JIRWAYE CHAPTER 1
Www.bankinhausanovels.com.ng
(Khalifa Al-Haydar sunan da yake yawo a gari, sunan matashin mai kudin da dubban mutane zasu yi komai dan su ga fuskar shi.
Layla the sensational lady, idan har akwai aji a karuwanci Layla ta fara bude shi.
Labarin su ba kaman labari bane nayau da kullum, ba ko da yaushe kake yanke hukunci akan kaddarar mutane ba. JIRWAYE, akwai shi a cikin labarin kowa)
Wasu dankararrun motoci ne guda biyu masu qirar Mercedes Benz E class suka tsaya a yayin da wutar traffic yayi nuni da su tsaya. Daga gani dai zaka san wannan motoci na mutum daya ne dun harta plate number dinsu ma iri daya ne, kuma customised plate ne. Ganin sun tsaya, wata ýar yarinya me bara ta rugo da gudu ta tsaya Jikin window din daya daga cikin motocin tana roqo. Yarinyar dai kwata kwata ba zata wuci shekara goma sha biyar ba da haihuwa. Rigar ta duk a kode, idanunta duk sunyi yellow sun shige ciki alamar yunwa. Da ganin yarinyar nan dai zaka gane tana cikin wani irin yanayi na yunwa da rashi.+
“Oga please sir….. Help….. food…. hungry…. Baba ba lafia”. Ýar yarinyar nan ke ta fadi shikuma driver din motar yayi hanzarin sauke glass din window dinsa ya daka mata tsawa.
“Gerrout of here! You filthy rag. If your parents can’t cater for you why did they bring you into the world, pathetic beings…..”. Ya buda baki zai sake magana aka dakatar dashi.
“Alex keep shut”.
“But boss”.
“Keep shut I said!”. Glass din bayan motar aka sauke aka jeho kudi ýan dari biyar guda biyu aka yi maza aka rufe glass din kan ýar yarinyar nan ta yi godia. Rufe window din ke da wuya traffic light yayi nuni da su wuce Ita kuma ýar yarinya ta ruga da gudu inda Baban ta da kaninta suke a zaune a gefen titi.
Wannan motoci basu tsaya a ko ina ba sai babban filin jirgin murtala Mohammed. Motocin na isa wani qaton namiji me sanye da suit ya fito daga motar farko yaje ya buda kofar back seat din mota na biyu wa boss dinsu.
“Yanzu sai yaushe?”. Amir P.A ya tambaya.
“I’ll relate when i’m coming back to you in due course. Insha Allah ina gama business zan juyo amma sai na tsaya a Egypt tukun”. Ta fadi cikin wata murya me sanyi.
“Toh Allah kiyaye hanya”. Ba tare da ta ansa ba ta juya ta fara tafia. A hankula take takawa kamar tana jin tausayin qasa. Sanye take da riga doguwa me tsadar gaske, idanunta kuma ta rufe su da wasu dark shades masu kyaun gaske. A haka take takawa sannu a hankali har ta shiga jirgi wanda yike cike da passengers zuwa qasar Australia. Wata air hostess ce me kirki ta riqe mata ýar chain bag dinta har zuwa seat dinta.
“Nagode” tayi murmushi ta anshi jakarta sannan ta zauna. Gefen ta, a kujerar da ke kusa da ita wani namiji ne a zaune ya rufe huska da newspaper sai sharar barci yike ta yi. Abun ya dan bata haushi har ta ja ýar tsaki saboda mutumin ya zauna a seat inda ya kamata ta zauna, kusa da window. About 45 minutes da fara tafiyar su sai wannan bawan Allah ya tashi.
“Hello” ya buda baki yace mata ba tare da ya jira answer dinta ba ya miqe da niyyar zuwa ban daki. Ba da sanin sa ba ya dan taka ta ya wuce.1
“Malam koh dutsen da ka taka bata ji maka ciwo ba”. Ta mai magana cikin gatse.
“Dutse kuma baiwar Allah? Koh dai shigar ki jirgin sama na farko kenan”. Ya fadi tareda tuntsurewa da dariya abun ya qara bata mata rai ta ja tsaki shikuma ya wuce bathroom.
Kan ya dawo ta tashi ta koma seat inda yike a zaune. Shikam wannan bawan Allah na dawowa ya ce alambaran baya yarda sai ta tashi mai amma ta qi.
‘Zan koh yi maganin ki’ ya fadi cikin zuciya.
