JIRWAYE CHAPTER 12
Www.bankinhausanovels.com.ng
Cike da tsoron abunda Begum zata fadi Nawfal ya daga wayar amma koh da ya daga, sai muryar Ameerah kanwar sa yaji.+
“Meerah? What are you doing with Begum’s phone?”. Abunda ya fara tambayar ta kenan.
“You have to come home immediately”. Ta fadi, da kaji voice dinta ka san kuka take “Begum had a heart attack, we’re at the hospital”. Miyau Nawfal ya hadiye yana kallon khalifa dan ya san ba kadan ba, he’ll be devastated in yaji abunda ya faru.2
“How’s she? Ya tambaya.
“In a critical condition. Tun dazu take ICU. No one’s saying anything”.
“Okay, okay keep calm. First thing tomorrow morning zamu dawo Abuja okay”. Ya fadi yana kashe wayar sa. Dago kai yayi ya kalli khalifa before breaking the news to him. Ganin yadda expression din khalifa ya sanja lokaci daya yayi. Miqewa yayi bayan yace wa Nawfal ya wuce ya hada kayan sa.
“But dare yayi khalifa”.
“I don’t fucking care! Get your things ready”. Ya fada kan ya sauka yana kwalawa Tariq kira. Yana fitowa ya fada masa cewa shima ya shirya sannan ya kira pilot dinsu, he didn’t care what time it was, shi dai a maida sa Abuja a daren. Dakinsa ya wuce ya sa wani simple Yankee joggers da black tee shirt ya fito, lokacin both Tariq da Nawfal duk sun gama shiri. Gaba daya hankalin khalifa yayi gida, yama mance da wata Laylah bare ya fadi mata abunda ya faru. Sai da suka yi landing a Abuja tukun ya tuna kwata kwata he didn’t inform her. Ya so ya kirata amma kuma sai yaga it was too early sai ya bari kawai.
Straight hospital suka yi inda suka tadda Ameerah da Saima zaune shuru. Ameerah ce ta fara dagowa ta gansu, daga ita har Saima duk tiredness was written all over their faces. Saima na hango Nawfal ta miqe kawai without thinking much about it ta fada jikinsa ta fashe da kuka.
“She’s in a bad state”. Ta fadi hawayen ta na sauka kan shirt dinsa. Shi dai khalifa koh ta kansu be yi ba, straight office din doctor ya wuce dan samun bayani.
“Shhhhh everything will be alright insha Allah”. Ya rarrashe ta. Khalifa ya dade a office din doctor din kan ya fito. Duk yadda suka so da a bar su su shiga su ganta an hana, dole suka haqura. Gari na wayewa sosai Nawfal ya hada su Saima with Tariq a maida su gida su huta because they all were exhausted tun bare ma Saima who had faced alot that week.
Da ya gaji da kai komo a corridor din ICU ward din, zama ya dawo yayi a kujerun da aka jera by the corridor. Nawfal ne yazo ya zauna kusa da shi ya miqa masa coffee.
“Here, have some coffee”. Sa hannu yayi ya karba ya fara kurba a hankula, none was uttering a single word. Tired of the dead silence which filled the ambience, Nawfal ya fara humming wani old song wanda suke yi tun suna yara.
“I have a joy in my heart….
And it’s because my Maamah loves me…”
Juyawa khalifa yayi ya kalli Nawfal with amusement. Memories din childhood dinsu ne kawai ya fara flooding mind dinsa. The first time Nawfal and his sisters moved in with them after the death of their mother wadda sister ce a gun mahaifin khalifa. Tuna lokacin da Begum would always sing that song to them kawai yike ta yi.
“I have a joy in my heart….
And it’s because khalifa loves me
I have love in my life
Because my Nawfal adores me…”. Haka Kullum a dinning zata ta yi musu waqan tana feeding dinsu. Begum tamkar nata ta dau Nawfal da sisters dinsa;Sarah and Ameerah. Amma kuma ta fi son Nawfal, it was too obvious. Bata taba nuna bambanci tsakanin sa da khalifa ba. Hakika ta riqe amanar Zulaikha.
“I have love in my life
Because my Begum loves me”. Dariya dukan su suka yi. Khalifa ne ya fara magana.
STORY CONTINUES BELOW
“Seriously! Baka mance ba”.
