JIDDATULKHAIR CHAPTER 56 BY KHALISAT HAIDAR

Ummi ta kalli Umma tace “Ahmad ai xai gane gidan shi ko?” Umma tace “Anya kuwa? Amma dai bari in kirasa in tambayesa” Daukar wayarta tayi ta wuce daki, bayan few minutes ta fito tace “Ai kam bai sani ba wai shi ma” Ummi dai kallonta kawai take, Aunty tace “Tunda duk basu sani ba ai sai mu wuce gida kawai a nemi wani solution din, don baxa mu kama hanyar xuwa inda bamu sani ba gaskiya,” Umma tace “Ai ko dai” Haka nan su Ummi suka koma gida, Aunty farin ciki fal xuciyarta, ai ko ita kadai ta isa ta hana xuwa gidansu Jiddah…. Hajja ce xaune parlon Abba ta dafe kai, cike da bakin ciki tace “Huhuhu… mutane dai yanxu tsoron Allah wuya yake masu ni Dije, da kyar al’ummar yanxu ke tsoron Allah wllh, yo banda rashin tsoron Allah ba a san gidan Aliyun bane da baxa a je a tisa keyarsa ya kai mu gun dangin yarinyar ba? Ko kuna da wata manufa da kuke boyewa a ranku ne ban sani ba, ni dai wllh ban ta6a sanin Masar rahama bace sai da na baro can, wllh da can ne duk haka baxai dinga faruwa ba, yo ina hakan xai faru kowa ya tashi ya girma da tsoron Allahnsa” Abba yace “Yanxu ya kike so ayi Hajja, ba fa sauri ake wannan lamarin ba…” Hajja ta dakatar da shi a fusace tace “Aa wllh sauri nake, kune dai baku sani ba, yanda xa ayi yanxu kuma shine a tashi a tafi gidan wancan mutumi Aliyu, idan kuma duk baxa ku ba, ni da kai na sai in dau gyale in je in dau yarinyar mu tafi gidan Aliyun in sa shi gaba ya kai ni unguwar tunda shi ya san asalinta” Abba yace “To gaskiya idan haka xaki dinga axalxalan lamarin nan ni Hajja xan cire hannuna, sai shi Mai martaban ya taho da kansa…” Hajja ta runtse ido tace “Qul Usman, kar ka sake fadin haka wani sai yace bakin ciki kake wllh, nima don na kai xuciya nesa ne da haka xance wllh, ba fa wani yasa gantalallan d’an ka ya saketa ba Usman, bakin ciki kake ma d’an yayan naka ne? Aa to gaskiya har ka ban tsoro, da kaina xan tashi yanxu in shirya in tafi gidan Aliyun, ai ba bakona bane gidan, irin wannan lamarin ance maka ana bin sa da sanyi sanyi ne” Tana fadin haka ta mike ta fice daga parlon, sai da ta fara sa aka kai ta gidan Umma wai xa ta tafi gidan Aliyun tare da Jiddah, daga can shi kuma sai ya kai su hayin, Umma dake tsaye bayan kujera tace “Toh ai bata nan Hajja sun tafi Islamiyya, kuma ba ma gidan nan take ba yanxu tana gidan Ahmad ne” Hajja na kallonta daga sama har kasa tace “Waye kuma Ahmad, ana magana sai ki dinga wani sako Ahmad… Ita kuma ba sai ki kira makarantar kice a turota gida ba, ko su basu san uxuri bane” Umma tace “Hajja idan kin je can gidan Aliyun kuma Allah ya sa kin samesa…” Da sauri Hajja ta katse tace “Yana nan ba inda xai je ana hutun karshen mako, ke dai kiyi ta kanki ki fada abinda xaki fada in tashi…” Umma tace “Shkkn, sai ya kai ki har gidan tunda nasan baxai rasa sani ba, amma xancen a kirawo makaranta ace yarinya ta dawo a katse mata karatu bai taso ba balle ma ni bani da number shuwagabannin makarantar” Mikewa Hajja tayi ta nufi kofa murya can kasa tace “Aniyarki ta baki, mata kin narka kiba kina ta xuba ma mutane iko, yaushe xa a ga haka a Masar, ‘ya yan bakin ciki kawai… Daga ke har Uban Aliyun” sannan ta fita…. Daga sama har kasa Aneesah ke kallo Hajja bayan ta bude