JALILA
Dady na fita daga dakin ta dau waya ta kira Mumy. Mumy na shigowa ta kalleta tace “ki shirya muje ganin daki.” Mumy tace “ganin daki kamar ya?” Inna tace ” au a aurar da yarki guda? Sannan babbar jika a gareni ina tunanin ya zama dole muje bayan an kaita muga muhallinta.” Mumy tai yar dariya tace “Lalai Inna, jikarki? Ni dai a kara za’a iya cewa ‘yatace amma Inna ke ai……” Kallanta tai fuska a d’aure tace ” me kike nufi?” Mumy tace “Inna ai kece bangane me kike nufi ba.” Inna ta ajiye wayarta sannan ta mike tace ” na rasa sai yaushe ne kwakwalwarki zata fara aiki yanda ya kamata.” Mumy ta mata kallan rashin fahimta, Inna tace “nikam wacece babbar ‘yarki?” Tace “Safeena mana.”+ Inna ta kalleta cikin takaici tace “wacece babbar yarki?” Mumy tace “ni Inna rudani kikeyi.” Inna ta harareta sannan ta girgiza kai cikin takaici tace “ni wuce muje ki shirya mu tafi, ni in munje gidan na miki bayani.” Mumy ta mike ta fita tana tunanin kalaman Inna, batagane wacece babbar ‘yarta ba, yo ai kowa yasan Safeena Qta fara haifa. Hart takai matattakala uku sai ta tsaya cak tace “ba dai……? Komawa tai da gudu saman ta bude dakin Inna, tace “Inna badai so kike ki cema mutane nice mahaifiyar Jalila ba?” Inna bata kalleta ba sai shafa man zafin da takeyi a kafarta da takeyi, Mumy cikin mamaki ta karaso kusa da ita tace “Inna?” Inna ta kalleta tace ” me? Kina tunanin is in possible?” Mumy cikin tsoro tace “Inna me kike tunani? Taya zaki canzama yarinya mahaifiyarta? Bayan mahaifiyarta nanan da rai?” Inna ta kalleta tace ” kina tunanin in Taura yasan gaskiyar al’amari akan ba yarinyarki bace zai yarda? Bakya tunanin zai ga yaudararsa mukai? In ya kwace kudin dayai investing a company dinmu fa saboda munyi betraying dinsa?” Mumy tace “to ai bai fito filli yace ‘yata yakeso ba, shidai babbar yarinyar gidan nan yace, sannan in ta sanar dasu fa kafin kije? Ni Inna wannan karan ban amince da abinda kika tsara ba.” Inna ta kalleta tace “shiyasa akoda yaushe nake ganin hankalinki da wayan ki na banza ne, ke wai haryanzu kina tunanin Abakar sanki yake?” Tace “Inna zaki fara ko?” Tufe maganin zafin tai tace ” kiyi gaggawar tashi daga baccin da kikeyi, kada ki kuskura kiyi relying akan kowa inba ni ba, sannan kada kiyi trusting din kowa inba ni ba.” Mumy ta kalleta sannan ta mike kawai batace komai ba ta mike ta fito, itakam duk abinda Inna tace mata tana bi sai dai wannan karan hankalinta bai kwanta da hakan ba. ********** Jalila kam da sutai sallar asuba falonsu na sama ta fito ta kwanta dan taga alamar baida niyyar mikewa daga gun. Wajen karfe tara ta farka, jitai jikinta ya ware, saukowa tai daga kan kujerar data ke kwance sannan ta karaso jikin kofar, hannu tasa a hankali ta murda kofar, kanta ta zuro a hankali tana lekawa, bata ganshi akan gadon ba hakan yasa tai tunanin baya dakin, tura kofar tai shiga, tana shiga ta hangoshi a kwance akan sallaya inda yai sallah, baki tadan tabe tace “kamar gaske.” Wucewa tai zata shiga toilet, gani tai ya fara wani abu harta je bakin toilet din, juyowa tai da sauri ta kalleshi, gani tai yana zufa sannan sai wani murkusus yake, idanunsa a rufe gam. Kallansa ta sakeyi tace “mafarki yake?” Kusa dashi taje tadan sa hannu tadan tabashi, hannunta ya rike da karfe yana wani irin numfashi, sankamewa taga yanayi, tsoro ne ya fara kamata, ga hannunta ya kankame da karfi wanda zafinshi ya isheta. Cikin tsananin tsoro ta fara cewa “Yaya!” Dan abinda taji suna cemai kenan, Yaya! Yaya! A tsorace take kiran sunan nasa. Ganin zufa tana keto mai ta ko ina ga sai kara kamewa yakeyi, yanzu kam hannunta ya saki yasa hannunsa a wuyansa yana kokarin jawo numfashinsa da yake mai wahalar shaka. Jikinta ne ya fara rawa, ganin yanda yake sa hannu a wuyansa yasa tai saurin sa hannu ta rike nasa da karfi, a tsorace take cewa “Yaya! Yaya! Menene?” Ganin abin karuwa yake yasa ta fara tofamai kulhuwallahu, falaqi da nasi, dan bata iya addo’oi ba. Hannunta data rike nashi ya jawo hakan yasa ta fada jikinsa, da sauri ta mike, sannan ta shiga kiransa tana tabashi. Ahankali yai wani dogon numfashi, sannan ya bude idanunsa wanda sukai jaa. Idanunsa ne suka sauka a kanta tayi tsuru tsuru kamar kace mata kyaa ta ruga a guje…. Kallanta yai cikin rashin jin dadi, dan shikam yasan abinda yake tsoro kenan, bayasan wani ya ganshi cikin wannan halin. Jalila kam tana nan a zaune kamar abu mara motsi har ya mike zaune, ganin yanda ta kame yasa ya mike tsaye ya zaune a bakin gado sannan yasa hannu ya shafi fuskarsa cikin takaici. Jalila a hankali ta juyo ta kalleshi bakinta na rawa tace ” hmm ka ka……” Kallanta yai fuskarsa a hade ga idanunsa sunyi jaa, wani irin tsoronsa ne ya kamata, gabanta ya shiga faduwa. Idanunsa na kanta yace ” ka me?” Kai ta girgiza da sauri tace “hm ba