“Ta ya zan mance. That would be forgetting my childhood memories with Begum, the most amazing moments I had as a kid”. Ya fadi yana dariya. A nan suka fara recounting childhood memories dinsu, days when they were mischievous and carefree. Sun dade suna dariya, forgetting all about their sorrow for those few minutes. A cikin dariyar ne kwalla suka fara zubowa khalifa, in no time dariyar sa ya koma hawaye. Dora kansa yayi a shoulder din Nawfal who didn’t utter a word dan ya san abunda ya san khalifa kuka, sanin kowa ne cewa duk duniya ba wanda khalifa ke so kamar Begum kuma ba abunda ba zai iya yi ba for her happiness and safety. Tsananin son da yike mata ne ya sa be taba objecting to her decisions regarding his life ba sai a wannan karan da ya aura wacca bata so. Sai da yayi kuka har ya gaji kan Nawfal ya miqo masa hankie.
“Nawfal”. Ya kira a hankula “Was that how you felt? When uncle Fadoul and aunt Zulaikha left? Did it hurt this much?”. Sai da ya ja dogon numfashi tukun ya ba khalifa answer.
“No, it didn’t hurt this much. Ka san meyasa?”. Ya tambaya “Because I had Begum, I had uncle Mumtaz, and I had you. I had family, koh na rana daya baku taba bari mun ji zafin maraici ba, Begum welcomed us with 2 arms into your family and filled up the void of a mother in our lives. Bamu da abunda zamu saka muku dashi”. Ya fadi “And please stop speaking that way, we still have Begum. She’ll be okay insha Allah. Ciwo ba shine mutuwa ba”. Basu gama magana ba doctor ya fito daga ICU.1
“Mr Al-Haydar?”. Ya kira.
Koh da Yasmeenah ta leqo dakin Laylah, samun ta tayi sai safaa da Marwah take round the room.
“You should be sleeping, it’s late”. Yasmeenah ta fadi.
“I can’t. I feel restless”. Riqo hannunta Yasmeenah tayi suka zauna bakin gado ta fara tambayar ta Meya faru.
“Anything wrong? You’ve gotten Al-Haydar now what? Koh amarya ta qosa ta tare ne”. Ta fadi tana murmushi.
“No, no, not that”. Ta ja dogon numfashi “I had a very bad dream. Na kwanta barci sai na fara mafarki, I was being chased by some scary creatures, ina ta gudu suna bina har na zo end of the road. What laid ahead was a cliff, there was no way out. Kawai out of nowhere Abdulmalik appeared, he was smiling at me, I cried out to him asking for help sai ya miqo mun hannunsa which I hastily took but instead of him to save me sai yayi pushing dina over the cliff…..”. Runtse idanu tayi as the dreaming kept replaying in her head.
“Sweetheart relax, it’s just a dream. He’ll never do that insha Allah. Ki kwanta ki sama barci kin ji and pray”. Yasmeenah ta fadi kan tayi mata sai da safe ta wuce samun barci. Koh da Yasmeenah ta fita Laylah ta dade awake, har waya ta dauko tayi trying number din khalifa amma ta samu a kashe dan haka kawai sai ta fada bandaki ta dauro alwala kan tazo tayi nawafil ta kwanta barci.
The next day, tun da safe jama’ar da suka rage a household din suka tashi aka gama aiki aka shirya zuwa gidan Auta dan yin final traditional rite for the wedding. Ita dai Laylah ba inda taje, aka barta a gida tare da Ummati and a few other people. Leek ce tayi volunteering ta zauna da Laylah to keep her company. Tun da ta tashi Laylah ke jiran isowar khalifa or at least a call from him amma shuru har asr ba koh daya. Gaba daya hankalinta na kan wayar ta, minti minti ta duba koh zata ga Shigowar call or a text amma ina.
“And what’s making Mrs Al-Haydar so restless”. Leek ta fadi bayan ta zauna kusa da Laylah a karamin living room inda ke sama.
“Yace zai zo ya ganni yau amma har yanzu shuru and his phone has been off. I just hope all is well with him”. Ta fadi kamar zata yi kuka.