kofar, can ta ja gefe ta kauda kai tace “Sannu da xuwa” Banxa da ita Hajja tayi ta shige parlon kai tsaye ta tafi kan kujera ta xauna, Aneesah ta bi ta da wani shegen hararan tsana, ita dai kaf kaduna bayan Jiddah bata da wanda ta tsana kuma kamar Hajja, Hajja tace “Zo ki kira min mijinki ni wajensa na xo ba wajen wani ba, kuma sauri nake yi” Babu yabo babu Fallasa Aneesah tace “To ai baya nan Hajja, da kin kirasa kafin ki xo….” Ko rufe baki bata yi ba sai ga Abuturrab yana sakkowa, tsaye shi ma yyi a stairs din karshe ganin Hajja, Hajja ta kalli Aneesah tace “Kika ce baya nan?” Aneesah tace “Ohh ban ma san ya shigo ba, ni ina kitchen ne” Hajja ta ja tsaki ta mike tace “Mu je Aliyu, ba xama na xo yi ba…” Bai yi musu ba saboda Aneesah ya bi bayanta suka nufi kofa, Aneesah ta kirkiro murmushi tace “Toh baki sha ko ruwa ba Hajja, ga girki ma ya kusa nuna yanxu” Hajja tace “Aa wllh Alhmdlh, ai daga gida nake, kuma ni wajen jikana Aliyu na xo ba xama na xo yi ba dama” Daga haka ta fice Abuturrab ya bi bayanta, Da sauri Aneesah tace “My captain abincin fa?” Yyi mata alama da hannu yana xuwa, yana fita tayi wani murmushi ta xauna saman kujera ta dau chips dinta ta ci gaba da ci. Suna fita parking space Hajja tace “Kaga da kyau ai da muka fito tunda maganar sirri ne, baxan bar wata 6are can taji cikinmu ba, wai don rashin kunya tayin ruwa take min saboda in sha in tsuge da gudawa, kai hancinka baya jin karnin da parlon nan ke yi ne kamar an fasa danyen kwai, ko iyayenta basu mata irin turarurrukan wutan xamanin nan da naga ana yi ne, wllh fa kazama ce, da a Masar ne dole a raba wannan auren naku don guje maka wata cutar, toh dai ba ruwana da abinda bai shafeni ba, yanxu so nake mu hau mota ka kai ni gidansu yarinyar nan Jiddah, naji ance a hayin rigasa take koh?” Ya dinga kallon Hajja kafin yace “Ehh, me xaki je kiyi a can?” Tace “Aa wannan sirri na ne, yanxu muje ka kai ni, ni kadai ma na ishi inje gun iyayen nata… Waye kuma Usman ko Umaru” Abuturrab yace “Toh bari in dauko makullin motar” Tace “Toh yi maxa” tana tsaye har ya shiga ya fito rike da makullin motarsa, ya bude mata back seat ta shiga sannan ya shiga maxaunin driver ya tada motar, yayi horn aka bude masa gate ya fita, Hajja tace “Ina gamawa da Bashir kai ma xan samar maka xukekiya mai tsafta kamar Jiddah, ko don saboda ka tsira da lafiyarka” Ta madubi yake kallonta, tace “Kar fa a ga ina ta koda tsaftar wannan yarinya Jiddah wllh tana da shi ne, ni fa na sha gwada in ga ko tsaftar ganin ido take amma wllh ashe ba haka bane, kaga ko shara ka sa ta duk sai ta bi ta dage ko mai ta gani ta share fess, sannan idan ta gyara maka gado sumul sumul kamar kar ka bar kowa ya hau… Sannan naga ta san muhimmancin turaren wutan nan na xamani, tana gama gyaran daki take sakawa, bandaki kuwa da na sa ta ta wanke sai da nayi xaton 6atan hanya nayi da na shiga, wllh har wani talli yake gwanin ban sha’awa, abinda kanninka su Aisha da Nafisah basu da shi, Allah bai basu ba… Toh amma dai ban sani ba ko ganin ido take, idan ma shi din ne dai ai ta iya aikin duk da haka, wasu ma na ganin idon basu iya ba” Abuturrab dai bai ce mata komai ba, har suka shigo Hayi Hajja bata yi shiru ba surutu kawai take a motar, tafiya kawai yake