komai.” Ta juya da sauri gaban wardrobe taje ta bude ta rasama me zatayi a kai sannan ta matso gaban madubi shima ta tsaya, sannan ta bude bandaki da sauri ta shiga ciki. Duk abinda takeyi idanunsa na kanta, idanunsa ya sake runstewa cikin takaici, gani nai ya bude idanunsa ya mike da sauri ya dau waya da key din motarsa. Yana kokarin fita itakuma tana fitowa, kallan juna sukai da sauri ya dauke kansa sannan yai waje. Kallan kofar daya rufo tai sannan ta zauna a bakin gado tana maida numfashi kai kace gudu tai, me ke nan? Me ya faru dazu? Aljanu ne dashi? Kansa kalau kuwa? Badai wannan bace matsalar da Ummy tai magana? Ta dade a zaune sannan ta mike tai wanka, haka ta sa kaya jiki a sanyeye sam hankalinta ya kasa kwanciya. Ameera ce ta kwankwasa kofa, Jalila ta bude mata. Tiren abinci ta miko mata tace “ga abincin yaya, ke kuma ki sako muje kasa.” Jalila ta kalleta cikin sanyin jiki tace “Bayanan, sannan ni banajin yunwa.” Ameera ta kalleta tace “yaza’ai kice bakyajin yunwa?” Jalila ta kalleta sannan ta koma ciki, gaba daya itakam abin duniya ya dameta, Ameera ta ajiye tiren sannan ta kalleta tace “ga na yaya nan sai kici anan, shi nasan ba yanzu zai dawo ba.” Ajiye abincin tai ta fita. Jalila kam a zaune kawai take akan gado tama rasa ta ina zata fara tunanin abinda ke faruwa. Ganin ta rasa amsa kawai ta dauko hijab dinta ta sauko, su Ummy na cin abinci ta sauko kasa, kusa da Ummy taje ta gaisheta sannan ta gaida Sagir, Ummy tace “zauna muci abinci.” Jalila wacce ta fito dan sanar da ita tana san zuwa gun Goggo tai shiru tana wasa a hannunta. Ummy ta kalleta tace “Ya akai Jalila? Wani abin kikesan fadamin?” Dagowa tai ta kalli Uncle sannan ta kalli Ummy. Sagir ya kalli Ummy yace “ko jikin ne? Ummy ta kalleta tace “Jikin ne?” Jalila da sauri tace “bashi bane.” Ummy tace “to menene?” Jalila ta kalleta sannan ta sake yin shiru, Sagir ya yace ” asibitin zaki koma?” Kallansa tai sannan ta kalli Ummy, Ummy tace “wai haka?” Jalila ta daga kai, Ummy tai murmushi tace “menene to da kika kasa fada? Ki zauna kici abinci sai kuje da Sagir.” Kallan Sagir tai da sauri, sai dai batace komai ba. Ummy tace “in bakya san ci anan ki hau sama kici kafin ya gama.” Jalila tace “nagode Ummy.” Sannan tajuya tai ta hau sama. Zama tai a falon tai shiru Hassan take hangowa abinda yai dazu. Kanta ta kwantar akan kujera, Muryar Ameera taji tana kiranta, nan ta mike ta sauko ko dakin bata koma ba. Da zata fita Ummy ta kirata, Jalila ta juya taje gunta, Ummy ta miko mata leda sannan tace ki gaisheta, dan gwarama da kika tuna min yau kije, dan Abban Ameera inya dawo ba lalai ya barki ki fita ba, bayasan fita.” Jalila ta amshi ledar tana godiya. A bakin mota ta hangoshi a tsaye, nan ta karasa kusa dashi, gani tai ya bude mata bayan motar sannan ya juya ya shiga gun zaman driver tare da kunna motar. Rufe kofar motar tai yaja suka fara tafiya, Motar tayi shiru sai karar redio dake tashi a cikin motar. Sunyi tafiya mai dan tsayi kafin can yace “Jalila.” Idanunta na jikin window tace “naam.” Yace “Jalila nasan na miki laifi sai dai nan gaba zaki fahimci dalili na nayin hakka sannan na tabbatar a lokacin zaki san abinda nake nufi da kalamai na.” Kallansa tai sannan ta daure tace ” magana ta wuce, sai dai meke damun Yayan naka?” Shiru yai kafin yace “Ni kaina ban sani ba, dukanmu yan gidan ba wanda yasan meke damunshi, shikadai yasan abinda ya faru a lokacin.” Lokacin? Yace ” eh lokacin da su Husain da Nazir dan kanin Abba.” Jalila tai shiru batace komai ba, Sagir ya kalleta ta madubin gaban motar, yana tsananin san yarinyar nan haka kuma yana tsananin tausayinta sai dai duk yanda yaso da so da kaunar ta bai isa ba…..bai isa ba.” Dagowa tai ta kalli madubin suka hada ido, kanta ta kawar sannan a hankali tace “Uncle!” Yace “naam.” Har zata cemai Goggo mahaifiyarta ce sai ta fasa, tace “shikenan ma.” Yace “menene? Dan Allah ki fadamin.” Shiru tai kafin can tace “Goggo nace a asibitin.” Yace “nayi tunanin Goggon da kike maganar ta ne amma ya kuke?ni da nadauka ai Goggon mahaifiyarki ce.” Zatai magana ya taka burki da karfi, juyowa yai ya kalleta yace “Jalila are u okay?” Tace “eh menene?” Yaran da suka tsallaka titin ya kalla yace ” yara ne wlh saura kiris su ja mana.” Shiru tai batace komai ba, gangarawa asibitin yai, parking yai sannan yace “Jalila ki yi hakuri dan Allah.” Kallansa tai tace “zancen hakuri da rashinsa ai ya kare, kafin ai abu ne ake neman canzashi ba bayan anyi ba.” Ta bude motar sannan tace “nagode.” So yake ya shiga amma bayasan ya kara bata mata rai. Bata dade da shiga ba sai gatanan hankali a tashe tace “Uncle na rasa Goggo na.” Sagir yace “ban gane ba?” Kuka ta saka hankalinta a tashe take cewa sunce an mata transfer zuwa wani asibitin kuma basusan sunan asibitin.” Yace “ban gane ba?” Tana kuka tace “wai basu sani ba……” ******** Abba kam dakyar ya samu bacci jiya, ya rasa meyasa gaba daya tunanin yarinyar da bata fi sa’an dansa ba ya dameshi. Ai kuwa da sassafe ya fada mota da driver dinsa suka nufo kano, ko kara bi ta contracts din baiyi ba. Me ya sameshi? Me ke faruwa dashi? *£********** Mumy ce ta kalli Sultan tace “Sultan bari muje gidan Jalila, ko zakaje?” Inna ce tai kakari wanda yake nuna mata ta daina, Mumy ta kalleshi tace “bari muje.” Nan suka fito daga gidan suka shiga mota. Kasa tsayuwa tai kawai ta tsugunna agun tasa kuka, Sagir ya koma cikin asibitin ya tambayesu, yanda suka fadamai haka suka fada mai, fitowa yai gunta yace ta shiga mota tunda ai sunce wanda ya kawota shine ya dauketa. Tanaji tace “Dady ne.” Nan suka shiga yaja motar da gudu suka nufi gidansu, basuyi nisa da fara tafiya ba wayar Sagir ta shiga kara, Sagir ya daga tare da cewa “Ummy!” Ummy tace “Sagir kuyi sauri ku dawo iyayen Jalila da kakarta sunzo.” Yace “gamunan.” Ya juya kan motar yana cewa “jalila iyayenki suna gida.” Hawayenta ta share tace “an fadama wa nene yazo?” Yace “kawai dai cemin tai iyayenki da ko kakarki ne?”+ Jalila tai shiru sai fatan Allah yasa ba wani abin bane ya faru, suna isa gidan ta fita da sauri ko motar bata rufe ba ta nufi cikin gidan. Da gudu ta shiga, a falo ta taradda Ameera rike da waya tana latsawa. Jalila ta matso tace “Ameera ina Mumy?” Kallan ta tai tace “suna sama.” Jalila tai sama da gudu, a falon sana ta taradda Inna, tsayawa tai sannan ta karaso a hankali, tsugunnawa tai ta gaida Inna kafin ta gaida Mumy. An ajiye musu kayan ciye ciye a gaban su. Ameera ce ta hawo saman sannan ta mika mata makullin dakinta, Jalila ta mike ta bude dakin sannan tace ku shigo. Mumy ce ta fara mikewa, Inna kuwa sai data karema falon kallo sannan ta shiga dakin, zama tai tana kallan dakin kafin tace “ina mijin naki?” Jalila tace “ya fita.” Inna ta kalleta tace “rufe kofar.” Jalila ta mike jiki a sanyaye ta rufe kofar, Inna ta kalleta ta mata alama data matso kusa da ita. Jalila gabanta sai faduwa yake ta matsa a hankali, ta tsugunna. Mumy ta kalleta tace “Jalila gun Goggo kika je?” Ta kalleta sannan tace “eh amma bata asibitin, ance Dady ya dauketa.” Mumy ta kalli inna, Inma ta kalli Jalila tace “ni nasa ya dauketa daga asibitin.” Jalila ta kalleta tace “Inna kikace in na amince da auran nan zaki kula da Goggo?” Inna ta kalleta tace “hakane.” Jalila tace “kuma…..” Inna tai murmushi tace ” ba dai kina tunanin wani abin muka mata ba?” Jalila a tsorace ta kalleta, Inna tace ” kinsanar ma wani a gidan nan Goggo ce ta haifeki?” Jalila jiki a sanyeye tace “a’a amma…….” Inna tace “Jalila wacece ta haifeki?” Kallan mamaki ta mata tace “ban gane ba Inna?” Har yaje zai shiga dakinsa yaji kamar ana magana a dakin Jalila bayan yasan Ummy ta rufe dakin, kuma yaga Ummy da Ameera a kasa. Hannu yasa kamar zai bude kofar yaji ance “tambayarki nake sannan amsarki nake so naji.” Jalila tace “to ai Inna tambayarki gaba daya na kasa fahimtarta, bangane wanene ya haifeni ba?” Har ya juya zai tafi dan shi mutum ne da bai damuwa da abinda bai dameshi ba. Jiyai ance ” abinda zamsanar dake inaso ya zama amsarki a duk lokacin da aka tambayeki, daga yau ko waye ya tambayeki mahaifiyarki ki tabbatar kince Mumy ce ta haifeki.” Da sauri Jalila ta kalli kofar, shima da sauri ya kalli kofar, meke faruwa? Shidai a iya saninsa bai taba ji inda ake sanar da d’a mahaifiyarsa ba. Jalila tace “Bangane Mumy ce ta haifeni ba? Goggon tawa rasuwa tai ko me? Ina kuka boyeta? Ta fada cikin wani yanayi mai ban tausayi wanda yasa Hassan din jingina da bangon jikin kofar. Inna tace “ko daya, ina dai sanar dake ne hakan shine kadai zaisa mu taimaki mahaifiyarki mu kuma bata rayuwa na gari.” Jalila jitai ta sa wata dariya mai tattare da bakin ciki da kuka, tana hawaye tace ” A lokacin da za’amin auran nan kunce in na amince zaku kula da Goggona, sannan bayan na amince yanzu kunce kuma gaba daya ma in canza mahaifiyar datai wahala akai……..” Marin da aka kifa mata ne yasa tai shiru, Inna tace ” dan kinyi aure a gidan nan ne yasa kika fara tunanin yin jayayya dani? Ina magana kina magana?” Haryasa hannu zai bude kofar saboda ransa ya baci sai kuma naga ya tsaya, hannunsa naga ya dunkule sannan a ja baya daga jikin kofar, cikin takaici. Saboda nine kenan? Saboda iyayena sun nemi auranta yasa har ake neman sata yin haka. Labansa ya ciza sannan ya bude dakinsa ya shiga, ya rufo kofar da karfinsa na gaske. Wanda yasa sukaji kara, Inna ta kalli Jalila tace “mijin naki ne?” Jalila tana hawaye ta daga kai, Inna ta tabe baki a ranta tace hauka yake muraran irin wannan buga kofa haka? Ai kanaji kasan na marasa hankaline. Maida kallanta tai kan Jalila tace “shawara ya