana danna mai kirjinsa, Aina’u da Ameera sai kuka sukeyi.+ Da kyar ya ja wani dogon numfashi sannan ya kallesu cikin takaicin halin da yake sa su. Wasu zafafun hawaye ne suka zubomai yana kallan mahaifiyarsa. Ummy jiki a sanyaye ta karaso inda yake ta rike hannunsa tace “Hassan!” Bakinsa ne ya shiga rawa, a hankali yace “Ummy kiyi hakuri.” Kai ta shiga girgizawa tana kuka tace “Hassan please kadaina fadar haka.” Sagir ma jiyai hawaye ya zubo masa saboda tausayi, Abba ya sa hannu ya d’agata yace ” ku je ku barshi ya huta.” Haka suka fito daga d’akin hankalinsu a tashe, Abba ya zauna kusa dashi yace “Hassan meyasa kake kokarin jefa rayuwarka cikin halaka? Sau nawa zamu sanar dakai abinda ya faru a baya ba laifinka bane?dan Allah ka taimakemu ka cirema zuciyarka wannan zargin da takeyi.” Hassan ya juya kansa gefe kawai baice komai ba, Abba ya mike ya fita, tabbas ya yarda da maganar likita aure ne ya dace dashi, yanzu in tsakar dare ne abin nan ya faru ba wanda zai kula dashi me zai faru?1 Ummy kam kuka tai tayi, Sagir yana zaune a kasanta ya rasa ta ina zai fara lallashinta, gaba d’aya gidan a wannan rana ba wanda yai walwala. *********** Yau da daddare Abba ya gama yanke hukuncinsa dan a daren jiya bacci kalilan yai. Yau da safe kuwa karfe 10 ya kira wayar Inna. Bayan sun gaisa ne yace “Hajiya nayi dogon nazari akan al’amarin nan, sai dai ina tunanin haduwa ya kamata muyi ko in sanar dake ta nan?” Inna tace “Taura duk yanda ka gani.” Yai shiru kafin yace “Bari in sanar dake ta nan in yaso in kikai tunani sai mu hadu dan yanke hukunci.” Tace “ba laifi hakan yayi.” Sai daya danyi shiru kadan kafin yace ” me zai hana muyi yar hadin gida.” “Yar hadin gida?kamar ya kenan?” Yace “eh, ina nemawa d’ana babba auran babbar jikarkarki.” Mikewa tai daga zaman da take tama kasa cewa komai, yace “Hello!” Tace ” Taura naji, ba matsala mayi magana daga baya.” Ta katse wayar hankalinta a tashe. Da sauri ta danna number Dady. Yana kwance akan gado Mumy ba kwance a kafadarsa suna hira. Yana ganin wayar Inna ya mike tsaye yace “plm ce.” Mumy ta turo baki tace “share ta kawai, na tabbatar maganar aiki……” Bata karasa abinda zata fada ba taji yana cewa “To.” Yana kashewa taga ya kalleta yace “Inna na neman mu.” Mikewa tai suka hau sama. Jalila na ta aiki sanda ta gansu sun hau sama, sun nutsu dan yanda suka ganta alamar ba lafiya. Inna ta dade kafin ta kallesu tace “Taura ya kirani.” Mumy tace “ya amince?” Tace “eh.” Mumy tace “lalai mutumin nan yanada kudi, wannan uban kudi da muka nema?” Inna ta mata kallan batada hankali, sannan ta daga waya ta kira Sani a gabansu ta sa a hands free. Bayan sun gaisa tace ” Sani me kacemin dangane da babban dan Taura?” Sani yace ” bashida cikakiyar lafiya, dan akwai wanda yacemin ma kwakwalwarsa ba daidai take ba.” Inna tace to nagode. Ta kashe wayar sannan ta kallesu tace “hadin aure Taura yake neman yi damu.” Mumy cikin halin ko in kula tace “Hadin aure da wa kenan?” Dady kallan Inna yai cikin mamaki, Inna tace “me yasa bakya amfani da kwakwalwarki ne?” Tace “to ai ni bangane da wa za’ai hadin aure…… ” Dady ne yai saurin tabata sannan ya kalli Inna yace “amma ai baiga Safeena ba.” Tace “nima abinda ya ban mamaki kenan daga farko, sai daga baya nai tunanin yaransa ashe fa ancemin ba hankali gareshi ba, kaga kuwa ta ya ya zai damu da sai ya ganta? Tunda shine dai kawai burinsa yaga ya sa marmai mata ne?” Mumy tace “hauka kenan, ta ya ya dan zai bamu kudi zai nemi hadin aure tsakanin mai hankali da mahaukaci?” Dady ma yace “gaskiya Inna nima ban amince abama Safeena mahaukaci ba.” Inna tace “me kuke tunani? Kuna tunanin nima a san raina ne?” Mumy zatai magana sukaji an kwankwasa kofa. Inna tace “waye?” Jalila tace “nice, abinci na kawo.” Inna tace shigo. Shiga tai ta ajiye abincin a inda tasaba ajiyewa sannan ta gaisheta, ta gaidasu Dady sannan ta mike tai waje. Tana rufe kofa naga idanun Mumy dana Inna sun kalli juna, Inna ta hade rai ta kalli Dady tace ” da Taura ya kira cewa yai yanasan hadin aure tsakanin babban dansa da babbar jikata.” Dady yace ” to yazamuyi?” Tace “baka fahimceni ba kenan?” Yace “kamar ya kenan?” Inna tace “a ka’ida wacece babbar yarka?” Da sauri ya kalleta dan yanzu ya fahimce me take san fad’a, jiki a sanyaye yace “Jalilah.” Tace “wa kake tunanin Taura na nufi?” Dady ya kalleta sai dai bai iya cewa komai ba. Mumy cikin kissa tace “Yanzu Inna ta ya zamu aurana Jalila mahaukaci? Gaskiya nikam ban yarda ba.” Inna tace ” to sai shi Abbakar din ya duba ya gani, da company dinmu ya durkushe mu rasa kudin mu, da mu daure mu aurama Jalila yaran wanne yafi? Sannan yaushe kikaji ance miki mahaukaci ne?”2 Dady yai shiru yama rasa me zaice, can yace “amma ai suna ganinta zasusan ba yar cikin gidan nan bace.” Inna tace “karka damu da wannan zansa yau din nan a maga dinkuna kala kala, sannan zansa a dauko mai aiki, ai dama na dade ina tunanin cewa ta bar aikin da takeyi, kuma yaran nan tunda yana da matsalar kwakwalwa gani nake bazai zama wani abu ba, gidan kudi zata sannan in haukar ta juyo mai zai iya sakintama a ranar kaga shikenan kowa ya huta.”4 Kallan mamaki ya shiga yima Inna, tabbas wannan kalaman nata sunzo da rainin hankali sai dai bayaji zai iya bijirewa domin shima ya tsani talauci a rayuwar sa, menene dan ya sadaukar da rayuwar yarinya d’aya? Inna tace “in kuma baka yarda ba…….” Yace “Inna waec…..” Tace “zanyima Taura magana a barta sai ta gama karatunta, sannan a gida ma banasan kowa ya sani har sai ta kammala karatunta yanda hankalinta zai kwanta.” Dady ya jinjina kai alamar gamsuwa. Haka suka cigaba da tsare tsarensu shidai Dady kome sukace yarda yakeyi.1 Kiran Taura Inna tai ta sanar dashi amincewarsu. Yaji dadi sosai ya ce zaizo karshen satin nan ya kawo kudi sannan su sa hannu akan contract din da sukai. Ummy dai batace komai ba, sai dai Abba yace “in zaije sai suje tare ta ganta.” Da haka ya rufe mata baki. ********* Jalila tayi mamaki sosai ran lahadi da yamma da Mumy ta nuna mata wata mata a matsayin mai aikinsu, sannan tace mata daga yau karta kara yin aikin gida. Abinci ma mai raia da lafiya aka aiko musu. Yau kam cike da mamaki tabar gidan. Da zata tafi har dari biyu Mumy ta bata wai kudin kashewa, yanda ake ba su Safeena. Suna isa makaranta ta sauko tana tafiya, tunani takeyi wannan kuma wani sabon salon ne ke faruwa? Sam bata kula dashi ba wanda missing dinta ya sashi fitowa da wuri. Yana kallanta har ta wuce bata kula dashi ba, sai datai nisa yace “Jalilah!” Juyowa tai ta kalleshi, jitai duk damuwar dake ranta ya tafi, wani sansanyan murmushi ne ya bayyana a fuskarta. Tace “Uncle.” Fuska ya daure sannan yace ” what are u thinking?” Tace “Something suspicious.” Ganin Zarah ta taho yasa yace “See u later.” Sannan ya juya. Da kallo ta bishi dashi tana murmushi. Zarah ta daka mata duka a baya tace “Anya Jalila bakida crush akan Uncle Sagir kuwa?” Jalila ta ture hannunta tace “to uwar sa ido, in ma inada shi laifi ne?”1 Zarah tai dariya tace “in shigar dake?” Jalila a ranta tace na shigar da kaina tuni, amma a fili tace ” ni banasan love one side.” Haka suka tafi suna hira. Sai da aka tashe aka watse tana tsaye, sai leken kofa take ko zataga fitowarsa, sai can ta hangoshi ya taho. Da sauri ta juya kamar bata kallan gun, har sai daya iso. Jitai yace ” Hajiyar tunani an cigaba ne?” Kallansa tai tace “Uncle kaine?” Murmushi yai sannan yace “bakima ji alamun na iso ba?” Tace “sry na tafi tunani ne.” Fuska ya dan canza yace “anya kuwa kinyi missing dina?” Idanu ta rufe wai ita kunya sannan tace” sosai ma.” Yace ” to kunyar ita kuma ta menene? Ni bude idanunki ki fadamin meke damunki?” Idanunta ta bude tace “Uncle me zakace ingaka wanda ya tsaneka ya fara nuna maka yana sanka?” Sagir yai shiru kafin yace “ya danganta da irin tsanar da kuma irin san.” Tace ” da ba wanda ya damu dakai haka kawai sai kuma kaga kowa yana ma mutunci yana kula da kai.” Yace cikin dayan biyu ne, ko sun fara santa da gaske ko kuma suna san wani abu daga gunta.” Jalila tai shiru tana tunani, itakam bataji akwai na biyun, to ko santa sukeyi yanzu? Da sauri ta girgiza kai tace “tunda aka haifen basa sona sai yanzu?????1 Nima nace gaskiya kam😝