har ya kusa karshen kwalta, ya ga wani d’an gida da aka rushe kusan rabinsa kasancewar a bakin titi yake, har sannan kuma ba a gyara gidan ba don kamar ma anyi abandoning din gidan ne, waje ya nema yayi parking yana kallon wajen rusasshen karamin gidan, can ya kalli Hajja ya nuna mata yace “Ga gidan can Hajja, naga kamar kuma ba kowa yanxu” Hajja ta sauko da sauri tace “Ba kowa kamar yaya? Wannan kuturum gidan ne gidansu Jiddar?” Yace “Ehh” karasawa tayi tana kallon wasu da suka kasa kayan siyarwansu a kasa tace “Ke yarinya ina masu rubabben gidan nan?” Yarinyar tace “Sun tashi tun da aka yi rusau” Hajja ta gwalo ido tace “Suka tashi suka je gidan uban wa?” Yarinyar ta buda hannu alamar bata sani ba, Hajja ta kalli Abuturrab da ya jingina da motarsa ya rungume hannu yana kallonta, tace “Kai kaji wai sun tashi ba a san inda suka je ba” Ya daga kafada shi dai bai ce komai ba, Hajja tace “Yau naga abinda ya isheni, yanxu babu wanda xa mu tambaya me d’an wayo a nan ko an san inda suka koma, ai dole baxa su wuce cikin hayin ba dai tunda dai naga alamar talaucin nasu ba na wasa bane…” Abuturrab yace “An ba ma wani gadinsu ne da xa su fadi inda suke? kinga kawai mu tafi Hajja, ranan nan ya fara damuna…” cike da masifa Hajja tace “In tafi ina banyi abinda ya kawo ni ba, ko wiwi kake sha ne?? kai da xaka tayani mu baxama neman inda iyayen nata suka koma tunda hayin ba wani girman a xo a gani yake da shi ba xaka wani ce mu tafi, wannan wace irin wiwi ka sha” Yace “Toh Allah ya baki sa’an ganinsu, kin xata hayi iyakarsa girman dakin ki ne ko gidan Alhaji Usman” Hajja tace “Atoh ni dama wani xagin naka ne ban saba da shi ba, har ubana dake kabari ka sha xagi kuma in hakura inyi shiru tun kan ma in tafi Masar…. Amma dai ni ba mahaukaciya bace baxan kulaka ba, kuma in sha Allahu ina nan har sai na hadu da iyayen nata sannan in tafi…” Hannu ya sa a aljihu ya ciro dubu daya ya sakala mata a katon jakarta yace “Duk ranan da Allah ya sa kika gansu sai ki dawo gida, ni dai na tafi, kin xata nan Masar din ki ne” Daga haka yayi shigewarsa mota ya wuce, Hajja ta gyara tsayuwa ta bi sa da kallo har yayi nisa. Da sallama Abuturrab ya shigo parlon Abbansa daren ranan, bai yarda ya kalli kowa a parlon ba ya nemi waje ya xauna a kasa sannan yayi gaisuwa, Abba yace “Why did u switch off ur phone?” Ya daga kai a karo na farko ya kalli Abba yace “Wayar ce ta samu matsala” Abba yace “But i told u xa ka raka mu Hayin Rigasa?” Yace “Abba ni ai ban san gidansu ba…” Abba yace “Sai ina ka sani?” Shiru Abuturrab yyi, Abba yace “Wajen mai anguwa?” Abuturrab ya sunkuyar da kansa yace “Eh” Abba yace “Toh gobe lahadi ka taho da safe ka kai mu wajensa” a hankali yace “Toh Abba, Allah ya kai mu” Abba yace “Ameen” D’aga kai yyi ya bi mutanen dake xaune parlon da kallo, sai kuma ya mike yayi sallama ya fita. Bangaren Ummi ya tafi, Ramlah ce kwance kan kujera a parlon Jiddah na xaune daga gefenta hannunta rike da wayar Ramlah tana game, duk suka daga kai suka kallesa, kallo daya ya ma Ramlah sannan ya xauna kan kujera, Jiddah dai bata sake kallonsa ba ta ci gaba da game dinta, Ramlah ta mike xaune da murmushi fuskarta tace “Sannu da xuwa Yaya” Yace “Yauwa” Tace “Ina yini?” Yace “Lafiya” Ta koma ta kwanta