rage naki, inhar kinasan kiga mahaifiyarki kiyi abinda na saki, in kuma bakyaso ki hakura da ganinta ne wannan ya rage naki.” Ta kalli Mumy tace “tashi mu tafi dan ba’a dadewa gidan surukai.” Jalila tana kallansu suka mike gaba daya inbanda hawaye ba abinda takeyi, Inna ta fita daga dakin ta juyo tace “bazaki rakamu ba?” Jalila ta kallesu, yanda Inna take kallanta ne yasa ta mike ta fito falon. Tana fitowa shima yana fitowa daga dakin, rufo kofa, fuskarnan tasa a daure kallo daya ya musu ya dauke kansa, yi yai kamar bai ga mutane a gun ba ya wucesu ya sauka. Inna ta kalleshi sannan ta kalli Jalila bayan ya sauka tace “shine?” Jalila ta daga kai, Mumy tace “amma yana ganinmi kamar yaga kashi?” Inna tace “ki mai uzuri……” Sai kuma tai shiru, kallanta Jalila tai badai sunsan matsalarshi ba? Ai a take tai tunani, haba itadai ta tabbatar da wani abun daga sanda ta iso gidan nan, ta tabbatar Bazasu taba ajiye Safeena su dauketa ba. Yanda take kallan Mumy ne yasa Inna tace” me kikeyi? Na dauka cewa nai muje ki rakamu.” Zubewa akan gwiwowinta tai tana hawaye tace “Inna dan Allah na rokeki kiyi hakuri, zanyi komai amma dan Allah banda gurbin mahaifiyata.” Inna ta kalli hanyar sama tace” me kike yi hakan? Salan wani ya ganki yace cutar dake mukeyi?” Jalila ta mike tana matse kwalla, Inna tace “muje.” Haka suka sauko kasa tana bayansu. Ummy ta fito daga daki tace “har zaku tafi?” Mumy tace “eh wlh.” Ummy ta kalli Jalila tace “Jalila ana kukan rabuwa ne?” Jalila ta sunkuyar dakai, Mumy tace ” Ga tanan mun barmuku amana.” Amana? Abinda ya darsuna zuciyar Jalila kenan, su basu riketa amana ba shine suke bada ita wai amana? Ummy taji tace “ai Jalila diyace agurina, insha Allahu yanda zan rike dan cikina haka zan riketa.” Inna tace “mun gode sosai, Allah yabar zumunci, amma Taura fa?” Ummy tace ” yana Abuja yau dai muke sa ransa.” Sannan ta kalli Jalila tace “ki daina kuka dan Allah.” Jalila ta daga kai tana share hawayenta. Haka suka fito Ummy ta mikoma Jalila leda tace ” ki basu.” Jalila ta amsa tama Ummy godiya. Sai da suka shiga mota sannan tamikama Mumy tace “tace gashi inji Ummy.” Inna ta kalleta tace ” ki tabbatar kinji abinda na fada miki.” Jalila batace komai ba har motarsu, ta fita daga gidan, wasu zafafan hawaye ne suka zubo mata. Komawa cikin gida tai, wucewa dakinta tai kawai ta zauna tana kuka. Ummy ce ta shigo dakin, itakanta Ummy tun jiya hankalinta ba’a kwance yake ba ta nemi number Abba harta gaji, yanzu kuwa bama ta shiga gaba daya.2 Hannun Jalila ta kamo, tace “ya isa haka nan, insha Allahu bazakiyi dana sanin auranki cikin zuri’ata ba, Hassan na cikin wani yanayi ne sai dai ba haka Allah ya halliceshi ba, lalurace ta afkomai shekarun baya da suka wuce wanda muke addu’ar neman mai lafiya, da taimakon ki.” Jalila ta kalli Ummy, Ummy tai murmushi tace “jiya a kasa kika kwana?” Jalila cikin mamaki tace “ya akai ki….” sai kuma tai shiru, Ummy tai murmushi tace ” ya miki magana?” Jalila tace “hmm amma baifi sau hudu ba.” Tace “Ba laifi dan banyi tunanin ma zai kula ki ba kwata kwata.” Shiru tadanyi kafin ta kara riko hannun Jalila cikin murya mai rauni da tausayi tace “Jalila ki taimakeni.” Jalila ta kalleta jiki a sanyaye, tace “Jalila ki taimakeni gun ceto Hassan daga halin da yake ciki.” Jalila tai shiru sai kallanta da takeyi, Ummy tace “Kiyi hakuri da duk abinda zai miki ma tabbatar wata rana zakiyi mamakin shi” Jalila ta share kwallarta tace “Insha Allahu Ummy.” Ummy ta jinjina kai cikin jin dadi tace “Jalila nagode sosai, sannan karki bari ya wulakantaki, inya miki ba daidai ba ki fito ki fadamai, hakan ne zaisa ya saki jiki dake.” Jalila tai shiru, Ummy tace “Sannan inaso duk wani abu da kikeso ko ya dameki ki sanar dani, inaso mu zama daya ni dake, yanda na dauki Ameera haka na daukeki, kema inaso ki daukeni a matsayin mahaifiyarki….” Kalmar mahaifiya itace ta sa jikinta yin sanyi, a ranta tace Goggo kina ina???? Ummy ce ta mike sannan tace ” bari naje lokacin abincin rana yayi.” Jalila ta mike da sauri tace “bari inyi abincin Ummy.” Ummy tace “ah hb? Daga yin aure sai girki?” Jalila tace ” dan Allah ki barni nayi.” Ummy tace “muje muyi tare to, dan ina tunani Abbansu yau zai dawo.” Haka suka sauko kasa abin sha’awa, sai dai zuciyar Jalila ciki take da tunani wanda take kokarin nemo ma kanta mafita.” Abba suna shigowa garin kano yacema driver dinsa su wuce gidansa na governor road, driver din yayi mamaki dan Abba ya dade bai ko leka gidan ba, ko yazoma sai dai yai abu minti kadan ya fita. Yau kam suna isa ya shiga ciki ya kwanta a falonsa, hannunsa yasa asaman goshinsa yana tunani.