Wata air hostess tazo giftawa ya kirata yace dan Allah orange juice yike so ta bashi. Cike da murmushi taje ta kawo mai wannan orange juice din. Ya karbi cup din daga hannunta yana mata godia. Ya sha sip din farko yana kallon abokiyar tafiyar sa wadda take sanye da earpiece tana jin kade kade daga ipad. Ya Kalle ta ya saki murmushi yana mata tayin juice. Yamutsa huskanta tayi alamar bata so. Can Can ba da dadewa ba aikuwa wannan mutum ya kifar da gaba daya juice din a Jikin rigarta. Wani irin tsawa ta daka mai tare da mai wani kallo me cike da tsana shi kam koh a jikinsa dun ya ci ma burinsa na sa ta ta tashi mai daga seat inda yake so ya zauna. Tashin ta ke da wuya zuwa ban daki ta wanke jikinta ya tashi ya koma kujerar ya zauna ya dau ipad dinta ya kunna waqa yana ji. Tana dawowa ta Kalle sa wani irin baqin ciki ya rufe ta ta rasa abun da zata mai kawai sai ta kwashi kayan ta tace ita sai dai a bata wani seat. A hanzarin sanja gun zama ta mance da ipad dinta a gunsa.1
STORY CONTINUES BELOW
Ashe dai ta gudu bata tsira bane ba dun sabon seat inda aka bata wata mata ce zaune da danta me kimanin shekaru biyar. Yaron baya ji gashi da surutu, a haka dai ta haqura har jirgin su ya isa qasar Australia. Tana fita jirgi washroom din airport ta fara nufa dun ta sanja kayanta. Ta cire wannan doguwar rigar tayi sabuwar shigar ta a cikin wani jeans wanda ya matse ta da hoodie dinta me kalar toka. Daga nan ta ja akwatin ta zuwa arrivals lounge inda ta hango wani bature, dan dattijo dashi riqe da wata cardboard da aka rubuta sunanta a kai. Da hanzari ta nufi mutumin tana ýar fara’a.
“Hello mister”.
“Hello ma’am…….. Laylah?”.
“Yes”.
“Ohhh Simon Yates. Nice to meet you”. Ya fadi yana miqo mata hannu.
“Laylah”. Ta fadi tana murmushi. Da sauri ya anshi jakarta ya cigaba da ja har zuwa inda yayi parking din mota ya buda mata gidan baya ta shige. Shima ya shiga driver’s seat ya rufa kofa ya hau titi. Suna tafe yana dan taba mata hira.
“Your first visit to Australia?”.
“Yes sir”.
“Simon….. you can call me just that”. Mutumin dai daga ganinsa yana da kirki ga fara’a don haka Laylah taji lokaci daya ya kwanta mata a rai. Tana ta kallon kyaun garin Melbourne har suka isa wata hadaddiyar gini wanda daga duka alamu hotel ne. A nan ya sama wuri yayi parking ya fito ya buda mata mota ta fito sannan ya buda boot ya dauko ýar akwatin ta ya fara ja zuwa cikin hotel din bayan ya miqa wa daya daga cikin valets na hotel din key din motar sa dun ya gyara mai parking.
Suna isa reception dun hotel din wata receptionist baturiya ta tarbe su cike da murmushi.
“How may I help you sir?” Ta tambaya Mr Yates.
“A reservation was booked by my boss for this beautiful miss here”.
“I see, name please?”. Ta tambaya.
“Laylah”. Ta ansa a sanyaye.
“Surname?”.
“Laylah Jaan, just that”. Laylah ta ansa da murmushi.
“Just a sec please” receptionist din ta fadi. Ta dau kaman minti biyu tana dube dube a computer kan ta miqo masu key gami da fadi “enjoy your stay at Castle hotel”.
Bell boy Mr Yates ya samu ya hadashi da akwatin Laylah sannan ya mata sallama tare da fadi mata saqon boss dinsa.
“Boss says he’ll meet you in 2 days time, i’ll come by tomorrow to transport you to his guesthouse. For now enjoy your stay here and call me incase you need anything”. Ya fadi tare da miqo mata wata zandareriyar waya wanda ya saka number dinsa a ciki.
“A gift from boss” ya fadi a lokacin da yike miqa mata wayar. Ta dan saki ýar murmushi kan tayi masa sallama ya wuce. Har kofar dakin wannan bell boy din ya kai ta ya ije mata jakarta a ciki kan ya juya ya wuce. Da gudu ta fada kan qatuwar gadon da ke bedroom din suite din tana tsallen murna. Da hanzari ta dauko wayar da Mr Yates ya bata tayi dialling wani number.
“Yasmeeeeeeeeeeeenah”. Ta fadi a cikin murya me qarfi.
“I’m in Australiaaaaaaaa”. Ta kuma fadi cikin murna. A haka dai suka ci gaba da hira da wadda ta kira. Can kan ta kashe wayar sai Yasmeenah tace mata bara ta bata wani albishir.
“Albishirin ki”. Yasmeenah tace
“Goro”.
“Menene tukwuici na?”.
“Duk abunda kike so”.
“Kin tabbata?” Ta tambaya Laylah tace ehhh.
“Khalifa Al-Haydar is in Australia”. Ta fadi da dan karfi.
“Ki bar wasa”. Laylah ta fadi tana daka tsalle. “Yes yes! Wannan karan sai na ci ma burina”. Ta fada cike da murna.
“Yanzu dan Allah Jaan don’t fall my hands. Make sure you get that dude”.
“Trust me Yasmeenah”.
“Yanzu mu koma ga tukwuici na”.
“Na san me zaki tambaya, let me save you the trouble. The Benz is all yours”. Ta fada. Cike da murna suka yi sallama da Yasmeenah ta katse waya ta ta tashi ta wuce ban daki don yi wanka. Wanka tayi ta dauro alwala. Bayan ta gama sa kaya ta shimfida sallaya ta kabbara sallah. Ta dade a zaune tana addu’a kan ta miqe ta ninke sallayar sannan ta hau gado dun ta huta amma duk taji ta kasa barci saboda tsananin murna.6
Ta dade tana baibayar Khalifa Al-Haydar amma bata taba saa ba. A duk lokacin da aka ce mata yana wata qasa da taje zata samu labari ya bar qasar zuwa wata sai kuma gashi yanzu cikin sanyi ta sama kan ta a qasa daya dashi.