“Easy, easy there”. Leek ta fadi tana dariya “Ki Kwantar da hankali ki, kin dai san you married a very busy man. Yana da harkoki da yawa and kinsan dai yanzu he’ll be busy with the press, ga jama’a and all. Just chill maybe zuwa dare ki gansa”. Tayi ta Kwantar mata da hankali. Sai da ta tabbatar cewa Laylah ta saki jiki tukun ta jawo remote ta kunna TV. “Bara mu dan yi kallo. Which channel should we watch sissy”. Ta tambayi Laylah.
“E Hollywood”. Laylah ta fadi fave channel dinta.
“No wait! I remember babe told me he’ll be on TV today. Let’s watch news a bit in ga rabin rai na”. Leek ta fadi referring to her hubby wanda naval officer. Aikam suna kai wa channels TV daidai ana zantawa dashi, a haka suka zauna suna ta kallo, Laylah ma kallo kawai take ba wai dun attention dinta na kan abunda ake yi ba. Kamar ance ta karanta headlines kawai idanunta ya ci karo da news about the Al-Haydars.
“Leek look look”. Ta fadi gami da kwace remote control din from Leek tayi saurin pausing news din saboda gudun kar headline din ya wuce basu gama karantawa ba.
“Mother of rich business tycoon khalifa Al-Haydar suffers a massive heart attack after son’s unplanned wedding in Adamawa,…..”.
Basu gama karantawa ba Leek ta anshi remote din back from Laylah ta sanja channel. Koh da suka koma AIT, the news was about the Al-Haydars.
Famous business tycoon khalifa Al-Haydar ditches fiancée Saima Mohammed on wedding day.
Identity of khalifa Al-Haydar’s bride still unknown.
“News about Sahar Al-Haydar’s condition still not revealed….”. Reporter din ya cigaba da reporting news about the health of Begum to the press. “Reporting right from the Regent hospital, I am Stanley Okoro”. Dip! Leek ta kashe TV din kan ta ja dogon numfashi.
“Oh my God Leek what’s happening”. Laylah ta fadi kan hawaye ya kufce mata. A lokacin Zubaidah ta shigo a guje tana tambayar if they’ve heard what happened su ka ce mata eh. Laylah duk hankalinta ya gama tashi gashi number din khalifa baya zuwa. Sai can daga baya idea yazo mata, ta daga waya tayi dialling number din Nawfal.Koh da Nawfal ya daga wayar, cikin nutsuwa Laylah ta gaisa da shi tayi tambayar me jiki kan ta buqaci tayi magana da khalifa. Koh da ya ansa sun dade shuru ba me cewa kowa komi kan Laylah tayi breaking silence din. Comforting din sa ta dinga, tana ta fadi masa soothing words har daga karshe ta fadi masa cewa first thing the next morning zasu taho Abuja. Khalifa yayi da ita akan ta bari, kar ta damu da zuwa but she was being adamant.
“It’s my duty. Please don’t deprive me of that right. Farin cikin ka yanzu ya zama nawa, haka ma baqin cikin ka. I want to be by your side through this phase habibi, let’s face it together”. Da kyar dai khalifa ya yarda sannan ya fada mata cewar ta shirya he was going to send his private jet the next day a zo a dauke ta.
Ranar da kyar Laylah ta iya samun barci, gaba daya ta qosa next morning din yazo ta ganta a Abuja, by her husband’s side. Shiryawa duka suka yi tsaf; da ita, Yasmeenah and Leek. Private jet din be yi arriving ba sai around 4 in the evening. A lokacin suka bar yola ana ta musu fatan alkhairi. Few clothes tayi parking dan ta san ba tafiya gaba daya zata yi ba, she’ll still come back home kan a mata proper send off ceremony. Koh da suka isa Abuja, gidan Yasmeenah suka sauka. Da kyar ta yarda ta ci abinci, ta watsa ruwa ta dan huta kan suka kama hanyar zuwa The Regent hospital, a hospital which belongs to the Al-Haydar family. Hospital wanda sai dan wane da wane kawai ke iya affording saboda high standard dinsu, gashi asibitin is well equipped with first grade facilities and well qualified medical practitioners dun hospital din har turawa akwai, da Indians all working under khalifa Al-Haydar.
Koh da ta tashi barci, bathroom ta shiga ta kuma watsa ruwa kan ta fito ta sa wani A-line gown na atamfa me kyau sosai. Bata tsaya wani kwalliya ba saboda powder and kohl kawai ta sanya ma face dinta but she was still looking pretty. Waya ta daga ta kira Tariq wanda ta sama contact dinsa ne gun Nawfal. Tambayar sa tayi koh su khalifa sun ci abinci.