+ Mamman driver ya juya ya fita da mota, yana kokarin shiga layinsu shi kuma lokacin ne Hassan ya fito shima. Ganin motar Abba yasa ya danyi parking, Maman ya bude motar da sauri ya matso jikin window din da yake zaune, Hassan ya zuge glass din sannan ya kalleshi. Mamman ya gaisheshi, bai amsa ba yace “Ina Abban?” Mamman yai shiru kafin yace “Yallabai na gidansa na governor road.” Kallan mamaki yamai yace ” me yake acan?” Yace “ban sani ba wlh, kawai cewa yai in kaishe.” Hassan ya tada motarsa yai gaba, direct gidan ya wuce ya shiga ciki. Kofar falon yai knocking sannan ya tura ta, Abba me kwanc akan doguwar kujerar dake falon, shima Abban jin motsin kofa yasa ya bude idanunsa. Hassan na tsaye a jikin kofar yana kallansa, Abba ya kalli Hassan sannan ya mike zaune yace “Hassan?” Hassan yana daga jikin kofar yace “me kake anan daga shigowarka gari?” Abba yai ajiyar zuciya yace “kawai!” Hassan yace “kawai? Taya Abba zaka taho nan bayan kasan Ummy dole tana jiranka? Ai tunda kake tafiya koda bana kula na tabbatar baka taba yin haka ba.” Abba ya mike tsaye ya tako zuwa inda yake yasa hannu daya kan kafadarsa yace ” kai fa?” Hassan yace “me?” Abbba yace “naji ni wannan karan ne kadai na tabayin haka kaifa? Kana kula da taka matar?” Hassan kallan mamaki yamai fuskarshi cike da mamaki yace ” ban gane ba? Abba ya muna maganar Ummy kana zancen wata?” Abba yai murmushi yace “kai namiji ne kafin d’a na yanda nima nake namiji kafin na zama mahaifinka.” Yanzu kam kallan zargi Hassan yama Abbansa yace “mekake nufi Abba?” Abba ya girgiza kai yace “nima bansani ba, kawai dai sanar dakai nai abinda nakeji.” Hassan ya kalleshi baice komai ba, kawai ya juya zai fita. Abba yace “sai ka maidani gida koba d’aukata kazoyi ka kaima mahaifiyarka ba? Dama kai a rayuwarka damuwarta ita kadaice abinda ka sani.” Hassan ya kalleshi kawai sannan ya juya ya shiga motar sa, zama yai yana tunanin kalaman Abba, me yake nufi? Fada sukai da Ummy? Shifa a duniya ran Ummynsa ne kadai bayasan yaga ya baci. Yana zaune sai ga Abban ya bude motarsa ya shiga gefensa. Hassan baice komai ba yaja suka fara tafiya………. Su Ummy na kitchen itada Jalila suna aiki, Ameera ta tafi gidan Aunty Nana kai sako, Ummy sai mamakin kwarewa da Jalila tai a gunki take, wanda haryasa tace mata “Jalila nayi mamakin yanda kika iya girki a shekarunki.” Jalila tai murmushi tace “ai kullum ni nake abinci a gida, daga na safe, na rana har na dare.” Ummy tace “makarantar fa?” Jalila tace “ina zuwa.” Ummy ta kalleta cikin jindadi sannan suka cigaba, suna cikin aikin sukaji muryar Abba yace “Amarya da kanki?” A tare suka juyo, Ummy ta kalleshi cikin kulawa sannan ta taho inda yake, Jalila kuwa sunkuyar dakai cikin kunya. Ummy ta karaso inda yake tace “Sannu da zuwa.” Murmushi ya mata yace ” yauwa.” Sannan ya juya, Jalila ce ta juyo, hada ido sukai da Hassan wanda batama san tare suka shigo ba sai yanzu, kallanta yai sannan ya dauke idonsa daga kanta. Itakuwa kura mai ido tai zuciyarta na raya mata meke damunshi? A haka dai gashi garau sai ta tuno. Abinda yai jiya, tace da daddare kuma sai ya rikide? Ko inyai bacci? Alamar kamawar dataji ne yasa tai saurin kallan tukunyar sannan ta cigaba da girkinta. Shikuwa Hassan sai dayaje zai hau sama sannan ya sake juyowa ya kalleta, ya suka kare da mutanen dazu? Tsaki yai sannan yace “meye damuwata?” Sannan yahau sama. Dakinsa ya shiga kawai ya zauna akan gado. Ummy kuwa a daki ta kalli Abba da ya zauna akan kujera tace “gajiya ko?” Ya kalleta yace “a gajiye nake tilis naje gidana na governor road in huta danki ya taso ni.” Tace “kamar ya?” Ya mike yana balle botiran jikin rigarsa yana cewa ” bari nai wanka.” Rigarsa ya cire ya shiga toilet da kallo ta bishi, danta? Hassan kenan dan Sagir tare suka fita da Ameera. A iya saninta Hassan kuma kamar abin da wuya, mikewa tai ta fito ta nufi kitchen. Jalila ta kalla tace “ko zaki kai mai abincin safe? Banaji ya karya.” Jalila tace “Ummy azahar fa?” Ummy tai murmushi tace “haka yake, ni kaina ina mamakin yanda yake tauyewa cikinsa hakkinsa, kamar bai san darajarsa ba.” Jalila tai shiru tana tunanin Goggonta wacce kullum take mata fada akan cin abinci, ashe ba ita kadai bace ga namijima da girmansa ana fama. Ummy ta kalleta tace “me kike tunani?” Jalila ta girgiza kai sannan ta nufi sama, a hankali ta tura kofar, sannan ta leko kanta. Yana tsaye jikin madubi daga shi sai dan towel, da sauri ta maida kofar ta rufe shi kuwa yana tsaye yana kallanta. Tana rufewa tai ajiyar zuciya tare dasa hannunta akan kirjinta tana maida numfashi, meye hakan? Taya katan namiji zai hau cire kaya haka? Kara tura kofar tai tana tunanin ai dole ya sa riga tunda dai yaga tana neman shigowa, gani tai ba kowa a dakin, baki ta tabe sannan ta shiga ciki tana cewa dole ai yaji kunya ya shige toilet. Motsi taji a bayanta ta juya da sauru bayanta, yanda yake dazu haka yake yana neman abu a cikin drawer, idanu ta zaro sannan