“Insha Allah bazan koma gida ba sai na ci ma burina. Sai na nemo Khalifa Al-Haydar, he has to see Laylah Jaan work her charms” ta fadi a fili.
☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆
Na san a yanzu masu karatu na cike da tambayoyi da yawa gami da rayuwar Laylah da manufar zuwan ta Australia. Na san kuma kuna so ku san wanene Khalifa Al-Haydar. The story is boring koh? Just keep calm and follow me. I promise you’ll never regret reading Jirwaye!Kiran sallan subh ne ya tayar da shi daga barcin sa. Yana tashi zaune azkhar ya fara kan ya miqe ya nufi ban daki. Sai da yayi wanka, ya wanke baki tukun ya shimfida sallaya yayi sallah. Yau be fita zuwa masjid ba a dalilin tafiyar da ke gaban sa. Yana idda sallah ya hau kan arranging box inda zai yi tafia dashi. Be huta ba sai da ya gama hada komi tukun. Sake shiri yayi cikin kaya masu kyau, ya fesa su turare da sauran su tukun ya wuce sitting room inda ke part dinsa ya dau laptop dinsa ya hau kan danne danne.+
Jim kadan sai ya ji motsin mutum ya buda kofar dakinsa ba tare da tambayar permission ba. Kanshin turaren da ya daki hancinsa kawai ya sanar dashi waya shigo.
“And here comes the lady before my heart”. Ya fadi ba tare da ya dago kai ba daga laptop dinsa.
“Ya akayi ka san ni ce?”. Ta tambaya bayan ta zauna kusa dashi.
“How can a son not recognise his mother?”. Yayi murmushi gami da dago da kansa ya kalli mahaifiyar sa. Kamar yadda ta saba a Kullum, yau ma tana sanye da kaya masu kyau, kayana alfarma gata dama da jiki me kyau. A Kullum tamkar kara kuruciya take, kwata kwata ba alaman tsufa a tare da ita. Murmushi tayi ta jawo danta jikinta.
“Khalifatullah….” Ta kira sunansa kamar yadda ta saba kira a cikin murya me sanyi “Do you have to have go? Ni kwata kwata hankali na be kwanta da wannan tafiyar taka ba”.
“Look here begum, you know I’m doing this for you and I. For both of us right? I promise zan kiraki each and every day and I’ll be back in no time. Ina gama abunda ya kaini zaki ganni gida”.
“Alkawari?”.
“Cikawa” ya fadi yana murmushi.
“Toh tashi muje kayi breakfast na kai ka airport. I know how hot headed you can be, don’t say no”.
“No begum, kema kinsan we can’t be seen together koh, i’ll take a bus”.
“Khalifatullah…..” yayi saurin rufe mata baki kan ta ce komi. Yayi amfani da dayan hannunsa ya share mata hawaye.
“Ba yaro bane ni, na san hanyar gida. Zan dawo I promise”.
“Shikenan, Allah yayi maka albarka da na”. Ta riqe hannunsa zuwa kitchen inda tayi serving dinsa abinci. Ta zauna ta basa da kanta a baki har sai da yace ya qoshi tukun ta daina bashi. Zata tashi ta wanke hannun ta ya zaunar da ita.1
“It’s now my turn to fulfill my obligation towards you”. Ya fara bata abinci yadda ita ma ta basa a baki. A duk lokacin da Khalifatullah ya ciyar da ita, wani irin murna mara misaltuwa ke rufe ta. A Kullum son dan ta kara cika mata zuciya yike ga kuma alfahari da take yi da shi a Kullum sai dai kuma rayuwar yaron nata na matukar bata mamaki, yadda yike tafiyar da alamuransa da kuma irin saukin kai da Allah ya basa.
Gama bata abinci yayi sannan ya kwashi plates din ya wuce dasu sink suka wanke hannun su yace bara ya wanke plates din ta hanasa.
“You’ll miss your flight”. Ta fadi tare da tura sa zuwa dakinsa ya shirya. Wucewa yayi ya sake kaya zuwa wani sweatpant da dan hoodie dinsa saboda yanayi weather ana dan sanyi. Bayan ya gama shiri ya fito yana jan ýar jakarsa. Yayi sallama da mamansa.
“Do give Hisham the keys to the apartment okay”. Ya fadi tare da kissing goshin maman nasa wadda har wannan lokacin tana cikin jimamin tafiyar da dan nata zai yi.
“Beguuuuum……. come on. Wannan fa ba shine karo na farko da nike tafia ba, i’ll be okay I promise”.
“I’ll miss you son”. Ta fadi “You sure you don’t want me to drop you off at the airport?”.