“Gaskia tunda muka dawo in ba coffee ba I can’t remember them ever eating”. Ya fadi mata dun haka da suka fita sai da ta cewa Yasmeenah suyi driving zuwa wani fancy restaurant su siya take outs for both men. Haka kuwa aka yi, abinci me lafia suka siya da desserts and cans of soda kan suka dau hanyar hospital din. Suna isa lobby din hospital din suka qarasa help desk suka wa receptionist inda ke wajen magana.
“Excuse me”. Laylah ta fadi cikin wata murya me sanyi.
“Yes, how may i help you ma’am”.
“Could you direct us to the special ward please”. Ta fadi. Sai da receptionist din ta dan tsaya, dumbfounded for a few seconds tana kallon Laylah as if she had just grown a second head.
“Could you come again please”.
“I said we need directions to the special ward. I’m here to see my husband whose mother is bedridden”. Ta mata bayani, dariya matar ta tuntsure mata da shi. Abun ya batawa Laylah rai but still tayi maintaining composure dinta.
“I’m sorry ma’am but you must be mistaken, only the Al-Haydars have access to the special ward, you could check your husband in the other wards”.
“Excuse me, I know what I’m saying, i’m here to see my hubby khalifa Al-Haydar”.
“What, come again”. Receptionist din ta kuma fadi tana dariya.
“Look i’m not here to joke. I need to see my husband”.
“If you’re Mr Al-Haydar’s wife then I’m Aisha Buhari”. Receptionist din ta ansa ta tana dariya. By that time haushi ya gama cika Laylah gashi ta mance wayar ta a mota bare ta kira Tariq and parking lot din was quiet far from the hospital’s main building. Suna cikin wannan hayaniyar sai Allah ya kawo Tariq.2
“Mrs Al-Haydar. Good day ma’am”. Kawai taji an gaida ta. Kallon expression din fuskar receptionist din tayi sannan tayi smirking before returning Tariq’s greeting. “This way please”. Tariq ya fadi yana karban take out boxes inda ta riqe a hannunta. Koh second glance bata yi sparing ma receptionist din ba whose expression was now apologetic kawai ta wuce ta bi bayan Tariq suka wuce. Ward din ya fi ko ina a gaba daya hospital din kyau da tsaruwa.
STORY CONTINUES BELOW
In the special ward, even the atmosphere seemed completely different. Iskan ward din had a perfumed scent and the seats by the corridor were plush, every details about the ward was very well incorporated. Everywhere seemed dustless. A nurse walked out of a room, tayi wa Laylah murmushi. The nurse was unhurried and she moved with a serene purposefulness. There were vases of flowers and beautiful framed pieces of art hung on the wall. There was a water dispenser at one corner of the ward and a split air conditioning system stood adjacent to the dispenser. Laylah gazed at him, the one person her eyes had been yearning for a sight of standing by a glassed wall by the end of the corridor. Da gudu ta qarasa inda yike tsaye tayi hugging dinsa ta baya. A hankula ta Kwantar da kan ta a bayan sa muttering the words “Habibi” in such a way that shi daya kawai zai ji.
“Zahra. Kin zo”. Ya fadi yana Juyawa. Jawo ta yayi to his arms, engulfing her in a proper embrace. “Ya kike”. Ya tambaya “I’m sorry for leaving just like that, without letting you know”.
“Shhhhh…..” Ta dora fingers dinta biyu a saman lips nasa “Say no more”. Ta fadi a hankula. Juyawa khalifa yayi suka gaisa da Yasmeenah wadda tai enquiring about the health of his mother sannan tayi Addu’ar Allah yayi restoring mata health din ta. For no reason, Yasmeenah had an unsettling feeling in her chest and she could feel the very rapid beating of her heart against her chest. Zama tayi shuru tana ta chanting “A’udhubillah minnas-shaytanir-rajim”. Bayan sun gama gaisawa sosai da Laylah yana tambayar ta mutan gida, ya riqo hannunta zuwa resting room, Yasmeenah na zaune ya mata magana cewar ta tashi su wuce resting room din tare. Har ta wuce qofar dakin da Begum take kawai taji wani mugun bugun zuciya with a very mad urge to take a few steps back and gaze at the woman laying almost lifeless in the room. Amma kuma sai dai bata sama damar yin haka ba saboda voice din khalifa da taji beckoning her. Quietly ta bi su zuwa resting room din wanda daki ne babba hadadde, an kayata shi da kayan more rayuwa iri iri, yadda kasan mutum na cikin living room dinsa a gida, har wani dan medium sized bed akwai a dakin. It’s a room specially designed for family din patients in sun zo dubiya. Koh wani section a special ward din has a resting room. Suna shiga suka izza Nawfal na waya, from all indications da Ameerah yike.