tasa hannu ta rufe idanta da sauri. Shaver zai dauka yana ganinta ya dauka yazo ya wuce kamar baisan da mutum agun ba, toilet ya bude ya shiga. Jin karar rufe kofa yasa ta bude idanunta a hankali sannan ta kara sakin ajiyar zuciya tana cewa “Woah! Kamar bai ganni ba?” Kallan kofar toilet din tai sannan ta fito, ta sanarma Ummy, suna kammala girkin Ummy ta zuba a kula ta bata tace “ki hau muku dashi sama, Jalila ta dauka ta hau sama, itakam batasan hawa saman nan kwata kwata.” Tana shiga ta taraddashi yana ninke sallaya, ya ajiye sannan ya kwanta tare da dauko littafin da yake karantawa. Abincin a ajiye ta dibi nata dan kadan ta fito falo. Yau gidan shiru kamar ba mutane, Ameera da Sagir basa nan, Ummy na daki ita da Abba shima waccan yana daki, sai ita kadai a falo. Ummy kam ta kula mijin nata bayasan dogon magana, da alama akwai abinda ke damunsa, haka ta fito daga dakin ta zauna a falo itama. Da daddare kuwa banda juyi ba abinda takeyi, abinda ya faru dazu da safe shine ke damunta, taya zasu nemi ita da kanta ta wulakanta Goggonta? Matar da batasan so ba a rayuwarta? Matar da duk duniya ita kadai ke santa? Ita kadai ta damu da ita? Ita kadai ce gatanta? Hawaye ne ya shiga zubo mata, wajen karfe daya ta mike ta zauna kawaj ta fara kuka, shikam duk abinda takeyi yan jinta, dan shi sam baya iya bacci in ana mutsu mutsu a kusa dashi. Jin yanda take kuka ne yasa shi mikewa zaune, fitilar gefen gado dake dakin ya kunna. Da sauri ta koma ta kwanta tana share hawayenta. Kallanta yai yace ” inkinsan kuka zakiyi ki fitarmin daga daki, dan banga dalilin da zaisa a hanani bacci a daki na ba.”2 Jalila ta dan turo baki wasu hawayen suka zubo mata, Hassan ya kashe fitilar sannan ya kwanta, mikewa tai tana neman fita, dayake dakin duhu ai kuwa ta bugu da jikin gado. Da karfi tace wayyo! Iska ya firzar sannan ya zauna ya kara kunna fitilar dakin, yace “meye…….” Ganin yanda ta rike kafarta ne tana kuka yasa ya kalli gun, karamin dan yatsanta ta buga gashi hargun ya daga yana jini sosai. Dama me neman kuka, ganin ya taso inda take kawai ta kara sa kuka. Bai kulata ba sai hannunta daya riko ya zaunar akan gado, tissue ya warwaro dayawa ya rufe gun ciwon idanunsa suka canza zuwa jaa. Daga bayama gani tai ya runtse idan nasa kamar bayasan ganin jinin. Kallanta yai sannan yace ” rike.” Rikewa tai tana kuka, mikewa yai ya juya ma inda take baya, sannan ya dan dafa kansa. Kwalin tissue din ya miko mata ta amsa tana kuka, yace “will u please keep quiet?” Hadiye kukan nata tai tana kallan bayansa. Juyowa yai inda take cikin zafin rai yace “are u a fool?” Shiru tai tana kallansa, hannu yasa ya dagota ya rike kafadunta da karfinsa ya matso cikin zafin rai yace ” me yasa sanda suke miki zancen banza baki basu amsa ba? Me yasa sanda suke neman sa ki abinda zai saki kuka baki sanar dasu abinda ke ranki ba? Nine marainin wayanki? Zakizo ki sani a gaba kina min kukan banza?” Idanun Jalila ne suka firfito gabanta sai faduwa yake da sauri da sauri saboda tsananin tsoronsa da ya shegeta, bare yanda ya matso daf da ita haka ba namijim daya taba mata haka, ga idanunsa sun canza, ga yanda yake mata fada, jitai gaba daya ta rasa abin cewa. Ya turata kan gado cikin takaici yace ” kinsan ma’anar uwa kuwa? Ko dabansan meye hadinki dasu ba, kada ki kuskura ki dauki uwa a bakin wasa, no matter how they threatened u , don’t u ever try that.” Ya juya zaiyi falo, gaba daya zuwan yarinyarnan yasa ana sashi magana mai tsayi haka, wanda rabon daya yita har ya manta.1 Harya kai kofa tana kuka tace ” kana tunanin nima asan raina akemin haka?” Tsayawa yai amma bai juyo ba, tana kuka tace “batada lafiya, batada lafiya sosai Yaya!” Ta kara sa kuka, juyowa yai ya kalleta, kuka take sosai wanda haryasa hannu zai bude kofar yasa ya fasa. Komawa yai ya zauna a kan gadon sannan yace “zan kwanta.” Mikewa tai ta sa tissue din a dustbin sannan ta koma kasa ta kwanta tana share hawaye. Kashe wutar yai dakin yai duhu sai sanyi dake kara ratsa dakin, dukansu idanunsu biyo sai juyi kawai da takeyi. Shikuma yana kwance rigingine. Can ta daure tace “yaya ya akai ka sani?” Bai kula ta ba hakan yasa tai shiru, can tace ” bansan yazanyi ba, Goggo na sun dauketa daga asibitin da aka kaita, bansan abinda zasu aikata ba inhar banyi abinda suke so ba.” Yanzun ma bai kula ta ba, sai dai a yanzu ya fahimci da mahaifiyarta ake sata abinda akaso, wanda yauce rana ta farko tun bayan faruwar abinda ya sameshi yauce rana ta farko daya fara tunanin yanasan jin dalilin abinda bai shafeshi ba, yanasan sanin me zata aikata akan abinda baishafeshi ba. Wajen sallar asuba tana bacci taji kakkari, idanunta ta bude a tsorace sannan ta mike tana neman fitilar jikin gado dan ta kunna, ji tai ta fada kan mutum a rikice tasa hanny ta taba shi. Kan fuskarsa ta taba, hannu yasa ya riko hannunta da karfi yana wani abu. Idanunta ne suka firfito saboda tsananin tsoro jikinta ya fara kyarma, da kyar takai dayan hannun nata ta samu ta kunna fitilar.