“Aah, i’ll be fine”. Da kyar dai Khalifatullah ya iya sallama da mamansa ya ja box nasa ya wuce bus station inda ya sama drop na taxi har zuwa airport. Ba tare da bata lokacin ba ya shiga queue duk ya gama formalities na airport. Yana shiga jirgi aka yi directing dinsa zuwa seat nasa ya sama wuri kusa da window ya zauna. Can ya daga magazine da akan ije ma passengers a jirgi ya fara dubawa har barci yayi awon gaba dashi kasancewar a daren jiya be samu isasshen barci ba. After what seemed like forever, Khalifatullah ya farka daga barcin da yike, hasalima fitsari da ya riqe sa ne ya tayar dashi daga barcin. A lokacin ne ya lura har jirgin su ya daga. Juyawa da zai yi, idanuwansa suka yi ido hudu da seat mate dinsa. Mace ce wadda a shekaru ba zata wuci shekara ashirin da hudu zuwa da biyar ba haka. Be tsaya kallon ta ba da kyau ya dauke idanunsa a kanta. Shi ya kasance mutum ne me matukar kunyan hada ido da mutane tun bare ma mata. Duk yadda yike da son wasa da barkwanci, da wuya ya kalli mutum cikin ido bare ma har ya tsaya kallon mace.
“Hello” kawai ya fadi ba tare da ya kuma kallon gefen ta ba ya miqe dan ya nufi washroom ya biya buqatan sa. Har ya dan fara tafia muryar ta ya tsayar dashi. Cikin wata murya tayi maganan, cikin bacin rai.
“Malam koh dutsen da ka taka bata ji maka ciwo ba”. Maganar kwarai da gaske ta dan sosa ran sa saboda irin muryar da tayi amfani dashi ba wai dun ya gane gatsen da ta mai ba kasancewar ba wata isasshiyar hausa yaji ba.
‘Even begum doesn’t use that tone on me’ ya fadi a ransa amma a fili sai ya maida mata da ansa me cike da tsokana. “Dutse kuma baiwar Allah? Koh dai shigar ki jirgin sama na farko kenan” ya fadi gami da tuntsurewa da dariya ganin maganar ta da da bata mata rai.
Wata tsaki yaji ta saki shi kam koh a jikinsa ya wuce washroom yayi fitsarin sa ya fito sai dai yana iso wa seat dinsa yaga hajia almasifatu ta koma seat dinsa wanda ke kusa da window ta zauna. In zaa bi gaskia, Khalifatullah ya san seat din nata ne but shi kuma a gaskia ya fi son window seat don haka yazo yace mata alambaran sai dai ta tashi ita kuma ta qi sai ya rabu da ita amma a zuci ya quduri niyyar sai ya koma seat dinnan kuma true to his word, haka aka yi. Sai da ya sa ta tashi daga seat din ta bar mai.
‘What Khalifatullah wants, he gets’. Ya fadi a zuci cike da murnan korar ta daga seat din baki daya dama shi mutum ne wanda ya tsani zama kusa da mata. Kwata kwata baya so abu ya hada sa da mata dun sha’ani dasu nada wuyan gaske kuma sai me haquri.
Da isan su qasar Australia ya shiga ya sanja kaya kafin ya fito ya nufa arrival lounge na airport din. A lokacin ne ya tuna da ipad din seat mate dinsa a jirgi wanda yike tare dashi.
“Shit! Where the hell do I start looking for her”. Ya fadi tare da jan ýar tsaki. Nan dai ya fara dan tafia yana sa ido koh Allah zai hadashi da ita. Yana cikin tafia ya ji an tabo sa daga baya. A zaton sa, koh ita ce ta gansa ta biyo sa dun ta karbi ipad dinta amma yana juyawa yaga ba ita bace.
Nawfal ne, amininsa kuma cousin brother dinsa. Kan ya ankara ya jawo sa zuwa jikinsa yana hugging dinsa cikin murna. “Man I missed you”. Nawfal ya fadi.
“I’ve missed you too”. Shima ya fadi cikin murna. Bayan gaisuwan yaushe rabo, suka fara takawa zuwa parking lot Nawfal na jawo dan trolley din Khalifatullah har su isa inda yayi parking motar sa.
“Mamu doesn’t know you’re in Australia, does he?”. Nawfal ya juya ya tambaya dan uwansa.
“No, I’m here for some work. I’d love to be uncovered for a while. Zan maka bayani in na huta”. Ya fadi ma Nawfal wanda har ya jawo hadaddiyar motar sa me qirar chevrolet camaro sun hayo kan titi. Can jim kadan, Khalifatullah ya fito da wannan ipad din luckily for him kuma ipad din baya da password koh pattern dun haka swiping kawai yayi sai ya bude. Nan da nan ya fara buga game din candy crush can kuma yaji kawai wata zuciya tana raya mai da ya shiga gallery dinta.
☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆
Barka jama’a….. how are we finding Jirwaye? Still boring aye. Kada ku damu, the story is just starting, like I said you won’t regret reading this story. That I assure you. Nasan hausan akwai mistakes da yawa, feel free to slid into my dm to correct me. Godia lodi lodi.