tace “Ya Aunty Aneesah?” Yace “Lafiya” Jiddah dai taki yarda ta dago, Yana kallon Ramlah yace “Idan akwai abinci a kitchen ki debo min” Ta kara tashi xaune tace “Toh” sannan ta mike tsaye ta nufi kofa, tunda Jiddah taga haka gabanta ya fara faduwa, tana ganin Ramlah ta bude kofa ta fita ita ma ta mike da sauri, amma tuni ya riga ta mikewa shi ma, tsaye tayi ta marairaice xuciyarta na bugawa tana kallonsa ya karasa gun kofar ya kulle, tana ganin haka ta shige bedroom din Ummi, saboda rudewa ta ma kasa sa makullin ya tura kofar ya shiga, durkushewa tayi kasa har hawaye ya kawo idonta tace “Don girman Allah kayi hakuri ka kyaleni, don Allah nace maka kar su Ummi su shigo….” Dukawa yayi yanda tayi ita ma ta rufe fuskarta da sauri jikinta na rawa tace “Wllh su Ummi xa su iya shigowa yanxu” Ta kusa minti daya a hakan ganin bata ji yace komai ba kuma bai ta6ata ba ta dago a hankali ta kallesa har sannan xuciyarta na bugawa, kallonta taga yana yi ganin yanda kirjinsa yake bugawa ta fara ja baya a hankali tace “Wllh su Ummi xa su iya shigowa” Ya fixgota yace “Aure kike so??” Ta xaro ido jikinta na 6ari tace “Ni bance haka ba” kana ganinta kasan a rude take, yace “Toh me yasa baki ce masu baki so ba?” Ta marairaice masa tace “Don Allah ka bar ni in fita kar su Ummi su shigo su ganmu mu kadai a nan?” Yace “Sai aka yi yaya idan sun ganmu?” Buda baki tayi tana kallonsa ta girgixa masa kai tace “Ai bai kamata ba…” Runtse ido tayi bayan ya kara fixgota har tana jiyo saukan breathing dinsa yace “A wajensu da wajenki ne bai kamata ba….” Rungumeta taji yayi, ita dai har sannan bata bude idonta ba, yanda kirjinsa ke bugawa haka ma nata, taji yayi kasa da murya yace “Tell them u are not interested, tell them….” Sai kuma yayi shiru, haka kawai taji jikinta yayi sanyi ta buda ido a hankali… babu abinda ta gani a lkcn sai ranan farko da ta fito daga cikin gidansu a hayi ta gansa tsaye kofar gidansu ya xo bata hakuri, a hankali ta daga kai ta ga idonsa a rufe suke, hannunta taji ya kamo cikin nasa, ta kalli hannun nasu sannan ta kara daga kai ta kallesa taga har sannan idonsa a rufe suke, lamo tayi jikinsa tana kara jin bugun xuciyarsa, bata san dalilin da ya sa taji hawaye ya taho mata ba, Saukan hawayen nata da ya ji a jikinsa ya sa ya bude idonsa ya kalli fuskarta suka hada ido, ganin hawayen da take yi ya hade goshinsa da nata murya can kasa yace “A ganin ki ina takura ki ko?” Ita dai bata ce komai ba har sannan hawaye na sauka idonta, a hankali yace “I want nothing but the best for u, ban shiga rayuwarki da wata manufa na daban da ya wuce taimakonki da inganta maki rayuwa ba, may be i was mistaken… a lot happened and are still happening…” Shiru yayi sai kuma ya rufe idonsa holding her more closer to him, calmly yace “I don’t know.. i was mistaken at many thoughts then… Things turn out the way they weren’t suppose to” Xaro ido Jiddah tayi jin an bude kofar parlor ta turasa da karfi, a tare suka mike tsaye, yana kallonta kafin yace komai ta bude kofa ta fice da sauri, Ramlah ce ta shigo parlon da abinci, Ramlah dai sae kallonta take ganinta a bedroom din Ummi, Jiddah ta nufi kofa ta fita don ta ki yarda su hada ido, Ramlah ta xauna kan kujera amma gaba daya kanta ya daure, sae