+ Yanda yake yi da jikinsa ne yasa ma ta kasa kokarin kwace hannunta, gaba daya tsoro ya gama kasheta. Tai tsuru tsuru da ido tana tabashi da dayan hannu tana cewa “Yaya! Yaya!” Hannunta ya saki ya sa a wuyansa kamar me shirin shake kansa, Jalila cikin tsoro ta rike hannu tana kiransa. Bakinta rawa kawai yake gun kiran sunan nasa, idanunta sun ciciko batama san sanda hawaye ya fara zubomata ba saboda tsoro. Yau abin yafi na jiya shiyasa hankalinta ya tashi gashi su biyu a daki, kuka kawai take tana jinigashi. Sai dan karatun data iya datake yi, idanunta ta rufe kawai dan batasan ganinsa a haka gaba daya ya canz kamar mahaukaci ko mai farfadiya ko mai aljanu. Kuka take tana kiransa wani sain tai karatun idanunta gam, har batasan abin ya lafa ya bude idanunsa ba. Addu’oi yai sannan ya kalleta, tausayinta ne ya kamashi, yarinya karama a maidata mai jinya? Hannunta da take tabashi dan ya tashi ya rike. Idanunta ta bude a hankali a tsorace, ta kalleshi. Yace “kukan meye hakan?” Bakinta na rawa tace “Yaya?” Yace “mutuwa akai?” Kai ta girgiza, yace “to meye hakan?”1 Tana kuka tace “bakomai.” Yace ” meyasa baki nemi sanin wanda za’a baki ba?” Tace “kamar ya?” Yace “bakida ‘yanci ne? Ko tsabar biyayya ce tasa? Ni naji inada lalura wanda ban isa in zabi matar da nake so ba, kefa?” Tace “nima.” Nima? Ta share hawayenta da dayan hannu “ni Goggo batamasan nayi aure ba.” Abinda ta fada kenan a ranta batasan a fili tai ba sai jitai yace ” Goggo?” Kallansa tai sannan ta kakaro murmushi tace ” hannuna.” Sakar mata hannu yai sannan ya mike zaune yana kallan agoggo, mikewa yai ya nufi toilet ba tare da ya sake kallanta ba. Kallansa tai a ranta tace ” ikon Allah, wato wani sa’in sai kaga Allah ya baka komai sai ya hanaka wani abun, kalli yanda ake sanshi a gidan nan, batasan ba kodan bashi da lafiya ne amma kaf gidan nan yanda suke mai sai kasan sanda sukemai daban ne, wanda ko kwana daya ko wuni mutum yai dasu zai fahimci hakan. Mikewa tai bayan ya fito tai alwala, kafin ta fito ya tada sallar ta fita falo tai sallarta sannan ta kwanta akan kujera, yau kam baccin bai dauketa da wuri ba tayi luff akan kujera tana jin kira’ar qur’ani mai dadin gaske wanda ta tabbatar radio ne yake aiki, tanasan taga tana karatun qur’ani ko ba kamar haka ba amma dai taga ta iyashi, in sultan na karatu a gida ji take inama itace. A haka har bacci yai gaba da ita. Hassan kam ya dade akan sallaya kafin ya kwanta. *********** _Bayan kwana hudu._ Goggo ce ta kalli lantana tace “Lantana Jalila bataso ba da ina barci? Lantana tace “eh.” Goggo tai shiru “yau kwanana hudu kenan a sabon asibitin nan amma banga Jalila ba wanda na tabbata indai har da lafiyarta bazata taba iya kwanakin nan haka batazo ba, sannan ba wanda take gani abinci kawai suke aiko mata, bayan sanda zasu canza mata asibiti sai da suka sanar da ita Jalila nacan ma tana jiranta. Meke faruwa? Anya ba wani abun sukama Jalilanta ba kuwa? Wannan tunanin ne yasa hankalinta ya tashi, har jininta ya sake hawa, matar da ake tunanin sallamarta nanda kwana biyu. Goggo kira kawai take a kira mata Jalila. ******* Itakam Jalila kalaman Hassan sune sukai ta mata yawo. Gashi hankalinta ya kasa nutsuwa saboda rashin Goggonta, duk da yanda Ummy ke iya kokarinta na ganin Jalila ta saki jiki da gidan. Sagir kam baifiya ma zama ba saboda hankalinsa tashi yake inyaga Jalila. A hankali ta turo kofar, yana kwance a kan gado yana karatu, ta rasa mai yasa ita ko irin wayarnan taga yanayi ko yana dannata bayayi. Shiga cikin dakin tai ta tsaya tana dan wasa da hannunta. Bai kalleta ba bakuma tasa ran zai kalleta din, hakan yasa ta matso kusa dashi kadan. Nan ma bai kalleta ba, daurewa tai tace “Umm Yaya!” Bai kalleta ba yace “menene?” Tana wasa da hannunta ta rasa mai zatace, ganin batada niyyar magana yasa ya cigaba da abinda yakeyi. Jalila kam ganin tsayuwar bamai karewa bace gashi ita tasan zata iya fadama Sagir sai dai ta ina zata fara kebewa dashi ta sanar mai? Sannan mai zaiyi tunani? Gwara dai Hassan din tunda koma menene at least yasan wani abin na daga rayuwarta. Ganin haka ma sai ya mike yadau waya da key din motarsa yana neman fita. Cikin hanzari ta riko gefen rigarsa, tsayawa yai sannan ya juyo ya kalleta sannan ya kalli rigar tasa inda ta rike. Tace “Hmm Yaya magana zamuyi.” Da kai ya mata alama da yanaji, ta sakeshi sannan ta tsaya. Yace ” in baka san me zakice ba ni zanyi gaba.” Jalila tana gani ya juya ta kara riko rigarsa da sauri, kallanta ya juyo yai sai dai yanzu yanayinsa yadan canza yace ” meke nan?” Tace “Yaya!” Matsowa ya