Maza ne kimanin su ashirin, duk sanye da suits suna zaune shuru a boardroom. Jefi Jefi suna dan kuskus da juna. Can kamar after minti goma sai ji suka yi an buda kofar boardroom din. Maza ne kosassu guda biyu suka fara shigowa kamun wani namiji sanye da suit na alfarma, da gani kasan ba karamin mutum ne zai iya affording wannan kalar suit din ba, domin limited edition designer suit ne na Giorgio Armani. Tsam duka mazan nan suka miqe ganin ya shigo ana ta gaida sa, wani bature ne dan dattijo ya fara nufo sa cike da fara’a.1
“Welcome sir”. Ya gaida shi “I’m glad to have finally met you. I’m the new managing director of khalif constructions, the Amsterdam branch actually”. Ya fadi. Murmushi kawai ya mai suka sha hannu kamun ya wuce ya zauna a kujerar sa ta alfarma, kujerar CEO. Sai da aka gama setting din smart board inda ke dakin, sannan duk mutanen da suke zama aka miqa musu wani file aka kuma umurci kowa da ya kunna computer dinsa tukun ya buda baki don yayi magana.
“Where’s Al-Mubaraq?”. Yayi maganar cikin wata sanyayyyar murya gami da kallon kujerar da ke facing dinsa directly, kujerar overall director din khalif airlines and group of companies. “Tariq? You heard me I believe”.
“Ye.yes… yes si.. sir”. P.A dinsa me ansa suna Tariq ya ansa cikin inina. “I sent an email to everyone you asked me to”. Ya ansa.
“Then why is Al-Mubaraq not here?”. Ya kuma tambaya amma kowa yayi shuru “Find out what’s wrong”. Ya umurci P.A dinsa.
“Yes sir”.
“Now!”. Ya kuma fadi wannan karan cikin murya me dan karfi. “Gentlemen I greet you all”. Ya fadi, huskar sa a hade ba alamun dariya koh murmushi. “As you all know I meet with all managing directors of this mighty group of companies every 6 months but I had to set this meeting up 3 months to the initial time for the meeting”. Ya fadi kamun ya tsaya gyaran murya sannan ya gama kallon faces din duk wanda suke gun.
“Embezzlement of this company’s money has been going on and the culprit or culprits i’m sure are here amongst us. A great chunk of money has been stolen and we don’t know how, when, where or by who”. Ya fadi. Ji kake mutanen da ke gun suna dan kananun surutu tsakaninsu.
“How much precisely are we talking about here?”. Khalid Shuraim, managing director din branch in Saudi Arabia ya tambaya.
“50,000 U.S Dollars. About 67,500,000,000 Saudi Riyals. That’s 18 billion naira in Nigeria’s currency”. Be gama fadi ba kowa ya buda baki cikin mamaki. Hakika kudi da aka sace ba kudade bane kananu. Dole a dau mataki. A nan meeting dai ya dau zafi, kowa na presenting progress din branch inda yike, ana nuna profit and loss chart na businesses din company din. Bayan kaman awa uku, aka gama meeting.
“We all meet in 3 months time insha Allah. I’ll have my P.A send the venue of the meeting to you all. Gentlemen, have a nice day”. Ya miqe yayi waje, bodyguards nasa suna biye dashi a baya. Wani tsararran office ya nufa, da isowarsu kofar daya daga cikin bodyguards nasa ya buda mai kofa ya shiga su kuma suka tsaya a wajen kofar. A hankula ya dinga takawa har zuwa kujerarsa ya zauna. Sai da ya sama ýan mintoci kadan ya na dan nazari kan ya buda computer inda ke gaban sa amma duk da haka ya sama kansa da rashin concentrating akan aikin da ke gaban sa, duk tunani ne iri iri suke ta yawo a kansa. Dago kai yayi ya qura idanunsa a kan qaton enlargement inda ke ije a office dinsa. Wata ýar murmushi ya saki tare ta miqewa ya nufi inda wannan enlargement yike.
Ya dauki lokaci yana kallon hoton kan ya dan shafa Jikin hoto. “I’m the man you’ve always dreamt for your son to become right? Na mijin zaki, a man like you… Mohammed Mumtaz Al-Haydar”. Wanda ke hoton nan dai ba kowa bane fa ce mahaifin sa wanda ya rasu kusan shekaru goma da suka wuce. Shekarar nan ta kasance me tsananin wuya a garesa kasancewar koh shekara mahaifin sa be yi ba da rasuwa ya rasa Fatima, matar sa wacca ta mutu a gun haihuwa.
Tuno wa yayi da Fatima da irin rayuwar auren da suka yi. Duk da auran su ba aure bane wanda akayi sa akan so, sun zauna cikin haquri da juna da kuma kwanciyar hankali. A lokacin da son Fatima ya fara shiga zuciyarsa, lokacin mutuwa ta raba shi da ita. Har yau ba ya iya mance randa ya rasa Fatima 8 years ago……..
“Mace ce”.
“Na ce maka namiji ne!”.
“Mace”.
“Na miji!”. Ta fadi cikin bacin rai “Cikin ba a jikina yike ba. Ni nasan na miji zan haifa”.
“Haba habibty.,… i’m sorry. We’re having a boy insha Allah. Daina hushi”. Ya rarrashe ta.
“Yawwa habibi na, ko kai fa”. Ta saki wata murmushi, irin wanda ke sanyaya zuciyarsa, wanda a duk lokacin da aka basa haushi a office da ya dawo gida ya kalli wannan murmushi a huskar ta sai yaji duk wannan bacin ran nasa ya tafi. A Kullum gode wa Allah yike yi da kuma Abban sa da yayi arranging auran sa da Fatima.