kallon kofar dakin Ummi take, bayan few minutes dai ta mike ta nufi kofar ta bude a hankali, tsaye ta gansa kusa da window staring into space, Ramlah ta yi yake bayan sun hada ido tace “Dama na kawo maka abincin ne Yaya ashe kana ciki” Yace “Ohk” juyawa tayi ta fita, ta koma saman kujera ta xauna a hankali with different thought in her mind. Ummi ce ta shigo dakin tare da Aunty Nafisah, Ummi na kallonta tace “Ikon Allah baku tafi ba, Ahmad din bai xo ba kenan” Ramlah tace “Bae xo ba Ummi” Ummi tace “Abuturrab ya shigo nan ne halan” Ramlah ta nuna mata bedroom alamar yana ciki, Ummi tace “Naji kamshin turarensa ne” Aunty Nafisah tace “Nima magana xan yi kenan kika rigani wllh, idan xan koma tsaraban irin turaren kawai nake so a wajensa” Ummi tayi dariya tace “Lallai kam” a nan parlon duk suka xauna, bayan kusan minti goma Abuturrab ya fito daga dakin, Ummi dai bin sa kawai tayi da kallo, ya xauna saman kujera ya kara gaida Aunty Nafisah, ta amsa tana murmushi tace “Ina Aneesah?” Yace “Tana Lafiya Alhmdlh” Kallon agogon wrist dinsa dake nuna karfe tara saura yayi, ya mike yace “Sai da safe” Ramlah tace “Abincin fa yaya?” Ya kalli abincin da ta ajiye masa yace “Ohk, dare yyi I can’t take heavy food now” Ummi tace “Toh tunda hanya ce ya ajiye ku a gida mana, ko lallai sae Ahmad din ya xo” Ramlah tace “Toh shkkn bari mu bi sa” Abuturrab yyi ma Umminsa da Aunty Nafisah sae da safe ya nufi kofa ya fita, Aunty Nafisah tace “Na gansa wani iri, what does that mean?” Ummi ta ta6e baki tace “Ae a haka yake kullum” Aunty Nafisah tace “Haka kuma?” Ummi tace “Dama shi bai da fara’a ae, sannan ba a sanin cikinsa balle kasan me ya damesa” Aunty Nafisah tace “Toh Allah ya kyauta” Ramlah ta dau jakarta da na jiddah tayi ma su Ummi sai da safe, Ummi tace “Jiddar fa?” Ramlah tace “Kilan tana dakin Hajja, can xan je in duba…” Daga haka ta fita, Jiddah na xaune tayi jigum tana ta kallon Hajja dake ta surutanta, amma kusan duk bata ma san abinda Hajja ke cewa ba, Ramlah ta shigo tana kallonta tace “Taso mu tafi Jiddah” Hajja tace “Toh xa ku tafi, Ahmad din ya xo ne?” Ramlah tace “Ehh” Hajja ta tabe baki tace “Shi dai baya ba mutane komai, bakar rowa kamar uwarsa wllh” Ramlah dai ta juya ta fita, Jiddah na kallon Hajja a hankali tace “Sai da safe” Hajja tace “To Allah ya kai mu, ai ni ban san gidan Ramlah kike ba da na dinga kai maku xiyara a kai a kai tunda babu wani babba a gidan, Shi kuma Bashir idan ya aiko wayar xan amsa in ajiye maki, kuma babu shegen da ya isa yace baxa kiyi amfani da shi ba da rai na dai” Murmushi Jiddah ta kirkira ta mike ta fita, sai da ta fara xuwa tayi ma su Ummi sallama sannan ta fito, parlor ta tarda Ramlah na jiranta, ta amshi jakarta a hannun Ramlah sannan suka fita, har suka fita kofar gida babu wanda yace komai cikinsu, Jiddah ta dinga kallon motar da Ramlah ta nufa, lkci daya jikinta yyi sanyi sosai ta bi bayanta walking slowly, back seat Ramlah ta bude ta shiga, a hankali ta kai hannu gaban motar ta bude ta shiga sannan ta kulle, Abuturrab na kallon Ramlah yace “Ke gidanki xa a ajiye ki ai?” Ramlah ta kalli Jiddah da d’an confusion, sai kuma tace “Ohk to shkkn” Jiddah ta xaro ido tana kallonsa sai kuma ta kalli Ramlah, ya tada motar suka bar layin.