fara yi tana matsawa baya, tsoro ya fara ratsa mata har sai da sukaje jikin gado ta fada kan gadon, gani tai ya rufo kanta, tsoro da fargaba suka kamata, idanunta suka firfito ganin namiji akanta haka. Idanunta ta runtse gam cikin tsoro, can taji shiru, a hankali ta bude idanunta a tsaye ta ganshi yace “2minute na baki.” Tace “Yaya……” Yace “will you stop calling me?” Magana nace kiyi ba kirana ba. Ta daure tace “Yaya bansan ya zanyi ba.” Ya kalleta alamar me take nufi. Tace “maganar Goggo.” Yace “to menene nawa a ciki?” Tace “naam?” Yace “menene nawa a ciki da kike fadamin?” Shiru tai dan batasan me zata ce ba, agoggon hannunsa ya kalla yace “minutes din da na baki sun cika.” Ya juya ya fita tana kallansa, ajiyar zuciya tai tace “Jalila u are really a fool.” Shikam yana fita ya sauka kasa zai fita, Ummy ce ta leko daga daki tace “Hassan?” Kallanta yai sannan ya matso yanasan jin menene, ta kalleshi tace “ina zaka kuma?” Yace ” fita.” Shiru tai alamar damuwa wanda yasa yace “menene?” Tace “Hassan na rasa meke damun Abbanka.” Kallanta yai cikin kulawa, sai dai baisan ta ina zai fara jin matsalarta ba, yace ” Me yayi?” Ta girgiza kai tace “bakomai, jeka kawai amma dan Allah ka dinga zama a gida kaga Ameera tunda taje gun Aina’u bata dawo ba, Sagir kuma na rasa me yakeyi yanzu sam ya rage zaman gida, ni kuma kasan dole tadingajin nauyi na, ka taimaka ka dinga zama ko da ba lalai ka yarda kuyi hira ba at least dai zataji motsinka a kusa da ita.” Kallanta yai kawai bai amsa ba sai cewa dayai “Abban me ya miki?” Tace “me zaimin kuwa? Kawai dai naga ne kamar akwai abinda ke damunsa” dan tasan intacemai ya canza mata gaba daya, ya daina zaman gida, ya daina zama suyi hirar business data duniya lalai tafi kowa sanin halin Hassan, abin ne ke cinta yake damunta shiyasa ma tamai magana. Kallansa tai tace “sai ka dawo.” Tai saurin komawa daki, haryakai jikin kofa sai naga ya juyo ya kalli sama sai kuma ya fita. Jalila ta zauna a kasa ta baza tagumi, takaicin kanta duk ya isheta, sai yamma ta sauko. Kofar Ummy taje ta kwankwasa, Ummy ta fito sanye da hijab da alama sallah ta idar. Jalila tace “Ummy me za’a dafa?” Ummy tai murmushi tace “dauko hijab dinki mu fita cefani. Jalila cikin mamaki tace “Cefane Ummy?” Gani tai tunda tazo gidan bata taba gani anje cefane ba masu aiki ne ke siyowa. Ummy tacemata yi sauri. Jalila ta juya zuwa sama, hijab dinta ta dauko sannan ta sauko. Ummy ta daga waya tace “Dan Ummy ka iso?” Yace eh, nan suka fita. Sagir na tsaye jikin mota yana hangosu ya fito ya bude musu baya yanama Ummy salute. Ta harareshi tace ” Officer ka iso?” Yace “barka da isowa.” Jalila tai dariya tana kallansu abin sha’awa, bata taba gani mace mai saukin kai kamar Ummy ba, tasan itakan Goggonta kadai ta sani sai yanzu dataga Ummy. Suka shiga baya dukansu, Ummy tace “Driver mu fara zuwa Wellcare. Nan suka tafi ahanya sai hira sukeyi, Jalila kam sai dai tai murmushi sai in an tambayeta tace eh ko a’a. Ummy kam ta fito ne dan ta debe musu kewa da ita da Jalila, dan tasan Jalila na bukatar kulawa, ita kuma saboda gudun tunani da zargi yasa take neman abinda zai debe mata kewa. Haka sukaje sukai siyayya sosai, sannan suka biya shagon wayoyi, Ummy da kanta ta zaboma Jalila waya irin ta hannunta Sumsung ce Note 9. Jalila kam gaba daya ta rasa me zatace, dan itakam batasan ta inda zata fara magana ba. Sagir kam dadi yakeji ganin fuskar Jalila na dauke da murmushin da yake har zuciyarta bawai na iya baki ba. Haka suka isa gida sannan sukai abinci ta dau nasu ta hau sama, yau kam zuciyarta ta ragu da damuwa, sannan ta kara samun karfin gwiwar yima Hassan magana. Bayan isha’i ya dawo ta jawo mai abinci kusa dashi, Hassan ya kalleta yace “nasha yogurt, later.” Jalila ta dauke tasa a gefe, zama tai a kan gadon daga inda kafafunsa suke can karshen gado, ta mikomai wayarta. Kallanta yai sannan ya amsa, yace “na meye?” Tace “Ummy ce ta saimin.” Ya juyata sannan ya mika mata yace “to.” Tace “bakasa number ka ba.” Yace “me zakiyi da ita?” Tace ” In wani abin ya taso.” Ya kalleta yace “kamar me?” Wayarta ta amsa tace “shekenan kawai kace dai bakasan sawa.”2 Kallanta yai yace ” kawo dai.” Ta mika mai tana dan tabe baki kadan kanta a kasa, ya amsa yace “in zaki harareni ko murgudamin baki, ko tabemin baki ki tabbatar kinyishi ina kallo dan ko ban kallekiba ina sanin inkinyi hakan.1 Jalila ta kalleshi tace “ni banyi komai ba.” Sannan sukai dan shiru, can tace “Yaya me zanyi in taimaki Goggona?” Kallanta yai yace “zancen dazu ne?” Tace “eh, na gane dazu na fara ma magana ne kamar i am hopeless bansan me zanyi ba, bani kuma da plan.” Littafin sa ya dauka baice komai ba, saukowa tai kasa ta tsugunna a kusa dashi tace “Yaya dan Allah ka taimakeni.”6 Littafin ya ajiye yana kallanta………..