“We’ll name our son muhammad Fadeel insha Allah” ta katse mai tunani. Murmushi yayi ya jawo ta kusa da jikinsa.
“I thank Allah each blessed morning for making you mine”. Ya fadi tare da sumbatar goshin ta.
“So now it’s settled, isn’t it?”.
“What?”.
“We’re gonna have a boy and he’ll be Muhammad Fadeel”.
“Such a party pooper, ko Kice mun you love me too”.
“Toh fa kai kace na daina karya ba kyau”. Ta fadi cikin tsokana.
“Kenan baki so na?”.
“Yo ehma….”. Ba ta gama magana ba ta ga ya miqe cikin hushi ya wuce bedroom ya barta. Ýar dariya tayi kan ta miqe ta nufi bedroom din ita ma “Habibi” Ta kira shi cikin muryar ta me sanyi amma sai yaqi kula ta. Ta matso kusa dashi ta zauna amma sai ya share ta ya juya yayi kwanciyar sa.
“Haba habibi… qalbi na, kaima ka san duk duniya ba irin ka a gu na. Sanyin idanu na, tauraro me haske zuciya ta, abun alfahari na a ko da yaushe, uban ýaýa…..”. Bata kai ga gama magana ba taji ya janyo ta jikinsa.
“You’re killing me with your words” Ta ji ya fadi hawaye masu dumi suna sauko wa daga idanunsa.
“Why are you crying?”.
“I’ve never felt love like this before. Never leave me please zahra”.
“Shhh mutu ka raba nida kai insha Allah”. Gyara kwanciya tayi a jikinsa suka dade a haka kan can tace mai su fita.
“Please please please let’s go do some shopping and stop by the new ice cream place”.
“Amma fa doctor yace ki rage shan kayan sanyi fa. Can’t we just stay like this, I enjoy cuddling with you”.
“Pleaseeeeeeee mana, Kaga I promised Aryaman zan siya mai birthday present kuma gobe ne. Kaima ka san I won’t breathe in ban siya mai abu ba. Kaji habibi”.
“Toh ya na iya dake. Ni kawai jikina yana mun wani iri ne, i’m having a bad feeling”.
“Kayi ta azkhar, Allah na tare da mu insha Allah”.
“Toh bara na watsa ruwa na zo”. Yana shiga bandaki ita ma ta miqe ta sanja kaya zuwa wata doguwar riga mai kyau wadda tayi matukar mata kyau dama kuma gashi ciki ya an she ta. Cikin ta ya fito dan madaidaici dashi dan in mutum ya gani ma bazai taba zaton ya kai wata bakwai ba.
Shima yana fitowa ya sa ýar tshirt da wando ýar three quater suka fito yana riqe da hannunta. Sun shiga mota kenan zaya tayar da motar ta dakatar dashi.
“Me nene kuma yanzu?”. Hugging dinsa kawai yaji tayi tare da fadi mai “I love you, in all situations. Come what may always know that I love you, with my whole being”. Ji yayi ta kashe mai jiki da kalaman ta.
“Why is my wifey being sweet all of sudden?”, ya tsokane ta kan ya yi starting mota, Idi me gadi ya buda musu kofa, nan ma kansu fita ta ce ya tsaya tana so ta dan zanta da Idi. Kwarai da gaske Fatima ta daure me kai yadda take ta abubuwa a ranar.
▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪
Hmmmmm koh me ke samun Fatima, Allah a’alam. Duk me son sani ya biyo ni a next
Sai da tazo fita da nufi zuwa sightseeing tukun ta tuno da ipad dinta. Nema take ta yi cikin kaya kan can after some minutes ta tuna ai ta mance sa a jirgi.+
“Damn!” Ta fadi gami da jan ýar tsaki dun takaici. Akwai abubuwa da yawa masu muhimmanci a gun ta da suke cikin wannan ipad din. Cigaba da shirin ta tayi ta saka wata jacket baqa me kyau da wando wanda ya dan matse ta sannan ta sa wasu boots masu kyau, ta dauko dan karamin veil baqi ta rufe baqin gashin ta wanda sai kyalli yike ta yi saboda tsananin kula da kashe kudi da ake yi a kan shi.
Waya ta dauka ta kirawo Simon dun yazo ya kai ta ganin gari tunda dama shine driver dinta wanda zai dinga tuqa ta iya zaman ta a Australia wanda be wuci na 2 weeks ba. Baa yi 15 minutes ba ya kira ta cewa ya iso harabar hotel din. Ta katse wayar ta saka a cikin wata ýar suspender tare da wallet dinta da sauran necessities dinta sannan ta jawo babban box inda tazo dashi saboda daga ganin gari ba zata dawo hotel ba. Special guest house din Senator zaa kai ta. Tana gamawa ta dan fesa turare sannan ta fita tana taku a tsanake kamar me tausayin qasa.
Mr Yates na hango ta ya nufo ya ansa box din ya cigaba da ja har zuwa inda yayi parking mota.wata mota ce hadaddiya, ta taka wadda ya dauko ta daga airport dashi.
‘Lallaima, senator babban mutum ne. Na ko yi babban kamu’ ta fadi a cikin zuciyar ta gami da sakin wata ýar murmushi a fili.