“Has she eaten?… da ta tashi make her eat, ask the chef to cook what she wants. Take very good care of her, don’t let her cry much. Zan zo gida anjima”. Nawfal ya fadi into the phone, from all indications he was speaking to his sister about Saima. Murmushi Laylah tayi masa tana waving hannunta saboda call inda yike. Cabinet in da ta hango standing next to a medium sized dinning table ta wuce ta ciro 2 porcelain plates and cups ta fara setting table din. Abincin da ta kawo tayi serving dinsu kan ta ce musu su zo su ci. Nawfal tashi yayi da sauri yana mata godia.
“Kamar kinsan i’m famished. Thanks”. Ya fadi before savouring the sweet taste of the food on his tongue. Khalifa ta kalli wanda be da niyyar cin abinci da ke gabansa.
“Eat. Please”. Ta fadi a hankula.
“I don’t want to. Begum hasn’t eaten tun day before yesterday, why should I?”.
“But habibi, you need the strength. Kana so ta farka taga ka rame ne? You know she won’t be happy. Gashi I bought all your favourite meals. Eat please”. Haka tayi ta masa rarrashi, karshe hannunta ta sa ta fara feeding dinsa. Grudgingly ya fara ansar abincin yana ci ita kam Yasmeenah tana can idanunta na kan TV amma hankalinta sam sam baya wajen.
A hankula Laylah ta dinga basa abincin yana karba, can kuma sai ya tambaye ta koh ta ci abinci ta fadi masa ta ci but he just wouldn’t hear any of it. Hannu shima ya sa ya fara feeding dinta kamar yadda yike wa Begum. Sai ji kuma yayi hankalinsa gaba ya karkata ya koma kan ta. Dogon numfashi kawai ya ja ya batse dan kar ya nuna damuwar sa gaban Laylah. After a few minutes Yasmeenah ta miqe ta wuce gida ta bar Laylah wadda suka rabu akan Tariq zaya dawo da ita gida. Ba ita ta bar hospital din ba sai around 9 khalifa yace a maida ta gida it was already too late daga nan kuma Tariq ya biya gida ya debo masa few clothes and other basic day to day necessities.
Koh da ta isa gida, everywhere was so quiet. Dakin Leek ta fara dubawa ta sama sunyi barci saboda the next day they had an early start, ita da Yaranta zasu wuce portharcourt. Wucewa dakin ta tayi ta shiga ta watsa ruwa kan ta sa kayan barci ta wuce dakin Yasmeenah. Samun ta tayi zaune a rocking chair dinta with the lights in her room all turned off except for the bedside lamps. Jingina tayi da Jikin rocking chair din ta dora hannunta daya akan forehead dinta, idanunta a rufe amma ba barci take ba, she was only lost in thought.
“Are you okay?”. Laylah ta fadi a hankula.
“Just walking down memory lane”. Ta fadi tana dan murmushi ba tare da ta buda idanunta ba “I’ve been having a very unsettling feeling lately. Why do I feel like I have a connection with the Al-Haydars?”. Ta tambayi no one in particular.
“Yasmeenah you need to open up to us. Ki fadi mana wani abu, just anything please”.
“Kuna so na fama tsohon miki. A past which I’d rather go to my grave with”.
“No, just anything please. For Leek’s sake. Yasmeenah please. Kin yi mun taimakon da a rayuwa ba wanda ya taba mun, you love me just as you love your own daughter. I want to be of help, dan Allah Yasmeenah, just anything”. Sun kai 15 minutes ba wanda yace komi kuma. Da dai Laylah ta ga Yasmeenah bata da niyyar magana sai ta miqe dun ta wuce dakin ta.
“Sai da safe”. Ta fadi a hankula.
“31st March, 1983…..” muryar Yasmeenah ya dakatar da ita.