Laylah dai ýar budurwa ce me tashe, wadda bata wuci shekara 24 ba da haihuwa. Tsayawa kwantata irin kyau da figure inda Allah ya mata bata lokaci ne, ga muryar ta wata sanyayyya da ita, irin muryar nan me sa me gida lattin office, ga manya idanu Masha Allah. Gashi kam har gadon baya, ga skin din ta irin wanda bature kan kira flawless, ba spot koh daya gashi da laushin tsiya wane fur din mage, tana da dan haske iya gwargwado ga farin jini a gun samari. Laylah dai kawai full package ce. Karya ne namiji ya mata kallo daya ya wuce, sai ya dago ya kuma kallon ta.
Shiga motar tayi ta zauna shuru a gidan baya shi kuma Mr Yates ya zauna a seat din driver ya fara jan mota. “should we start with the museum?”.
“No, take me to a park”. Ta fadi.
Cikin dan qanqanin lokaci suka isa wani qayataccen park wanda yike cike tam da mutane, ga yara suna ta wasa da guje guje. Masu sai da snacks da ice cream duk gasu nan ana ta musu ciniki, harta masu sai da abinci ma duk gasu nan. A hankula take tafiya tana wasa da wani dan fure da ta tsinka. Wasu tsoffi biyu ta hango, turawa ne su kuma daga ganin su mata da miji ne. Zaune suke a wani carpet mijin na ba matar abinci a baki ita kuma tana ansa. Jin wani abu tayi a zuciyan ta kallon wannan tsoffi guda biyu, gasu dai sun tsufa tukub amma basu daina so da kula da junan su ba. Ta dade tana kallon su cike da shaawar rayuwar su.
“I wish”. Ta fadi gami da dan lumshe ido kan ta cigaba da tafia tana tunanin koh zata taba iya samun masoyi wanda zai so ta, yayi accepting dinta a yadda take har suyi aure su tsufa tare. Tana gaba kuma kadan, wasu couples ta hango da dan su wanda bazai wuci shekara daya da ýan watanni ba. Tafia suke riqe da hannun juna, sun sa dan yaron a tsakiyarsu. Can sai yaron ya balle ya rugo da gudu iyayen na biye dashi suna dariya, shima yaron dariya yike. Kawai bata ankara ba taji an auko mata, an riqe kafafun ta. Dan yaron nan ne da ke gudu.
“What’s your name?”. Cike da murmushi ta miqa mai hannayen ta biyu ta dago sa zuwa jikinta.
“Bubble” ya fadi yana dariya ita kuma sai wasa take da gashin sa mai laushi.
“Your name is bubble?”. Ta tambaya tana dariya.
“Bubble!” Ya kuma maimaitawa. Kan ta buda baki tayi magana taji muryan maman yaron ta katse su.
“Owen! You naughty kid”. Yana juyo wa ya kalli mamansa ya fashe da dariya. Ita kuma Laylah ganin mahaifiyar sa ta miqa mata danta. Cikin fara’a ta anshe sa.
STORY CONTINUES BELOW
“He’s a cute kid” ta fadi kan ta mai waving hannu ta wuce. Wuri ta je ta samu ta zauna shuru bayan ta siya cold drink. Ta dade a zaune tana nazari iri iri. Kallon wasu ýan yara, ýan mata biyu suna wasa abun su ya sa ta tuna gida, ta tuna da Auta. Bata san lokacin da hawaye ya fara sulalowa daga idanunta ba sai ji kawai tayi an kamo hannun ta an ije mata abu a ciki. Hannun ta fara dubawa taga hankie aka ije mata kan ta dago idanu domin ganin me karambanin da ya riqo mata hannu har ya sa abu a ciki. Sai dai me zata gani? Tana dago kai suka yi ido hudu da wannan mara hankalin mutumin wanda ta zauna dashi a jirgi.
“You!” Ta fadi da dan qarfi.
“Na tsani naga mutane suna kuka, barin ma ýar budurwa kyakyawa”. Ya fadi yana mata murmushi.
“Malam ina ruwanka dani”.
“Ai ga irin ta, ka taimaki mutum amma ya watsa maka qasa a ido”. Ya fadi ya tuntsure da dariya.1
“You always love making jokes out of people, don’t you?”. Ta fadi tana share hawayen idanunta da hankie inda ya bata.
“Whenever distressed, remember Allah and say Alhamdulillah. You’ll feel okay”. Ya fadi ba tare da ya Kalle ta ba ya miqe. Har ya fara tafia ya juya da nufin mata magana “Can I get your address?” Ya tambaya.
“Why?”.
“Kin mance ipad dinki a gu na”.
“Koh dai ka dauka mun ipad ba da izini na ba har na mance sa a gunka ba”. Murmushi kawai yayi be ce mata komi ba “Jk guest house” ta fadi mai sunan guest house din Senator inda nan ne sabon masaukin ta.
“Okay, I’ll drop it by tomorrow”. Ya fada ya cigaba da tafiyar sa. Tafia kawai yike amma hankalinsa baya jikinsa. Fuskar ta kawai yike tunawa, hakika wannan baiwar Allah sa bai tambaya sunanta ba kyakyawa ce. Mace daya ce kawai ta taba sa shi yaji abunda yike ji a zuciyar sa yanzu, ya kasa gane me ke faruwa dashi. Har ya isa inda ya bar Nawfal tunanin ta kawai yike yana Fuskar ta, yadda ya izza ta tana kuka. Duk da dai kuka take, Fuskar ta ba wata walwala sai da tsananin kyaun ta ya bayyana.
“KHALIFAH!”. Nawfal ya kira sunansa da karfi “Tunanin me kake haka?”. Khalifa ya dan sosa kan sa yayi murmushi kan yace me ba komi.
“Kai dai fadi gaskia”.
“Nace ma ba komi, wani abu kawai na tuna”.
“Chuchu wanted to talk you in the morning amma nace baka kusa”.
“Shine baka fadi mun ba tunda na dawo” ya dan bata rai.
“Kayi haquri, na mance ne sai yanzu na tuna”. Khalifa be ce komi ba ya fara laluben tablet dinsa dun ya kira chuchu’n sa.
Ita kam Laylah zama tayi shuru, tana ta tunanin wannan mysterious man din wanda da farko zuciyar ta ke cike da tsanarsa sabida abunda ya mata a jirgi amma kuma yanzu take jin zuciyar nata na wani irin bugu duk sanda ta tuna abunda ta kankama tsakaninsu ýan mintoci da suka wuce. Dago hankie inda ya bata tayi ta kai hanci, wani kan shi ne me dadi yayi welcoming nostrils dinta. Kanshin shi ba mai karfi ba sosai sai wani dadi da sanyi sanyi da yike dashi.
Har zuwa yamma sosai tana park din, sai da mutane aka watse sosai kan ita ma ta miqe lokacin Simon ya zo daukan ta, ta shiga mota suka wuce. A cikin motan ne yike fadi mata ai senator na can yana jiran ta dun ya gama duk meetings inda yike dasu.
“Lay lay Laylah!”. Senator Junaidu ya dinga waqa da sunanta a lokacin da suka isa guest house din.
“Haba baby, sai yau ka tuna ni”. Ta dan tabe baki cikin shagwaba.
“Haba Laylah na kema kinsan Kullum kina cikin raina, ban samu zama bane tunda na zo Australia gashi wancan addababbar matar ta nace sai ta biyo ni, sai jiya na samu na sha iska bayan na sa ta a jirgi zuwa dubai”. Ya mata bayani “kiyi haquri kinji sweetheart”.1
Ita kam kallonsa take cike da mamakin yaudarar ďa namiji. Addababbar matar nan da yike magana ba kowa bane fa ce matar sa, Uwar ýaýansa wadda ta zauna dashi tun baya da komi har ya iso matsayin da yike a yau. ‘Lallai namiji ba dan goyo bane’ ta fadi a zuciyar ta.
“Kiyi haquri mana. Karki bari Baraka ta hada mu rigima”.
“Amma ka iya biya mata kudi zuwa Dubai bayan ni tun yaushe nike ce maka ina son zuwa Dubai”. Ta fadi rai a bace shikuma senator ya matso kusa zai rungume ta amma ta ja da baya.
“Haba Laylah, kar muyi haka mana. Dubai ne dai kike son zuwa Ince? Zaa samo miki visa, Karki damu”.
“Da gaske” ta fadi tana dan murmushi.
“Na taba miki wasa?”.
“Aah baby na. Allah ja zamani”. Ta fadi gami da kissing kumatun sa.
“Yau dai special package zaa bani koh”. Ya fadi yana dariya.
“Yanzu dan visa inda zaa mun na Dubai shine kake son special package. Lallaima senator, kaima ka san special package din Laylah Jaan kudin sa daban yike. Ai visan Dubai na ban haqurin share ni da kayi ne”.1
“Wallahi koh Baraka bata mun wannan iya shegen”.
“Toh ai Baraka kace, ni koh Laylah ce, yarinya son kowa qin wanda ya rasa”. Ta fadi tana neman jan jakarta “kace ma zuwa na bayi da wani amfani, sai kaje Baraka ta baka special package din”.
“Haba, yaa ki dawo. Yaushe ma zaki hada package dinki da na Baraka, mata sai qiba duk ta cika wuri kamar wata bull dozer. Koh dan kiss nace ta mun sai tace wai ita kunya, har yau ta kasa waye wa, kayan takaici. Yi haquri ki zauna baby”, ya jawo ta ta zauna a kan cinyar sa. “Karki damu, zan rubuta miki cheque na 6 million, yayi koh?”.1
“Toh ya na iya, I will just manage. Baby baby kenan” ta fadi tana dan manna mai kisses a Jikin sa. Tsam ya daga ta suka shiga daga cikin bedroom ni ko aka yi slamming door a Fuska na wai na cika kwakwaf😢😢.1
Wannan ita ce rayuwar Laylah Jaan….. rayuwar karuwanci, rayuwar bin mazan wasu, maza masu hannu da shuni a qasa; manyan ýan kasuwa, ýan siyasa da dai sauran masu kudi. Laylah Jaan ta kasance burin duk wani mutum wanda ya mallaki kudi da suna.
▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪
Hmmmmm ni har jikina yayi sanyi wallah. Koh ya aka yi Laylah ta tsinci kanta a cikin wannan mummunar sana’a oho, sai kun biyo ni a labarin tukun zaku sani.